Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   39 / 82

114K to 117K   out of 244.2K words

ne, kuma rayuwarsa ba abar wasa ba ce."

Ammy ta fashe da kuka tana cewa:

"Kana gani ko? Kana gani fa? Wannan yarinya karuwa ce, ta zubar da ciki a club! Shin wannan ce kake so ta zama matar ɗanmu?.."

Abba ya daka mata tsawa cikin bacin rai ya ce:

"Shiru!! Ba ki da ikon yanke hukunci akan rayuwar ɗana. Ni ne uba, kuma na yarda da abin da zai zaɓa. Duk abinda ya so, shi ne za’ayi. Kuma wallahi, bana son sake jin ki da sunan karuwanci ko zubar da ciki a gaban ɗana! Idan kin kasa gane magana, zan tabbatar iyayenki sun koya miki darasi."

Tsofaffin iyayen Ammy wanda shigowarsu kenam, basu koma garin da suke ba suna jiran tashin Maleekh, jin tattaunawarsu yasa suka gyaɗa kai, suka ce da ita cikin tsawa:

"Ai ke kika ja wannan bala’in da rashin biyayya da bijirewa tunda kina yarinya. Ki ci gaba da ganin sakamakon dabi’arki yanzu."

Ammy ta saki kuka tana girgiza kai, amma babu wanda ya tausaya mata.

Maleekh a gefe yana sauraron wannan maganganu, hawaye na fita daga idonsa. Zuciyarsa ta ƙara rikicewa, ƙaunar Amal, tsanar Amal, da soyayyar iyayensa da kuma tsanar Farha duk sun gauraye cikin zuciyarsa.


A ɗakin, shiru ya mamaye bayan hayaniyar Ammy da iyayenta ta lafa. Kowa ya fita, aka bar Maleekh a kan gadonsa, da Farha a gefen gado tana kuka.

Farha ta tsuguna ƙasa, tana riƙe da hannayensa cikin rawar jiki. Idonta ya cicciko da hawaye, muryarta na rawa tace:

“Yaya Maleekh… wallahi ina matuƙar kaunarka. Ka sani ko? Shi ya sa kake ganin ina abubuwa marasa kyau. Ni ba wai saboda mugunta nake ba, kawai burina shi ne na mallake ka a matsayin mijina.”

Ta kalli fuskarsa, amma ba amsa. Sai ta ƙara fashewa da kuka mai ƙarfi:

“Amma tinda baka sona… shikenan. Ni ba zan tilasta kaina a gareka ba. Ka huta kawai, ka manta da ni.”

Ta saki hannuwansa ta rufe fuskarta a cikin tafin hannunta tana kuka sosai.

Maleekh ya juyo da kyar, idanunsa sun cika da hawaye, ya dube ta na ɗan lokaci. Sai zuciyarsa ta motsa da tausayin kalmarta. Wani abu ya shige shi, ƙaunar, soyayya duk ya watsar da su gaba ɗaya, amma jinin ɗan’uwantaka ya motsa...

Cikin rauni, muryarsa ƙasa ƙasa sosai, ya furta

“Farha… kin cancanci a so ki… amma ni… na haƙura da soyayya gaba ɗaya. Na haƙura da ita har abada. Ke, ko Amal… babu wanda zai sake samun zuciyata.”

Ya lumshe idonsa, hawaye suka zubo daga gefe yana ƙara cewa cikin rauni:

“Zan rayu ba tare da mace ba… tunda babu komai a soyayya sai ciwo kawai.”

Farha ta yi ƙara cikin kuka ta riƙe gadon, tana faɗin:

“Wayyo Allah naaa! Yaya Maleekh kada ka ce haka. Ni bazan iya jurewa ba.”

Ya rufe ido gaba ɗaya, bai sake magana ba..


Farha tana kuka tana jingina da gefen gadon, sai taga Maleekh ya rufe idonsa gaba ɗaya. Kafin ta sake magana sai ga ƙarar buɗe ƙofa.

