Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
zubar da hawayen da ba zai iya hanawa ba, yana faɗin:
"Idan ban kasance ɗanki ba, to ɗan wa nake?? Me yasa kika ce haka a kaina, mahaifiyata?? Wane ne ni yanzu…?!"
Ƙarar fashewar glass da ihunsa suka kai ga falon ƙasa. Ammy ta tsaya tana kallon Arfat da Farha, ko ta saurari yanda ihun yake fitowa, ta nuna kamar bata ji ba, sai ɗaukan ruwan sanyi da tayi a frig tana yayyafawa Arfat..
Islam kuwa ba ta iya jurewa ba, da gudu ta haura upstairs...
Cikin ɗakin Maleekh ta shige...
Islam ta shigo cikin razana, ta tarar da ɗakin a hargitse. Maleekh yana tsaye cikin kuka, hannunsa sai ɗigar da jini yake yanda glass ɗin mirror ya tsatstsaga masa fata... haka yake cakurkud'e sumar kansa yana ihu...
Ganin Islam yasa ya fara gurnanin cewa:
"Ammy ta kore ni daga zuciyarta, ta ce ni ba ɗanta bane… Islam, to ni ɗan wa ne in ba ɗanta ba?! Ina zan dosa yanzu??"
Islam ta ƙaraso cikin kuka, ta rungume shi da ƙarfi..
Itama kukan take tana faɗin:
"Dan Allah Yaya ka dakata haka. Ka yi haƙuri. Wallahi kai ɗan Ammy ne, kai ɗan gidanmu ne! Kada ka bari kalamanta su hallaka maka zuciya. Ka yi haƙuri dan Allah!"
Maleekh yana sakin nannauyar zuciya cikin kuka ya durƙusa ƙasa, ya jingina da bangon ɗaki, Islam itama zama tayi a tare da shi, ta rungume shi sosai. Dukansu suna kuka...
Maleekh a raunane cikin rawar murya ya ce:
"Islam… zuciyata ta karye. Na fi jin zafin wannan kalaman fiye da duk abinda aka taɓa mun a rayuwa. Ni ɗan waye yanzu, idan ba ɗan mahaifiyata ba?"
Islam ta share masa hawaye ta ce:
"Yaya, kai ɗan daraja ne. Kai ɗan halak ne. Kai ɗan da Allah ya ba a wannan gidan ne. Kada ka taɓa mantawa da hakan."
Maleekh ya rungumi Islam da ƙarfi, hawayensa na digowa a kafaɗarta, suna kuka tare. Ɗakin ya cika da ƙarar hargitsewar zuciya....
Suna zaune a wannan lokacin har dare yayi sosai, suna zaune rungume da juna, haka Islam take jin yanda jikin Yayanta Maleekh yake kakkarwa kamar wanda yake jin tsananin sanyi... ga jikinsa ya yi mungun ɗaukan zafi, alamun tsananin zazzabi ne ke damunsa..
Ga wani irin fitar da deep breathing da yake kamar last breathing ɗinsa kenam..
A tsorace ce Islam ta kokarta ɗaga shi, ta tallafa masa zuwa kan gadonsa ta kwantar da shi...
Da gudu ta fita daga ɗakin ta nufi down stairs, ba kowa a falon domin a lokacin misalin ƙarfe 12 na dare ne..
Kai tsaye medicines room ta nufa domin ɗauko first aid box..
Tana ɗauka ta koma part ɗin Maleekh dake itama Islam ɗin ɓangare likitanci ta karanta..
Tana aiki a wani babban hospital...
Tana zuwa tayi saurin masa allurar zazzabi sannan ta ɗaura masa drip a ɗakin, dake suna da komai da komai na emergency...
Sannan ta jiko ƙaramin towel da ruwan ɗumi tana matsa masa jiki da kan goshinsa gaba ɗaya...
A wannan ranar Islam bata samu yin bacci ba har asuba...
