Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
masa fushi saboda yadda yake ta nuna kulawa da barkwanci..
Bayan meeting
Zayd ya sake shigowa office ɗin Amal. Yana riƙe da wani ƙaramin gift box da aka nannade da ribbon.
“Pretty, this is for you. Ba komai bane, just a little something da na gani kuma na ji ya dace da ke. Ki buɗe ki gani.”
Amal ta girgiza kai tare da faɗin:
“Ba sai kayi wannan ba, ni ba na son ɗaukar kyauta haka.”
Zayd ya ce:
“C’mon, don Allah. Ba soyayya ba ce, appreciation ne kawai. Kin cancanci a yaba miki. Kowa yana cewa kina aiki sosai. Please ki karɓa.”
Ya saka ƙarfin halinsa ya sa box ɗin a kan tebur ɗinta. Amal ta kalle shi cikin tausayawa amma bata ce komai ba....
Ba yanda ta iya haka ta karɓi gift ɗin.
Shi kuwa bayan ya gama surutansa ya fice daga office dake lokacin tashi yayi....
_____________________________________☆
Part ɗin Maleekh, a daren yau..
Maleekh yana zaune yana nazarin files, amma zuciyarsa gaba ɗaya tana rikicewa. Zayd yana kwance a kan kujera ya gama waya da wani abokinsa dake London..
Ya dubi Maleekh cikin dariya ya ce:
“Bros, ai yanzu I’m in love, wallahi. Pretty ta fara sakin jiki dani a hankali, har na fara yi mata kyaututtuka. Na siyo mata wani ƙananan diamond pen today – ai da kanta zata gane Zayd ba mutum bane, prince ne.”..
Maleekh ya runtse idanu yana jin kamar zuciyarsa zata fashe. Bai ce komai ba, kawai ya riƙe biro yana danna shi da ƙarfi, sai kuma ya miƙe ya ce da ƙarfi cikin sanyin murya:
“Zayd, remember she is my assistant. Don’t cross limits.”
Zayd ya ɗaga hannayensa yana dariya tare da faɗin
“Hahahaha! Ai ba na crossing limits, bros. Ina dai bin hanyar soyayya ne kawai. Kuma ban taɓa yin soyayya da wadda ba ta cancanta ba.”
Maleekh ya juya ya bar ɗakin cikin takaici, zuciyarsa na ƙonewa, amma yana riƙe komai a silence...
☆☆☆☆☆☆
Ending weekend. Monday morning...
Amal ta shiga office ɗin Maleekh da files...
Bayan ta gaishe shi cikin ladabi ta ce:
“Sir, ga reports ɗin da aka nema. Na tabbatar da dukkan bayanai.”
Maleekh ya karɓa ba tare da ya duba files ɗin ba. Ya jingina da kujera yana kallonta da idanu masu zurfi. Amal ta saki hannunta tana jin bugun zuciya.
A sanyaye ya ce:
“Amal… kina jin daɗin wannan kyaututtukan da ake kawo miki kullum?”
Amal ta yi shiru, zuciyarta ta tsinke. Ta san yana magana ne akan Zayd.
Ta sauƙe kai sannan ta ce:
“Ni ba na buƙatar su… amma na kasa hana shi.”
Maleekh cikin taushin da ya haɗu da haushi ya ce:
“Kina iya hana shi, idan kina so.”
Ta ɗago idonta tana kallonsa kai tsaye, sannan ta ce:
“Kai kace bani da matsayi a zuciyarka. So why ka damu?”
Maganar ta bugi zuciyar Maleekh. Ya riƙe biro yana murɗawa da ƙarfi, kafin ya ce:
“Because… you’re still my assistant. Kuma ban yarda wani ya raina ni ta sanadiyyarki ba.”
Amal ta yi murmushi mai cike da baƙin ciki. Ta tattara takardunta ta fita ba tare da ta ce komai ba.
Maleekh ya biyo ta da kallo, zuciyarsa na ƙonewa da soyayya da kishi, amma yana riƙe komai a silence.
A rana ya ta yau ana gudanar da Big Event na campany..
An hallara a babban taro. Manyan baƙi da Ma'aikata sun hallaru, ana gabatar da company achievements. Amal tana tsaye a gefe cikin kyau da nutsuwa, da files a hannunta.
Zayd ya kasa ɗauke idonsa daga kanta. Kafin kowa ya ankara, sai kawai ya yi magana cikin fara’a:
Da ƙarfi, yana dariya ya ce:
“Ladies and gentlemen, allow me to appreciate someone special to me… my Pretty! Amal.”..
