Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
su ya kalli Amal cikin tsattsauran ido yace:
“Ke ce kika yi wannan laifin?”
Amal ta ɗora hannaye a kai tana kuka tana girgiza kai:
“Wallahi ba ni na kashe ta ba… ni ma ban san ta faɗi haka ba. Na shiga uku, Allah ya sani ban yi niyyar kashe ta ba…”
Inna da sauri ta durƙusa tana roƙon ƴan sandan:
“Don Allah kuyi hak’uri, ku barta, komai ne ya faru dai matsala ce ta afku, kar ku ɗauki ƴar matashiyar yarinya ku jefa ta cikin kurkuku…”
Ammy ce ta miƙe tsaye cike da haushi, fuska a ɗaure, tana kallon Amal ta wutsiryar ido tana huci tace:
“Wallahi ba zan lamunta ba. Wannan matsiyaciyar yarinya ba zata kashe min ɗiya ba ta ce zata tsira. Sai dai ku kama ta, ku tafi da ita yanzu! Ni da kaina zan tabbatar ta ɗanɗani ɗaci irin wanda ta jefa ni a yanzu.”
Ƴan sandan suka yi wa Amal dirar mikiya, suka kama hannunta da ƙarfi.
Amal ta fashe da kuka mai ban tausayi, tana faɗin:
“Don Allah ku yi hak’uri, ban kashe ta ba. Ku tambayi Allah! Ku tambayi zuciyar ku. Na shiga uku, ni Amal, babu kokai a wannan rayuwar sai sharri?!”
Ammy ta ƙara tunkarar ta da magana marar daɗi, tana harara tana faɗin:
“Ke matsiyaciya! Kina tunanin Maleekh zai aureki? To idan mafarki kike ki tashi kiyi sadaka, domin bazan taɓa aurawa yarona tsiya ba....kina burin zama matarsa ko? Sai dai ki lalace a kurkuku wallahi...”
Ƙirjinta ya buga, zuciyarta ta narke da baƙin ciki. Amma saboda tsoron abin da zai biyo baya, Amal tayi shiru da sauran ƴan gidan. Jigum-jigum suke kallon yadda ƴan sandan ke jan Amal kamar wata barauniya.
Hankalin Amal ya ƙara tashi ganin suna shirin ficewa da ita. Ta zube a ƙasa tana roƙo cikin kuka:
“Don Allah kuyi hak’uri, ku kyaleni, ba ni na kashe ta ba… wallahi ba ni ba ce!”
Sai dai Ammy ta ɗaga hannu ta tsawatar musu da cewa:
“Ku ɗauke ta! Sai ta ɗanɗani ɗakin kurkuku, sai ta gane shiga rayuwarmu ba abu ne mai sauƙi ba...”
Ƴan sandan suka ja Amal suka nufi ƙofar fita da ita, kukan Amal yana cika ko'ina, idonta cike da hawaye, zuciyarta cike da tsoro da baƙin cikin zargi…
Inna zama tayi tare da fashewa da kuka...
Maleekh yana nan a ɗakinsa, yana zaune a gefen gado, idonsa jajur saboda kwanaki yaƙi bacci. Zuciyarsa cike da ɓacin rai da ruɗani, bai san meke faruwa ba a waje. Kamar kullum sai juyi yake yi a kan gado, yana tunanin yanda zai kuɓuta daga wannan kulle da Farha ta tsare shi. Bai ma san cewa a wannan daren rayuwar Amal za ta sauya ba.
A can waje kuwa, ƴan sanda sun ja Amal kamar wata 6arauniya, kuka take tsaye tana roƙo amma babu mai sauraro. A cikin mota suka sata, suka kaita police station, suna isa suka jefa ta cikin cell mai ƙunci da wari, tare da wasu mata masu laifuffuka daban-daban. Hawaye ke zuba mata ba tare da tsayawa ba, zuciyarta na tsinke-tsinke da baƙin ciki.
Amal ta kwana daren nan cikin kuka, cikin tsananin tsoro da fargaba. Bata taɓa tunanin rayuwa zata jefa ta irin haka ba. Tana zaune a tsugunne, hannayenta riƙe da ƙafafunta, idonta a rufe, zuciyarta cike da addu’a:
“Ya Allah! Ka tsare ni daga sharri. Ka kawo gaskiya fili. Ka tabbatar da cewa ban taɓa kisan kai ba, Allah kai ka san ni marainiya ce. Kada ka bar ni a wulakance a duniya.”
A gefe guda kuma, Farha wacce ta fara motsawa daga sumar da ta kwashe lokaci mai tsawo, sai ranta a ɗaure da ciwo da wani irin kasala. Numfashinta na fita a wahalce, idanunta a lumshe, jikinta kamar wanda ya sha miyagun ƙwayoyi.
