AMALEEKH by Asmeetah writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   80 / 82

237K to 240K   out of 244.2K words

tana tayata hawaye da cewa:

​ “Na yafe miki Farha, tun a baya na yafe miki, kuma insha Allahu zaki cigaba da rayuwa damu, kuma na fahimci cewa wannan harin ani aka kawo sai kuma ya same ki, ban so Maleekh ya janye ni ba domin da yanzu kina cikin lafiya da burin cigaba da mijinki, kiyi haƙuri…”

​Farha ta ce,

“Kar ki damu, Allah daman ya rigada ya rubuta hakan, idan Allah ya kare bawansa ba wannan ya isa yayi masa komai, don haka kina daga cikin kariyar Ubangiji domin Allah ya dubi maraicinki sannan ki cigaba da kula da yaranki…”

​Farha ta ja dogon numfashi ta ci gaba da faɗin

​ “Waɗanda suke son ɗaukan rayuwarki ba ƙananan azzalumai bane, kuma su ɗin ba wasu bane face iyayena… Suna son ganin bayanki Amal saboda su suka kashe miki iyaye…”

​Amal ta ji wani abu kamar daga sama, tana kallon Farha ido cike da hawaye.

​Ta cigaba da faɗin
“Nasan bazaki ji daɗi ba, to amma ya zakiyi kina tare da manyan makiyanki, wanda kike tunani ba shi bane, Abban Maleekh mutumin kirki ne, bashida hannu ko masaniya akan mutuwar iyayenki, sharri aka ɗaura masa…”

​Ta ci gaba da tona asiri..

​“A lokacin da za a kashe iyayenki, an tilasta wa mahaifinki akan ya sanar cewa Abban Maleekh ne ya kashe su, idan baiyi haka ba to anyi barazana da za a kashe ki da mahaifiyarki hakan yasa yayi haka… daga baya kuma suka aikawatar da kisan....
​To mahaifina ne da abokinsa Alhaji Gusau sai kuma daga baya Mahaifiyata taji labari itana ta rufa musu asiri… kuma take goyon bayansu… Amal Maleekh ya gano hakan kuma akwai shirin da yake son aiwatarwa dalilin da yasa yaso aurena kenan…”

​Ta bayyana dabarar Maleekh.

​ “Yana so ya ɗauke ni daga gaban iyayena yanda idona bazai ga abinda zai aiwatar ba, sannan yana son aure na saboda mummunan ƙudurin da iyayena suke shiryawa… Nasan zakiji kamar almara amma gaskiya nake gaya miki…”

​ “Maleekh yasan gaskiya ta hanyar dasa mun mic a cikin sumar gashina ba tare da na sani ba, iyayena suna yawan magana a gabanmu ni da Yaya Zayd abinda ya shafi sirrin nan saboda suna ganin sun rufe mana baki ta hanyar asiri, bazamu iya sanar da wani sirrinsu ba, ta hanyar nan Maleekh ya saurari komai ta mic da ya dasa mun…"

​ “Na gano haka lokacin da nake gyaran gashina, na ciro na gani kuma na tuna lokacin da ya sanya mun, a lokacin naji daɗin hakan sosai na ƙara maidawa cikin gashina, daga lokacin nake yawan zama a cikin iyayena sannan ni zanta janyo maganar da zaisa suyi ta maganganu akai suna faɗan abubuwa da yawa da ya shafi rayuwarsu da kuma ƙudirinsu sannan su suka tura a kone asibitin da Abbah yake ciki har aka ɗora miki laifin hakan…”

​Daga nan Farha ta fara jan numfashi da ƙyar.
​Amal ba abinda take sai kuka tana riƙe da hannun Farha.

​ “Jikina ya ɗau zafi da sanyi…” a cewar Farha tana numfashi sama-sama..

​Amal ta tashi a zabure ta ninka mata mayafi.

​Farha ta ce,
“Ƙafata ciwo suke…”

​Amal ta je saitin sawayenta ta fara mata tausa a hankali tana kuka. Taji ƙafar ta ɗau sanyi sosai kamar kankara.
​Amal ta daɗe tana ɗan tattausa mata Ƙafar daga bisani Farha ta ce: “Ya isa haka kizo ki huta…”

​Amal ta zo ta zauna tana riƙe da hannun Farha tana mata wasa da hannu. Har dare ya tsala sosai sai da Amal ta tabbatar da Farha ta fara bacci kafin itama ta kifar da kanta a bakin gado hannunta riƙe da na Farha. Ba jumawa bacci ya ɗauke ta itama..