Duk aka juya a lokaci guda. Amal ta tsaya cak, zuciyarta ta tsaya, ganin abinda bata zata ba..
Zayd ya tsaya a gefenta tare da zagayo da hannunsa ta bayanta, ya jawo ta kusa da shi ya riƙe kunkuminta...
Zayd yana kallon jama’a ya ce:
“She’s so amazing, ba zan gaji da jin daɗin kasancewa kusa da ita ba.”
😳 REACTIONS
Maleekh: A inda yake zaune gaba ɗaya idonsa ya kaɗa ya yi jawur. Zuciyarsa na narke wa kamar wuta. Hannunsa ya matse glass cup da yake riƙe da shi har kusan tsage wa. Ya so ya miƙe ya tunkare su amma ya danne fushinsa, ya ci gaba da zama kamar dutse amma idanunsa suna sauƙa a hannun Zayd da yake kan kunkumin Amal...
Amal: Gabanta ya mungun faɗuwa, hannunta ya saki files suka kusa faɗuwa ƙasa. Idonta na kan Maleekh, zuciyarta ta yi sanyi gaba ɗaya. Bata iya magana ba, jikinta yana rawa.
Jama’a: Wasu suna dariya suna ganin kamar abin soyayya ne, wasu kuwa suna musayar kallon mamaki.
🌙 Bayan Event
Ana kammala taro, kowa ya watse. Amal ta yi saurin kwace kanta daga wajen Zayd.
Babu wata magana da ta yi, kawai ta tattara kanta cikin damuwa ta nufi motarta.
Zayd yana kiranta:
“Pretty wait! I can drop you home…”
Amal ta girgiza kai, cikin rawar murya ta ce:
“No thanks…”
Ta shiga motarta, zuciyarta na bugawa da tsoro da kunya, sannan ta bar wurin.
Daren nan, bayan sun dawo daga event ɗin. Maleekh ya shige cikin ɗakinsa ba tare da ya yi magana da kowa ba. Ya cire rigarsa ya zauna daga shi sai singlet, ya zauna tare da jingina da kujera, ya ɗauki glass na wine amma bai sha ba kawai yana wasa da shi ne...
Idonsa jajur, zuciyarsa na bugawa da sauri. Duk abinda ya faru a wurin yana dawowa masa a rai.
Haka yake magana da kansa, cikin ɓacin rai.
“Hannu… a kunkumin Amal? … Zayd ya isa ya riƙe ta haka a gaban idona? … Kuma ita ta tsaya kamar dutse tayi shiru? Amal fa!…”
Ya miƙe da sauri, ya daki bango da ƙarfi.
“Zayd… you bastard. Ka ɗauka zan bar maka ita? Never!”
Sai ya ja tsaki, ya shiga tafiya a ɗakin yana juya kansa. Yana ƙoƙarin lulluɓe zuciyarsa da cewa
“she’s just my assistant”, amma zuciyarsa na ƙaryata shi.
✨ Meanwhile Zayd
A gefe guda, Zayd yana ta waya da wani abokinsa yana dariya tare da faɗin:
“My friend, ka ga yadda na tsaya nake riƙe da wuyan ɗuwawun Amal kuwa? Gaba ɗaya jama’a suka tsaya kallon mu! She’s mine, ba wanda zai hanani…”
Yana dariya yana waya da abokinsa...
🌹 Amal
A gida kuwa, Amal ta zauna a gado tana riƙe da pillow. Idonta cike da hawaye, zuciyarta tana tunawa da yadda Maleekh ya kalleta.
Cikin rauni ta furta..
“Ya Allah, me yasa zuciyata bata iya ƙin Maleekh ba? Kuma yanzu Zayd ya fara nuna ni a bainar jama’a… ya zanyi?…”
NEXT NEXT NEXT
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 49 to 50
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Washegari da safe, suna cikin parlor suna breakfast. Zayd yana ta faman hira kamar kullum, shi kaɗai yake magana, Maleekh kuwa ba daɗi yake ji ba amma yana danne zuciyarsa.
Zayd yana ɗan dariya ya ce:
“Bros gaskiya wannan Amal ɗin… wow! Yarinyar na da class wallahi. Na kasa bacci jiya saboda ita. Yanzu kam dole ka tayani jan hankalinta… ko ka mata magana game dani.”
