Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   52 / 82

153K to 156K   out of 244.2K words

kallonsa da tambaya.

Ammy ta ce:

“Laifi kuma? Wane laifi?”

Maleekh yana numfasawa cikin fushi ya ce:

“Laifin da ta aikata wa Amal. Farha ce ta haɗa shirin da kawayenta suka tozarta Amal, suka kai ta gidan club, suka mata ƙaryar cewa na ina wurin, sannan suka yi sharri da cewa ta zubar da ciki! Duk ita ce ta tsara komai, saboda kishin da take yi. Sai ta faɗi gaskiya a gaban kowa kafin wannan auren ya tabbata!”

Faloo ya ɗauki shiru.

Farha ta zaro ido, ta kasa motsi.
Ammy ta kalle ta cikin mamaki.
Abbah ya ɗan murmusa, yana kallon Maleekh cikin gamsuwa da jarumtar sa.

Maleekh ya miƙe ya ƙarasa kusa da Farha yana faɗin

“Idan kina so a ce ni mijinki ne, sai kin faɗi gaskiya yau. Idan ba haka ba, auren nan ba zai taɓa faruwa ba.”

Amal ta ɗago kai, hawaye suna sauƙa a kumatunta, amma bata ce komai ba.
Farha ta fara kuka tana faɗin:

"Wallahi Ammy kuyi hakuri, ba haka nake nufi ba… kawai ina son… ina son Maleekh ne shi yasa nayi wannan sharrin. Ban san zai kai haka ba..."

Abbah ya juyo da sauri, yana duban ta da fushi ya ce:

"Farha! Kin san abinda kika aikata kuwa? Kin yi ƙarya akan yarinya marar laifi, kin wulakanta sunanta a gaban duniya! Wannan abin kunya ne, har ga iyayenki!"

Ammy ta share gumin fuska da mayafi tana faɗin:

"To ai abunda ya wuce ya wuce, ba sai an je Television ba. Me kake nufi Maleekh? Kanaso ka zubar da mutuncin ‘yar uwarka ne saboda waccan marainiya? Hakan ba za ta iya dawo da darajarta ba."

Maleekh ya ɗago kai, idonsa ya rine da ƙwalla, amma muryarsa cike da ƙarfi ya ce:

"OK. To a idonku Amal ba ta da daraja, ko? Fine. Amma a idon al’umma tanada matsayi. Kuma zan dawo da martabarta, ta hanyar wanke sunanta daga ƙarya da zargi. Na ɗauki alkawari a gaban kowa sai na goge wannan ƙazantar da aka ɗora mata."

Sai ya juyo da fushi ya dubi Farha:

"Ki tashi yanzu mu tafi kamfani. A gaban kowa, a gaban ‘yan jarida da kafafen TV, zaki faɗi gaskiya. Zaki faɗi abinda kika aikata da bakin ki!"

Farha ta dafe ƙirjinta cikin tsoro, tana kallon Ammy:

"Ammy don Allah… ki ce masa ya barni. Na tuba wallahi…"

Ammy ta ce cikin gaggawa:

"Ba sai an kai hakan ga jama’a ba Maleekh. Ka daina. Wannan magana ta gida ce, mu rufe ta a gida."

Abbah ya sau numfashi yana tsaki ya ce:

"A’a. Ba a rufe gaskiya da sirri. Farha, tashi ku tafi. Ka ji, Maleekh? Kaje ka tabbatar gaskiya ta fito. Ba mu da wani abin da muke tsoro idan gaskiya ce."

Maleekh ya ɗauki makullin motarsa yana cewa cikin daci:

"Mu tafi yanzu. Amma Amal ma zata tafi. Domin yau zan tabbatar duniya ta san cewa ita ce wacce aka zalunta, ba wacce ta aikata zunubi ba."

Sai suka fita gaba ɗaya, Maleekh, Farha, Amal.
Zasu nufi kamfanin CashTalk Media House, da niyyar wanke gaskiya a gaban kowa...


Ammy tana zaune a kujera, tana riƙe da kai cikin damuwa, yayin da Arfat da Islam ke kallonta cikin shiru, Farha na kuka a wajen ƙofa, sai dai ba mai dawowa daga wannan hukuncin da Maleekh ya ɗauka...


🎬 GASKIYA ZATA BAYYANA...

Location: babban studio na TV station, mutane da yawa sun hallara, cameras suna kunne, haske na ɗaukar fuska, murya tana rawa. A gefe Maleekh da Amal suna tsaye, fuskokinsu a cike da damuwa. A gefe kuma Farha ce tana sanye da farar riga mai sauƙi, ba kwalliya, idonta jawur kamar marar bacci, tana kallon camera a gajiye...

