AMALEEKH by Asmeetah writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 82

3K to 6K   out of 244.2K words

biyu waɗanda aka kashe su ba tare da sun ci hakkin kowa ba, kuma har ila yau an kasa ɗaukan mataki akai...

Ta kawo ƙarshen labarin cikin harshen turanci..

Amal ta share hawayen ta da tissue, tana matuƙar kame kanta, tana kuka, ta kammala bada labarin masoya biyu kuma Aminan ta...

Ta kuma cewa.

“Rest well, Hadiza and Fahad.
The world failed you but history will remember your truth.”

Sautin slow instrumental piano ya shiga a bayyane yayin da kukan jama'a ke tashi a comments da wayoyi da messages da ke shigowa kai tsaye a tashar RAYUWAR FM.

England Maleekh’s Private Apartment

Maleekh yana zaune a kan white leather couch ɗinsa, sanye da 3-quarter da singlet, ƙafa ɗaya a ɗore kan ɗaya, hannunsa yana riƙe da remote amma idanuwansa ba sa ko motsi daga laptop ɗin gaban sa, Amal ce akan Screen ɗin laptop cike da hikima, da harshen turanci mai girgiza zuciya, tana kuka tana magana...

Maleekh tsaki ya ja cikin jin haushin Amal, ya furta:

"Look at her...
What kind of manipulation is this?
So this is the game now? Make the world cry so they forget your status?"

Ya miƙe tsaye ƙirar jikinsa kamar basamude domin ko ina a jikinsa a cike yake, full built, jikinsa fari tas kamar madara, yana motsa kai kamar wanda ke buƙatar tashi daga wani irin mafarki...

Maleekh yana son kashe laptop amma ya kasa, tsayar da hand ɗin sa ya yi ba tare da ya motsa ba, fuska a yamutse, gira a haɗe sai faman huci yake, cikin muryar tsawa yake faɗin:

"This is nonsense, absolute nonsense,
Why... why is she still echoing in my head?"

Ya sunkuyar da kansa yana hargutsa gashin kansa da hannu daya, ya girgiza kai a hankali
yana magana kamar yana ƙoƙarin tsoratar da zuciyarsa
Ya ce:

"She's nothing, Just a radio girl, A local girl, A nobody.
How dare she touch the part of me I buried years ago?"

Kwantar da kansa ya yi a jikin bango, yana numfashi da ƙarfi, ba tare da ya san me ke tafiya a ransa ba, ya tuna kalmomin Amal da take cewa

“You are heard, you deserve better...”

Wani abu yana girgiza a cikin zuciyarsa... Amma Maleekh ya ƙi amincewa da cewa wani abu daga maganganunta ya taɓa wani yanki a zuciyar sa..

Yayin da labarin Amal ke ƙara karɓuwa a faɗin ƙasar, wani fitaccen dan jarida mai suna Rikky Blaze, wanda ke da shahararren podcast ɗin “Nigerian Voices Unfiltered”, ya kalli clip din Amal daga RAYUWA FM. Hankalinsa ya koma kanta nan take.

Rikky Blaze yana magana da PA ɗinsa cewa:

“Wannan yarinyar... Amal... tana da murya, tana da harshe mai daɗin saurare, she speaks from pain and depth.
I want her on the next episode! live from Abuja!
Arrange it, komai da komai, tikitin jirgi, hotel, VIP treatment. Kaduna is too small for that kind of voice.”

Da daddare Amal na zaune tana karanta littafin journalism cikin fitilar lantarki mai launi, Inna na kan sallaya tana jan carbi,
wayar Amal ne ya yi ƙara saƙon email ya iso...

Amal cike da mamaki ta ce:

“Inna... kinga sun ce wani shahararren podcast daga Abuja yana so in zo tattaunawa kai tsaye, sun ce ba tare da na kashe kuɗina ba, hatta jirgi da hotel sun riga sun shirya komai...”

Inna ta ɗaga gira tare da faɗin:

“Lah! To wa ke bibiyar ki haka Amal? Ai wannan... akwai ƙalubale a cikin sa in har zaki fara zuwa garuruwa ke ba ƴar kowa ba, amma idan da gaske ne kuma halal ne Allah ya buɗa miki.”

Amal ta riƙe hannun Inna da murmushin dole ta ce:

“Inna, wallahi ban san ko me yasa mutane ke bani kulawa haka ba... amma dole ne idan kana irin wannan aiki, ka sa rai da farin ciki yana iya janyo kishi da ƙiyayya.”

