Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   38 / 82

111K to 114K   out of 244.2K words

buɗe su a hankali, muryarsa ta sake yin rauni ya ce:

"Na gaji… da rayuwa… Na gaji… da soyayya… Ba na son kowa… sai ku…"

Islam ta rushe da kuka ta rungume hannunsa tare da faɗin:

"Dan Allah kar ka sake faɗin haka Yaya. Kana da mu, kai rayuwarmu ne…"

Abbah ya share hawayensa ya ce:

"Ka kwantar da hankalinka, ɗana. Zamu tsaya a tare da kai har sai ka farfaɗo gaba ɗaya. Babu wanda zai sake cutar da kai."

Maleekh ya lumshe idanu, hawaye na sauƙa daga gefen kumatunsa, sannan ya furta cikin rauni:

"Ina… so… na huta…"

Sai ya sake lumshe idanu yana shaƙar numfashi a hankali, ya koma shiru.

Doctor ya matsa kusa da Abbah da Ammy. Ya da fa kafaɗar Abbah cikin girmamawa, sannan ya dubi Ammy da ido mai cike da gargaɗi.

Sannan ya ce:

"Don Allah ku kula da kalamanku a gabansa. Zuciyarsa tana da rauni sosai yanzu, duk wata magana da zata tada masa hankali na iya sake rikita bugun zuciyarsa. Wannan halin da yake ciki ya samo asali ne daga tashin hankali da damuwa mai tsanani. Idan kuna so ya warke, to ku tabbatar komai da yake ji daga gareku yana da sauƙi, babu zafi, babu fushi."

Abbah ya jinjina kai cikin nauyi ya ce:

"Insha Allah, zamu kiyaye. Wannan yaron mu ne gaba ɗaya."

Ammy ta share hawayenta da sauri ta ce:

"Doctor, wallahi zan riƙe alƙawari. Ba zan ƙara masa ciwo ba, sai dai farin ciki."

Doctor ya dube ta yana faɗin:

"Ki tabbata kin aikata hakan. Wannan ba wai maganin asibiti kaɗai bane, soyayya da kwantar da hankali suna cikin maganin sa."



Scene ɗin Amal...

Tun daga daren da ta dawo daga asibiti, kullum ƙoƙari take ta ƙira Maleekh amma wayarsa a switch off. Hankalinta ya fara tashi.

A daren nan ta ɗauki wayarta ta ƙira PA ɗin Maleekh, wanda shine manager ɗinsa a campany.

Amal cikin damuwa ta kara wayar a kunne bayan ya ɗaga ta ce:

"Hello… don Allah, ina Yaya Maleekh ne? Na kirashi tun kwanaki amma wayarsa a kashe. Ko yana lafiya ne?"

Manager ɗin ya yi shiru na wasu sakanni kafin ya amsa da wata murya mai nauyi:

"Eh… Madam Amal, gaskiya akwai wani hali da yake ciki. Yana asibiti yanzu, tun kwanaki biyu kenan yana kwance."

Amal a firgice ta ce:

"Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Hospital kuma? Amma me ya same shi?!"

Manager ya ce:

"Ni ma ban san cikakkun bayanai ba. Amma dai likitoci suna ƙoƙarin ganin ya warke. Ki kwantar da hankalinki…"

A ruɗe ta kashe wayar tare da rufe baki da tafin hannunta, hawaye suna zubo mata ta ce:

"Ya Allah… Maleekh a asibiti kuma ni ban sani ba…!"

Sai zuciyarta ta ƙara tsinkewa lokacin da ta ga results ɗin asibiti nata da aka kawo mata a envelop.

Ta buɗe da hannu mai rawa… idonta ya sauƙa akan rubutu:

“Evidence of miscarriage, 4 months pregnancy.”

Amal ta zaro ido tana kallon saƙon, jikinta ya ɗau rawa. Sai ta riƙe cikinta a gigice tana magana da kanta:

"Ciki kuma? Wai a jikina? Na rasa gane komai amma ina aka ɗauko wannan sakamakon? Shin Maleekh ya sani?.."