🎙️Presenter a hankali ya furta:

“Yanzu muna da bayani mai mahimmanci wanda zai iya canza fahimtar jama’a game da shari’ar Amal da Maleekh... Gaskiya zata fito daga bakin Farha da likita da suka san komai.”

Camera ta tsaya kan Farha. Microphone a gabanta. Jikinta yana rawa...

Cikin kuka ta fara da cewa:

“Ni... ni ce... na jawo komai! 😭
Ni ce na tura Amal gidan club... Na yi mata ƙaryar cewa Maleekh yana can yana jiran ta...

Na kuma tura wasu ƙawayena suka ba ta kwayoyi, suka haɗa mata da abin sha da maye...
Lokacin da ta suma, suka kwantar da ita a toilet suka zuba mata jini a jikinta...
Sannan suka ajiye maganin zubar da ciki a gefe don a nuna kamar ita ta yi ne!”

(ta share hawaye, tana karkarwa)

“Ni... ni ce silar rabuwar da suka shiga. Saboda kishi, saboda tsanar ganin Maleekh na son wata mace fiye da ni...”

(Camera ta ɗan matsa kusa. A gefe Amal ta fashe da kuka, tana riƙe da hannun Maleekh. Abbah yana kallon TV a gida yana girgiza kai. Inna kuwa ta dafe ƙirji tana kuka tana faɗin:

“Subhanallah! Ashe hakane? gaskiyar ta fito... Ashe jikata bata aikata komai ba...”

Farha: ta cigaba da kuka sosai tana bayani..

“Bayan haka... na je wurin Doctor ɗin da ya karɓi Amal lokacin da Maleekh ya kaita asibiti.
Na ba shi kuɗi masu yawa... Na roƙe shi da ya rubuta result ɗin ƙaryar cewa Amal ta zubar da cikin wata huɗu...
Ya yarda... ya karɓi kuɗin... ya karya gaskiya saboda ni... saboda son zuciyata!”

(Ta durƙusa ƙasa tana kuka sosai. Muryar ta na rawa.)

“Na aikata zunubi! Na lalata rayuwar mutane biyu da soyayyarsu ta gaskiya! Na aikata laifi ga Allah, ga Maleekh, ga Amal...”

(Camera ta motsa zuwa likita wanda yake zaune a gefe yana sanye da farar rigar doctors. Ga fuska a farfashe duk ya kumbura kamar wanda yayi hatsarin mota, wannan hukuncin Maleekh ne kafin ya bayyanar da a gaban television..)

Doctor ya ce:

“Eh... abin da Farha ta faɗa gaskiya ne. Ni na karɓi kuɗi daga gareta.
Na rubuta result ɗin ƙarya domin na kare mata suna... Na karya alƙawarin da na ɗauka a matsayin likita.
Na tuba... Na nemi gafara daga Allah da daga waɗanda na cuta.”

(Camera ta dawo kan Farha da Amal. Amal ta kasa tsayuwa, ta durƙusa tana kuka. Maleekh ya rungume ta yana lallashi cikin taushi, ya ce:)

“Na yarda dake, Amal... na yarda dake tun farko, sai dai zuciyata ta kasa yarda da gaskiyata. Amma yanzu na san... kina da gaskiya tun farko.”

Farha tana kuka sosai, tana faɗin:

“Don Allah ku yafe mini... Wallahi ba da gangan nake son kashe muku soyayya ba, kawai zuciyata ce ta rufe ni da kishi!”

(Camera ta rufe da slow zoom inda Amal da Maleekh suka rungume juna tana kuka, Inna tana kallon TV tana hawaye, Abbah yana dafe kai da tausayi, yayin da Farha ta durƙusa tana kuka tana karanto istigfari...)

🎬 Fade out background voice:

“Gaskiya ba ta ɓuya. Ko da ta jinkirta, sai ta fito...”

NEXT NEXT NEXT...


asmeetahwriter✍️

*🎤AMALEEKH🎤*


*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.


*Writing and Storytelling By*

Asma'u Muhammad Auwal

Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*

*MARUBUCIYAR:*

*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*

Bauchi State Nigeria.