♡♡♡
♡♡


Maleekh yana duba social media sai poster ya bayyana a fuskar laptop ɗinsa an rubuta:

“Coming Up: AMAL ABDULSAMAAD The Voice Behind Kaduna’s Radio Gold, Live on Nigerian Voices Podcast with Rikky Blaze!”

Maleekh ya tsayar da numfashi, a cikin ransa yake faɗin:

“So... she’s really trending now? Abuja? Seriously? wannan ƴar talakawan yarinya ta kai wannan mataki?
Nigeria really is upside down, but let’s see... let’s see how far she can go.”

Ya janyo wayarsa tare da ƙiran ɗaya daga cikin abokan cinikinsa a Abuja... yana shirin tura mutum don ganawa da Rikky Blaze...

♡♡♡
♡♡

AMAL A AIRPORT ZUWA ABUJA

Amal na sanye da doguwar riga da ƴar hijabin ta marar nauyi tana lanƙaye da jakar ta, Mutane da dama na kallonta a harabar jirgi suna murmushi.

Yaran wasu ma na cewa: “Mama kinga Aunty Amal ta cikin rediyo!”

Amal ta ce a zuciyarta

“Duniya kenan... tun da na fara aiki a ƙaramin gidan rediyo, ban taɓa tunanin har podcast na ƙasa zai gayyace ni ba, amma wallahi zan tsaya akan gaskiya, ba zan canza wa kaina ba.”

Wasu zafafan motoci ne suka zo ɗaukan ta, kai tsaye babban hotel na masu kuɗi aka kaita, yanda aka tanadar mata da komai...

Bayan ta ci ta sha tayi wanka tare da tsayar da sallah ta huta cikin kwanciyar hankali har bacci ya ɗauke ta, ga sanyin A.C na ratsa ta kamar ba'a duniya take ba, ita kanta tasan ta shigo duniyar masu kuɗi,

Washegari da safe ta kammala shirin ta tsaff, already motar na jiran ta a compound na hotel zasu je wurin da za'a gudanar da shiri....

THE NIGERIAN VOICES PODCAST"

Amal ta tsaya a gaban duniya, domin a wurare da dama ana kallon tattaunawar da zasu gudanar...

Abuja, babban studio na Rikky Blaze. Amal na zaune a gaban mics guda biyu, sanye take da rigar abaya da gyalenta marar nauyi,
Rikky ya zuba mata ido cikin girmamawa yana murmushi, gyaran murya ya yi tare da faɗin

“Ladies and gentlemen, today we have with us a very special guest,
she may not have a mansion, or billions in her bank account,
but her voice has broken down walls and reached the souls of thousands.
Amal Abdulsamaad welcome to Nigerian Voices.”

Amal cikin nutsuwa ta furta:

“Thank you very much, Mr. Blaze, It’s an honour to be here.
And I speak not with power, but with pain because pain is universal.”


Rikky ya gyara zama sannan Ya ce:

"Akwai lokacin da kika ce, "Idan har ya zama dole ne sai ka cutar da wani, to kar ya zamana ka cutar da wanda ya taɓa ƙaunarka’
wannan magana ta bazu sosai a duniya.... Daga ina kika samo ta?"

Amal ta ɗan gyara zamanta, ta kalli mic cikin sassanyar murya ta ce:

"Na samo ta ne daga ganin mutanen da suke shan wahala a asirance,
na taɓa yin hira da wata yarinya da aka kashe mijinta saboda ya kare ta daga ‘yan ƙungiyar asiri,
ba ta kai wa kowa kukan ta ba… sai dai kawai ta zuba ido,
kuma hakan ya karya zuciyata.
Ba kowace zafi ke yin ihu ba, Malam Blaze…
wasu dai suna nan kawai… suna jiran a ji yo kukan su...."

Wannan maganar ta saka ɗakin yin shiru, har cameraman ya tsaya yana kallon ta.

Rikky cikin nutsuwa Ya ce:

“You don’t speak, you cut.
But in a good way like surgery.”

Amal ta murmusa kaɗan, idanunta sun kaɗa da ƙwalla, tayi gaggawar kawar da kai ta tsaya cikin ƙarfin hali.

Ta ce:

“I’ve seen people mock the poor...
I’ve seen people say, your background is your curse
But wallahi, Mafi ƙarfafa mutane da na taɓa haɗuwa da su,
su ne waɗanda ba su da wani ginshiƙi sai Allah kaɗai,
kuma ina magana ne a madadinsu.”

