Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 82

78K to 81K   out of 244.2K words


*🎤AMALEEKH🎤*


*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.


*Writing and Storytelling By*

Asma'u Muhammad Auwal

Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*

*MARUBUCIYAR:*

*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*

Bauchi State Nigeria.

*WhatsApp 09065443871*

Follow my channel 👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


BOOK ONE page 29 to 30

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹

Ɓangaren Amal kuwa bayan ta koma gida..

Tana shiga cikin falon gidan da sallama, zuciyarta cike da gajiyawar rai, sai ga Inna da ke zaune tayi tagumi, idonta cike da hawaye. Da jin muryar Amal ta firgita, ta miƙe da sauri kamar za ta faɗi.

Inna da kuka, ta rungumi Amal da ƙarfi tana faɗin

“Alhamdulillahi, Alhamdulillahi! Na san ai dole Maliku ya karɓo ki daga hannun waɗancan ƴan sandan nan. Allah ya tsare ki, Amal na… Wallahi ina tsoron kada wani abu ya same ki!”

Amal ta ji jikinta ya ɗan yi sanyi, ta rungumi Inna sosai kamar ƙaramar yarinya da ta dawo jikin uwa. Hawaye suna zuba daga idonta, tana goge wa Inna hawaye..

Ƴan aikin gidan da ke cikin kitchen suka fito da gudu, kowacce ta rungumi Amal, suka ce cikin farin ciki

“Alhamdulillah! Mun yi kewarki Hajiya Amal! Kin dawo lafiya, mun gode wa Allah!”

Falon ya cika da hawaye na farin ciki da godiya wa Allah, kamar ba su da abin da zasu ce sai

“Alhamdulillah”.

Amal ta zauna a kujerar falon, tana goge hawaye, ta dubi kowa da murmushi cikin kuka, ta ce:

“Ku daina damuwa, ku kwantar da hankalinku. Ni dai Allah ya ceto ni, wallahi idan ba saboda Maleekh ba, da yanzu ban san halin da nake ciki ba…”

Kowa ya jinjina kai, falon ya koma cikin shiru na tausayawa, amma a zuciyar Amal akwai wani irin nauyi da ƙuduri na cewa dole ta fuskanci wannan ƙalubalen da karfin imani.


A can hospital kuwa..

An sallami Farha daga asibiti, an dawo da ita gida. ta shiga ɗakinta ta zauna Ammy itama ta shigo tare da zama a kusa da ita... Fuskar Farha cike take da damuwa, koda yake har yanzu akwai ɗan murmushi saboda farin cikin samun kulawar Ammy..

Farha ta ɗago ta dubi Ammy cikin raunin murya ta ce

"Ammy, dan Allah yanzu ya zanyi in shawo kan Maleekh zuwa gare ni..? Kullum sai gudu na yake..."

Ammy ta kalleta da idanu masu cike da ƙauna da kuma tsananin ƙuduri, ta kama hannun Farha tana shafa shi ta ce:

"Ina so ne, Farha, nasa ranar baikon ku. Ba zan wani ɓata lokaci ba."

Idon Farha ya cika da walƙiya na farin ciki, ta sau murmushi na jin daɗi, ta rungumi pillow tana jin kamar mafarki take, ta ce

"Ammy, idan har da gaske haka ne, ai yana da kyau mu haɗa ranar baiko da ranar birthday ɗinsa. Kin manta kuwa? Jibi ne birthday ɗinsa..."

Ammy ta yi dariya cikin jin daɗi, ta girgiza kai:

"Taya zan manta shekarun yarona? Tabbas jibi zai cika shekara talatin cifff. A ranar birthday ɗin, bayan kowa ya taru, zan mayar da ita rana ta musamman ranar baikon ku ke da shi. Zan ƙira dangi, abokan arziki, har da iyayenki daga London."

Farha ta zaro ido cike da murna, ta riƙe hannun Ammy tana murza shi tare da faɗin

"Ammy, wannan fa bazai zama abin alfahari ba kawai, zai zama mafarkin rayuwata! Amma shi zai yadda da wannan baikon? Kinsan fa Ya Maleekh baya ƙaunata kamar yanda yake faɗa..."

Ammy ta danne murmushi, ta yi ƙwafa, sannan ta jinjina kai cikin girmamawa da girman kai irin na uwa mai iko ta ce

"Farha, ki bar wannan damuwar a hannuna. Zan tilasta shi. Daga yau za a fara shirye-shiryen birthday ɗinsa. Zan sanar masa ya fara gayyatar abokansa da sauran jama’a. Amma maganar baiko? Wannan sirrinmu ne. Ba za mu sanar masa ba sai a ranar birthday ɗin. A lokacin, babu yanda zai yi domin bazai iya bijirewa ba, saboda kowa zai taru, sai dai ya amince dole."

