Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
ta kasa shiga tsakaninsu.
Nan take cacar baki ta 6arke, Amal da Inna suna mayar da martani cikin rashin mutunci. Sa’annan rikici ya tashi!.
Farha ta rufe Amal da duka lokaci guda, Arfat itama ta rufu kanta, haka suka kai mata duka da hannaye..
Amal tana ƙoƙarin kare kanta da ƙarfi, amma sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi. Duk da ƙoƙarin ta, haka suka kayar da ita ƙasa, suka ci gaba da dukan ta ba ƙaƙautawa.
Inna kuwa da ta ga haka, ta sa karfi ta shiga tsakani, tana kai musu duka itama duk da tsufarta. Ganin ba sa bi ta kanta ne yasa ta cafke Farha ta garzaya mata uban cizo akan nonuwanta.. 🤣🤣
Lokaci guda Farha ta saki ihu cikin zama ta ture Inna da ƙarfi, har sai da tsohuwar ta kife a kan kujera. Masu aikin gidan ne suka yi saurin ɗaga Inna cikin tashin hankali, suna ƙiran Amal da ta tashi ta karɓi ƴancin ta..
Amal kuwa tana ƙoƙarin miƙewa, tana mayar da martani amma duk da haka suka ci galaba. Farha da Arfat suka yi mata duka har sai da ta kasa tashi...
Islam dai tana tsaye gefe, zuciyarta ta riga ta ɓaci da tunanin:
“Idan Yaya Maleekh ya ji labari, shin wane hukunci zai ɗauka akanmu?”
Bayan sun gama dukan Amal, sai Farha ta ɗauki ƙarfen flower stand ɗin falon, tare da Arfat suka fara bugun plasman. Sai da suka farfasa gilashin nan baki ɗaya, suka bar shi a wargaje a ƙasa.
Daga nan suka kama hanyar fita cikin dariyar mugunta. Amal kuwa ta kwanta a ƙasa tana kuka, tana ihu cikin rauni...
Inna da zuciyarta ta ƙone saboda zafin ganin yadda aka rufe jikarta da duka, ta nufi kitchen da gudu, ta ɗauko wuƙa mai kaifi, ta fito da gudu tana bin Farha da Arfat tana faɗin:
“Sai na yanke muku wuyan ku yau! Ku tsaya in kun isa, dabbobin yara kawai, marasa hankali..”
Da ganin haka Farha, Arfat da Islam suka ruɗe da tsoro, da gudu suka fice daga gidan. Motarsu suka shiga cikin sauri, suna dariya mai cike da mugunta da rashin imani.
Inna ta tsaya a bakin get tana huci, ga wuƙar a hannu, tana faɗin:
“Wallahi sai Allah Ya isa tsakanina da ku!”
Falon ta koma cikin ruɗani plasman a wargaje, Amal a ƙasa tana kuka cikin jin raɗaɗin abin da suka mata, masu aiki suna ta duban ta cikin tashin hankali...
Inna tana huci, tana zazzaro ido da ƙarfi ta ce wa masu aikin gidan:
“Ku ƙira mun Maliku yanzu-nan! Yazo ya ga irin tashin hankalin da ‘yan uwansa suka kawo mana cikin gida.”
Ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗauki waya suka ƙira Maleekh.
A lokacin kuwa Maleekh yana mota, yana kan hanyar komawa gida... Amma da jin ƙiran gaggawa daga gidan Amal, zuciyarsa ta bada saƙo mai nauyi. Nan take ya juyar da motarsa cikin sauri ya nufi gidan Amal.
Da isarsa, ya tarar da tashin hankali! Ga Amal a ƙasan carpet tana kuka, jikinta cike da raunukan yakushi da duka, jikinta ya yi jawur abin ka da farar fata ga duk sun yayyaga mata kayan jikinta da ƙarfi.. Ga plasma falon a farfashe, wargajjen gilashi ya bazu a ko’ina...
Zuciyar Maleekh ta tsaya cak, ya zaburo yana tambaya cikin tashin hankali:
“Meya faru haka? Shin 6arayi ne suka shigo muku?..”
Inna, wacce ranta yake har yanzu tana huci, ta zaburo ta dubi Maleekh tana faɗin da tsawa:
“Ɓarayin ƙannenka marasa mutunci baaa! Sun zo nan suka yi wa Amatu dukan tsiya, sannan suka farfasa mana tv muna kallo! Wannan marar mutunci, yarinyar nan Fara, ta hankad’e ni da ƙarfi har sai da na kifu a kujera, da ba ƙaramin sa’a na yi ba, da karyewar wuyana kenan! To wallahi, Maliku, ko ka dakatar da su yanzu, ko kuma na ɗauki hukunci da kaina!”
