Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   59 / 82

174K to 177K   out of 244.2K words

don haka dole ne aure..."

Shiru ya cika falon.
Sai Maleekh ya sauƙe numfashi, ya ɗan murmusa cikin gajiyar rai.

“Shikenan Abbah... ba damuwa. Na amince.”

Abbah ya saki murmushi, yana duban Ammy da fuska mai natsuwa.

“Alhamdulillah. Da wannan magana, zuciyata ta huta.”

Ammy kuwa ta yi shiru kawai, tana kallon Maleekh, zuciyarta na ɓoye da damuwa, saboda ta san ba soyayya bace ta sa ya amince ba, kawai biyayya ce ga mahaifi. Kuma sannan ba wani ƙaunar Amal take ba..."

Ammy ta buɗi baki ta ce.

"Amma da sharaɗin idan mun koma za'a je a fito da Farha..."

Abbah ya ce "wannan ba abun damuwa bane.."

Sai falon ya sake komawa cikin nutsuwa, sai muryar TV da take showing a gefe.

Zuciyarsa ta mutu, amma fushin da yake da Amal bai mutu ba…domin har yanzu yana kallon ta da Zayd ne a kan idonsa.
Kuma ya ci alwashi duk san da ya ƙara ganin su a haka sai yayi musu hukunci marar misaltuwa...

Yana cikin duba wayarsa, ga kuma saƙon WhatsApp da suke ta shigo masa, bai yi niyyar duba wa yanzu ba har sai ya gama huta gajiyarsa kwatsam sai yayi ido huɗu da wani group da bai san shi ba samm...

Saboda wannan group ne yasa shi shiga WhatsApp, kai tsaye kafin ya duba meye a cikin group ɗin sai da ya duba su waye a ciki, ganin duk babu wanda ya sani sakamakon rashin sanin numbobin, yana shiga group ɗin abinda ya gani kawai a cikin group ɗin shine photuna..

Da farko yayi tunanin group ɗin BF ne har zai fita kafin photunan su buɗe, sai kawai ya hango fuskar Amal da wani a rungume da ita ta bayanta.. ga videos..

Zaro ido yayi yana duba wa. Nan ƙirjinsa ya tsananta bugawa..

Abbah da Ammy ganin canjin da ya shigo lokaci guda yasa su tambayarsa "lafiya kuwa?.."

A zabure ya ɗago kamar zai fashe da kuka ya ce.

"Ba komai, komai na ga campany na ya ja baya, babu wani ribar da ake samu yanzu..."

Abbah ya ce "kuma shine abun damuwa? Kana komawa komai zai yi normal...itama Amal bata cikin nutsuwa shiyasa..."

Ammy dai kawar da kai gefe tayi, ta bar su da halin halinsu domin yanzu ta cire hannunta. A cewar ta...

Abbah ya kuma cewa.

"Amma babu wani damuwa akan batun auren koh?..."

Maleekh ya jinjina kai cikin sassanyar murya ya ce

"Sosai ma.."

Daga nan ya bar falon, kai tsaye bedroom ya nufa. A wannan ranar gaba ɗaya ya kasa bacci sai kallon hotunan da video....

_NEXT NEXT NEXT_

asmeetahwriter✍️

*🎤AMALEEKH🎤*


*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.


*Writing and Storytelling By*

Asma'u Muhammad Auwal

Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*

*MARUBUCIYAR:*

*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*

Bauchi State Nigeria.

*WhatsApp 09065443871*

Follow my channel 👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


BOOK ONE page 67 to 68

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹


Yamma liss misalin ƙarfe 6:30. Rana ta faɗi sai launin duhu dake sauƙa daga sararin sama..

Amal ta fito daga Office ɗin “The Awaken Project” dake cikin Campany CashTalk, da gajiya a fuskarta domin tun safe take aiki ba kakkautawa, tana bin bayanin wasu bayanai da ta samu daga manema labarai game da batun shari’ar Maleekh da kuma waɗanda suka kitsa sharri a kansa...

A cikin zuciyarta akwai farin ciki, saboda labarin cewa Maleekh ya fito daga kurkuku ya bazu, amma ba ƙaramin tsoro ke ratsa jikinta ba tun mako guda take jin ana bibiyarta..

Ganin duk ma'aikata sun tashi babu kowa yasa itama ɗaukan jakarta ta nufi harabar campany domin shiga motarta... Sai security ne kawai dake ta zirga-zirga....

Ta kunna motarta cikin nutsuwa, ta ɗan lumshe ido sannan ta ce a hankali:

“Ya Allah, ka tsare ni daga sharrin makiya...”


