Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
ta ƙara haɗiye zuciya, idonta cike da ƙiyayya. Amal kuma ta juya tana kallonta da tsananin kishi, ganin yanda Farha take ta harararta yasa itama ta mayar mata da martanin hararar sannan ta ce
“Ki sani, yanzu ba a gidan ku nake zaune ba. Ki kama kanki, domin Amal bata rasa abin faɗi. Tambayi kowa ki ji wacece Amal Voice.”
Farha ta yi ƙoƙarin danne fushinta, a hargitse tazo wuce ta bugi kafaɗar Amal da ƙarfin tsiya sannan ta buɗe ƙofar da ƙarfi ta fice.
Ƙamshin turarenta ya bi bayanta..
Amal ta juya tana kallon Maleekh, da murmushi a fuskarta, duk da cewa zuciyarta tana tsalle-tsalle da kishi.
Shi kuma ya tsaya yana kallonta, zuciyarsa ta ji daɗin ganin yadda ta tsaya kai tsaye ta kare kanta a gaban Farha.
Bayan Farha ta fice daga ofishin cikin ƙiyayya, wurin ya dawo da nutsuwa. Maleekh ya saki ajiyar zuciya, sannan ya ɗauki basket ɗin abincin da Amal ta kawo, yana murmushi yana kallonta ya ce
“Na saba da irin fitinun Farha. Amma yau na ji daɗin yadda kika tsaya ki ka bata amsa. Amal, kin burge ni sosai.”
Amal ta lumshe ido, fuskarta cike da jin kunya da farin ciki ta ce.
“Ni dai bana son ta ci gaba da shiga tsakanina da kai. Na san kai mutum ne da kowa ke so, amma ni bazan yarda a raina ni ba..”
Maleekh ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallon idonta kai tsaye.
Hannunsa yasa yana buɗe kulolin abinci ɗaya bayan ɗaya. Ƙamshin miyan taushe ya cika ɗakin...
Maleekh ya ce
“Masha Allah… girkin nan da kanki kika haɗa shi? Na rantse, wannan shi ne mafi daɗin gift da aka taɓa kawo mun.”
Ya ɗauki spoon, ya ɗan ɗibo tuwo da miyar taushe mai kyau, ya miƙa mata kai tsaye yana faɗin
“Come on, open your mouth. I want to be the first to taste this with you.”
Amal ta yi murmushi tana girgiza kai.
Ta ce “A’a, kai dai ka fara. Ni ba zan iya cin abinci haka a ofishinka ba, idan wani ya shigo fa?”
Maleekh ya yi dariya, yana ɗan danna spoon ɗin a gaban bakinta. Yana faɗin
“Ba wanda zai shigo. Kuma idan suka shigo, sai su ga yadda masoyiyata ta fi kowacce mace a duniya.”
Cikin jin kunya da sanyi, Amal ta buɗe baki a hankali, ya saka mata spoon ɗin. Yana kallonta sosai har sai da ta haɗiye.
Lumshe ido tayi tana faɗin
“Hmmm… ai na ce maka zaka ji daɗin sa. Amma ya Maleekh, ka dena irin wannan magana da kake yi, zuciyata tana tsalle kamar zata fito daga kirjina.”
Maleekh ya yi dariya cikin tsantsar shauƙi, sannan shi ma ya ɗauki spoon ya ci. Ya lumshe ido yana jin ɗanɗanon abincin.
“Wallahi Amal, da za a bani damar zaɓen abincin duniya, sai dai na zaɓi wanda kika girka. This is heavenly.”
Ya furta yana santy..
Amal ta ɗan sunkuyar da kanta, tana murmushi. Ta ji wani irin ƙarfi a zuciyarta, tana jin soyayyar Maleekh ta wuce dukkan tunaninta.
Suka ci gaba da cin abincin tare. Wani lokaci shi ke feeding ɗinta, wani lokaci kuma ita ke ɗaukar spoon ta miƙa masa. Suna hira mai daɗi da tsokanan junansu...
A ƙarshe, bayan sun gama, Maleekh ya jingina da kujera yana kallonta.
Ya furta
“Amal, kin san me yasa nake so in kasance kusa da ke kullum? Domin idan na kasance tare da ke, komai na duniya ya zama kamar baya da muhimmanci. Ni da ke kaɗai nake gani.”
Idon Amal ya kaɗa da hawaye, ta ji kamar ta rungume shi a nan take, amma ta danne kanta. Ta ce cikin murya mai sanyi:
“Ni ma haka nake ji. Ina jin kamar duk duniya babu abinda nake so face kasancewa tare da kai.”
