Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
a ƙasar da ba ruwan kowa da gaskiya."
Maleekh ya lanƙwasar da kansa, cikin sassanyar murya ya ce:
"Lokacin dariyarta ya ƙare. Yanzu lokaci ne na hawaye. Kuma zan tabbatar hawaye ya maye gurbin karfin halinta."
Daga nan ya kashe wayar, yana kallon fuskar Amal daga wani video da aka ɗora a online yana jin wani abu mai nauyi a zuciyarsa, wanda ya kasa fassara shi, ya ce:
"Me ya sa tunaninta baya barin kaina, duk da irin ƙiyayyar da nake mata?"
---★★★
A cikin ɗakin Amal...
Ƙofar ɗakin aka buɗe da ƙarfi.
An kawo wani babban ɗan siyasa wanda shine shugaban hukumar ɗaya daga cikin manyan bangarorin gwamnati. Ya zauna gaban Amal yana kallonta tamkar ba mutum ba:
Shugaban Hukuma ya ce:
"Idan kin yarda zaki zauna lafiya to ki daina magana, zamu baki gidan zama, mota, da naira miliyan ɗari. Amma sai kin yi alkawarin komai ya ƙare."
Amal ta ɗago kai cikin ƙarfin zuciya tana murmushi ta ce:
"Ba zan siyar da gaskiyata da farashi ba. Ko zaku bani duniya gaba ɗaya, idan talaka yana kuka saboda zaluncin ku, zan cigaba da magana... In har na mutu a haka, Allah zai karɓi hakkin talakawa da bakin da suka nema masa."
Wani security ne ya shaƙeta da hannu yana zazzaro mata ido amma shugaban ya dakatar da shi yana kallon Amal da tsantsar mamaki da takaici ya ce:
"Bata tsoron mutuwa....
Haƙura ya yi, shima ya bata wuri...
A gida...
Inna ta kwanta rashin lafiya. Mutane sun zo suna ɗaukar nauyin kulawa da ita. Tana ta kuka tana faɗin:
"Allah ka dawo mun da
Jikata lafiya... Amal zata iya shiru amma ba zata iya cin zalunci ba..."
Zuwa yanzu...
Gwamnati tana cikin tashin hankali. 'Yan jarida daga kasashen waje sun fara bibiyar batun. Tura ta kai bango. Haka nan mutane sun fara tashi da zanga-zanga a Abuja da Kaduna, suna ɗauke da hoton Amal tare da tambari:
“TA BA Da ƘARFI GA MURYAR MARASA ƘARFI!”....
Wata mace ce ta shigo cikin ɗakin da Amal take,
Tana sanye da kayan masu aiki, ta zauna kusa da Amal cikin sautin muryar da ba kowa ke iya ji ba.
Matar ta ce:
"Sun ce in kawo miki abinci… Amma na zo da saƙo daga waje. An fara neman ki. Duniya na magana. Ki ƙara juriya, zan dawo da labari."
Amal ta zuba mata ido da hawaye a idonta ba tare da ta iya cewa komai ba. Matar ta latsa mata hannu a asirce, ta miƙa mata ɗan karamin zare alamun cewa ba ita kaɗai bace a cikin gidan da ke goyon bayanta.
A GIDAN GWAMNATI...
Wasu daga cikin shugabannin gwamnati sun fara yin shakkar tsare Amal. Labarai sun bazu zuwa kasashen waje. Ana barazanar dakatar da haɗin gwiwa da gwamnati idan ba a fito da bayanin da ya shafi Amal ba.
Ministan Cikin Gida ya fuskanci matsin lamba.
Ya ƙira taro na manyan jami'an tsaro da 'yan siyasa da su ka tsare Amal.
Cewa:
"Duk abinda za ku yi, ku yi shi da wayo. Idan aka samu gawarta a matsayin evidence, mu ne za mu durƙusa. Kiyasta illar hakan..."
A RAYUWA FM...
An gudanar da wani gagarumin shiri na musamman da aka ƙira "AMAL, MURYAR GASKIYA".
A cikin shirin, an sake kunna sautin wasu daga cikin tattaunawarta da talakawa da labarinta na masoya biyu da aka kashe wanda ya taɓa zuciyar mutane a baya.
A ƙarshe anchor ya furta:
"Idan har gaskiya ce laifi, to duk mai gaskiya zai ɓace kamar Amal... Amma Amal ba zata ɓace ba. Rayuwarta ta riga ta zama muryar al'umma!"
