Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
ce ta ziyarce ta bayan barinta gidansu Maleekh da sauran ƴan uwanta...
Inna tana zaune a falo tana lissafin abubuwa sai ga ƙarar horn ɗin mota ta dawo da ita daga cikin tunani.
Kafin a ankara, motoci uku suka tsaya a harabar gidan bayan maigadi ya buɗe musu. An buɗe ƙofar mota, sai ga Hajiya Sa’adatu, mahaifiyar Farha, ta fito cikin hargowa da matsananciyar fushi. Tare da ita akwai wasu ‘yan uwa mata guda su biyar, duk sanye da kayan alfarma, amma fuskokinsu cike da ƙyama da hargowa.
Maigadi ya yi gaggawar ƙarasowa yana tambaya,
“Hajiya lafiya kuwa?”
Ta ce da ƙarfi,
“Ina Amal take? Muna son ganinta yanzu haka! Idan ba ta fito ba sai na sa an fito da ita da ƙarfi.!”
Inna ta fito da sauri tana murmushi cikin tsoro,
“Hajiya sannu da zuwa… lafiya kuwa?”
Hajiya Sa’adatu ta ce cikin tsawa,
“Lafiya? Lafiya ce bayan yarinyar nan ta jefa ‘yata cikin tashin hankali?! Ke kike zaune lafiya ita kuma Farha tana kwana a cikin kurkuku saboda irin ɗabi’un wannan yarinyar..!”
Inna ta tsaya cak, ta kasa cewa komai. Sai Amal ta fito daga ɗaki cikin sanyin jiki, ta tsaya a bakin ƙofa tana kallonsu.
Hajiya Sa’adatu ta kalle ta sama da ƙasa sannan ta matsa kusa da ita tana nuna ta da yatsa tana faɗin,
“Ke ce Amal ko? Ke ce dalilin da yasa Farha take cikin wahala yanzu ko? Wallahi idan har ba ki sa Maleekh ya je yasa an yafewa ‘yata ba, rayuwarki zata zama ɗaya daga cikin ƙalubalen da ba za ki iya jurewa ba!”
Amal ta ɗaga kanta a hankali, ta ce cikin murya mai rauni,
“Wallahi Hajiya ba ni na saka Farha ta shiga gidan yari ba… komai da ya faru…”
Hajiya Sa’adatu ta katse ta da cewa,
“Karya kike yi! Ba sai kin faɗa min komai ba! Amma zan faɗa miki abu guda indai ba ki tsugunna kika nemi yafiyar farha ba, ki sa yaron nan Maleekh ya je ya sa Farha ta fito daga kurkuku ba, to zan tabbatar da kin fuskanci bacin rai da wahala da ba ta da misali!”
Daya daga cikin matan da suka zo tare da ita ta ce,
“Ai irin wannan yarinya ya kamata a koya mata darasi, saboda ta manta da asalinta! Tana ganin ta sami soyayyar ɗan masu kudi sai ta fara raina mutane.”
Inna ta tsala kuka tana roƙon su da su yi hakuri,
“Don Allah kuyi hakuri, wannan ba hanyar warware matsala bace..."
Hajiya Sa’adatu ta ce
"Daman ce miki akayi munzo warware matsala ne? Ai mu duk yanda matsala take nan muke tunkara, mu da kika ganmu nan bama son zaman lafiya ko kaɗan, idan har Amal bata sa an ciro mun ƴata ba to wallahi sai mun ƙona gidan nan da ku kan ku...."
Daga nan tayi shiru domin ta san abun da ya faru da iyayen Amal kenam...
Inna ta ji kanta ya fara juyawa tana tunanin ɗanta da yanda aka ƙona su da azabar wuta... haka jikinta ya fara rawa, gaba ɗaya ta gama tsurewa...
