Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
tana wanzuwa cikin wani irin shauƙin da bata taɓa jin makamancin sa ba.
Maleekh yana raɗawa a hankali..
"Bakinki… ya fi kowanne abu da na gani kyau. Na kasa hana kaina kallo, Amal."
A lokacin, Amal ta kasa motsawa. Jikinta ya yi sanyi gaba ɗaya, zuciyarta ta cika da ƙaunar Maleekh, soyayyar da ta ɗauke mata hankali. Hannunta ya motsa kaɗan kamar tana son ta riƙe hannunsa da ke shafawa a lips ɗinta.
Sai shiru ya mamaye su. sai numfashinsu da bugun zuciyoyinsu ke cika bathroom ɗin.
Maleekh ya matsa gaba ɗaya kusa da ita, har Amal ta ji ƙirjinsa yana gogan nata. Hannunsa guda ya sauƙa kan kafaɗarta, ɗayan kuma yana bin gashin kanta yana yawo..
Amal ta buɗe idanunta da sauƙin numfashi, ta haɗa kallo da shi. Idanun su sun zamo kamar maganarsa da maganarta na haɗuwa a wuri ɗaya, babu kalma, babu magana sai soyayya mai kauri.
A hankali Maleekh ya sauƙe hannunsa daga kafaɗarta zuwa bayanta, yana jan ta zuwa jikinsa. Amal ta kasa motsa wa, Sai ma jikinta da ya sake, Idonta a rufe, tana jin wani irin nutsuwa da ƙauna...
Maleekh har ya kusan rungumar ta gaba ɗaya.
Sai dai a wannan lokacin zuciyarsa ta yi wani irin harbawa. Wani murya a ransa ta tunasar da shi:
"Ka manta da fansarka ne Maleekh? Ita ce za ta biya maka laifin da ta aikata, ka manta? Kada ka bari soyayya ta mamaye ka..."
Ya runtse idonsa da ƙarfi, yana ƙoƙarin danne abinda zuciyarsa ke hura masa.
A hankali ya janye hannunsa daga bayanta, ya ɗan matsa gefe kaɗan. Yayi kamar bai so ya janye ba, amma zuciyarsa ta tilasta shi.
Amal ta buɗe idanunta a hankali, tana kallonsa cikin rashin fahimta. Ta ji kamar akwai wani abu da ya kusan faruwa amma ya tsaya cak. Ta ji daɗi da kuma ɗan haushi lokaci guda...
Maleekh ya ɗan yi murmushi mai rikitarwa, wanda babu wanda zai iya gane ma’anarsa, baƙin ciki ne ko jin daɗi? Sai dai murmushin ya nuna ɓoyayyen abu a ransa...
Maleekh cikin murya mai rauni, kamar yana danne zuciya ya ce
"Amal… na kasa fahimtar yadda nake ji a kanki. Amma lokaci zai nuna."
Sai ya juya, yana sakin numfashi mai zurfi, ya bar ta a wajen tana kallonsa cike da mamaki..
Fita yayi daga bathroom ɗin...
Bayan ya fita ne Amal ta nufi ƙofa ta sa key, sannan ta shigo ciki ta shire kayan jikinta gaba ɗaya ta nufi bathtub..
Sai da ta ɗau mintuna kafin
ta fito daga bathroom ɗin, tana ɗaure da towel har zuwa kirji. Tana fitowa idonta ya faɗa kan rigar da suka siya a supermarket, Maleekh ne m ya zaɓa mata a cikin sauran rigunan ya ajiye a kan gadon...
Cike da murmushi ta ɗauki doguwar riga mai siririyar shape, riga ce milk-white mai ɗauke da ɗan glitter a gefe, cike da zumud'i ta sanya rigar..
Rigar ta rufe jikinta tsaf, amma ta fito da siffar hips ɗinta, shape ɗin ƙirjinta, da siririn kugunta.
A gaban madubi ta tsaya, tana gyara rigar da kanta, tana taɓa gashin kanta wanda ya bazu har gadon baya...
Amal ta tsaya gaban mirror tana gyara rigar jikinta, rigar ta kama jikinta har sai da ta fito da dukkanin surar da Allah ya yi mata. Hannunta na kan sumar kanta tana janye shi gefe, idonta kuma na ƙafe akan hoton kanta da yake cikin glass...
Maleekh ne ya shigo falo da sallama a bakinsa yana ɗauke da kulolin abinci, ya ajiye a kan dinning dake falon, sannan ya ɗauko drinks a frig ya ajiye su...