Doctor ya shigo da file a hannunsa, yana takowa har kusa da gadon. Idonsa ya sauƙa kan Farha da ke tsugunne a ƙasa, sannan ya duba fuskar Maleekh da ke lumshe ido, hawaye na zuba masa a gefe.

Doctor ya ɗan tsaya yana nazari kafin ya yi magana da tausasawa da ƙarfi ya ce:

“Hajiya, kiyi hakuri, amma yanzu dole ne ki bar ɗakin. Yana cikin damuwa sosai. Idan kina ƙara saka shi cikin kuka ko tashin hankali, hakan na iya cutar da lafiyarsa fiye da jinyar da muke yi masa.”

Farha ta ɗago kai cikin kuka, ta dubi Doctor da idanunta jawur ta ce:

“Ni ba wai son tashin hankalinshi nake so ba Doctor… wallahi ni ina ƙoƙarin kwantar masa da hankali ne.”

Doctor ya girgiza kai cikin ladabi, ya ɗan sauƙe numfashi sannan yace:

“Na fahimta, amma yanzu ba wannan lokacin bane. Lafiyarsa tafi buƙatar kwanciyar hankali. Ki bari ki fita ki barshi ya huta. Zaki iya dawowa daga baya idan ya samu sauƙi.”

Sai ya matsa kusa da ita cikin tausayawa, yana nuna mata ƙofa da hannu.

Farha ta share hawayenta, zuciyarta na karyewa, ta dubi Maleekh da bai buɗe ido ba. Ta miƙe a hankali, tana jin jikinta ya yi nauyi, kafin ta fice daga ɗakin cike da ƙunci.

Doctor ya juya ya duba Maleekh, ya ɗan murmusa da tausayawa a gefen baki, yana rubuta wani abu a takarda.


☆☆☆

Amal ta shigo gida da hawayen da ta kasa dakatawa, duk jikinta yana rawa saboda nauyin damuwa da tashin hankali. Hannunta a rufe akan fuska da gyale, ta shige falo ba tare da ta wa Inna kallon kirki ba.

Inna tana zaune a kujerar falo, tana zare ido tana haɗa rai. Da sauri ta daga murya cikin yanayin tsawa:

“Can miki dai! Ki ƙarata sama ki zauna. Wawiya kawai! Kin tsaya kina rawar jiki saboda wani namiji da ya watsar dake? Taya kike tunanin Maliku zai sake kallonki bayan wannan abun kunyar da kika aikata? Kin tozarta kanki kin tozarta mu gaba ɗaya!”

Kalmar “tozarta” ta shiga kunne Amal kamar wuƙa, ta ƙara ratsa zuciyarta da raɗaɗi. Bata tsaya sauraren ƙarin magana ba, ta wuce da gudu zuwa sama.

Da ta shiga ɗaki, ta rufe ƙofa da ƙarfi, sannan ta faɗa akan gadonta. Ta dunƙule jikinta kamar ƙaramar yarinya, hawaye suna tsiyaya tamkar ruwan sama.

“Ya Allah… me yasa zuciyata ke son shi haka? Me yasa Maleekh ya zame min kamar rai na? Duk inda na juya, shi kawai nake gani…” ta furta cikin shessheƙar kuka.

Tsanannin kaunar Maleekh ya yi mata nauyi kamar dutse mai murƙushe zuciya. Zuciyarta na neman hallaka, jikinta gaba ɗaya na rawa da sanyi.

Ta matse pillow tana goge hawayen da basu daina zuba ba. Duk da kalaman Inna sun ɗora mata raɗaɗi, amma ƙaunar Maleekh ta mamaye duk wani tunani nata.

