Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
faɗi a ƙasan baki:
“Wannan ai soyayyar da ta wuce ƙa’ida ce. Don lips da hanci sun ɗan fashe, sai kamar za'a tashi duniya...”
Amal bata san lokacin da dariya ya kuɓce mata ba. Duk ciwon da take ji, sai ta kasa daurewa ganin yadda Maleekh yake ta surutai yana korafi ga doctors da nurses tamkar an kawo mace da tayi mummunan accident.
Ɗaya daga cikin nurses ta kalli Amal tana murmushi tace:
“Kin ga dole kiyi dariya, wannan ciwon naki fa bai wuce aje chemist a ɗauko maganin hanci da lips balm ba. Amma gashi an tada mana hankali.”
Doctors ma suka murmusa, suka shiga kallon Maleekh da mamaki.
Maleekh ya yi saurin hararar Amal yana faɗin:
“Au, dariya ma kike yi ko? To ki ci gaba, amma wallahi idan baki warke ba, sai nayi wa dukkan likitocin nan rigima.”
Amal ta cigaba da dariyar cikin hawaye, zuciyarta na ƙara narkewa da yadda yake nuna tsantsar damuwa da ƙauna.
Bayan sun goge mata jinin hanci da lips ɗinta da auduga, aka ɗora mata maganin ointment kaɗan, suka ce shikenan.
Maleekh ya zuba musu ido yana faɗin:
“Shikenan fa ku ka ce? Wannan kawai kuka iya yiwa matar da zuciyata take kanta? Wallahi bana jin daɗin yadda kuke sakaci da aikin ku.”
Doctors suka yi shiru suka cigaba da rubuta prescription ɗin magungunan da za a siya.
Amal kuwa ta tashi tana dariya tana riƙe da hannunsa. Haka suka fita daga ɗakin emergency kamar wacce aka yiwa babban tiyata. 😅
Maleekh da Amal suna fita daga emergency suka hangi Ammy tana nufar wani side na marasa lafiya, women ward. Suka zuba mata ido, tare da bin bayanta, domin sun tabbatar Farha tana kwance a cikin wannan hospital.
Bayan Ammy ta shiga room ɗin da aka kwantar da Farha, sai ga Maleekh da Amal suma suka shigo.
Farha a wannan lokacin tana zaune akan gado, jikinta ya ɗan warware sosai. Ganin Maleekh ya sa ta tsure, jikinta ya fara rawa, zuciyarta ta faɗi rasss. Tasan ba ƙaramin hukunci zai yi mata ba kan laifin kulle shi da tayi har tsawon sati uku.
Ammy kuwa ganin Amal yasa ta tunzura, ta ɗaga murya cikin fushi tana faɗin:
“Waye ya bada izinin sako ki daga police station?..”
Maleekh ya yi saurin cewa cikin tsawa:
“Nine!”
Ammy ta zuba masa ido cike da mamaki, zuciyarta cike da takaici. Ba ta taɓa tsammanin ɗanta zai tsaya a gaban idonta ya kare wata mace irin haka ba.
Sai kuma ya juyo da hancin fushinsa kan Farha. Kallo ɗaya ya yi mata, sai jikinta ya fara rawa. A tsawace ya ce.
“Wa ya baki izinin kulle ni a ɗaki?”
Shiru tayi, tana sunkuyar da kai.
Maleekh ya darara mata tsawa, har Ammy da Amal suka zabura da tsoro.
“Magana nake miki! Ko baki da kunne?!”
Cikin rawar murya, Farha ta ce da kyar:
“Babu…”
Maleekh ya ci gaba da magana, zuciyarsa kamar wuta:
“Amma ban taɓa sanin ke daƙiƙiya, jahila, banza jaka marar class ba, sai yau. Wacce kwakwalwarta datti ya cika. Shin a tunaninki, a haka zan aure ki? To wallahi ko mata sun ƙare a duniya, bazan taɓa aure ballagaza irinki ba. Na tsane ki Farha, na tsane ki da zuciya ta gaba ɗaya! Kuma ki tabbata, daga yau zaki tattara ki koma can gaban iyayenki. Bazaki cigaba da zama a gidan mu ba!”
