Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
haɗakar dangin biyu a yau.
Sanda Maleekh da Amal suka taka zuwa wurin zama, an kunna wakokin soyayya na ƙasashen waje masu sanyaya zuciya, inda Maleekh ya nuna wa Amal cikakkiyar girmamawa a gaban Farha da sauran jama'a.
Wannan shigar ta Amal cikin Wedding Gown kamar amarya ta ruɗe kowa a wurin; mutane sun kasa gane wa ce ce asalin amaryar...
Bayan an zauna, sai aka miƙa wa Maleekh microphone don yayi jawabi.
Maleekh ya fara da godiya, sannan ya ce:
“Kamar yadda ku ka sani, yau na cika alƙawari biyu.. Na farko, na auri Farha Wadata don cika alƙawarin mahaifiyata. Na biyu, na sake ɗaura sabon aure da matata ta farko kuma Uwar ƴaƴana, Amatullah Abdulsamaad, wanda shine na farko da na ƙarshe a gare ni. Don haka, ku yi min fatan alkhairi a kan matana biyu, amma ku san cewa Amal ce ta musamman.”
Jawabin ya firgita Farha wacce ta ji kishi, amma ya sanya Amal ta ji ƙwarin gwiwa sosai a karon farko.
An fara rawa ta musamman inda Maleekh ya fara da Amal har tsawon minti uku, yana yi mata wasanni masu nuna ƙauna ta gaskiya a fili.
Sannan ya je wurin Farha don rawa na minti ɗaya kacal, yana nuna mata girmamawa amma ba sha’awar soyayya ba.
Zayd da Islam suma sun fito sun yi rawa, wanda hakan ya nuna farin cikinsu na gaskiya..
An raba motoci biyu a wurin shagalin a matsayin kyaututtuka.
Maleekh ya miƙa wa Farha mabuɗin motar alfarma (Luxury Car) a matsayin kyautar aure...
Sannan ya miƙa wa Amal wani zoben hannu mai matuƙar tsada, da kuma takardun mallakar gida (Deed of Ownership) na sabon gidan nasu na alfarma wanda ya ce shine Gidansu na Har Abada wato The Eternal Home...
Wannan shagalin ya nuna wa kowa cewa Maleekh ya cika dukan alƙawuransa, amma kuma ya bayyana wace ce mafi daraja a wurinsa....
_NEXT NEXT NEXT_
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 97 to 98
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Bayan an kammala shagalin, aka fara ɗaukan hotuna.
Maleekh da Amal aka yi musu hoto na musamman.
Sannan aka kawo yaran suka ɗauki hoto tare, da ƴan uwa.
Farha ma ta shiga aka ɗauka da ita.
Nan ma aka ɗauka da Amal da Farha, ko wacce tana riƙe da yaro ɗaya sai Mijin a tsakiyarsu.
Zayd ma da Islam an tsattsara musu hotuna na Musamman.
Daga bisani Maleekh ya riƙe hannun Farha a yayinda take ja baya. Ya matso da ita jikinsa yana kallonta ya ce:
“Sauran hoto mu biyu kawai…”
Farha ta saki murmushi. Aka ɗauki hotonsu.
Haka akaita musu kalolin Hotuna na musamman.
Kala na farko The Romantic Embrace, Maleekh yana rungume da Farha daga baya, hannayensa suna kewaye da ƙugunta, yayin da Farha ta jingina kanta a kafaɗarsa tana murmushi.
Na biyun The Gazing Stare, suna fuskantar juna, Maleekh yana riƙe da haɓar Farha (chin) yana kallon idanunta da tsananin kulawa, yayin da Farha ke lumshe idanunta cike da jin daɗi.
N ukun The Hand Kiss, Maleekh ya durƙusa ɗan kaɗan, yana sumbatar hannun Farha a hankali, yana nuna girmamawa da mallaka.
Na huɗu The Forehead Touch, Goshinsu a haɗe, suna numfashi tare a hankali, hannayensu suna riƙe da juna.
Amal tana daga gefe tana riƙe da Arhaan sai kallonsu take tana jin takaicin cewa,
“Wai Maleekh ne yayi aure bayan ita?…”
Maleekh yana riƙe da hannun Farha, ɗayan hannunsa a bayan ƙugunta (hips), yana mata raɗa cewa,
“Kar ki damu da abinda kika gani dangane da kyautar da nayi, ganin ke mota ce ita kuma gida da zobe…”
Farha tayi saurin katse shi da cewa.