Motar ta tafi a hankali ta bar harabar kamfani.
Titunan Abuja suna cike da hasken fitilu, yanzu kusa magariba, cunkoso yayi yawa.
Amal ta zaɓi hanya mai sarari domin gujewa cinkoso, hanyar da bata da yawan jama’a, Airport link road extension..

Sai dai yau, ƙaddara ta rubuta wani abu dabam...

Da ta shiga tsakiyar hanya, kwatsam sai ta hangi wata baƙar mota daga nesa, black Prado tana tahowa da sauri kamar mai tuƙi cikin fushi.
Tana tunanin kamar motar da yake bibiyanta ne, cikin kankanin lokaci motar ta iso gabanta, ta shige mata gaban hanya da ƙarfi!

Amal a firgita ta ce,

“Subhanallah!”


Ta juyar da sitiyarin cikin hanzari, tana ƙoƙarin kaucewa.
Amma kafin ta daidaita kansa sai ga ƙaton trailer daga bayan ta, yana tahowa da gudu!
Wani irin ƙara trailer ya yi, “Tuuuunnn!!!”

Sai a nan lokaci ya tsaya!
Komai ya haɗu cikin daƙiƙa:
Motar Amal ta yi wani irin juyin juyi, ta yi tsalle kamar ƙwallon roba, sannan ta faɗa cikin rami mai zurfi a gefen hanya.

Wurin babu jama’a, hanya ce da ba a yawan bi.
Taya ta ƙone, gilashin motar suka watse.

Cikin hayaki da ƙura, motar ta tsaya cak.
Sai ɗaya daga cikin mutanen cikin baƙar motar ya fito, sanye da farin riga da hula baki, ya duba cikin ramin da wayar torchlight.
Yadda Amal ta kwanta, jini na malala daga goshinta, jikinta ba motsi.

Ya ce da muryar ƙarfi,

“Boss, ta gama! Babu numfashi!”

Wani daga cikin motar ya amsa daga ciki cikin murya mai sanyi:

“Ka tabbatar. Ba zan so a bar wata shaida ba.”

Sai ɗayan ya ɗaga torchlight ɗin ya sake duba jikin Amal, ya taɓa ƙirjinta da yatsansa.

“Laf! Ta mutu... Babu motsi ko numfashi.”


“Good.”
“Mu tafi.”

Motarsu ta bar wurin da sauri, tana shirin bacewa cikin duhun dare.
A bayan su, motar Amal tana nan cikin rami, tana ta hayaƙi kamar wanda akayi gobara...

Dare ya gama shigowa, iska tana busa ganyaye a hankali.
Cikin duhun da bai da haske, ƙarar wata ƙaramar tsuntsuwa ce kaɗai ke ji kamar tana kuka...

Sai dai a can nesa, wani mai babur dake wucewa ya tsaya yana kallon hayaƙi da ke tashi daga ƙasa.
Ya ce da mamaki:

“Innalillahi… wace irin hatsaniya ce kuma haka?”


Ya fara saukowa daga babur ɗinsa zuwa ƙasan ramin, yana ƙira da murya mai sauti:

“Hello! Hello! Wani yana ciki?!”


A lokacin da ya haska torchlight ɗinsa, fuskar Amal ce ta bayyana jini a goshinta, numfashinta a hankali kamar wacce duniya ta fara barinta...

Ganin irin halin da take ciki ne yasa ya lalumo wayarsa zai ƙira ƴan sanda, cikin tashin hankali ganin ba credit a wayar ne yasa ya dubi Amal da rabin kunkuminta ke cikin mota, zuwa samanta kuma na wajen motar..

"Baiwar ALLAH! Baiwar ALLAH kina ji na?..."

Haka yake ta tatta6a fuskarta babu wani motsi... anan ya cigaba da gadinta ko akwai wanda zai zo.
Shiru babu kowa ga dare yayi sosai, gashi har 11 ta wuce.
Anan wani dabara yazo masa, ya fara bincika motar ko zai samu wayarta yayi amfani da ita, cikin sa'a ya samu amma sai dai ta farfashe.. Amma bata mutu ba, sai dai kuma wani tashin hankali akwai security. Ganin Amal ta tafi dogon suma yasa yayi amfani da fingerprint ɗinta, cikin sa'a ya buɗe anan ya samu damar ƙiran lambar gaggawa ta police (199)...