*WhatsApp 09065443871*

Follow my channel 👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


BOOK ONE page 59 to 60

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹


Daga cikin gidansu Maleekh labarai a TV suna nuna yadda Doctor da Farha suka amsa laifinsu. Wani ɗan shiru ne ya rufe falon. Bayan nan duniya ta fara girgiza da labarin…

TV na kunne, labarin yana fita:

“...an tabbatar da cewa Farha, tare da haɗin gwiwar wani likita, sun yi amfani da miyagun dabaru wajen cutar da Amal... Hukuma ta tabbatar da kama su don bincike...”

Ammy ta miƙe a hankali daga kujera, tana kallon TV da rikitattun idanuwa.
cikin zafin rai ta ce:

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Maleekh kenan, abun nakan har ya kai ga yaudara mu? har zaka kai ƴar uwarsa hukuma? Ya kai ƴar uwarsa hukuma? Wannan wane irin hauka ne haka?!”

Abbah ya kalli Ammy cikin nutsuwa sannan ta ce

“Maryam ki kwantar da hankalinki... gaskiya dole ta bayyana, ko ta ɓoye shekaru goma. Amma ni ma ban yarda da matakin da Maleekh ya ɗauka ba. Ya kamata ya bari mu muyi hukunci a gida, ba a kai hukuma kai tsaye ba.”

Ammy ta girgiza kai tana hawaye.

“A’a Alhaji! Wannan abun zai tarwatsa zumunci! Farha ai ɗiyar ƙanwata ce... yanzu duk duniya sun ganta a TV kamar wata mai babban laifi, hakan ma bai wadatar ba har sai a haɗa da hukuma?..!”

Zayd ya shigo cikin fushi, yana ɗauke da wayarsa...Yana faɗin

“Abbah, Ammy... yanzu danginmu suna ƙira suna zagin Maleekh a WhatsApp group ɗin family! Wasu suna cewa Maleekh ya fifita wata ƴar talakawa akan jinin jikinsa... kuma nima nace Maleekh bai mun adalci ba, inda kara ai Farha ƙanwata ce jini ɗaya, shin zai iya aikata haka wa ƴar uwarsa uwa ɗaya uba ɗaya?...”

Ammy ta kalli Zayd da ido mai cike da hawaye da fushi ta ce:

“Ai wannan abin kunya ne Maleekh ya aikata, ni dana haife shi ma zai iya yi mun abunda yayi wa Farha balle, Hmmm! yau ya juya mana baya saboda yarinyar da bamu san asalinta ba!”

Abbah ya miƙe, yana kallon su sannan ya ce

“Kuyi shiru kawai! Ku manta da jinin dangi idan ana magana akan gaskiya. Farha ta yi abin da ba ta kamata ba. Likita ya ci amanar ƙasa. Kuma Maleekh yayi abin da ya dace, ya tabbatar da gaskiya. Idan mu ne, mu ma da za mu yi haka!”...

Ammy a hargitse tana kallon Abbah ta ce

"Eh! Ai daman kai da ɗanka bakwa son farin ciki na, duk abinda yayi da mai kyau da marar kyau koda yaushe kana kan goya masa baya, to wallahi zaku ji kunyar duniya ne wata rana..."


Daga nan Ammy ta bar falon..

Shima Zayd a fusace ya wuce ɗakin da yake..

Shiru ya rufe falon. Sai wayar Abbah da ke yin ƙara, ƙira daga wurin ɗan uwansa, Malam Salihu, daga Kano....

Sai ji nayi ABBAH na cewa:

“Salihu, naji... eh, gaskiya ne. Eh, shi ya kai Farha hukuma... to ai doka ta fi zumunci idan zunubi ya wuce ƙima. Ka daina magana da fushi, mu ma muna cikin zafin lamarin...”


Daga nan ya kashe wayar a hankali yana sakin numfashi...


Ƴan uwa sun taru suna kallon TV. Muryar TV na fita, hoton Farha tana riƙe da hannun Police...
Sam babu wanda yaji daɗin wannan al’amarin..

Daga ƙasar london, saƙo ya iske su...
Mahaifin Farha kamar zai yi hauka, ya rasa yanda zai yi, gaba ɗaya yaji ya tsani Maleekh da yarinyar da yayi wa ɗiyarsa wulakanci akan ta...

Mahaifiyarta tana kuka tana faɗin.

“Ya Allah, wannan wane irin abin kunya ne? Maleekh ya lalata sunanmu! Ashe Maleekh bashi da tausayi, sai ya wulaƙanta ƴar uwarsa haka, me muka masa haka?”