A CIKIN ƊAKIN MALEEKH, ENGLAND...
Yana zaune cikin duhu, kofin coffee yana hannunsa, yana kallon projectorin da ke nuna masa tashar Rayuwa FM da yadda mutane ke zanga-zanga a ƙofar gidan rediyon da hoton Amal a saman banner.
Ya yi murmushi cikin rashin jin daɗi, yana ƙara karanta wani email da Rikky Blaze da ya turo masa:
Rikky yana cewa:
"Sir, we may need to drop the girl soon... The pressure is building. She may die, but her voice won’t..."
Maleekh ya runtse idanu yana faɗin:
"Damn it, Rikky... why is this girl messing with my world?"
Ya jefa glass cup na coffeen a bango yana buga ƙafa cikin fushi.
Daga nan ya ɗauki waya ya ƙira wata lamba yana faɗin:
"Release her. But make sure she learns something first... Let her walk out, but her heart will broken."
TO PAH TASHIN HANKALI, ASHE DAI ƁATAN AMAL DA SA HANNUN MALEEKH🤔🤔
A CIKIN GIDAN GOMNATI...CIKIN DARE!
Amal tana zaune a cikin duhun ɗaki. Aka buɗe ƙofa, wasu mutane biyu masu baƙaƙen kaya sun shigo. Ba tare da an yi mata komai ba, suka kwance ta, suka cire mata ɗaurin baki.
Mutum na biyu ya ce:
"Zaki koma gida. Amma ki sani... wannan ba ƙarshe ba ne. Wannan faɗa ce tsakanin ƙarfi da ƙasa. Ki nutsu, Amal..."
Suka sa mata fuskar rufe ido (eye mask), suka fitar da ita daga gidan.
Sai da suka yi tafiya mai nisa sosai a mota kafin suka fitar da ita a cikin duhu suka cilla ta cikin wata mota, suka bar ta kusa da wani titi mai duhu inda wasu masu mota suka same ta da safe....
LABARI YA KARAƊE KO INA...
An same ta a rana mai ɗumi, da 'yan sanda da ma'aikatan Rayuwa FM suka kai ta asibiti. Ta zauna jinya tsawon makonni biyu sakamakon fesa mata tiyagas da akayi..
Inna ta yi kuka sosai tana rungume da ita, tana faɗin:
"Amal... na riga na sani, ke ba za ki yi rayuwa kamar sauran mata ba... Amma Allah yana tare da mai gaskiya!"
Bayan wasu kwanaki,
A gaban tagar asibitin da rana ke haskawa, Amal na zaune a kan kujera sanye da farin hijabi da doguwar rigar marar ado. Kamar wacce ba ta da ƙarfi, amma idan ka duba cikin idanunta zaka ga karfi da sabuwar fahimta.
Inna tana gefenta, tana riƙe da hannunta, tana faɗin:
"Na ce miki ki bar harkar siyasa, amma na fahimci ba ke ki ke zaɓar wannan hanyar ba, kamar dai mutanen ki ne ke zaɓar miki wannan hanyar ta fuskar tausayi...."
Amal ta juyo, da hawaye a idanu cikin murmushi ta ce:
“Inna, da ace ba ni aka yi wa wannan ba, wata rana wata ce za ta fuskance shi. Amma yanzu da na riga na faɗa ciki wallahi zan kare kaina, da sauran masu rauni da ba su da murya.”
Inna cikin kalar tausayi ta rungume ta tare da faɗin:
"Allah ya cigaba da tsare mu gaba ɗaya..."
★★★
Kwana biyu bayan fitarta daga asibiti, Amal ta koma Rayuwa FM.
Kowane ma’aikaci ya rungume ta cikin tausayawa suna jajanta mata, Sun ajiye mata wani guri na musamman a matsayin “Mai Tsaron Gaskiya”.
A shirin ta na farko bayan dawowarta, ta fara da ƙasa da murya, tana kallon microphone kamar tana kallon duniya:
Ta ce:
“Na rayu a inda yawancin mutane ke barin ran su. Suka ce zan mutu, amma Allah ya raya ni. Na dawo da murya ta, ba don jin daɗi ba sai don kare gaskiya.”
Jama’a a gari sun fara yi mata kallon girmamawa fiye da da. Tashar Rayuwa FM ta karɓi goyon baya daga ƙungiyoyi na duniya da kafafen watsa labarai na kasashen waje.