Hajiya Hauwa’u wacce aka taho da ita ta ƙara da cewa:
“Idan ba ki gaggauta ganin Farha ta fito ba, wallahi za ki ga tashin hankali a rayuwarki, aure? Ki manta da shi! Rayuwa? Zamu tabbatar kin shiga wahala fiye da ta Farha!”
Inna ta shige tsakani cikin fushi ta ce:
“Ku ji tsoron Allah! Wannan wane irin hari ne haka a gidan mu? Me yarinya tayi muku da kuka zo da cin mutunci haka? Saboda Kuna da ikon raina kowa? To wallahi Amal tafi ƙarfinku, idan baku ƙona mu ba, baku cika mutane ba...!”
Hajiya Sa’adatu ta kalli Inna sama da ƙasa cikin raini, ta ce:
“Ke ma tsohuwa, ki kula da bakinki! Idan ba ki koyar da ita hankali ba, zamu koya mata da hannunmu!”
Sai ta juya tana nuna Amal da yatsa, muryarta tana rawar fushi:
“Idan har kika wuce sati biyu ba’a saki Farha daga kurkuku ba, ki shirya da Inna taki! Rayuwarku za ta zama darasi ga masu taɓa mu!”
Suka juya suka shiga motarsu suna ta harara da cizon baki, suka bar Amal da Inna cikin firgici da hawaye.
Amal ta durƙusa ta dafe ƙirji tana faɗin cikin kuka:
“Ya Allah… me yasa rayuwata ta zama irin haka?.. Ina zan saka kaina yanzu?”
Inna ta zauna kusa da ita tana share mata hawaye tana faɗin:
“Ki kwantar da hankalinki yarinyata… Allah ne kawai zai kareki daga mugayen mutane, ki dage da addu’a…”
☆☆☆☆☆☆☆
Maleekh bai dawo gida ba sai dare misalin ƙarfe 12.
A falo ya tarar da Abbah yana zaman jiransa. Abbah yayi saurin miƙe wa tare da faɗin.
"Maleekh aina ka tsaya haka sai yanzu? Baka saba kaiwa wannan lokaci a waje ba meyasa yanzu?..."
Maleekh yana lumshe idanu alamun bacci yake ji sosai, ya ce
"Abbah saboda gudun matsala ne yasa ban dawo da wuri ba, kowa jira yake yayi magana dani ni kuwa duk girman mutum bai isa ya shiga gonata na gyale ba in ba iyayena ba, ni nasan kaina ba hak'uri ne dani ba hakan yasa na dawo yanzu..."
Abbah ya ce "okay to wuce ka je ka kwanta. .."
Kowa ya kama part ɗinsa....
_WASHEGARI DA SAFE_
Maleekh ya fita office da wuri...
An kunna AC, fitilun ofis suna haskawa cikin sanyin yanayi. Maleekh yana sanye da farin suit, yana kallon cikin laptop ɗinsa, idonsa na cike da gajiya da tunani.
Sai kawai ƙofar ta buɗe da ƙarfi, Amal ta shigo cikin hanzari, idanunta sun kumbura saboda kuka. Hannunta na riƙe da jakarta da waya alamun yanzu isowarta, ko office ɗinta bata samu shiga ba, tana murɗa zoben hannunta cikin damuwa...
Ta ce da sauti mai rauni, tana rawar murya:
"Please... Maleekh... in har kana sona da gaske, to ka taimaka, ka sa a fito da Farha... don Allah..."
Maleekh ya ɗago da mamaki, yana kallonta kai tsaye:
"Amal, me kika ce? Na fito da Farha? Wannan magana ba a hannuna take ba, kin ji ko?."
Amal ta matso kusa da tebur ɗin, tana kuka ta ce:
"Na sani... amma kai mai faɗa a ji ne, kai ɗan babban mutum ne, kai ɗan hamshaki mai faɗa a ji ne. Kai zaka iya faɗa su janye ƙarar, ko su jawo maganar kotu a sake ta! Farha tana can a kurkuku saboda ni, saboda soyayyata da kai!"
