Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   19 / 82

54K to 57K   out of 244.2K words

take shirin mallake ka, to wallahi bokanta bazai taɓa yin aiki a gidan nan ba…”

Amal ta kasa jurewa, zuciyarta ta buga da ƙarfi jin an kwatanta ta da boka, amma kafin ta buɗe baki Maleekh yayi saurin faɗin:

“Enough, Mom! Enough! bazan bari ku wulakanta min ita ba. Amal ba matsiyaciya bace kamar yadda kuke ƙiran ta. Duk wani abu da nake mata daga zuciyata yake fitowa. Kuma ki sani Mom, duk wanda ya ɗaga mata hannu, tamkar ya ɗaga mun hannu ne!”

Ammy ta ce

"And so what idan an ɗaga maka hannun? Ubanka ma ai bai fi ƙarfin a ɗaga masa hannu ba balle kai, to ka kiyaye ni..."

Maleekh ya kawar da fuska gefe ba tare da ya furta komai ba,
Ya kama hannun Amal yana ƙoƙarin jan ta ya nufi saman upstairs da ita...

Arfat ce tayi dariya tana faɗin

“Wow, lallai Amal, kin yi nasara! Amma ki sani ba wannan ke nufin za ki ji daɗin zama a gidan nan ba. Ki jira ki gani…”

Maleekh ne ya juyo a fusace ya zabga mata mari daman a gefensa take...

Arfat tinin ta riƙe fuska tana zunduma ihu...

Farha ce ta riƙe ta tana shafa mata wurin marin, tare da faɗin

"Yanzu saboda wannan matsiyaciyar zaka raunana ƙanwarka?..."

Islam kuwa hannu tasa ta toshe baki tana gusar da dariyar marin da Arfat ta sha...


Ammy kuwa dariya ta yi cikin tsaki tana girgiza kai ta ce

“Maleekh, wallahi baka da hankali. Ka je sama ka ci gaba da wawantarka, amma ka sani wannan ƴar jarida ba zata taɓa zama ‘yar gidan nan da daraja ba. Ni ce mahaifiyarka, na fi sanin abin da ya fi dacewa da kai.”

Maleekh ya juyo yana ƙoƙarin haɗiye zuciyarsa ya ce

“Mom, idan kina son darajata, to ki fara daraja ni ta hanyar daraja wacce nake so. Wannan shine karshen raini da cin fuska akan Amal a gidan nan. I won’t take it anymore.”

Ya ɗauki jakunkunan siyayya, sannan ya ja hannun Amal da ƙarfin gaske ba tare da ya sake kallon kowa ba, Maleekh ya ja Amal suka nufi sama, a wannan lokacin part ɗinsa suka nufa tare...
matakan gilashin beni mai walƙiya suna bayyana tsantsar tsadar gidan. Amal idonta akan glass ɗin benin, gani take kamar zai fashe, just a tsorace take takawa...
Kowa yana kallonsu cike da bacin rai da tsananin kishi, musamman Farha da idonta ya kaɗa saboda tsananin baƙin ciki.



✨ Part ɗin Maleekh’s Area

Bayan sun haura upstairs, Amal ta tarar da wani sashe mai faɗi wanda ya bambanta da sauran wurare na gidan. Wannan part ɗin na Maleekh yana da private sitting room (falo na musamman), wanda aka yi wa ado da farin paint da fitilun chandelier masu launin haske. A gefen falon akwai glass table mai ƙyalli, sofas masu launin grey da cushions masu taushi.
Daga gefen hagu, akwai ƙofar da ke kaiwa master bedroom ɗinsa, wanda shima ke da king-sized bed, bedsheet ɗinsa mai launin fari da launin navy blue mai kyan gaske..

A cikin bedroom ɗin akwai side ɗin walk-in closet mai cikakken shelves na tufafi da takalma da dabam..

A gefen dama kuma akwai ƙofa da ke kaiwa private bathroom, wanda aka gina da tiles masu sheƙi, jacuzzi mai faɗi, da gilashin shower room mai tsada. AC ɗin ɗakin yana busar da sanyi mai ɗaukar hankali, yana haifar da kwanciyar hankali da nishaɗi...

Da suka shigo cikin falon nasa, Maleekh ya ajiye jakunkunan akan glass table, Amal kuwa ta zauna a gefen sofa cikin nutsuwa. Duk da kukan zuciyarta da takaicin wulakancin da ta sha daga Ammy da Farha, sai ta yi murmushi mai rauni tana kallon Maleekh.

Shi kuma ya nufi bedroom ɗinsa domin rage kayan jikinsa. Tunaninsa ya cika da damuwa da fushi, amma ya daddage domin kar Amal ta ji wani tashin hankali.