Mahaifin yana huci ya ce:

“Wallahi wannan Maleekh ɗin ya raina mu. Ba zai ƙara samun goyon bayanmu ba. Ya fifita wata banza akan jininsa, yanzu abun da zamu yi shine zamu koma Nigeria, domin bazan bari ɗiyata ta wulaƙanta ba...!”

Hajiya Sa’adatu uwar Farha ta ɗauki waya ta ƙira Zayd, bugu ɗaya ya ɗauka. Yana ɗaga wa ta fara zaginsa da cewa:

"Kai wawa ne marar amfani, kana kallon ina har Maleekh zai tozarta ƴar uwarka haka? Meye amfanin zamanka a Nigeria idan bazaka iya kula da Sister ka ba? Mun tura ka can ne fa akan ka sa ido akan Family gidan, sannan ka rasa Maleekh da yarinyar da yake nema amma har yanzu bamu ga wani abun arziki ba, Zayd kana ji ba? Aiki na ƙarshe da zan saka yi mun shine, inaso ka kashe mun Maleekh, bana so na ƙara ganinsa a duniya, daman abu ɗaya ne yasa zan haɗa ƴata da shi shine munaso mu karɓe duniyar da mahaifinsa yake da shi, da shi kansa Maleekh ɗin amma tin da hakan bai yi ba, just ka kawar da shi daga doron duniya...."

Daga nan suka katse wayar...

A washegari jirgin su zai ɗaga zuwa Nigeria...


JAMA’A A SOCIAL MEDIAyy

Hotuna na yawo a Instagram, TikTok, da Twitter. Hashtag ɗin #JusticeForAmal da #FarhaTrial sun ɗauki hankalin jama’a...

COMMENT 1:

“Allah ya saka wa Amal! Yau kowa ya ga irin zaluncin masu kuɗi, Allah ya tabbatar da gaskiyar Amal!”


COMMENT 2:

“Farha da likita sun jawo wa family ɗin su abun kunya. Amma ai gaskiya ta fi komai!”


COMMENT 3:

“Maleekh ya yi abin da ɗan gaske zai yi, sai dai ya lalata zumunci, meyasa bai yi hakuri an magance matsalar a cikin gida ba?”

A TV, ana nuna Amal tana fita daga ofishin lawyers da hawaye a idonta duniya ta fara rarrabe tsakanin masu goyon bayan Amal da masu kare Farha...


GIDANSU AMAL

Inna tana kallo, tana jin labarin da murmushi mai sosa zuciya.

“To Alhamdulillah... Allah ya fito mana da gaskiya. Amma wannan rikici ne da zai shude, mu dai mu ci gaba da addu’a. Gaskiya da zuciya sun fi dangi da dukiya.”

Amal wacce ta dawo gida ta share hawayenta tana kallon Inna..

“Ni banji daɗi da ya kai su kotu ba, Inna... amma ni dai na gode Allah da gaskiya ta fito fili. Duk duniya ta san ba laifi nayi ba.”

Inna ta ɗora hannu a kafaɗarta tana faɗin

“Toh hakane Amatu. Komai ya wuce, sai ki tashi ki roƙi Allah ya sassauta zuciyoyin jama’a. Duniya da baka zaune da ita lafiya, sai gaskiya ta baka kariya.”

Su Malam Yawale sun zuba ido basa cewa komai, tin da Auren nan ya wargaje gaba ɗaya suka cire hannunsu akan lamarin Amal...amma har yanzu suna zaune a gidan..


A wannan ƴan kwanaki.
Ba Maleekh ba hatta Abbah ya samu matsin lamba a wurin ƴan uwa... domin duk dangi babu wanda ya goyi bayan Maleekh...
Abbah yana zaune a part ɗina bakin gado yana ta tunanin wannan al’amarin..

“Lokacin da gaskiya ta fito, ba kowa ne zai iya jure ta ba. Amma wanda yake da gaskiya, ko duniya ta juya, Allah zai tsaya masa.”

Abbah yana maganar zuci...

A babban falo.
Maleekh ya shigo cikin gidan, fuskar sa cike da gajiya, idanunsa sun ɗan kumbura kamar wanda bai kwanta ba tun jiya. Yana shigowa falon Ammy ta taso a zabure. Kafin ya iya cewa komai, ta ɗaga hannu ta zabga masa mari sau ɗaya, sau biyu, sau uku, sau huɗu, har sau biyar a take... har sai da gefe na bakinsa ya fitar da jini, abunka da mai taushin lips...