Maleekh ya miƙe tsaye, yana jujjuya alkalami a hannunsa ya ce:
"Kin manta me Farha ta aikata? Kotun ce ta yanke hukunci, ba ni ba. Ba zan iya tsoma baki a cikin hukuncin doka ba, Amal."
Amal tana girgiza kai, cikin kuka ta ce:
"Zaka iya komai idan kana so... za ka iya sa duniya ta motsa idan ka buƙata, to me yasa baza ka iya ceto Farha ba? Ka ji yadda nake jin wannan a raina? Taya zanyi farin ciki idan na san yar’uwarka tana can cikin wahala saboda ni?"
Maleekh ya ɗan dafa tebur, yana kallonta cikin ƙunci ya ce:
"Kin san ba Farha ba ce kawai ta shiga matsala saboda ke, har ni ma... duk gidan mu ya rikice saboda soyayyar nan, Amal. Amma inaso ki ji kalmomi na, ba ni da iko akan kotu, ba ni da iko akan dokar ƙasa."
Amal ta share hawaye, ta ce da muryar raɗa:
"To me kake da iko akai, Maleekh? In baka iya kare Farha ba, in baka iya kare soyayyarmu daga iyayenka ba, to me yasa kake cewa kana sona?.."
Maleekh ya ɗauke kai, yana riƙe kansa da hannu ya ce:
"Amal... kada ki faɗi haka... bana son ki rikita ni da wannan zancen."
Amal ta ce cikin ɓacin rai.
"To sai ka tabbatar da kalmarka... idan kai kaine Maleekh ɗin da nake so, ka je ka fitar da Farha saboda ita yar’uwarka ce, kuma saboda kai ne dalilin da yasa take cikin wannan hali..."
Ta juya a hankali, ta kama ƙofar zata fita, tana kuka sosai.
Sai kawai Maleekh ya ƙira sunanta cikin raunannen murya.
"Amal..."
Ta tsaya, bata juyo ba.
Ya ce:
"Zan yi iya ƙoƙarina... amma ki sani, ba komai a hannuna yake ba. Ki yarda dani..."
Amal ta amsa ba tare da juyo ba:
"Na daina yarda da ƙoƙarinka idan bata ceto waɗanda suka shafe rayuwata ba..."
Ta fita, ƙofar ta rufe da ƙarfi...
Maleekh ya tsaya cikin shiru, yana kallon ƙofar, zuciyarsa cike da tashin hankali da soyayya mai zafi.
Ya jingina da bango, yana maimaita a hankali:
"Farha... Amal......"
_BAYAN SATI GUDA_
Amal da Maleekh sun daina mu'amala kamar yanda suka saba, Amal yanzu tunaninta da damuwarta shine Maleekh yasa a fito da Farha...amma samm ya ƙi, hakan yasa kullum suke cikin samun matsala...
Falon Amal yana ɗauke da hasken wuta mai launin zinariya, wanda ke ba da sanyi da natsuwa...
Amal tana kwance akan kujerar falo, ta lullube kanta da blanket. Idonta a rufe, amma zuciyarta tana tafasa da tunanin Farha da kuma barazanar mahaifiyarta....
“Farha tana gidan yari saboda ni…
Ko da kuwa ta tozarta ni, bai kamata hakan ya kai ta wurin hukuma ba.
Kuma Maleekh… meyasa yake jin haushin ta haka?”
Sai ta lumshe ido, hawaye ya zubo.
Cikin zuciyarta tana fadin:
“Allah ka sa duk abinda ke tsakaninmu ya warware lafiya… bana son ganin ɓacin ran kowa saboda ni.”
Cikin wannan tunanin sai ta ji ƙarar bugun ƙofa, ƙarar da ta firgita mata zuciya.
Ta miƙe a firgice, ta nufi ƙofar.