“A’a Ya Maleekh, ban damu ba domin ta cancanci haka, tana da matsayi a zuciyarka kuma itama haka, ta juri duk wani kalubale na soyayyarku… Sannan duba ita batada iyaye ni kuma inada su, batada kuɗi ni kuma inada kuɗaɗen da bansan adadinsu ba, kyautarka bazai ƙara mun komai daga cikin dukiyata ba to akan me zan damu? Gidaje nima inada su fa…”
Ta matsa kusa da shi tana rage murya,
“Kuma a halin da Amal take ciki yanzu tana buƙatar kulawa na musamman duba da yanda bata juma sosai da haihuwa ba… tana buƙatar kulawa ita da jariranta a wurinka, wallahi tausayinta ma nake ji… kasan meye? Inda nice a matsayin Amal ba, wallahi da bazan zo shagalin bikin nan ba saboda zafin kishi na… saboda bata samu wadataccen kulawa ita da jariranta ba a wurinka kuma kazo mata da batun aure…”
Maleekh ya ja numfashi sannan ya ce
“It's okay, na fahimci ban ɓata miki rai ba kuma nagode da hakan da kuma fahimtata…”
Amal daga gefe ta rasa tattaunawar da suke domin a iya tsakaninsu suke yi. Tana cikin nazarin nan sai taji ana ƙiran wayan hannunta wanda ya kasance wayar Maleekh ne. Taga unknown number ne. Cike da mamaki ta katse kiran.
Sai da aka kira sau uku (3), ana ukun ne ta nufi wurinsa can saman hall da yake tare da Farha.
Tana zuwa ta ɗora hannunta akan kafaɗarsa ganin ya shagaltu sosai da hira da Farha kuma suna rungume. Ya ɗan juyo yana kallonta cike da fara'a.
Wani irin harara ta wurga masa sannan ta ce:
“Idan kun gama ana ƙiranka a waya…”
Ya karɓa. Tana shirin juyawa ta bar wurin yayi saurin riƙo hannunta. Da sauri ta juyo tana masa wani irin kallo har idonta ya rine ya koma ja.
Cikin ƙarfin hali ta fisge hannunta daga riƙon da yayi mata.
A lokacin MC ya miƙa mata mic akan tayi jawabi yanda take ji akan shagalin nan. Sun bayyana akan zasu fara jin daga bakin uwar gida kafin su koma kan Amarya.
Amal bataso ba, sai da aka tilasta mata kafin ta tsaya tana fuskantar jama’a dake zazzaune. Maleekh na gefenta a yayinda Farha take ta bayan Amal tana murmushi (kamar mai jiran gado), idan Amal ta kammala ita zata maye gurbinta.
A can gefe kuma Zayd da Islam ke tsaye su ma.
Alhaji Wadata yana cikin Hall ɗin, wurin shagalin. Ya ga yadda Maleekh ya yi amfani da auren Farha don girmama Amal a fili.
Murmushi ne ya faɗaɗa a fuskarsa, amma murmushin mugunta..
Ya ji Maleekh ya yi rashin adalci a gare shi, amma kuma ya san cewa Maleekh ya ba shi dama a fili.
Wadata ya danna call sannan ya kara a kunne, ba tare da kowa a wurin zamansa ba, domin sai da ya ja gefe tukun yayi waya.
“Ta fara jawabi a mic, zaku iya aiwatar da shirin, wannan ne damar da muke da shi…”
Daga nan ya katsar da ƙiran. Wanda zasu aiwatar kuwa already sun shigo cikin hall sun saje da mutanen cikin.
Ɗaya ne ya nufi cikin wani wuri mai sirri yanda baza a ganshi ba. Ya saita bindigarsa yana facing Amal tana nesa-nesa.
Amal cikin hawaye ta ɗan fara jawabi. Ta karɓi makirufo tana duban Maleekh.
Muryarta na rawa, hawaye na zuba a fuskarta ta fara faɗin.
“Yau rana ce mai zafi a gare ni, kuma rana ce mai daɗi a gare ni. Zafi saboda na raba mijina da zuciyarsa da wata… Daɗi saboda na tabbatar cewa duk inda ya je, ni ce gidansa na farko da na ƙarshe…
Wannan aure ya zama juna-biyu a gare ni. Sai dai Maleekh ya san cewa kowace mace tana buƙatar ƙaunataccen mijinta a gefenta. Ina roƙonku da addu’a don Allah ya sanya adalci a tsakaninmu. Kuma a matsayina na uwar gida, zan kula da dukkan matsalolin gidansa, kuma insha Allahu zamu zauna lafiya da Amaryar mu tin da har Allah ya kaddarar da anyi, Allah ya sanya alkhairi. …”
Maleekh yana kallonta yana murmushi don nuna wa jama’a cewa yana goyon bayanta, still ya kai idonsa kan jama'a..