Farha ta riƙe ƙirjinta tana rawar jiki, hawaye suka fara sauƙa a idonta.
Ammy ta tsaya dafe da goshinta, tana mamakin irin kalaman da ɗanta ya zuba wa Farha a gaban Amal..
Amal kuwa tana tsaye a gefe tana kallon Maleekh, zuciyarta na tafarfasa da soyayya da alfahari da irin yadda yake tsaya mata.
Farha ta riƙe kirjinta tana rawar jiki, hawaye na zuba kamar ruwan sama. Tana faɗin cikin kuka:
“Don Allah kayi haƙuri Ya Maleekh… Na yi kuskure ne saboda sonka… Wallahi sonka ya rufe mun ido… Na rasa tunani saboda kai…”
Maleekh ya yi wani tsaki mai ƙarfi, idonsa jajir kamar wuta.
“Sonka fa kike cewa? Wannan abin kunya da kika yi ne soyayya? Kulle ni cikin ɗaki kamar zakin da aka saka a keji? Ki hana ni zuwa masallaci? Ki hana ni aiki? Ki hana ni zuwa ga masoyiyata? Wannan ba soyayya bace, hauka ce, haukar banza!”
Farha ta fara matsawa baya tana girgiza kai, hawaye na kwaranya.
“Wallahi ban yi nufin cutar da kai ba…”
Maleekh ya katseta da cewa
“Karya kike! Ba wai cutar da ni ba kawai kika yi ba, kin cutar da Amal! Kin je gidanta, kin je kin tada mata hankali, kin saka mata fargaba, har kin sa aka ɗauke ta zuwa police station saboda sharrinki! Yanzu ki gaya min, menene laifinta? Menene kuskurenta da za ki wahalar da ita haka?!”
Farha ta kasa magana, tana kallonsa da idanuwanta da suka kumbura da kuka.
Maleekh ya matso kusa da ita, muryarsa ta sake kaɗawa cikin ɗaki:
“Na rantse da Allah Farha, kin gama da ni. Kada ki sake furta sunana, kada ki sake bibiyata, ka da ki sake kusantar Amal. Wallahi idan kika sake kusantar ta ko da a mafarki ne zan sa kiyi kuka na gaske. Na gama da ke, kuma kema kin gama da ni!”
Farha tana kwance a gado, tana ɗaure da drip. Maleekh yana tsaye da fuskar ɓacin rai, yana ɗaga murya:
Ya ci gaba da faɗin
“Farha! Yanzu na gane baki da hankali ne ko kaɗan, Wannan wautar takin tasa kin zubar da mutuncina. Kin raina ni saboda me?”
Yana nuna ta da yatsa cikin hargowa. Farha ta runtse idonta, ta kasa magana..
Ammy ta katse shi a fusace
“Maleekhhh!!!”
Ɗakin ya ɗan ɗauki shiru. Kafin ya ankara Ammy ta zabga masa mari mai ƙarfi.
Ammy tana faɗin
“Kada ka sake ɗaga mata murya haka! Ka manta marar lafiya ce? Ka manta asibiti muke? Maleekh bana son wulakanci irin wannan!”
Ta tsaya tana huci.
Maleekh ya dafe kuncinsa yana kallonta da mamaki.
Ammy ta cigaba da cewa
“Ka sani yau, auranka da Farha ba fashi! Babu wata Amal da za ka aura! Wannan yarinya ta kulle ka ne saboda soyayya, ba saboda ƙiyayya ba!”
Farha ta fara kuka cikin rauni.
Sai a nan Doctor ya shigo da file a hannunsa, ya tsaya daga bakin ƙofa, yana kallon hayaniyar.
Doctor a tausashe ya ce
“Excuse me… kuyi hak’uri. Wannan asibiti ne, akwai majinyata da basa son hayaniya..”
