Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
amma al’umma ta hana su damar rayuwa.
Saboda kawai ba su da suna, ba su da kuɗi, ba su da iko… an kashe muryarsu.”
Amal cikin kuka Ta ce:
"May Allah grant them peace. Ameen."
A lokacin da take magana, a can nesa a England, Maleekh na kwance kan gadon sa, yana sanye da 3quarter a jikinsa da singlet, laptop ɗinsa na nuna live stream na Rayuwa FM. ya harari screen ɗin yana tura keyboard da karfi.
Ya ce:
“Damn it! wannan yarinyar har yanzu tana da baki? ta ɗauki kanta kamar wacce tasan komai... Ƴar talakawa ke baƙin ciki da soyayya...”
Yana buɗe wata folder a laptop ɗinsa wanda yake ɗauke da sunan:
"CASH TALK FM PRIVATE."
Maleekh yana murtuƙe fuska yana faɗin:
“Zan janye ta daga Rayuwa FM... by force or by money... She will work for me. She must!”
Sai ya ɗaga waya ya ƙira wani hadiminsa daga Abuja.
Maleekh Ya ce
“Hello!...Prepare the contract, i want Amal Abdulsamaad. She'll join us at CashTalk FM. Abuja is waiting...”
Bayan Amal ta ci gaba da aikinta a Rayuwa FM, koda yake tana ƙunshe da damuwa a ranta sakamakon matsin lambar siyasa da kuma saƙonnin barazana da ake aiko mata daga Abuja TV. Duk da haka, ta cigaba da shigowa cikin shirye-shiryenta cikin ƙwazo, musamman shirin “Ra’ayinka Hakkinka” inda take ba mutane dama su bayyana damuwarsu game da rayuwa da halin ƙasar.
Sai dai, bayan kowanne shiri, Amal ta fi zama shiru a cikin office. A zuciyarta tana jin kamar tana yaƙi ne da manyan da ke son murƙushe ta, amma shawarwarin Inna kullum su ke kwantar mata da hankali:
"Ki tsaya da ƙafafunki, Amal. Talaka baya rasa daraja idan har yana da gaskiya da himma."
A Ƙasashen Waje
A can England, Maleekh Cashbank ya gama tsara duk wata hanya da zai jawo Amal zuwa sabuwar tashar sa, CashTalk FM. Amma ba don yana sha’awar ta ba, A'a, yana so ne ya mallake ta da kuɗi, ya ɗorata a ƙarƙashin ikonsa, domin ta yi masa mummunan rauni a gaban duniya.
Yana zaune cikin ɗakin sa na musamman, yana duba zafafan shirye-shiryen Amal da ke ta yawo a social media, yana wani tsaki da cizon yatsa. Kallonsa ya koma sama, ya furta:
"Ƴar talakawa ce fa! Me yasa nake jin kamar maganganunta suna shiga jikina? wannan wulakancin da ta min ta rediyo sai na rama shi a duniya."
Ya buga laptop ɗinsa da ƙarfin zuciya, yana ƙara hura hayaƙin shisha...
Location: Kaduna...
Amal ta samu wani ƙira daga wata baƙuwar lamba a cikin mako, tana ɗagawa sai wata murya ta ce:
"Miss Amal, muna so mu tattauna da ke akan wata sabuwar dama a tashar rediyo, muna neman fitattun muryoyi masu rinjayar jama’a."
Amal Ta ce:
“Waye ke magana? Kuma wace tasha ce?”
Other site:
“Zaki ji komai idan kika zo Abuja, muna fatan zaki ɗauki wannan damar da gaske.”
Amal ta amsa cikin ladabi amma a zuciyarta ta ƙuduri aniyar ba zata sake barin Rayuwa FM ba....
★★★
Maleekh ya aika da tawagarsa ta PR su je Kaduna a asirance domin su fara tattara duk wata dama da zata iya kawo Amal zuwa CashTalk FM. Ba don yana buƙatar taimakonta ba, sai don ya wulakanta ta ya nuna mata duk ilimin ta da basirar ta ba zasu hana shi murɗa ta ba......
NEXT TARGET 🎯🎯
READERS INASON JIN DAGA BAKIN KU, A CIKIN AMAL DA MALEEKH WAYE KUKE SON JIN SCENE ƊINSA?....
