Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
yi kuɗi su ma...
Amal ta ce "Inna mun yi kuɗi amma bana taɓawa bane..."
Cike da mamaki Inna take kallon ta sannan ta ce "to uban me zamu yi da ƙudin in ba taɓa wa ba? Haka kawai sai mu zuba musu ido muyi ta kallon su kamar madubi?....."
Amal tayi murmushi sannan ta ce "Inna idan muka bar su zuwa gaba zasu yi amfani, zamu cigaba da zama a yanda muke yanzu...."
Inna ta turo baki tare da kawar da fuska gefe ba tare da ta furta komai ba...
Amal da ta fahimci haka, ta sa hannu a jaka ta ciro 50k ta bawa Inna tana faɗin
"Ga shi Inna, dubu hamsin ya yi miki ko? nasan ba wani abun kirki zaki saya ba...."
Inna da sauri ta juyo tare da sa hannu ta karɓa tana faɗin "ba ni! ba ni!! zasu mun amfani nikam a yanzu, kuɗin haram nake gudu bana halal ba, ato...."
Murmushi Amal ta yi tare da kwantar da kanta akan cinyar Inna....
Wata daga cikin ma'aikatan gidan rediyo wanda suke tare da Amal..
mai suna Zulaihat tana zaune tana ƙiran waya cikin fushi, ta kasa ɓoye damuwar ta duk da bata bayyanar abinda ke damunta ba.
Zulaihat fitacciyar ce da ake yiwa kallon jaruma mai class a gidan rediyon a shekarun baya kafin zuwan Amal, amma tin zuwan Amal tana ganin kamar ana barinta baya, shafin ta ya rufe, taurarinta suka daina haskawa dake bata kai Amal jarumta da tsayar da magana ɗaya ba...
Zulaihat tana waya cikin hawaye take faɗin:
"Look, Amal tana ta ɗaukaka ne kamar wata waliyyar Allah, alhalin ni na fara sanuwa kafin ita, Na san me zanyi da ita, za mu ga wanda zai ƙara reposting bayan wannan."...
Cikin zafin rai ta kashe wayar sannan ta fara duba laptop dinta tana shirya wata ƙarya da za ta farfaɗo da wani scandal akan Amal tana hada hoton jabu na Amal da wani tsohon saurayi da ta taɓa yi masa hira a gidan rediyo, tana fassara hoton da kalmomin soyayya da cin amanar aiki.....
Washegari da dare, wani asusun bogi (@_ExposedGistNG) ya wallafa hoton Amal da rubutun cewa:
“Shin wannan ce jarumar da kuke yi wa ƙirari? Ga hoton Amal da wani babban ɗan siyasa suna soyayya cikin sirri a lokacin da take aiki... Kuɗin wane ne ke ɗaga ta?”
#Scandal #AmalExposed #ƳarTakiJaruma
A cikin awa ɗaya, comments sun fara zuwa da zagi da tambayoyi. Wasu na goyon bayanta, wasu kuma sun fara baza magana da zargi. Amma Amal bata ce komai ba tukun na amma ta ga duk abubuwan da suke faruwa, sai dai ta ɗauki hakan a matsayin jarabawa....
Amal tana zaune a ofishinta na gidan rediyo tana karanta comments cike da raɗaɗi....
Faruk da lawyer suna kallonta cikin tausayawa.
Faruk Ya ce
"Ki ce komai mana, Amal! Maza suna ta rubuce-rubuce, wasu sun fara janye goyon baya."
Amal cikin nutsuwa Ta ce:
"Faruk... Idan ina da gaskiya, ba zan buƙaci in ɗaga murya ba. Amma wannan karon zan maida martani. Amma ba da zagi ba ko cin mutunci ba, domin ba hali na bane...."
Lawyer Ta ce:
"Kiyi shirye-shiryen rubuta statement. Kuma mu fara gano waye ya wallafa wannan, za mu yi barazana da court order. Wannan cyberbullying ne...."
Bayan sun gama tattaunawar su, daga baya Amal ta sanar cewa zata yi jawabi a tashar su na rayuwa FM..