​Asirin shekaru ashirin ya tonu! Abokan gaba sune iyayen Farha. Maleekh ya riga ya kama ƴan farmakin da suka harba Farha, kuma zai yi amfani da su don tonawa Wadata asiri..

Da misalin tsakar dare, Maleekh da Zayd suka isa Ofishin ‘Yan Sanda inda aka ajiye waɗanda suka kai farmaki (ƴan ƙunar baƙin wake). An yi wa mutanen dukan tsiya kafin Maleekh ya iso.
​Maleekh ya shiga cikin ɗakin tambayoyi. Ganin waɗanda suka harbi matarsa Farha, Maleekh ya cika da fushi da damuwa game da rayuwar Farha..

​Da murya mai ƙarfin tsoro da azaba ya ke faɗin

“Ku gaya mun wa ya aiko ku! Da sunan waye kuke aiki?!”

​Masu laifin sun yi ƙoƙarin ɓoye sunan Wadata, amma Maleekh bai yarda ba. Ya ɗauki wani ƙaton ƙarfe, ya fara dukan su ba tare da tausayi ba...

​ “Ku faɗa! Ko zan tabbatar da cewa wannan dare shine na ƙarshe a rayuwarku!”

​Maleekh ya ci gaba da dukansu har sai da jini ya fara tsiyaya daga jikinsu. A ƙarshe, ɗaya daga cikinsu ya faɗi gaskiya a tsorace.

​“Mu na roƙonka, Ranka ya daɗe! Alhaji Wadata ne! Shi ya umarce mu! Amal ya ce mu harba, ba Farha ba!”

​Maleekh ya daina dukan su, yana haki breathing heavily cikin fushi. A wannan lokacin, Zayd ya shigo ɗakin tambayoyi. Gaskiyar da Farha ta faɗa wa Amal, yanzu ta raunana layan rufe baki da ke kan Zayd da Inna..

​Zayd ya kalli Maleekh da idanu cike da hawaye da kuma tuna baya..

​Zayd murya cikin tsawa kamar an cire katanga a makogwaronsa.

“Ni zan faɗa maka! Daddy ne! Gaskiya ne! Shine! Shine makiyinmu duka!”

​Maleekh da DPO wanda ke gefe yana sauraro sun zaro ido suna kallon Zayd cikin mamaki da firgici.

​Maleekh ya ce,
“Zayd! Wane ne Daddy?.."

Nan Zayd ya gaya musu komai game da mahaifinsa da abokinsa Alhaji Gusau..

Already Maleekh ya san da hakan kawai ya nuna bai sani bane saboda a samu hujjoji..

​DPO ya tsaya mutum-mutumi, yana jin gaskiyar da ta girgiza shi fiye da harbin bindiga...

​DPO ya kalli Maleekh sannan ya ce,

“Malik, a kwantar da hankali! Ku rubuta duk wannan a takarda! Wannan shaida ce mai ƙarfi! Zayd, zo ka rubuta duk abin da ka sani! Yanzu za mu damƙe Alhaji Wadata da Alhaji Gusau nan take!”

​Zayd ya shiga rubuta dukkanin sirrin da aka rufe a kansa na shekaru da yawa. Maleekh ya bar wa DPO waɗanda suka harba don su ci gaba da aiki, amma zuciyarsa ta riga ta koma Asibiti inda Farha ke kwance.

Maleekh da Zayd basu bar wurin jami’an ba sai dab da asuba. Suka nufi asibiti kai tsaye domin Maleekh yana fargaban kasancewar Amal a wuri ita kaɗai saboda neman rayuwarta da ake yi, kuma masu son kasheta zasu iya binta asibiti domin suga bayanta..

​Haka yake ta tunani a tsorace. Basu wuce ko ina ba sai asibiti.
​Da gudu Maleekh ya sauƙa a mota ya nufi cikin Hospital. Zayd a bayansa. Suna isa suka tura ƙofar suka shiga. Daidai lokacin ake ta kiraye-kirayen sallar asuba..

​Ganin Amal tana kwance da kanta a kan gadon da Farha take kai, tana shan bacci.
​Maleekh ne ya zauna a bakin gadon yana shafa sumar kan Amal da ke bacci. Sannan ya maida idonsa kan Farha wacce itama idonta a rufe suke. Yasa hannu yana shafa mata fuska cikin kulawa...

​Zayd yana tsaye ya sau murmushi tare da faɗin
“Yanzu fa duk waɗannan zafafan matan matanka ne koh?”

​Maleekh ya furta “Uhmmm!”

