Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
dauuu har ɗaukan ido yake..
Inna ce ta leƙo daga ƙofar gida tana faɗin
"Ki tsaya na makj addu’a ƴarnan...."
Amal ta tsaya Inna
Ta ɗora hannu a kanta, tana karanta ayoyi cikin murya mai raɗa. Bayan haka, ta ce:
“Ki je da aminci. Idan alkhairi ne ki dawo da ƙarin daraja. Idan sharri ne, Allah ya 6atar da shi kafin ki isa.”
Amal ta amsa da "Amiin"..
A cikin motar, Amal tana kallon waje cikin natsuwa. Duk inda suka wuce, mutane suna tafiya da abubuwan rayuwarsu amma zuciyar Amal na tafiya da saƙo.. tana magana a ranta
"Zan je, zan tsaya a cikin taron masu daraja. Amma zuciyata za ta zauna cikin ƙasƙanci, domin ni yar gajiya ce, ba ƴar isa ba..."
An shirya wajen bikin yayi kyau fiye da yadda Amal ta hango a tunaninta. Babban filin da aka tanadar ya sha kwalliya da furanni, fitilu masu launi, da gilashi masu walkiya. Kowane mutum da yake cikin bikin yana nuna jin daɗi, daraja da kima.
Kamar yadda A’isha ta faɗa, sai da katin gayyata ne ake shigowa.
A lokacin da Amal ta ƙaraso bakin shiga, jami’an tsaro suka tsaya suna duban ta.
Miƙa musu katin tayi a hankali, suna dubawa suka ce:
"Welcome, ma’am."
Ta shiga....
Kamar wani wutar lantarki da aka kunna, idanuwa da dama suka karkata gareta. Tana tafiya cikin nutsuwa, tafiyarta na ɗauke da tarin tausayi da kima. Wasu daga cikin ƴaƴan masu kuɗi da ke cikin bikin sun ganta ne daga cikin video da ya yaɗu, video ɗin Maleekh yana kwance a kanta.
Wasu suka fara magana suna faɗin
“Wannan ba ita bace wadda Maleekh ya faɗi a kanta?”
“Yar talakawa ce fa… amma tana da kwarjini.”
“Kin san sun ce sun kore ta daga aiki saboda politics?”
Wasu kuwa sun hau ƙiran sunanta a social media, suna cewa:
#QueenOfCourage
#AmalOfThePeople
#MaceMaiKwarjini
A nesa daga cikin VIP section, shigowar Maleekh kenam, ya zauna cikin rigar shadda white color, mai bala'in tsada, domin bazaka taɓa samun irin shaddar a Nigeria ba, ga ya ɗaura white glass ɗan siriri akan golden eyes ɗinsa, yana motsi da ɗan ƙaramin lips ɗinsa da ya sha lip glowin sai sheƙi yake, ga wata farar hula da ya ɗora akan sumar sa da ya sha gyara, shima ba ƙaramin kyau ya yi ba, chocolate handsome guy, ga wani gyara da yayi wa sajensa sai ɗaukan ido yake.... Duk ƴan matan wurin idonsu akan sa yake, farashin Maleekh na da matukar tsada, ga kyau ga kuɗi ga ilimin boko da Arabic, ƙaramin shekaru, bazai wuce 30 ba...
Yana tare da wasu manyan baƙi, ciki har da wasu ministoci da mutanen ƙasashen waje, yana duba yanayin taron, dake bikin ƙanwarsa ake, sai dai ita A'isha ba mahaifiyarsu ɗaya da Maleekh ba, A'isha da kannenta mata biyu da mahaifiyarsu suna zaune ana Kaduna. Maleekh kuma da kannensa mata biyu da mahaifiyarsu su kuma suna Abuja...
Ɗago kai da zaiyi kwatsam idanunsa suka sauƙa a kan Amal dake zaune ita kaɗai..
Zuba mata ido yayi ko kibtawa babu, a zuciyarsa ya ce
"Tana kallon kamar ba ta damu da duniya ba. Amma duniya ce ta damu da ita yanzu..."
🌟
A lokacin da MC ke gab da gabatar da wani ɓangare na shirin, aka sanar da cewa za’a bawa wasu baƙi kujerun VIP saboda "irin jajircewar su a rayuwa." Abin mamaki Amal na daga cikin jerin sunaye!
MC ya faɗi suna da ƙarfin murya tare da faɗin
"Amal Abdulsamaad, mace mai daraja daga cikin matan ƙasar nan da suka tsaya da gaskiya fiye da kuɗi da ƙarfi!"