Zuciyar Maleekh ta buga sosai. Ya sauƙe dogon numfashi, zuciyarsa ta yi nauyi. Ya rasa kalma da zai furta a daidai lokacin, domin wutar tashin hankali ta yi yawa sosai.
Sai ya durƙusa a gaban Amal, yana riƙe da hannunta, yana share mata hawaye cikin sanyin murya ya ce:
“Yi haƙuri Amal… ki yi haƙuri dan Allah.”
Hannunsa ya yi sanyi kamar ruwan sanyi a zuciyarta, duk da hawayenta basu tsaya ba.
Ya juya ya kalli Inna, shi ma a sanyaye ya ce:
“Inna, ki yi haƙuri… Ni zan gyara komai, ki bar komai a hannuna. Dan Allah ki kwantar da hankalinki.”
Sai da ya rarrashe su sosai, kafin Inna ta samu ta zauna tana huci tana girgiza kai.
A daren nan kuwa, Maleekh ya tabbatar da an kawo musu sabon plasma wanda ya fi wanda aka farfasa girma da tsada, domin ya gamsar da Inna da Amal, ya kuma dawo da nutsuwa a gidan.
Bayan ya tabbatar sun samu natsuwa, da kansa ya ɗauki motarsa, ya fita daga gidan Amal cikin damuwa. Kai tsaye ya nufi gidansu, zuciyarsa cike da tunani marar daɗi...
☆☆☆▪︎☆☆☆
Arfat, Islam da Farha suna zaune suna dariyar abin da ya faru, suna ta hira akan irin dukan da suka yi wa Amal. Har Arfat tana ɗaga hannu tana nuna yadda Amal ta faɗi, suna dariya kamar masu hauka..
Sai ga ƙarar motar Maleekh ya shigo cikin compound da ƙarfi. Zuciyarsa cike da fushi, fuskar nan ta kumbura kamar an hura wuta a cikinta.
Ko sallama bai yi ba, ya shigo falon da gaggawa. Kafin kowa ya yi wani motsi, sai ya rufo kan Arfat ya ɗago ta da ƙarfi ya zabga mata mari har sau biyar a jere!
“PAT! PATT! PATTT! PATTTT! PATTTTT!”
Arfat ta fasa wani irin ihu tana riƙe da kunci tana karkarwa...
Bai tsaya ba, ya juyo ga Islam, ya ɗago ta da mugun fuska. Da sauri Islam ta durƙusa tana kuka:
“Dan Allah Yaya kayi haƙuri! Wallahi banda ni… su Aunty Farha ne suka ce muje…”
Maleekh ya tsayar da hannun nasa yana huci, idonsa jawur, ta wani ɓangare baya son taɓa Islam domin kaf yafi ji da ita, jininsu yafi haɗuwa...
Farha da take zaune a gefe ta ga abin da ke faruwa, da sauri ta miƙe da niyyar guduwa. A fusace Maleekh ya kai mata harbi da ƙafarshi, ya canke ta kamar kwallo. Sai da tayi sama ta doki a ƙasa da ƙarfi...
Kafin ta samu daidaita kanta, ya ɗago ta a fusace tare da yin wurgi da ita da ƙarfi har sai da goshinta ya bugi a jikin bango, nan goshin ya fashe sai jinin da yake zubo wa nan take...
Arfat kuwa tana durƙushe sai ihu take, Maleekh ne ya ƙara ɗagota ya ɗaga ta sama kafin ya buga ta da ƙasa. Ihun ta ɗaya ya tsaya cak – ta sume!
Islam ta sulale ta shiga bayan kujera tana kukan razana, jikinta sai rawa yake kamar zata mutu..
Maleekh ya sake rufa kan Farha, ya ɗago ta ya ƙara buga kanta da jikin bango a karo na biyu. Jinin na ƙara zuba, ta saki ihu tana neman taimako...
A nan ne Ammy ta fito daga part ɗinta cikin razana, ta tsayar da kallon ta kan Maleekh!
A tsawace ta ce:
“Subhanallah! Maleekh!!! Wannan wanne irin hauka ne ka shigo da shi gidan nan?! Zaka kashe su ne saboda sun je sun taɓo ƴar gold? To ni na tura su, eh! Ni na ce su je suyi wa yarinyar can dukan tsiya, shine yanzu zaka zo ka kashe mun ‘ya’yana?!”
Ta nuna Arfat dake sume a ƙasa ta ce;
“Ka kashe mun yarinya saboda waccan matsiyaciyar ƴar talaka?! Ashe haka ƙiyayyarka ta kai?!”
Ta dubi Farha da jini ke kwarara daga goshinta tana kuka.