Suka yi shiru. Sai Doctor ya juya ya kalli Farha, sannan ya buɗe file ɗin.
Doctor cikin girmamawa da muhimmanci ya ce
“Yanzu dai za mu faɗa muku ainihin matsalar. Dalilin da yasa Farha ta faɗi dogon suma saboda ƙaramin abu shi ne, jikinta ya raunana… saboda tana amfani da wasu miyagun kwayoyi na maye.”
Ya ɗan ja numfashi.
Sannan Doctor ya cigaba da faɗin
“Mun gano tana shaye-shaye kafin rikicin ya faru. Wannan shi ne ya jawo suma, kuma idan ba’a kula ba, yana iya fara taɓar mata kwakwalwa. Don haka ku sani, matsalar tana da girma sosai.”
Ɗakin ya ɗauki shiru. Ammy ta yi diri-diri tana kallon Farha. Maleekh ya zaro ido, ya kasa magana. Farha ta rufe fuska da hannunta tana kuka.
Maleekh a firgice ya tsaya cak sannan ya ce
“Shaye–shaye??”
Ya runtse ido yana jin tamkar asibitin ya juye akansa.
Ammy ta ce
“Wannan ba gaskiya bane! Ba zai yiwu Farha ke shan miyagun kwayoyi ba! Doctor, ka tabbatar da abinda kake cewa kuwa?!”
Doctor cikin nutsuwa ya ce
“Mun tabbatar, ta sha kafin rikicin ya faru kuma ta daɗe tana sha. Wannan dalilin ne yasa jikinta ya raunana da sauri, kuma suma ta tsawon lokaci fiye da yadda ake tsammani.”
Farha ta fashe da kuka tana girgiza kai:
Fcikin kuka take faɗin
“Wallahi ba da son raina nake sha ba… wallahi! Na shiga cikin wannan abu ne saboda matsin rayuwa… saboda… saboda nake jin bana da kowa sai soyayyar Maleekh. Amma na kasa daina…”
Ammy ta dafe kirjinta cikin tashin hankali ta ce
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Farha… shaye–shaye kuma?!”
Ta matso kusa da Farha tana riƙeta, amma a fili tana jin kunya da takaicin halin da Farha take ciki...sannan tana tunanin idan iyayenta suka san da wannan maganar ya zata yi..
Maleekh ya nuna ta cikin fushi da zafi ya ce
“Shiyasa kika kulle ni a ɗaki? Shiyasa kika jefa ni cikin tashin hankali? wannan itace ‘soyayyar’ da kike ikirari? Wauta da lalaci!”
Ya juya kamar zai fita.
Ammy da ƙarfi tana tsawatar masa ta ce
“Maleekh! Idan baka amince da auren ta ba, ka sani ka karya mini zuciya. Wannan yarinya zata zama matar ka, ko da kuwa kana so ko baka so. Ka taimaka mata, ka gyara ta, ka ceci rayuwarta. Wannan shine nauyin ka a kanta.”
Farha tana kuka sosai tana girgiza kai.
Cikin kuka mai nauyi
“Ban cancanci ka taimake ni ba Maleekh… amma wallahi bana so in rasa ka. Kai kaɗai nake da kai a duniya.”
Doctor ya kalle su duka da tausayi, ya ja numfashi sannan ya ce
“Idan har kuna so ku ceci rayuwarta, sai an saka ta a rehabilitation program. Idan ba haka ba… wannan al’ada zata ƙara tsananta, kuma tana iya zama tabin hankali gaba ɗaya.”
Ɗakin ya sake yin shiru. Amal ta tsaya gefe tana kallon komai da idanu cike da hawaye, zuciyarta cike da tausayi da kuma rikici.
Maleekh ya fice daga ɗakin cikin fushi, yana riƙe da kansa kamar zai fashe da kuka. Zuciyarsa cike da fushi, takaici, da ruɗani.