Shiru ya ratsa tsakaninsu, sai kukan zuciya da bugun numfashi. Amma dukansu biyu sun san cewa soyayyar da ke tsakaninsu ta fara shiga wani sabon matsayi da ba zata taɓa komawa baya ba…
Cikin wannan lokaci zuciyar Maleekh ta fara sauya salo. Duk da akwai wani sirri a boye a ƙirjinsa, sai dai soyayya ta fara hura wutar da bai taɓa zato ba. Ya fahimci cewa kasancewar Amal kusa da shi na sa zuciyarsa ta huce, duk da cewa har yanzu yana da wani ƙuduri na ɓoye a cikin ransa.
Amal kuwa ta fara jin wani irin nishaɗi da kwanciyar hankali fiye da da. A lokuta da bai samu ya zo gidan nata ba, sai wayar su ta ɗauki dare suna hira da dariya kamar sabbin masoya da suka yi asarar shekaru da dama ba tare da sanin juna ba...
Da safe idan Amal ta farka, zuciyarta kan cika da farin ciki, ta ji kamar komai na duniyar ya tsaya cak domin jin muryar Maleekh. Haka shi ma idan ya shige cikin aiki, bai da sukuni har sai ya ji labarinta.
Wannan kusanci ya zama tamkar sabon babi a rayuwarsu. Amma akwai wani zazzafan ƙuduri da Maleekh ke ɓoyewa, wanda shi kaɗai ya san yadda zai bayyana nan gaba.
Farha tana komawa gida ta fara ihu, tayi wurgi da basket ɗin kulolin abincin da ta kawo, suka watse a ƙasa.
Ammy ce ta fito da gaggawa tana tambayarta cikin tashin hankali:
“Farha meya faru haka? Me yasa kike ihu kamar wacce aka ci zarafi?”
Farha tana kuka tana sheshsheka tace:
“Ya Maleekh bai yi mun adalci ba Ammy, ya fifita wata a kaina? To wallahi bazan yadda ba!”
Ammy ta ɗan runtsa idanu kafin tace:
“Wace yarinya ya fifita a kanki? Ki faɗa min gaskiya.”
Farha tana huci tana share hawaye ta ce
“Wacece inba wancan matsiyaciya ba?”
Ammy ta ɗaga gira a rikice ta ce
“Wa kuma?!”
Farha ta tura baki cikin jin haushi tace:
“Amal ƴar jarida. Ya nema mata gida anan Abuja Ammy! Kuma kullum take kai masa abinci office…”
Ammy ta dafa ƙirjinta da hannu biyu, fuskarta ta nuna firgici, ta furta da ƙarfi:
“Meeeeee? Ya nema mata gida? Shi Maleekh ɗin? Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Abun da zai yi mun kenan? Yau sai ya dawo ya same ni, sai nayi maganinsa!”
A wancan ɓangaren kuma, Maleekh bayan sun gama lunch da Amal, sun sha soyayyarsu cikin annashuwa, sai suka fita tare. Shi ya kaita har gida da motarsa.
Sai da ya shiga ya gaishe da Inna cikin ladabi kafin ya juya gida da daddare, misalin ƙarfe 8 na dare lokacin da bai saba komawa ba...
A falo kuwa Ammy ce take zaman jiran dawowarsa, zuciyarta da ƙuna..
Da ya shigo da motarsa ya ajiye a wurin parking, sannan ya nufi compound ɗin gidan, ya shiga falo da sallama yana riƙe da jakar office ɗinsa...
Ammy tana jin sallamar tasa, tayi saurin miƙewa, ta tsaya cak tana kallonsa kafin ta fara masifa:
“Wato Maleekh ban isa na faɗa maka ba kenan? Ashe duk ladabin da kake nuna min ƙarya ne? Meye ya zaunar da Amal a garin nan? Har tana kai maka abinci? Shikenan ta zamo dadironka?”
Maleekh ya ja numfashi, daman yasan dole Farha zata sanar mata. Ya dubeta a hankali yace:
“Mom, ba zaman dadiro nake da ita ba. Kin fi kowa sanin ɗanki, ba manemin mata bane. Kar ki ɗora min wannan shaidar, dan Allah.”
Ammy ta girgiza kai cikin tsawa:
“Oh to me yasa ka nema mata gida anan Abuja?!”
Maleekh ya sauƙe numfashi mai nauyi sannan yace:
“Na siya musu gida ne ita da kakarta.”
A ruɗe Ammy ta ɗaga murya:
“Ka siya musu gida? Maleekh kasan me kake faɗi kuwa? Anan Abuja har kayi kyautar gida?”