Farha ta sake dariya cikin farin ciki, ta jingina kanta a kafaɗar Ammy tana furta cikin sirri:

"Ammy… kina da hikima sosai. Wallahi ina sonki da zuciyata dukkaninta."

Ammy ta shafa gashinta a hankali, tana murmushi mai cike da annashuwa ta ce

"Ni ma ina sonki, ƴata. Ki kwantar da hankalinki. Jibi rana ce da ba za ki taɓa mantawa da ita ba."

A haka Farha ta kwanta saman gado tana ta tunanin yadda wannan ranar zata zame mata babban nasara, zuciyarta na cike da mafarki da buri. Ita kam Ammy kuwa, zuciyarta na daɗa ƙarfafa cewa zata cimma burinta na ganin ɗanta ya auri Farha, ko da kuwa hakan ba da yardarsa ba.

Bayan Ammy ta bar ɗakin Farha, part ɗin Maleekh ta nufa...
Tana zuwa ta fara knocking, a hankali yazo ya buɗe mata...

Ta shiga sannan ta zauna akan sofas falonsa, ta bashi umarnin ya zauna kusa da ita, shima zama yayi, Ammy ta riƙe hannunsa tana murmushi ta ce

"Suprise my son.."

Maleekh yace "Suprise ɗin me?.."

Ammy ta ce

"Jibi birthday ɗinka, za'a haɗa dinner party na musamman, zan sa a shirya mana hall mai girman gaske, a shirya komai zuwa jibi.."

Maleekh ya ce

"congratulation to me.."

Ammy ta ce

"Inaso ka gayyato abokanka na kasashen waje dana nan Nigeria....sannan iyayen Farha zasu zo daga London.."

Maleekh ya ce "Shikenan idan sun zo, sai su ɗauki ƴarsu su tafi da ita, domin bazata lalace da shaye-shaye anan gaban mu ba, mutane zasu ce don ba ke kika haifeta ba shiyasa kika barta ta lalace, kinga daga shaye-shaye zata fara bin maza..."

Ammy ta ce

"Ya isa haka Maleekh, dan Allah kada idan iyayenta sun zo ka nuna musu ƙiyayyar da kake yiwa ƴarsu.."

Maleekh ya jinjina kai yana kallon gefe..

Daga nan Ammy ta fice a ɗakin ba tare da ta sanar masa maganar baikonsa da Farha ba...

Washegari Ammy ta sa an fara shirye-shiryen party birthday ɗin Maleekh...


RANAR BIRTHDAY DINNER, PARTY NA MALEEKH

An kai ga ranar da Ammy ta sha alwashin ta zamarwa ɗanta suprise. Tun daga safe gidan ya cika da hayaniya da shirye-shirye. Ana shiga ana fita, an ɗauko masu kwalliya, decorators, caterers, DJs, da security.

An zaɓi Hilton Event Center a cikin Abuja, hall ɗin da aka san shi da girma da walwala. Aka kawata wurin da gold da white. Daga ƙofar shiga har zuwa ciki, aka shimfiɗa red carpet, tare da golden lights da balloons masu kyau.

A tsakiya an kafa manyan LED Screens suna nuna hotunan Maleekh tun yana ƙarami har zuwa girmansa. A gefe kuma aka kafa photo booth da aka rubuta:

✨ “Maleekh @30 – The King’s Birthday Dinner” ✨

An shirya teburori masu kyau da gilashi mai ƙyalli, aka sa fresh roses da candles a tsakiyarsu. Kowa da aka gayyata yana samun invitation card mai golden foil, saboda VIP event ne.

Lokacin da manyan baƙi suka zauna, aka kunna background music. Aka kashe wutar hall ɗin gaba ɗaya, sai fitilu masu colour suka fara haskawa.

Sai jin ƙarar horn ɗin motor daga wajen hall, alamar cewa Lamborghini Urus mai launin black-gold ta iso.

Security masu baƙin suits suka buɗe masa hanya.. Cameramen ne suke ta ɗaukar hotuna, dron ɗin sama yana capturing cinematic entry ɗinsa.

Maleekh ya fito cikin royal tuxedo mai launin navy blue da golden tie, yana tafiya a kan red carpet kamar sarkin da ake masa coronation. Duk hall ɗin ya tashi da tafi da murna.

