Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   63 / 82

186K to 189K   out of 244.2K words

yanzu. Ban gani ta dawo ba.”

Farha ta ce da mamaki:

“Ba yanda za'ayi Ya Maleekh ya tsaya a waje ba tare da shigo wa gidan ba… wannan abin akwai matsala.”

Mai gadi ya buɗe musu gate.
Suka fita, waje wayam. Shiru. Hasken fitullun titi kawai ke haskawa.

Suka dawo cikin gidan, zuciyoyinsu na bugawa. Amal ba ta dawo ba.
Haka suka yi ta ƙira, har wayarta ta daina shiga gaba ɗaya.

A cikin daren kafin Asuba misalin ƙarfe 3, Inna ta fito daga ɗaki da tsoro a idonta jin hayaniya..

“Wai menene ke faruwa?”

Farha ta ce cikin kuka:

“Tun jiya da daddare Amal ta fita, bata dawo ba har yanzu.”

Anan aka ƙira Abbah, aka sanar masa.

Abbah ya ƙira Maleekh, ya tambaye shi cikin tashin hankali:

“Maleekh, ina Amal take? Ya zaka ɗauke ta ba tare da ka sanar ba?.”

Maleekh ya amsa da muryar bacci:

“Amal kuma? Wallahi bayan mun rabu a walima ban sake ganin ta ba. Na shiga ɗakina kai tsaye bayan na dawo. Me ke faruwa ne?”

Kowa ya rikice. Cikin mintuna kaɗan gida ya cika da hayaniya, kukan mata da ruɗanin dangi.

“Amarya ta ɓace! Amarya ta ɓace fa a daren daurin auren ta!”

A daren Abbah da Maleekh suka zo gidansu Amal..

Mai gadi yana ta rantsewa:

“Ni wallahi ta fita da kanta, motar baki ce kawai na gani.”

Abbah ya riƙe kai yana cewa:

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… Amal fa yarinya ce mai kamun kai… wa zai yi haka?”

Maleekh kuma yana tsaye, a filin gidansu Amal da Abbah da kowa da kowa.
Zuciyarsa na bugawa cikin tashin hankali, bai san ko mafarki yake ba ko gaskiya.

Daren farin ciki ya koma daren kuka.
Amarya ta ɓace a daren kafin ɗaurin aurenta.
Gobe da safe, duniya za ta firgita.

Da safe gari ya waye cikin tashin hankali da hayaniya.
Labarin bacewar Amal, amaryar da za a ɗaura aurenta yau, ya baza ko’ina.
Daga unguwa zuwa social media, daga bakunan dangi har zuwa gidajen makwabta kowa na magana:

“Amarya ta ɓace kafin ɗaurin auren ta!”
“Wai me ya faru ne?!”

Gidansu Amal ya cika da jama’a, wasu suna kuka, wasu suna addu’a.
Abbah ya ƙira Maleekh, yana faɗin cikin tashin hankali:

“Ka ƙira ‘yan sanda yanzu, ba za mu zauna mu jira ba. Dole a bincika ko ina!”

A Ofishin Tsaro

Maleekh yana zaune cikin tashin hankali da damuwa, idonsa ya kumbura saboda rashin bacci.
Jami’an tsaro suna zagaye da shi a ofishin CCTV, ana kallon footage ɗin gidansu Amal.

A screen ɗin aka ga Amal ta fito daga gidan da kanta, cikin doguwar riga, ta tsaya a bakin get.
Ta yi magana da mai gadi, sannan ta nufi wata baƙar mota mai gilashin tint.
Ta buɗe motar da kanta ta shiga, ba wanda ya ja ta ko ya tilasta mata.

Jami’an tsaro suka kalli juna.
Ɗaya daga cikinsu ya ce,

“Gaskiya, daga yadda ta fito da kanta, wannan ba sacewa bace. Wannan alama ce ta wanda aka ƙira a waya.”

Wani jami’i ya ƙara cewa,

“Yuwuwar saurayinta ne ya ƙira ta. Yana waje, sai ta fito.”

Maleekh ya cije leɓensa yana duban screen ɗin da idanu jawur.
Ya ce da mai sarrafa CCTV:

“Please, ɗan dawo baya. Inason duba wani abu kafin ta shiga motar.”

Aka dawo kaɗan, sun ga lokacin da Amal ta ɗaga kanta sama, ta dubi CCTV camera kafin ta shiga motar.