Maleekh ya kalli gefen bango kafin ya mayar da kallonshi gareta:
“To Ammy, meye amfanin dukiyar da bazaka kyautar da ita ba, sannan bazaka sadakar da ita ba? Amal marainiya ce, bata da iyaye. Daga ita sai kakarta. Gidan da suke ciki a Kaduna gidan haya ne. Please Mom, ki bar ni na taimaki waɗanda basu da ƙarfi.”
Ammy ta tafa hannu cikin huci:
“To idan kana son kyautar gida, sai a nan Abuja? Meyasa bazata cigaba da zama a Kaduna ba? Ko dole sai ita zaka yiwa kyautar?”
Maleekh ya girgiza kai da sanyin murya ya ce
“Ina kyautata ga duk wanda na ga dama Mom. Kafin Amal, nayi kyautar dukiya fiye da adadi. Ba abinda ya ragu a hannuna. Allah bai bani arziki don in sa a gaba naita kallo ba. Ki yi haƙuri, biyayya zan ci gaba da yi miki a matsayin mahaifiyata. Amma kada ki shiga hurumin abinda zan kyautar da shi cikin dukiyata. Ni ba bin mata nake da dukiyata ba. Ba shaye-shaye nake ba. Ba gidan club nake zuwa ba. Ba safarar miyagun kwayoyi nake yi ba. Shiyasa kullum Allah bai hanani ba. Kuma dukiyata kullum ƙaruwa suke, ba raguwa ba.”
Sai ya ɗan ɗaga murya cikin ƙarfin hali:
“Zan yi kyauta, zan yi sadaka, zan yi zakka. Duk garin da na zagaya naga basuda masallaci zan gina musu. Zan tono rijiya ko in saka fanfoo. Lokacin layya waɗanda basu da hali zan raba musu. Duk ba saboda riya ba. Kuma ba kowa yasan irin abubuwan da nake yi ba, ko ke baki sani ba sai yanzu da nake gaya miki. Gida kuwa, ba Amal kaɗai ba, duk wanda nayi niyyar taimaka masa da gida zan yi. Ko a England ne, indai inada hali zan yi. Saboda haka ku gani kawai ku yi shiru.”
Ammy tana huci kamar zata yi kuka tace:
“Uhmmm! Amma Amal dai saboda soyayya kayi mata.”
Maleekh ya murmusa cikin ƙarfin hali:
“Kusan haka. Abinda nake so dole na kyautata masa. And so what idan ina sonta? Ra’ayina ne. Tinda ba wanda zai zauna mun da ita. Kuma duk munafikin da yazo ya sanar miki wallahi sai nayi maganinsa.”
Ammy ta yi tsaki sannan ta miƙa masa hannu:
“Bani wayarka nan.”
Ba tare da musu ba, Maleekh ya ciro wayarsa ya bata.
Ammy ta kalle shi sannan tace:
“Wannan wayar nayi sizing ɗinta!”
Maleekh ya yi dariya kawai, ya ratsa ta gefenta, ya wuce sama kai tsaye zuwa part ɗinsa.
Ammy tana tsaye da wayar a hannunta cikin huci.
Sai ga Farha ta shigo tana laɓe, ta tsaya ta ji duk hirar su.
Da ta ƙaraso kusa da Ammy tace cikin lallashi:
“Ammy, don Allah ki bani wayar. Nasan Amal zata ƙira shi. Ina so in caccaki durun uwarta a daren nan.”
Ammy ta yi murmushin mugunta, ta miƙa mata wayar sannan ta wuce part ɗinta.
Farha kuwa ta riƙe wayar tana murna, ta fice zuwa ɗakinta.
Ta zauna tana jiran ƙira daga Amal, zuciyarta cike da shirin tada rikici...
Misalin ƙarfe goma da rabi na dare, Amal ta gama shiryawa cikin nutsuwa. Ta ɗauki wayarta, zuciyarta cike da ƙaunar Maleekh, ta ƙira lambar shi domin ta yi masa magana kafin ta kwanta.
A ɓangaren Maleekh kuwa, wayar tana hannun Farha da ke zaune a ɗakinta tana jiran wannan lokacin. Da taga sunan Amaleekh a jikin screen ɗin, ta danne dariya, sai ta ɗaga da sauri, ta kai kunne tana shirin caccakar ta, ta ce
“Hello matsiyaciya, wani irin rashin mutunci ne zaki ƙira wayar mijin Aure na. Ke waca iriyar marar zuciya ce?” Farha ta yi magana da kakkausar murya.
Amal ta yi shiru na ƴan daƙiƙu, ta ɗan yi murmushi sannan ta ce cikin lafazi mai tsauri...
