Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
daɗa ƙarfafa ta, sun bata kwarin gwiwar cigaba da tafiyarta. Sai dai ta yi ƙoƙarin boye wannan farin ciki daga kowa, har ma daga kawarta A’isha.
Shi kuwa PA ɗin Maleekh yana gefe yana kallon wannan shirin, yana dariya cikin ransa. Shi ya fi kowa sanin cewa duk wannan shirin Maleekh akan Amal akwai zurfi babu wasa a ciki. Kuma saboda yana goyon bayan shi, ya riga ya ɗauki wannan al’amarin tamkar nasu su biyu ne.
A’isha kuwa bata fahimci komai ba. A ganinta Maleekh dai mutum ne mai son fitowa fili yana yabon kowa. Bata san asalin dalilin da yasa yake ƙoƙarin shiga zuciyar Amal ba. Ita dai abin da ta gani shi ne Yayanta yana ƙoƙarin nuna soyayyarsa a bainar jama’a...
A ranar kuwa A'isha ta koma gidan su Amal..Suna zaune su biyu, Inna kuwa bata nan..
A’isha tana dariya tana kallon Amal ta ce
“Amal, kin ga yadda ya fito a tv saboda ke? Yayana fa ya fito duniya ta sani saboda soyayyarki. Kina da sa’a wallahi.”
Amal ta ɗauki remote ta kashe ƙaramin tv dake manne a ɗakinta, ta yi ɗan murmushi ba tare da ta dubi A’isha ba ta ce.
“Wannan ba yana nufin zan amince da shi bane. A’isha, kin san halin Yayanki. Ban ga dalilin da zai sa in ɗaura kaina a rayuwarsa ba.”
A’isha ta ɗan turo baki sannan ta ce
“Ke dai kin fi kowa sani. Amma wallahi ina ganin wannan soyayyar gaskiya ce.”
Amal ta ɗauke fuska, amma zuciyarta na cike da farin ciki ta ce
“Bari dai lokaci ya nuna gaskiya. Amma ni ban amince ba tukuna.”
Suna cikin hira sai ga wayar A'isha na ƙara, tana dubawa taga sunan Yaya Maleekh ya bayyana akan Screen, murmushi tayi tare da ɗaga wa, a bangaren Maleekh kuwa cewa yayi.
"Kina tare da Amal ne?..."
A'isha ta bada amsar "eh..."
Ya ce
"Toh! Ki ɗauke ta kuje kiyi mata shopping, ta taya ki zaɓen duk abinda take so a supermarket, Nima zan je wurin zan biya kuɗin..."
A'isha ta ce "To ba damuwa..."
Ta katsar da wayar tana duban Amal, sannan ta ce.
"Yanzu dai tashi ki rakani shopping.."
Amal ta dube ta tace "kinga ban fa yi wanka ba, kuma ki bawa Angonki yayi miki mana..."
A'isha ta ce "ai ba Angon ne zai sa abinda zan saka ba, kuma inaso ki taya ni zaɓen kayayyaki ne.."
Amal ta ce "To jira ni nayi wanka.."
A'isha ta jinjina kai, tana jira har Amal ta kammala komai sannan suka tafi..dake A'isha da motarta a cikin motar suka wuce...
Bayan sun shiga, suka cika cart da kaya iri-iri. Amal tana taimaka mata ɗaukar kayan da suka burgeta ba tare da ta san a ita ake wa shopping ba.
Da suka iso wajen biyan kuɗi, sai Cashier ya sanar dasu cewa.
“Madam, ba sai kin biya ba. An riga an biya dukkan kuɗin kayan nan.”..
Amal ta kalli A’isha cikin mamaki ta ce
“Waye ya biya kuma?”
A'isha ne ta sanar mata cewa "Duk kayayyakin nan nata ne.."
Amal ta ce "nawa kuma taya?..."
A'isha tana murmushi ta ce.
"Yaya Maleekh ne yace na kawo ki shopping, shi ya biya kuɗin...."
A’isha ta fara fito waje da kayayyakin, Amal tana tsaye tayi tsumuuu, itama daga baya ta biyo A'isha, suka fito...
Cikin mamaki Amal ta hango Maleekh tsaye a wajen motarsa a bakin titi, yana murmushi kamar wanda ya gama nasara,
Amal ta tsaya cak, zuciyarta tana bugawa ta ce
“Meyasa ku ka yi haka ba tare da kun sanar mun ba?”
A'isha ta ce "unsuspecting ne ai..."
