Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 82

42K to 45K   out of 244.2K words



Amal ta zuba wa wayarta ido, tana dubanta, ta kasa natsuwa. Kwana biyu kenan bata ji ƙiran Maleekh ba, bata kuma ga saƙonsa ba. Zuciyarta ta ƙara rikicewa, zuciya na ta bugawa kamar zata fito.

Ta jawo wayarta ta sake dubawa. Sai lambar A’isha ta faɗo mata a rai. Cikin tsoro da shakku ta danna ƙira.

A can ɓangaren A’isha kuwa, tana zaune taji wayar tana ringing. Takaici ya cika mata zuciya a fili take faɗin

“Amal ce? Wacce ta mari Yayana a gaban jama’a? Haka nan kuma duniya ke yi masa ba’a saboda ita?” Ta jinjina kai cikin ɓacin rai,
Ta ɗauki lokaci kafin ta ɗaga. A ƙarshe ta ɗauka tare da faɗin.

“Assalamu alaikum.”

Amal ta runtse idanu, muryarta na rawa ta ce

“Dan Allah A’isha kiyi haƙuri da abinda ya faru. Nasan bakiji daɗi ba…”

A’isha ta amsa cikin ƙunshi, tana ɗan sauƙe ajiyar zuciya ta ce

“Ba komai. Amma yanzu, meya faru ne?”

Amal ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta furta cikin rauni.

“Maleekh ne… ban ji labarinsa ba, na damu sosai. Shin yana lafiya?”

A’isha ta yi dariya sannan ta kaɗa kai kamar tana magana da kanta...Ta ce

“Yanzu kuma Yaya Maleekh kike tambaya? Bayan wulakanta shi da kika yi a bainar jama’a? Haba Amal, kin bani mamaki. Kin san irin takaicin da iyayensa zasu ji akan wannan al'amarin? Taya kike tunanin zasu bar shi ya cigaba da zama a Kaduna bayan sun ga abinda kika masa? Ina mai miki fatan kada Allah yasa mahaifiyarsa ta biyo ki har nan kaduna domin tafi wuta ƙuna, saboda bala'inta yasa mahaifin mu ya raba musu gari da mahaifiyata, ita tana can Abuja da iyalanta, mahaifiyata kuma tana nan kaduna da mu, saboda bala'i kinga ko bikina mahaifiyarsa da ƙannensa basu zo ba sai iya Yaya Maleekh ne kawai ya ziyarci bikina, kin yi kuskure Amal .."

Zuciyar Amal ce ta karye, hawaye suka fara zubo mata. Tayi ƙasa da murya, tana jin kamar zuciyarta zata fashe ta ce

“Maleekh ya koma Abuja kenan…?”

A’isha ta lumshe idanu, ta amsa da taƙaice.
“Eh.”

Ba tare da ƙarin magana ba, ta kashe wayar.

Amal ta zube akan gado, kuka mai tsananin raɗaɗi ya kwace mata. Zuciyarta na tsananta da tambayoyi.

“Shin hakan me yake nufi kenan? Shin shikenan ya gudu daga gare ni saboda abin da na yi masa? Ko kuwa iyayensa ne suke ƙoƙarin rabani dashi?”

Inna ce ta shigo ɗakin, ganin Amal tana kuka yasa tayi ƙwafa ta ce "kaɗan kika gani, indai mutum wulakanci ya iya wata ran zai cusa barkono ne a tsuriyarsa ba tare da saninsa ba..."
Inna tayi tsaki bata ma son kallonta. Tun bayan abin da ya faru ta daina kula ta, domin a idanunta Amal ce ta jawo musu ƙasƙanci da tozarci...


ABUJA CITY

Maleekh ne yake zaune a bakin katafaren gadonsa dake cikin tsararren bedroom ɗin sa...

Yana sanye da short 3quarter da rigarsa mai gajeren hannu na shan iska.. shi kaɗai yasan irin tunanin da yake yi..

Bai san an buɗe ƙofar ɗakin bama tsabar yayi nisa a tunanin da yake.

Sai ji yayi an rufe ƙofar da ƙarfi, bugun ƙofar da akayi ne yasa ya dawo daga tunanin da ya zurfafa, sleepy eyes ɗinsa ya sauƙe akan mahaifiyarsa, wacce kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin fushi...

A tsawa ce ta fara faɗin.

"Maleekh! Wannan abinda kayi a Kaduna ai babban abin kunya ne. Haba! kai fa mutum ne babba, ɗan manya, ya za ka bari wata ‘yar talaka ta mare ka a bainar jama’a? A fuska fa? Ka sani kai ba kamar kowa bane."..