Asuba, gari ya ɗan fara waye wa.
A kan titin da hatsarin Amal ya faru, an riga an zagaye wurin da igiya, motar FRSC da ta ‘yan sanda na wurin tun cikin dare duk ana bincike kuma har yanzu ba'a samu wani shaidar da zai sa da ganga akayi hatsarin...
A lokacin da suka ciro Amal daga cikin motarta, jikinta a jike yake da jini, rigarta kalar fari duk ya rine kamar ba farin riga ba, idanunta a rufe kamar wacce take barcin mutuwa.

“Gaggawa! Ku ƙira ambulance!”
“Ba zata iya rayuwa ba idan ba a kai ta yanzu ba!”

Motar ‘yan sanda ce ta ɗauke ta, aka nufi babban National Hospital Abuja da ita.
Likita ne yake bada umarni cikin tashin hankali:

“Blood level ɗinta ƙasa da kashi 10%. A nemo masu jini nan take! Waye ‘yar uwarta? Waye nata?”

Amal na kwance babu numfash..Da farko duk wanda ya ganta bazaiyi tunanin akwai rai a jikinta ba..


🇬🇧 A London

A gidan da Abbah da Ammy ke zama, labarin hatsarin ya iso da safiyar nan.
Wani daga cikin ma'aikata campany ne ya ƙira:

“Sir, Madam Amal had an accident last night... she’s in a critical condition.”

Da wannan kalma guda, wayar Maleekh ta sulale daga hannunsa..
Hankalinsa ya tashi kamar wanda aka cire masa rai.

“What? Amal? Accident?!”

Ya ɗauki wayarsa ya nufi part ɗin da Abbah yake da sauri.

“Abbah! Amal ta samu hatsari! Ba zan iya zama ba, dole mu tafi yanzu!”

Ammy ta riƙe ƙirji, ta ce cikin tsoro:

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Meya haddasa hatsarin?... Allah Ya bata lafiya, idan kuma ta mutu Allah ya jikanta. Amma meye namu da zamu tafi haka da gaggawa sai kace Islam ce ko Arfat tayi hatsari..”

Abbah ya ce "Insha Allahu tana nan da ranta, kuma itama Amatu ƴa ce a wurina, dole mu tafi ko bakya so..."

Nan Maleekh ya ji do musu akwatuna...

Ba a ɓata lokaci ba, aka nufi filin jirgi.
Duk tafiyar ta Maleekh ta cika da hawaye da addu’a.
Yana cikin jirgi, hannunsa na riƙe da hotonta a wayarsa, hoton da take dariya da idanu masu cike da kyalli...

“Amal, ki tsaya ki jirani... don Allah kar ki barni.”


✈️ A Abuja

Da suka sauƙa, Abbah ya sanar cewa su fara zuwa hospital. Ammy ta ce
"Ni kam zan wuce na gaji.."

Abbah ya ce "Sai mun je kinga halin da sirikar ki take.."

Ba yanda ta iya haka ta haƙura.
Kai tsaye hospital suka nufa cikin gudu da motar da aka kawo musu airport..
Jikin Maleekh sai rawa yake, zuciyarsa kamar zata faso ƙirji..
A bakin ƙofar asibiti, likitoci da nurses ne suka cika wurin, haka suka kutsa ciki, Maleekh yana shiga kowa ya tsaya kallonsa saboda hotunansa sun bazu a kafafen labarai, kama shi da akayi a london sakamakon miyagun kwayoyi da aka gani a jakarsa...

Abbah ne yayi magana da cewa:

“Excuse me! Where is Amal Abdulsamaad? The accident victim from last night!”

Wata nurse ta ce:

“Room 204… but sir, her condition is very critical.”


Suka nufi ɗakin kamar zasu fira.. Ita kuwa Ammy a nutse take takun ta..
Abbah shima dakatawa yayi sakamakon wata Nurse da ta sanar musu cewa
"Ku ɗan dakata ana duba majinyaciyar, ga can wurin zama..."

Kafin ta ƙarasa Maleekh har ya buɗe ya shige ciki.
Abbah girgiza kai yayi yana mamakin ɗan nasan da taurin kai. Haka suka nufi wurin zama kafin ayi musu iso..


Bayan ya shiga, Maleekh ya tsaya cak..
Amal na kwance cikin farin zanin asibiti, fuskarta duk raunika ga an zagaye kanta da bandeji, jinin da aka ɗaura mata ya kusan ƙarewa..
Hankalinsa a tashe ya ƙarasa kusa da ita ya riƙe hannunta, muryarsa na rawa:

“Amal… kina ji na? It’s me… Maleekh. Don Allah ki buɗe idonki… kar ki barni.”