Kowa ya zaro ido.
Amal ta tashi cikin ladabi, amma zuciyarta cike yake da mamaki...
Maleekh cikin murmushi yake kallonta domin shi yasa a bata...
Bayan ta zauna..
A cikin nutsuwa da salon kwarjini, Maleekh ya tashi daga kujerarsa, yana matsowa kusa da ita. Mutane ne suka zuba ido, domin kowa idonsa akan su yake...
Amal jin mutum a gefenta yasa ta kalli wurin, ganin Maleekh ne yasa ta zaro ido waje tana kallon sa..
Maleekh cikin sassanyar murya ya ce
"Zan iya magana dake Amal?"
Kafin ta amsa, A’isha ta zo yanda suke cikin kayan Amare ta ce:
"Let me steal her for a second Yah Maleekh."
Ta janyo Amal gefe, sannan ta raɗa mata a kunne:
"Duniya tana kallon ku. Ki tsaya da gaskiyar ki, ko ma meye zai biyo baya."..
Maleekh ganin yanda mutane suka zuba masa ido yasa ya koma yaje ya zauna a yanda yake...
MC ne ya bayyana a filin wurin.
(Jama’a kowa ya nutsu. Fitilu na lilo a sama. Idanun mutane suka koma kan dandalin yayin da MC ya taka gaba cikin kwarjini.)
MC cikin fara’a ya ce
"‘Yan uwa maza da mata, da fatan za ku tar6i wata baiwar Allah wacce bata buƙatar gabatarwa, jaruma, hazika, muryar matasa Amal Abdulsamaad!”
Tafi ya karaɗe wurin. Wasu na tafawa saboda kaunar da suke wa Amal, wasu kuwa domin sha’awa, wasu kuma saboda mamaki....
Amal ce ta miƙe cikin natsuwa, tana tafiyarta cike da nutsuwa ta sa kowa kallonta. Ta isa muryar mic, ta sauƙe numfashi. Ta fara...
“Assalamu alaikum warahmatullah.
Sunana Amal Abdulsamaad.
Ni ƴar asalin Kaduna ce, kuma yanzu haka ina da shekaru 22 da haihuwa.
Na rasa iyayena ne tun ina da shekara uku a duniya, sanadiyyar wani hari na siyasa da ya shafi iyayena. Tun daga wannan lokaci, kakata take kula dani wato mahaifiyar mahaifina.
Ita ce ta koya min gaskiya. Ita ce ta gina ni akan jarumta. Kuma ta koya min cewa talauci ba laifi ba ne amma rayuwa ba tare da gaskiya ba, tabbas azaba ce.”
(Jama’a kowa yayi shiru. Har Maleekh sai da ya ɗan matso gaba daga inda yake zaune.)
“Ban taso a cikin dukiya ba. Na tashi a cikin gaskiya.
Ban yi makaranta a ƙasashen waje ba. Amma a makarantar mu ta ƙasata na samu abokiya ta gaskiya wato ita ce A’isha.”
(Ta kalli amarya A’isha da murmushi wanda ya bayyana zurfin kaunarsu.)
“Tun a makaranta A’isha ce ta fara raba abincinta da ni lokacin da ba ni da nawa. Ita ce ta fara tsayawa min idan ana yi min dariya saboda talaucina ko saboda natsuwata.
Ta daina kallon banbancin mu. Iyayenta na gwamnati, nawa kuwa na cikin kabari amma mu mun kasance ‘yan mata, abokai, ƴan uwa....
**“Rayuwa ta raba hanyoyin mu, ni na zama mai magana da jama’a, A’isha kuma ta kasance jakada ta ladabi da ilimi.
Amma yau ga mu nan kuma komai bai canza ba. Ina alfahari da ita, kuma ina alfahari da kaina.”**
(Ta tsaya. Muryarta ta lafa, cikin tausasa murya)
“Idan akwai abu ɗaya da nake so kowa ya tuna daga wannan jawabi, shi ne:
Ba sai kana da babban suna ba kafin ka zama babban mutum.
Ba sai kana da izini ba kafin ka faɗi gaskiya.
Kuma ba sai kana da iko ba kafin ka zama mai ƙarfi.”
(Matasa suka fara tashi suna tafi. Wasu manya suka bi sahu. A’isha tana goge hawayen farin ciki)
Amal ta rufe da cewa:
“Gare ki amarya A’isha nagode da kasancewa kamar yadda kika kasance.