Maleekh ya ɗago kai da sauri, idonsa ya ɗan kaɗa.
Cikin nutsuwa da murya mai nauyi ya ce
“She’s my assistant, Zayd. Ba zan bari ta raina ni ba. Tunda tana ƙarƙashina, don’t cross the line.”
Zayd yana dariya, bai fahimci zurfin maganar ba ya ce
“Ohh bros… kai fa kullum serious! Ai ba wani abu bane. Assistant ɗinka ce, amma ba ka nuna min akwai wata alaka tsakaninku ba ko? Ni fa kawai ina son ta, kawai ka barni da ita.”
Maleekh ya ɗauki cup ɗinsa ya sha coffee a hankali, yana ƙoƙarin danne fushinsa. Amma zuciyarsa na tafarfasa.
Cikin siririyar murya, yana kallon ƙasa ya ce
“Zayd… don’t try to touch what you can’t handle. Karka shiga inda bai kamata ba…”
Sai ya miƙe daga kujerar, ya nufi stairs ya bar Zayd a wurin.
Zayd kuwa ya biyo shi da ido, yana murmushi, yana magana da kansa.
“Bros fa ya ɗauka wasa nake ko? To wallahi wannan Amal kam dole sai na mallaketa. Zayd baya rasa abu…”
A Campany
Amal tana office ɗinta tana typing report da aka barta ta kammala. Cikin natsuwa take, tana ƙoƙarin mantawa da abin da ya faru jiya.
Sai ga knocking.
Ba tare da ta ɗago ba ta ce:
“Come in…”
Zayd ya shigo cikin shigar suit mai kyau, yana ɗauke da ƙaramar box mai kyau da ribbon a jikinsa.
Yana murmushi sosai ya ce:
“Pretty, na san kina da aiki sosai… amma na ce yau zan kawo miki little something… just for you.”
Ya ajiye gift ɗin a kan desk ɗinta. Amal ta ɗago da mamaki ta ce.
“Gift? For me?… But why?”
Zayd ya ce:
“Because you deserve it. Kullum kina aiki, kina supporting bros, kuma honestly… na kasa samun kwanciyar hankali in ba na nishaɗi da ke.”
Amal ta tsaya tana kallonsa, ba ta ce komai ba. Sai ta juyo da box ɗin a hankali ta buɗe…
Cikin box ɗin ƙaramar zinariya necklace mai kyau sosai, da wata karamar gold bracelet.
Idanun Amal suka canza da mamaki, a hankali ta furta.
“Zayd… this is too much. I can’t accept this.”
Zayd yana matsawa kusa da ita tare da faɗin
“Why not? Ni fa ba na yi miki komai face because you’re special. Ko ki sa yanzu na gani…”
Yana kai hannu zai ɗauki necklace ɗin. Amal ta ja baya da sauri, zuciyarta tana bugawa ta ce:
“Please, don’t. I appreciate it, but I don’t think I can…”
A lokacin ƙarar buɗe ƙofa ta cika office ɗin.
Maleekh ya shigo cikin nutsuwa idanunsa suka sauƙa kai tsaye kan Zayd da Amal, da kuma necklace ɗin da ke kan desk.
Zuciyarsa ta yi wani irin nauyi. Ya tsaya kallon su seconds kaɗan, sannan ya ce cikin sanyin murya amma mai cike da ƙarfi:
“What’s going on here?”
Amal ta tsure gaba ɗaya. Zayd kuwa ya kalli Maleekh yana murmushi, kamar bai damu ba, ya ce.
“Bros… ai ba komai. Just showing appreciation to your hard-working assistant. Ka ga necklace ɗin nan? Perfect for her ko?”
Maleekh bai ce komai ba sai ya juyo ya kalli Amal. Idonsa ya nuna alamun ƙunci da ƙona zuciya, amma sai ya danne ya ce:
“Amal… we need to talk. Now.”
Ya juya ya fice daga office ɗin.
Amal ta tsaya kallon Zayd cikin tashin hankali, zuciyarta na bugawa da sauri..
Zayd yana murmushi yana jingine da kujera ya ce.
“Don’t worry pretty… bros ɗinai yana da girman kai kawai. Ni da ke ne fa future…”
Amal ta gyara gyalenta da sauri ta bi bayan Maleekh, zuciyarta cike da fargaba.