Ammy na tsaye a kanta tana kuka tana girgiza ta:
“Farhata, ki buɗe idonki, ki dubeni. Don Allah kar ki barni, idan kika mutu me zance wa iyayenki?!”
Sai da ta ji Farha ta motsa da ƙyar ta ɗaga hannu, ta sake faɗowa gefe kamar zata sake suma. Da gaggawa Ammy ta ƙira direba, ta ɗauke ta da hannunta ta saka ta cikin mota.
“Hospital za mu nufa yanzu! Na rantse sai wannan yarinyar Amal ta biya kuɗin halin da Farha ta shiga,” ta faɗa tana kuka tana riƙe da hannun Farha...
Motar ta nufo babban titi da gudu, yayin da zuciyar Ammy take huci da haushin Amal. Ita kuwa Farha sai sauƙe numfashi take yi kamar wacce take kan shan wahala mai tsanani.
A haka suka nufi asibiti, yayinda Amal kuwa ta kwana cikin ƙunci a ɗakin kulle na ƴan sanda…
Washegari gari na wayewa, ƙarar ƴan ƙiran sallah daga masallatai daban-daban ke ratsa kunnuwan mutane. Amma Amal ta buɗe idanu a cikin ɗakin kulle, babu wani hasken rana face ɗan ƙaramin wutar lantarki mai walƙiya a sama.
Tana juyi a ƙasa, ƙasa mai sanyi ga duhu da wari, duk jikinta ya kankame saboda sanyi. Idonta ya kumbura saboda kuka, zuciyarta cike da tsoro da damuwa.
Ƴan sanda biyu suka shigo suna mata ihu a kai.
“Ke! Tashi ki fito..."
Amal tayi tsitt kamar bada ita ake ba sai rawar sanyi take..
Ɗaya ne ya sake daka mata tsawa..
"Ki fito mana! Kin yi shiru kamar gawa.”
Amal ta ɗago a tsorace, ta daidaita kanta. Aka ja ta zuwa ofishin DPO, inda aka fara yi mata tambayoyi cikin tsawa:
“Wacece ke? Me kika yiwa Farha? Kin bada guba ta sha, sannan kin shaƙe ta, har ta faɗi. Shin kisan mai kike shirin yi ne?”
Hawayen Amal suka zubo tana cewa:
“Wallahi ban bata komai ba. Gaskiya nake faɗi, mun yi faɗa ne kawai saboda ta zo gidana ta ci mun mutunci. Ni ban san tasha wani abu ba. Don Allah kuyi adalci.”
Ƴan sandan suka kalli juna suna dariyar rainin wayo:
“Ke yarinya, kin yi laifi kin kawo kanki. Idan ba kin sami wanda zai tsaya miki ba, za ki cigaba da kwana a nan. Kuma idan aka tabbatar ta mutu, to lallai kin shiga uku.”
Amal ta fashe da kuka, zuciyarta na karyewa...
Sannan aka maida ta cikin cell..
A gefe guda kuma, Maleekh yana zaune a ɗakinsa a kulle, fuskar sa cike da gajiya. Yana zaune a bakin gado, hannunsa na tallafe da kansa, yana tunanin:
“Me yasa Mom za ta ɗaure ni haka? Wani hali Amal ke ciki yanzu? Shin tana lafiya? Ko kuwa ta ɗauka na watsar da ita ne?”
Ya ɗago yana kallon saman ceiling, zuciyarsa na wani irin bugawa da tashin hankali. Ya tuna da wayarsa da aka kwace masa...
“Idan dai suna ƙiran wayata, to nasan zasu yi tunanin na gudu ko na guje su. Ya Allah! Ka fito da ni daga wannan halin.”
Ya miƙe a tsorace, ya ɗauki kwalbar ruwa ya sha sannan ya nufi bathroom, ya ɗauroalwala. A cikin ɗakinsa ya tsaya ya tayar da sallah...
Bayan ya idar da sallah.
Idonsa ya rufe yana jin wani irin zafi a zuciya, zuciyarsa ta cika da tsanar Farha..
Maleekh yana zaune a daddumar sa, sai yaji budar ƙofar ɗakin sa, a zabure ya miƙe tare da nufan falonsa da gudu,
Islam ya gani a tsaye da key a hannunta...
Haka yayo kanta kamar zai rufe ta da duka..
Islam a tsorace ta ce "Yaya ka tsaya kaji.."
Maleekh yana tambaya "waya rufe ni? Meyasa aka rufe ni har tsawon sati uku?.."