Cikin bedroom ya nufa..
Yana shiga ya tsaya a bakin ƙofa kamar an dasa shi. idonsa na kan Amal...
Numfashinsa ya tsaya na ɗan lokaci. Ya ji kamar duk wani tunanin tsanar Amal da ke ransa ya ɓace a wannan mintuna..
Ita kuwa tana tsaye a jikin mirror ta kasa ɗago idonta ta kalli ƙofar, duk da tasan Maleekh ya shigo.
Idonsa ya zame mata kamar camerar da ta makale akan kyanta. Yana kallonta tana kallon kanta a madubi.
Amal ta fito da wani irin kyau da har haske na mirror ɗin ya ninka mata kyau ɗin da take dashi..
Shima fa Maleekh ba'a barshi a baya ba..
Kyansa ya sha bamban.
Kyakyawa ne irin wanda idan ya shigo taro, kai tsaye idanun kowa yake sauƙa kansa.
Tsayinsa ya zarce, cikakke ne da girman da ya dace da namiji...
Jikinsa faffad'a ne, broad chest ɗin da yake nuna ƙarfinsa, amma bai yi nauyi da yawa ba.
Launin fatarsa chocolate mai haske, irin wanda yake kama hasken rana da ɗan sheƙi.
Fuskar sa mai ɗan faɗi ce mai ɗaukar ido, ga dogon hanci madaidaici, ga girar da ta cika masa saman ido kamar an zana..
Ga ƙaramin bakin sa mai laushi da pink lips ɗinsa da kallo ɗaya kaɗai ya isa ya rikitar da mace.
Ga sumar sa mai ɗan tsayi, baƙi mai sheƙi, da siririn waves kamar sabon aski..sajen nan ya kwanta kamar wanda yayi masa shampoo...ma sha Allah..
Sai ka rantse Maleekh ba ɗan Nigeria ba ne, sai ka ce hoton wani ɗan jarumin Bollywood actor da aka hado da cikakken tsari na asali..
Maleekh ya tsaya yana kallon Amal, idonsa bai motsa daga kanta ba.
Sai dai Amal duk da ta san yana kallonta ta ci gaba da shafa rigar tana kallon kanta a madubi. Zuciyarta na bugawa da sauri, amma ta kasa juyawa ta kalli idanunsa saboda jin nauyin wannan kallo da yake mata.
Numfashin Maleekh ya ɗan canza. Zuciyarsa na rawa, kyan Amal a cikin wannan riga ya rikita shi. Ya sha ganin mata masu kyau a duniya, amma kyanta na yau ya bambanta.
Sai ya matso da takunsa a hankali, kamar wanda yake jan kansa zuwa wani abu da bai shirya ba…
A hankali ya ƙarasa kusa da ita, ya tsaya a bayanta idanunsa suna kallon hotonta a cikin mirror. Amal ta lura da shi ta cikin reflection ɗin, sai zuciyarta ta buga da ƙarfi. Amma ta kasa juyowa ta kalle shi kai tsaye.
Sai dai jikin ta ya bayyana gaskiyar zuciyarta: numfashinta ya fara hargitsewa, launin fuskarta ya ɗan sauya, jikinta ya yi sanyi.
Maleekh ya matso sosai tare da ɗago tafin hannunsa ya sauƙar akan gashin kanta...
Ya shafa gashin nata a hankali, yana kallon idonta cikin madubi.
“Amal…” ya furta da muryar da ta raɗaɗa zuciya, mai nauyin so da tsananin shauƙi.
Amal kuwa ta rufe idonta na ɗan lokaci, tamkar tana jin wani abu ya taso daga ƙasan zuciyarta har ya shige dukkanin jinin jikinta. Duk da tana so ta guje masa, amma sai ta kasa.
Maleekh a sannu a hankali ya sauƙe yatsunsa daga gashin kanta zuwa gefen fuskarta, ya bi layin lips ɗinta ta cikin reflection ɗin, yana shafa a hankali.
Numfashinsu na fita a hankali, glass ɗin mirror ɗin ya kama hucin zafin numfashinsu.
Wani irin shiru ne ya lulluɓe ɗakin, sai bugun zuciyoyinsu kawai suke ji.
A wannan lokacin, soyayyar da suke ɓoye tana bayyana cikin sauƙin shauƙi, kamar wani fim ɗin soyayya na Indiya inda idanu da jiki suke magana ba tare da kalma ba...