Kowa ya yi shiru.
Sai Maleekh ya furta cikin ƙasa-ƙasa:

“Ta san ana kallonta... ta kuma san za a ga wannan... Amma duk da haka ta tafi.”

Wani jami’i ya ce cikin sanyi:

“Yallabai, wannan ai kamar ta tafi da niyyarta ne. Ba alamar karfi ko tsoro a jikinta.”

Maleekh ya dafa kansa, sannan cikin ƙarfi ya ce:

“Enough! Ku bar komai. A janye ƙarar. Idan da gaske sace ta akayi, da wata alama za ta nuna. Wannan dai ita ce ta shirya tafiyar.”


Ya tashi tsaye, ya dube su da idon da ke cike da ɓacin rai.

“Munafurcinta ne kawai. Idan ta gama sharholiyarta, zata dawo kamar yadda ta tafi.”

Jami’an suka kalli juna cikin mamaki. Amma babu wanda ya ce komai.


A gida kuwa, Abbah, Inna, Farha, Ammy da dukkan dangi sun hallara.
Kowa na jiran zuwan Maleekh da wani labari.

Inna tana kuka sosai, ta miƙe tsaye cikin tashin hankali, ta damƙi rigar Farha tana faɗin:

“Da haɗin bakinki kika sa aka sace mun Amatu na ko? Ki gaya min gaskiya a gaban kowa! Daman tubarki ba gaskiya bace! Na san halinki!”

Farha ta ruɗe, tana kuka tana cewa:

“Wallahi Inna, bana da hannu! Tallahi bana da hannu akan bacewar Amal! Na tuba, amma wannan ba laifina bane!”

Abbah ya matsa kusa da Inna ya ce cikin tausasawa:

“Kinga Mama, ki bari ta sake jikinta. Babu tabbacin haka. Mu saurare ta.”

Ya juyo ya kalli Farha cikin nutsuwa:

“Ki gaya mana gaskiya, Farha. Shin da haɗin bakinki aka ɗauke Amal?”

Farha ta share hawayenta, ta ce da rawar murya:

“Wallahi Abbah, ban san komai ba. Ni yanzu nayi hankali, wallahi zuciyata tsaf, bana da hannu a bacewar Amal.”

Ammy, ta ce cikin murya mai ƙarfi:

“Haba Alhaji! Ta ce ba ita bace, me yasa za ku tozarta yarinya haka a gaban jama’a? Ba zaku iya ɗora mata laifi ba akan abin da babu tabbaci!”

Inna ta ce cikin kuka mai ƙarfi:

“Na rantse da Allah idan ba ta da hannu, to waye zaiyi haka! Wayyo Amatu na... wayyo yarinya ta!”
Ta rushe da kuka, tana faɗin,
“Ai wannan bikin ya zama bakin ciki! Waye zai iya jurewa?”

Kowa ya kame yana ta sauraron ruɗani a cikin falon.
Sai ga Maleekh ya shigo cikin hanzari, fuska cike da ɓacin rai.

Kowa ya juya yana kallonsa.
Sai shiru ya mamaye falon gaba ɗaya.

Maleekh ya tsaya a tsakiyar falon, ya ce da murya mai sanyi.

“Farha bata da hannu a bacewar Amal.”

Duk suka juya suna kallonsa, suna jiran abin da zai ce.
Ya ɗauko laptop daga hannun ɗaya jami’i, ya kunna bidiyon CCTV.

A screen ɗin aka ga Amal ta fito da kanta, ta dubi sama, ta nufi mota, ta shiga da kanta.
Kowa ya kalli juna, wasu da hawaye, wasu da mamaki.

Maleekh ya ce cikin muryar da ta karye:

“Ga shaida. Ita da niyyarta ta fita daga gidan, ba wanda ya sace ta. Ta ƙi auren saboda ta tozarta ni. Ta bi wani saurayi daban.”

Wani ƙara ya fito daga bakin Inna:

“Karya ne! Ƙarya kake Maliku! Amal ba zata yi haka ba!”

Abbah ya ce cikin ɗaga murya:

“Kai Maleekh, kana hauka ne? Taya yarinya a daren aurenta zata bar gida da kanta? Tana so fa, ba wai tilasta ta akayi ba! Taya zaka ce ta tozarta ka?”

Maleekh ya ce cikin tsanani:

“Haka ta tsara makircinta! Da gaske bata so na. Ta yi wannan don ta ɓata min suna.”

Aisha, ƙawar Amal, ta ce cikin tsoro:

“Amma fa, kafin ta fita, mun ga text ɗinka a wayarta! Ka turo mata message cewa ta same ka a waje!”