Da jin ƙiran sallah Maleekh ya buɗe ido, a hankali ya tashi zaune yana bin Islam da kallo wanda bacci bai daɗe da ɗaukar ta ba, tana zaune akan ƙarami chair a bakin gado, ta kwantar da kanta a bakin gadon..
Murmushi ya yi ganin yanda ta bashi kulawa, ɗaga kansa ya yi yaga drip na ruwa har leda uku duk ya ƙarar, ya samu an cire masa, ga alluran da ta masa ciki har da na Anxiety (damuwa)..
Yana ƙoƙarin tashi a zabure Islam ta buɗe ido tare da ɗago wa tana kallonsa, ta ce
"Yaya ya jikin dai? Yanzu me kake ji a jikinka?..."
Maleekh ya ce
"Ba komai Sweet Sis, normal.."
Murmushi tayi tare da faɗin
"To bari naje na haɗa maka breakfast sai na kawo maka ko?..."
Ta fice, shi kuwa ya bita da kallon Murmushi, daga bisani ya miƙe ya shiga toilet domin ɗauro alwala...
☆ _This Morning_ ☆
Gida gaba ɗaya ya yi shiru, kamar gidan da aka gudanar da jana’iza. Ba kowa ya yi bacci da kyau ba.
Farha na zaune a kujera tana duba wayanta..
Arfat kuwa har yanzu tana jin ciwon marin da Maleekh ya riƙa mata jiya, tana zaune itama tana game a wayarta...
Islam ce ta sauƙo daga part ɗin Maleekh zata wuce kitchen baya yi wa kowa magana ba..
Farha ta tsayar da ita da cewa.
"Kin ga Islam, zo ki taya ni zaɓan kayan ɗakin da aka turo mun daga Malaysian, kin san yau ne auren kuma a yau za'a kawo mun kayan....
Islam harararta tayi tare da faɗin.
"Wai ke kin ɗauka da gaske za'ayi auren yau ne?..."
Ammy wacce shigowar ta kenam falon ta ce:
"Ku saurara da kyau. Wallahi ban ga dalilin da zai hana a ɗaura auren Maleekh da Farha yau ba. A shirye nake. Ni uwa ba zan ƙi ganin auren ɗana ba. Idan kuwa shi yaron ya raina ni, to sai dai ya kashe kansa da ƙiyayya. Ba zan canja ra’ayina ba!"
Islam tana tsaye ta kasa magana, zuciyarta cike da tausayi. Ta tuna halin da ta ga Maleekh a ɗakinsa jiya. Ta kalli Ammy tana hawaye ta ce:
"Ammy… ki ji tausayin Yaya. Kalamanki sun yi masa ciwo sosai jiya. Wallahi ban taɓa ganin shi cikin wannan hali ba. Don Allah ki yi haƙuri da shi, kar ki tilasta masa wannan aure…"
Ammy ta kalli Islam da idanunta masu zafi..ta ce:
"Ke ma ko? To yanzu kin fara goyon bayan waccan yarinyar kenam? Ki saurara mun sosai Islam, ni ce mahaifiyar ku! Duk abin da zan ce kuyi, dole kuyi shi! Kuma wallahi sai na ga auren nan ya tabbata, ko Maleekh ya so, ko kar ya so wannan ya rage nasa.!"
Farha tana yatsina fuska ta ce:
"Ya yanzu Ya Maleekh ya soni ne?..."
Ammy ta ce da ita:
"Ke dai kiyi shiru! ki bar ni da shi. Idan har ya zama mijinki, to dole ya koyi yanda zai zauna dake. Ba son zuciyarsa nake nema ba, abin da nake nema shi ne buri na ya cika. Kuma sai ya cika, wallahi sai ya cika!"