Maleekh ya ci gaba da kallon Amal ta cikin mirror, numfashinsa yana sauƙa akan wuyanta. Yatsunsa har yanzu na kan lips ɗinta, yana shafawa a hankali..
Amal ta lumshe idonta gaba ɗaya, jikin ta ya mutu tamkar ba nata ba. Wani irin sanyi mai daɗi ya lulluɓe ta, zuciyarta ta shiga wata sabuwar duniyar soyayya da bata taɓa tsammani ba.
A hankali Maleekh ya manno jikinsa a nata ta baya. Zafin numfashinsa yana sauƙa a saman wuyanta, hakan yasa jikinta ya ɗauki rawar shauƙi.
“Amal…” ya ƙira sunanta a hankali, muryarsa kamar ƙarar raɗa daga zuciya.
Tayi shiru, amma shiru da ya fi kowanne magana. Idonta na rufe, hancinta yana shaƙar ƙamshin jikinsa wanda ya cika ɗakin.
Maleekh ya ɗora hannunsa ɗaya a kan kafaɗarta, ɗayan kuma yana biye da gefen kuncinta har zuwa ƙaramin bakinta.
Sannu a hankali ya sunkuyo sosai har fuskokinsu suka haɗu ta cikin reflection.
Lips ɗinsa yana gogan nata a hankali, ba tare da sun haɗu gaba ɗaya ba. Wannan kusanci ya rikita Amal fiye da duk wani abu da ta taɓa ji a rayuwarta.
Sai ta buɗe idonta a hankali ta kalle shi ta cikin madubi. A can cikin reflection ɗin, ta hango soyayya da shauƙi, amma a zurfin idonsa akwai wani abu da bata iya fassara ba.
Hannunta ne ya fara karkarwa, da sauri ta ɗora shi a kan hannunsa da yake riƙe da fuskarta.
A hankali tace da muryar da ta cika da rawar zuciya:
“Maleekh…”
Shi kuwa ya ƙara kusantar fuskarsa sosai, har numfashinsu yana gaurayuwa. Ya ɗan murmusa cikin wani irin salo, sannan yace:
“Ke ce abinda zuciyata ta daɗe tana jira… na tabbata, bazan taɓa barin wani ya rabani dake ba…”
Sai ya lumshe idonsa ya ɗan goga dogon hancinsa a kan wuyanta cikin shauƙi, ba tare da ya janye jikinsa ba.
Amal kuwa ta kasa motsawa, ta shiga duniyar da soyayya ta mamaye ta baki ɗaya.
Lokacin da numfashin Maleekh ya gauraye da nata, zuciyar Amal ta yi wata irin tsalle. Ta ji tamkar wani abu ya fashe a cikinta, shauƙi ya mamaye ta har ta kasa jurewa.
Ba tare da wani tunani ba, ta juyo da sauri daga inda take tsaye a gaban madubi, ta faɗa cikin ƙirjinsa da ƙarfi. Hannayenta biyu ta zagaye masa wuya tana rungumarsa da tsananin ƙarfin zuciya.
“Maleekh…” ta ƙira sunansa cikin rawar murya, hawaye na zubo mata ba na bakin ciki ba, sai dai na farin ciki da nutsuwar da ta tsinci kanta a ciki.
Shi kuwa ya tsaya sumamme, bai taɓa tsammanin Amal zata nuna irin wannan kuzarin ba. Zuciyarsa ta yi wani irin bugu, a lokaci guda soyayya da fansa suka fara gwabza wa a ransa.
Ya ɗora hannayensa biyu a bayanta, ya matse ta a jikinsa sosai. Numfashinsa ya yi nauyi, zuciyarsa tana son zaucewa gaba ɗaya.
“Amal…” ya ƙira cikin murya mai zurfi, yana ɗora habarsa a kanta.
“Kin sani a matsayin da babu wanda ya taɓa kai ni…”
Amal ta ɗago kanta tana kallonsa, jikinta har rawa yake saboda ƙarfi da zafin da zuciyarta ta ɗauka.
“Saboda kai nake rayuwa yanzu… idan ba kai ba, to waye?” Ta faɗa tana ƙura masa ido..
Maganarta ta ratsa shi kamar wuƙa, sai ya ɗan runtse idonsa. Ya ɗora ɗan yatsansa a kan lips ɗinta yana share hawaye a hankali.
Sai suka tsaya a haka, jikin ta ya lulluɓe ƙirjinsa, zuciyarsu biyu suna bugawa cikin daidaito, tamkar ana kunna kiɗan soyayya da ba a iya ji sai da rai.