A fusace Amal ta ɗauki kayayyakin da aka siya, ta nufi inda yake. Tana isa ta watsa kayayyakin a gabansa, wasu suka bugu akan fuskar sa.
Cikin fushi, da murya mai ƙarfi take cewa
“Ka fita daga rayuwata, Maleekh! Ban sonka, bana kuma son abinda ya fito daga hannunka!”
Wurin ya cika da mutane suna kallo. Wasu suna mamaki, wasu suna kwaɗaituwa da magana...
A’isha ta ɗaure fuska, zuciyarta na tafarfasa ta ce
“Amal! Ki daina wannan rashin mutuncin a bainar jama’a!”
Amal ta ce
"To dole ne? dole ne sai yayi rayuwa dani?..."
Ta kalli Maleekh tana nuna masa yatsa ta ce
"Kana ji ba, ka saurare ni, kana tunanin kaci nasara ne akan soyayyata? fitowa television da kayi ba shine yake nuna cewa na amince da kai ba, saboda haka join yourself..."
Maleekh ne ya kamo hannunta da ƙarfi yana faɗin.
"Wallahi sai kin Aure ni dole..."
Yana ƙoƙarin sanya mata wani zoben gold a yatsanta, wanda haka na nufin ƙarfafa soyayya...
Kokuwar janye hannunta take tana faɗin
"Ka sakar mun hannu nace, Maleekh..."
Da ƙarfi ta janye hannunta daga riƙon da yayi mata, cikin ɗaga murya ta ce
"I said join yourself..." ta tafka masa wani irin gigitaccen mari.......Har sai da ya karkatar da wuyansa tare da kama wurin marin da hannu, yana mata kallon mamaki...."
Amal idonta a cikin nasa tana kuka domin bata so ta mare shi ba..
Kowa ya firgita da ganin wannan al'ajabin...
A'isha dake gefe sakin baki tayi tana kallon ikon Allah..
Jama'a kuwa sun daɗe suna ɗaukar video...
PA ɗin Maleekh ne ya nufi Amal yana zagin ta da cewa
“Ke wace irin yarinya ce? wacece ke har zaki ci mutuncin Boss ɗina haka a gaban mutane? Ke ba kya da hankali ne?”
Maleekh ne ya juyo da sauri, ya ɗaga hannu ya zabga wa PA mari yana huci cikin fushi ya ce
“Kaɗan ya rage in kore ka! Waye kai da zaka ɗaga mata murya? Ka sani kamar yadda nake a matsayin Boss ɗinka, Amal ita ma Madam ɗinka ce. Ka girmama ta!”
PA ya sunkuyar da kai yana bashi haƙuri....
Sannan Maleekh ya maido da idonsa kan Amal, cikin fushi ya dam'ko hannunta cikin ɗaga murya ya ce
"Ko ki soni, ko kar ki soni wannan ya rage naki, zan tafi dake dole sai kin soni..."
Ya fara jan ta zai shigar da ita mota, a lokacin Amal ta fara ihu tana neman taimako..
"Ka sake ni, ka sakar mun hannu nace bana sonka, ka sake ni Maleekh..."
A'isha ce ta buɗi baki ta ce
"Ina zaka kaita Yaya?..."
Wasu matasa ne ƴan daba su biyar suka sha gaban Maleekh suna faɗin
"Ina zaka kaita, a gaban mu zaka sace ta? ashe ma bata sonka har da fitowa gaban tv kana zayyana soyayya?..."
Maleekh cikin fushi ya ce "su waye ku? ku matsa mun daga kan hanya..."
"Matasan suka ce
"Baza ka tafi da ita ba..."
Maleekh ya ce "Ku dakatar dani idan kun isa..."
Ai kuwa Matasan nan suka afko masa, Maleekh ne ya sakar wa Amal hannu tare da tinkarar su, nan take suka fara gwabzawa, matasa su biyar suka rufu masa, shima Maleekh haka yake kai musu naushi, duk wanda ya samu a cikinsu zai kaiwa naushi....
Ganin haka yasa PA ɗinsa shiga masa, shima PA haka yake kai musu duka, mutum biyu suka haɗu wa PA, mutum uku kuma akan Maleekh...
A'isha ba abinda take sai ihu tana faɗin
"Wayyo Allah zasu kashe mun Ɗan uwa, taimako jama'aaaa...."
Amal kuwa gaba ɗaya ta rikice, ba abinda take sai kuka, tana so ta dakatar da mutanen amma ta kasa...