Arfat ta turo baki tana shafar kumcinta ta ce:
"Ammy, gaskiya Yaya Maleekh ya yi mun tsauri sosai. Zai iya kasheni wallahi, jiya ya kusan hallaka ni da duka…dan Allah a haƙura da auren nan, wallahi tsoro nake ji..."
Ammy ta wurga mata ido cikin tsawa ta ce:
"Ke wato kin ji tsoro saboda ɗan marin da aka yi miki kenan? Idan ba ki shirya ba, sai ki fita daga harkata kema! Wallahi ba zan bar Farha ta zauna haka babu aure ba. Ko da duniya zata guje ni auren nan sai ya tabbata!"..
Tana faɗin haka ta miƙe tsaye ta bar falon.. Zuciyarta cike da tsananin fushi...
Bayan ya idar da sallah.
Idanunsa sun kumbura saboda kuka. Ya tuna da kalaman Ammy na jiya:
“Kai ba ɗana bane… Ba daga cikin jikina ka fito ba!” Sai zuciyarsa ta sake karyewa. Ya dafe kansa da hannaye biyu...
Yana magana shi kaɗai, da murya mai sanyi:
"Ammy… yau kike son ɗaura auren da Farha? To wallahi… idan wannan aure ya tabbata, sai dai a ɗaura shi ne da gawa ta…Domin nasan zuciyata ne zata buga, ga nauyin kalamanki ga nauyin ƙiyayyar Farha.."
Ya nufi window yana kallon rana wacce ta fito da haske, amma a zuciyarsa babu haske. Zuciyarsa ta cika da ƙiyayya, ciwo, da rashin bege...
Anata shirye-shiryen ɗaurin aure. An kawata falo da flowers da ƙananan kayan ado. Farha tana zaune cikin wani sabon gown mai tsada, tana cike da ƙyashi da girman kai. Arfat da Islam da wasu ƙawaye suna kusa da ita...
Sai ga Amal ta shigo cikin ruɗani, idanunta a kumbure da kuka. Ta shigo falon kamar wacce take neman mafaka, tana ƙiran suna da rawar murya...
"Maleeeekh! Maleeeekh!! Ina Yaya Maleekh ɗi naaa??"
ƴan mata a falon suka tsaya kallonta. Farha kuwa ta tashi da sauri, ta sha gabanta kafin ta nufi stairs ɗin...
A tsawace, tana hararar ta ta ce:
"Ke tsaya nan! Yau ranar aurensa da ni, ba zaki taɓa ganinsa ba. Domin mijina mai tsada ne, ba kowace kucaka bace zata iya ganinsa..."
Amal ta fashe da kuka, tana ƙoƙarin turata ta wuce tare da faɗin:
"Don Allah ki barni, ki barni na ganshi, ki barni kawai na ganshi…"
Da ƙyar Amal ke tura hannun Farha, sai kuma suka ji muryar Ammy daga sama, muryar da ta tsinke zuciya da ƙarfi kamar tsawa...
"KEEEE!! Dakata nan nace!!"
Amal ta tsaya cak! Ta juya a zabure tana kallon Ammy wacce ta sauƙo daga stairs ɗin part ɗinsa, fuskarta cike da ɗaci da fushi...ta ce:
"Me ya kawo ki gidan nan?!"
Amal tana kuka sosai ta ce:
"Ammy… wallahi ni Yaya Maleekh nake nema…"
Ammy ta katseta da tsawa cewa:
"Kin ji labarin aurensa kenam!? Ko shi ya gaya miki? To Da ke da Maleekh ɗin kunci kutumar buro uban ku! Kina jina kooo?!! Maza kama hanya ki barmun gida kafin in sa gadawa su fita mun dake..!!"
Amal ta gudu ta ƙaraso gabanta, ta durƙusa, ta riƙe ƙafar Ammy tana kuka da rawar murya.