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 5 to 6
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
___________________________________________
Kaduna Gidan rediyon Rayuwa FM
Amal ta dawo cikin ayyukanta amma a bayyane take cewa "An fara sanyaya yanayin da nake ciki..."
Daga ranar da ta gabatar da shirin da ya fallasa yanda wasu ‘yan siyasa ke yin amfani da talakawa don cimma burinsu, wasu na jin tsoro, wasu na jin karayar zuci amma Amal bata tsaya biye wannan ba.
A bayanin ta a gidan rediyo Tana cewa:
“Ku sani, talaka ba ƙaramin abu bane, kada ku yarda a rinƙa amfani da ku a lokacin zaɓe, sannan a watsar da ku bayan an ci zaɓe, Kuyi hankali da waɗanda ke muku alƙawuran ƙarya. Ku tambayi kanku: ina ƴan takara suke bayan zaɓe?”
Wannan magana ta yaɗu sosai, har aka ɗora ta a TikTok da X (Twitter), inda mutane suka rinƙa cewa:
“Amal ce muryar gaskiya!”
“Allah ya kare ki Amal, daga sharrin masu sharri...!”
Amma akwai wasu da hakan bai yi wa daɗi ba.
Bayan kwana biyu
Wata rana, Amal na tsaka da shiri a ofis ɗin Rayuwa FM, sai aka kawo mata wata leda mai ɗauke da kwali. A ciki akwai envelope guda ɗaya, a jiki aka rubuta:
"Ki yi shiru kafin a rufe miki baki da ƙarfi."
Cikin takardar, akwai hotunan Amal tana fita daga gidan rediyo da kuma wasu bayanai da ke bayyana cewa ana bin sawunta. A ƙarshe akwai kalmar da taji wanda ya sanyaya mata zuciya:
“Mu muna da ikon gyara muryarki kar ta mutu.”
Amal ta daɗe tana kallon takardar. Hankalinta ya tashi, amma ta daɗe kafin ta nuna damuwa a fili. A zuciyarta, tana addu’a kawai. A bakin ta kuwa murmushin ƙarfin hali take tare da faɗin:
“Toh su sani zan cigaba da faɗan gaskiya. Idan zasu kashe ni, to su fara kashe gaskiya gaba ɗaya kafin nan...”
Bayan Amal ta dawo gida da dare, tana zaune a ƙasan tabarma gaban Inna tana ta ƙarewa letter barazana da kallo. Inna na kallon fuskarta, cikin damuwa ta ce:
“Ki daina gaya musu gaskiya cikin ƙarfin murya haka Amal. Ki tausaya mana. Me zamu ce idan wani abu ya same ki? Gaskiya gaskiya ce, amma a Nigeria gaskiya tana buƙatar wayo.”
Amal ta share hawayenta. Ta ce:
“Inna, idan muka yi shiru, su waye zasu kare talakawa? Idan ba ni ba, wa zai faɗi makircinsu? Su sun daɗe suna rura wuta, yanzu lokaci yayi da za’a haska gaskiya.”
A can Abuja, wasu manyan mutane sun fara tattauna yanda zasu “rufe bakin Amal” ta hanyar amfani da hukumar da ke kula da watsa labarai National Broadcast Control Commission.
Sun nemi hukumar ta dakatar da Amal daga gabatar da shirye-shirye saboda "kalaman tada zaune tsaye".
A yau an samu wata jarida da ta fara ɓata sunanta da wasu rubuce-rubuce marasa tushe, suna cewa:
“tana tada zaune tsaye ne saboda tana neman suna daga ƙungiyoyin waje.”
Duk da waɗannan matsaloli, Amal ta koma rediyo da safiya take cewa cikin murya mai ƙarfi:
“Wanda ke tsoron gaskiya shi ke son murɗe ta. Amma ku sani, mutuwar muryata ba zata rufe gaskiyar da ta fita daga bakina ba. Idan Allah Ya so, rayuwarmu zata canza.”
A lokacin da take faɗar hakan, Maleekh yana duba ta daga laptop ɗinsa a England, kifa kansa ya yi a kan tebur yana furta:
“Wannan yarinyar ba ta tsoro? me yasa na kasa kawar da tunaninta a raina?”