Islam ta ce
"Yaya Wallahi Aunty Farha ce ta kulle ka, sannan ta hana kowa zuwa yanda kake, ita take ɓoye da key ɗin ka sannan wayarka ma a hannunta yake....yanzu ma tin jiya da safe Aunty Farha ta fita bata dawo ba, har dare Ammy ta fita neman ta, nayi waya da Ammy da safen nan take sanar mun wai suna hospital, Farha bata cikin hayyacinta sakamakon shaƙar da Amal tayi mata a gidanta, yanzu haka Amal tana police station a kulle..."
Maleekh jin haka hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba, jin Amal tana police station, cikin fushi yake cewa
"Tin da Farha tayi mun wannan danyen aiki sai na wulakantata, ko tana gadon asibiti sai naci mutuncinta, har tana da kwarin gwiwar rufe ni a ɗaki har tsawon kwanaki? Sannan meya kaita gidan Amal?..."
Islam ta ce "wallahi ban sani ba Yaya, yanzu ma ɗakin ta naje na dubo yanda ta ɓoye key ɗin ɗakin ka, nazo na buɗe maka, kasan ina kaunarka Yayana..."
Maleekh ya rungumi Islam yana jin daɗin yanda jininsu yazo ɗaya da ƙanwarsa Islam...Yana ji da ita sosai sa6anin Arfat marar kunya...
Maleekh ko tsaya gyara kansa baiyi ba ya fita...
Yana fita harabar gidan ya nufi wurin parker motoci, ya shiga motarsa sabuwar Mercedes-Benz CLE 450 4MATIC Coupé mai sheƙi, wanda ko a Abuja da Lagos ba a cika ganinsa ba. Duk da yana cikin tashin hankali bai tsaya gyara kansa ba, ko kallon gilashin motar.
Zuciyarsa na tafasa kamar wuta, yana maimaita a zuciyarsa:
“Amal a kulle? Kuma saboda wannan wautar da Farha tayi? Wallahi sai ta gane ni ba yaro bane.”
Kai tsaye ya nufi gidan Amal, ba tare da tsayawa ko’ina ba. Yana tafe da gudu, yana jin kamar hanya ta yi masa kaɗan saboda tsananin fushinsa.
Da isarsa gidan Amal, bai tsaya daƙile hayaniyar zuciyarsa ba, ya sauƙa daga motar da sauri, ya nufi ƙofar gidan...
Knocking yake da ƙarfi, mai gadi yana tambaya amma Maleekh bai tsaya bashi amsa ba, ganin buga get ɗin yaƙi ƙarewa ne yasa Mai gadin buɗe wa, yana buɗe get Maleekh ya hankad'a shi tare da shige wa...
A falo ya tarar da Inna zaune sai hawaye take tayi, Maleekh ne ya rarrashe ta tare da tambayarta "shin wani police station aka kaita?.."
Inna cikin kuka tace
"Ni ina zan sa ni..."
Sai da ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta shigo ta sanar masa..
Maleekh bai tsaya jiran komai ba ya miƙe tare da fice wa...
A gefe guda kuwa, Amal tana cikin azabar duka a hannun wata ‘yar sanda mace. Ta na ƙoƙarin kare kanta da kuka da magiya, amma taurin zuciyar wacce ke dukan nata ya fi ƙarfin tausayawa. Kowane dukan sanda yana ratsar da ita yana kuma hura mata ƙarin zafi. Duk abin da suke nema daga gareta shi ne ta faɗi cewa wani abu ta ba Farha tasha domin ta mutu.
Amal tana kuka cikin wahala tana cewa:
“Wallahi ban ba ta komai ba! Na rantse da Allah, babu wani abu a hannuna. Don Allah ku yi adalci!”
Amma babu wanda ya saurareta.
Sai dai a lokacin, ƙarar motar Maleekh da ya tsaya a gaban police station ɗin ya jawo hankalin kowa, ciki har da wacce ke dukan Amal...
Da ƙarfi Maleekh ya tura ƙofar police station ɗin ya shiga, zuciyarsa a hargitse, fuskarsa cike da bacin rai.
Ƙarar takalminsa da ke ƙaraso wa da gudu-gudu ta sanya jami’an da ke tsaye kallon sa, wasu daga cikinsu ma suka ɗan ja da baya ganin irin hankoron da ya shigo da shi.
Da sauri idanunsa suka sauƙa kan Amal da ke cell, jikinta ya kumbura, hancinta yana zubar da jini. Wata ‘yar sanda mace na tsaye da sanda a hannunta, alamar ba ta kammala dukanta ba..