"Dan Allah Ammy! Dan Allah kar ki rabani da shi! Wallahi inasonsa da zuciyata gaba ɗaya. Ki taimake mu, ki ji tausayinmu Ammy. Idan ma zaki aura masa Farha, to don Allah ki saka sunana a matsayin mata ta biyu. Ki haɗa aurenmu gaba ɗaya, dan Allah! Zan iya jure komai domin kawai na kasance da Maleekh…"
Ammy ta zare ƙafarta daga hannunta, ta ɗaga Amal da ƙarfi ta zabga mata mari! Mari har sau biyar a jere, tana huci.
Ta ce:
"Ke! Ki rabu da yarona. Kin hallaka shi da hauka saboda soyayyarki marar mutunci. Wace irin mayyar yarinya ce ke? Jarababbiya mara zuciya!"
Amal tana kuka tana riƙe da kumcinta ta ce:
"Ammy, idan auren ne… wallahi na yarda ki yi mun duk wani hukunci. Ki saka ni a cikin masu gasar shad'i idan haka ne. Zan iya jure bulala ɗari biyu kawai don na auri Maleekh…"
Ammy ta ja dogon tsaki tare da faɗin:
"Ni bani da lokacinki! Kafin minti biyu, ki bar min gida, kafin na ƙira maza su fitar dake da ƙarfin tsiya!"
Daga nan Ammy ta juya a fusace..
Amal ta juya zata tafi.
Farha ta sha gabanta, tana dariya cikin kyashi ta ce:
"Na gaya miki hanyar da zaki samu Maleekh? To ki tafi gidan club. Ki je can zaki same shi, kuyi bankwana na ƙarshe."
Farha ta ci gaba da yi mata dariya tana faɗin address ɗin wani club sananne a Abuja, inda aka fi cusa mata ƴan iska da masu shaye-shaye. Amal ba tare da ta yi tunani ba ta ɗauka da gaske ne. Da gudu ta fita daga gidan, ta shiga mota kai tsaye ta nufi wurin da aka faɗa mata...
Maleekh kuwa a wannan lokacin yana ɗakinsa, yana kwance cikin damuwa, bai san komai daga abin da ke faruwa a ƙasa ba. Islam tana falo, zuciyarta na tafasa da tausayin Amal da Yayan nata, amma ta kasa yin komai....
Kafin Amal ta isa.
Farha ta ƙira wasu kawayenta a waya tana sanar da su cewa:
“Ku saurara da kyau! Amal za ta shigo club, ka da ku bata damar shan iska. Ku dabaibayeta, ku tilastata ta shan kwayar maye. Idan ta fara rikicewa, sai ku mata injection, da zaran ta fara maye sai ku kaita toilet na maza, ku kwantar da ita, ku yayyaga mata kayan jikinta. Ku zuba mata jini a ƙasan wandonta, ku tabbatar ya gangaro har ƙafarta. Za a ɗauka cikin da take da shi ta zubar ne.
Bayan nan, ku ajiye kwayoyin zubar da ciki kusa da ita don a tabbatar da sharrin. Sai ku gudu ku bar ta can… Zan tabbatar duniya ta tsane ta!”..
Dariyar mugunta suka yi kowacce ta ɗauki nata aikin da za ta yi.
Farha kuwa ta ci gaba da zaman jiran saƙon kammala aiki...ɗaurin aure kuwa an ɗan taru a gidan ana jiran isowar Abbah kafin a shafa Fatiha....
Amal ta isa Club
Amal ta shigo club ɗin a ruɗe, tana duba ko za ta hangi Maleekh. Idonta ya rufe saboda tashin hankali da ruɗewa.
Cikin mintuna, kawayen Farha suka iso kanta. Ɗaya daga cikinsu ta yi kamar tana yi mata sannu da zuwa..
Amal kallonsu tayi tare da faɗin
"Ku ɗin su waye ne?.."
Suka sanar da ita cewa, su ɗin ƙawayen Maleekh ne..