Maleekh yana ɗaure da fuska, ya ce

"Ammy, ba wai ban san darajata bane. Amma wallahi soyayya ce ta ruɗani. Ban taɓa ɗaukan Amal a matsayin ‘yar talaka ba. A idanuna… ita ce komai."

Ammy cikin jin haushi ta ce

"Komai? Komai har da wulakantaka a gaban mutane? Ka ji abin da kafafen yaɗa labarai suke ta yayatawa kuwa? Wannan ai abin kunya ne ga iyayenka. Ni fa ban yarda da wannan Amal ba, ba za ta taɓa zama matarka ba! Ga Farha wacce take masifar son ka amma ka ƙi ta gida kana ƙoƙarin jan yo mana magana..."

Maleekh yana huci, ya ɗan miƙe yana fuskantar Ammy ya ce

"Ammy, me yasa kullum sai Amal kike gani a matsayin barazana? Ta fi kowa gaskiya da amana! Ni dai ba zan iya auran Farha ba, ko da kin tilasta ni."

Ammy cikin ɗaga murya ta ce

" Farha ai ba irin waccan Amal ɗin bace matsiyaciya. Farha ‘Yar manya ce, ‘yar dattawa, ta girma kuma da tarbiya, za ta kare mutuncinka, ba wai ta zubar maka ba, Kuma duba iyayenta, za ka samu haɗin kai da amfanin ahali, Kai fa dole ne ka auri Farha!"..

Maleekh yana kallonta cikin rashin fahimtar abinda take nufi da dole sai ya Auri Farha, haka yake yatsina fuska ya ce

"Wallahi ba zan aure ta ba! Ni bana sonta, bana ma jin ko daɗin ganin ta. In har Ammy aure kike so, sai dai ki manta da ni. Soyayyata ta tsaya ne akan Amal, kuma ba zan canza ba!"


Daga nan Maleekh ya fice a ɗakin, da sauri yake sauƙa daga upstairs zuwa ƙasin falo, yana sauƙa ya zauna a kujerar falon yana fuskantar plasman...

Farha wacce fitowar sa kenam, ganin Maleekh yasa ta huce wurin ƙaton frig ta ɗauko juice da glass cup guda ɗaya, ta nufi cikin tsakiyar falon yanda yake zaune...


Farha ta shigo da murmushi, ta kawo masa juice tana faɗin

"Sannu Yaya Maleekh, na zo ne saboda Ammy ta ce kana cikin damuwa. Ka sha ruwa, ka huta."

Maleekh ya karɓi glass ɗin, ya ajiye shi ba tare da ya sha ba ya ce

"Farha, kin dai san bana buƙatar wannan kulawar da kike yi. Me ya sa baza kiyi zuciya ki daina zuwa gidan nan ba? ya kamata ki koma Ƙasar da kika fito, zai fi kyau ki zauna a gaban iyayenki, Ni bana sonki, bana son wannan abokantaka ma."...

Farha ranta ne ya ɓaci, amma tana ƙoƙarin yin murmushi domin danne ɓacin ran, ta ce

"Ban yi zaton zaka furta haka ba a fili, Yaya Maleekh. Inda kara ai nan gidan ma gidan iyayena ne, tinda Ammy Yayar mahaifiyata ce, maganar soyayya kuma na ɗauka lokaci ne kawai zaka buƙata domin yin tunani akan soyayyata...."

Maleekh yana kallonta cikin tsana ya ce

"Lokaci? Ko shekara ɗari ne ba zan canza ra’ayina ba. Ni bana sonki Farha. Don Allah ki bar cikin rayuwata. Kar ki takura ni, kar ki takura kanki."




Ammy wacce sauƙowar ta daga upstairs kenam ta ce

"Maleekh! Yanzu duniya tana magana ne akan wannan Amal ɗin. Me yasa kake ƙara damuwa a kanta? Ka manta da waccan yarinyar, ka zaɓi Farha ka huta."..

Maleekh fuska a ɗaure, yana danna wayarsa ya ce

"Ammy, sau nawa kike so na faɗa miki ne? Ba ni da wata mace sai Amal. Ko duk duniya ta tsaneta, ni ba zan ƙi ta ba. Ba zan iya rabuwa da ita ba."

Farha tana kallonsa cikin hawaye ta ce

"Ni fa ban taɓa jin ciwo irin haka ba, Yaya Maleekh. Amma me Amal ta baka da har ka manta da mutuncin kanka?"

Maleekh yana murmushi ya ce

"Amal ta bani abin da ba ku fahimta ba, soyayya ta gaskiya. Kuma duk abinda zaku ce, wallahi bazan taɓa sakinta."

