Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
biki.”
Amal ta ji ƙirjinta ya buga. Wani irin shock ya rufe jikinta gaba ɗaya. Amma ta daure ta yi shiru, ta ƙuduri cewa baza ta bata martani ba..
Sai ta buɗe ƙofar office ta window side yanda take hutawa tana kallon kowa dake ƙasin building..Tana kallon ƙasan compound ɗin daga sama, zuciyarta na yi mata nauyi.
Kawai sai ga Farha ta biyo ta, ta tsaya a ta bayanta, tana murmushin mugunta ta ce
“Me ya faru Amal? Allah yasa yau ba zuciyarki ce za ta buga ba, sai kin ga bikina da Maleekh”
Amal ta ji hawaye sun fara gangaro mata. Ta juya da tsananin kishi da zafin zuciya ta ce cikin rawar murya.
“Irin ranar da kike mafarki kenam? To bazata taɓa zuwa ba. Shiyasa kike addu’ar kar na mutu. Amma ki sani, Maleekh bazai taɓa auranki ba!”
Farha ta yi tsaki tare da faɗin
“Hmm, to mu gani! Shin umarnin mahaifiyarsa zai bi ne ko umarninki? Wacce matsayi kike da shi a rayuwarsa?!”
Amal cikin tsawa ta furta:
“Ƙarya neeeee!!!”
Cikin hargowa suka shaƙi juna, suka fara tururuwar dambe a saman bene, wuri mai cike da haɗari. Daga ƙasa, mutanen company da security suka taru suna kallonsu da firgici.
A nan ne sai aka ga wata mota ta shigo cikin harabar company, motar Maleekh!
Ya fito cikin hanzari, yana ɗaga kansa sama. Ganin Amal da Farha a tsaka da dambe a wuri mai haɗari, zuciyarsa ta tsinke!
Maleekh yana ɗaga murya, zuciyarsa na harbawa ya ce
“Amal!!! Farha!!! Ku dakata da wannan shirmen! Wane hauka ne wannan?!”
Amma basu tsaya ba. Amal da Farha suna faman turje-turje, saboda hayaniya ba sa jin komai.
Maleekh ya riƙe kansa, yana kallon inda suke, zuciyarsa kamar zata tarwatse. Idanunsa suka kaɗa da ja, jin tsoron kada wani abu mai muni ya faru..
Farha ce ta yi turus ta tura Amal baya da ƙarfi!
Amal cikin razana ta yi figici, bayanta ya bugu da ƙarfen da ke zagaye bakin tsalalleku. Sai kawai jikinta ya kife, ta tsallake ƙarfen da baya, ta kai ga faɗuwa ƙasa.
Sai dai cikin azama, Amal ta yi saurin riƙe ƙarfen wurin da hannunta ɗaya. Amma jikinta gaba ɗaya na ƙasa, yana kaɗawa cikin iska. Da zarar ta sake wannan ƙarfen, tana faɗowa kai tsaye mutuwa ce kawai, domin tsakanin su da ƙasa akwai tazara sosai..
Maleekh wanda yake kallon sama yanda suke, zuciyarsa ta yi wani irin tsalle. Cikin razana ya shiga kururuwa:
“Amal!!! Amal!!! Kada ki sake! Ki riƙe! Zan iso gareki yanzu… zan iso…!”
Amal kuwa cikin tsananin fargaba da hawayen tsoro, ta riƙe ƙarfen da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ta kama ƙafar Farha da take tsaye a sama.
Amal tana kuka tana faɗin
“Farha… don Allah… kada ki bari na faɗi…!”
Sai dai, saboda mugunta da hassada, Farha ta fara dukan hannun Amal da ta riƙe ƙafarta. Tana take hannun da ƙafarta, tana yakushin hannunta da ƙarfi domin ta sake ta faɗi ƙasa.
Farha ta na ihu cikin mugunta tana faɗin
“Ki sake ni Amal! Ki faɗi ɗin mana! Duniya ta huta da ke! Maleekh zai zama nawa ni kaɗai!”
Ƙasa kuwa jama’a sun taru suna kallon tashin hankalin da ake ciki, kowa addu’arsa kada Amal ta gaji ta sake ƙarfen..
Maleekh yana ganin haka, zuciyarsa ta yi wata irin guguwa. Ya ruga da gudu cikin gaggawa zuwa elevator, zuciyarsa na bugu kamar ta tsinke ƙirji.
Maleekh a ransa yake faɗin
“Ya Allah, kar ka ɗauke min Amal a haka! Kar in rasa ta a idanuna…!”