An shirya zama, Amal na zaune a cikin studio ɗin gidan rediyo. tana fuskantar cemara ba tare da ado ko yanayin farin ciki ba, tana zaune cikin hijabinta, murya cike da natsuwa take faɗin:
“Akwai wani abu da na koya a rayuwa, gaskiya bata buƙatar ihu. Kuma wanda ke da komai a zuciyarsa ba ya jin tsoron ƙarya da aka ɗinka masa daga waje.
Na ga hoton da aka watsa kuma na san me ke ciki. Hoto da aka ɗauka shekaru biyu da suka wuce lokacin da nake hira da wani baƙo a studio. Wani da yake son wulakanta ni ta hanyar shirya ƙarya, sai ya fassara abin da bai fahimta ba.
Ina da iyayen da suka koyar da ni tsoron Allah. Ina da Kakar da ta raineni da hawaye da addu’a. Kuma ba zan yarda a gina sunana a kan ƙarya da hasashe ba.
Amma wannan abu ya koya min abu guda cewa, akwai mata da yawa da ake mana haka kullum ana ƙulla mana sharri saboda kawai muna da tsayin daka da nutsuwa.
Don haka wannan bai shafeni ni kaɗai ba, Ya shafi kowace mace da ta gina kanta akan gaskiya kuma ake neman cin zarafin ta saboda dai ta ƙi lankwasuwa.
Ina tare da ku. Kuma zan ci gaba da wakiltar ku cikin gaskiya da ɗaukaka....”
Dakata wa tayi tare da sakin murmushi kaɗan, ta ƙara da faɗin:
“Ba wai ni ce jaruma ba ku ne jarumai da kuke tsaye akaina. Na gode.”
Ƙarshen tattaunawa...
A kafafen sada zumunta
TikTok, Instagram, da Twitter sun ɗauki bidiyon yana yawo kamar wutar daji.
Mutane da dama sun fara reposting da kalmomin: #DignityNotDrama #AmalStandsTall #VoiceOfDignity
Wani sanannen ɗan jarida ya rubuta cewa:
“Wannan ba kawai magana bace, wannan darasi ne. Amal ta koya mana cewa mace mai gaskiya ba buƙatar shela.”
Wata likita a Abuja ta rubuta cewa:
“Ni ban san Amal da farko ba, sai yanzu ganin farko naji ta burge ni, zan so ƴaƴana su girma su zama kamar Amal.”...
A wani sashen, Maleekh na kallon bidiyon Amal daga wayarsa, yana a zaune a cikin motarsa mai sanyi da leather seat. Ya dafe kansa, yana juyayi...
a hankali ya furta:
"Ta fi kowa. Wannan ba ƴar talaka ce kawai ba... wannan wata Queen ce.
amma hakan ba yana nufin na goyi bayan ta bane...."
Wani babban kamfani da ke da alaƙa da gwamnatin jihar, suna da hannun jari a gidan rediyon Amal ke aiki. Sun ƙira taro a sirrance.
CEO ɗan manyan mutane, mai suna Alhaji Ma’aruf yana faɗin:
“Wannan yarinya tana yawan fitowa da ra’ayoyi masu motsa mutane. Muna son kwanciyar hankali. Idan mutane suna sauraren Amal, ba za su saurari shugabanni irin mu ba.”
Wani daga cikin su ya ce:
“Za mu samar mata da wata hanyar da zata shigo cikinmu, mu rufe bakinta da kuɗi… ko kuma mu wanke ta gaba ɗaya daga kafar sadarwa.”...
Washegari, Amal ta karɓi gayyata zuwa wani taro.
A can ta iske babban mutum Alhaji Ma’aruf yana mata tayin aiki: albashi mai girma, gida, mota, kwangila. Amma da sharaɗi guda.....
Alhaji Ma’aruf cikin ƙwarewa yake faɗin:
“Kina da wayo, Amal. Muna son ki shigo mu gina Najeriya tare. Amma ki rage yawan fitar da abubuwan da ke ɗaga hankali. Duniya bata son masu sa mutane tunani sosai.”
Amal cikin kwanciyar hankali ta ce:
“Ina son ƙasata, kuma ina son gaskiya. Amma idan wannan tayin yana nufin in yi shiru akan abubuwan da ke damun mutane to ku ci gaba da neman wata mafita....”
Ta miƙe cikin natsuwa ta bar wurin, kowa yana kallonta cike da mamaki...
Bayan kwana biyu da faruwar haka..