Tsaya wa ya yi tare da wani ɗan nazari daga baya ya ɗauki wayarsa tare da ƙiran wani Manager campanyn sa a Nigeria garin Kaduna, kamfanin gudanar da kasuwancin chanjin kuɗaɗe daga Dala zuwa Naira da kuma kamfanin tace finafinai da shooting, sunan kamfanin sa CASHBANK hakan yasa ake ƙiran sa da suna Maleekh cashbank, asalin haifaffen garin Kaduna ne iyayensa suka koma Abuja amma akwai sauran family a Kaduna,
Bayan ya ƙira Manager bugu ɗaya aka ɗauki ƙiran,
Manager ne ya fara faɗin:
"Hello Sir! Barka da wannan lokaci...."
Maleekh cikin izzah yana yamutsa fuska Ya ce:
"Campany na! komai yana tafiya normal?..."
Manager Ya ce:
"Komai normal Ogah, ana tafiyar da komai yanda ya kamata, sannan ana samun ƙaruwa sosai...."
Maleekh Ya ce:
"Good! Gobe da safe zan shigo Kaduna, inaso zan ziyarci gidan rediyo Rayuwa FM, sannan zan zauna na ɗan wani lokaci domin gudanar da aiki a kamfani na...."
Manager Ya ce:
"Haba Ogah ka rasa ina zaka kai ziyara sai a wannan ƙaramin gidan rediyo? ga manya-manyan gidan rediyo masu capacity....."
Kafin manager ya ƙarasa maganar Maleekh ya katse shi da cewa
"Nan nayi niyyar zuwa...zan sauƙa a gidana na GRA a mun gyara na musamman...."
Manager Ya ce:
"Okay Sir...."
Daga nan suka yanke wayan...
Maleekh ya sa a karɓa masa tikiti domin a yau zai bar England, yana so zai sauƙa a Abuja domin gaishe da iyayensa, idan ya kwana da safe sai ya wuce Kaduna.....
Bayan Awanni Maleekh ya sauƙa a Nigeria, motoci sun fi goma waɗanda suka zo ɗaukan sa a airport, iyayensa sun yi matuƙar farin ciki da ganinsa tsawon shekaru a ƙasar england, duk da su ma iyayen suna yawan zuwa ƙasashen waje har su ziyarce shi...
Maleekh shine babban ɗa a wurin Minister Alhaji Abdul-Majeed. sai ƙannen sa mata biyu, bayan ya bawa iyayensa isasshen lokaci washegari da safe sai da ya ziyarci gidan rediyon sa mai suna CashTalk FM. ba ƙaramin kuɗi aka kashe a wurin ba, komai na musamman, duk ƙofofi da winduna na glass ne, upstairs mai hawa takwas ne a gidan rediyo, amma ba'a fara gudanar da aiki a cikin sa ba, wurin yana nan a tsare sai matakan tsaro da aka zuba da sojoji....
Yana gama wa da nan kai tsaye Kaduna ya nufa amma a wannan lokacin shi kaɗai yake tafe ba escort, domin idan ya isa akwai wasu security sa acan masu jiran sa...
A gidan rediyo Rayuwa FM kuwa an sanar musu cewa zasu yi babban baƙo, an tanadar masa wuri na musamman.....
Ya sanar wa mutanen sa cewa sai ya fara sauƙa a masauƙinsa dake GRA kafin ya zo gidan rediyo...
Bodyguard's ne sun kai sha biyar waɗanda suka je gidan rediyo, suna tsaye da bindigu a hannayensu, kowa yasan cewa za'a yi babban baƙo kuma sun san ɗan hamshaƙin mai kuɗi ne, mai ji da kansa domin kaf Kaduna babu wanda bai san Maleekh cashbank ba da Mahaifinsa Alhaji Abdul-Majeed...
Da wasu baƙi na musamman masu kuɗi kafin kace mai wurin ya cika da motoci masu bala'in tsada, domin kaf ƴaƴan masu kuɗi ne babu talaka a cikin su ko mai rufin asiri.. kafin zuwan Maleekh..
Director gidan rediyo ya sanar wa Amal ta waya cewa ta fito da wuri domin akwai hira ta musamman da zata jagoranci shirin.....