Elevator ya kai shi kai tsaye hawa na goma sha takwas. Bai tsaya ko da dakika ɗaya ba, ya fito da gudu kamar mahaukaci. Kai tsaye ya nufi ofishin Amal.
Da ya shigo, ya nufi window sides ya hango Amal a kasalance tana riƙe da ƙarfen da hannu ɗaya, ɗayan hannun nata ta riƙe da ƙafar Farha, yayin da Farha ke ta dukanta da ƙarfi.
A lokaci guda, tsananin ciwon da Farha ta jefa hannun yasa Amal ta sake ƙafar, saboda tsananin gajiya yasa ta sake ƙarfen da take riƙe da shi gaba ɗaya..
Tayi wani irin ihu, cikin kuka ta ce
“Maaaaleeeeekhhh!!!”
A nan ne Maleekh ya yi wani irin tsalle mai ban mamaki ya kama hannun Amal kafin ta yi ƙasi gaba ɗaya...
Maleekh cikin rawar murya yake faɗin
“Amal! Bazan bar ki ba! Bazan taɓa barin ki ba! Ki riƙe ni sosai!”
Amal cikin kuka da firgici ta riƙe hannunsa, jikinta na lumshewa saboda gajiya.
Farha kuwa, ganin Maleekh ya riƙe Amal, ta fara ture shi da ƙarfi tana ihu:
“Ka saketa ta faɗa! Ka barni na huta da ita! Ka saketa, so nake ta mutu ta bar rayuwarka har abada!”
Cikin ɗacin rai, Maleekh ya kasa jurewa. Ya zabga mata mari da hannunsa na hagu...yayinda yake riƙe da hannun Amal da ɗayan hannunsa..
Maleekh cikin tsawa ya ce
“Ke wace irin marar imani ne!? Ke wace iriyar marar tausayin ɗan adam ne!? Ki ture ƴar uwarki haka bayan kinsan ba cigaba da rayuwa zata yi ba, da zaran ta faɗa?!”
Da hannu ɗaya ya ƙara tura Farha gefe, sannan ya ɗaga Amal da ƙarfin zuciya. Ya yi ƙoƙari sosai har sai da ya jan yo ta sama da hannaye biyu, ya rungume ta sosai a jikinsa.
Amal ta saka ihu tana kuka, tana riƙe Maleekh da ƙarfi kamar zata shige jikinsa.
Tana kuka ta ce
“Wayyo Maleekh… na shiga uku…Sauran kaɗan na mutu..!”
Maleekh kuwa yana huci, zuciyarsa kamar zata fashe, yana fitar da numfashi cikin tsananin tashin hankali.
A gefe, Farha cikin tashin hankali, Ta riƙo Amal tana ƙoƙarin janye ta daga jikin Maleekh.
Farha cikin hauka take faɗin
“Na ce maka sai ta mutu! Sai ta tafi yanda ba'a dawowa! Ni kaɗai ce za ta zauna da kai!!!”
A wannan lokacin, Maleekh ya ɗauki kwalbar ruwa mai kauri da ke kan window side table, ya fasa kwalbar da jikin bango, ƙasan kwalbar ta zama makami mai kaifi.
Ya riƙe Farha da ƙarfi, ya manna ta da bango. Idanunsa sun kaɗa da ja, yana shirin caka mata kwalbar a kirjinta.
Maleekh cikin kakkauran murya ya ce
“Kafin ki kashe ta ni zan fara kashe ki Farha! Na rantse da Allah, idan kika sake kusantar Amal zan caka miki wannan kwalbar yanzu yanzu!!!”
Farha ta zaro idanu, jikinta ya fara rawa, zuciyarta ta nuna tsoro karara.
Amal kuwa cikin tsananin firgici da kuka, ta ruga da sauri ta riƙe hannun Maleekh.
Cikin kuka da roƙo take faɗin
“A’a Maleekh… Dan Allah… kada ka aikata haka! Ka dube ni, ni kake son karewa, ni kake so, amma…! Kada ka zubar da jinin mutum saboda ni… Dan Allah ka janye wannan hannun!”
Amal ta sake ihu tana faɗin
“Ka tuna Maleekh, idan ka kashe ta, za ka zama mai kisan kai… Ni ba zan iya rayuwa da hakan ba! Ka ajiye kwalbar, Dan Allah…!”
Maleekh yana rawar hannu, idanunsa na tsananin huci, zuciyarsa na girgiza tsakanin ƙaunar Amal da kuma mugun fushin da yake ji.