Sai ta rushe da kuka tana riƙe da ƙirjinta.

Bayan ta gama shan kukan ta.
A ruɗe ta ɗauki gyale ta yafa, ta sauƙa down stairs a falo ta tarar da Inna..

Wani irin kallo Inna ta yi mata..

Amal a ruɗe take faɗin

"Inna Maleekh yana hospital ba lafiya inaso zanje na dubo shi.."

Inna ta kawar da kai ko kallonta bata yi ba.

Amal har zata tafi ta juyo tana kallo Inna, tace

"Inna anyi auren Maleekh kuwa?.."

Nan ma Inna bata kula ta ba.
Ganin inna bazata kulata ba yasa ta girgiza kai zata tafi...

Inna ta daka mata tsawa da cewa

"Bayan ke kikayi silar kwanciyarsa jinya shine yanzu zakije ki ƙarasa kashe shi koh?.."

A firgice Amal ta juya tana kallo Inna.
Muryarta na rawa tace

"inna ni kuma?.."

Inna ta ce

"Mutumin da yake burin aurenki, yazo yaji cewa kin zubar da cikin wata huɗu ya kenam? Kowa ya sani, an tallata ki a tv da ko ina, ke ko kunyar fita bazaki ji ba?..."

Amal ta ja dogon numfashi sannan ta ce

"Koma menene tinda ina da gaskiya, zanje, zan tabbatar shin Maleekh baya sona yanzu ko kuma har yanzu yana sona.."

Inna taja tsaki tare da kawar da kai..

Amal ta fice, kai tsaye motarta ta shiga tare da fita daga gidan...

Amal ta hau mota jikinta yana kyarma, zuciyarta kamar zata fito daga ƙirji. Hannunta a kan sitiyari sai rawar sanyi yake, idanuwanta sun cika da hawaye amma ta share su da bayan hannunta tana faɗin:

"Ya Allah, idan da gaske Maleekh yana sona, ka haɗa ni da shi cikin alheri… kar ma'kiya su rabamu da ƙiyayya. Kar cutar zuciyata ta zama gaskiya..."

Yayin da ta ƙarasa bakin asibitin, motarta ta tsaya cak a bakin gate. Security ya matsa kusa yana tambaya, kafin ta ce komai sai ta nuna musu sunanta da sunan Maleekh. Nan take aka buɗe mata hanya.

Cikin tsoro da ruɗu ta shige cikin babban building ɗin, ƙafafunta kamar ba ya jikinta. Tana shiga cikin reception ta ce da rawar murya:

"Excuse me… ina wajen da aka kwantar da patient ɗin nan, Mr. Maleekh?"

Nurse ɗin ta dube ta da mamaki tace:

"Kin shigo da ɗan ɗaukar rai ne… ke ce Amal?"

Amal ta kasa amsa sai da ta ɗaga kai kawai, zuciyarta ta cika da tsoro. Nurse ɗin ta nuna mata hanyar ward.

A hankali Amal ta nufi hanyar, ƙafafuwanta suna jijjiga, hawaye suna tsiyaya a fuskarta. A zuciyarta kalmomi ɗaya ke maimaituwa:

"Ya Allah kar ya ƙi ni… kar ya ƙi ni…"

Da ta isa bakin ƙofar ɗakin, sai zuciyarta ta tsinke kamar zata tsaya. Hannunta ya tsaya cak a kan handle ɗin ƙofar.

Ta ɗauki numfashi tana kuka a ranta:

"Ko zai ƙi ni, zan sani yau… zan ji da bakinsa. Tinda Inna ta ce ni ne silar ciwonsa, bari ya gaya min da kansa…"

A hankali ta murɗa ƙofar ta shiga...

Sai idonta ya sauƙa a kan Maleekh, kwance a gadon asibiti, gaba ɗaya ya rame, yana sanye da oxygen pipe a hancinsa.