A hankali Maleekh ya ɗora bakinsa a saman goshinta, ya yi kissing mai daɗi da tsawo. Wannan ya saka Amal ta sake ƙara matse shi da ƙarfi, tamkar zata shige jikinsa gaba ɗaya.
Amal ta kasa jurewa irin yadda zuciyarta take harbawa, ta ɗaga hannuwanta a hankali kamar mai jin tsoro, sai kuma ta jingina jikinta a kirjin Maleekh, ta rungume shi da ƙarfi tamkar mai neman mafaka.
Numfashin su biyu ya haɗu, shi kuwa ya runtse idanu yana jin zafin sha’awa da sanyi na soyayya ya lulluɓe shi.
Cikin wannan yanayi ne, muryar mace ta katse su:
Farha cikin tsawa da rawar murya ta ce
“Na shiga uku! Mai zan gani haka? Amal… kina da hankali kuwa zaki rungume mun miji?”
A razane Amal ta yi saurin janyewa daga jikin Maleekh, jikinta har rawa yake. Ta juyo da kallon bakin ƙofa, ta hango Farha tsaye bakin ƙofa, hannunta a ƙirji, tana zazzaro da ido waje..
Maleekh ya ƙanƙance ido yana kallonta da mamaki da fushi lokaci guda. Ya matsa gaba kaɗan, yana faɗin
“What nonsense is this? Waye ya baki damar shigo mun ɗaki haka ba knocking, ba excuse? Haba Farha!”
Farha cikin hararar Amal, tana yatsina fuska ta ce
“Ni fa matar gidan nan ce. Ko dole sai na nemi izini in shiga bedroom ɗin mijina?”
Maleekh yana daga murya ya ce
“Matar gidan nan? Kin manta wannan ɗaki ba naki bane? Kin wuce gona da iri Farha! Kin sa kanki inda bai dace ba.”
Farha ta matso gaba tana huci ta ce
“Ai kuwa sai ka shaida a yau, domin bazan yarda da wannan abu ba! Ni a gabana wani abu irin wannan ya faru, ka kuma ce ba ni da hurumin magana?”
Amal ta sunkuyar da kai kamar wata tsohuwar munafuka tana tsoron kallon Farha. Ta matso gefe, jikinta kamar zai faɗin tsabar kakkarwa...
Maleekh ya kalle ta tare da riƙo hannunta yana matsawa alamar ta kwantar da hankalin ta,... lokaci guda ya mayar da hankalinsa ga Farha, yana tsananta fushinsa:
“Farha, ki fita kafin nayi wurgi dake. Ki fita yanzu kafin na sa ranki ya ɓaci fiye da haka.”
Farha ta yi dariyar raini mai ɗaci, sannan ta juyar da idanu, tana faɗin:
“Lallai yau na tabbatar soyayyar da kake yiwa Amal ta wuce tunani… Amma wallahi, ka fara shiryawa, domin ni ba zan bari ta cinye mun zuciya a gidan da nake da hakki ba!”
Ta juya da sauri ta fice daga ɗakin tana harba ƙafafu kamar mai fareti..
Dakin ya ɗauki shiru, numfashin Amal da Maleekh kawai ke cike da sararin bedroom ɗin....
NEXT NEXT NEXT....
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 23 to 24
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Bayan Farha ta fice tana bubbuga ƙafafu, sai bedroom ɗin ya koma shiru. Maleekh ya tsaya hannunsa a ƙugu, tsabar tsananin fushi haka yake bin ƙofarda Farha ta tsaya da kallo. Numfashinsa na fita da sauri...
Amal kuwa tana tsaye a gefe tana riƙe da hannun rigarta, zuciyarta na dukan uku-uku. Bata iya ɗaga ido ta kalle shi ba, saboda tsoron abinda zai faru.
Cikin rawar murya ta furta:
“Ka ga irin abinda ya faru koh?… ka ga abin da ta gani…”
Sai kawai Maleekh ya juya da sauri ya ƙaraso inda take. Ya ɗora tafin hannunsa a kan hannunta da take riƙe da rigarta, ya sa ta sake a hankali. Yana kallon idonta kai tsaye, yana furta
“Stop it, Amal. Don’t blame yourself. Ba ke kika karya ƙa’ida ba… ita ce ta karya. Ke baki da laifi.”
Ya matso kusa sosai har tana iya jin zafin numfashinsa a fuskarta. Idanunsa suka cika da wani irin tsananin kulawa da ƙauna.