💥
Ƙara ƙiran wayarsa akayi da unknown number. Ya ɗaga tare da karawa a kunne.
Ji yayi an furta:
“Kana lura akwai ƴan ƙunar baƙin wake a cikin hall ɗin nan…”
Daga nan aka katsar.
Daga nan ya kalli Zayd dake bayansa domin yaji kamar muryarsa ne. Haɗa ido sukayi, Zayd ya masa voting da babban yatsarsa (thumb’s up) alamun dashi yayi waya
.
Maleekh ya jinjina kai daga nan ya fara baza idanu a cikin taron.
Ya ciro black glass ɗinsa mai matuƙar tsada wanda kimaninsa zai kai 50M wanda yake ɗauke da sirrin da ba kowa ya sani ba. Nan take yake hango abu da glass ɗin (Thermal/X-ray Vision). Kuma duk saurin abu zai iya ganin tafiyarsa.
Baiyi minti biyar da sanya glass ɗin ba kwatsam ya hango wani harsashi ya saito wurin da Amal take tsaye.
Da sauri ya kai hannunsa ya janyota gefensa cikin hanzari kamar Spider-Man. Bullet kuwa dake da gudunsa wanda ba wanda zai iya ganinsa Maleekh yana janyo Amal, bullet ya wuce ya sauƙa a saitin ƙirjin Farha dake tana ta bayan Amal ne.
Nan Farha ta faɗi tare da dafe ƙirjinta.
Duk mutanen wurin ne suka mimmike suna zaro ido a rikice.
Maleekh yayi saurin cire glass yana kallon Amal wacce take a tsorace tana kallonsa. A tunaninsa ya tsiratar da ita da harsashi.
Jin an ambaci "Farhaaaaa…" Daga wajen jama'a
Nan ya juya baya ya ganta a zube a ƙasa. A ruɗe yayi kanta da gudu ya durkusa tare da ɗagota ya ɗora ta akan cinyarsa.
Amal itama zaro ido tayi ta toshe bakinta cikin ruɗani..
Zayd a hargitse yayo kan Kanwarsa yana furta sunanta.
Aure ya koma tashin hankali! Maleekh ya ceci Amal, amma ya rasa Farha..
Maleekh yana riƙe da Farha a kan cinyarsa, jinin Farha na zubowa a jikinsa. Ya kasa yarda da abin da ya gani. Aiki ya kasance kan Amal, amma Farha ce ta biya sadaukarwa.
Zayd ya durƙusa gefensa cikin ruɗani, amma Maleekh ya riga ya shiga cikin yanayin aiki na gaggawa (professional mode).
Maleekh ya ɗago Farha da gaggawar gaske a hannayensa.
Da ƙarfi yake faɗin
“Maza ku kira motar asibiti! Kuma ku kulle hall ɗin nan! Kada wanda ya fita!!”
Ammy da Inna suka yi tsalle cikin firgici..
Amal tana tsaye, jikin ta na rawa tana kallon Maleekh yana tafiya da Farha wacce yanzu ta zama jini gaba ɗaya.
Cikin kuka mai zafi take faɗin "Maleekh! Maleekh!..."
Amma Maleekh bai ko juyo ba. Ya fara gudu da ita daga saman hall zuwa ƙasa.
Duk mutanen da ke hall ɗin sun fara ihu da gudu don tsira.
Ammy ta rungume Amal don kwantar mata da hankali, yayin da kuma Inna ta fara addu’o’i da furuci na al’ajabi game da muguntar mutane.
Maleekh ya fita da Farha daga hall ɗin. A halin da ake ciki, motocin Maleekh na alfarma suna nan a waje. Ya sanya Farha a cikin motar sa kai tsaye, sannan ya shiga gefen direba ya fara tuki da gudun gaske zuwa Asibiti mai zaman kansa wanda ya sani.
Zayd da Islam da kuma wasu ƴan sanda na sirri waɗanda ke tsaron Maleekh sun bi bayansu nan take.
Suna isa Asibiti, an kai Farha ɗakin tiyata (Emergency Surgery) nan take.