PROGRAM ENTERTAINMENT

MC (AY) ya ɗauki mic yana yiwa kowa barkwanci cikin annashuwa... Sai kuma DJ mai suna DJ Neptune ya saka kiɗa mai armashi.

Live Band suka fara rera waƙa domin Maleekh, suna cewa “Happy Birthday, The King @30”.

An yi special dance presentation daga ƙungiyar rawa cikin uniform mai kyau.

Wani celebrity singer, Davido, ya rera waƙa ta musamman domin bikin birthday...

Bayan shagalin farko, aka buɗe buffet. An kawo abinci kala-kala:

Nigerian Dishes: jollof rice, fried rice, tuwo da miya.

Intercontinental: Chinese noodles, pizza, pasta.

Seafood section: prawns, shrimps, lobsters.

Dessert corner: ice cream, chocolate fountain, cake slices, da fruits carving.

Drinks kuma kala-kala: mocktails, cocktails, champagne popping, har da tiger nuts da zobo ga masu avoiding alcohol.

(Kan bala'iiii har da ni a wurin cin Abinci domin mu acici ba'a barin mu a baya🤣🤣)

BIRTHDAY CAKE

An shigo da cake mai layers 7, mai launin gold da white, wanda aka kawata shi da diamonds designs. A kan cake aka rubuta

🎂 “Happy 30th Birthday, Maleekh The King” 🎂

Maleekh ya yanka cake tare da Ammy da Farha a ɗayan gefensa, aka kunna fireworks a cikin hall...

Bayan an gama didimar Birthday sai kuma

SURPRISE ANNOUNCEMENT 😳😳

Bayan kowa ya zauna cikin farin ciki, Ammy ta miƙe tsaye da mic a hannunta. Tana murmushi cikin nishaɗi, ta ce:

“Alhamdulillah. Yau rana ce ta farin ciki a gareni da iyalaina. Na ga ɗana ya kai shekara 30, kuma Allah ya yi masa arziki, lafiya, da daraja. Amma wannan ba kawai birthday bane…”

Kowa a hall ɗin ya ɗaga kai cikin mamaki.

“…bayan birthday sai kuma ranar baiko a yau. Ina farin cikin sanar da ku cewa yau ɗana, Maleekh, zai ɗaura baiko da Farha.”

Hall ɗin ya ɗauki ihu da mamaki. Wasu suka tashi tsaye suna tafi, wasu kuma suka dubi Maleekh da ido domin ganin yanda zai yi, shin da son ransa ne ko kuma Suprise ne kamar yanda aka sanar..

Maleekh ya tsaya cak kamar wanda aka yi masa sihiri. Bai taɓa tsammani wannan ba...


Amal tana zaune a falonta, falon da aka kawata cikin nutsuwa da kyan gida na zamani. Wani ƙaramin flower vase ke tsakiyar table, TV ɗin da ke manne a bango kuwa na nuna live cinema broadcast na taron da Ammy ta shirya domin ɗanta.

Amal na zaune ne gefen sofa tana cin abinci a hankali, sai kawai ta ji jawabin Ammy....zaro ido tayi tana kallon TV daga baya MC a hall ɗin ya nanata da cewa:

“Ladies and Gentlemen, please rise and welcome… Farha & Maleekh the couple-to-be tonight!”

Amal ta zabura! Abincin hannunta ya zube ƙasi, kofin drink ɗinta ya biyo baya ya zube a tiles. Hannayenta suka fara rawa, zuciyarta na bugawa kamar zata fito daga kirjinta.

Ta miƙe da sauri, idanunta sun cika da hawaye tana faɗin:

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… baiko? Baiko kuma Maleekh da Farha? Maleekh ya yaudare ni?”

Ta kai hannu kan zuciyarta tana jin wani irin bugawa da ciwo. TV ɗin na nuna Farha cikin wata farar riga mai tsada, rigar da aka kawata da diamonds stones masu walƙiya. An zaunar da ita kusa da Maleekh a kujerar da aka tanadar musu.

Farha ta yi kyau sosai, tana murmushin alfahari, kamar wacce ta ci nasara. Iyayenta daga London suma suna zaune a gaba cikin kujera ta musamman, suna ta tafa hannu cike da jin daɗi da alfahari.