A hankali ya kuma cewa
“Na tsani ganin kin shiga damuwa saboda wani. Na tsani ganin kin firgita. Ki kwantar da hankalinki, ba zan taɓa bari Farha ko wata ta cutar dake ba. You’re mine, Amal.”
Yana faɗin haka ya kamo hannayenta biyu ya ɗaure su da nasa, ya ɗaga sama ya jingina su da ƙirjinsa.
Amal cikin hawaye ta ce
“Amma Maleekh… maganganunta suna da zafi sosai. Ni kam tsoron rikici nake ji…”
Maleekh yana girgiza kai cikin ƙarfi ya ce
“Rikici? To let her dare. Let her dare, Amal. Wallahi babu wanda zai iya rabani dake. In na faɗi abu, sai ya tabbata. Babu mai tsayawa tsakanina da ke.”
Ya ɗora hannunsa ɗaya a bayan kanta, ya jawo ta jikinsa sosai. Yana faɗin
“Ki saurara da kyau, Amal… babu wata mace a rayuwata da zata iya mamaye zuciyata kamar ke. Ko da me zata yi, ko da me zata faɗa… you’re the only one.”
Sai ya ji jikinta ya yi sanyi a jikinsa, tana ɗan fashewa da kuka a hankali, zuciyarta na narkewa da kalaman nasa.
Bayan shiru mai ɗaukar lokaci, Maleekh ya saki ajiyar zuciya sannan ya ɗan raba jikinsa da nata, yana kallonta cikin lumsasshen ido. Ya ce
“Come on… zo mu je falo. Kina buƙatar kwanciyar hankali, sannan kuma kina buƙatar cin abinci.”
Ya kama hannunta a tausashe ya ja ta zuwa falo, kai tsaye zuwa dinning area ɗinsa da ya jera kulolin abinci a kai. Amal tana tafiya a hankali, tana jin yadda hannunsa ke riƙe da nata tamkar kada ya sake.
Bayan suka isa, ya zame kujerar dinning ɗaya ya ja ya zaunar da ita, sannan ya zauna a gefenta. Kulolin abinci masu ƙanshi ya buɗe, ƙamshi ya gauraye wajen.
Sai ya ɗauki cokali ya zuba mata cikin faranti, yana murmushin da bai saba yi ba. Idonsa na lumshewa kamar na wanda ya shafe dare bai huta ba.
Amal tana kallon sa ta ce
“Maleekh… ka dai bari ni zan ci da kaina.”
Ya girgiza kai cikin izza da taushin murya ya ce
“No, Amal… tonight ba zan bari ki yi komai da kanki ba. Ki huta kawai, ni zan kula dake.”
Ya ɗauki spoon ɗin ya ɗebo abinci ya kai mata baki. Amal ta tsaya kallonsa, zuciyarta na rawa da wani irin zafi mai daɗi. A hankali ta buɗe baki ta karɓa.
Maleekh ya kasa cire idonsa daga fuskarta yayin da take taunawa. Hannunsa da ya riƙe spoon ɗin ya tsaya cak, yana jin tamkar lokaci ya tsaya a wurin.
Maleekh a hankali kamar yana furta a ransa ya ce
“Allah ya sani… kina da wani abu a jikinki da ke rikita ni…”
Amal ta ɗaga ido ta kalle shi, idanuwansu suka haɗu, suka tsaya suna kallon juna cikin nutsuwa.
Sai ya sake ɗaukar wani ya sake bata, yana murmushin da ya fi na baya taushi.
Amal cikin ƙanƙanin murya ta ce
“Na gode… Maleekh.”
Sai kawai ya sa hannunsa ɗaya ya dafa ƙaramar fuskarta, yana shafa gefen kumatunta mai taushi, sannan ya kai spoon ɗin gaba cikin kulawa.
Har abincin ya ƙare, suka ci cikin natsuwa. Duk da kulawar da Maleekh ya nuna mata, Amal zuciyarta na karyewa...
Maleekh ya sanar mata cewa su shiga cikin ta kwanta...
Ta san idan har ta kwana a part ɗinsa, idanun gidan gaba ɗaya za su sauƙa akan ta da wata mummunar fahimta. Amma a lokaci guda, ta kasa faɗa masa kai tsaye...
Bayan sunci abinci ya ja hannunta zuwa bedroom ɗinsa. Katafaren gadon yana shimfiɗe da blanket mai laushi, sannan ya jawo ta a hankali ya kwantar da ita..
Maleekh da saukin murya, yana kallonta daga tsaye ya ce
“Amal… ki kwantar da hankalinki. Babu wanda zai