A zuciyarta, ta yi addu’a cikin rawar murya:

“Ya Allah, idan wannan soyayya zata zama abun da zai hallaka ni, ka bani ƙarfin zuciya in jure. Amma idan ƙaddara ce ta haɗa mu, to ka sauƙaƙa min… ka dawo min da shi…”


Darenta ya yi tsawo kamar shekara. Amal ta juya ta baya, ta juya ta gaba, amma idanunta sun ƙi rufuwa. Kallon ceiling ɗakin kawai take yi, amma abin da zuciyarta ke gani daban ne – fuskar Maleekh ce kawai a cikin idanunta.

Hawayen da suka gama bushewa sai suka sake sabunta. Duk lokacin da ta lumshe idanu, sai zuciyarta ta cika da muryarsa, yadda yake kiranta “Amal” cikin salo na musamman da babu wanda zai iya kwaikwayo.

Sai a hankali barci mai nauyin damuwa ya ɗauke ta.

A cikin mafarki ta tsinci kanta a cikin wani fili mai yalwa, duk wurin fari ne kamar ƙasar hazo. A can gaba kuwa, ta hangi Maleekh tsaye cikin farin kaya, yana mata murmushi irin na da.

Da gudu ta nufi wurinsa tana cewa:

“Ya Maleekh! Ka dawo gare ni, ka ce baza ka barni ba…”

Amma kafin ta kai shi, sai fili ya fara rikicewa. Maleekh ya fara ja da baya, kamar wani ƙarfin duhu ke jansa daga gareta.

“Amal… bazan iya zuwa gare ki ba… kin ci amanata…” muryarsa ta fito kamar wuƙa, tana yankan zuciyarta...

Amal ta durƙusa cikin kuka tana ƙiran sunansa, tana miƙa masa hannaye amma ya ƙi kamo su. Hazo ya lulluɓe shi gaba ɗaya, ya ɓace daga ganinta

“A’a! Maleekh, wallahi ban ci amanarka ba! Ka saurare ni, ka dawo! Don Allah ka dawo!”

A firgice ta farka daga barcin, tana tsalle daga gadon kamar wacce aka jefa a wuta. Kafafunta suna rawa, jikinta duk ya jike da zufa.

Ta dafe ƙirji tana kuka mai tsanani, zuciyarta kamar zata tarwatse.

“Wayyo Allah! Har mafarki ya koma azaba saboda Maleekh… Ni me nayi ne haka? Ina ruwana da wannan ƙaddara? Wayyo Allah …”

A daren, Amal bata sake iya rufe ido ba. Ta zauna tana kallo cikin duhun ɗakin, tana jin soyayyar Maleekh na hura mata wuta a ƙirji tamkar ana zuba gishiri cikin raunannen zuciyarta.


Washegari bayan sallar asuba, Amal ta zauna a kan sallaya, idanuwanta sun kumbura saboda kukan daren jiya. Kafin ta miƙe, wayarta ta fara ringing. Ta ɗauka cikin sanyin murya.

“Hello…”

Manager ya ce:

“Madam Amal, mun jiki shiru daga gare ki. Kema baki zo company ba. A matsayinki na assistant CEO, yanzu da oga Maleekh ba shi da lafiya, ya kamata ki tsaya ki wakilce shi. Ayyuka sun yi mana yawa sosai…”

Amal ta rufe idanunta tana jan numfashi mai nauyi. Kalaman sun bugi zuciyarta domin har yanzu tana cikin baƙin ciki, amma bata so ta nuna raunin ta..


Ta ce:
“Kar ku damu. Zan dawo aiki yau.”

Suka yi sallama, ta kashe wayar.

Ta shiga bathroom ta watsa ruwa, sannan ta sha kwalliya kamar wata sarauniya. Ta shafe fuskarta da makeup, ta sanya Atamfa riga da skirt da suka matse jikinta sosai, sun fito da surar jikinta. Ta sanya takalmi masu tudu a ƙafarta, ta ɗan yafa gyale a kafaɗa gefe guda, sannan ta ɗauki farin glass siriri ta ɗora a idonta. Sai ƙamshin turare masu sanyi da daɗi suka mamaye jikinta.