Maleekh ya tsaya a wajen ɗakin tiyata yana duban jinin Farha da ke jikinsa, yana kallon hannunsa wanda har yanzu yana riƙe da tabon jinin Farha. Ya dafe kai cikin damuwa da haushi kan makircin da aka tsara...
Ya san cewa harbin ba don a kashe Farha bane..
A zuciyarsa ya fara furta.
"Alhaji Wadata! Ka nuna min cewa ba kawai kai ɗan siyasa bane, kai ne kasurgumin mai kisa... Yanzu zan nuna maka cewa ka yi kuskure!"..
Bayan da aka harbi Farha, Alhaji Wadata ya fita daga Hall ɗin cikin ɓacin rai, yana fafatawa da mutanen da ke gudu don tsira. Ya yi hasashe cewa Amal za a harba, ba Farha ba.
Yana isa wajen Parking Lot, ya kira mai aikin sa wanda ya harba.
Cikin tsawa da murya mai rawa ya ke cewa
“Waye ya gaya maka ka harbi ƴata? Waye?!”
Mai Harbin ya ce,
“Muna neman gafara ranka ya daɗe! Mun saita bindigar ne a kan Amal, amma Maleekh ya ɗauke ta da gaggawa… Bullet ɗin ya wuce ya kama matar da ke bayanta…”
Wadata ya katse wayar ya jefar da ita a ƙasa. Ya shiga motarsa cikin tsananin takaici da haushin gazawa.
Ya nufi Asibitin da aka kai Farha.
Wadata ya isa Asibitin cikin shiga ta tashin hankali. Ya tarar da Maleekh a wajen ɗakin tiyata, har yanzu yana cikin kayan ango amma da jinin ƴarsa a jikinsa.
Wadata ya nufo Maleekh da gaggawar gaske, ya ɗaga hannu zai mare shi.
Maleekh ya riƙe hannun Wadata a sama da ƙarfi. Ya kalli Wadata da idanun da suka yi ja saboda haushi.
Alhaji Wadata ya ce,
“Maleekh! Ka kashe min ƴata! Ka taɓa furta cewa 'za mu yi amfani da auren don cin nasara' Sannan ka nuna rashin adalci a shagalin, yanzu kai ka jagoranci kisan kai! Me kake son aiwatar wa da Farha?”
Maleekh ya furta "kai ne wanda zai kashe ƴarsa domin kawai ya ga Maleekh ya mutu!”
Zayd ya fito da sauri daga wani gefe, ya tsaya a tsakanin su, yana hana su rigima..
“Daddy! Don Allah a kwantar da hankali! Yanzu ba lokacin wannan bane! Mu yi wa Farha addu'a! Maleekh, don Allah a kwantar da hankali!”
Maleekh ya saki hannun Wadata ya ja baya.
Alhaji Wadata Yana huci da fushi ya ce,
“Maleekh! Nayi nadamar baka auren ƴata! Zan tsige ka daga dukiyarka! Zan nuna maka ainihin ni! Ba za ka yi amfani da Farha don girmama karuwar da kake aure ba!”..
Maleekh ya kalli Zayd, sannan ya kalli Wadata da murmushi mai zafi.
“A yanzu Farha matata ce! Kuma zan kasance mijinta har sai ta warke! Amma zan gano wanda ya yi wannan harbin! Kuma zan nuna maka ba kai bane ka kawo ni duniya ba, kuma ba kai bane zaka fitar da ni! ”..
🪸🪸🪸
A wurin Hall, sumar Hajiya Sa’adatu biyar ana farfaɗo da ita ganin Ƴar ta aka harba. Da ƙyar ta yunkuro. Gaba ɗaya iyalai suka nufi Hospital.
A wannan ranar a Asibiti suka kwana har da Amal. Kowa hankalinsa a tashe. Amal ma ta shiga tashin hankali sosai ganin halin da Farha take ciki, duk da har yanzu ba a basu damar ganinta ba.
Har aka wayi gari, aka sake wuni. Sauran duk sun koma gida banda Maleekh, Zayd, Amal, da mahaifiyar Farha (Hajiya Sa’adatu). Alhaji Wadata bai zo asibitin ba domin ya shiga tashin hankali sosai kuma ta silar sa hakan ya faru.
An tsawaita bincike sosai akan wanda ya kawo farmaki domin ba a tantance waye ba, amma Zayd ya san shirin mahaifinsa ne amma ya kasa faɗi sai kuka.