Nurse dake kusa ta ce:

“Bamu da isasshen jini, kuma jinin nata AB positive ne mai wuyan samu, wannan ma da ƙyar muka samu, yanzu muna neman ledar jini uku.”..


Maleekh ya miƙe, yana faɗi cikin murya mai ƙarfi:

“Ni O- ne. Ku ɗauki nawa! Ku ja jini daga jikina yanzu! Don Allah ku ceto ta!”

Nurse ta kalle shi da mamaki:

“Kai ne za ka bayar?”

“Eh! Ba tare da tunani ba. Ku fara yanzu!”

Maleekh ya ce yana jan ye hannun rigarsa...

Ɗakin ya cika da sanyin AC, duk da haka gumi ke keto a goshin Maleekh saboda tashin hankali. Amal tana kwance, oxygen a hancinta, jini na gudana daga bututun da aka haɗa a hannunta..

Likita ya fito daga wani ƙaramin ɗakin dake cikin room ɗin da sauri yana faɗin

"Meke faruwa anan?..."

Nurse ce ta sanar masa cewa.
"Sir wannan ɗan uwanta ne yazo..."

Maleekh ya ce "Me kuke kike jira ne? Ki ja ki farfaɗo mun da ita..."

Doctor ya kalli Nurse sannan ya ce "Kun yi ne akan zaki ja jininsa? Sannan kin sanar masa adadin jinin da ake buƙata ne?.."

Nurse ta sunkuyar da kai cikin kikkina ta ce

"Sir. Shi ya ce a ja ukun..."

"Mtssww you are not serious..." Doctor ya ce tare da kallon Maleekh ya ce...


“Mun jira babu wanda yazo a cikin ƴan uwanta, meyasa sai yanzu? Shin baku damu da ita bane?...."

Maleekh ya goya hannayensa akan ƙirji ya ce "Look Doctor! Kar ka nemi ka gaya mun magana, yanzu haka daga London nake, a yau nake jin labarin, kuma ni mijinta ne..."

Doctor ya ce

"Okay! Bamu da isasshen jini, kuma jinin nata AB positive ne, wanda yake da wahalar samu a halin yanzu. Wannan ma da ƙyar muka samo leda ɗaya, yanzu muna neman ledar jini uku kafin ta iya farfaɗowa gaba ɗaya.”

Maleekh wanda ke tsaye yana fuskantar Doctor ya ce cikin murya mai ɗaure kai,

“Nurse ta mun bayani. Amma taya AB zai yi wahalar samu? Jini na O-negative ne, ku janye daga jikina yanda zai iya mata..!”

Likitan ya kalle shi da mamaki,
“Amma Sir Maleekh, jinin O- yana da tsada sosai ga jikin mutum, kuma jini leda uku bazai jitu da lafiyarka ba. Zai iya raunata zuciyarka.”

Maleekh ya ɗan ɗaga murya cikin ƙarfi, idonsa ya cika da hawaye,
“Na ce ku janye! Tunda rayuwarta tana cikin haɗari, babu wani abu da ya fi muhimmanci fiye da ta rayu. Ku janye ku bata tunda jinin nan da kuke gani yana gudana ne saboda ita!”

Likita ya tsaya na ɗan lokaci kafin ya ce,
“To shikenan, amma dole mu lura da lafiyarka. Wannan haɗari ne, sai mu shiga can bangaren ka kwanta bayan an gama don a saka drip ɗin ƙarfi a jikinka.”

Dake room ɗin babba ne, ya kwanta a ɗan nesa da ita wanda glass ne ya tare tsakaninsu..amma yana iya hangota ta cikin glass ɗin...

Maleekh ya ɗan murmusa cikin damuwa, yana duban Amal daga nesa ta cikin gilashin ƙofar d'akin jinya,
“Ina roƙon Allah ya karɓi wannan jinin ya mayar da shi da albarka a jikinta. Ko da zan rasa rayuwata, ta rayu kawai.”

Likitan ya girgiza kai da tausayi,
“Wannan soyayya ce mai haɗari, amma Allah ya sa ta tashi lafiya.”

Sai aka ɗauki bututun jini aka haɗa da hannun Maleekh, zuwan jinin a cikin bututun yana fitowa a hankali. Maleekh ya lumshe ido, jikinsa yana rauni amma zuciyarsa cike take da natsuwa.

A gefe, Ammy da Abbah suka shigo cikin gaggawa. Bayan nurse ta sanar dasu halin da ake ciki... Suka shiga Ammy ta nufi Maleekh da gudu.