Gare ku masu saurare nagode da wannan dama.
Kuma gare ku ƴan Kaduna daga kowanne gida muryarku na da tasiri.”
(Ta sunkuyar da kai cikin girmamawa ta koma kujerarta. Hotuna na ci gaba da ɗauka. Wurin taron ya cika da amo.)
MALEEKH yana kallonta
Bai tafa hannuwa ba.
Yana zaune ne kawai, laɓɓansa a gimtse, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, yana maganar zuci
"Ba kawai murya ce ta rediyo ba... juyin juya hali ce a cikin jikin Amal...."
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 13 to 14
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
MC ne ya karɓi mic ɗin daga hannun Amal cikin fara'a, ya juya ya dubi taron, sannan ya kalli Amal wacce take shirin barin wurin.
MC ya ce
“Eh-eh! Amal bamu gama dake ba fa!
Mutane da yawa suna da tambaya, mu ma muna da tambayoyi.
Kuma nasan akwai waɗanda suka zo ne saboda ke.”
Jama’a ne suka fara dariya da tafi. Amal ta murmusa kaɗan, ta tsaya daidai gefen MC. Ya miƙa mata mic.
MC cikin nishadi ya ce
“Amal, mun san ki ba kawai a nan ba, har a kafafen watsa labarai na ƙasashen waje.
Yanzu idan da ace wani ne ya samu irin shahara da goyon bayan da kika samu, da tuni yana da gida na alfarma, manyan motoci, kudi a account amma meyasa har yanzu kina zaune a irin yanayin da mutane da dama ke ƙira ‘talauci’?”
Amal ta ɗan gyara tsayuwarta. Ta ɗago kai cikin natsuwa ta ce
“Na gode da tambayar.
To gaskiya talauci ba laifi ba ne, kuma arziki ba a tantance mutum da shi.
Ni na zaɓi rayuwar gaskiya akan rayuwar ƙaryar kuɗi.
Inada ikon in karɓi cin hanci in gina gida na alfarma, in mallaki motocin da mutane ke mafarki amma hakan zai nufe ni da sayar da gaskiyata, na sayar da zuciyata.
Rayuwata ta ginu ne bisa gaskiya.
Kuma gaskiya ba ta da tsada amma ta fi kuɗi daraja.”
(Wani sassa na taron ya fara da tafi. MC ya kalli Amal cikin girmamawa.)
Ya ce
“Tabbas, abin burgewa ne.
To Amal, zamu so ki gaya mana me ya ja hankalinki kika shiga aikin jarida? Kuma me ya sa kika zaɓi ki dinga faɗa da ƴan siyasa maimakon ki nutsu da aikinki?”
(Amal ta dafe mic kamar wacce ke maganar zuciya.)
Sannan ta ce
“Na shiga aikin jarida ne domin rayuwa ba ta bani damar yin shiru ba.
Na ga abinda ake yiwa talakawa.
Na rasa iyayena saboda tsagwaron karyar siyasa.
Su da ba su da laifi an hallaka su kawai don sun tsaya akan gaskiya. Wannan shi ya haifi ƙiyayyata da ƙarya, ya sa na rantse zan yi amfani da muryata wajen ƙwato wa marasa murya haƙkinsu.
Ina faɗa da ‘yan siyasa ne domin yawancinsu ba su da gaskiya.
Suna cin zarafin al’umma, suna karkatar da dukiyar ƙasa kuma ba wanda ke cewa a’a.
Na yarda da Allah, na yarda da mutuncina kuma idan muryata zata mutu saboda gaskiya, to inaso ta mutu cikin daraja.”
(Wani sashi na jama’a suka ce “Allah sarki!” Tafi ta kaure.)
MC ya gyara murya cikin salo ya ce
“To Amal, ba za mu bar ki da duka tambayoyin zuciya ba yanzu me zaki ce: kina soyayya?”
Taron ya ƙara kankama. Kowa yana jiran amsa. Amal ta murmusa kaɗan ta sauƙe idonta kafin ta dago ta ce
“Bana soyayya.”
MC ya ce
“A’a kenan, amma akwai wanda ya furta miki soyayya kuwa?”
Amal ta ɗan yi dariya sannan ta ce
“Eh, akwai su da yawa. Amma ni soyayya ina kallonta a matsayin shashanci ne..
Ina tunanin yawancin waɗanda ke soyayya yanzu suna soyayya da abin da suke gani, ba abin da suke ji ba. Ina buƙatar soyayyar da zata gina ni, ba wacce zata rushe ni ba.”