Yana cikin bedroom ɗin yana sauya kaya, sai ya fito da t-shirt mai sauƙi da trouser. Amma da ya fito, sai ya tsaya cak. Amal ce akan sofa, tana kwance idanunta a rufe gaba ɗaya. Ta miƙe akan kujera tana sharar bacci cikin nutsuwa, gashin kanta ya warware duk ya zubo akan kafaɗarta...

Maleekh ya tsaya yana kallonta, Sanyin AC ɗakin ya lulluɓe ta gaba ɗaya, har take bacci cikin nutsuwa, ba tare da ta damu da komai ba...

Ajiyar zuciya ya sauƙe, ya sunkuya ya ɗauke ta a hankali cikin hannayensa kamar jaririya. Numfashinta mai sanyi yana bugan wuyansa...motsi ta fara yi tana ƙoƙarin gyara kanta a saman kafaɗarsa. A hankali ya shiga cikin bedroom ɗinsa...


Maleekh ya isa kusa da gadon ya kwantar da Amal a hankali, tamkar bai son ta tashi daga baccinta. Ya ja blanket mai laushi ya lulluɓe jikinta gaba ɗaya. Duk da haka, idanunsa ba su iya barin fuskarta ba.

Ya tsaya a tsaye gefen gadon, hannuwansa a aljihunsa, yana kallonta da irin kallon da mutum ke yi wa abu mai daraja wanda bai taɓa tsammanin zai mallaka ba.


A zuciyarsa akwai tarin ƙiyayya, amma a wannan lokacin wani sabon abu ya taso masa, abin da bai iya fahimta ba. Idanunsa suna biye da kowanne ɓangare na fuskarta:

Farar fatar ta mai ɗaukar ido, wacce take da laushi kamar auduga.

Idanunta duk da a rufe suke, girman su da tsawon gashinsu na sa mutum ya ji tamkar za su yi magana koda ba ta buɗe su ba.

Ƙaramin bakinta, tare da launin lips ɗinta mai color ja tamkar sabuwar pomegranate, suna yi masa wani irin kallo koda ba ta motsa su ba.

Gashin girarta mai kauri mai siffar natural, wanda ya yi kyau daidai da surar fuskarta.

Tsayin hancinta madaidaiciya..


Idanunsa suka sauƙa ƙasa, suka tsaya a kan kirjin ta. Breast ɗinta a cike masu girma suna lulluɓe da blanket, amma shaid'an ya shiga masa rai. Da sauri ya ɗauke kansa cikin ƙarfin hali, zuciyarsa tana wani mummunan bugawa...

Shape ɗin hips ɗinta da ya bayyana cikin lulluɓin blanket ya sa shi ƙara yin shiru yana danne zuciyarsa.

Kyakkyawar surarta ta zarce misali, irin kyan da yake haɗe da na Indian beauty...

Maleekh ya ja numfashi mai nauyi. Ƙila zuciyarsa ta fara karkata gareta....girgiza kai yayi tare da matsawa daga jikin gadon, yana jin kamar idan ya ƙara tsayawa kusa da ita, zai rasa ikon kansa...

“Ba yanzu ba… fansa ta fi wannan muhimmanci.” Ya furta a zuciyarsa.

Sai dai, idanunsa sun ƙi barin jikinta...


Maleekh ya tsaya gefen gadon, yana kallon Amal da ta yi nisa a baccin ta. Numfashinta mai sauƙi yana fita cikin nutsuwa, tamkar ba ta taɓa shiga cikin wahala ko tashin hankali ba.

A zuciyarsa ya fara magana da kansa:

“Amal… ke ce mace ta farko da ta taɓa tsallake iyakokina, ta mare ni, ta wulakanta ni a bainar jama’a. Na rantse cewa ranar fansa ta ba zata wuce ba. Amma yau… ga shi kina kwance a kan gadona, kina baccin nutsuwa kamar wata sarauniya.”

Ya lumshe ido, ya haɗa hannuwansa ya goya akan kirjinsa..Ya ci gaba da faɗin

“Kina da kyau fiye da misali… farin fatarki, idanuwan nan masu girma, bakin ki mai ɗaukar hankali… komai naki abin sha’awa ne. Amma, Amal… wannan kyau ba zai hana ki biyan fansar da kika jarabtar da ni da ita ba.”

Ya ƙara matsawa kusa, idanunsa suka tsaya kan blanket ɗin da ya lulluɓeta, yana iya hango siffar jikinta a ƙarƙashin sa.