Maleekh ya juyo da idanu masu cike da zafi:

“Ta nuna muku message ɗin ne? Ta nuna muku number da ya turo mata ne?”

Aisha ta girgiza kai, hawaye na gangarowa.

“A’a... bata nuna mana ba...”

Farha tana kuka, ta ce:

“Ni dai na tabbata akwai lauje cikin naɗi. Amal ba zata aikata haka ba. Tana ƙaunarka fiye da komai. Wallahi akwai wanda ya shirya wannan.”

Maleekh ya ja dogon numfashi, sannan ya ce cikin sanyi da raɗaɗin zargi:

“Ku bar komai. Kada kowa ya saka kansa a cikin damuwa. Idan ta gama shan sharholiyarta, zata dawo. Ba zan ƙara bata minti ɗaya daga zuciyata ba.”

Ya juyo cikin fuska mai cike da ciwo, ya fita daga falon, ya buga ƙofar da ƙarfi.
Shiru ya rufe wurin.

Kowa ya kame, zuciya cike da tambayoyi.

“Amal ta tafi da kanta?”
“Ko dai wani ya yi amfani da sunan Maleekh ne ya jawo ta?”

Duk suka kalli juna cikin shiru, duniya ta canja musu launi a ranar da ya kamata ta zama farin ciki...

《》《》《》《》

Haske kaɗan ne ya shigo ta ramin taga. A cikin ɗakin, Amal tana zaune a kujera; an ɗaure mata ƙafa da hannu, an toshe mata baki gam. Jikinta gabaɗaya na rawa, idanuwanta sun kumbura, hawaye suna zuba amma ba za ta iya ihu ba. A gefenta wasu gafza-gafza matasa ne, fuskokinsu a rufe da baƙar hula, hannayensu na riƙe da bindigogi. Tana ta kuka a sirrance..



Farha ta koma gidansu. Mahaifiyarta ta sata a gaba sai masifa take ta mata.
"Wallahi yanzu ban san wani irin rashin zuciya Allah ya ɗora miki ba Farha, saboda rashin zuciya har kije bikin Maleekh? Mutumin da ya gujeki ya nuna baya ƙaunarki har ki saura da shiga jikinsa, wani abun baƙin ciki har ki kwana a gidan su Amal? Mutanen da suka tozarta ki suka durkufa ki a gaban kotu suka sa kika zauna a prison amma har ki shiga jikinsu....
Gashi abinda ya faru ai, Ƴar su ta gudu sun makala miki sharrin ke kika sa aka sace ta, madalla gobe kya ƙara zuwa yanda suke ai.."


Farha tana kallon mahaifiyar ta, idanu cike da hawaye ta ce,

“Mom... anjuma ma zan koma gidansu Amal na ji ko an samu labarinta… wallahi ban san yanda matsalar take ba ..”

Hajiya Sa’adatu tana ɗaga murya ta ce,

“Kin yita marar zuciya! A haka zaki ƙare! Banza shashasha! Sai sun ƙara makala miki wani sharrin ai…”

A wannan lokacin Zayd ya shigo cikin falon, ya tsaya a tsakiyar falon yana kallon mahaifiyarsa da Farha ya ce,

“Ya! Meke faruwa anan?”

Farha ta miƙe cikin hanzari, ta juya zuwa ga Zayd:

“Yawwa Yaya! Dan Allah idan kasan kana da hannu a ɓatan Amal ka gaya mana! Ka fita daga rayuwarta! Nasan ba mai haka sai kai, daman ka ci alwashin raba soyayyarsu!”

Hajiya Sa’adatu ta juya zuwa ga Farha ta ce.

“Au ke! An ɗora miki sharrin sace ta, ke kuma kin zo ki ɗora wa ɗan uwanki sharrin sace ta? Me kike nufi kenan!?”

Zayd ya kalli mahaifiyarsa yana sarrafa fushinsa, ya juya zuwa ga Farha cikin tsananin iko:

“Na rantse idan ban kwaɗa miki mari ba, ki sanja mun suna! Kin raina mun wayo, ni da nake shirin kwamushe ta, kwatsam naji labarin bacewar ta, kuma yanzu kin zo kina mun wani irin question? ‘Yarinyar da akace tabi saurayinta. Kuma shima Maleekh ya tabbatar da hakan…”

Hajiya Sa’adatu ta ƙara murya da cewa:

“Ka rabu da ita! So take azo a kamaka! Ai idan zaka ji tawa, kawai ka nemi wata! Amma wannan kam ta gama amfani...”