Maleekh yana tsaye yana riƙe da kwalbar da aka fasa, idanunsa sun ƙanƙance, jikinsa na rawa. Wani irin huci yake yi kamar zaki da aka tsokane.
Amal kuwa tana kuka tana roƙonsa, tana riƙe hannunsa da ƙarfin hali.
Amal ganin ya ƙi ajiye kwalbar sai za'kami yake tayi ga yana shaƙe da wuyan Farha, ba ƙaramin shaƙa kuma yayi mata ba domin har ta fara firfito da eyes, Amal ta ce da shi..
“Maleekh… ka duba idanuna… ka ga soyayyata gare ka… kada ka yi hakan. Idan ka kashe ta, kai da kanka ka hallaka ni, saboda ni ba zan iya rayuwa da mai kisan kai ba… Dan Allah, ka ajiye wannan kwalbar…”
Wannan kalmomin Amal ne suka shiga zuciyar Maleekh kamar ruwan sama da aka zuba wa wuta. Numfashinsa ya sake nauyi, amma zuciyarsa cike da raɗaɗi da fushi.
Ya ɗaga kwalbar da sauri, sannan da ƙarfi ya jefa ta ƙasa!
Tsssssshhhhh!
Ƙarar fashewar kwalbar ta cika wurin, sassan gilash suka watse a ko’ina. Amal ta runtse idanu tana riƙe da kunnenta saboda tsoro.
Maleekh ya janye daga bangon da ya manne Farha, yana huci da ƙarfi. Hannunsa na rawa, idanunsa sun cika da ƙwallah.
Maleekh da murya mai sanyi da ƙarfi ya ce
“Farha… wallahi kin kusa hallaka ni yau...Amma kin san meye? Idan ba saboda Amal ba… da yau kin daina numfashi. Ki fita a rayuwata, ki fita a raina, ki fita a zuciyata! Na tsane ki!”
Amal ta riƙe hannunsa tana kuka, tana ƙoƙarin kwantar masa da hankali.
Amal ta ce:
“Shhhh… ya isa haka, my bee… don Allah, ka kwantar da zuciyarka. Ka bar komai a hannun Allah…”
Maleekh ya dafe kansa yana huci, sannan ya durƙusa a ƙasa, yana maida numfashi da ƙyar. Amal ta durƙusa a gabansa, ta rungume shi tana hawaye...
A gefe kuwa, Farha tana tsaye tana jijjiga jikinta cikin tsoro, tana mamakin ganin yanda Maleekh ya kusan hallaka ta saboda Amal....
Cikin takaici ta ɗauki kwalbar da ya dagargaje a ƙasi ta yi masa kyakkyawan riƙo kamar zata yanka wani, sai kawai ta saita tsakiyar tafin hannunta ta yanka da ƙarfi...tayi haka ko zata fi samun sauƙin raɗaɗin da take ji a zuciyarta.....
_*NEXT NEXT NEXT*_
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 37 to 38
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Ma’aikatan company da security ne suka ruga da gudu cikin tashin hankali. Wasu suka tsaya a bakin ƙofa suna leƙowa, wasu kuma suka kutsa ciki.
Suka tarar da Amal tana durƙushe tana rungume da Maleekh tana kuka, shi kuma yana riƙe da kanta yana huci kamar zakin da ya ga nama. A gefe kuwa Farha ce take riƙe da hannunta da jini ya ɗan zubo mata sakamakon gilashin da ta yage fatar tafin hannunta da shi..
Gaba ɗaya ofishin ya hau hayaniya, kowa sai tambayar:
“Me ke faruwa haka?!”
“Lafiya dai CEO?!”
Sai kuwa suka jiyo muryar Maleekh, mai ƙarfi cike da fushi, har sai da ofishin ya amsa:
“Ku saurara mun haka..."
Ya maida kallonsa kan Farha cikin fushi..
Ofishin ya ɗauki shiru daga ɗaruruwan idanu da ke kallonsa. Kowa sai ya juya kai yana kallon Farha...
Maleekh ya ce yana nuna ta da yatsa:
“Kin kusan kashe Amal yau! Idan ba saboda Allah ya tsare ta ba, da yanzu tana gadon asibiti ko kuma kabari. Amma ki sani, inda ace wani rauni ya same ta uhmmm! Wallahi wallahi wallahi da sai na kashe ki...Sai dai na ƙare rayuwata a gidan prison ko kuma nima a kashe ni.