A gefe kuma aka nuna A’isha ƙawar Amal daga Kaduna tare da mahaifiyarta wato kishiyar Ammy, da ƙannenta mata biyu. Sai camera ya nuna Ammy na nuna rashin jin daɗinta, ta ƙarasa wurinsu Mahaifiyar A'isha tana habaici tana cewa:

“Meya kawo ku wannan shagali? Ai ban gayyace ku ba, kuma ku ka zo. Amma dai ku zauna ku gani, wannan baiko ne da ba ku isa ku hana ba.”

Amal ta ɗan ja da baya, tana tari sakamakon kwaruwar da tayi, ta ɗauki ruwa ta kora, hawaye na silalowa. Tana faɗi da ƙarfi:

“Wallahi ba haka ba ne! Taya Maleekh zai mun haka? Kenan yasan da maganar baiko shine ya bani card ɗin gayyata da hannunsa...kuma ya zauna tare da ita?”

Ta fashe da kuka, zuciyarta na tafarfasa. Sai ta ji ƙarfin zuciya ya shige ta.

Ta fice daga gidan ba tare da ta shirya ba. Babu gyaran kai, babu kwalliya, babu mayafi mai kyau. Kawai ta ɗauki jakarta ta rataya a kafadarta..Ta riƙe wayarta da ƙarfi a hannu ɗaya, ta zura takalmin slippers, ta fita da gudu kamar wacce zuciya take tura ta.


A HALL ƊIN TARON

Maleekh kuwa, duk da cewa yana zaune kusa da Farha, gaba ɗaya jikinsa a takure yake. Idanunsa na yawo cikin hall ɗin yana kallon ko'ina domin duba ko Amal tazo..

Ya roƙe ta akan tazo, yana zaune sai kuma ya tuna lokacin da ya bata VIP invitation card yana ce mata:

“Amal, koda duniya zata yi gaba dani, kin zama wata ta musamman a rayuwata. Kawai ki kasance tare da ni ranar, zan gabatar dake a matsayin masoyiyata..."

Amma yanzu babu ita, babu kamshinta, babu murmushinta. Zuciyarsa ta cika da baƙin ciki.

Abokan sa na gefe suna ta murna, suna tura masa cup na wine suna cewa:

“Happy Birthday King Maleekh!”

Amma kwata-kwata baya jin daɗin wannan ranar. A ransa yana cewa:

“Ina Amal? Me yasa bata zo ba? Ko kuwa an dakatar da ita ne? Ko… bata ɗauki rayuwata da mahimmanci ba?”

Ya ji ransa yana tafarfasa, amma bai nuna wa kowa ba...

☆☆☆☆

A wannan lokacin Amal na ta gudu tana ƙiran taxi. Taxi ɗin ya tsaya, ta shige ciki tana hawaye.

Ta ce

“Driver, please… Hilton Event Center… yanzu yanzu, kayi gudu!”

Driver ya dubeta ta madubi, ya ga fuskarta cike da hawaye. Ya ɗaga kai kawai ya ce:

“Okay madam.”

Motar ta yi saurin tafiya cikin titunan Abuja da fitilun titin ke walƙiya. Amal ta jingina kanta jikin glass, hawayenta na gudu tana faɗin a hankali:

“Ya Allah ka bani ƙarfin zuciya. Wallahi idan na shiga hall ɗin, Allah kada ka bawa Maleekh damar da zai amince da baikon nan....”


Wurin nada nisa da gidan Amal, hakan yasa har yanzu bata iso wurin ba.

A hall kuwa ana kan gudanar da wani wasa.
An tayar da Maleekh tsakar filin, aka ɗaura masa farin kyalle a idonsa. Wani wasa ne irin na masu kuɗi, sunan wasan dumi-dumi tsakanin ƙawayen Farha, manyan ’ya’yan masu kuɗi...

Ka’ida: Maleekh zai rinƙa tafiya a hankali, ido a rufe, hannunsa a miƙe. Duk wacce hannunsa ya sauƙa a kanta, ita ce za suyi rawa tare a gaban jama’a.

Shi kuma Maleekh ya tsare fuskarsa da ɗan murmushin dole. A ransa kuwa ba ma wasa yake so ba, ba kuma baiko da Farha yake muradi ba.... Sai dai abokansa da suka fahimci akwai damuwa a tattare dashi sai suka fara lallamin shi akan kada ya nuna rashin jin daɗinsa a bainar jama’a, kada ya kunyata iyaye, kada ya lalata yanayin shagalin. “Ka bari komai ya wuce, daga baya sai kayi komai,” suka shawarce shi...