A zabure Maleekh ya nufe ta yana huci kamar zaki, da sauri ya fisge sandar hannunta ya wurgar gefe, yana ɗaga muryarsa:
“Ke wacce irin rashin imani kike yi ne? Wace ƙa’ida ce ta ce ku ci zarafin mace a hannunku? saboda Amal ce shiyasa kuka yi mata haka?”
‘Yar sandar ta ja da baya tana rawar jiki, amma kafin ta ce komai, Maleekh ya wuce wurin Amal. Ya zauna a gefenta, zuciyarsa na tsananta da tausayinta.
Ya kamo hannunta cikin tausayi, idonsa cike da hawaye da fushi lokaci ɗaya:
“Amal… me suka yi miki haka? duk saboda ni kika shiga wannan hali? Ki kalle ni, wallahi duk abinda ya same ki Farha ce ta jawo amma zanyi maganinta..!”
Amal ta ɗago da ƙyar, muryarta a raunane, idanunta sun kumbura da hawaye ta ce
“Maleekh… wallahi ban aikata komai ba… suna zargina da wani abu… amma na rantse da Allah ban ba Farha komai ba.”
Maleekh ya ɗaga kansa ya kalli jami’an da ke tsaye da ƙarfi, muryarsa na girgiza ɗakin ya ce
“Duk wanda ya sa hannu aka ci zarafin ta, sai na sa a bincike shi! Wallahi sai kun gane illar zubar da mutuncinta da ku ka yi...”
Yayin da yake magana, manyan jami’an station ɗin suka fito daga ofis ɗin su saboda hayaniyar. Gani Maleekh yasa ɗaya daga cikinsu ya ce cikin ladabi:
“Sir Maleekh, kayi haƙuri. Wata matsala ce ta biyo baya, amma za mu warware komai yanzu…”
Maleekh ya miƙe tsaye, yana huci, ya dube su da idanun da suka cika da fushi:
“Ba ku isa ku ci zarafin ta ba! Da izinin wa kuka yi haka? Amal zata fita tare da ni yanzu, kuma sai na san duk wanda ya bayar da umarnin a daketa.”
Ya juya ya dubi Amal, ya kama hannunta da tausayi yana cewa:
“Tashi mu tafi, Amal. Wannan wulakanci ba zai sake faruwa ba.”
Duk jami’an suka shiga rikicewa, wasu suna ƙoƙarin kwantar da hayaniyar domin sun san halinsa idan yaga ba daidai ba zai iya sawa a cire su a aikin, duk station kowa ya san Maleekh ya shigo, kuma an karya masa zuciya saboda abinda aka yi wa Amal...
Police station ɗin ya ɗauki shiru, sai kukan zuciya da Amal ke yi a raunane, tana zaune kamar marar ƙarfi.
Dukkan jami’an da suka taru suna sunkuyar da kai suna ba da haƙuri. Wani babban officer ma ya matso da ladabi yana faɗin:
“Sir Maleekh, wallahi ba mu yi haka da kanmu ba. Hajiyarku ce ta bayar da umarnin a hukuntata… mu dai umarnin ta muka bi…”
Maleekh ya ɗaga hannunsa ya dakatar da shi, idonsa jajir cikin fushi, ya ce da ƙarfi:
“Ba ni zaku bawa haƙuri ba! A Amal za ku bada haƙuri! Ita kuka wulaƙanta, ita kuka ci zarafi! Ku tsaya ku nemi afuwarta…”
Nan da nan suka ƙarasa wurin Amal ɗaya bayan ɗaya, suna ƙoƙarin lallashinta cikin ladabi:
“Ki yafe mana Hajiya, wallahi ba mu san ƙarya akayi miki ba…”
“Ki yi haƙuri, hakan ba zai sake faruwa ba.”
Amal kuwa hawaye kawai take zubarwa tana jin ɗacin abinda aka yi mata.
Maleekh ya kalli jami’an, muryarsa ta sake yin nauyi:
“Ku sani, daga yau, ba wanda ya isa ya ɗaga mata yatsa a gabana. Ita ce matar da zan aura, kuma duk wanda ya kuskura ya sake tabata… sai na nuna masa babu wanda ya isa ya tauye mata daraja a wannan ƙasa.”
Kowa ya sunkuyar da kai..
Da haka Maleekh ya kamo hannun Amal, ya taimaka mata ta miƙe da ƙyar, sannan ya ja ta har zuwa motarsa. Ya buɗe mata ƙofa da kansa ya tabbatar ta shiga, sai ya zagaya ya shiga driver’s seat.