“Na san duk wani namiji da zai ganki a wannan yanayi zai ruɗu ya manta da komai, amma ni… Maleekh… ban saba barin mace ta ci karfina ba. Sai dai gaskiya Amal, yau na kasa ɗauke idona daga gare ki. Kamar wanda kika mun sihiri?.”

Ya jinjina kai, ya yi murmushin gefen baki, mai ɗauke da duhu da alamar mugun shiri...

“Zan nuna miki soyayya, zan lulluɓe ki da alheri da kariya… amma duk a fuska ne. A ɓoye kuwa, zan jefa ki cikin wuta. Ki ɗanɗana wahalar da ta fi marin da kika yi min sau dubu.”

Ya yi shiru na ɗan lokaci, yana lumshe idanuwansa cikin nutsuwa, sai daga baya ya furta a hankali, tamkar yana magana da ita amma ba ta jin sa:

“Amal… kiyi bacci, ki huta a kan gadona… domin wannan hutu zai zama farkon hanyarki zuwa cikin azabar da nake shiryawa a zuciya ta.”

Ya ja blanket ɗin da ta ɗan zame, ya rufe ta sosai, sannan ya juya ya fice daga ɗakin da wani irin nauyi a zuciyarsa, nauyin soyayya da yake ƙoƙarin hana shigar sa cikin zuciyarsa, da kuma nauyin mungun fansa da yake ran sa...

Yanayin tsarin bedroom ɗin gwanin burgewa, domin bedroom ɗin ba kawai ɗaki bane, mazauni ne na sarki...

Katafaren gadon king size bed ne, mai frame ɗin Italian mahogany wood wanda aka yi masa zane a gefuna. Headboard ɗinsa an yi shi da leather quilted design mai taushi, wanda fitilar gefen gado (bedside lamp) ke haskawa yana fitar da walwali.

Blanket ɗin farar fata ce mai ɗauke da silk embroidery, pillows kuwa sun cika gadon, manya-manyan masu taushi da ƙananun masu launi daban-daban, suna sa gadon yayi kamar wani gado na princess..

Bangon ɗakin an yi masa marble wall panels na farin dutse, sannan a tsakiyar bangon da gadon ya jingina aka saka babban frame mai ɗauke da painting na art ɗin ocean view.
An yi hidden lighting a saman bangon (ceiling) wanda yake bada hasken mai laushi, yana sa ɗakin yayi romantic.

Ƙasa kuwa Persian carpet ce mai launin ruwan haske, ta rufe tsakiyar ɗakin, yayin da sauran ƙasan Italian marble tiles ne masu kyalli.

An saka manyan windows masu gilashin tempered glass, sai dai an rufe da long curtains na velvet wine color da aka ja daga sama har ƙasa, suna bada yanayin royalty.

Sofas biyu masu launin fari, Italian leather da aka saka a gefe...

Ga akwatin glass center table wanda yake kan carpet.

Wardrobe ɗin walk-in closet ne a gefe, sai bathroom mai ƙyalli da aka yi da marble tiles da kuma jacuzzi bathtub a ciki.


Hancinki zai ji ƙamshin oudh perfume mai haɗe da vanilla da sandalwood, da zaran kin shiga ciki.... sai wani dim light wanda yake bada nutsuwa da ɗan “romantic tension”.


Amal tana kwance akan gadon nan mai girma, blanket ɗin silk ya rufe jikinta, gashinta ya bazu a kan farin pillow kamar sarauniya da aka kwantar.
Fitilar gefen gado tana haskawa a saman fuskarta, ta sa farin fatarta da kyan idanuwanta sun ƙara walwali.
Baccin da take yi ya haɗu da luxury ambience ɗakin, tamkar wata Indian princess da aka kwantar a masarauta...

Maleekh kuwa yana tsaye a gefen gado, idanunsa suna kai-kawo tsakanin kyawunta da kuma tunanin mungun shirin da yake yi.


Idan aka koma kan Bathroom ɗinsa...bathroom ɗin yana da sliding glass door mai gilashin frosted wanda ba’a iya ganin ciki sosai. Idan ka shiga ciki iska mai sanyi na air freshener ne zai bugi hancinki da ƙamshin oudh & lavender.

An yi bangon bathroom da Italian white marble mai ƙyalli, an zana masa gold streaks kamar layukan zinare..

Ƙasan kuwa heated floor tiles ne wato tiles ɗin suna bada ɗumi a ƙasa duk lokacin da ka taka, ko da a lokacin sanyi ne.

Babban abu da ya ɗauke ido shine Jacuzzi bathtub ɗin da aka saka a kusurwar hagun..

An yi shi da porcelain white finish mai sheƙi..