Ta bi bayan Maleekh zuwa part ɗinsa na office. Hannunta har rawa yake yi, zuciyarta na tsalle-tsalle saboda yadda ta ga irin kallon da yake mata a cikin taron...
Da ta shiga, ta ganshi tsaye a gaban desk ɗinsa, hannuwansa a riƙe da gefen desk ɗin kamar yana ƙoƙarin danne wani bacin rai da ya kasa sarrafawa.
Amal a hankali, tana shigowa ta ce:
“Sir… ka ce kana buƙatar magana da ni?”
Da sauri ya juyo, idanunsa jawur, numfashinsa yana fita da sauri. Kafin ta iya wani motsi ya ƙarasa wurinta da sauri, ya riƙo damtsenta da ƙarfi, ya mannata da bango. Shi ma ya kwanto kanta da hannunsa guda, suna kallon fuskar juna, numfashinsu na haɗuwa.
Maleekh cikin ƙasa-ƙasan murya, mai cike da ƙarfi ya ce:
“I hate you, Amal… I hate the way you make me feel. I hate the way you let him touch you, call you names, gift you…!”
Yana zazzaro ido cikin tsananin bacin rai da kishi.
Amal ta ƙurawa idanunsa ido, jikinta har rawa yake, amma sai ta tattara ƙarfin guiwa ta ce:
“Tin da kai ka zaɓi ka bar ni, ka tura ni gefe… ka bari wani ya samu damar kusanto ni. Ka ce baka buƙatar soyayyata. To yanzu… idan akwai wani da yake so na da gaske, me zai hana na ba shi zuciyata?”
Maleekh ya matso kusa sosai, hancinsu kusan ya haɗu. Idonsa ya ƙafe cikin nata, zuciyarsa na bugawa da karfi.
Cikin rawar murya ya ce:
“Don’t you dare… don’t even think of it, Amal. Karki kuskura ki bari wani ya shige wurin da ni kaɗai nake da shi a zuciyarki…”
Amal ta runtse idonta, hawaye suka taru a gefen idon ta ce:
“Wannan wurin da kake faɗi… kai ne ka yashe shi. Kai ne ka ƙi kallo na lokacin da nake jiran ka. Ka ce bana da daraja a gurinka… yanzu kake nuna kishi?”
Maleekh ya ɗan saki hannunta, amma bai bari ta motsa ba. Ya ɗaga hannunta da ya riƙe cikin fushi, ya ce:
“I hate myself… saboda na bar ki. I hate myself saboda na bari wani ya ƙira ki ‘pretty’. But Amal… wallahi duk da na faɗi cewa bana sonki, amma ban daina son ki ba. Ban daina buƙatarki ba.”
Amal ta girgiza kai da sauri, tana ƙoƙarin janye jikinta amma idonta ya kasa barin nasa.... Cikin rawar murya ta ce:
“Stop it, Maleekh… ka riga da ka yanke hukunci. Ka bar ni in rayu da zafin rabuwa. Idan ka ce baka sona, to ka bar ni in nemo farin ciki na a wani wuri.”
Ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, sannan ya buɗe su da wani irin yanayi cike da kishi, sha’awa, da tsananin soyayya. Hannunsa ya sauƙe daga bangon zuwa kuncinta, yana shafa fuskarta cikin raunin zuciya.
A hankali, kamar yana furta wani sirri ya ce:
“You’re mine, Amal… whether you like it or not. Ko da zan ƙone da kishin Zayd, ko da na tsani kaina, amma bazan yarda na rasa ki ba…”
Amal tana hawaye, tare da lumshe eyes ɗinta..
Numfashinsu na ci gaba da haɗuwa, ɗakin ya cika da wani irin zafi da ba su iya magancewa.
Numfashinsu na ci gaba da haɗuwa a hankali, bugun zuciyarsu yana ƙaruwa kamar kiɗa. Maleekh ya sauƙe hannunsa zuwa kuncin ta yana shafawa. Hannunsa na rawa..
Ya yi wani irin tsaki a ƙasin harshensa, ya ce cikin rawar murya:
“Amal… kin sani… na daɗe ban yi kewarki irin yanzu ba.…”
Idanunta sun cika da hawaye, amma ta kasa magana. Sai dai ta tsaya kallonsa, jikinta har rawa yake.
Ya lumshe idonsa, ya ɗan jingina goshinsa da nata. Hancin su ya haɗu, numfashinsu ya haɗu. Wani irin zafi ya ratsa su duka biyun.