Maleekh yana furta a ransa cikin zafi.
“Ni aure da mai shaye–shaye? Wannan abin kunya ne, wulakanci ne! Ammy har ta mare ni saboda ta kare ta?!”
Amal ta bi shi a baya da sauri tana ƙiran sunansa:
Amal cikin tsoro da tausayawa ta ce
“Maleekh… please, ka tsaya… don Allah ka saurare ni.”
Ya tsaya cak, ya juya da hanzari, idonsa jawur saboda fushi da takaici.
Cikin tsawa ya ce
“Me kike so in saurara Amal? Ba ki ga halin da ake ciki ba?! Saboda an raina ni, a gaban mutane ake cewa in auri wacce take shaye–shaye! Za'a naɗa min ballagaza mai dattin shaye-shaye?!”
Ya dafe bango, zuciyarsa tana tafarfasa. Amal ta matso kusa da shi da nutsuwa, ta ɗora hannunta a kan kafadarsa ta ce.
“Na san wannan abu ya girgiza ka… amma ka kwantar da hankalinka. Idan kana son yin hukunci a yanzu, zai iya zama a cikin fushi. Ka bari ka nutsu kafin ka ɗauki mataki.”
Maleekh ya kalleta sosai, kamar idanunsa za su cinye ta ya ce
“Amal… ba ki gane bane. Ammy ta ce dole ne in aure ta. Ke fa? Kina nufin ke za ki zama a gefe…? laifin me kika yi da aka sa ki cikin wannan azabar?!”
Hawaye ya taru a idon Amal, ta runtse ido tana jin nauyin kalmarsa.
Amal a hankali, cikin murya mai rauni ta ce
“Ban san dalilin da yasa duniya ta ɗora min wannan nauyin ba… Amma duk da haka, ina nan tare da kai. Ka tuna ka ce min ni matar da zaka aura ce. Wannan magana taka tana bani ƙwarin gwiwa, duk da abinda nake fuskanta.”
Maleekh ya yi shiru. Numfashinsa yana nauyi, yana kallonta tamkar yana son ya rungumeta amma zuciyarsa tana cikin rikici saboda maganar Ammy.
Sai ya ɗan matsa gefe, ya furta da ƙarfi:
“Na rantse da Allah Amal, ko da meye, ba zan taɓa yarda a tilasta min auren Farha ba! Ko da hakan zai sa na yi gaba da mahaifiyata.”
Ya ja numfashi ya wuce gaba yana tafiya cikin hanzari. Amal ta tsaya a wurin, idonta cike da hawaye...itama ta bi bayansa
Maleekh ya shiga mota cikin hanzari, ya tada engine da ƙarfin zuciya. Fuskar sa cike da fushi, numfashinsa yana tsananta. Amal ta shige a gefensa, ta dafa ƙafarsa a hankali tana kallonsa.
Shiru ne ya mamaye motar, sai karar AC da numfashinsu kawai ake ji.
Amal ta juyo da nutsuwa tana kallon Maleekh.
A hankali cikin murya mai rauni da ƙarfi a zuciya ta ce
“Maleekh… akwai kalmar da ka furta ta yi nauyi a zuciyata.”
Maleekh ya ɗan kalleta cikin mamaki, ya ce da ita.
“Me na ce? Na fa yi magana ne cikin fushi Amal.”
Amal ta ce
“Ka ce koda hakan zai sa ka yi gaba da mahaifiyarka.”
Ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya, hawaye ya taru a idonta saboda nauyin kalmar.
Amal ta ci gaba da cewa.
“Maleekh, mahaifiya darajarta babba ce a rayuwarmu. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: ‘Ku bi uwa! Ku bi uwa!! Ku bi uwa!!! Har sau uku, sannan ya ce ku bi uba.’ Wannan ya nuna mana uwa ita ce ginshiƙin rayuwa, ita ce hanyar rahamar Allah gare mu.