Kafin sai ga motar security Maleekh da ta police, a nan aka raba su, a fusace Maleekh ya ciri bindiga daga aljihun ɗaya daga cikin security sa ya kunna kunamar bindigar yana shirin harbe su...
Wani ɗan sanda ya riƙe shi yana bashi haƙuri...
Ga yanda suka fasa masa lips ɗin baki, duk da suma matasan sun ji jiki, domin ba ƙaramin naushi suka sha a wurin Maleekh ba, duk da su uku ne amma haka suka kasa kayar da Maleekh, haka shima PA ɗinsa ya nuna jarumta sosai domin duka yayi wa sauran biyun da suka yi kansa...
Ƴan sandan ne suka kama matasan duk suka sa musu ankwa, za'a kulle su...
Maleekh kuwa Security sa ne suka shigar da shi mota suka tafi...
Amal da gudu ta tari napep ta koma gida a tsorace, bata ma lura da zoben da ya sa mata ba, sai sheƙi yake a hannunta....
A'isha kuwa itama motarta ta shiga a tsorace tabi bayan motar su Maleekh...
🌹 Page 15–16 ends here 🌹
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 17 to 18
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Maleekh yana zaune a motar zuciyarsa na tafasa a yayin da PA ɗin sa yake driving...
Ga wasu motocin security a tafe a bayansu..
Maleekh ya lumshe idanu yana faɗi a hankali cikin rawar murya ga lips a fashe sai ɗigar da jini yake..
“Duk abinda tayi min zan rama. Amma sai soyayyata ta mallake ta gaba ɗaya kafin ta san irin azabar da zata fuskanta.”
PA ya jinjina kai yana ƙara zuga shi da cewa
“Boss, yarinyar nan ba ƙaramin raina ka tayi ba. Lokacin fansa ne kawai ya rage.”
Maleekh ya yi murmushi mai cike da takaici da mugunta, yana shirin sabuwar dabarar da zai ɗauka a kan Amal…
Tin a napep Amal ta lura da zoben da Amal ya sanya mata da ƙarfi, ɗago hannunta tayi tana kallon zoben sai sheƙi yake, ga wasu zafafan hawaye dake zubo mata...
Amal na dawowa gida, zuciyarta ta rikice tamkar an jefa ta cikin ramin da babu mafita. Tana shiga ɗakinta ta rufe da karfi tare da sakale sakata, ta sulale a ƙasa tana kukan da ya huda zuciya. Hannayenta na rufe akan fuska, zuciyarta na bugawa da sauri, tana jin nadamar yadda ta wulakanta Maleekh a gaban duniya.
Cikin kuka take faɗin
"Me yasa na bari masifar zuciyata ta rinjaye ni? Me yasa na zubar da mutuncinsa haka?” Ta tambayi kanta cikin kuka...
Amma duk da haka, wani ɓangare na zuciyarta ya ƙi yarda da cewa kuskure ne, sai cewa tayi a fili
“Zan cigaba da gwada shi har sai na tabbatar da gaskiyar soyayyarsa. Idan ya fita daga rayuwata saboda wannan, to shi ba nawa bane.”....
A gefe guda kuwa, Maleekh ya koma cikin duniyar gidansa cikin bacin rai. Zuciyarsa ta ƙone da wuta..
Bayan ya shiga falonsa, ya zauna a kujerarsar falon, sai sauƙe numfashi yake yi tamkar wanda aka ɗora masa wani nauyi...
Ya jan yo shisha gabansa, yana zuƙar hayaƙi tamkar yana neman mafita daga rantaƙiyar da ke ci masa zuciya. Idanunshi sun sauya launi, wani yanayi na ɗacin rai yana wanzuwa masa..
A fizge yake faɗin
"Amal… wannan wulakanci ba zai tafi a banza ba. sai na nuna miki kuskuren da kika fara tin farko har zuwa yanzu...”
Yana raba hayaƙi, fuskarsa kamar wanda aka watsa wa tafashashshen ruwan zafi...
《☆☆☆》
Bayan kwana biyu
A Abuja, gidan su Maleekh.
Farha tana kwance a kan tsararren gadonta, ta kifa kanta sai sharar kuka take, zuciyarta na ƙuna da kishin da ya kasa boyuwa...
Sai ga ƙofar ɗakin ya buɗe a hankali, Hajiyar gidan wanda duk gidan ke ƙiran ta da Ammy, mahaifiyar Maleekh kenam, ta shigo cikin nutsuwa. Tana sanye da kayan alfarma, kyakkyawar mata mai cike da ƙima da isa..