Ta ɗauki handbag da wayarta ta fito.

A falo ta tarar da Inna zaune. Ta yi mata sallama cikin ladabi, amma Inna ta kawar da kai kamar bata ji ba.

Ta kuma cewa:

“Ni zan tafi wurin aiki.”

Inna ta kalleta da ido mai cike da tsana ta ce:

“Ai idan kin ga dama ki wuce wurin club ɗin ma. Domin na tabbata nan ne wurin samarinki.”

Amal ta tsaya cak, sai murmushin da ta yi sannan cikin takaici ta ce:

*“Inna, idan har tunaninki bai gushe ba, gaya min. Da wa kika taɓa ganina tunda kike? Eh, gaya mun? Idan ciki ne ai Maleekh za a zarga, domin ban taɓa kula wani ba sai shi. To wallahi ya isheki, Inna.... Kuma shi Maleekh ɗin, idan akwai hukunci a kaina, ya rage nasa, tunda shi ya san gaskiyar Amal ɗinsa.”

Inna ta miƙe cikin masifa tana zaginta, itama Amal ta ƙara ƙarfafa murya cikin zafi ta ce:

“Inna, ko tsine mun kikayi, wallahi bazai kamfani ba. Domin ba ke kika haifeni ba. Mahaifina kika haifa, ba ni ba. Shi ya mutu balle… Ni jikarki ce, amma ba ƴarki ba!”

Kalmar ta girgiza Inna, ta tsaya tana haki tana kallonta da mamaki da fushi. Amal kuwa bata tsaya ba, ta juya cikin isa ta bar falon...

Tana fita ta shiga motarta kai tsaye ta nufi company, zuciyarta cike da haushin rayuwa amma ta daure ta sanya fuskar izza domin ta san yanzu dole ta tsaya ta kare matsayin da Maleekh ya bari a hannunta.

Motar Amal ta tsaya a bakin harabar CashTalk Empire. Security da receptionists suka yi saurin tashi da girmamawa, kowannensu na zuba mata ido. Sun ji tsoro da mamakin irin labarin da ya bazu akan Amal cewa ta zubar da ciki a gidan rawa. Amma babu wanda ya furta komai, saboda sun san matsayin ta: Assistant CEO.

Amal ta fito daga motarta a hankali, dogayen takalmin da ta saka na ɗaukar hankali. Gyalen da ta ɗora ya ɗan zame gefe yana ƙara fito da tsantsar kamalarta. Idanuwanta da farin glass ya lullube suka bada wani irin izza da basira.

Kowa da yake kallonta ya ɗan sunkuyar da kai, suna yin gaisuwa cikin ladabi.

Ma’aikata suka miƙa gaisuwa da cewa:

“Good morning, Madam Amal.”

Amal ta ɗan ɗaga hannu a hankali, muryarta a nutse ta ce:

“Morning.”

Ta wuce kai tsaye zuwa elevator, kafafuwanta na yin taka-tsantsan kamar sarauniya. Duk inda ta bi sai kallonta ake yi, amma babu wanda ya ƙara magana. Wasu ma’aikatan mata suka yi shiru suna bin ta da ido cike da hassada da kuma mamaki.

Bayan ta shiga office ɗinta, ta rufe ƙofar da ƙarfi ta jingina da ita. Ta runtse idanuwanta tana jan numfashi mai nauyi. Zuciyarta tana tuna zagin Inna, kalaman Ammy, da kuma yanda Maleekh ya nuna mata baya son ta. Sai dai ta girgiza kai, ta tafi ta zauna a kan kujerar executive chair mai juyawa.

A gabanta akwai takardun contracts, files masu yawa da suke jiran signature ɗin Maleekh. A hankali ta fara ɗauka ɗaya bayan ɗaya, tana nazari sosai.

Amal a cikin zuciyarta ta ce:

“Ba zan bari mutanen nan su raina ni ba saboda abinda suka ji. Ni Amal ce Assistant CEO. Kuma na san kowa a nan da yake aiki yana jiran ganin ikon da zan nuna.”