Maleekh ya tambaye shi akan ya sanar masa waye, domin ai shi ya kira ya sanar cewa akwai ƴan ƙunar baƙin wake. Amma Zayd ya kasa faɗi...
Maleekh ya dafa kafaɗarsa yana faɗin
“Zayd! Ka daina ɓoye min! Ka kira ni a waya! Waye ya aikata wannan? Muryarka ce na ji! Don Allah ka gaya min kafin na ɗauki mataki marar kyau!”..
Zayd yana jujjuyawa cikin kuka, yana ta ƙoƙarin magana amma bakinsa ya ƙi buɗewa,
“Ni-ni… wallahi ni… ban sani ba… ba zan iya…” Ya kama kansa cikin zafi...Yana jijjigawa.
Maleekh ya furta yana kallonsa.
“Ka tuna! Na san layar rufe baki ne a kan ka! Ka yi ƙoƙari ka kashe shi! Waye ya harbi Farha?!”
Zayd Ya dafe kirjinsa, idanunsa na nuna tsananin zafi na rashin iya magana.
“Aure… Aure ya ci nasara… Farha… ita ta sani… ” Ya faɗi ƙasi yana tari...
Maleekh ya haƙura da tambayarsa duk da yana zargin mahaifinsu ne ɗari bisa ɗari. Maleekh ya kudirta cewa: “Koma waye asirinsa zai tonu…”
A daren yau an bada izinin ganin Farha, an fito da ita daga ɗakin tiyata. An kaita wani ɗaki na musamman.
Bayan sun shiga: Maleekh, Zayd, Amal, Hajiya Sa’adatu, da Alhaji Wadata da Alhaji Gusau sun zo a wannan lokacin. Ammy da Inna dasu Islam da sauran ƴan uwa da suka zo biki duk an hallara a ɗakin Farha.
Farha ta farfaɗo ba abunda take sai kuka. Ta kasa yin magana da kowa.
Mahaifiyarta (Hajiya Sa’adatu) ce ta zauna a bakin gadon tana rarrashinta, amma Farha sai ta fizge hannunta daga na uwar.
Cikin sanyin murya take faɗin
“Ku tafi! Bana buƙatar kowa, ku tafi!”
Hajiya Sa’adatu ta ce,
“Farha kinga…”
Farha ta katse ta da cewa,
“Bana son ganinki! Ki fita!”
Ba yanda ta iya haka ta fita. Alhaji Wadata yazo zaiyi mata magana, ta ce:
“Kar ka mun magana! Bana son jin muryarka! Daga yanzu har zuwa ƙarshen numfashina bana buƙatar ka!”
Alhaji Gusau ya ja Alhaji Wadata suka fita. Haka kowa ya fita domin tana buƙatar hutawa.
A daren nan iya su uku kawai suka kasance a ɗakin Farha: Maleekh, Amal, da Zayd.
Farha ta ɗago hannu tana shirin yiwa Maleekh magana. Da sauri ya riƙe hannun yana ɗan shashshafa mata. Ta sa ɗayan hannun ta buɗe tafin hannunsa ta ajiye masa mic ɗin da ya sanya mata. Wanda ya gano sirrinsu da shi.
Maleekh ya ɗago yana kallon Zayd ya ce,
“Ga Amal ka kaita gida please, zan zauna da Farha…”
Amal ta ce cikin kuka.
“A’a ka bari zan zauna da ita, tinda mace ce duk abinda take buƙata zanyi mata…”
Maleekh ya girgiza kai ya ce:
“Ki je ki kula da yara kawai, Zayd ku tafi…”
Amal ta juya, suna shirin tafiya sai sukaji an ƙira wayar Maleekh, Ya ɗaga. Jami’ai sun sanar dashi akan cewa an kama waɗanda suka kai farmaki.
“Okay ina zuwa yanzu…” Abin da Maleekh ya furta kenam.
Ya kalli Amal ya ce: “Ki zauna da ita…” Ya ce da Zayd: “Mu tafi…” Nan suka fita..
Amal ta zauna a kujerar jikin gado ta ce,
“Sannu Farha, ya jikin nakin?…”
Farha idonta akan Amal cikin sanyayye murya ta ce:
“Amal dan Allah ki yafe ni, na miki abubuwa da dama a baya, kuma lokacin da zan tafi ya gabato, nasan bazan cigaba da rayuwa a doron duniya ba, ki yafe mun…”
Amal ta riƙe hannunta da yayi sanyi sosai