Kafin ta kai hannu ta buɗe, sai aka ƙara buga ƙofar da ƙarfi....
“Subhanallah! Waye ne haka?” ta furta cikin tsoro.
Kafin ta ankara, Zayd ya shigo cikin huci da fushi, idonsa a rufe da ɓacin rai.
Hannunsa na motsawa kamar wanda yake neman abinda zai bugawa mutum.
Amal a tsorace ta ce: “Zayd! Lafiya kuwa? Meyasa zaka shigo mun haka ba sallama?”
Kafin ta ƙara cewa komai Zayd ya zabga mata mari.
“PATTT!”
Muryar mari ta cika falon, blanket ɗin da ke jikinta ya faɗi ƙasa, daga ita sai kananan kaya short jeans da best...
Amal ta riƙe fuskarta, idonta suka cika da hawaye da mamaki...
“Zayd… yau ni ka mara? Ni?!”
Zayd a fusace ya ce:
“Abinda yafi mari ma zan miki idan baki gyara kuskurenki ba, Amal!
Kin wulakanta ‘yar uwata, kin sa an kai Farha gidan yari!
Duk son da nake miki, yanzu ya zama ƙiyayya! Indai baki sa Maleekh ya ciro mun ƙanwata ba, ki manta da zaman lafiya!”
Amal ta matso kusa da shi cikin kuka, tana girgiza kai:
“Zayd… nice fa Pretty ɗinka… wannan maganar shin ba'a cikin mafarki kake yin sa ba kuwa?”
Zayd ya murtuke fuska tare da faɗin
“Pretty ɗin banza!
Idan kina son ki huta, je ki samu Maleekh ya fitar da Farha daga gidan yari.
Idan ya ƙi, to ki rabu da shi.
Idan ya ga kun rabu, zai yi abinda kike so!”
Amal cikin kuka ta ce "na rabu da shi kuma?..."
Ya ce
"Kwarai kuwa, in ba haka ba zai cigaba da buga wasan sa akan soyayyarki, Maleekh ba sonki yake ba, domin inda yana sonki da gaske to da zaiyi abin da zai sa kiyi farin jini a wurin ƴan uwansa ba wai kiyi baƙin jini ba, yanzu kowa ya tsane ki a kaff dangi. Babu mai goyon bayan akan Maleekh ya aure ki, ki auna ki gani, Maleekh yau yayi wa ƴar uwarsa wannan tozarci to gobe kuma a ke zaiyi wa, kiyi hankali da shi domin yana can yana cikin farin ciki ke kuma ya barki da tashin hankali, abun nan da yayi ba laifinsa ake gani ba duk ya ɗora miki laifin ne saboda haka Maleekh ba masoyinki bane na kwarai..."
Daga nan ya juya ya fice daga falon yana fizgar ƙofar da ƙarfi...
Amal ta tsaya da hawayenta, zuciyarta kamar za ta faso ƙirjinta.
“Zayd… kai ma…? Duk duniya babu wanda ya fahimce ni…”
Ta share hawayenta da bayan hannu, ta ɗauki hijabinta, ta fita da sauri, ta shiga motarta....
In the Evening
Gidan na cike da natsuwa, an saka turaren wuta, ƙarar kiɗa mai natsuwa na tashi a hankali daga parlour.
Amal ta shigo da sauri, tana jin bugun zuciyarta.
Ta tsaya a tsakiyar falon ayayinda ta tarar da Ammy a zaune, tana kallon wani fashion show a TV.
Ammy ta ɗaga kai a hankali, idanunta suka haɗu da Amal.
Ta miƙe, tana ɗaure fuska, ta ɗauke kai tana cewa.
“Lafiya? Me ya kawo ki nan, bayan haukar da kika sashi yayi akan ‘yar uwarsa?
Kinsa ya kai Farha gidan yari! To yanzu me kika zo yi? Kin zo neman afuwa ko neman cigaba da cusa masa hauka?”