Wasu saƙonni marasa suna sun fara shigowa wayarta:
“Kada ki ɗaga murya fiye da haka…”
“Ki zabi zaman lafiya, ko zaman lafiya ya ƙi ki.”
“Mun san inda tsohuwar da ta raine ki take.”
Inna jin labarin tashin hankalin da suke shirin shiga, sai kawai ta fashe da kuka...
Amal fashe wa tayi itama da kuka tana rarrashin Inna tare da faɗin:
"Inna in sha ALLAH babu abinda zai faru da mu, muna kan hanyar gaskiya, kuma Allah yana tare da mai gaskiya, ki kwantar da hankalin ki Inna...."
Itama Inna kuka take tana rawar murya ta ce:
"Amal ina tsoron wannan rayuwar da kike gudanar wa, ina tsoron rasaki Amal, in da hali ki bar aikin gaba ɗaya kizo mu zauna a gida..."
Amal ta ce:
"Kar ki damu Inna akwai lokaci..."
Da haka Amal ta rarrashi Inna har suka yi bacci...
★★★★★
Maleekh kuwa cike da jin haushin Amal yake kwana yake tashi, gaba ɗaya ya tsani yarinyar har cikin ransa, cike da damuwa yake faɗin "Ni zata tozarta a idon duniya? ballagazar yarinya ƴar talakawa..."
Cikin zafin rai ya nufi gaban mirror, nan ta ke ya fara farfasa mirror yana ihu, yana tarwatsa kayan ɗakin sa...
Jin ihu yasa mahaifiyarsa ta shigo da gudu tare da ƙannen sa mata, daƙer Uwar ta riƙe shi tana rarrashin sa domin tinda abun ya faru ya kasa kwantar da hankalinsa, ko ci da sha baya samu damar yi, kullum a cikin tunani yake, takaicin sa tinda yake babu macen da ta taɓa tozarta shi sai Amal da take talaka faƙiriyar yarinya....
Sai da iyayensa suka tura shi England kafin ya samu kwanciyar hankali, domin a Nigeria kullum zafin takaicin Amal hana shi sukuni yake, da ya koma wa can kuwa sai abubuwa suka fara fita masa a rai, ya rage damuwa amma ya kasa manta da Amal...
Dake a can akwai masu kula da shi sosai, basa barin sa yana shiga damuwa, da haka ya koma normal kamar bai je Nigeria ba, amma idon sa akan Amal yake a TV da laptop ɗin sa......
★★★★
Washegari bayan Amal ta kammala aikin ta na yau a gidan rediyo Rayuwa FM......
Amal ta fito daga gidan rediyo Rayuwa FM tana shirin tsallaka titi domin komawa gida, sai ga wata baƙar mota ƙatuwa tazo ta sha gabanta tare da jan yo ta ciki suka wuce da gudu ba tare da mutane sun an kara ba,
Wani tsararren gidan gomnati aka kaita wurin da Governoni da manyan ƴan siyasa suke taruwa,
Zaunar da Amal akayi a ƙasin carpet an rufe mata baki da fuska gam, a lokacin aka cire mata baƙar hular da suka rufe mata fuska da baki, idonta ne suka sauƙa akan wasu manyan ƴan siyasa wanda bata taɓa ganinsu ba sai a poster da kuma jin labarin su, yau ta gan su a zahiri,
Ga wasu manyan security a tsaye a gefe guda suna riƙe da bindigun su,
an tsawatar wa Amal sosai tare da barazanar zasu sa a kasheta idan ta cigaba da fito da gurɓatattun bayani akan su,. Suka zazzage ta tare da ƙiranta da ƴar talakawa, sunyi barazanar zasu kashe ta kuma su kashe Kakarta kuma babu hukumar da ta isa ta hukunta su domin sune suke riƙe da hukuma,
Amal ko kaɗan bata ji tsoron su ba ko fargaba haka ta tsaya tana musayar yawu da su, cikin jarumta.....
Wani dattijo mai tumbi wanda ta taɓa ganinsa a poster na zaɓe, ya buɗe baki cikin murya mai cike da izza ya ce:
"Kece Amal Abdulsamaad? Wannan baƙin ciki da kike yaɗawa a radio da social media zai ƙare yau. Mun gaji da sharrinki!"...