Ta ɗaga wayarta ta ƙira secretary.

Amal ta ce:

“Kawo min dukkan reports na kwana biyun nan da na yau. Ina son ganin komai kafin ƙarfe goma. Kuma ka sanar da managers ɗin departments su shigo da briefing yanzu.”

Secretary ya bada amsa da cewa:

“Yes, Madam.”

Bayan ‘yan mintoci kaɗan, manyan ma’aikata da managers suka shiga office ɗinta cikin ladabi. Sun tarar da ita zaune, ta cire glasses tana kallon files a gabanta.

Amal ta ɗago da idanu masu kaifi ta ce:

“Ku zauna. Ina so in ji matsayin kowane department yanzu. Maleekh baya nan, amma aiki bai tsaya ba. Ku tuna, company ba ta tsaya wa akan mutum guda sai dai akan tsarin aiki da jajircewa.”

Managers suka kalli juna, kowanne yana girmama ƙarfin halinta. Duk da ƙazafin da ake mata, ta zauna a matsayin shugaba mai cikakken iko.

A lokacin, ɗaya daga cikin managers ɗin ya ɗan gyara murya cikin girmamawa ya ce:

“Madam, gaskiya muna mamakin yadda kika zo da ƙarfi haka. Mun san komai da ake magana a waje, amma yanzu mun ga da idonmu kin fi ƙarfin duk wata jita-jita. Zamu ba ki haɗin kai.”

Amal ta ɗan murmusa, murmushin da ya cika da takaici da izza a lokaci guda.....ta ce:

“Kyakkyawan aiki shine amsar da zan bawa maƙiyi. Babu wanda zai ce Amal ba ta da daraja. Ni zan tabbatar da haka.”

Sai ta ɗora hannunta akan files ɗin gaban ta ta fara briefing, tana ƙiran department ɗaya bayan ɗaya.

Duk da zuciyarta na ta ƙuna da zafin kaunar Maleekh, a wajen aiki ta bayyana kamar wadda babu wata damuwa da ta taɓa zuciyarta.


Bayan ta kammala meeting ɗin managers, Amal ta koma office ɗinta. Duk wani aikin da aka kawo mata ta duba shi da tsantsar hankali, ta sanya signature inda ya dace. Duk da gajiyar zuciya da ke cin jikinta, ta tsaya daram ta tabbatar da babu wani abu da zai tsaya a gaba saboda rashin Maleekh.

Sai dai lokacin da ta kalli agogo ta ga ƙarfe 3:30 na rana. Zuciyarta ta fara bugu da ƙarfi. Ta san akwai wurin da zuciyarta ke jan ta: Office ɗin Maleekh.

Da sauri ta miƙe, ta ɗauki glass ɗinta ta ɗora, ta ɗauki jakarta ta fita daga office ɗinta. Bata tsaya sauraron kallon da ma’aikata ke mata ba, ta nufi babban office ɗin CEO....

(Oh ko ina dai sai ka samu magulmata..).

Bayan ta isa bakin ƙofar, zuciyarta ta buga sau uku kamar zata fito. Ta jingina da ƙofar tana jan numfashi mai nauyi. A hankali ta murɗa handle ɗin ta shiga ciki.

Office ɗin na Maleekh ba kowa a ciki. Sai duhu, sai shiru, sai kuma ƙamshin turarensa da ya lulluɓe ɗakin gaba ɗaya.

Amal ta tsaya cak a bakin ƙofa. Idanuwanta suka rufe, zuciyarta ta fara rawa. Kamar Maleekh yana zaune a kan kujerarsa yana mata kallon ƙauna.

Ta ja ƙafar ta a hankali ta ƙarasa zuwa kujerar executive chair ɗinsa. Ta taɓa bayan kujerar da hannunta, hawaye suka zubo mata.