★★★★★
A cikin wata safiya mai ɗan sanyi a Kaduna, Amal ta tashi daga karamin ɗakin da ta ke tare da Inna, tsohuwar da ta raineta tun tana shekara biyar. Ta shirya cikin doguwar riga mai launin ruwan-saman madara ta ɗaura gyale a kai, sannan ta ɗauki jakar aikin gidan rediyo. Yau akwai wani shirin tattaunawa da za ta jagoranta, ba ta san cewa shi ne zai zama karo na farko da za ta haɗu da Maleekh ba.
A gefe guda kuma, Maleekh ɗan gidan Minister yana sanye da rigar designer, agogon zinare a wuyan hannunsa ya fito daga sabon masauƙin sa a GRA, lokacin yanzu yana ɗokin bayyana sabbin manufofin da zai tallafa wa kamfaninsa. Manajan sa ya shirya masa hira da tashar rediyo domin ya yi tsegumi ga jama’a game da sabuwar kungiyar tallafawa al’umma da su ka kafa. Amma a zuciyarsa, hira ce kawai za ta ƙara masa sunayen jaridu, ba wai ya damu da jama’a ba.
A Studio ɗin Rediyo
Lokacin da Amal ta ga jerin baƙin da za su shiga shirin, ta ɗan murmusa, sunan Maleekh Cashbank ne a rubuce, a cikin ranta Ta ce:
“Hmm, waɗannan ƴan manya ne da ke yawan ɗaukan iska,” ta furta a hankali. Ta gyara na’urorin sauti, ta ƙira editan shirin Ta ce:
“Ku tabbatar an dai-daita mic ɗin babban baƙon, kar ya zo ya fara ƙorafin ‘voice quality.’ ”
Ba a ɗauki lokaci ba, ƙofar studio ta buɗe. Shigowar Maleekh ta cika ɗakin da ƙamshin turarensa mai tsada, sannan yana wani ji da kai kamar shi kaɗai ne mai kuɗi a faɗin duniya, Ya kalli Amal daga sama zuwa ƙasa, kamar yana tantance ta.
Maleekh a zuciyarsa yana faɗin
" Haka kawai za a ce wannan ce mai jagorantar shirin? Wata ƴar diploma da ita...."
Amal a zuciyarta Ta ce:
"Tafiya ɗaya ne da yaro mai jin kansa, zan nuna masa ba duka za a wulaƙanta ba...."
Amal ta yi masa sallama cikin ladabi da kwanciyar hankali. Ta nuna masa kujerar zama da microphone, sannan ta fara shirin da sallama ga masu sauraro.
Sauti na kunna intro jingle…
Amal cikin sassanyar murya Ta ce:
“Assalamu alaikum warahmatullah. Masu sauraro barkan mu da warhaka daga tashar Rayuwa FM. Ni ce Amal Abdulsamaad, kuma yau muna da baƙo na musamman… ɗan siyasa, ɗan kasuwa, kuma ɗan gidan Minister, Malam Maleekh Abdul-Majeed. Barka da zuwa.”
Maleekh cikin dariyar ƙasaita Ya ce:
“Barkan ku Amal. Yana da kyau ganin yadda kuke ƙoƙari… duk da cewa studio ɗin nan da ku kanku sai kun ƙara tsabtace kan ku kaɗan...”
Ya ƙare kallon ta daga sama.
Amal cikin murmushin ladabi Ta ce:
“Za mu yi la’akari da shawarar ka… mun gode. Za mu fara da tambaya: mene ne dalilin dawowar ka Najeriya bayan shekaru da dama a ƙasashen waje?”
Maleekh Ya ce:
“Hmm, kin sani, wasu daga cikinmu ba za su iya rayuwa da ƙalubalen waje ba. Ni dai na ɗauki digiri na acan, sannan na yi Masters ɗina a England, sannan na yanke shawarar cewa lokaci ya yi da zan taimaka wa ƙasata. Yana da wahala ki fahimta idan baki taɓa fita daga Najeriya ba.”
Amal cikin sakin fuska Ta ce:
“Wannan ra’ayi ne mai kyau. Amma na sani yawancinmu da muke nan cikin ƙasar muna iya bada gudummawa, koda ba mu taɓa fita ƙasashen waje ba.”
