Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
take wulaƙanta mu?”
Maleekh ya ɗago kansa a hankali, murya a karye:
“Ammy, karki ci gaba da cewa haka. Amal bata da laifi… bata taɓa cutar da kowa ba. Ita ce rayuwata… idan har ba ita ba, to babu wacce zata iya maye gurbin ta a zuciyata.”
Abbah ya hura iska cikin takaici, ya juyo da murya mai taushi da ƙarfi yana faɗin:
“Maleekh! Ka saurare ni sosai… ba haka rayuwa take ba. Idan ma soyayya kake, akwai iyaka. Kai ɗan manya ne, ka san irin matsayi da nake dashi a ido al’umma. Ba zamu iya bari ka zubar mana da mutunci saboda mace ba.”
Maleekh ya matso kusa da su, muryarsa na rawa ya ce:
“Abbah, wallahi bana neman abin duniya. Bana neman gadonku. Abinda nake nema kawai shine ita. Ita ce nake so. Kuma idan wani ya sake ƙoƙarin ɗaura mata aure, wallahi sai dai a mayar da wurin, gurin jana’iza!”
Ammy ta rintse ido cikin fushi, ta ɗaga hannu tana nuna masa ƙofa:
“To sai ka fice daga wannan gida! Idan soyayyar Amal tafi iyayenka, tafi martabarka, to fita ka koma wajenta! Amma wallahi a wannan gidan, baza ka taɓa auren ta ba. Na rantse da Allah!”
Shiru ya ratsa ɗakin. Sai numfashin Maleekh da ya tsananta.
Abbah ya kalli Ammy ya ce
"Kin ga, ɗauko mun ruwan sanyi, makogorona ya bushe..."
A fusace Ammy ta bar falon kai tsaye frig ta nufa...
Abbah cikin murya mai sanyi ya ce:
"Maleekh... kai da nake ganin ka fi kowa nutsuwa, sai ka zama abin mamaki? Shin wannan aikin da ka aikata daidai kake ganin yayi ne? Gidan mutane ka shiga da wuƙa a hannu, ka firgita jama'a, ka tozarta sunan iyayenka?"
Maleekh ya kasa ɗaga kai. Idanunsa sun kumbura, a hankali ya furta:
"Abbah… ba zan iya kallon Amal tana auren wani ba… wallahi ba zan iya ba."
Abbah ya girgiza kai cikin takaici. Ya ce
"Amal mace ce, kuma auren nan addini ne, ba hauka ba. Kana so mutane su ce ɗana ya haukace saboda mace?"
Kafin ya ƙarasa, Ammy ta shigo cikin falon da sauri. Tana ɗauke da tray da jug ɗin ruwan sanyi da cups kananu, tana harararsa cikin fushi...
Ta ajiye glass ɗin ruwan da ƙarfi a tebur..
Ta cigaba da faɗa tana faɗin:
"Bazan taɓa yarda ka auri yarinyar nan ba! Wacce bata da asali, bata da daraja. Kai ɗana ne, ɗan mutunci da ƙima — ba zaka lalata rayuwarka saboda ita ba!"
Maleekh ya ɗaga kai cikin zafi, hawaye na zubo masa, murya na rawa ya ce:
"Ki faɗi duk abinda kike so, Ammy… Amma wallahi bazan iya rayuwa babu Amal ba. Ko dai ta zama matata, ko kuma ni na bar wannan duniyar gaba ɗaya!"
Ammy ta ɗaga hannu cikin mamaki da haushi, ta ce:
"Inna lillahi! Ka fara hauka kenan Maleekh?! saboda mace?"
ABBAH a tausashe ya ce:
“Daina faɗin haka ɗana. Ka bar wannan fushin. Idan har kaddara ta ce ita ce taka, babu wanda zai iya hanaka. Amma yanzu, ka kwantar da hankali. Ka barni da wannan maganar.”
Maleekh ya girgiza kai, hawaye suka zubo masa a kunci.