Sai ya yarda da haka, ya fara tafiya a filin, ido a rufe, yana miƙa hannu, yana neman wanda zai kama. ’Yan matan a gefe kuwa suna tsalle-tsalle da dariya, suna ɓuya suna ƙara motsa nishaɗi. Jama’a suna ta tafi suna dariya.

A gefe kuwa mahaifin Maleekh na zaune, fuskar sa cike da farin ciki da alfahari da ɗansa, yana ta jinjinawa taron.

A wannan lokaci ne Amal ta iso.
Ta nuna card ɗin da Maleekh ya bata tun farko, security suka dubeta, duk da shigar ta ba ta masu kuɗi bace, sai suka barta ta shiga. Tana sanye da doguwar riga, kanta babu gyaran salo irin na taro, ƙafarta sanye da slippers. Hasken fuskarta da kamalarta sun bambanta ta a cikin jama’a.

Da ta shiga, idonta ya sauƙa kan Maleekh da aka ɗaura masa farin kyalle a idonsa. Yana yawo cikin filin, yana wurga hannu yana neman kama wata. Zuciyarta ta buga. Bata tsaya tunani ba ta ruga da gudu ta nufi tsakiyar filin, zuciyarta na tafasa da niyyar kada a aikata abinda zuciyarta zai buga...

Kafin ta yi wani abu, sai ga hannun Maleekh ya cabke ta!..

Lokaci guda ya ji wurin yayi tsittt, ba dariya, ba ihu, ba tafi....ganin haka yasa ɗayan hannunsa ya cire kyallen da aka ɗaura masa, ɗayan hannun kuma yana riƙe da kafaɗar Amal...

A nan idonsa suka haɗu da nata.

Tsitttt!
Wurin ya yi shiru! Kowa ya dakata da numfashi, idanun kowa ya sauƙa kan kyakkyawar fuskar Amal wacce bata daga cikin ’yan matan masu kuɗin....

Wata nutsuwa ta bayyana a idanun Maleekh lokacin da ya gane yana riƙe da hannun Amal ne..

A gefe kuwa Farha da aka zaunar da ita a kujera ta miƙe da zafin rai, fuskarta ta canza daga farin ciki zuwa baƙin ciki, zuciyarta tana tafasa da haushin wannan yarinyar da ta kutsa musu wasa...

Ammy kuwa ta kaɗa kai a fusace, tana hararar Amal, zuciyarta cike da ɓacin rai, tana jin kamar Amal ta zo ta ɓata musu shiri a gaban iyayen Farha da kowa da kowa...

Sai dai A’isha, ƙawar Amal, na cikin jama’a. Ganin Amal ya sanya ta tashi da farin ciki, tayi dariya da tafi tana goyon bayan abokiyar tata...A fusace Ammy ta juyo ta kalle ta tana hararar ta kamar idanu zasu faɗo, ai ba shiri A'isha ta zauna tare da nutsuwa, domin a wurin iya tafin ta ne kawai ya ratsa kunnuwan kowa...


(Ina Amaleekh fan's readers, shin ya ku ka a wannan lokacin?😅😅🫣)


MC, wanda bai san komai game da Amal da Maleekh ba, ya ɗauka wannan al’ada ce ta wasa. Shi ma sai ya nufi mic ɗin ya ce da murya mai ƙarfi:

“Alhamdulillah! An samu wacce aka kama. Yanzu kuwa babu sassauci tare zasu yi rawa!”

Sai ya ƙira DJ ya kunna kiɗan rawa..

Kafin a sake DJ, Farha ta daka uban tsawa cikin zafin rai, ta ɗaga hannu faɗin

“Ku dakata! Ba wani rawar da za a yi a nan. Wannan yarinya ai ba kowa bace face wata matsiyaciya ballagaza! Bata daga cikin mu, wai ita a dole son Ya Maleekh take. ta ƙuduri aniyar cewa sai ta mallake shi!”

Jama’a suka ɗaga kai, wasu suka yi tsit suna kallon abin da zai biyo baya. Amma kawayen Farha da ’yan uwanta kuwa, sai suka kwashe da dariya, suna nuna Amal da hannu, suna yi mata kallon ƙasƙanci da raini...

“Shine zata shigo cikin mu? Ni kam ba zan taɓa yarda ba!” wata daga cikinsu ta faɗa tana harararta.

Sai dai abokan Maleekh ba duka suka ji daidai da wannan kalaman ba. Wasu daga cikinsu suna kallo suna murmushi, suna ganin Amal da gaske ta dace da Maleekh. A idanunsu, kyawunta ya wuce kima, kyakkyawa ce mai tsarin halitta, idan dai

27 / 82