Amal ta dafe ƙirji tana sauƙe kuka mai ƙarfi. Cikin zuciya ta ce:

"Wayyo Allah na, ciwon har ya kai haka? Innalillahiwa’innailaihirraji’un, Ya Maleekh dan Allah kada kace nine silar rashin lafiyarka.."

Ta ƙarasa kusa da shi da rawar jiki, ta durƙusa a gefen gadon, ta riƙe hannunsa.
Hannu mai sanyi da rauni..

A hankali, kamar wanda yake jin muryar da zuciyarsa ta fi so fiye da komai, Maleekh ya motsa idanunsa. Suka buɗe a hankali, yana lumshe su a slow, sannan suka tsaya kan Amal...

Shiru ya cika ɗakin. Na’urar heartbeat yana beep beep beep a hankali.

Sai Maleekh ya ɗan motsa leɓensa. Muryarsa ƙasa sosai, amma kalmomin suna ɗan fitowa...

"Amal… kina nan?"

Amal ta fashe da kuka mai ƙarfi tana faɗin:

"Eh, ni ce… ni ce My bee. Na zo… na zo duba ka…"

Sai Maleekh ya ƙara lumshe idanuwansa, yana ƙoƙarin yin murmushi mai rauni, ya ce
"Ban taɓa daina sonki ba…"

Amal ta durƙusa tana riƙe da hannunsa, idanuwanta na cike da hawaye, ta ce:

"Ka daina kuka Ya Maleekh, don Allah… ka tsaya ka dubeni, ni ce… ban taɓa daina sonka ba nima..."

Sai dai Maleekh ya lumshe idanunsa gaba ɗaya, zuciyarsa na bugawa da sauri. A ƙwaƙwalwarsa sai muryar Doctor ta dawo yanda yake faɗin:

"Mr. Maleekh, result ɗin ya nuna cewa Amal ta zubar da cikin wata huɗu…"


Zuciyarsa ta ƙara karye wa! Wani irin raɗaɗi ya shige shi fiye da duk wani ciwon jiki da yake ji. Numfashinsa ya ƙara sarkewa, idanunsa suka ƙumbura da hawaye masu zafi..

A cikin ransa ya ke faɗin:

“Na yarda da ita… na amince da ita… yanzu kuwa?”

Sai hawaye suka kwaranyo masa, ya girgiza kai yana ta faman zubar su.

Amal ta firgita, ta miƙe tana share masa fuska tare da faɗin:

"Wayyo Allah! Me yasa kake kuka haka? Na baka tsoro ne? Ko jikinka ne ke maka zafi?!"

Maleekh ya zame hannunsa daga nata da ƙarfin da ba’a zata zai iya ba. Idanunsa suka canza, suka cika da huci da tsanar da take neman cinye shi.

Ya ɗan motsa bakinsa da ƙarfi ya ce:

"Ke… me kika yi min? Ke wacece Amal?!"

Amal ta tsaya cak, jikinta ya ɗauki rawa ta ce:

"Ni? Ni na yi maka me, Maleekh?"

Ya lumshe idanuwansa yana ƙoƙarin tattara ƙarfin magana..

"Na ji… na sani… asibiti… result ɗin ki… kin zubar da ciki na wata huɗu! Me kike nufi da wannan? Wane namiji kika aura da har kika yi masa ciki, kika zubar?!"

Amal ta durƙusa tana rikicewa ta ce:

"Subhanallah! Maleekh, ni fa ba haka bane! Wallahi ba haka bane! Ka yarda da ni… ba gaskiya bane wannan…"

Amma Maleekh ya juyo da fuskarsa gefe, hawaye na zuba, zuciyarsa ta cika da haushi da kishi mai ban tsoro. A cikin ransa kalma ɗaya ce ke maimaituwa:

"Ta ci amanata… ta ci amanata…"

Sai muryarsa mai rauni da tsawa a lokaci guda yana cewa:

"Ki fita! Ki fita daga ɗakin nan kafin ki kashe ni da ƙaryar da kike zubawa! KI FITA!!!"