Wani ɗan siyasa ya ƙara da zazzafar murya cewa:
"Ƴar talakawa mai rainin hankali! Me kika sani game da mu har kike shisshigi cikin rayuwar mu? Mu muke riƙe da wannan ƙasa!"
Amal ta ɗago kai, tana kallon su ba tare da rawar murya ba, duk da hannunta a ɗaure yake. Muryarta cike da ƙwarin gwiwa ta ce:
"Na sani, ku da kuke cewa kuna riƙe da ƙasa, ƙwarai kun riƙe da zalunci. Amma Allah yana kallon ku. Ku ne kuka haddasa halin da talakawa ke ciki, kuna sace hakkin marasa galihu kuna fakewa da dokokin da kuka rubuta da kanku."
Wani daga cikinsu ya ce:
"Zamu kashe ki! Kuma ba wani hukuma da zai sani balle yayi bincike!"
Amal ta ce:
"Ku kashe ni, amma gaskiya ba zata mutu ba. Ina jin kunyar cewa ni marainiya ce kuma talaka wanda bani da halin taimaka wa talakawa, amma ni ba zan ji kunyar faɗin gaskiya ba. Ku ne matsalar ƙasar nan, kuma ku ne dalilin da yasa yaran da ke da basira kamar ni ke cikin wahala. Sai ku ke raina mu, kun hanamu ci gaba a rayuwa!"...
Wani babban jami’i ya matso da bindiga a gefe yana huci, yana kallon Amal cikin ƙyashi.
Amma Amal ta cigaba da magana cikin fushi da karyewar zuciya:
"Idan da gaske kuke kuna da iko, to me yasa kuke tsorata da murya ta? me yasa baku so na bayyanar da gaskiyar halin da mutane ke ciki? Wannan ƙasar ba mallakin ku bace. Ku ne kuke damun ta!"
Sauran 'yan siyasan ne suka fara kallon juna cike da mamakin ƙarfin gwiwar yarinyar. Ba yanda suka iya da ita haka suka bada umarni a ɗaure ta a ɗaki har sai sun yanke hukunci akan rayuwarta....
An nemi Amal an rasa, Inna ta shiga damuwa, gidan rediyo Rayuwa FM tayi sanyi jin labarin anyi kidnapped Amal...
A Rayuwa FM, ma’aikata sun ruɗe.
Sun katse shirye-shiryensu, suka bada sanarwar bacewar Amal. Jama’a sun fara magana a gari, an fara ƙirarin za'a yi zanga-zanga na rashin tsaron lafiyar marubuta da 'yan jarida masu gaskiya.
A gefe guda... Inna tana kuka a gida, tana addu’ar Allah ya fitar mata da Amal....
"Ya Allah ka dawo mun da jikata lafiya... Amal, ki dawo gida mana."
A nesa, cikin ɗaki a ƙasar england, Maleekh ya zuba coffee a cikin cup, yana sanye da singlet da 3quarter.
Ya kunna laptop, yana kallon rahoton da ke cewa Amal ta ɓace. Sai ya saki wata ƙaramar dariya mai cike da izza yana faɗin:
"that's good! Nasan wannan lokacin zai zo, yarinya marar kamun kai, zaki gane da ruwa ake shayi a hannun manyan mutanen Nigeria....
Ya yi wasu maganganu da rashin damuwa akan abinda ya faru da Amal,
Sannan ya furta:
"Let her learn the hard way, This is Nigeria, ba wani yanki bane inda 'yan talakawa ke zagin manya su tsira lafiya."
★★★★★★
A cikin ɗakin da aka ɗaure Amal...
Tana zaune a ƙasa, an ɗaure hannayenta da ƙafafunta, amma zuciyarta bata ɗaure ba. Kamar mai jin ƙarfin wata iska daga sama, ta ɗago kai tana sauƙe ajiyar zuciya. A hankali ta fara karanta addu’o’i da ayoyi cikin ranta, ba ta yi kuka ba sannan ba ta girgiza ba, amma jikin ta yana bada wani sanyi da tsantsar jarumta. ɗaya daga cikin jami’an tsaro ne ya matso da abinci ya ajiye a gabanta ba tare da ya kalle ta ba, ya since mata hannaye tana gamawa aka ƙara ɗaure ta ..
A lokaci guda a waje...