“Ke yarinya, kina sauraron kanki kuwa? Kin san da wa kike magana? Ni ce Amal Voice, wacce idan ta yi magana ana sauraro a jihohi da dama, ba wai don ina son a ji ni ba, a’a, don kalamaina suna da nauyi.”
Farha ta yi tsaki sannan ta ce
“Kina yi min ihu da wannan sunan banza naki? To wallahi ba zan taɓa barinki ba. Ni ce matar Maleekh, na fi ki komai, daga asali har ƙarshe.”
Amal ta yi dariya mai sauti, sannan ta mayar mata da martani .
“Farha, ki ji tsoron Allah. Soyayya ba da ƙarfi ake jantaba. Ni da Maleekh mutu-karaba ne, babu wanda zai iya tsayawa tsakanin mu. Ke ana soyayya dole ne? yace baya so, please ki rabu dashi ba, ko har sai kin masa fyade kafin hankalinki ya kwanta? kawai ki sa a ranki zuciyar shi ta riga ta zaɓe ni. Kuma idan zuciya ta zaɓi abu, babu sarauta, babu iko, babu kuɗi da zai iya hana hakan.”...
Farha ta yi rau-rau da ido tana cizon yatsa saboda takaicin yanda Amal ke gasa mata magana cikin natsuwa...
Amal ta ƙara da cewa:
“Ke ki bi hanyarki daban, amma wallahi idan kika cigaba da shigowa tsakanin mu, sai kin gane cewa bana wasa da yara irinku. Karki manta ni ƴar jarida ce, na san kalmar da zata zame miki tukunyar zafi. Ina da harshen da zai iya tsinewa mutuncin duk wanda ya tsaya mun a gaba. Amma ban zo yin faɗa da ke ba, kawai ina sanar miki gaskiya ne. Ke da Maleekh ba wani abu bane, haɗin bai yi ba sammm, ni kuma da shi, kalmar da ke tsakanin mu: shine Mutu-karaba.”
Ta kashe ƙiran a nan, ta bar Farha sai huci take tayi...
Farha ta cije baki, hawaye suka cika mata ido saboda takaici. Ta furta cikin tsawa:
“Wallahi Amal, sai na ga bayan ki. Ko da zai zame min mutuwa, ba zan bar ki ki more wannan soyayya ba. Sai dai mutuwa ta rabaki da Maleekh.”
Amma zuciyarta ta tabbatar mata da abu guda ɗaya, Amal ta fita iya magana, ta fita iya nuna ƙarfin zuciya. Wannan ne abinda yafi mata ciwo fiye da komai...
Farha tana gama wayar da Amal, zuciyarta ta cika da wutar haushi. Tayi saurin miƙewa, da sauri ta sauƙa falo, zuciyarta cike da muguwar manufa. Ba tare da wani tunani ba, ta nufi part ɗin Maleekh...
A hankali ta zuƙo key ɗin da aka ɗaura a jikin ƙofa. Ta tsaya jim kaɗan tana runtse ido, tana jin zuciyarta na bugawa kamar ana wasan doki. Sai ta janyo ƙofar ta saka key ɗin, ta jiyo “Klik!” alamar ta kulle shi daga waje...
Tayi murmushin mugunta, tana jin kamar ta yi nasara. Da sauri ta janye key ɗin daga ƙofar, ta riƙe shi a hannunta sannan ta juya ta nufi nata part ɗin.
Tana tafiya tana maganar zuci...
“Wallahi Amal, ni Farha ba zan bari soyayyarku tayi kwari ba. Tinda har kika raina ni zaki gane kuranki. Sai Maleekh yayi sati a kulle a ɗakinsa, ba zai ga fuskarki ba. Wallahi sai na hana shi fita, sai naga yadda soyayyarku zata dawwama a kulle.”
Ta ɗan tsaya a tsakiyar falon babban gida tana dafa ƙirji, hawaye na cika idonta saboda tsananin kishi. Sannan ta ƙara cewa a zuciya:
“Ke Amal, ba zaki taɓa cin nasara akaina ba. Idan da gaske ne ‘Mutu-karaba’ ne tsakaninki da Maleekh, to bari mu gani ko kulle ba zai iya raba ku ba. Wannan shi ne farkon shirin da zan ɗauka akan ki. Na rantse da rantsuwa, daga yau soyayyarki zata fara ruguje wa a idonki.”
Tana gama wannan tunanin ta nufi ɗakinta da murmushin mugunta a fuskarta, key ɗin na hannunta tamkar tayi wata gagarumar nasara.