Ya ce:
“Abbah, ko da me zai faru, bazan taɓa bari a raba ni da ita ba. Babu wanda zai iya raba zuciyata da Amal. Koda hakan zai zama ajali na…”
Abbah cikin murya mai ƙarfi, yana ɗaga hannu ya ce:
"Is enough! Ku daina wannan maganar a gaban na.. Maleekh, wannan abun da kayi ba daidai bane. Amma yanzu… kayi shiru. Idan har kana son kiyayewa da wannan yarinya, to sai ka nutsu. Ka bar min maganar. Amma ka sani —"
Ya ɗan ja numfashi.
"Duk wanda ya kuskura ya sake jawo irin wannan tashin hankali, sai hukunci ya ziyarce shi. Amma, idan soyayyarka gaskiya ce, zan bincika wannan al’amari."
Maleekh ya zube a ƙasi yana share hawaye, yana kallon Abbah kamar ɗan da yake neman gafara. Ya ce
"Abbah, wallahi bana neman komai… burina ka bari Amal ta zama tawa. Zan iya fuskantar komai saboda ita."
Abbah a hankali, yana kallon shi da tausayi ya ce:
"Ka tashi ka je ka huta. Zan yi magana da Inna Delu… amma idan har na sake jin wani tashin hankali, ka sani wannan karon ba zan tsaya ba."
Maleekh ya tsaya tsayin daka yana kallon ƙasi. Ammy ta tsaya tana kallonsa da mamaki, ganin hawaye suna zubo masa...
Maleekh ya ce:
"Ko me zaku yi, ba zan bar Amal ba. Soyayya ce, ba son zuciya ba."
Ammy ta yatsina fuska ta ce:
"To mu gani… wane ƙarfin soyayya ne zai doke ikon uwa da ɗanta."
Yayi shiru yana kallon su, ya juya a hankali, ya fice daga falon cikin nutsuwa amma a zuciyarsa wuta ce take ci.
Abbah ya bishi da ido cikin damuwa, ya sauƙe numfashi.
Ammy ta zauna ta dafe kai, tana faɗin:
“Allah Ya shirya mana wannan yaro… saboda ina tsoron abin da soyayyar nan zata haifar.”
Falon ya koma shiru kamar ba kowa...
☆☆☆☆☆
Washegari da safe, zuciyar Abbah cike take da nauyi. Duk daren jiya bai runtsa ba. Kalaman Maleekh, duk suna masa yawo a cikin zuciyarsa. Yasan yanzu lokaci ne da ya kamata ya ɗauki mataki mai kyau domin rikicin ya kai matakin da idan bai shiga tsakani ba, zai iya lalata komai.
Ya shirya cikin farin babban riga, ya ɗauki hularsa ya fita da nufin gidansu Amal.
Lokacin da ya isa, gidan yana cike da natsuwa. Inna na zaune a falo tana lissafin kuɗin da aka kashe wajen shirye-shiryen auren da aka wargaza. Ganin Abbah yasa ta ɗan firgita ta tashi da girmamawa.
Ta ce da murmushi mai nauyi,
“Alhaji, sannu da zuwa, ai bamu tsammanin ganinka yau ba.”
Abbah ya gyara zama, ya ɗan shafa gemunsa cikin natsuwa, sannan ya ce:
“Inna Delu, na zo da magana ta hankali. Akwai abubuwa da suka kai yanzu dole sai an fahimta.”
Inna ta girgiza kai, ta ce:
“To ai yanzu duk duniya ta ji abin da ɗanka yayi jiya. Wani irin abin kunya wallahi. Idan ba don kai mutum ne mai mutunci ba, da na fadi abinda zuciyata ke ji.”
Abbah ya sauƙe ajiyar zuciya. Ya ce
“Inna, wallahi abin ya bani haushi fiye da kowa. Amma ki fahimci abu guda — ɗana yana cikin soyayya, kuma soyayyar da ta kai mutum ya yi wauta irin waccan… ba ƙaramin abu bane.”