Amal ta fashe da kuka, ta juyo da rawar murya tana faɗin:

"Na rantse da Allah, ni ba haka bane! Ka yarda da ni Maleekh, wallahi ban ci amanarka ba!..."

Ta miƙe da kuka, amma zuciyarta ta kasa barin ɗakin. Ta tsaya a gefen gadon tana kallon shi yana cigaba da zubar da hawaye cikin raɗaɗi, zuciyarta ta karye fiye da tunanin kowa.

A daidai lokacin da muryar Maleekh ke ƙara ɗaga ɗaki yana tsawatawa da ƙarfin da bai kamata ba, ƙofar emergency ɗin ta buɗe da sauri. Doctor ɗin ya shigo da nurses biyu a ruɗe.

Doctor ya daka-tsawa tare da faɗin:

"What is going on here?! Waye ya saka shi magana haka?!"

Ya matsa kusa da gadon da sauri, yana riƙe da stethoscope ɗinsa, ya duba hancin Maleekh da kirjinshi.

Sai ya juyo yana hararar Amal da fushi ya ce:

"Young lady, baki fahimci halin da marar lafiya yake ciki bane?! Zuciyarsa tana a critical stage! Koda kaɗan ba zai iya ɗaukar tashin hankali ba. Idan kika cigaba da tayar masa da hankali, zai iya mutu nan take! Kina son hakan ya faru?!"

Amal ta zabura da rawar jiki, ta saki kuka tana girgiza kai ta ce:

"Wallahi ban nufin cutar da shi ba, Doctor… ban nufin haka ba…"

Doctor ya tsawata mata da ƙarfi cewa:

"Sai dai ke kika jawo wannan! Ki fita daga ɗakin nan yanzu! Lafiyar marar lafiya ce a gaba, ba damuwar zuciyarki ba!"

Nurses suka matsa kusa da Amal, suka riƙe hannunta cikin tausayawa, suka fitar da ita..
Amal tana cewa cikin kuka mai ƙarfi:

"Na rantse da Allah, ban ci amanarka ba Maleekh… Wallahi sai gaskiya ta tabbata, sai Allah ya saka min…!"

Ta juya da gudu cikin kuka, ta bar wurin, ƙafafuwanta na jijjiga kamar zata faɗi.

Doctor ya kalli Maleekh da idanu masu ƙarfi ya ce da shi:

"Ka saurare ni, Mr. Maleekh. Idan baka kwantar da hankalinka ba, zuciyarka zata iya tsaya maka. Ka tuna kai babban mutum ne da rayuwarka take da daraja a gaban iyayenka da jama’a. Idan kana son mutum to ka kiyaye lafiyar ka, idan kuma baka so, ka kwantar da zuciyarka..... Idan baka so ka rayu saboda kanka, to ka rayu saboda waɗanda suke ƙaunarka."

Ya nuna nurse ɗaya ya ce da ita:

"Ku saka masa oxygen sosai, sannan ku duba ECG. Na ce babu wanda zai sake shiga ɗakin nan sai na bayar da izini!"

Nurses suka amsa:
"Yes Doctor."

Doctor ya sake kallon Maleekh cikin tausayawa ya ce:

"Don’t waste your life on anger. Heart is too delicate for that."

Ya juya ya fice daga ɗakin, nurses suka cigaba da gyara masa kayan da aka jona.

Maleekh ya lumshe idanu yana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, amma hawaye na ci gaba da gudana. A zuciyarsa kalma ɗaya ce ke murɗawa:

"Na so ta fiye da komai… amma ta ci amanata…".


_NEXT! NEXT!! NEXT!!!_


asmeetahwriter✍️

*🎤AMALEEKH🎤*


*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.