Amal ta share hawayenta, tana murmushi cikin nutsuwa da nauyin zuciya:
“Ban zo faɗa ba, Ammy. Nazo ganin Maleekh ne kawai.”
Ammy ta kwaɓe baki ta ce:
“Wai ganin Maleekh? Bayan kin jefa shi cikin bala’i da sunan soyayya?
Ashe baki da kunya ban sani ba? Ƴar matsiyata..!”
Amal ta kasa magana, hawaye suka fara zuba.
Ta juyo da niyyar fita sai ta ji muryarsa.
Maleekh daga sama ya furta: “Beb? Me ke faruwa ne nan?”
Ya sauƙo daga upstairs sanye da farin shirt da wando mai duhu, yana kallon Amal da mamaki da damuwa.
Sai dai kafin ya ƙaraso, Amal ta juya gare shi da fuska cike da zafi da rauni.
"Ina so ka gaya mun, me kake nufi da wannan hukuncin?
Ka kai ‘yar uwarka kotu saboda ni, hakane ko? Kuma haka danginka ke cewa, Duk da cewa ban so haka ba?
Kasa danginka sun tsane ni, suna zagina, cin mutunci ba kalar wanda ba'a mun..!
Shin hakane soyayya?..”
Maleekh cikin nutsuwa da ɓacin rai ya ce: “Na yi hakan ne don kare mutuncinki, Amal.
Ba zan bari a ci zarafinki ba!”
Amal tana kuka ta ce:
“To ni ban so!
Ni ban ce ka kai Farha kotu ba!
Ni na yafe mata tuni…
Me yasa baza ka saurare ni ba, Maleekh?”
Ammy ta tsaya gefe tana kallon su da ɓoyayyen murmushi tana jin daɗin rabuwar da take gani ta fara tasowa...
Maleekh cikin ɗaga murya shima ya ce:
“Ke Amal, kina bani umarni ne? For what?
Ki tsaya ki ji, ba zaki faɗa mun abinda zan yi ba!
Na yanke hukunci ne saboda gaskiya, ba don son rai ba!”
Amal itama cikin ɗaga murya ta ce:
“Gaskiya?
Gaskiyar me? Wacce ta sa ni cikin baƙin ciki?
Idan ka fi kowa sanin adalci, me yasa kake cutar da zuciyata? Idan har kana sona da gaske inaso ka aure ni a yau, aure ni nace Maleekh...”
Cikin fusata sosai ya ce:
“Stop it Amal!
Don’t talk to me like that!”
Tana hawaye ta ce:
“Na gaji da wannan soyayyar, Maleekh.
Soyayyar da ba aure, hauka ne, soyayyar da sam ba'a ganin mutuncin ta, kuma bata da kariya daga danginka.
Idan haka kake so, ka riƙe soyayyarka da su, ni na yafe komai!”
Maleekh ya tsaya kallonta, idonsa ya canza launi saboda ɓacin rai.
Cikin fusata ya ɗaga hannu ya zabga mata mari.
“PAATTT!”
Shiru ya cika falon na wani ɗan lokaci...
Amal ta tsaya cikin rawar jiki, tana kallonsa cikin girgiza kai, hannunta na kan kumatunta.
“Ni ka mara, Maleekh?
Bayan duk wannan soyayyar?”
Maleekh cikin nauyayyen murya ya ce:
“Na mare ki. So what?
Zaki rama ne?”
Hawaye na zubo mata sosai, zuciyarta na tafarfasa.
Tana riƙe da key ɗin mota, ta furta cikin rawar murya:
“Shikenan. Tunda haka kake so, daga yau ba kai, ba ni.
Ba zan tsaya ɓata lokaci na akan soyayyar da nake wulakanta ba.!”
Maleekh ya yi dariyar takaici tare da faɗin:
“So what idan kin tafi? Oya Go. Go get out!”