Maleekh: Tashin Ƙiyayya da Shirinsa na Dawo Nigeria
A cikin ofishin Cash Empire da ke England, Maleekh na tsaye gaban mirror. Yana kallon kansa da gilashi a idanu, yana sanya necktie. A gefensa Rikky Blaze ya tsaya da wani file mai taken: “Project: CashTalk FM Abuja Launch.”
Rikky ya ce:
"Kafafen yaɗa labarai sun fara canza salo, Rayuwa FM da Amal sun fara samun ƙarfi da motsin da ba kowa zai iya dakatar da su ba."...
Maleekh ya juyo cikin fushi. Idonsa ya yi jajur.
Ya ce:
"Don dakatar da murya, ba sai ka rufe ta ba. Kana nutsar da ita ne da hayaniya mafi ƙarfi. Mu yanzu muna ƙirƙirar murya da ta fi tata ƙarfi...."
Ya kama jacket dinsa, ya fesa turare mai ƙamshi da tsada yana faɗin:
“CashTalk FM za ta zama gidan ‘yan Nigeria masu iko. Ba gidan gajiyayyu ba. Ba wurin kuka da hauka ba .....gida ne na gidan makamai da babbar murya. I’ll give them the opposite of Amal.”
★★★★★
Maleekh ya iso Nigeria da ƙungiyar sa a boye. A wani sirrin fili kusa da Maitama, an fara ginin CashTalk FM. Tashar da ke da fasahar zamani fiye da Rayuwa FM.
Ya sanya mutane su fara neman sabbin masu gabatarwa amma duk wani tallace-tallace yana da manufa guda: Yi wa Amal ƙasa a gwiwa da jawo hankalin matasa daga gareta.
Maleekh yana so ya yi ganawar sirri da Amal...
Yana maganar zuci a yayin da yake zaman kaɗaici shi kaɗai domin a yanzu ya zaɓi ya yi maganar sirrin sa da zuciyar sa a kan ya sanar wa wani, domin ya koyi darasi a gun abokinsa Nasir....
"Ba sai na kashe ta ba. Zan goge ta a hankali… da suna, iko, da tasiri. Kafin ta gane me ke faruwa, zata dawo ita kaɗai babu kowa a gefenta.."
🔊 GIDAN REDIYO RAYUWA FM. ZUWAN MALEEKH CASHBANK A KADUNA
Washegari da safe
Amal na zaune a ofishinta mai tsabta da kyau, tana gyara wasu takardu. Wata ma’aikaciyar FM ta shigo da hanzarin ta
Ma’aikaciya ta ce,:
“Amal, akwai wani mutum daga Abuja... ya ce sunansa Maleekh Cashbank, ya ce ke ya zo nema.”
Zuciyar Amal ne ta buga da ƙarfi. Ta ɗago kai da mamaki da tausayi a lokaci guda.
Amal Tayi shiru na ɗan lokaci sannan ta ce...
“Shigo da shi.”
Bayan ýan seconni.
Ƙofar ce ta buɗu, sai ga Maleekh ya shigo sanye da suit mai kyan gaske da tsada, yana ɗauke da tabarau. yana mata kallon sama da ƙasa kamar wanda ya zo yi wa ƙasa gadin mulki. Yana dubanta cikin raini,
kamar bai san darajarta ba. Ya zauna a kujera yana ƙare ta da kallo daga sama har ƙasa, sannan ya murmusa da wulakanci ya ce:
“Toh, ke ce Amal? Ashe ba da microphone kawai kike da ƙarfi ba... a zahiri sai na gane ke ‘yar talakawa ce dai dai misali.”
Ya yi mata magana ba tare da ya nuna ya santa ba, kamar bai taɓa sanin ta ba haka yake ta yatsina fuska...
Amal na zaune ba tare da ta yi motsi ba, tana kallonsa ido cikin ido.
cikin ladabi ta ce:
“Na gode da ziyara. Wannan gidan rediyo ne na kowa da kowa....
Maleekh ya ce:
"So... kece Amal da ake ta surutu a social media? Muryar marasa gata... ƴar talakawa da take firfitar da batun siyasa kamar wata jagora?"
Amal ta kalli agogo sannan ta kalle shi cikin kulawa ba tare da damuwa ba Ta ce:
“Ni ce. Barka da zuwa Rayuwa FM, gidan da yake sauraren kowa, ba tare da fifita darajar mutum bisa dukiya ba.”