MC yana murmushi ya ce
“Toh... toh... toh!
Amma akwai jita-jita. Amal da Maleekh Cashbank kuna soyayya ko a’a?”
Amal ta ɗan dakata. Taron ya koma cikin natsuwa. Kowa na jiran ta ce “eh” ko “a’a.”
Ta juyo cikin natsuwa ta ce
“Ban san zancen ba.”
MC ya taɓe baki sannan ya ce
“To ba zaki mana bayani ba kenan?”
Amal ta ce
“Na san mutane da yawa na jin labarai, na ga bidiyo, na ji maganganu…
Amma a gaskiya, ni kaina har yanzu ban fahimci me Maleekh yake nufi da rayuwata ba.
Ni ba na jin kalmomi, na fi karanta hali.
Idan ya zo da gaskiya, lokaci zai bayyana.
Amma har yanzu, ina da damuwa da tambaya ɗaya: shin yana da gaskiya ko kuma yana wasa da wuta ne?”
Taro ya kaure da tafi, wasu ma sai da suka taso tsaye. Haka shafin ya ƙare cikin nishaɗi, lulluɓe da mahangar gaskiya da jarumta..
Amal na ƙoƙarin janye jikinta cikin ladabi domin komawa kujera, tana ƙoƙarin tserewa hasken idon mutane. Sai kwatsam… ƙafarta ta zame! Ta ɗagu sama tana shirin faɗuwa ƙasi amma kafin ta faɗo hannuwan Maleekh suka riƙo ta!...
Riƙe shi ta yi da ƙarfi kamar mai neman mafaka. Ta kama wuyansa, idonta cikin nashi. Shi kuwa ya riƙe kunkumin ta da hannunsa ya manne ta sosai a jikinsa, yana kallon ta da idon da babu wata magana da ya fi dacewa da shi sai shiru mai sa bugun zuciya..
Wurin ya ɗau tsit. Kowa ya tsaya, kowa ya zuba musu idanu, daga manyan baki zuwa ƙanana, daga masu kirga numfashinsu zuwa masu ɗaukar bidiyo. Har sai da wani daga cikin manyan bak’i ya katse shiru da faɗin
“Soyayya phone storee!!!”
Wurin ya kaure da dariya da tafi. Ihu da nishaɗi suka mamaye ɗakin taron. Kamar abin da mutane ke jira kenan. Wasu suna cewa
“babu shakka Amal da Maleekh soyayya ce”, wasu suna ɗaukar video suna turawa kai tsaye. Har Amarya A’isha da angonta suna dariya cikin farin ciki da tafawa.
Amal jin yanda ya ɗora hannunsa akan boob ɗin ta, sannan mannuwan da suka yi ba ƙaramin mannuwa bane domin tana jin yanda take gogan banana bananansa 🍌🫣.
Ƙirjinta ne yake wani irin dukan uku uku..
Ganin yanda ta firgita ne yasa ya ɗaga ta yayi mata ɗaukan lud'a kamar karamar yarinya, yana kallon ta da murmushin da ta rasa fassara. Ya kai ta kujera, ya zaunar da ita a hankali..
Amal cikin jin kunya ta sunkuyar da fuskar ta, miƙa mata mayafinta yayi da ya zame ƙasi, dasauri ta karɓa tare da rufe fuskarta da shi..
Haka hawaye yake gangaro mata tsabar tsananin kunya da baƙin ciki...
MC ya kalli Maleekh yana dariya ya ce
“Toh toh toh! Toh yanzu daga ‘phone store’ zuwa ‘heart store’…
Yallabai, ka iso nan. Kai ma akwai tambayoyi da ke jiran ka!”
Tafi da dariya suka sake kaurewa yayin da Maleekh ya ɗan goge gefen rigarsa ya ƙaraso ya tsaya a gaban mic. Ya sauƙe bakinsa yana kallon Amal da har yanzu take kokarin ɓoye kunyar ta.
MC cikin murmushi ya ce
“Maleekh, kafin mu fara tambayoyi da gaske wannan rikewa ce ta gaggawa, ko kuwa da shiri aka zo da ita?”
Jama’a suka yi dariya. Maleekh ya ɗan yi murmushi ya jinjina kai, ya ɗauki mic, murya cike da kwanciyar hankali ya ce
“Da ace shiri ne da na tabbata zuciyarta tuni ta bar jikinta.
Amal fa ba mace bace da zaka shirya wasa da ita..."