♡♡♡
♡♡


Maleekh na zaune kan sofa, yana kallon wani big screen, amma ba podcast ba yana duba data a kasuwancin sa. A gefe guda kuma laptop ɗinsa na nuna thumbnail ɗin Amal a podcast amma bashi da lokacin duba ta...

Maleekh yana maganar zuci..

“Tunanin ta ya isa haka, i don’t need this noise,
there are millions like her why should i care?”

ɗaukan remote ya yi yana shirin kashe screen ɗin gaba ɗaya, amma kafin ya kashe, yana ganin Amal cikin nutsuwa tana faɗin

“Muna tashi ne ta hanyar ɗaga waɗanda ke ƙasa da mu…”

Maleekh jan tsaki ya yi yana faɗin:

“Ƴar talakawa kawai, ƙaramin abu ya dameta, kuma yanzu kowa na wahalar da kai wurin sauraron maganarta.”

Ya ɗauki wayarsa ya ƙira PA ɗinsa, bugu ɗaya aka ɗauka, Maleekh Ya ce:

“Tell Alhaji Dikko in Abuja he should handle that oil deal directly.
And tell him to stop this social media buzz about any radio girl.
I’m not interested.”

Recording Amal da Rikky ya janyo tasiri har zuwa duniyar siyasa, sannan wata kafar TV ta Abuja tana neman ta zama host ɗinta, lamarin da ya tayar da hankali a RAYUWA FM. 🌍🎙️

A cikin maganganunta ta sako har da ƴan siyasa, duk wata gaskiyan da suke ɓoyewa tana shirin binciko wa, tana ƙaryata maganganun su akan talakawa na cewa zasu taimake su nan kuma cin amana ne da kuma yaudara, truth out maganganun ta akan siyasa ta yi su, kuma ta ba da isasshen lokaci.....

THE ECHO OF TRUTH” LABARIN AMAL YA GIRGIZA MANYA

A babban ofishin wani ɗan siyasa da ake zargi da cin hanci a Abuja, TV yana nuna podcast ɗin Rikky Blaze tare da Amal, wani babban hadimi yana kallon boss ɗinsa da fargaba

Ya ce:

“Sir… ina ganin wannan yarinyar za ta zama matsala,
ta ambaci matsalar ƙarancin ruwa, har da adadin alkaluman da ka umarce ni in ɓoye.”

Ɗan siyasan ya miƙe da sauri yana kaɗa hannu cikin zafin zuciya Ya ce:

“Who gave her that data? Ta yaya ƴar gidan rediyo ta Kaduna ke da wannan cikakken bayani?
Shut it down! Cancel the links, do damage control! I don’t want her voice on the internet again!”

Hadimi Ya ce:

“But sir... it’s already viral. The clip is trending on Twitter, YouTube, even BBC Africa quoted her...”

Ɗan siyasan ya ɗaga hannu cikin tsawa yana faɗin:

“To hell with BBC! If we don’t silence her now, she’ll open more cans we thought were buried,
find out who trained her. And who she works for.”...

Abuja TV Headquarters

Bayan kwana biyu..

A cikin babban ɗakin taro da aka yi wa ado da fatauci da na’urorin zamani, Amal zaune ce a gaban babban kwamiti na Abuja TV. A gabanta akwai wata fitacciyar producer, Madam Ebun, mace mai lallausar murya da kuma cike da dabara.

Madam Ebun cikin murmushi Ta ce:

“Amal, your voice touches the soul, we are impressed,
but on national TV, we don’t just speak we control narratives.”

Amal ta ɗaure fuska tare da faɗin:

“I control only the truth. Nothing more.”

Wani daga cikin committee ya kalli wata takarda sannan Ya ce:

“Kin ce Ministan Muhalli ya yi amfani da kuɗin ruwa wajen abin da bai dace ba,
wannan magana ta yi haɗari da yawa,
kin ƙira hakan cin amana ga yaran da ke cikin jin ƙishirwa,
idan muka ɗauke ki aiki, muna son kauce wa maimaita irin wannan magana kai tsaye a fili.”

Amal ta lumshe ido cikin nutsuwa Ta ce:

“Abin da na faɗa ya fito ne daga rahoton da tashar ku ta yi watsi da shi
If you’re scared of truth, then I’m not your girl.”