Maleekh yana dariyar raini ya ce:
“Kina da ƙwarewa, zan ba ki hakan. Amma kuɗi basu tare da ƙwarewa a Nigeria. Na zo ne in ba ki wata dama. Ki bar wannan gidan rediyo mai ɗan ƙaramin tasiri, ki zo CashTalk FM tashar da zata fi Rayuwa FM nesa da gani.”
Amal ta saki murmushi cikin nutsuwa ta ce:
“Dama tana iya zama mai kyau, amma ba kowacce dama ce ta dace da kowane mutum ba. Rayuwa FM ba ta ciyar da ni kuɗi amma ta ciyar da ni gaskiya da ƙaunar talakawa.”
Maleekh ya ce:
“Kina nufin ba kya son ƙaruwa? Kina son ki zauna da ƴan talakawa har abada? Kina gudun cika mafarkin ki ne? ko kina jin tsoron canji?”
Amal ta ce:
“Ina son ƙaruwa. Amma ba zan sayar da zuciyata ba saboda hakan. Na fi son in bar tarihi da murya mai amfani fiye da na bar makudan kuɗaɗe da aka samu ta hanyar wulaƙanci.”
Maleekh ya daka tsaki, yana ƙare ta da kallo Ya ce:
“You talk too much for someone who is replaceable. Don’t forget, I can build a station, create a voice louder than yours, and bury your name in days.”
Amal ta gyara zama, ta ɗaga kai cikin murya mai sassauci ta ce:
“To bury someone’s name, dole ne ka goge, yadda sunan tasa wasu suka tashi domin binne ta. Kuma Maleekh murya ba ta girma da speakers, son samu ta girma da gaskiya.”...
Shiru ne ya ratsa ofishin. Maleekh ya kasa ce wa komai. Ya kalle ta da wani irin kallon ƙiyayya da mamaki....
Maleekh a hankali ya furta
“Hmm... interesting.”
Ya juya ya fita ba tare da sallama ba. Amal ta lumshe ido, ta ce a ranta...
“Da wuya babban mutum ya yarda da ƙaramin murya, sai dai idan muryar tana da gaskiya.”.....
Yayin da Maleekh ya shigo ofishinta a Rayuwa FM, Amal ta riga ta kunna ƙaramar mic recorder da ke haɗe da tsarin studio ɗin su. Ba mic ɗin da ake gani ba ne, amma yana da ƙarfin ɗaukar duk wata magana da ta faru a cikin ɗakin.
A zuciyar Amal tana faɗin:
"Zan bar duniya ta saurara da idanuwanta. Zasu ga wanda suke ƙira ‘jagoran zamani’ da ainihin halayensa."
📻 'ON AIR' BA SANI BA SABO!!!!
Tattaunawarsu da suka cika da wulakanci, kaskanci da rainin hankali daga ɓangaren Maleekh ta cigaba kamar yadda muka tsara a baya. Amma wannan karon duk maganganun suna tafiya kai tsaye zuwa wani system na backup audio a cikin ofishin Amal, kuma daga baya wani technician ya yanke hukuncin ya ɗora su a shafin YouTube da X (Twitter).
Bayan awa guda Maleekh ya bar FM, recording sautin yanda ya ƙasƙantar da Amal ya bazu kamar gobara! Mutane sun fara posting da hotunan fuskarsa da sautuka na yanda yake cewa:
“Ke ƴar talakawa ce kawai... ki gode da na zo…”
“I can bury your name in days!”
👇
(Zan binne sunan ki cikin ƴan kwanaki...)
“CashTalk FM za ta maye gurbin wannan ƙaramar tashar ku...”
🔥 Comments a social media suka fara tashi kamar haka:
@ArewaRight: “Shin wannan ne shugaban da zai kafa sabon gidan rediyo? Me ya sa yake wulakanta mace mai gaskiya?”
@NaijaWoke: “Yadda Amal ta ba shi amsa cikin nutsuwa ya nishadantar...
Maleekh ya ci karo da ƙaramar mace mai girman zuciya.”
@TalakawanVoice: “Idan yana da gaskiya, me ya sa yazo da barazana da cin mutunci? Kuɗi ba su da daraja idan babu mutunci.”
Haka maganganu suka rinƙa yaɗuwa ....
MALEEK CASHBANK NA FUSKANTAR RIKICI
A daren nan, PR team ɗinsa a London da England da Abuja sun shiga tashin hankali. Yana kallo a gida, yana shan coffee, sai ya ga trending topic:
#WhoIsMaleekCashbank
#IStandWithAmal
#TalakawaMukaNe
Ya finciki remote ya buɗe rikodin yana sauraro da ido wujiga-wujiga...