Allah Maɗaukakin Sarki ma ya umarce mu a cikin Alkur’ani: ‘Mu yi wa iyaye biyayya da kyautatawa, musamman uwa da ta ɗauki ciki da wahala, ta haife ka da zafi, ta shayar da kai da ƙauna.’ (Suratul Luqman: 14).”
Ta ɗan kama hannunsa da ƙarfi.
“Wallahi Maleekh, ko da mahaifiyarka ta yi kuskure, bai kamata ka furta kalmar gaba da ita ba. Ka yi haƙuri, ka nemi hanyar da zaka yi magana cikin hikima da ladabi. Wannan shi ne darajar da musulunci ya ɗora mana akan uwa.”
Maleekh ya yi shiru. Hannunsa a kan sitiyari ya ɗan yi sanyi, zuciyarsa ta fara raguwa daga zafin da take. Ya kalli Amal cikin mamaki, yana ji kalmarta tana shiga zuciyarsa kamar ruwa mai sanyaya wuta.
Maleekh a hankali ya furta.
“Amal… kin yi gaskiya, Kin tuna min darajar uwa, na ji a raina… Wallahi bana nufin in yi gaba da ita. Fushin ne kawai ya rinjaye ni.”
Amal ta yi murmushi mai taushi, ta share hawayenta sannan ta ce
“Haka nake so na ji daga gare ka. Fushi baya ƙara mana komai sai haɗari. Amma idan ka daidaita kalmomin ka da addini ya koyar mana, zaka kasance cikin nasara. Ka roƙi Allah ya yi maka jagora wajen kyautatawa uwa da yin adalci tsakanin soyayyata da ita.”
Maleekh ya ɗan kai mata hannu ya kama nata da ƙarfi, yana jin zuciyarsa ta yi sanyi sosai.
Ya ce
“Na gode Amal. Zan kiyaye kalamaina. Kuma zan nemi hanyar da ba zata cutar da ke ba, ba kuma zata ɓata wa uwa zuciya ba.”
Suka cigaba da tafiya, kowannensu yana jin wani irin salama a zuciya.
A ƙarshe motar ta tsaya a kofar gidan Amal. Amal ta sauƙa cikin nutsuwa, ta juya ta sake kallon Maleekh.
Ta ce cikin sanyin murya
“Ka tuna… uwa ita ce aljannah ko wuta a gare mu...”
Maleekh ya gyaɗa kai da ladabi, zuciyarsa cike da tunani mai zurfi...
Maleekh ya dawo gida da dare, fuskar sa cike da nutsuwa duk da zuciyarsa tana ɗauke da zafi. Ya shigo falon da sallama cikin ladabi.
Ammy tana zaune a kan kujera mai faɗi, tana jiran dawowarsa. Fuskar ta a ɗaure, ta ɗago kai ta kalleshi cikin tsananin fushi ta ce.
“Maleekh! Kaje asibiti ka yi hayaniya, ka rufe wa mutane ido, ka ɓata mana suna. To yanzu, a nan gidan, ka gaya min gaskiya. Wannan miskilar yarinyar Amal ce ta rufe maka ido har ka yi min tawaye?!”
Maleekh ya durƙusa a gabanta, ya dafa ƙafafunta cikin ladabi, yana kallonta da idanu masu cike da hawaye.
“Ammy… bana son ɓata miki rai. Uwa ke ce ginshiƙina, ina girmamaki sama da komai. Amma wallahi Ammy, akan batun Farha, ina roƙonki ki fahimce ni. Bazan iya aurenta ba.”
Ammy ta fizgi ƙafarta daga hannunsa cikin bacin rai
tana ɗaga murya ta ce
“Ka yi mun shiru! Kai ɗana ne, kuma kai ne farin cikina. Amma idan ka yi tawaye a kaina, kai da kanka zaka yi asarar wannan uwar takan. Aure ne da Farha, kuma dole ne! Ka ji ni kuwa?!”