​Zayd ya cigaba da faɗin
“Allah sarki masoyiyata da yanzu muna tare a ɗaki ɗaya…”

​Maleekh ya ce,
“Yanzun ma zaka iya zuwa ka sameta ai…”

​Ya ce, “A’a kamm! Shalelen ƙanwata tana cikin wannan halin ina zan samu ƙarfin zuciyar aiwatar da wani abu…”

​Maleekh ya sau murmushi yana kallon Fuskar Farha.

​Can sai ga Doctor ya shigo sanye da glass ɗinsa. Ya musu sallama suka gaisa.

​Doctor ya sanar musu
“Yanzu na dawo daga masallaci nasan bakuyi sallah ba, ku je akwai masallacin da basu shiga sallah ba yanzu anan kusa…”

​Maleekh ya furta.
“Shikenan Doctor amma ya jikin marar lafiya?…”

​Doctor ya ce,
“Normal jikinta, amma bari na ƙara dubata ko akwai wani abun da za a mata…”

​Doctor ya ɗora mata stethoscope (abin gwada numfashi) a saitin kirjinta.
​Yana gwadawa nan Doctor ya dube su a ruɗe ganin akwai abun da ba daidai ba. Maleekh da Zayd ganin yanayin Doctor suka zuba masa ido.
​Doctor ya gama gwada ta, yaji ba numfashi. Da sauri ya kalli wurin computer da yake nuna mutum yana numfashi ko ya mutu. Nan yaga ya nuna line mai tsayi (flatline).
​Doctor a tsorace ya cire abun kunnen yana salati.

​Zayd a tsorace ya furta.
“Lafiya Doctor?…”

​Maleekh kuwa ba bakin magana ganin yanda Doctor ya zama.
​A hankali Doctor ya furta:

​“Allah ya yi mata rasuwa…”

​Wani irin hajijiya ne ya d'ebi Maleekh sauran kaɗan ya faɗi. Kawai ya dafe jikin bango.
​Zayd hannu ya ɗora a kai yana faɗin..

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…”
_NEXT NEXT NEXT_

asmeetahwriter✍️

*🎤AMALEEKH🎤*


*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.


*Writing and Storytelling By*

Asma'u Muhammad Auwal

Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*

*MARUBUCIYAR:*

*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*

Bauchi State Nigeria.

*WhatsApp 09065443871*

Follow my channel 👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


BOOK ONE page 99 to 100

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹


​Maleekh yana jingine da bango, jikin sa na rawa saboda abin mamaki da raɗaɗin rasuwar Farha. Zayd kuma ya fita daga ɗakin, ya tsuguna a bakin ƙofar shiga ya kifar da kai yana kuka.
​Amal tana kan bakin gado, hannunta riƙe da na Farha. A hankali ta fara motsi, tana shirin tashi daga baccin ta na gajiya.
​Ta ɗan murmusa tana tunanin ko Maleekh ya dawo..
​Amal ta ji sanyi a hannun da take riƙe da shi. Ta so zame hannunta don miƙewa ganin ɗan haske alamun asuba tana son yin sallah, amma hannun Farha na riƙe da hannun. Ta sake janyowa, amma Farha ta kankame hannunta da ƙarfi kamar tana riƙe da wani abu mai daraja wanda take son kare shi kafin ta tafi.

​Amal ta buɗe idon ta gaba ɗaya. Ta kalli Maleekh da ke jingine da bango, da kuma Doctor da ke tsaye kusa da gadon, dukkanin su cikin yanayin tashin hankali da baƙin ciki.
​Sai ta kalli fuskar Farha wacce ke da alamun nutsuwa, amma launinta ya canza zuwa fari fat. Hannun Farha kuma ya yi sanyi sosai kamar kankara.

"Ya Maleekh meke faruwa ne?.."

A hankali ya furta "ta rasu.."

A razane ta buɗe ido sosai tana kallonsa, sai dai numfashinta ya ɗan tsaya kafin ta waigo ta kalli fuskar Farha..

Hannu tasa tana ɗan bubbuganta tana ambaton sunanta "Farha! Farha!! Farha ki tashi mana nasan bacci kike yi..."

Doctor ya ce "ta riga ta rasu fa, taya zata amsa miki.."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un " abun da Amal ta iya furta wa kenam.
Can tana ƙoƙarin barin wurin tana kuka sai kuma taji still hannun Farha na riƙe da hannunta..
Tana kuka tana ƙoƙarin cire hannunta sai kuma taji abu yaci tura, abu kamar wasa ya zamo firgici, Farha ta riƙe hannunta gamm ko motsi baya yi..

Ganin alamun hannun bazai sake ta ba yasa ta fara ihu tana kuka saboda firgici da tsoro na sanin gaskiyar cewa Farha ta rasu amma kuma hannunta yaƙi rabewa da nata..