Ta zauna a bakin gadon, ta dafa kafaɗar Farha cikin lallashi...
“Meye amfanin kukan nan, Farha?” Ammy ta tambaya cikin murya mai taushi mai cike da iko..
Farha ta ɗago da idanunta da suka yi ja, kuka ya sa sun kumbura, ta ce cikin karyayyen murya.
“Haba Ammy! Baki ga abin kunyar da Maleekh ya jawo mana ba? Yana fitowa a television yana yayata soyayyar wata matsiyaciyar yarinya, ƴar talaka marar gata! Wannan ba mutuncinsa bane…”
Ta fashe da wani sabon kuka tana girgiza kai, sannan ta cigaba da magana cikin zafin rai.
“Ammy, ya zanyi da soyayyarsa? Har yanzu yaƙi kallona a matsayin masoyiyarsa, yaƙi saurarona, kuma nasan saboda waccan yarinyar yaƙi dawowa daga Kaduna. Wallahi idan baki aura mun Maleekh ba, mutuwa zanyi!”
Ammy ta sauƙe dogon numfashi, tana kallon Farha da idanun ta cike da wani irin haske na muguwar natsuwa. Ta ɗan yi shiru, sannan ta furta
“Ki kwantar da hankalinki, Farha. Bazan taɓa barin Maleekh ya auri wata matsiyaciyar yarinya ba. Na miki alƙawarin Maleekh naki ne, kuma zan aura miki shi.”
Farha ta share hawayenta da sauri, tana kallon Ammy da wani irin hope ta ce.
“Ammy… amma ba ya sona fa. Ko kallona baya yi…”
Ammy ta ɗaga gira, ta murmusa da irin murmushin mace mai cike da shirin da babu wanda ya iya fassara shi, sannan ta ce
“Dole zai soki, Farha. Zan sa ya dawo daga can Kaduna, kuma da kansa zaki ga yadda zai fuskanci soyayyarki. Ba zai ƙi umarnina ba.”
Farha ta rungume Ammy da sauri, hawaye suna sake zubo mata amma wannan karon hawaye ne na begen cikar burinta....
Farha yarinyar ƙanwar Ammy ce, iyayenta da ita suna zaune a ƙasar London, ita farha ta dawo Nigeria ne saboda Maleekh, tana zaune a gidansu a gaban Ammy..
Suna zaune Ammy da Farha sai ga Arfat ƙanwar Maleekh ta shigo da gudu tana kwallawa Ammy ƙira
“Ammy! Ammy!!”
Ammy ta zabura ta kalleta, zuciyarta na bugawa cikin firgici ta ce
“Meya faruwa ne haka, Arfat? Wannan irin ƙiran fa sai ki tsoratar da mutum!”
Arfat ta fitar da numfashi kamar wanda tayi gudun kilo mita hamsin, tana zufa tana huci ta ce
“Ammy, zo kiga television… Yaya Maleekh ake nunawa! Budurwa ta mare shi a bainar jama’a, ta wulakanta shi sannan tasa yayi faɗa da wasu matasa. Kamar ya ji ciwo!”
Da gudu Ammy ta miƙe, Farha ma ta miƙe duk suka fice zuwa babban falo inda television ke kunne...
A can kuwa rahoton yana ci gaba. An nuna video Amal ta ɗaga hannunta, ta zabga mari a fuskar Maleekh a gaban jama’a, da irin wulakancin da ta masa..
Gari ya ɗauki zafi. Kaduna ta kaure da maganganu. Duk inda aka shiga sai a ji ana maganar “Wai Amal ta mari ɗan gidan minister Alhaji Abdul-majeed a bainar jama’a!”
Anata posting a social media, hotunan sun bazu fiye da yanda ake tsammani..
Maleekh, a ɗaki ya jingina da kujerarsa, idanunsa sun kaɗa sunyi jaa, yana kallon television. Ganin yadda Amal ta mare shi duba da ƙarancin asalinta, hakan ya sa ya rafka uban harara, zuciyarsa na tafarfasa kamar wuta. Ya riƙe sumar kansa yana cukurkudawa, kamar zai haukace da kunyar da aka jawo masa.
Amal kuwa a ɗakinta a Kaduna, ta shagaltu da damuwa. Kuka ne kawai ke tserewa daga idanunta, saboda ta san duniya ta fara kallonta da ido ɗaya, suna tallata wannan abin kunya da ita da Maleekh.