Farha tana kuka, ta ja numfashi mai ƙarfi tare da faɗin:

“To dole na yi zargin haka… saboda ku kuka yi silar hatsarinta sannan kuke shirya kashe ta! Duk naji komai ai.. ”

Hajiya Sa’adatu ta tsaya, kirjinta na bugawa da ƙarfi, ta kalli Farha da mamaki da fushi lokaci guda ta ce:

“Ke! In ƙara jin wannan maganar ta fito daga bakin ki wallahi sai nayi mungun sa6a miki, wawuya kawai...!”

Farha ta ru ga da gudu saman upstairs yanda ɗakinta yake...


Hajiya Sa’adatu ta riƙe ƙirji tana kallon Zayd ta ce

"Ka duba yarinya zata jawo mana bala'i?..."


Bayan Sati guda...

Yanda Amal take a wannan karon an rufe mata fuska gaba ɗaya.
Wani hamshakin mutun ne mai tafiya akan iska ya fito daga cikin tsararren motarsa. Yanayin tafiyarsa kasan handsome guy ne, yana tafiya yana zukar shisha.
Bodyguards suka yi escort ɗinsa har ciki yanda Amal take.
Yana shiga ya tsaya a gabanta ba tare da yayi magana ba yayi alama da hannu cewa 'a miƙo masa wayarta..'

Hakan akayi ya karɓa ya buɗe wayar sannan ya shiga wurin message ya goge saƙon da aka turo mata, ya shiga wurin Gmail ya goge domin yasan kan wayar duk abinda ya shigo cikin wayar sai yayi saving a email...

Sannan ya kashe wayar ya bayar akan a cigaba da riƙe wa...
Ƙerarren mutu yana tsaye, komai nashi a tsare, yatsun hannayensa a jere da zobina kala-kala, ga hannun farin tas irin na ƴan hutu. Ɗayan hannun yana riƙe da shisha.
Ya durƙusa a gaban Amal da fuskarta yake a rufe ga baki a toshe, hannaye da kafafuwa a daddaure....
Haka yake zuƙo da hayaƙin shisha yana busa mata akan fuskar da yake rufe...
Ya gama yin sa ba tare da ya furta komai ba, daga bisani ya manna mata kiss akan goshi sannan ya miƙe ya fita. Bodyguards suna biye dashi a baya, wasu kuma sun cigaba da tsaya wa a gun da Amal take ɗaure...
Shiga tsararren motarsa ya yi, ya zauna a backseat sannan security yayi driving ɗinsa.
Sauran Bodyguards kuwa suka tsattsaya suna gadin dajin...


(Ni iya ƙafafunsa da hannayensa zuwa wuya na gani 😄 ban ga fuskar ba balle nayi muku gulma 🤭😝😝....)

AMMA ZAN BADA CHANKI-CHANKI!... DUK WANDA YA CHANKI DAIDAI ZAN MASA KYAUTA MAI TSOKA 🤣🤣🤣🤣

SHIN WAYE????.....


*_NEXT NEXT NEXT_* ...


asmeetahwriter✍️

*🎤AMALEEKH🎤*


*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.


*Writing and Storytelling By*

Asma'u Muhammad Auwal

Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*

*MARUBUCIYAR:*

*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*

Bauchi State Nigeria.

*WhatsApp 09065443871*

Follow my channel 👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


BOOK ONE page 73 to 74

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹


Sati Biyu Bayan Bacewar Amal

Gidansu Amal ya koma gidan shiru.
Sai ƙarar agogo da ke bango shi kaɗai ke yi, tik...tik...tik...
Gidan da yake cike da dariya, kiɗa da annashuwa, yau ya koma gidan jimami.

Inna ba ta da wani natsuwa. Ba ranar da zata faɗi, ba ta ambaci sunan Amal ba.
“Ya Rabbi... ina jikata? Me ya same ta? Me Amal ta yi har ta cancanci haka?…”
Hankalinta ya tashi sosai, har ta ɗan rame. Idanunta sun kumbura da kuka, jikinta ya yi sanyi kamar mara rai.

Duk lokacin da zata yi sallah, sai ta roƙi Allah cikin kuka:
“Ya Allah ka dawo min da Amatu ta, ko da matacciya ce kawai in ganta in saka ta a idanuwa na...”