Wasu daga cikin ma’aikatan gidan gomnati suna ta waya da mutane daban-daban suna yunkurin ɓoye labarin bacewar Amal. Amma a waje, duniya ta fara motsawa.
Rayuwa FM sun fitar da sanarwa cewa:
"Mun rasa ɗaya daga cikin ƙwararrun ma’aikatan mu, Amal Abdulsamaad, bayan fitowarta daga ofis jiya da yamma. Muna ƙira ga hukumomi da jama’a da su taimaka wajen gano inda take..."
Social Media ta karaɗe da hoton Amal da rubuce-rubucen:
#FreeAmalNow
#JusticeForAmal
#TruthIsNotACrime
Gaba ɗaya gari ya ɗau zafi.
Ƴan jarida da kungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun fara yawo da labarin. Wasu fitattun mutane suna wallafa goyon baya gareta, wasu suna cewa: “Kalmar gaskiya duk wanda ke faɗin ta sai an ɗauke shi”, hakan ya jefa tsoro cikin zukatan wasu, amma ya ƙara juriya cikin zukatan wasu da dama.
A wani ɓangare kuma...
Maleekh yana zaune yana kallon wannan hayaniya a tv. Cikin zuciyarsa yana fargaba amma a fili sakin murmushi ya yi,
Ya ƙira Rikky Blaze ta video call yana faɗin
"Rikky, ina so ka kawar da wancan yarinyar daga labarai... ba damuwata me za ka yi ba, amma dole muryarta ta ɓace!"
Rikky ya ce:
"She’s already disappeared, boss. The problem is people won’t shut up."
Maleekh ya ce:
"Then shut them up. Everyone has a price....
Bari ta gama shan wahala, zata gane rayuwa ba wasan yara ba ne. A Najeriya take ƙasar da ‘yan ƙasa irin ta ba su da wata kima idan sun raina manya. Wacce 'yar talaka ce za ta fito tana zagin giwa ta kuma yi tsammanin zata tsira? Ai sai ta ɗanɗani azaba, ta gane cewa hauka da raini na da farashi mai tsanani!"
Rikky ya ce:
"Ogah! Yarinyar tana da taurin kai ne, sannan tana da jarumta dubi yanda ta tozarta sunan ka a ƙasar...."
Maleekh cike da mugunta yake faɗin:
"Zata sha wahala ne, zan koya mata darasin da zai ɗaure mata kwakwalwa har abada. zan nuna mata cewa ƙasata ba kasar tatsuniya bace, Najeriya ne! Inda ‘yan talaka ba su da murya idan sun taka layin manya. Wacce ce ita? Wacce 'yar raini ce da za ta fito tana zagin giwa a gaban jama'a? Ai sai ta ɗanɗani wahala, ta gane cewa a Najeriya, rainin hankali yana da farashi. Kuma wallahi, zan tabbatar an biya wannan farashin sau biyu!...."
Yana huci ya kuma cewa: "ƴar matsiyata jikan talauci, ban da talakawa wa zai tsaya ɓata lokacin sa wurin sauraron ta...."
Rikky ganin yanda ran Maleekh ya yi matuƙar ɓaci yasa shi cewa:
"Sorry Ogah...."
Maleekh Yana magana idonsa na haskawa da ƙiyayyar Amal yana faɗin:
"A gaban duniya za ta fallasa ni? Ni Maleekh?! Wacce ce ita? Wace ‘yar tasha ce zata tsaya a gabana ta ce wai zata yi magana akan gaskiya? Gaskiya? A ƙasar da kowa ke sayar da gaskiya don ceton kansa?"
Zama ya yi daga tsayen da yake ya miƙar da ƙafa tare da durƙar da kansa akan table ɗin gaban sa yana magana yana ƙwanƙwasa teburin da yatsarsa:
"Zan koya mata darasi ta hanya mai tsanani. Zan nuna mata cewa Nima ɗan Najeriya ne, Ba a waje nake ba da ‘yan talakawa ke wulakanta manya su tsira. Wallahi sai ta gane cewa rainin hankali a kasar nan yana da tsada, kuma zan tabbatar ta biya da wahala."
"Ka yi mata fiye da haka,"
Rikky ya ce shima cikin ɓacin rai.
Sannan ya ci gaba da cewa
"Za mu nuna mata yadda ake wasa da wuta