Maleekh ya haɗiye yawu, cikin ladabi ya ce
“Ammy, ki gafarta mun. Ni ɗanki ne tabbas, ban isa in yi musayar yawu dake ba. Amma ki duba gaskiya da adalci, ki duba irin halayen Farha. Kin ga abinda ya faru a asibiti, kin ji da kanki likita ya ce tana shaye-shaye. Ina jin tsoron aure da mace irin wannan, Ammy. Wannan ba ƙiyayya ba ce, gaskiya ce.”
Ammy ta yi shiru na ɗan lokaci, zuciyarta na tafasa. Sai ta juya ido gefe, tana jin kalamansa amma ta ƙi sassauta wa, ta ce
“Ko shaye-shaye take, ni ce na ɗora ta a kanka. Kuma ni mahaifiyarka ce. Idan kana son ka nuna kana mun biyayya, to ka ɗauke ta da halinta. Idan ba haka ba… to ka sani, bana goyon bayanka akan Amal!”
Maleekh ya lumshe ido, zuciyarsa na tsananin girgiza. Ya share hawayen da ya taru a idanunsa.
“Ammy, zan yi biyayya a kanki akan duk wani abu. Zan baki girmanki da darajarki. Amma akan wannan aure… zan yi addu’a Allah ya sa ki fahimce ni. Bazan iya ɗaukar Farha a matsayin mata ba. Ki yi hakuri.”
Ya durƙusa har kasa, ya gaisheta da kyau sannan ya miƙe cikin nutsuwa ya fice daga falon, zuciyarsa cike da nauyin kalmomin ta, kai tsaye part ɗinsa ya wuce..
Hospital – ɗakin da Farha take..
Washegari
Ammy ta dawo hospital, ta shigo ɗakin da Farha take kwance, ta barta da Arfat ne akan ta taya ta kwana, bayan sun gaishe da Ammy, Ammy zama tayi a kujerar gefen gadon tana ɗauke da saƙon da zai girgiza zuciyar Farha....
Farha ta zaro ido tana jiran jin abinda Maleekh ya ce.
Farha da rawar murya ta ce
“Ammy… Yaya Maleekh fa? Yanzu ya yarda da aurenmu ko?”
Ammy ta zauna kusa da gadon, ta dafa hannunta tana sauƙe numfashi ta ce
“Farha, ki kwantar da hankalinki. Na yi magana da Maleekh. Yana girmama ni sosai, amma… akan aure… sai dai na ce miki, ya ƙi.”
Farha ta zaro ido, zuciyarta ta buga da ƙarfi.
Ta ce
“Ya ƙi?! Ammy kina gaya min da bakinki cewa shi da kansa ya ce ba zai aure ni ba?! To wai ni waye zan Aura idan ba Maleekh ba? Me yasa ya raina ni haka bayan duk irin ƙoƙarin da nayi?!”
Ta fashe da kuka tana bugun ƙirji, tana murɗa hannayenta.
Ammy cikin lallashi ta ce
“Ki natsu Farha. Na rantse, zan tilasta masa. Aure ba fashi. Kin ji na rantse. Maleekh ɗana ne, bai isa ya ƙi mun biyayya ba. Ki daina kuka.”
Farha cike da tsananin fushi ta ce
“Ammy ki saurara! Idan Maleekh ya ci gaba da bijirewa, sai na ɗauki fansa akan shi da waccan matsiyaciyar yarinyar Amal! Wallahi sai na nuna musu babu wanda zai yi min wulakanci a duniya!”
Ta share hawayenta da hannun rigarta, idanuwanta suka canza launi kamar wacce take cikin hauka, tana ta huci da kishi da tsanar Amal...
Ammy ta ɗan ja da baya tana kallonta da mamaki, zuciyarta na tunanin “Ko dai shaye-shayen nan ya fara shafar kwakwalwarta?”
Arfat itama bakin ƙofa taje ta tsaya ganin yanda Farha take wani irin huci kamar mayunwacin kare...
NEXT NEXT NEXT....
asmeetahwriter✍️