Suka zaunar da ita tare da bata juice wanda suka sanya kwaya a ciki, sun sanar mata cewa.
"Ta jira Maleekh yana nan zuwa.."
Amal bata zargi komai ba, ta karɓi drink ɗin. Da ta sha, jikinta ya fara sanyi. Idonta ya fara juyawa, zuciyarta na bugawa da sauri.
“Me ke faruwa da ni haka…?” Ta furta da rawar murya.
Wata daga cikinsu ne ta watsa masa ruwan lemo ta nuna rashin sani ne, Amal ta zabura ta miƙe tana karkade ruwan jikinta, anan suka tura ta toilet akan ta je ta gyara jikinta, suka mata kwatancen toilet ɗin maza, ai kuwa nan Amal ta je..
Tana zuwa kuwa kanta yayi wani irin sarawa, maganin ya fara mata aiki..
Anan ta faɗi...
A cikin male’s toilet suka tarar da ita, suka kulle ƙofa. Wata ta riƙe hannunta, wata ta cire mata hijab ɗinta. Suka buɗe mata jiki da karfi, suka yi mata injection.
Amal ta fara rawar jiki, idanunta sun yi nauyi, numfashinta na sauƙa a wahale.
Suka yayyaga rigarta da ƙarfin tsiya, sannan ɗaya ta zuba mata jini da suka riga suka tanada a cikin kwalban roba. Jinin ya biyo ƙafafunta ya watse a tiles ɗin toilet.
“Hahaha yanzu duniya zata ɗauka ciki ta zubar. Muna da tabbaci wannan yarinyar ta lalace!”
Suka ajiye kwayoyin zubar da ciki kusa da ita, suka gama mata video sannan suka fice da gudu suna dariya, suka tura wa Farha video yanda suka yi mata daga farko har ƙarshe..
Misalin ƙarfe 10 na dare aka samu Amal a kwance a cikin male’s toilet. Tana kwance a cikin jini, idonta a rufe, numfashinta ya tsaya..
Mutane suka taru, suka fara ihu. Wani ya ɗauki hoton ta, ya saka a social media...
Aka ƙira an jarida..
Ƴan jarida suka isa, suna video da cewa:
“Abun mamaki, Amal Abdulsamaad shahararriyar ƴar jaridar nan, ga ta a gidan club a male's toilet kwance cikin jini, abin da bamu sani ba shine 'shin wani ne ya mata fyade ko kuwa?' Amma bisa alamun ciki ta zubar, domin ga kwayoyin zubda ciki a gefenta...."
Ƴan sanda suka shiga cikin hayaniya suna ƙoƙarin ƙiran motar asibiti, amma kafin hakan hotunan da bidiyon suka baza a duniya.
Maleekh yana kwance yana tunani. Wayarsa ta yi ting. Ya duba WhatsApp ya ga hoton Amal kwance a jini!
Message ya biyo baya:
“Idan baka yarda ba, kunna TV.”
Zuciyarsa ta buga, jini ya hau kai. Ya kunna TV sai ya ga rahoton kai tsaye na club ɗin, Amal kwance a jini, mutane suna ta kallonta, ƴan jarida suna ta yayata zancen
“Amal!!” Ya furta sunan a ruɗe..
Ya fice da gudu daga ɗakin sanye da farar jallabiya. Bai tsaya sauraron kowa a falon ba. Farha ta bishi da kallo tana tauna lebenta cikin shauƙin mugunta.
A wannan rana kuma, daidai da lokacin bikin Maleekh da Farha, Abbah ya dawo daga Amurka. Cikin fushi ya dawo zuciyarsa na harzuka, yana zuwa daman ya wargaza taron bikin, ya kori kowa a gidansa sannan ya ƙira iyayen su Farha ya sanar da su cewa kada su zo, an fasa bikin...
A wannan ranar wuni Abbah ya yi yana balbale Ammy da masifa..