Abbah ya dage sosai. Ya kasa kwantar da hankalinsa, kullum sai ya nufi ofishin ƴan sanda.
Kusan kullum sai an nemi wayar Amal ko za'a samu damar yin tracking ɗin wurin da take amma lambar kullum “The number you have dialed is not reachable at the moment…”
Ƴan sanda sun bazama suna bincike daga CCTV har zuwa makwabta, daga motar da ta ɗauke ta, har zuwa duk inda ake zargi.
Sun saka hotonta a gidan rediyo da talabijin.

“Wannan yarinya mai suna Amal Abdulsamaad, shekaru 22, ta ɓace tun ranar walimar bikinta. Duk wanda ya ganta ko ya san inda take, a tuntubi ofishin ƴan sanda mafi kusa.”

Kowa ya ji labarin.
Mutane suna ta fassara lamarin da zato..

“Wata kila saurayinta ta bi...”
“Ko an sace ta ne saboda kishi...”
“Ko dai akwai makirci a tsakanin danginsu…”

Amma Inna ta san jikarta ba irin waɗannan mata bace. Ita dai kuka kawai ta iya sai addu'a.

A ɓangaren Maleekh kuwa, babu alamar damuwa.
Yana kwance a ɗakinsa, ya jingina da gadonsa, yana kunne da headphones.
Gaba ɗaya ya cire kansa daga lamarin..
Ƴan sanda sun zo har gida, amma bai damu da su ba.
Idan Abbah ya ƙira shi, sai ya ce,

“Amal dai ta bi hanyar da ta zaɓa. Ina fatan tana jin daɗinta.”

Kowa ya daina gane Maleekh..

Duk san da akayi masa maganar Amal sai ya ce

“Inda ta je, ta sani. Zan jira ranar da gaskiya zata fito..”

🕯️

Mutanen da suka zo daga Borno da Kaduna sun koma gida.
Gidansu Amal ya watse.
Sai Inna da ƴan aiki, kowa ya koma yanda ya fito.
Inna kullum tana zaman jiran saƙo. Duk lokacin da taga motar da ta tsaya a bakin titi sai ta miƙe da sauri, tana cewa:

“Ko Amal ce? Ko labari ne daga gareta?”

Sai dai kullum amsar duniya ɗaya ce, shiru.

Abbah yana zuwa kullum da safe, yana bata haƙuri da cewa:

“Ki daure, Mama. Allah yana gani. Insha Allahu, Amal zata dawo lafiya.”

Inna ta share hawaye, ta ce da murya mai rauni:

“Alhaji, ni dai bazan daina addu’a ba. Allah ya dawo min da jikata, ko da a mafarki ne.”


☆☆☆☆☆

Haske ɗaya kacal ne ke fitowa daga ƙaramin rami a bango, yana zana layin fuskokin mutane da inuwa.
A cikin ɗakin, Amal tana zaune a kujera; an ɗaure hannaye da ƙafafu da igiya mai ƙarfi. An toshe mata baki, sai ƙanƙanin numfashin da take fitar wa. Gashin kanta ya zubo gaba ya rufe mata fuska...

A kusa da ita, wasu matasa uku ne, fuskokinsu a rufe da baƙar hula, hannunsu riƙe da bindigogi, wasu kuma suna riƙe da wayoyi. Sun zauna kamar suna tattauna aiki, amma a kowane lokaci suna duba Amal kamar dabbobi cikin yunwa...


Jagoransu ya zauna a kan kujerar kusa da ita, ya buɗe kwalin abinci, ya ɗan ciro lemo a leda. Ya dubi Amal a hankali, murya tamkar goge tabo,

Jagoran ya ce, “Kar kina jin kunya, yarinya. Wannan ba kuɗin banza ba ne. Aiki ne kawai. Ki yi shiru, ki zauna da haƙuri, za mu juya miki labari.”

Amal ta lumshe ido, ta gwada motsa leɓe, ta ƙara yin ƙoƙarin faɗi wani abu amma gam ɗin baki ya hana ta..

Ya yi dariya mai ƙarfi sannan ya ce “A, kina ƙoƙarin magana ne? To dai ki tuna, komai zaki faɗa zai koma gefen mutumin da ya aika mu. Don haka shiru kawai.”

Ya ji wayarsa tayi ƙarar shigowar message ya duba sannan ya ce,
“Boss, client ya aiko saƙo yanzu: ‘Ku an kare guys domin kar ku bari bincike ya yo ta wurin ku, ƴan sanda suna kan bincike kar ku bari a same ta, ku shirya yadda za ku ɓoye

63 / 82