Ta ɗago tana nuna shi da yatsa “Stay away from me!”
Maleekh a fusace, ya riƙo hannunta: “Zo na taimaka miki ki fita!
Daga yau bazaki sake ganin fuskar Maleekh ba! Zan koma England inda babu irin ki!”
Ya ja ta da ƙarfi zuwa ƙofar harabar gidan.
Amal tana kuka tana ƙoƙarin kwacewa, amma zuciyar Maleekh ta rufe da fushi.
Yana fitar da ita ya wurga ta gefe.
“Out! OUT!”
Amal ta zauna ƙasa tana kuka mai ƙarfi, a lokacin ruwan sama ya fara zuba a hankali kamar sama na tausaya mata...
Wani irin harara ya wurga mata tare da juya wa cikin gidan..
Ammy tana tsaye bakin ƙofa da murmushin mugunta..
A hankali ta furta:
“Da kyau, ɗana. Wannan karon, ka faranta mun sosai.”
Maleekh ya hau sama da sauri, ko tsaya kula Ammy da ƙannensa bai yi ba.
Ya shiga ɗakinsa, ya buɗe akwati yana haɗa kaya cikin fushi da tashin hankali.
“Ba za ta sake raina ni ba…
Ba wata Amal a rayuwata daga yau.”..
Amal a waje tana cikin ruwan sama, tana kuka, tana faɗin cikin sanyi:
“Ya Allah… idan wannan soyayyar ta zama hukunci, ka bani ƙarfin yin haƙuri…”
A hankali ta miƙe da ƙyar ta shiga motarta, ta ja a hankali cikin ruwan, idonta cike da hawaye..
Gidansu Amal yayi shiru kamar ba kowa. Kukan ta ya cika falon amma babu wanda yake nan. Zuciyarta na bugawa da nauyin kalmomin Maleekh da suka tsaya a kunnenta kamar ƙaho.
"Daga yau bazaki sake ganin fuskar Maleekh ba! Zan koma England inda babu irin ki!”..
Tayi murmushi cikin hawaye tana faɗin,
“Ni kuma babu kai babu rayuwata…”
Sai ta share hawayenta ta hau sama zuwa ɗakinta, tana ji kamar gabanta na faɗuwa. Ta sa hannu ta buɗe ƙofar ɗakin, wani sanyi da tsoro suka ratsa ta...
Ganin Zayd a tsaye, ga duhu ya fara shiga, yana kallonta da idanu masu cike da nufin da ba a iya fassara shi...
Amal ta ja baya tana faɗin cikin firgici:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… Zayd? Me kake yi a ɗakina haka?”
Zayd ya saki murmushi marar daɗi, yana matsowa kusa da ita,
“Na zo karɓar abinda zaisa in mallake ki, tunda kin rabu da masoyin ki… yanzu ni zan zama sabon masoyin.”
Amal ta dafe ƙirji, murya na rawa,
“Zayd, me kake faɗi haka? Wane irin hauka ne wannan?”
A take ya cafke hannunta ya ja ta kusa da shi, yana shakar ƙamshin jikinta kamar wanda ya haukace.
“Wani irin kamshi kike da shi, Amal… kin manta ni ne nake son ki tun farko?”
“Ka sake ni! Zayd don Allah ka sake ni!” ta faɗa tana ƙoƙarin kwacewa, amma ƙarfin sa ya rinjaye ta...
Ya jefa ta kan gado, tare da binta da sauri yana shashshafa jikinta cikin tsananin sha’awa da mugunta. Amal tana ƙoƙarin tura shi, ta buɗe baki zata yi ihu yayi saurin toshe mata baki da nasa, yana sumbatar ta da ƙarfi. Hawaye da gumi suka gama gauraye jikinta gaba ɗaya.
Cikin wannan lokacin, zuciyarta ta cika da addu’a,
“Ya Allah, ka ceci ni