Ya kunna motar, zuciyarsa na cike da fushi da tausayinta lokaci guda. Ba tare da ɓata lokaci ba ya nufi hospital domin a duba jikinta, ganin yanda bakinta da hancinta suka fashe suna ɗigar da jini...
Bayan sun isa hospital ɗin, motar Maleekh ta tsaya da ƙarfi har sai da mai gadin wurin ya zabura. Ba tare da ya tsaya ɓata lokaci ba ya fito ya buɗe ƙofar Amal, ya ɗaga ta kamar karamar yarinya ya shigar da ita cikin babban reception na hospital ɗin.
“Doctor! Doctor!!” Ya ƙwalla ƙira, muryarsa na ɗaukar hankalin kowa.
Ma’aikatan asibitin kamar ba su damu ba, suna ta dube-dube suna tambayar “card” da “payment” kafin su shiga aiki.
Wani doctor ya ƙaraso da nutsuwa, yana faɗin:
“Sir, please calm down, mu a nan muna bin order ne, dole sai an rubuta file kafin—”
“Ka tsaya nan!” Maleekh ya katse shi da ƙarfi, idonsa ya ɗan firgita shi.
“Kana ganin wannan yarinyar a wannan hali, baka da hankali ne, kace za a fara rubuce-rubuce kafin a taimaka mata? Wane irin rashin imani ne wannan?!”
Nurse ɗin dake gefe ta ce a hankali:
“Sir, rules ne, dole mu cike bayanai kafin—”
“Rules ɗin ku ku watsar dasu!” Maleekh ya ɗaga hannu yana nuna Amal da hannunsa yana jijjiga. “Idan wani abu ya same ta saboda sakarci da rashin gaggawar ku, wallahi sai na rufe muku wannan hospital ɗin gaba ɗaya! Kun san ni da kyau! Ba zan bari wani ya ƙara wulaƙanta ta ba!”
Dukan reception ɗin ya shiga ruɗewa, nurses da doctors suka fara ƙoƙarin haɗawa da sauri. Wani likita ya fito daga Emergency room, ya ga tashin hankalin, nan take ya umarci su:
“Quick! Take her inside, emergency ward now!”
Suka karɓi Amal daga hannun Maleekh a hankali suka ɗora ta kan gurneti. Duk da haka, Maleekh ya ci gaba da bin su har cikin hallway, yana rera musu magana da ƙarfi:
“Kada wani ya kuskura ya yi wasa da rayuwar Amal! Duk wani abu da take buƙata, ku kawo yanzu! Ku tuna, idan wani abu ya same ta… kai ne na farko zan hukunta!”
Doctors suka shiga yin gaggawa fiye da yadda suka saba, saboda kowa ya san irin tasirin Maleekh a ƙasar, babu wanda zai so ya shiga cikin fushinsa.
Maleekh bai tsaya sauraron kowa ba. Duk wata nurse da ta ce masa ya tsaya a waje sai ya ɗaga hannu yana tsawatarwa.
“Na ce bana son ji! Wannan hannunta zan riƙe har sai ta samu ƙarfin jiki! Ku dai kuyi aikin ku kawai!”
Nurse ɗin da ke kusa da shi ta girgiza kai, tana faɗin:
“Sir, please, ka tsaya a waje mana, ai ba manyan ciwuka bane—”
“Ki yi mun shiru anan!”
Maleekh ya dakatar da ita da murya mai cike da izza.
“Kin ce ba ciwo bane? To kina ganin wannan jinin da yake fita a hancinta da lebenta wasa ne? Wannan ita ce rayuwata! Ki shiga ki kula da ita kafin na maka ƙarar ki cewa kina sakarci da aikinki..!”
Likitan da yake tsaye ya kasa ɗaga kai ya kalle shi kawai, zuciyarsa na cewa:
“Ai wannan fa ƙaramin rauni ne, amma yana wani rikicewa kamar wacce tayi accident da ya tawarwatsa ta.”
Amal kuwa tana kwance tana ɗan motsa idanu.
Tana jin yadda Maleekh yake ƙara tada hankalin kowa a asibitin saboda ita. Duk da zafin da take ji a hancinta da lebenta, dariya na ƙoƙarin ƙwace mata saboda irin yadda yake nuna tsantsar ƙauna...
Sai dai ita ta kasa furta komai, sai ta matse hannunsa wanda yake riƙe da nata.
“Amal,” ya faɗa cikin rawar murya, yana lumshe ido,
“wallahi babu wani da zai sake cutar da ke a gabana. Ko ƙwayar jini ɗaya naga ya zubo, sai na tabbatar da an biya mun kuɗin ta da rayuwarsa.”
Nurses suka kalli juna da murmushi marar sauti, ɗaya tana