A Abuja, Alhaji Abdulmajeed mahaifin Maleekh, yana zaune a ofis ɗinsa, an kawo masa rahoton. Yana ganin hoton yadda mace ta sa hannu ta mari ɗansa a bainar jama’a, ransa ya yi matuƙar ɓaci...
Ammy ma ta ji tamkar ta haɗiye ranta saboda takaici. Farha kuwa ta daure ta furta cikin ƙiyayya.
“Ammy, yanzu da ni nayi masa haka, kin san ba zan kwana da ƙafafuna ba. Da ya kakkarya ni tun a wurin! Amma ga matsiyaciyar yarinya ta mareshi a bainar jama’a, kuma sannan ya sharar da ita. Har da faɗa saboda ita!”
Ammy tana cikin tsananin fushi, hannunta na rawa saboda takaici. Ta kasa furta komai...
A ɓangaren Mahaifinsa dake office.
A fusace ya ɗauki wayarsa, ya ƙira lambar Maleekh.
A ɗayan ɓangaren, Maleekh ya ɗauki ƙiran da muryar da ta sha bamban, kamar wanda ya yi shaye-shaye. Ya ce
“Hello, Abba…”
Abba bai tsaya gaisawa ba. Da murya mai nauyi ya ce.
“Inaso ka dawo Abuja yau ɗinnan. Kada ka ƙara kwana a Kaduna.”
Maleekh ya lumshe idanu, ya sauƙe ajiyar zuciya sannan ya ce
“Na ji, Abba…”
Ya amsa a taƙaice, zuciyarsa na nuni da cewa daga wannan rana lamarin zai ɗauki sabon salo....
Maleekh yana jingine da kujera, hannunsa na riƙe da wayar da ya gama magana da mahaifinsa. Zuciyarsa ta cika da tsananin fushi, amma fuskar sa ta nuna sanyin jiki..
Ya ɗaga shisharsa ya shaƙi iska mai ƙamshi, ya sauƙe ta cikin takaici yana faɗin
“Kaduna… ban shirya barin cikinki ba saboda ban gama aiki akan Amal ba. Amma yanzu Abba ya ƙira ni, dole sai na koma Abuja.”
Ya juya yana kallon PA ɗinsa, wanda ya tsaya a gefe yana huci shima.
Maleekh ya ce
“Ka shirya kayana. Ba zan ƙara kwana a nan ba. Abuja na jira.”
PA ɗinsa ya yi shiru na ɗan lokaci, sai ya ce cikin ɗan ɗaga murya
“Boss, wannan yarinyar ta raina mu sosai. Wallahi ban taɓa ganin mace ta yi maka irin wannan ba… me za ka yi game da ita?”
Maleekh ya ɗan yi murmushi, murmushin da ya ƙunshi mugunta da takaici ya ce
“Ba yanzu ba. Amma zan nuna wa Amal bana yafiya. Da zarar na koma Abuja, za ku ga yanda zan karkatar da komai zuwa hannuna.”
Ya miƙe tsaye, ya nufi bedroom ɗinsa, PA ne yabi bayansa, yana shiga ya nufi wardrobe yana ɗaukar kaya masu tsada yana ajiye wa PA don shirya masa a jakunkuna.
Zuciyarsa ta yi nauyi sosai. Amal ta mare shi a bainar jama’a, abin da bai taɓa faruwa da shi ba tun da aka haife shi. Yanzu kuwa duniya ta gani, duniya ta yi sharhi. Kuma mahaifinsa ya ƙira shi da umarni mai zafi...
Ya tsaya a gaban madubi, ya kalli fuskar sa, saitin wurin da ta mare shi. Hannunsa ya ɗago a hankali ya taɓa fuskar, zuciyarsa ta cika da tsanar Amal...
“Amal…” ya furta cikin sirri. “Kin fara yaƙi, amma ni zan kawo ƙarshensa. Abuja ce matakin farko.”
Sai ya juya ya saka agogon hannunsa mai tsada, ya ɗauki wayarsa yana faɗin
“PA, ƙira min jirgin Abuja. Na fi son private jet ɗina ya jira ni kafin karfe biyu na rana.”
“Yes, Boss.” PA ɗin ya ce, yana bin shi da idanu, zuciyarsa na mamakin irin natsuwar da Boss ɗinsa yake nuna wa duk da irin wutar da yake ƙonewa a cikin zuciyarsa..