Ɗakin yayi shiru kamar ba mutane. Amal ta miƙe, ta ɗauki jakarta tana shirin barin wajen, amma wani daga cikin
Committee Member
Ya ce:

“Wait. Kina da jarumta,
amma ki sani ƙin amincewa da mu yana nufin yanzu kin zama abin bibiya.
’Yan siyasa sun san sunanki yanzu. Ki yi hattara.”

Amal Ta ce:

“They should be careful too. I have a microphone.”

♡♡


England, Maleekh's Private Apartment

Maleekh yana zaune a gaban babban taga yana kallon gari da motocin dake wuce wa, hannunsa na cikin gashinsa yana murɗawa cikin takaici, ya koma ya zauna kamar marar lafiya.

A gefensa laptop na nuna headline:

“Kaduna Girl With Radio Courage Lands Abuja TV Offer”

Yayi tsaki, ya tura laptop ɗin gefe, ya miƙe yana shawagi cikin ɗakin da kayan alatu ke ko’ina, yana lumshe da idon da ke bayyana karfin hali da ƙiyayya.

Maleekh yana zancen zuci yana faɗin :

“Ajin me?
Yarinyar da bata da kafa da tuta a rayuwa tana ƙoƙarin taka manya?
wane irin raini ne wannan?”

Ya ɗauki waya ya ƙira wani ɗan sanda dake aiki a Abuja.

Maleekh Ya ce:

“I need someone to pull her files, i don’t trust that girl,
i want to know who is backing her or if she’s just another loud mouth.”

Muryar ɗan sandan ne ya fito yana faɗin:

“Sir, you want us to tail her?”

Maleekh Ya ce:

“No... Not yet. Let her shine small.
But if she crosses me again, i will remind her that power...
is not in the mic. It's in money.”

Ya kashe wayar yana fitar da numfashi, amma wata kalma daga bakin Amal tana yawo a kunnen sa:

“Gaskiya ba ta da albashi, amma tana biya da gadon suna bayan barinka duniya....”


Maleekh ya ƙara jan tsaki yana faɗin:

“Tsk! Yar talakawa da poetry…”

♡♡♡

Rayuwa FM, Kaduna...

Amal ta dawo daga Abuja da takardun offer da ta samu, Babban producer tasharsu, Mr. Salis, ya ƙira ta ofishinsa.

Amal bayan ta huta gajiyar ta a gida duk da jirgi ta shiga, daga baya ta amsa ƙiran Ogan ta dake gidan rediyo Rayuwa FM..

Gidan rediyo na RAYUWA FM, Amal na shigowa, fuskarta ɗauke da fara'a, tare da karfin zuciya. Babban editan tashar yana tsaye yana taya ta murnar dawowa..

Editor yana ƙoƙarin bayyanar da murmushin sa
Ya ce:

“Amal... welcome back. Yayi kyau.
Amma akwai batun da zamu tattauna da gaggawa.”

Amal ta tsaya, tana dubansa kai tsaye Ta ce:

“Na san me kake nufi. Abuja TV sun aiko mun da offer.
They want me to be their national youth host for a new program.
They want truth and i have it.”

Editor ya ɗan dafe goshinsa sannan Ya ce:

“But this is RAYUWA FM, Amal.
We trained you. We gave you the mic.
Ba za mu iya kallon ki kina tafiye tafiye ba... and Abuja TV na da sauƙin sayar da ra’ayi you’ll be controlled.”

Amal Ta ce:

“But wallahi a nan ma ana ƙoƙarin dakatar da ni,
i speak for the people ba wai domin na yi suna bane,
Idan rayuwa zata zama cin hanci da gori, to ba zan ci albashi dubu ashirin haka nan ba...”

Shiru ya biyo baya kamar an kunna recorder a zuciyar kowanne ma’aikaci.

Amal ta bar wurin kai tsaye ofishin Mr Salis ta nufa daman shi ke neman ta, haka ta shiga office ba tare da jin komai ba, a zuciyarta tana tunani tare da maganar zuci:

“If they want to fight me for speaking truth, I’ll still speak.
One mic. One voice. Millions of hearts.”

Murya cike da damuwa.

Mr. Salis Ya ce:

“Amal, muna farin ciki da irin cigaban ki. Amma… idan kika karɓi wannan offer, za ki fice daga Rayuwa FM ne....”

Amal ta kalle shi kai tsaye tare da faɗin:

“Na zata zaku yi alfahari da ni, ba ku ja ni ƙasa ba.”