*Writing and Storytelling By*

Asma'u Muhammad Auwal

Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*

*MARUBUCIYAR:*

*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*

Bauchi State Nigeria.

*WhatsApp 09065443871*

Follow my channel 👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


BOOK ONE page 41 to 42

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹



A corridor ɗin hospital Amal ke tafiya tana kuka, hawaye na sauƙa kamar ruwan sama. Gyalen jikinta ta ɗora akan fuska gaba ɗaya, ta kasa ganin inda take nufa.

Sakamakon hakan ta buge wani babban mutum da ke tsaye yana waya, takardun da ke hannunsa suka watse ƙasa.

Amal a firgice ta dafa ƙirji, ta durƙusa da sauri tana tattara takardun:

"Innalillahi! Na shiga uku, don Allah ranka ya daɗe kayi haƙuri wallahi ban lura ba…"

Hannunta na rawar sanyi tana miƙa masa takardun cikin ladabi.

Shi kuwa mutumin, Abbansu Maleekh ya ɗago yana dubanta. Yana kallon yadda take kuka kamar mara galihu, fuska cike da hawaye, zuciyarsa ta ji tausayinta duk da bai san wacece ba...

Abba ya karɓi takardunsa, sannan ya sa hannunsa ya ɗagota a tausashe:

"Tashi ki tsaya yarinya, babu laifi. Amma meyasa kike kuka haka?. Me ya same ki haka?.."

Amal ta share hawaye cikin ƙaryar ƙarfin hali, tayi murmushi mai ciwo tare da faɗin:

"Ba komai wallahi… wata ƙaddara ce kawai. Na gode sosai."

Abba ya girgiza kai yana kallonta cikin tausayawa ya ce:

"Kada ki yarda damuwa ta raunana miki zuciya. Rayuwa ba ta wuce gwaji ba. Ki roƙi Allah ya kawo miki mafita, domin shi ne mai iko akan zuciya da ƙaddara."

Kalamansa sun shige jikin Amal kamar wutar lantarki. Ta ɗan lumshe ido tana jin sanyi a ranta, kamar an shafa mata magani. Ta kasa cewa komai sai dai ta yi masa godiya tana murmushi cikin hawaye:

"Na gode ranka ya daɗe, Allah ya saka da alheri."

Ta yi gaba tana fita daga corridor ɗin. Abba ya bita da kallo, zuciyarsa na tambaya “Wacece wannan yarinya mai ɗauke da baƙin ciki haka?” Sai ya juya ya nufi ɗakin da Maleekh yake.


A harabar hospital, Amal na tafiya a hanzari zuwa motarta. Amma kafin ta isa, sai ta yi kucuɓus da Ammy, Farha, Arfat, da Islam waɗanda yanzu suka shigo asibitin.

Ammy ta tsaya cak tana harararta, muryarta cike da izza ta ce:

"Me ya kawo ki asibiti? Shin baki ji na yi muku iyaka ba? Ko kina so ki kashe ɗana da hannunki?!"

Farha ta haɗe fuska, ta turo baki cikin raini ta ce:

"Eh mana! Ai yanzu Yaya Maleekh ya daina ƙaunarki. Ba zai taɓa mu’amala da karuwa ba, don karuwai kawai suke zubar da ciki a club!"

Amal ta tsaya kyam, sai ta saki murmushin takaici. Ta juya kai a hankali ta dubi Farha da idanu masu ƙarfi sannan ta ce:

"Haka kuma ba zai taɓa mu’amala da yar shaye-shaye ba."

Farha ta ɗaga hannu cikin hargowa za ta mari Amal. Cikin zafin nama Amal ta cafke hannunta da sauri, tana murɗawa kaɗan har sai da Farha ta ji zafi. Idanunta sun canza launi zuwa ƙiyayya, muryarta a tsanake take faɗin:

"Kada ki sake taɓa ni Farha. Idan kika kuskura, sai nayi gutsi-gutsi da yatsun ki nan take."