Ammy ta ce cikin rawar murya,
“Me ya faru da shi? Me yasa aka haɗa shi da na’urar jini?”

Likitan ya kalle su cikin ladabi,
“Yana ba wa Amal jini ne, saboda babu wanda yake da jinin da ya dace da nata.”

Abbah ya tsaya ya goya hannayensa akan ƙirji, yana kallonsa da idanu masu cike da ƙauna da damuwa,
“Maleekh… ka cika jarumta. Amma me yasa baka faɗa min ba kafin ka yanke wannan hukuncin?”

Maleekh ya buɗe ido a wahalai, ya ce cikin rauni:

“Abbah… idan na rasa jini saboda ita, to hakan ma bai kai na rasa Amal ba.”

Ɗakin ya ɗauki shiru na mintuna biyu, sai ƙarar na’urar jinin da ke motsi, tana nuna ana cigaba da tsotsar jinin.

Likitan ya kalli ma’aikata ya ce da sauri,
“Ku kula, kada ku wuce pints biyu kawai. Wannan jarumin zai iya faɗuwa a nan idan kuka wuce.”..

Bayan mintuna talatin, aka sake ɗaura wa Amal jinin da aka ja daga Maleekh...

Doctor yana kallon Maleekh ya ce "ka jira zuwa nan da awa 5 za'a sake jan na biyu..

Maleekh ya ce "Ni kam ku cire gaba ɗaya bana son jinkiri, 2 pints ku ka ce, sannan 3 ake buƙata kuma kun cire 1..."

Doctor ya ce, "Sorry..."

Kafin ya ƙarasa Maleekh ya katse shi da "Sorry for what?..."

Doctor ya cigaba da jan jinin kamar yanda ya buƙata...

Jinin Maleekh yana shiga cikin Amal a hankali, likita yana kallon monitor ɗin zuciyarta.
Sai suka ga bugun zuciya ya fara motsawa a hankali.

“Doctor! Heartbeat is rising!”
“Keep it steady. Don’t stop the transfusion!”

A cewar wata Nurse...

Maleekh juyar da kansa yayi cikin damuwa yana tuna abubuwan da suka faru a tsakaninsa da Amal..

Haka al'amura suka cigaba da tafiya...


Bayan doguwar suma na kwanaki uku, Amal ta fara motsi. Idanunta sun fara buɗewa a hankali, Inna da Abbah dake ɗakin, ba ƙaramin farin ciki suka yi ba, suna hamdala cikin nutsuwa...

Likita ya shigo, ya dubi lafiyarta da bugun zuciyarta.

“Lafiyarki tana nan, amma za ki buƙaci hutu da kulawa sosai,” in ji likitan.

Amal kuwa ba abunda take faɗi illa ƙiran Maleekh:

“Ina ya Maleekh? Ina yake? Ina son ganinsa...”

Ganin ta damu da ganin shi, Abbah ya ɗauki waya da gaggawa, ya ƙira Maleekh.
Bayan wasu mintuna kaɗan, sai ga Maleekh ya shigo cikin haɗa rai. Fuskar sa cike da damuwa, idonsa na nuna nauyi da ƙiyayya, tunanin hoton da ya gani na Amal da kuma ganinta akan gado da Zayd a ɗaki ya cika ransa da rikici. Amma zuciyarsa ta ɗan tsaya: zai amince ya aure ta bisa umarnin Abbah, duk da cewa yana son Amal sosai.

Maleekh ya zauna a gefen gadon asibiti, bai kalli Amal ba. Kamar yana ɓoye wani abu a zuciyarsa, ya nisanci kallonta da duk wani murmushi da zai iya bayyana.

Amal ta ɗan yi motsi, ta gane cewa shi ne ya shigo, sai hawaye suka gangaro mata tare da murmushi mai rauni a bayyane akan fuskar ta. Ta riƙe hannunsa tana jin ɗumin jikinsa, tana jin ƙaunar sa da kewar sa...

Maleekh ya yi ƙoƙarin daidaita numfashinsa, bai jan ye hannunta ba haka ya daure yana danne fushinsa.
Daga baya, Inna da Abbah suka tashi suka bar ɗakin, suka basu wuri su biyu kaɗai..

Amal ta ɗan motsa, idanunta suka haɗu da na Maleekh. Hawaye suna gangarowa amma fuskar ta na cike da farin ciki. Ta miƙa hannu ta shafa fuskarsa tana wasa da gemun...

59 / 82