Ya miƙe cikin fushi ya fita daga falon, yana tafe cikin izza, ya bar su cikin bacin rai, kai tsaye waje yayi ya nufi wurin parking motoci, kafin ya isa ya matsa key ɗin motar da zai shiga nan take ƙofar motar ta buɗe, shiga yayi a ɗari ya bi hanyar da zai kai shi get.
Mai gadi ne yayi saurin buɗe masa ya bar gidan gaba ɗaya, cikin ƙananun kaya na shan iska...


A Kaduna... Bayan wata guda..

Amal tana juya zuciyarta, tana kai-komo tsakanin tsoro da ƙauna. Duk lokacin da ta tuna da fushin Maleekh da kuma shiru da ya yi mata, sai zuciyarta ta cika da kunci. A ƙarshe ta yanke hukuncin cewa ba zata iya ci gaba da hukunta kanta ba...

Ta sanar wa Inna cewa zata je Abuja...

Inna a firgice ta dafa kirjinta tana faɗin:

"Abuja dai? Uban me zakiyi acan, garin manyan mutane zaki dosa?... Amal kin san garin bana wasa bane..."

Amal ta ɗago ido cikin nutsuwa ta ce:

"Inna, babu abinda zai faru. Ni addu’arki kawai nake nema. Ba don komai ba, sai don zuciyata ta huta daga wannan azabar shirun."

Inna ta juya kai, hawaye suna cika a idonta. Tana kallon jikar tata mai ƙaramin hali da girman zuciya. Cikin taushin murya ta ce:

"To Allah ya kare mun ke Amatullah. Ki sani ba ki da wani gata sai addu’ata. Ki kula sosai… Amma nasan Maleekh ɗin zaiji daɗin ganin ki."

Amal ta jingina kanta a kafaɗar Inna, tana jin wani irin ƙarfin hali ya mamaye ta...


Da Asuba bayan ta idar da sallah, already ta kammala shiryawar ta...

Ta shirya tafiya. Ƴan kuɗaɗen da ta daɗe tana ajiye su, ta raba gida biyu. Rabi ta ba Inna, tana faɗin:

"Inna, wannan ki riƙe, ko kayan abinci ya ƙare, ko wata buƙata ta taso, za ki samu. Ba daɗewa zan yi ba, iya kwana ɗaya ne kawai."

Inna ta karɓa cikin jinƙai, zuciyarta cike da addu’a.

Ƙarshen rabin kuɗin kuma Amal ta tanada shi domin kuɗin mota da ƙananan buƙatu.

Ta ɗauki jaka ta rataya a kafaɗarta, ta zuba ido tana kallon Inna da murmushin dole.
Ta ce

"Inna, ni zan tafi..."

Inna ta ɗaga hannu tana maimaita:

"Allah ya tsare ki Amatullah, Allah ya miki jagora."

A haka Amal ta nufi tashar mota, zuciyarta cike da tsoro da bege, kamar mace da ke barin ƙauye zuwa wani sabon duniyar da bata san menene ke jira a ciki ba.

A tashar mota mutane suna ta cunkoso, kowa da kayansa, kowa da nufinsa. Amal ta tsaya gefe da jaka ɗaya a hannunta tana jiran direban ya cika mota. Wani irin sanyi na ratsa jikinta...

Direba ne ya fara ƙwala ƙira: "Abuja! Abuja! Azo a tafi! Ku shigo mu tafi!" sai ta matso a hankali ta shiga, ta zauna a gefen taga.

Motar ta tashi, Amal ta jingina kanta da gilashin taga, idonta na kallon gari da nisan da yake raguwa a bayanta. A zuciyarta kuwa, tunani na kai komo kamar ruwan sama.

"Shin Maleekh zai karɓe ni? Shin zai ji daɗin gani na? Ko kuwa fushinsa zai ƙara muni?... Amma duk da haka ba zan iya jure wannan rabuwa ba."

Tana rufe ido sai ta ji muryar Inna na sake dawo mata:
"Allah ya tsare ki Amatullah…"
Wannan kalma ta Inna ta ba ta ƙarfin zuciya, sai ta ɗan yi murmushi da hawaye a idonta.

Hanyar Kaduna zuwa Abuja ta yi tsawo a gare ta fiye da yadda ta taɓa yi. A duk lokacin da direban ya taka birki ko motar ta yi tsalle, zuciyarta sai ta buga da ƙarfi, tana addu’ar Allah ya kai ta lafiya.