Amal ta ji hannunsa ya sauƙe a wuyanta yana shafa mata a hankali. Shi kuwa ya kasa danne kansa. A hankali ya ɗaga fuskarta, ya ƙura mata ido, idanunsa suna magana da duk abinda zuciyarsa ta kasa faɗi.
Ya ɗan matsar da bakinsa kamar zai ce wani sirri a kunnenta, amma murya ta makale. Amal ta runtse idonta tana girgiza kai..ba tare da ta furta komai ba...
A hankali ta ji numfashinsa yana ratsawa a fuskarta. Ya ce cikin wata murya mai rauni:
“Na rasa tunanin da zan yi… Na rasa yadda zan ce miki…”
Sannan ya matso da fuska sosai, lips ɗinsu suka yi karo da juna a wani irin shiru mai cike da zafi, suka yi lips touch na tsawon lokaci da aka yi missing juna. Amal ta kasa jurewa ta buɗe idonta, lokaci guda ta rufe su ta sakar da wani irin numfashi mai taushi...
Sun tsaya haka na ‘yan dakiku suna jin numfashin juna, hannayensa a gefen fuskarta, nata hannayen a kirjinsa. Wani irin kewar juna ya lulluɓe su gaba ɗaya...
Sai daga baya Amal ta ja numfashi ta janye jikinta ta koma gefe a hankali, idonta a ƙasa, hawaye suna gangarowa. Maleekh kuwa ya sauƙe hannayensa, ya juyo gefe, zuciyarsa na bugawa kamar zata fashe...
A hankali cikin rawar murya ta ce:
"Ni zan tafi ..."
Ba tare da ya bata amsa ba ya ƙara tako wa yanda ta ke. Yasa hannu yana ɗago da ha6arta..kallon juna suka yi daga bisani ya ƙara mannata a jikin bango...
Ya ce: "kina so ki je wancan yaron ya ci gaba da shiga jikinki?.."
Ya matseta sosai a bango, idanunsa suna tsiyayar da ƙiyayya da kishi, amma zuciyarsa ta cika da kewar da ya kasa ɓoye wa.
“Na tsane ki, Amal…!” ya furta cikin rawar murya, amma idanunsa sun bayyana akasin maganar.
Amal ta runtse idonta tana hawaye, zuciyarta tana karyewa. “Ka tsane ni… amma zuciyarka har yanzu tana kirana Maleekh. Idan ba haka ba, me yasa kake tsayawa kusa dani haka?..”
Shiru ya ratsa su. Numfashinsu ya haɗu, jikinsu ya haɗu.
A hankali hannunsa ya zame daga jikin bango zuwa fuskarta, ya ɗago haɓarta. Amal ta buɗe idonta ta kalle shi, su biyun suka tsaya kallon juna, idonsu na magana da ɗaruruwan kalmomi.
Sannan kamar wani abu ya rinjaye shi, Maleekh ya sauƙe ƙaramin bakinsa akan nata a hankali. Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar Amal, ta yi ƙoƙarin janye kanta amma ta kasa.
Ya fara soft, yana tsotsa a hankali kamar mai roƙon gafara. A hankali ta lumshe ido tana mayar masa da martani, sai sumbatar ta rikid'e zuwa mai zafi, kewar da suka daɗe suna dannewa ta fashe gaba ɗaya.
Hannayenta suna kan kirjinsa, jikinta a manne da jikinsa. Hannunsa ya koma bayanta yana rungumeta sosai, tamkar zai haɗiye ta gaba ɗaya.
Sun tsaya cikin doguwar sumbata mai ɗauke da soyayya, ciwo, da kewar juna. Duk wani ɓacin rai da zargi ya rikide zuwa zafi mai cike da soyayya.
Da ƙyar suka rabu da juna, dukansu sun kasa numfashi yadda ya kamata. Amal ta jingina kanta a kirjinsa tana sauƙe numfashi, shi kuma yana shafa kanta yana rarrashi zuciyarsa na bugu..
Numfashinsu ya ragu ya koma nauyi, kallo ɗaya suke iya yi wa juna.
Amal ta ɗago idonta, idanunta sun cika da hawaye. A hankali ta furta da murya mai rawa:
“Wannan… bai kamata ya faru ba, Maleekh.”
Ta zame jikinta da ƙarfi daga hannunsa, tana girgiza kai kamar wacce aka yi wa asiri. Hawaye suka cika a idanunta...
“Ka daina… kar ka ƙara kusantata haka,”