Amal a cikin ranta ta ce:

“Oh Maleekh… har yanzu ƙamshinka yana nan. Har yanzu zuciyata ta ƙi yarda da cewa baka sona. Me yasa kake min haka bayan dukkan so da ka nuna mun?…”

Ta zauna a kujerarsa, ta jingina da kujerar tana runtse idanu. Hannunta ta ɗora akan teburinsa tana shafa wani pen da yake ɗauke da rubutunsa.

A hankali ta ɗauki hotonsa da ke kan teburin wanda aka ɗauka lokacin award ɗinsa na CEO of the Year. Ta ɗauki hoton ta kalle shi sosai, hawaye na zuba.

Amal a hankali da murya mai rawa ta ce:

“Ko da duniya ta juya mun baya, ko da iyayenka basu fahimce ni ba, na rantse ba zan taɓa daina sonka ba. Koda kuwa ka tsane ni…”

Sai ta ɗora hoton akan ƙirjinta, ta rufe idanu tana jin tsantsar ƙauna da zafi a zuciyarta.

A waje kuwa, wasu daga cikin staff sun hango Amal na fita daga office ɗin CEO ɗin daga baya, suka kalli juna cikin mamaki. Wata daga cikinsu ta ce da sannu-sannu:

“Lallai wannan yarinyar akwai ƙarfin hali… Da ace ni ce a irin halinta, wallahi ba zan iya zuwa ko kusa da wannan campany ba. Amma ita, har tana iya shiga ta zauna.”

Staff ɗin namiji ya ce:

“Shi ne bambancin mace mai kishin zuciya da ƙuduri. Ko da kuwa duniyar bata yinta, sai ta tsaya tsayin daka akan abinda take so.”

Amal ta fito daga cikin office ɗin Maleekh, ta nufi ƙofar fita daga campany. Sai dai a tsakar corridor ta hangi wasu ma’aikata mata biyu suna ta magana da dariya, suna kallonta a ɓoye. Da ta matsa kusa ta ji da kunnenta suna faɗin:

“Ko kunya bata da ita wallahi. Kin manta irin yadda aka ɗauke ta a cikin jini daga gidan club? Ai magungunan zubar da ciki ta sha...”

Ɗayar ta ce:

“Haka fa. Amma yanzu gashi tana tafe da wani isa kamar ba ita ake nunawa a TV ba. Wallahi akwai wauta a rayuwa.”

Amal ta tsaya cak! Ta ja numfashi ta juyo a hankali. Da glass a idonta, fuska cike da izza, ta taka cikin tafiya mai natsuwa zuwa wajen reception. Sai ta tsaya a tsakiyar hall ɗin inda ma’aikata suke cike.

Ta ɗaga hannunta sama ta ce da murya mai ƙarfi:

“Ina son waɗanda na jiyo suna gulmata su fito nan yanzu. A gaban kowa. Ku fito!”

Sai aka yi shiru, kowa ya kalli juna. Su biyun da suka yi maganar suka fara rawar jiki suka fito a kunyace. Amal ta juya da kafaɗarta, ta cire glass ɗin daga idonta a hankali, ta dafa tebur ta ɗan jingina, sannan ta ce da murya mai kaushi:

“Kun ce bani da kunya? Kun ce an ɗauke ni cikin jini daga club? Kun ce magungunan zubar da ciki ne suka kaini can? To ku saurara! Ƙaddara bata san gidan kowa ba. Wallahi idan wata rana irin wannan ta same ku, da kun san babu abinda ya fi shiru da adalci a rayuwa. Amma saboda ƙarancin tunani, ku kaɗai kun fake kuna munafurci, wawaye kawai, marasa kishin kai...”

Sai ta kalli sauran ma’aikata gaba ɗaya, ta ɗaga hannu tana girgiza musu yatsa ta ce:

“Ina so a san wannan a matsayin gargaɗi. Duk wanda na sake jin ya tsoma baki cikin rayuwata ko kuma ya kuskura ya sake

39 / 82