"Akan me zaki yanke bikin ɗana ba tare da sanina ba? Saboda kin mayar ni mahaukaci bansan me nake yi ba?..."
A falon akwai wata tsohuwa wato mahaifiyar Abbah da Mahaifiyar Ammy duk suna zaune har da Mahaifin Ammy...
Jin wannan al'amari yasa duk suka zo...
Wannan bikin an soke shi a wannan ranar.
Maleekh bai san meke faruwa ba dake ya kulle ƙofarsa ya hana koma shigo masa..
Sai a yanzu da ya fita a ruɗe...
Kuma har wannan lokacin kowa yana falo, sai dai su ɗin ma kallon television suke, kan labarin Amal...
Wannan ya ƙara ɓacin rai ga Farha, amma duk da haka tana jin daɗin sharri da ta kitsa wa Amal.
Maleekh ya isa club ɗin da gudu, zuciyarsa kamar za ta faso ƙirjinsa. Ya shiga cikin cunkoson mutane. Ƴan sanda na son dakatar da shi amma ya ture su gefe.
Ya ga Amal kwance, ga jini a jikinta, ga wayoyi a sama suna ɗaukar hotuna. Idanunsa suka cika da hawaye.
Ya faɗi a kanta ya riƙe hannunta:
“Amal! Ki tashi, ki dubeni, don Allah kar ki barni haka. Ba zan bari su lalata miki suna ba. Zan gano wanda ya yi wannan sharri, kuma sai na ɗauki mataki akan hakan..!”
Ƴan jarida suka yi wuf da kyamarori suna ɗaukar hotonsa da ita...
“Amal! Amal! Open your eyes, please! Don’t leave me… Wallahi ba zan bari ki tafi ba!”
Haka Maleekh yake ta jijjiga ta amma ko motsi..
Mutane suka tsaya kallonsa, ƴan jarida suka ɗauki hoton shi yana kuka a kan Amal. Ɗaya daga cikinsu ya ce da sauti:
“Shin wannan ba shi ne Maleekh, babban ɗanbusiness, wanda a yau aka shirya aurensa da wata ba?”
Kowa ya fara raɗa: “To yaya ake ciki kenan? Ai Amal ita ce budurwarsa ta asali...”
Zuciyarsa ce ta fara masa wani irin zogi. Yana tuna kalaman Ammy da cewa ba ɗanta ba ne, yanzu kuma Amal tana shan mugun zargi..
Ya riƙo haɓarta da rawar hannu yana faɗin:
“Na rantse da Allah, zan binciko gaskiya. Zan wanke ki daga wannan sharri! Duk wanda ya yi miki wannan sharrin zai biya kuɗinsa da rayuwarsa…”
A lokacin, ƴan sanda suka nufe shi da nufin ɗaukar Amal. Amma Maleekh ya ɗaga Amal ya nufi ƙofar waje...
A wannan daren, duniya ta tsaya ga Amal da Maleekh.
Cikin hanzari Maleekh ya ɗauke Amal a hannuwansa, yana daka tsawa ga ƴan jarida:
“Kafin safe duk posting ɗin da kuka yi game da Amal ku share shi! Duk hotunan da kuka saka ku cire su yanzu! Idan kuwa wani ɗan jarida ya sake taɓa wannan magana, sai na tabbatar an kamashi, kuma bai sake ganin hasken waje ba sai ya mutu a prison!”
Ƴan jarida suka tsaya a tsorace, wasu suka fara sharewa nan take. Ƴan sanda suka matsa kusa, amma Maleekh ya ɗaga musu hannu da cewa:
“Ku kuma! Ba ruwanku da wannan case. Ku ja baya ku barta a hannuna!”
Ya fito da Amal cikin karfi, yana riƙe da ita kamar zai cinye duk wanda ya kusance ta...
Haka ya nufi hospital da ita...
A asibiti
Amal an kwantar da ita a kan gado, da drip a hannunta.