Inna ta saki dariyar takaici,
“Soyayya fa kake cewa, Alhaji? Wannan hauka ce, ba soyayya ba. Kasan irin abinda ya aikata a gaban jama’a kuwa? Ya ɓata mun suna, ya ɓata sunanku. Yaronka fa ya ɗora wuƙa a wuyan ɗan mutane!”
Abbah ya ɗan lumshe ido, yana magana cikin tausasawa,
“Inna, na fahimci damuwarki. Amma ki saurare ni — ni a matsayina na uba, bana son wannan auren Amal da Kabiru, domin hakan ba zai kawo mata farin ciki ba. Maleekh ya fi ƙarfin da kike tunani, kuma soyayyarsa ta kai matakin da idan kika ƙi, zai iya lalacewa gaba ɗaya.”
Inna ta jinjina kai da takaici,
“To ai wannan ba dalili bane da zai sa a mayar da abin da ya aikata kamar wasa. Ko a ƙauyensu waɗancan ma da mutum yayi haka da wuƙa, ai tuni an ɗaure shi.”
Abbah ya ce cikin natsuwa,
“Na sani, amma yanzu ina so mu duba gaba. Ki faɗa min gaskiya Inna — Amal, har yanzu tana son Maleekh?”
Inna ta ɗan yi shiru, sannan ta ce,
“Wallahi ina ganin tana son shi. Duk da kuka da ƙuncin da tayi, tun jiya bata ci abinci ba, bata yi bacci ba. Amma ni ban yarda da shi ba, tunda mahaifiyarsa ta riga da ta nuna bata son ‘yar talakawa kamar mu.”
Abbah ya sauƙe numfashi a hankali, ya ce:
“Inna, ni zan daidaita komai. Zan je na zauna da Uwar yaron da kaina. Idan Allah ya yarda, zamu warware komai cikin mutunci. Ba a son ta auri wanda bata so. Kuma ni a matsayina na uba, bana son wulakanta ɗiyar da nake ganin kamar ‘yata ce.”
Inna ta ɗan share hawaye tana murmushi,
“Alhaji, Allah ya saka da alheri. Idan har zaka iya daidaita wannan, to ni na yafe masa. Amma fa, ka gaya wa matarka ta kiyayi yi wa Amal rashin mutunci.”
Abbah ya miƙe, ya ce da nutsuwa,
“Zan gaya mata. Na yi alkawari. Insha Allah wannan soyayyar bazata zama jaraba ba, sai dai rahama.”.
Ya ciro damin kuɗin wanda zai kai 300k ya bata akan ta rage asara..
Inna tana washe baki ta fara godiya, ta durƙusa har ƙasa tana masa albarka...
Suka yi sallama da nutsuwa.
Abbah ya fita yana tunani “Yanzu lokaci ne da zan fuskanci Maryam. Amma da yaushe zata fahimci cewa zuciyar ɗa ba a mulkinta?”
✨ Inna tana kallon ƙofar da Abbah ya fita tana faɗin cikin zuci:
“Allah ka shirya wannan al’amari. Kada a sake jefa Amal cikin wani tashin hankali…”
A daren yau..
A cikin babban falon gidan Abbah, ƙarshen daren ranar da ya dawo daga gidansu Amal.
Wurin ya cika da nutsuwa, sai ƙamshin turaren oud da aka kunna. Abbah yana zaune a kujerar fata yana sosa gashin kansa cikin gajiya. A gefe kuwa Ammy ta shigo da sauri, tana sanye da rigar babu da ya lulluɓe jikinta, idonta kuwa cike da fushi...
Ammy cikin ɗaga murya ta ce:
"Alhaji! To ka dawo ko? Ashe gidan su waccan yarinyar Amal ka je?