Yana da hydro-massage system wato ruwa na fitowa a jikin bangon tub ɗin yana yi maka tausa yayin da kake ciki.

Sannan aka zagaye gefen tub ɗin da small LED lights masu launin blue, suna bada wani romantic glow.

A gefen bathtub aka ajiye wine glass holder da kuma scented candles masu ƙamshi...


Shower area..
A gefe guda akwai walk-in glass shower, frameless transparent glass.

Shower ɗin rainfall shower head ne, idan an kunna, ruwan yana sauƙa kamar ruwan sama..

A gefe an saka hand shower don tausa da goge jiki.

Fuskokin bangon an yi musu waterproof golden mosaic tiles.


Mirror & Sink Area
A tsakiyar bathroom akwai double sink vanity wato basin biyu masu ceramic finish da golden faucets.

A sama akwai huge mirror mai ɗauke da backlit LED frame wanda yake bada haske mai kyau idan mutum na duban kansa.

A gefen sink aka jera designer perfumes, aftershaves, da kuma expensive skincare products (Versace, Dior, Tom Ford).


Towels Arrangement...
Towels masu taushi (Egyptian cotton) aka nannad'e su a cikin golden towel rack.

An jera manya (bath towels), ƙanana (hand towels), da robe mai alama da sunan Maleekh da aka yi da embroidery.


Other Luxury Touches..

An saka sound system speakers a cikin ceiling, don haka mutum zai iya kunna kiɗa yayin da yake wanka.

A gefen jikin mirror akwai automatic soap dispenser da kuma flower vase mai ɗauke da fresh white roses.

Fitilun bathroom ɗin ba su da tsanani an yi su dim light option domin ya bada nutsuwa yayin da mutum ke hutawa cikin Jacuzzi.


Amal tana kwance kan katafaren king-sized bed ɗinsa har bacci ya fara kaurace mata, a hankali ta fara motsi daga baya ta farka gaba ɗaya.... Idanunta suka ɗan lumshe saboda AC mai sanyin daɗi da ƙamshin turaren da ke tashi a ɗakin...

A hankali ta miƙe daga gadon, tana bin ƙyallin fitilun LED lights da ke gefen bangon bedroom ɗin. Ganin wata ƙofa mai frosted glass da haske ke fita daga ciki yasa ta je wurin...

Da ta buɗe ƙofar, sai iska mai daɗi da ƙamshin lavender & oudh ya buge mata hanci. Gabanta ya ɗan faɗi rass, wannan shine bathroom ɗin Maleekh...

👣 Ta taka cikin marble tiles masu ɗumi a ƙasa, idanunta suka lumshe saboda nutsuwar da ta shige ta.

A gabanta, huge backlit mirror ne ya bayyana mata. Tana kallon kanta cikin madubin, tana ganin irin yadda gajeriyar tafiyar da ta sha wahala ta haggard ɗin fuskarta, amma kyawunta bai gushe ba.

Hannunta ya sauƙa a kan golden faucet, ta kunna ruwa sai crystal clear water ya fara gudu da ƙamshi. Ta ɗan wanke fuskarta tana shaƙar nutsuwa...

Idonta ya sauƙa kan Jacuzzi bathtub a gefen kusurwa, da LED lights masu launin blue suna kyalli kamar taurari a ƙarƙashin ruwa. Sai ta ɗan yi murmushi kaɗan tana faɗin a ranta:

"Kai wannan rayuwar alatu... ni ce na tsinci kaina a ciki yau? Har cikin gidan su Maleekh, cikin ɗakin sa...

Sai ta ji jikinta yana rawa da tsoro da kunya lokaci guda.

Amal ta juya zuwa gefen towel rack, ta ɗauki ƙaramar towel mai laushi, ta ɗora akan kafaɗarta. Idanunta suka sake komawa kan madubi, inda ta tsaya tana duban kanta.

Kyawunta ya bayyana fiye da ko yaushe..

farar fatar ta ta haske ƙarƙashin hasken LED.

gashin girarta masu kauri da kyau suna rufe manyan idanunta masu launin hazel.

ƙaramin bakinta mai launin pink natural lips ya yi laushi...

tsayin hancinta madaidaici, ga surar fuskarta mai kama da Indiyawa.

Kayan dake jikinta ya lulluɓe jikinta sosai amma duk da hakan perfect body curves ɗinta sun fito: hips ɗinta masu shape, ƙirjinta da ya yi kyau daidai gwargwado.


Ta lumshe ido tana rufe fuska da towel ɗin kamar tana ɓoye kunya.