Arfat ta ɗan ja da baya tana kallon Amal da mamaki. Islam kuwa ta runtse baki tana ƙoƙarin boye murmushinta.

Ammy ta katse su da tsawa:

"Enough! Warning na ƙarshe nake baki Amal, ki fita daga rayuwar ɗana. Bana son sake ganin ki kusa da shi!"

Amal ta ja dogon numfashi, ta ɗan yi shiru kamar wacce ke tunani. Sannan ta ɗaga ƙafa ta taka gaba, ta tsaya a gabansu cikin ƙarfin hali, muryarta na rawar zuciya cike da tabbaci take faɗin:

"Ammy, sai dai idan Maleekh ne ya mutu, ko ni na mutu, amma ƙaddara ta riga ta haɗa mu. Kuma ƙaddara ba a goge ta da kalma, a rubuce take a littafin Ubangiji."

Ta wuce su kai tsaye, ta buɗe motarta, ta shiga. Ta kunna engine, a ɗari ta bar hospital ɗin ba tare da ta sake waiwayen su ba.

Ammy ta tsaya kallonta da tsananin haushi, har sai da motar ta ɓace daga gani.
Farha ta harare Amal cikin ƙiyayya tana turo baki, tana huci ta ce:

"Tabbas dole mu kawar da wannan yarinya daga rayuwar Ya Maleekh, kafin ta kashe shi da hannunta."

Islam kuwa ta kasa ɓoye murmushi, ta yi gaba ta bar su a tsaye.


☆☆☆☆

Abba yana shiga cikin hospital, zuciyarsa na tunani akan yarinyar da ya gani a corridor. Ya ji kamar akwai wani abu a tattare da ita, baƙin cikin da yake ɗauke da shi ya ratsa shi sosai.

Yana shigowa ɗakin Maleekh ya tarar da shi kwance, har yanzu bai farfaɗo da kyau ba, idanu a lumshe, numfashi a sarƙe. Likitoci sun fito daga emergency room sun ce a barshi ya samu hutu.

Abba ya zauna a gefen gadonsa, ya riƙe hannunsa da ɗumin ƙauna. Idanunsa suka kaɗa da hawaye, sai ya ce cikin sanyi:

"Yaro na… Maleekh. Ka tashi ka ga yadda kake jefa mu cikin tashin hankali. Ni mahaifinka ne, kuma na rantse da Allah, ba zan taɓa bari a tilasta maka abin da ba ka so ba. Duk yarinyar da kake so, zan tsaya a bayanka."

Ya yi shiru, ya goge idonsa. Sai kuma ya sake magana cikin tausayi:

"Ka san meye ɗana? yanzu na haɗu da wata yarinya a corridor. Na ji tausayinta. Amma ban san wacece ba. Sai kawai zuciyata ta ce, wannan yarinyar akwai wani abu mai girma a ranta. Kamar ƙaddarar rayuwarka tana haɗe da ita… Amma Allah ne masani..."

Maleekh ya motsa a hankali, kamar yana jin maganganun. Ya ɗan buɗe ido kaɗan, hawaye suka gangaro masa, amma bai iya magana ba.

Abba ya matse hannunsa da ƙarfi ya ce:

"Ka kwantar da hankalinka ɗana, Allah zai baka mafita. Na fasa, babu wata yarinyar da zan saka ka aura. Babu tilas. Zan tsaya a bayanka da gaskiya."

Ya ji motsin ƙofa. Sai ga Ammy ta shigo tare da iyalanta. Ammy ta tsaya cak, ta hango Abba yana riƙe da hannun Maleekh. Fuskar Abba ta nuna rashin jituwa.

Abba ya dubeta da ido cike da gargaɗi ya ce:

"Kina ji ko? Na ce babu tilas ga ɗana. Na gaji da wannan mulkin da kike yi na rashin hankali. Ki bar wannan doka taki, saboda wannan ɗan ba naki bane ke kaɗai. Shi ɗana

38 / 82