​Wani irin Ihu mai tsananin tsoro ta sake.. “Ahhhhhh! Hannuna! Maleekh! Me ke faruwa? Hannunta yaƙi rabuwa! Nima mutuwa zan yi?!”

​Doctor ya matso da gaggawa, yana ƙoƙarin dabararsa don raba hannun Farha daga na Amal, amma hannun yaƙi sake wa. Ko da ya danna wurin, kankamewar tana nan daram.
​Maleekh ya fara gudu zuwa wurin. Ya san cewa Farha tana ƙoƙarin bayyana wani abu na ƙarshe ne.
​Ya rungume Amal yana rarrashinta duk da raɗaɗin zafin mutuwar Farha da yake ji a zuciyarsa.

​Muryarsa cike da baƙin ciki yake furta...
“Shhh! Kada ki tsorata! Ba zaki mutu ba! Farha ta riga mu gidan gaskiya! Ba ta so ta sake ki ne, saboda tana son ta kare ki ne har na dawo!”


​Doctor ya ce, "Wannan kam sai dai a yanke hannun mai rai ɗin a bisine da gawar..."

Amal jin haka yasa ta sakin fitsari a wurin..
Fitsari cikin baho duk ta juye shi a wurin, ga yanda jikinta yake kakkarwa gaba ɗaya ta haɗa zuffa tako ina.
Idonta yayi jawur..

Maleekh dake rungume da ita yana iya jin bugun zuciyarta.
Yayi akan hannun ya rabu shima ya kasa..

A lokacin ya fara tofe hannayensu da addu’a, adduoi yake ta karantowa yana tottofe hannun, bayan can ya matsa kusa da Farha, ya shafa mata goshinta a karo na ƙarshe.

​Ya raɗa mata a kunne
“Nagode Farha! Na ji abin da kika yi, kuma na fahimci sadaukarwarki! Na riga na kama su! Kin cika alƙawari! Yanzu ki saki Amal! Zan kula da ita da dukkanin gaskiya da ƙarfi!”

​Bayan Maleekh ya faɗi haka, hannun Farha ya sake hannun Amal a hankali.
​Amal ta ciro hannunta da tsananin tsoro.
Ta rungume Maleekh da ƙarfi tana kuka mara sauti.
​Zayd ya shigo ɗakin, jikin a sanyaye. Ya durƙusa a gaban gadon, ya ɗauki hannun Farha ya sumbace shi cikin girmamawa da baƙin ciki.


Amal ta durƙusa sai kuka take domin ta ji mutuwar sosai. Haka take ta kuka ba kakkautawa. Da ƙyar Maleekh ya samu ƙarfin zuciyar ɗago ta ya rungumeta.
​Bayan nan aka sa Farha a Ambulance domin kaita gida, ba tare da an sanar wa kowa ba don hana rikici kafin a binne ta. Maleekh da Zayd da Amal sai wasu likitoci masu rakiya. Kai tsaye gidansu Maleekh suka nufa.



​A falo tuni labari ya tarwatsu. Ammy da Mahaifiyar Farha (Hajiya Sa’adatu), wacce tayi danasanin goyawa mijinta bayan aiwatar da laifi, sai Inna wacce ta gama sanar dasu gaskiyar labarin kashe iyayen Amal da akayi.
​Ammy ta girgiza sosai domin bata taɓa tsammanin Alhaji Wadata zai aiwatar da haka ba. Sai kuka take tayi. Hajiya Sa’adatu ta sanar cewa Amal akaje kashewa ba Farha ba.

​Inna tana kuka ta ce, “Yanzu rashin imanin har ya kai a kashe iyayenta sannan itama a kashe ta?!”


​Hajiya Sa’adatu tana kuka itama tana neman yafiyar Inna da kuma Allah.
​Suna cikin wannan sai suka ji ƙarar jiniya na Ambulance. A zabure suka miƙe domin sun san ba lafiya ba. Suna falo sun kasa motsawa.
​Can sai ga Maleekh ya shigo da Zayd suna ɗauke da Farha a nannade da mayafi. A kan kujera suka kwantar da ita.

​Ammy cikin kuka ta furta “Meye wannan Maleekh?…”


​Maleekh kai a sunkuye ya ce,
“Ku ƙira wacce zata mata wanka a suturtata, Allah yayi mata rasuwa…”


​Ammy da Inna lokaci guda suka furta “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Baki a haɗe.

​Hajiya Sa’adatu kam dafe kirji tayi daga nan ta faɗi sumammiya.