Kuma last warning da zan miki shine daga yau bana son ganin ki a cikin wannan kamfani! Babu inda kika dace a rayuwata, babu inda kika dace dani..! Fita! Fitaaa daga nan kafin na manta da cewa ke mace ce!”..
Wannan kalmomin sun soki zuciyar Farha fiye da kowanne mari. Ta ji kamar ƙasa ta buɗe ta shige. Idanunta suka cika da hawaye, tana rawar jiki ta fara ja da baya. Mutanen company suna kallonta da mamakin rashin zuciyarta...
Farha ta dafe ƙirji tana kuka ta fita da gudu daga ofishin, tana rera kuka tare da faɗin
“Zan rama! Zan rama wannan wulakanci!”
Ta shige cikin motarta a harabar company tana huci, sai kawai ta yi ƙwafa da gudu ta bar wajen.
A ciki kuwa, Amal har yanzu tana kuka tana riƙe da Maleekh.
Maleekh ya tallafo fuskarta da hannuwansa biyu, yana share mata hawaye, yana furta cikin tausayi:
“Beb… shhh… ki kwantar da hankalinki. Na yi miki alƙawari, a duniyan nan bazan bari wani ya cutar dake ba. Ki bar komai a hannuna.”
Security da sauran ma’aikata suka tsaya kallonsu cikin nutsuwa, suka ga irin soyayyar da Maleekh yake nunawa Amal, sai su kaɗai suka fahimci asalin darajar Amal a zuciyar CEO.
Farha ta isa gida cikin rawar jiki, idonta jawur tsabar kuka, tana ihu kamar wacce ta rasa iyayenta. Ta buge ƙofar falon da ƙarfi, cikin ƙyarma ta na ihu:..
Ammy tana zaune a kujerar falo ita da yaranta Islam da Arfat.
Ammy hankali a tashe ta ce
"Lafiya kuwa?.."
Farha tana kuka ta ce:
“Ammy! Yaya Maleekh ne ya mun duka a kan Amal! Yayi mun wulakanci a gaban mutane!”
Ta nuna hannunta da ta yanka da kwalba, jini ya ɗan zube kadan a gefen yatsun hannunta. “Kinga! Ya yi min haka saboda ita! Ya yi min haka saboda Amal!”..
Ammy ta yi saurin tashi daga kujerar falon, idonta cike da takaici. Ta kalli Arfat da Islam sannan ta ɗaga muryarta, tana faɗin:
“Kada ku tsaya ɓata lokaci! Ku tafi ku je gidan su Amal ku murkushe ta, kuyi mata dukan da sai an kwantar ta a gadon asibiti...!”
Ta kalli Farha sannan ta ce
"Wa ta ƙila ki rage raɗaɗin da kike ji yanzu haka..."
Arfat da Islam suke yiwa Ammy kallon kama-da-wane; sun san halin mahaifiyarsu, sun san ba sauƙi ne da ita, kuma abin magana bata gudunsa...
Islam ce ta buɗe baki zata yi magana Ammy ta katse ta da tsawa mai nuni da umarni:
“Na ce ku tafi! Wannan umarni ne ba shawara ba!”
Farha, tana kuka cikin rawar murya, ta ce:
“Ni ma zan tafi! Zan rama! Zan nuna mata cewa ba za a wulakanta ni a haka ba!”
Daga nan ta fice daga falon.
Arfat da Islam duk suka bi bayan Farha cikin sauri, suna ƙara shirya kansu da mugun nufi. A zuciyarsu dai akwai haɗuwa tsakanin kishin ɗan uwa da kishin gida...
✦ A gidan Amal..
Amal ta bar company cikin halin damuwa sosai. Ta yi kuka sosai a cikin motarta, a zuciyarta tana godewa Maleekh saboda yadda ya tsaya mata; hakan ya ƙara bata tabbacin: akwai wanda yake kula da ita sosai..
Ta isa gidan su, bayan ta shiga parlour, ganin ba kowa a falon yasa ta jingina da bango sannan ta sauƙe nannauyar numfashi....
Inna, itama shigo wa tayi alamun daga unguwa take, ganin Amal yasa ta yi turuss tana kallonta, ta ƙaraso wurin ta da tsananin mamakin ganin halin da jikarta take ciki, Inna riƙo hannun Amal tayi tare da zaunar da ita akan sofas, itama ta zauna kusa da Amal, ta riƙe hannunta cikin tausaya wa ta ce:
“Amatu… me ya faru? Ki gaya mini komai.”