Da asuba, Maleekh ne ya miƙe daga gado cikin nutsuwa. Ya ɗauro alwala a bathroom, sannan ya saka farin jallabiyarsa tare da riƙo misbaharsa, zuciyarsa cike da natsuwa da niyyar nufar masallaci...
Sai dai, da ya isa ƙofar falonsa ya murɗa handle ɗin ƙofar, ya juya da nufin buɗewa… “Klik!”
Ya ɗan tsaya, ya ƙara juyawa da ƙarfin gaske… amma sai yaji ƙofar tamau! Wani irin yanayi ya ratsashi lokaci guda.
Ya janye hannunsa ya matsa gefe, ya ƙara gwadawa. Amma ƙofar sai juyawa take, ba buɗewa!
Ya tsuguna ƙasa yana kallon ƙofar da kyau. Glass door ce, mai ƙyalli da ƙarfinsa, wacce idan aka kulle daga waje ba mutum da zai iya buɗewa daga ciki.
Zuciyarsa ta buga. Ya miƙe ya ɗan bubbuga ƙofar, sai dai babu wanda zai jiyo shi domin part ɗin nasa yana nesa da inda masu aikin gidan suke.
Numfashinsa ya ɗan rikice, sai ya dafe kansa. “Me ke faruwa haka?..”
Daurewa ya yi, ya koma ɗaki, ya shimfiɗa sallaya, ya yi sallar Asuba cikin ɗaki da zuciyar da ta cika da damuwa. Bayan ya iddar..
Sai ya zauna a gefen gado, ya haɗe hannuwa guri ɗaya, yana girgiza kai cikin ɗan murya:
“Wannan ya nuna akwai wani shiri da ake kullawa a kaina..."
A Ranar ya kwana cikin ɗaki, babu fita, babu ganawa da kowa. Abinci ma ba wanda ya kawo masa, sai ruwa kawai da ya ɗauko daga fridge ɗin ɗakin.
Yayin da yake zaune, zuciyarsa kullum na yawo wajen Amal. Tunani yake, ko dai ita ma an hana ta ganinsa? Ko kuwa har yanzu tana zaune cikin kwanciyar hankali ba tare da ta san halin da yake ciki ba?
A wancan gefen kuma, Amal ta tashi da safe cikin shauƙi. Tun kafin gari ya waye, zuciyarta na ta ɗokin jin muryar Maleekh kamar yadda suka saba. Tana ɗaukar wayarta ta ƙira shi, sai dai shiru. Kiran na shiga, amma babu mai ɗauka.
Ta sake ƙira sau biyu, uku… har ta ƙara a karo na biyar, amma babu amsa. Zuciyarta ta fara bugawa da sauri. Cikin ranta ta ce:
"Ko dai yana barci ne? Amma ko barci yake, da ya ji ƙiran wayata yake ɗaga wa. Me yasa yanzu shiru?"
Cikin rikicewa ta jefa wayar gefe, ta ɗan jingina da gado tana mai lumshe ido da tunani. Amma zuciyarta ta kasa samun natsuwa. Ta sake ɗaukar wayar ta ƙira, amma har yanzu babu amsa.
A gefe guda, Farha ce ke riƙe da wayar Maleekh tun daren jiya bayan ta kulle shi a ɗaki. Da ta ga ƙira daga Amal, zuciyarta ta ƙara ƙone wa da haushi. Ta ɗan bushe da dariyar mugunta, ta ajiye wayar gefe tana mai faɗin cikin zuciya:
"Kin yi fatan jin muryarsa ko? Wallahi yau sai kin shiga ruɗani, zaki sha mamaki. Zan koya miki how to respect someone."
Haka Amal ta wuni cikin damuwa, tana ɗaukar waya tana ƙiransa lokaci zuwa lokaci, amma babu alamar amsa. Zuciyarta ta shiga kullewa da tunani iri-iri.
🌹🌹🌹🌹
A gefe guda kuwa, Maleekh a ɗaki yana zaune kamar mai zaman kurkuku. Sai dai yayi sallarsa a ɗaki yayi wanka ya cigaba da zama, ya zauna yana ta nazari. Ga wayarsa kuwa bata kusa da shi, saboda tana wurin Ammy. Wannan yasa shi bai san cewa Amal na ƙiran shi ba...
Maleekh yana zaune a bakin gado, zuciyarsa cike da tunani mai nauyi.
Wayarsa Samsung Galaxy Z Fold 6, wacce kuɗinsa ya kai miliyoyi, bata wurinsa balle ya yi ƙira...
Ga ɗayar wayarsa iPhone 17 Pro Max ɗinsa wanda ya bar wa Amal saboda ya fi