Ƴan mata biyu a motar suna hira da dariya a kusa da ita, amma ita gaba ɗaya zuciyarta nesa take can wurin Maleekh. Tana jin kamar kowane irin abu ne zai iya faruwa da ita muddin ta same shi.

Lokacin da suka fara shiga cikin birnin Abuja, hasken manyan fitilun tituna da ginin gine-ginen birnin suka bayyana a gaban Amal. Ta zaro ido tana kallon birnin, cike da bege.. domin zuwan ta Abuja na farko bata tsaya kalle-kalle ba, domin tin lokacin da Rikky Blaze ya gayyato ta zuwa podcast ɗin su, nan ma daga jirgi ne zuwa airport, anan kuma ta shiga mota sai hotel, daga hotel sai podcast, har ta koma bata wani zagaya Abuja ba...

A hankali ta furta.

"Ashe haka Abuja take... Duniyar manyan mutane, duniyar da zan yi gwagwarmaya domin zuciyata ta huta."

Ta dafe kirjinta, tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa.

"Maleekh... na iso."

Ta furta a hankali...

Tana sauƙa daga mota anan Amal ta fara tsorata, domin bata san ina zata je ba, shin idan ta hau napep ina za'a kaita? haka take zuru-zuru da ido...

Tambaya ta fara yi tana faɗin.

"Dan Allah aina zan samu Maleekh?..."

Gaba ɗaya kwakwalwarta ya toshe da inkiyar sunan Maleekh 'Maleekh Cashbank...' sannan ya toshe da sanin shi ɗin ɗan gidan Minister ne, but Minister meye? tinda ba iya Minister guda ɗaya bane...

Amma inda tayi kwatance da 'Maleekh ɗan gidan Minister Alhaji Abdul-majeed' zai fi sauƙi...
Amma gaba ɗaya sunan mahaifinsa ya kwanta mata a rai, ta rasa yanda zata yi..

Duk wanda tace
"Dan Allah ina neman Maleekh..." Sai dai a bata amsar da ba'a san shi ba...

Kuma a yankin da take a Abujan ba nan ne yanki masu kuɗin ba, domin yankin unguwar gomnoni da shugaban ƙasa da ministoci da chairmomi da sauran su babu wanda yake shiga yankin sai da izini...

Har dare ya fara yi Amal bata samu mafita ba, ga number Maleekh baya shiga kwata-kwata..

Dare yayi sosai. Tana zaune a bakin wani babban supermarket, hannunta na riƙe da ƙaramin jakarta. Ta gaji sosai ga yunwa na neman cinye ta gaba ɗaya, sai dai zuciyarta ta ƙi ba ta damar yin barci. Duk inda ta juyo, babu Maleekh, babu labarinsa.

Wayarsa kuwa koda ta ƙira sau nawa, sai dai ta ji muryar machine ɗin waya na cewa

“The number you are trying to call is switched off.”

Kifa kanta tayi a kan gwiwowinta tana huci da ƙarfin gajiya. Har gari ya waye, motoci suka fara cunkoso, mutane suka fara kai-komo, amma ita nan take zaune, idonta ya kumbura saboda rashin barci ga kukan da take sha...

Da ta ga babu wata mafita, sai ta yanke shawarar ta ƙira A’isha.

Lalumo lambar A'isha tayi bugu ɗaya kacal A’isha ta ɗauka, kamar daman wayar a hannunta yake..

Amal ta yi sallama cikin raunanniyar murya..

A’isha ta amsa, ta ce:
"Amal? Me meya faru kika ƙira da sanyin safiyar nan?"

Amal ta gyara zama sannan ta ce cikin rawar murya

"Ni yanzu haka ina Abuja A’isha... na zo neman Maleekh tun jiya, amma har yanzu ban same shi ba. Dan Allah ki taimaka ki turo min lambar da yake amfani da ita yanzu."

A’isha ta zaro ido kamar za ta fasa wayar, ta ce cikin mamaki:

"Abuja kuma Amal? So kike ki ɓatar da kanki? Ni fa wallahi lambar Yaya Maleekh yanzu ba ta shiga kwata-kwata...."

Amal ta fashe da kuka, ta ce:
"Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un..."

A’isha ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce:

"Sai dai wata hanya ɗaya zan iya turo miki lambar ɗaya daga cikin ƙannensa, zasu iya kwatanta miki gidansu, ki neme shi ki ji ainihin inda yake..."

Amal ta girgiza kamar wacce take gabanta, ta ce da sauri:

"Gidansu kuma? A’a... ba zan iya zuwa gidansu haka ba."