Mr. Salis Ya ce:

“Wannan ba batun kishi bane, batun tsari ne.
Gidan rediyo yana da policy idan an same ki da wata kafa na waje, sai an cire ki daga jerin ma’aikatan nan...”

Amal cikin takaici ta furta:

“To ni wallahi idan akwai inda zan iya faɗin gaskiya ba tare da an tsoratar da sunan gwamnati ba ni can zani.”

Ta miƙe ta bar ofishin, a bakin ƙofa ma’aikata da yawa suna kallonta da mamaki da tausayawa, wasu na ta cewa

“kada ki tafi Amal, kin fi ƙarfin Abuja TV su rufe ki da dokokin su...”

Amma Amal bata tsaya ba. A zuciyarta murya ɗaya take faɗi:

“Mic ɗina ba mallakin ku bane. Na talakawa ne.”

Amal ta dawo gida daga aiki, fuskarta cike da gajiya da damuwa, bata tsaya ko'ina ba sai a ɗakin Inna, a zaune Inna take akan tabarma tana tsane ganye, Idonta ya sauƙa akan Amal da take ƙoƙarin boye damuwarta.

Inna ta ɗaga ido cikin tausayawa Ta ce:

“Amal, zo ki zauna mana, ki zauna nan gaban Inna, yau zaki saurari shawara, ko ba haka ba?”

Amal ta zauna a gefen Inna kamar wata yarinya da aka kama da laifi, ta ɗaura hannu biyu a cinya, idanunta sun kaɗa da kwalla...

Inna Ta ce:

“Amal, ki dubi maraicinki ki zauna kiyi haƙuri, ki tuna ke ƴar talakawa ce, karki manta da asalinki, wannan Abuja da kike shirin komawa, meye a cikinta? Siyasa? Kuɗi? Ko alfahari?”

Amal ta kalli Inna tana share hawaye, amma bata iya cewa komai ba.

Inna ta cigaba da faɗin:

“Masu kuɗi sun fi ki iko, a lokacin da kike haskawa, kowa zai dinga ƙiran sunanki, amma idan kika faɗi ƙasi wallahi babu wanda zai tsaya miki, su masu mulki sai sun ɓata miki suna, su wulakanta ki, su jefar da ke kamar marar daraja, bayan ke kaɗai kika rage mun, idan kika tafi Abuja, wa zai dinga kula da ni?”

Amal ta fashe da kuka tana faɗin:

“Inna...idan har bakya son na koma Abuja...zan haƙura. Wallahi zan zauna dake, zan ci gaba da aiki a Rayuwa FM.”

Inna ta janyo Amal ta rungume ta tana share mata hawaye.

Inna Ta ce:

“Allah ya miki albarka, wallahi ban hanaki ci gaba da rayuwa ba, amma bana son ki afka cikin tarkon siyasa da haɗin kai da masu kuɗi, ki dage akan ilimi da gaskiya nan ma za’a gan ki.”


RAYUWA FM....

Bayan kwana biyu Amal ta koma tashar Rayuwa FM da murmushi a fuska, kowa ya nuna farin ciki da dawowarta, shirin ta na yau ya kasance mai taken: “Kaunace ko Wulaƙanci?”

Amal ta shiga studio cikin kwanciyar hankali, ta ajiye headset ɗinta, sannan ta fara magana cikin tausasawa:


“Assalamu Alaikum wa rahmatullah masu sauraro na Rayuwa FM. Ina tare da ku ni ce Amal Abdulsamaad. A yau zan ɗan ba ku labari mai raɗaɗi labarin soyayya da ƙyama...”

Ta ɗan yi shiru, tana murza idonta da tissue, muryarta na ɗan karyewa.

Ta cigaba da cewa:

“Wani saurayi da budurwa ɗalibai sun shafe shekaru uku cikin soyayya mai tsafta, basu da komai sai soyayya da girmama juna. Amma wata rana...an tarar da gawar su a cikin motarsu...an harbe su.”

Daga nan muryarta ta shiga rawa sosai.

Ta cigaba akan cewa:

“Wai meyasa ƙiyayya take cin nasara akan soyayya? meyasa mutane basa jin zafin rasa wanda suke so? wannan duniya fa babu tabbas…”

Idon Amal ya cika da kwalla, amma har yanzu kalmominta na fita cikin turanci mai hikima.

Tana faɗin:

“Matasa ne, talakawa,

2 / 82