Maleekh ya zaro ido, yana ɗan dariya sannan Ya ce:
“Toh kenan Amal, idan zan tambaye ki a ina kika tsaya ne a karatun ki?”
Amal Ta ce:
“Na gama diploma a fannin sadarwa. Kuma ina ci gaba da karatu yanzu a matakin digiri.”
Maleekh ya kwashe da dariya tare da faɗin:
“Diploma? Subhanallah. Wannan ai kamar keke ne a gaban mota! Amma kinsan ba laifin ki ba ne, ai ba kowa ke da damar zuwa Cambridge ba.”
Ya tafa hannayensa biyu yana dariyar raini yana faɗin:
“Ku dai ƴan talakawa ku na jin kuna da ilimi, amma…”
Ya kawar da fuskarsa gefe, sannan ya tofa yawu a gefe ɗaya kamar yana ƙyamar abin...
Amal ta ɗaure fuska, tana danne zuciyar ta cikin kwanciyar hankali Ta ce:
“Eh, gaskiya ne. Ba kowanne ne yake da damar zuwa Cambridge ba. Amma ba kowanne ɗan Cambridge ne ke da ilimi na ainihi ba. Wasu su na da takarda, amma babu tarbiyya. Wasu kuma suna da ƙwarewa da mutunci ko da suna da ‘diploma’.”
Maleekh ya ɗan ɗaga gira cikin ɓacin rai Ya ce:
“Oh, ke kina nufin kina da ƙwarewa a fannin rediyo kenan?”
Amal Ta ce:
“Eh. Kuma wannan ya fito fili. Hira ce kake yanzu da ni kuma jama’a suna sauraron ka. Za su iya auna nagarta, ba sai na gaya musu ba. Ilimi ba wai inda ka karanta shi ba ne kawai, har da yadda kake amfani da shi.”
Maleekh yana ɗan harararta Ya ce:
“Kin iya magana sosai. Amma ki sani, a wannan ƙasa, kuɗi da suna ne ke tafiyar da komai. Ba diploma ba.”
Amal Ta ce:
“Eh, amma a kowanne lokaci ƙasar da ke gina kanta kan kuɗi da girman kai faɗuwa ƙasi take Amma ƙasar da ke amincewa da kishi, basira da aiki tuƙuru tashi sama take....”
Gaba ɗaya shiru suka yi cikin studio. Edita da sauran ma'aikata suna kallon juna. Kowa na sauraron tattaunawar..
Maleekh ɗan yatsina fuska ya yi, tare da ɓoye mamakin sa Ya ce:
“…Wannan magana ce mai nauyi. To mu gani a ƙarshe, wanne ne zai fi ƙwaƙwalwa ko kuɗi?”
Amal ta ɗan saki murmushi tare da faɗin:
“Ko wanne yana da kyau a mallake su, zaman lafiya tsakanin su ne zai gina ƙasa. Ba raini ba.”
Sauti yana ƙarewa da outro music...
A karshe shirin ya kare, Amal ta yi godiya ga Maleekh, Da suka fito daga studio, Maleekh ya matsa kusa da ita yana faɗin:
“Kin san dai baki yi min adalci ba, maganar ki ya yi yawa....”
Amal ta sake murmushi ta ce:
“To idan ka san kana son yabo, ka shirya tambayoyi kafin hira amma ni aikina na ke yi.”
Kafin ya yi ƙarin magana, wata ƙiran gaggawa ta shigo wayarsa. Maleekh ya yi tsaki ya juya, ya tafi ba tare da sallama ba amma zuciyarsa ta fara tunanin wannan yarinya mai kuzari.
Maleekh ya bar studio ɗin da zuciyar sa a ɓace, amma yana ɓoye baƙin cikin sa saboda mutanen da yake tare da su...
. Amal ta dawo ofis cikin numfashi mai nauyi, amma tana jin daɗin yadda ta tsaya da mutuncinta. Wannan ya zama matakin farko na rikici, kuma watakila farkon juyawar tunanin Maleekh kenan ...…
Bayan rana guda, wani bidiyo na shirin ya yi trending a social media. Masu sauraro sun yaba da yadda Amal ta ɗan yi masa “ƙwaɓe” cikin ladabi. A gefe guda, an fara sharhi kan girman