A’isha ta ɗan yi dariya mai ɗaci, sannan ta ce:

"To shikenan, idan haka ne ki nufi Kamfaninsa, CashTalk. Ai sananne ne a nan Abuja. Idan kika je, sai ki ce a kai ki can. Wannan shi ne mafi sauƙi."

Sai yanzu Amal ta tuna. Ta share hawayenta, ta ce da ƙarfin zuciya:

"Eh, I remember... CashTalk. Zan tafi can."

Da wannan suka kashe wayar, zuciyar Amal na dukan uku-uku...

Bakin hanya ta nufa da ƴar jakarta a hannu, ta tari mai napep, tana cewa 'akai ta kamfanin CashTalk, mai napep ya amsa mata, amma sai wurin yana da nisa sosai, iya kuɗin jikinta kenam ta bashi gaba ɗaya, nan ma saida ta bashi haƙuri akan ya taimaka mata domin kuɗin basu kai ba....

Suna zuwa daga nesa-nesa ta fara ganin tsayin kamfanin, da irin tsaruwar kamfanin, ko wani ƙofa glass ne amma baka iya ganin wanda yake ciki, amma na cikin zai iya ganin abinda ke faruwa a waje...

Mai Napep ne ya ajiye ta a wurin...

Amal tana kallon bakin get ta ga security sun fi goma suna tsatstsaye dake mashigar get d'in biyu ne, akwai bangaren dama da hagun...

Abun da ta lura da tsarin shine..
Idan zaka shiga cikin kamfanin get ɗin shiga da ban yake, kuma akwai security masu duba mai shiga...
Sanna ɓangaren ɗayan get kuma idan za'a fito daga cikin kamfanin, nan ma kawai security masu duba waɗanda zasu fita...

A tsorace ce Amal ta nufi wurin, gaba ɗaya tayi wujiga-wujiga da ita, tana zuwa suka tare ta...

Cikin rawar murya da yunwa yaci ƙarfinta take faɗin

"Maleekh nake nema?..."

Ɗaga daga cikin security cikin tsawa ya ce
"Wani Maleekh?..."

Amal kamar zata yi kuka ta ce "Maleekh dai..."

Ɗaya daga cikin su ne ya ce

"Wannan fa! Boss take magana akai..."

Bata ankara ba taji security na gabanta ya ɗauke ta da mari tare da zazzaro mata ido yana cewa.

"Baki da hankali ne, cikin rashin respect zaki ambaci sunan sa kai tsaye? to bari kiji shine mai wannan kamfani gaba ɗaya...."

Security yayi magana yana nuna girman kamfanin da hannunsa, sannan ya cigaba da cewa

"Duk mu ɗin nan da kike gani shi yake mulkan mu, a ƙarƙashin sa muke..."

Wani daga cikin security ne ya ce

"Haba dallah, har sai ka tsaya kana ɓata yawun bakin ka wurin mata explain... ta je bamu san shi ba..."

Amal tana kuka tana riƙe da fuskarta da ta sha mari ta ce
"Dan Allah ku taimaka wallahi saboda Maleekh nazo garin nan..."

Security cikin tsawa ya ce
"In baki gyara wannan sunan ba sai mun karairaya ki a wurin nan..."

Cikin kuka ta ce

"To Yalla6ai Maleekh..."

Wani irin ran'kwashi security gabanta yayi mata a tsakiyar kanta yana faɗin

"To dole sai kin furta Maleekh ɗin ne a gaba?...."

Amal 6are baki tayi tana kuka hannunta a tsakiyar kai tanashafawa ta ce

"Ya Y YA Yalla6aiiiiiiii...."

Security ya ce

"To bai zo ba, sai ki jira zuwa jumawa, kije can ki zauna ki jira shi..."

Amal ta juya tana kuka hannu a tsakiyar kai yana mulmula wurin rankwashin... hannu ɗaya kuma na riƙe da jaka...

Amal ta zauna a ƙarƙashin inuwa a wajen nesa da get sosai, jikinta ya yi sanyi saboda yunwa da gajiya, ta zauna a gefe tana kallon yadda ma’aikata ke shige da ficen kamfanin CashTalk...

Ta juma sosai, tin safe har yanzu misalin ƙarfe 12 na rana.
Tana zaune kawai sai taga wata babbar mota mai haske white color, ta shawo kwana da gudu.
Motar ta tsaya a gaban gate, sai ga security suka ruga da gudu, suna buɗe masa get cikin ladabi da girmamawa.

Motar ta shige cikin harabar kamfanin, aka rufe gate. Amal ta runtse idanu da sauri, zuciyarta na bugu da ƙarfi: “Shine kenan... Maleekh ɗin da nake nema,

15 / 82