AMMY cikin ɗaga murya take faɗin:

“Wai me kake nufi da wannan haukan, Maleekh?! Aure kai da Amal na janye! Na janye wallahi! Ni ce na yarda akan ka aure ta da Farha amma yanzu na fasa! Na fasa gaba ɗaya!”....

Maleekh yana tsaye cikin shiru, hannayensa a sake alamun babu wani ƙarfi a tattare da shi, ga saƙonni na zagi da ƴan uwa suke ta turo masa, yana ɗan girgiza kai cikin kunar rai.

AMMY ta cigaba da cewa

“Yanzu ina Farha? Kasa an kaita cell ko? Daga nan sai kotu! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Maleekh, anya ni ce na haife ka kuwa?! Ka zubar mana da mutunci a idon duniya! Kai ɗa ne da ake alfahari da shi yanzu ka zama abin tausayi da zargi!”

Da sauri Abbah ya fito daga upstairs, yana sanye da jallabiya, yana kallon Ammy da Maleekh ya ƙarasa kusa da su.

Cikin muryar tsawa yake faɗin.

“Me ke faruwa ne haka cikin gida? Maryam, me ya faru?”

Tana kuka da huci ta ce:

“Ka tambaye shi, kaima kasan abunda ya aikata ai! Wannan ɗan naka yana da hauka! Farha yarinyar nan yanzu tana cikin cell! Ka tambaye shi me yasa ya saka ta a hannun hukuma kamar wacce bata da gata!”

Abbah ya juya yana kallon Maleekh kai tsaye.

“Maleekh! Wane irin abin kunya ne ka ƙara kawo mana haka? Shin ba ka sanar mana cewa a TV zata sanar ba? Me yasa har da hukuma?!”

MALEEKH cikin muryar tausayi, ya ce:

“Abbah... ba hukuncin kaina nayi ba. Hukuma ta riga da ta shiga cikin case. Babu komawa baya. An samu gaskiya, kuma duk masu laifi sun amsa laifinsu.”

AMMY ta zabura cikin takaici ta ce:

“Ka ce gaskiya?! Gaskiyar me? Wannan ita ce ‘yar da na raina da hannuna, da nake kallon ta tamkar ‘yata! Ka kasa daurewa ka tafi da lamarin cikin gida?”

MALEEKH ya ɗago kai yana faɗin:

“Ammy, babu wanda ya fi ni son a warware komai cikin gida. Amma idan abu ya kai ga cin zarafi, da cutar da wanda bai da laifi to adalci dole ne ya yi aiki!”

Abbah ya ja numfashi mai zurfi yana girgiza kai, zuciyarsa na tafasa da ciwon abin da ke faruwa.

ABBAH ya ce:

“Maleekh, ka sani… rayuwar mutane ba wasa bace. Idan dai kotu ta shiga, to babu wanda zai iya ja da hukuma. Amma, na baka shawara: ka kwantar da hankali, ka bar doka ta yi aikinta kawai...”

AMMY ta juya da hawaye tana kallon Abbah:

“Au kaima Alhaji yanzu haka zaka tsaya masa? Kana ganin ɗanka ya hallaka zumunci? Ni bazan taɓa yarda da wannan auren Amal ba! Tunda har ya zaɓe ta akan ƴar uwarsa, ku je kotu ta yanke hukunci ɗin...!”

Maleekh ya kalli iyayensa da idanu masu cike da tausayi ya furta a hankali.

“Ku yi haƙuri, amma hukuma ta riga ta kama hanya. Kotun ce zata yanke hukunci, ba zuciyar mutum ba.”...

Ya nufi part ɗinsa cikin natsuwa, ya bar Abbah da Ammy cikin mamaki da tsoro yayinda iska mai sanyi ta lulluɓe Ammy...

Ammy ta zube a kujera tana kuka, Abbah na zaune cikin tunani mai nauyi, yana cewa a hankali:

“Rayuwa... idan ɗa ya fara tafiya akan hanyar da yake ganin ita ce adalci, babu wanda zai iya ja da shi.”..


Washegari iyayen Farha sun sauƙa a Airport.
Zayd da kansa yazo ɗaukan iyayensa a motarsa.

Zayd ne yake tambayarsu cewa gidan su Maleekh zasu nufa?..."

Mahaifinsa a firgice ya ce

"Allah ya kiyaye, ai akwai gidan mu anan, don haka akai mu can, ai mun daɗe da raba zumunci da su. Babu mu babu su don haka mu tafi gidan kanmu..."

Zayd ya ce

"Saboda haka yasa nasa aka gyara muku gidan domin nasan bazaku taɓa rayuwa

52 / 82