Abbah: cikin natsuwa, yana ɗan sauƙe numfashi ya ce:
"Na tafi ne saboda neman lafiya, Maryam.. Na je ne in fahimci gaskiyar abin da ke faruwa tsakanin Amal da ɗanmu Maleekh..."
Ammy ta taka zuwa gabansa ta ce:
"To meye abunda zaka faɗa yanzu? Wancan matsiyaciyar yarinyar nan da bata da komai face tsiya? Wallahi bazan yadda ta shigo gidanmu a matsayin suruka ba!.."
Abbah yana kallonta cikin tausasawa ya ce:
"Maryam, ki kwantar da hankalinki. Wannan al’amarin ya rigaya ya fita daga ikonmu. Maleekh yana sonta, kuma na ga soyayyar nan bata wasa bane. Ki barshi ya samu nutsuwa..."
Ammy ta dafe ƙirjinta cikin jin haushi ta ce:
"Nutsuwa kake faɗa? Wato bayan duk abinda aka riga aka shirya, bayan Farha, yanzu za’a wurgar da ita kamar jaka saboda wata yar talaka? Alhaji, wallahi wannan ba zai taɓa faruwa ba! Ba da ni ba!.."
Abbah ya miƙe a hankali yana dubanta da murmushi mai natsuwa ya ce:
"Maryam... na fahimci kina son Farha kamar ƴarki. Amma mu bar Allah ya zaɓa wa ɗanmu abinda ya fi alkhairi. Duk mu mun ga yadda yake fama tun da aka fara wannan maganar. Ki duba zuciyarsa, ya fita hayyacinsa saboda soyayya..."
Ammy ta juyo da ƙarfi tana nuna shi da yatsa tare da faɗin
"Kai dai ka sani, ko Maleekh ya auri Amal, wannan ba zai taɓa zama cikin farin ciki ba idan har ba a daidaita al’amura ba!.."
Abbah ya zauna yana tambaya cikin natsuwa.
"Me kike nufi da “daidaita al’amura” Maryam?.."
Ammy ta tsare shi da ido, muryarta ta ɗan yi sanyi ta ce:
"Sharadina guda ɗaya ne, Alhaji. Idan har kana so in yarda Maleekh ya auri waccan Amal ɗin, to sai ya haɗa aure da Farha. Na ce dole sai ya auri mata biyu Amal da Farha a lokaci guda. Idan ba haka ba, wallahi ba zan taɓa yadda da wannan auren ba!.."
Abbah ya tsaya kallonta cikin mamaki, yana jin nauyin maganarta ya ce:
"Maryam… wannan sharaɗi naki yana da nauyi sosai. Kin tabbata wannan shine abin da ke ranki?.."
Ammy ta ɗaga kai da tabbaci ta ce:
"Na tabbata. Idan har Amal zata shigo gidan nan, to Farha ma zata shigo a lokaci guda. Babu mace guda da zata mallaki zuciyar ɗana gaba ɗaya..."
Abbah ya sauƙe numfashi, yana jinjina kai ya ce:
"To... Maryam, na ji. Amma ki sani, wannan al’amari sai dai mu bar Allah ya hukunta shi. Domin soyayya bata da dokar da mutum yake rubutawa da hannunsa...
Ammy ta ɗan juya tana kallon ƙasa ta ce
"To kai dai ka sani Alhaji, na faɗa maka abinda ke cikin zuciyata. Wannan shine sharaɗi na ƙarshe..."
Ta juya ta bar falon, tana daidaita numfashinta. Abbah ya zauna yana kallonta a yayin da take barin falo, ya dafe kansa da hannuwa biyu, yana faɗin a hankali...
“Subhanallah… soyayya ta fi ƙarfin iko. Amma wannan gwagwarmaya zata ba da tarihi mai tsawo.”