MC ya ce
"Toh wane hali kake ciki yanzu, ganin yadda duniya ke alakanta ka da Amal, gashi nan kun rungumi juna a bainar jama’a, kana ɗaukar ta kamar amaryarka...”
Maleekh ya ɗan yi shiru. Sannan ya ce cikin nutsuwa, yana kallon inda Amal take ya ce
“Abin da ke faruwa tsakanin ni da Amal ba ni ke da ikon fassara shi ba, ita ce zata iya fassara shi.
Ni dai na san abu ɗaya: duk lokacin da take kusa da ni, nakan ji kamar zan manta da duniya gaba ɗaya.
Idan soyayya ne wannan to ban isa na musanta ba.
Amma har yanzu, ina jiran zuciyarta ta yarda da ni ba saboda bidiyo ko taro ba sai saboda gaskiya.”
Wurin taron ya sake kaurewa da ihu da tafi. Amal ta juyo a hankali ta kalle shi. Ya kalle cikin murmushi mai ƙayatarwa. Cikin shiru suka ci gaba da kallon juna… wanda bai da fassara..
Bayan mutanen wurin sun kaure da dariya, tafi, da ihu, MC ya ƙara miƙa mic ga Maleekh yana faɗin.
“Toh yanzu da ka furta cewa ‘ina jiran zuciyarta ta yarda da ni ba saboda bidiyo ko taro ba sai saboda gaskiya’… kana nufin kana sonta ne?”
Shiru ya sake ɗaukar wurin. Amal ta ƙara boye fuskarta da mayafi. Har MC ya ɗan cije leɓensa yana jawo kulawa sosai.
Maleekh cikin bugawar zuciya, wanda bai san fassara haka ba, ba tare da yasan abunda zai furta ba ya ce
“Ina son ta.”
Yayi shiru, sannan ya ƙara da wani muryar da ta cika taron kamar ana wasa da zuciya.
“Ba saboda kowa ya ce mun dace ba, ba saboda bidiyo ba, ba saboda ta shahara ba...
Sai dai saboda wata nutsuwa da nake samu idan ina kallon idonta.
Ina son ta kamar yadda ake son zuciya a ɓoye, cikin daɗi da tsoro.”
Ya ƙarasa kalaman idonsa akan ta..
Wurin ya ɓarke da ihu. Wasu na cewa "Allah ya kaimu biki!" wasu suna ɗaukar bidiyo suna cewa “Wannan speech ɗin yafi na proposal!” Amal kuwa... hawaye ne kawai ke gangarowa a gefen fuskarta, tana kallon ƙasa amma zuciyarta na motsi da wata sabuwar jin daɗi da tsoro...
MC ya ɗauki mic ya ce:
“Maleekh, muna godiya da ka tsaya tare da mu a wannan liyafa duk da irin girman matsayin ka. Amma akwai wasu ‘yan tambayoyi daga al’umma, suna so su ƙara tabbatar wa...”
Maleekh ya gyara tsayuwa cikin kwanciyar hankali, yana duba inda Amal take zaune, har yanzu tana rufe da fuskarta da mayafinta.
MC ya cigaba da cewa
“Tambaya ta farko daga jama’a: Maleekh, me ya ja hankalinka zuwa wurin wannan bikin da aka san yana da matuƙar zaman lafiya da mutane masu sauƙi kamar mu?”
Maleekh ya murmusa, ya ɗauki mic sannan ya ce
“Wannan ba ɓoyayyen al'amari bane, kusan kowa a wurin nan yasan cewa A'isha ƙanwata ce ta jini, wacce muke uba ɗaya..."
Amal ta ɗago tana kallonsa bata taɓa tunanin Maleekh da Aisha suna da wata alaƙa ba, ashe ma alaƙa ta kusa ne sosai, ta fara tunanin meyasa A'isha take supporting ɗin ta akan ɗan uwanta..."
MC ya katse mata tunani da cewa.
“Mun gode. Tambaya ta biyu, shin kai da Amal kuna soyayya ne? Duk da ka sanar cewa kana sonta, amma munaso mu ƙara tabbatar wa...”
Maleekh ya fara tunanin cewa ashe dai a fili ya furta cewa 'yana son Amal...'
Jama’a suka kaure da dariya da ihu ‘eeeeeeeeh!’
Maleekh ya ɗan yi shiru sannan ya ce:
“Ban san inda soyayya take zuwa ba, amma zan iya faɗa da amincewa cewa Amal ita ce mace ta farko da ta sauya min tunani