Amal ta share hawaye, rai-rai ta fara ba da labari, ta faɗa wa Inna yadda abubuwa suka faru, yadda Farha ta zo ofis da irin maganganun ta, yadda rikici ya tashi har Maleekh ya zo ya ceci ta. Inna ta rufe bakinta hannayenta nata zazzaro ido tare da faɗin
"Ki ce yau ina zaune sai dai a kawo mun gawarki Amatu, wannan yarinya Fara Allah dai ya kwashe mata wallahi..."
Inna ta gama surutan ta sannan ta fara yi wa Maleekh addu’ar fatan alkhairi...
✦ A CashTalk.
A company kuma, Maleekh ya tsaya ƙarasa aikin da ya taru masa. Bayan tashin hankali, ya tsaya a ofishinsa yana ƙoƙarin tsara abin da bai kammala ba; kansa yana cike da damuwa. PA da wasu ma’aikata suka tsaya wajen, suna ta dubansa cikin kulawa kowa na gani ya san wani abu ya faru, amma babu wanda ya san cikakken abun da ke faruwa sai PA...
PA ya kawo masa wasu takardu, ya ɗan yi magana cikin natsuwa:
“Boss, kana lafiya? Na ga ka kusan kammala wa duk da iya na yau ne, Madam Amal duk tayi maka sauran ayyukan, abu ɗaya ne ya rage. Zan kawo maka summary ɗin meeting ɗin yau da safe.”
Maleekh ya ɗan miƙe, ya ɗaga kansa ya kalli taga inda gilashin building yayi hasken yamma...
Ya ce:
“Na gode. Ku ci gaba, ku shirya komai kamar kullum.”
Ya juyo, idonsa ya tsunduma cikin duhu na tunani; ya yi alƙawarin in Allah ya yarda, zai ɗauki mataki akan duk wanda ya cutar da masoyiyarsa ya kuma sani, ya zama dole ya natsu yanzu, ya dawo daga wannan tashin hankali don kada ya yi abin da zai yi nadama.
Zama ya yi tare da kifar da kansa akan table ɗin office, yana ta tunani da dama...
A zuciyarsa akwai ƙauna mai zurfi ga Amal, amma akwai kuma rashin sulhu da mahaifiyarsa da bukatar girmamawa ga Malam. Yana jin nauyin zaɓin, amma a zuwansa yanzu akwai abu ɗaya: kare Amal, dawo da kwanciyar hankalinta, da gyara duk irin barnar da rikici zai iya haifarwa.
✦
Misalin ƙarfe 6 na yamma...
Babban falo ya cika da shiru, sai ƙarar plasman da yake haske yana nuna wani shirin fim. Amal da Inna tare da mata masu aikin gidan guda biyu suna zaune suna kallo, kowannensu cikin nutsuwa.
Sai kuma kwatsam! Suka ji an turo ƙofar falon da ƙarfi, Farha ta shigo a gaba tana huci, a bayanta Arfat da Islam. Fuskar Farha ta cika da tsananin fushi, idanunta sunyi jawur alamar ta sha kuka sosai..
Amal ta miƙe tsaye da gaggawa, idonta na kallon Farha da tambaya:
“Me kuke nema a gidana, zaku wani shigo wa ba sallama kamar wanda aka muku sata?”
Farha ta yi tsaki, ta kalli Amal daga sama zuwa ƙasa:
“Ai satar kika yi, baki sani bane? kin sace mun abu mafi girma a cikin zuciyata, yanzu shi nazo karɓa..."
Amal tayi murmushi sannan ta ce:
"Ai abin da ya fito daga cikin zuciya ba ya koma wa gurbinsa, sai dai kawai ki haƙura..."
Farha ta harare ta tare da faɗin:
"Kina mun abubuwa da yawa, Amal! Ke ce kika jawo min wulakanci a company, kika sa Yaya Maleekh ya wulaƙanta ni a gaban jama’a! To yau sai kin sha ɗan buro uban duka, domin ban zo da niyar koma wa haka nan ba...”
Inna ta miƙe cikin mamaki, ta ɗauki gyalenta ta ɗaura a kunkumi, ta kalli Farha da mugun kallo ta ce:
“Ke yarinya! Wani dalili ne zai sa ki shigo gidanmu kina wasu surutan banza? Waye ya turo ku?”
Arfat ta sa dariya, tana duban Inna cikin raini sannan ta ce:
“Kowa ya turo mu, mu ne za mu koya muku hankali yau.”
Islam dai tana tsaye gefe, zuciyarta na bugawa. Tana ganin tashin hankali yana ƙaruwa, amma