​Cikin awanni an sanar da rasuwar Farha a ko’ina.
​Alhaji Wadata da ke gida yana zaune yana shan tea. Aka ƙira shi a waya aka sanar dashi mutuwar ƴarsa. A lokacin kofin tea ya faɗi daga hannunsa. Ya miƙe a zabure tare da furta: “Whatttt…”
​Bayan an katsar da ƙiran a ruɗe ya ɗauki key ɗin mota kai tsaye gidansu Maleekh ya nufa domin an sanar masa tana gidan.
​Yana isa ya samu har an suturtata an fito da ita za a yi mata jana’iza. Mutane an taru sosai. Ta ko ina zuwa suke. Ta samu mutane sosai domin har daga wasu garuruwa an zo.
​Ran Alhaji Wadata ya ɓaci sosai ganin ba a sanar masa a lokacin da ta rasu ba, sai da har daga wasu garuruwa sun zo. Amma haka ya haƙura suka yi jana’izarta sannan aka kaita gidanta na gaskiya.
​Zayd kam ba bakin magana, idonsa yayi jawur domin sai da ya zauna a kabarinta ya yi mata addu’a da kuka gaba ɗaya. Da ƙyar Maleekh ya ɗago shi suka dawo gida.

​Bayan an dawo, Alhaji Wadata ne ya shiga gidan. Ya tarar da mata sun cika a babban falo. Hajiya Sa’adatu itama ta farfaɗowo amma da wani irin bala’in kuka ta tashi, ta kasa yiwa kowa magana sai kuka.
​A lokacin da Wadata ya shigo, bai dubi kowa ba ya fara maganar:

​ “Saboda rashin mutunci yarinyata ta mutu amma a kasa sanar mun a lokacin? Nine fa ubanta kuma ina gari!”


​Sai a lokacin Hajiya Sa’adatu ta miƙe tazo gabansa, kai tsaye ta ɗauki hannu ta zabga masa lafiyayyen mari!

​Alhaji Wadata yana zazzaro ido cike da mamaki yace, “Ni kika mara Sa’adatu?!”

​Hajiya Sa’adatu ta ce,
“Ban taɓa marinka ba tun da nake sai yau, kuma yanzu ma idan bakayi wasa ba zan ƙara maka! Marar mutunci kawai! Wallahi nayi danasanin aurenka domin da kai da babu duk ɗaya ne, na auri mijin da zai kashe mun ƴa da hannunsa! Tirrr!”


​Mutane haka suka tsaya kallonsu cike da mamaki.

​Tana kuka tana faɗin “Allah ya isa tsakani na da kai jahili kawai!”

“Sa’adatu nine jahili?!”

​Hajiya Sa’adatu ta ce, cikin kuka
“Na faɗa jahili, dabba, tsinanne, ɗan jahannama!”

​Amal tana zaune tana kallonsa, ji take kamar ta tashi ta murɗe masa wuya.

​Suna cikin wannan hayaniya kawai Alhaji Wadata yaji an kwaɗa masa katako a tsakiyar kansa.
​Yana waiwayawa yaga Inna ce da katako a hannunta tana kuka. Nan ta cigaba da kwaɗa masa tana tsine masa:

​ “Allah ya isa na Wadata tsinanne! Daman ina jiran wannan ranar da farin cikinka zai ƙare har abada! Ka kashe mun ɗana ɗaya tilo da matarsa saboda rashin imani sannan kazo kana neman rayuwar jikata! To ta Allah ba taka baaa!”

​Alhaji Wadata ne ya riƙe katakon da Inna take kwaɗa masa. Inna ta rungumoshi ta fara cizonsa a ta ko ina. Haka take jan naman fatarsa da ƙarfi. Ta kama naman wuyansa ta ja da ƙarfi sai da fatar ta ɗage.
​Da ƙyar ya karɓe kansa ya ruga da gudu ya fito. A sama sama ya gaggaisa da mutanen da basu san me ke faruwa ba, da sauri ya shiga motarsa ya ja a ɗari ya tafi...


Bayan kwana uku da rasuwar Farha, an gama ta'aziyya.

​Alhaji Wadata da abokinsa Alhaji Gusau suna zaune a falon gidan Wadata. Hajiya Sa’adatu da Zayd suna can gidansu Maleekh.
​Wadata da Gusau suna zaune suna shirya neman mafita domin sun san asirinsu ya tonu. Suna shirya barin ƙasar gaba ɗaya ta wata hanyar sirri.
​Sai suka ji an turo ƙofar falon ba tare da neman izini ba. Maleekh ne ya fara

80 / 82