Washegari da sassafe a gidan su Maleekh. Sanyin safiya na shiga cikin babban falon da yake cike da nutsuwa da ƙamshi. Abbah yana zaune a kan kujera mai faɗi, A gefe Ammy tana zaune cikin ɓacin rai. Maleekh yana gefe yana jujjuya zoben hannunsa, Farha na kusa da shi tana ɗaure fuska. Sai ga Amal an kawo ta gidan cikin hijabi, idonta cike da nutsuwa amma a bayyane akwai tsoron abin da ke gabanta...
Abbah a hankali, yana kallon Amal ya ce:
"Ki zauna nan, ‘yata. Muna so muyi magana cikin natsuwa..."
Amal ta durƙusa har ƙasi ta ce:
"Na’am Abbah… ina kwana.."
Abbah ya amsa da...
"Lafiya lau..."
Amal ta gaishe da Ammy. Ammy ta kawar da kai tare da jan dogon tsaki ta kawar da kai gefe...
Abbah yana fuskantar Amal ya ce.
"Kin ga, wannan magana ba ta yara bace, saboda tana da nasaba da rayuwar mutane uku — ke, Maleekh da kuma wannan yarinya (ya nuna Farha).
Ni dai ban so wannan rikici da ya faru ba, saboda ni kai na na ji kunya a gaban jama’a..."
Maleekh ya ɗago kai da ƙarfi ya ce.
"Abbah, ni ba na jin kunya! Na aikata abinda na yi ne saboda bana so a cuce ni. Amal tawa ce, kuma ba zan bari a ɗaura mata aure da wani ba!.."
Ammy ta tsawata masa da cewa:
"Kai kayi mun shiru, Maleekh!
Tun da na haifeka ban taɓa tunanin zaka zubar min da mutunci irin haka ba.
Ka shigo cikin manya, kana ɗaga wuƙa da alfaharin zaka kashe mutum! Idan ba hauka ba, menene haka?.."
Maleekh yana yatsina fuska ya ce:
"Hauka kike cewa? Saboda ina son Amal?
Ammy, ina girmamarki, amma ki sani soyayya ba ta kallon arziki..
Kina so ne in auri wadda kike so, ba wadda nake so ba?.."
Farha cikin muryar kuka tana kallon Maleekh ta ce:
"To me yasa sai ita?
Ina sonka Maleekh, ka san hakan.
Tun muna yara ake cewa mu biyu mun dace da juna, Amma yanzu, sai wata talaka ta kwaceka? Me take da shi da ni ban dashi?.. "
Amal tana kallon Farha cikin nutsuwa ta ce:
"Farha… ban so in shiga tsakaninku ba.
Farha, wallahi ba ni na nemi wannan soyayya ba. Ƙaddara ce ta haɗa ni da shi. Ba nayi ne da ganganci ba. Ki daina ganina a matsayin mai kwace...."
Ammy ta tsuke baki, tana dariya cikin raini ta ce:
"Kaddara ko? Kaddarar talauci?. Ki ji ni da kyau Amal, bana son ki cusa kanki a cikin zuciyar ɗana. Idan kika ci gaba da kusantarsa, sai kin ga abin da bai miki daɗi ba!.."
Abbah ya ɗaga hannu cikin natsuwa ya ce:
"Maryam! Iska ce ta fi zafi yanzu. Ki bari nayi magana..."
Ya kalli Amal da ta sunkuyar da kai.
"Amal, na san kina cikin tashin hankali. Amma ki sani, ba wanda zai iya raba soyayya ta gaskiya da niyyar Allah.
Ni da kaina na ga irin ruɗanin da Maleekh yake ciki, kuma wannan abu ba zai daidaita sai an zauna an fahimta..."
Ya kalli Maleekh da idanu masu nauyi sannan ya ce
"Kai kuma, Maleekh, daga yau ban so in sake jin tashin hankali daga gareka.
Idan wannan soyayyar taka gaskiya ce, za mu bi ta hanya mai kyau. Amma idan wata zuciya ce ta hauka, ka kwantar da kai ka gyara halinka..."
Maleekh ya sauƙe numfashi, yana girgiza kai ya ce:
"Abbah, wallahi bana hauka.