Maleekh cikin zafin rai
Ya ce:
"Taya wannan sirrin ya fito fili?!"..
Ya jefa kofin coffee ƙasa da karfi. Kunnensa yana ƙara kamar sauro. yana faɗin:
“She played me... she outsmarted me!”
(Ta yaudare ni… ta fi ni wayo!").
Washegari, kafafen yaɗa labarai sun fara ɗaukar labarin. Wasu suna gaya wa Amal "kin farka mana idanunmu", wasu kuwa suna tambayar:
"Shin Maleekh da yake shirin kafa rediyo, haka zai kula da ma’aikatansa?"
Rayuwa FM ta samu karɓuwa sosai. Amal ta koma bakin aikinta kamar ba abun da ya faru, amma ƙarfin ta ya ninka nasa sau ɗari.
A labarai ana sanar da labarin MALEEKH...
Maleekh Cashbank ɗaya daga cikin attajirai mafiya ƙarfi a Najeriya, ɗan asalin Kaduna ne, amma mahaifinsa babban ɗan siyasa ne mai tarin dukiya wanda ke zaune a Abuja. Shi kuma Maleekh ya kwashe rayuwarsa a ƙasar Ingila yana gudanar da wasu kasuwanci kafin ya dawo don kula da sabon tashar rediyon sa CashTalk FM da ke Abuja.
Maleekh ba ƙaramin fusata ya yi ba, ya yanke hukuncin komawa tashar rediyo inda Amal take aiki...
A cikin motar sa mai tsada, yana sanye da farin suit, baƙin glass, da ƙamshi mai ƙayatarwa. Yana tunanin tashar rediyo Rayuwa FM da ke Kaduna inda Amal ke aiki...
Bayan isar sa ko tsayawa bai yi anyi mata sallama cewa ya zo ba, kai tsaye ya kutsa ciki...
Da ƙarfi ya buɗe ƙofar office ɗin ta har sai da ta tsorata, tsaya wa ya yi yana kallon ta cikin takaici...
Itama miƙe wa tayi tsaye ganin Maleekh...
Yana da niyyar tattaunawa da ita a fili, amma ba tare da sanin cewa Amal ta ƙara kunna mic ba domin duk abinda zai faɗa ya isa kunnuwan al’umma kai tsaye.
Maleekh yana kallon Amal daga sama zuwa ƙasa
Ya ce:
“To me kike tunani da har kike yawo kina faɗin magana kamar ke ce mai kula da rayuwar al’umma? Me kika sani game da siyasa da iko? Kin taɓa ganin naira miliyan ɗaya da idon ki kuwa?”
Maleekh tsabar kansa ya ɗau zafi bai san wani magana yake yi akai ba, haka zuciyar sa take harbawa tana bugawa da ƙarfin gaske...
Amal ta ƙyalkyale da dariya cikin kwanciyar hankali ta ce:
“A'a, ban taɓa gani ba. Amma na taɓa jin yunwa, na taɓa zama da kakata da safe ba tare da mun ci abincin rana ba. Na kuma san cewa duk wanda bai ji zafin talauci ba, bazai iya jin raɗaɗin talaka ba.”
Maleekh yana girgiza kai ya ce:
“That’s why you’ll always be poor. Ke da kika yi tashin baƙin ciki, me zai canza? Wannan shine dalilin da yasa CashTalk FM zai ɗauki ragamar rediyo a Nigeria. Ku dai Rayuwa FM sai ku ci gaba da sauraron kan ku ...”
Amal cikin nutsuwa, ba tare da ɗaga murya ba ta ce:
“Mu dai ba mu da ruwa da kuɗin ku. Amma muna da murya. Muryar da zata faɗi gaskiya koman zafi. Kuma wallahi, idan muryar talaka ba zata kai ga wayar da kai ba, me zata yi?”
A lokacin jama’a da dama sun fara bibiyar shirin a wayoyinsu da rediyoyi. Sun fara rubuce-rubuce a social media:
"Shin wannan Maleekh Cashbank mai yake nema ne?"
"Wai da gaske yana ƙasƙantar da 'yan Najeriya haka?"
"Amal tana da gaskiya! Muryarta tana buɗe mana ido."
Maleekh a hankali, ya fara lura da cewa tattaunawarsu ta na fita kai tsaye. Ba shakka wannan sauyi ne da zai fara tayar masa da hankali a fagen da ya raina muryar talakawa.....
NEXT NEXT NEXTT
*MASU KARATU BANA GANIN