Sai kawai ta ji ƙarar ƙofar bedroom ta buɗe, Maleekh ya dawo daga falon ɗakin nasa. Yana riƙe da wayarsa a hannu, amma da ya hango ƙyallin hasken bathroom ɗinsa, sai ya tsaya cak.

A hankali ya je bakin ƙofar bathroom ya tsaya..

Knowing ya fara yi tare da furta.
"Kin fara ne ko na shigo?..."

Jin shiru yasa ya ɗan tura ƙofar, ganin ta yayi a tsaye a jikin mirror...

Tsaya kallonta yake,
Kallo mai haɗe da soyayya da ƙiyayya a zuciyarsa lokaci guda.
Amal kuwa tana tsaye gaban madubi tana share fuskarta da towel, sai gashinta mai tsawo da ya zubo kan kafaɗunta...

Maleekh a hankali ya busar da slow deep breath, sai murmushin gefen baki ya bayyana a fuskarsa, yana faɗin a ransa:

"Kin shiga ragar da na kafa miki da kanki, Amal."

Ya ɗan jinjina kai, idanunsa suna sauƙa a kan kowace siffarta, kafin ya furta da murya mai nutsuwa da kuma izza..

"Amal… me kike yi cikin bathroom haka? Kina son kaɗa mun zuciya ne?"

Amal ta juyo da sauri, idonta ya haɗu da nasa. Towel ɗin da ta ɗora a kafaɗarta ya zame ƙasa. Ta matsa baya kaɗan, zuciyarta na bugawa da sauri...

Amal cikin jin kunya ta ce

"Ni… ba haka bane. Ban san bathroom bane, kawai… na ga ƙofa na haskawa, sai na shigo."

Maleekh ya ɗan yi murmushi sannan ya matsa kusa da ita, Amal ta ja baya tare da yin saurin ɗaukar towel ta rungume a ƙirjinta..

Cikin rawar murya take faɗin

"Maleekh, dan Allah ka daina irin wannan kallon. Ka sani… ni ba irin ‘yan matan da kake gani ba ne."

Maleekh ya tsaya yana kallonta cikin madubin sannan ya ce

"Kuma wannan shi ne dalilin da yasa na kasa samun natsuwa, Amal. Kin bambanta. Kina da wani abu da sauran basu da shi. Idan kina tsaye a nan, cikin bathroom ɗina… me kike tsammani zan yi?"

Amal ta yi shiru, idanunta suka cika da hawaye. Ta ƙi kallonsa kai tsaye, sai ta ce da sanyin murya

"Abin da nake tsammani shine… ka barni da mutuncina. Ka bari na fita daga nan cikin kwanciyar hankali. Ban zo duniya don in kasance abin wasa ba, Maleekh."

Bayan ta furta hakan, sai bathroom ɗin ya yi shiru na ɗan lokaci. Maleekh ya zuba mata ido kamar zai cinye ta da kallo. Sai kuma ya matsa kusa, yana ɗan lumshe ido ya ce:

"Mutunci…? Ni ma mutuncin ki ne, Amal. Amma ki sani… kin shiga rayuwata, kuma babu fita. Ko da kina so ko baki so."

Amal ta ji jikinta ya mutu da tsoro da wani abu da ta kasa fassara. Ta ƙara matse towel ɗin, zuciyarta na bugawa kamar zata fito...

Maleekh ya matsa sosai dab da ita, har numfashinsa yana busawa a fuskarta. Hannunsa ya kai ya kama gashinta mai taushi, ya shafa shi a hankali tare da murzawa.... Amal ta rufe idonta tana jin jikinta ya mutu gaba ɗaya, babu kuzari sai na zuciya da take bugawa da sauri.

Maleekh cikin murya mai taushi, yana shafa gashinta ya ce

"Amal… kina sane da irin abin da kike haddasa min? Kin taɓa sanin yadda kike da iko a kaina?"

Amal bata iya magana ba, sai shiru da rawar numfashi. Idanunsa suka sauƙa kan fuskarta gaba ɗaya, yana bin girarta da kallon sha’awa.

Ya zame hannunsa daga gashi ya kai gefen fuskarta, ya shafa ƙuncinta da yatsunsa cikin taushi. Amal ta buɗe idanunta a hankali, idonsu suka haɗu. Sai suka tsaya kallon juna na wasu daƙiƙu da suka ji kamar lokaci ya tsaya cak.

Numfashinsu ya gauraya, ƙamshin jikinsa yana gauraya da nata. Maleekh ya kai yatsarsa kan lips ɗinta, ya shafa a hankali kamar yana karanta wani sirri a ciki. Amal ta lumshe ido, zuciyarta

19 / 82