Ni dai ba zan bar Amal ba. Idan za’a hukunta ni saboda haka, to na amince..."
Abbah da murya mai tausayi ya ce:
"To idan haka ne, za mu fara da sulhu.
Na ƙira ki (ya nuna Amal) da ke (ya nuna Farha) domin yau in ji gaskiya daga bakin kowanku.
Saboda wannan soyayyar ta zama rigima..."
Yana kallon su uku a jere Maleekh, Amal, Farha.
Abbah ya sauƙe murya cikin tausayi ya ce:
"Wannan gida nawa ne. Ba zan bari soyayya ta zama dalilin rarrabuwar kai ba. Amma duk wanda ya ci gaba da tada hankali to dole sai ya fita daga rayuwarmu..."
Amal ta share hawaye, ta yi murmushin ƙarfin hali. Maleekh ya ɗaga kai yana kallon mahaifinsa da girmamawa, sannan ya kama hannun Amal a hankali yana farin cikin haɗuwarsu. Abbah ya yi shiru, ya zuba musu ido cikin tausayi, yayin da Ammy ta ɗauke kai tana jin haushi...
Maleekh cikin murya mai taushi ya ce:
“Abbah, ni fa ba zan bari a ɗaura auren Amal da wani ba. Tunda rayuwata ta haɗu da tata, ita ce nake so, kuma ba zan iya rabuwa da ita ba.”
Ammy tana huci ta ce
“Ka daina faɗin hakan, Maleekh! Wallahi bana so inji sunan wannan yarinyar a bakinka. Yarinyar da bata da asali, jikan talakawa, matsiyaciyar da ta lalata gidanmu! Ba zan yarda ka aureta ba!”
Maleekh ya ɗaga kai yana kallonta kai tsaye ya ce:
“Ammy, ki ce komai, amma ba zaki raba ni da ita ba. Ni Amal zan aura, ko da zan rasa komai.”
Ammy ta miƙe tsaye tana daka masa tsawa..
“To shikenan! Idan har ka nace zaka auri wannan yarinyar, to sai ka aura da Farha a lokaci guda. Ita da Amal! Wannan shine sharadina, kuma haka na tsara da mahaifinka, in shi ya kasa sanar maka to ni zan faɗa domin ba tsoronka nake ji ba..!”
Abbah ya ce cikin murya mai nutsuwa..
“Ka ji abin da mahaifiyarka tace, yarona. Ka yarda da ita. Ita uwa ce. Ka faranta mata, ka bi umarninta. Ka aure su duka biyun, Allah zai sa albarka.”..
Ya kalli Farha, wacce ke zaune cikin jin daɗi da ƙasa da murya:
“Ke kuma Farha, na roƙeki da ki riƙe Amal, ki zauna da ita lafiya. Bana son tashin hankali a cikin gidan.”
Sai ya kalli Amal, wacce take gefe, idonta cike da hawaye..
“Amal, kiyi haƙuri. Komai sai da jarumtaka. Wannan rayuwa ce, kuma idan kika dage da addu’a, Allah zai saka miki. Ki yadda a haɗa ku, domin zaman lafiya.”
Amal da murya mai rauni ta ce..
“Na ji Abbah… amma…” (ta kasa magana, tana share hawayenta)...
Maleekh ya ɗaga kai, yana murmushin dole, cikin dariyar da ke cike da ciwo ya ce:
“To, idan haka ne, zan yarda in aure su biyu…”
Kowa ya kalle shi da mamaki.
Sai ya juyar da kallonsa zuwa ga Farha.
Maleekh cikin murya mai ƙarfi, yana kallonta kai tsaye ya ce:
“Amma kafin hakan ta faru, akwai sharaɗi guda ɗaya. Idan Farha tana so in aureta, to sai ta zauna a gaban television ta amsa laifinta. A gaban kowa.”
Kowa ya juyo, yana