Nan ma Ammy ta ce:
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Matar da zaka aura kayi mata irin wannan mummunan duka na wulakanci? To wallahi, na rantse da Allah, gobe za a yi taron aurenka da ita! Ba wani shiri tinda kai ɗan banza ne! Kai ba ɗa bane da zan tsaya kallon abin da kake aikatawa!...”
Maleekh ya juyo a fusace, yana huci kamar wuta zata fito daga bakinsa ya ce:
“Ammy, ki saurare ni da kyau…! Wallahi sai dai a ɗaura auren da gawa ta! Ki je ki shirya jana’iza, amma ba aure da ni da Farha! Na tsani wannan yarinyar fiye da mutuwata..!!!”
Ammy ta zaburo, idonta cikin nashi, a tsawace ta ce:
“Kai Maleekh, Saboda wata ‘yar matsiyaciya ka juyawa mahaifiyarka baya? Ɗan banzan yaro kawai, sai ka auri Farha, ko da kuwa ta sanadiyyar haka zaka rasa rayuwarka! A gabana sai an ɗaura wannan auren..!”
Islam ta miƙe da sauri tana kallon Ammy jin furucin da tayi..
Maleekh jinjina kai ya yi yana murmushin dole ya ce:
“A gabanki da duniya gaba ɗaya, ba za a taɓa ɗaura auren nan ba! Wallahi Farha bata da wata nasaba da ni, domin ita ɗin maƙiyata ce! Duk inda Amal take, ita ce ƙauna ta, ita ce zuciyata ni da ita zan zauna har ƙarshen rayuwata..!”
Ya juyo yana kallon Farha wacce ke kuka ga jini duk ya ɓata mata fuska, ya ce:
“Ke kuma, ki ci gaba da shirinki, Amma wallahi zan nuna miki cewa ni ɗan halak ne, sannan ni ba ragon namijin da zaki raina bane, ki ci gaba da shishshige mun rayuwata wata rana wallahi sai kin rasa numfashinki ta sanadiyya ta...."
Har ya juya zai nufi part ɗinsa...Sai ya ji an ƙira wayar gida (telephone)..
Maleekh da sauri ya nufi wurin ya ɗaga ƙiran, jin ana ta ambatar.
"Hello Hajiya, Hajiya kina ji na?...idan kina ji na aikin Maleekh zai tabbata.."
Maleekh kallon Ammy ya yi tare da saka wayar a speaker..
Kowa yana ji, domin yana mamaki ne ta yanda aka nemi Ammy ta wannan wayar gida, ya ɗauka wani sanarwa ne, tin da shine namiji yanzu a gidan, Abbah baya ƙasar....Sannan ya ji an furta sunansa...
Ammy zaro ido tayi jin muryar Salamatu...
Salamatu ta ci gaba da cewa.
"Hajiya ni bana jin ki, idan kina ji na to na ƙira wayarki baki ɗauka ba shiyasa na ƙira wayar gidan nakin, nasan yanzu ke kaɗai ce shiyasa....na je na samu malamin nan akan batun haɗa Maleekh da Farha sannan na bashi sunan Amal ɗin da photonta, insha Allahu ba za ta kai next week a raye ba, domin sai ta sha mungun jinya kafin ta mutu....."
Maleekh zaro ido waje ya yi yana kallon Ammy..
Islam buɗe baki tayi tare da toshe wa da hannayenta biyu..
Arfat kuwa tana kwance a sume bata san halin da ake ciki ba....
Ita kuwa Farha dake bakinsu ɗaya da Ammy saita sunkuyar da kanta ƙasi...
Ammy kuwa kasa motsi ta yi, haka zuciyarta ke bugawa ta kasa cewa komai...
Maleekh da yake riƙe da wayar sai ya ci gaba da sauraron matar tana faɗin...
"Malamin ya mun lissafin cewa, kuɗin kawar da Amal zai kai kimanin 1.5...Sannan kuɗin haɗa soyayyar Maleekh da Farha 2.5 ne domin yace zasu rayu ne har karshen rayuwa...domin Maleekh zai rinƙa bin Farha kamar raƙumi da akala, soyayya kuma mai ɗore wa, amma ya ce dole sai kin je ke da kan ki, abu ne mai muhimmanci idan har kina son burinki ya cika, jibi da asuba ki shirya zamu tafi, kafin nan ya gama haɗa mana komai...."
Ammy a fusace ta je ta fisge wayar daga hannun Maleekh... A tsawa ce take magana da matar cikin wayar..
"Ke wata iriyar jahila ce, jaka! Dabbiya, ai ko meye kya bari muyi waya ata wayata tin da private secret ne, ko kuma ki zo ki sameni a gida, amma saboda ke jaka ce shine za ki ƙira ni a public phone? ni kaɗai ce a gidan? ina da yara fa, shin kin san waye zai ɗauka a cikin su? ko kuma a misali idan mijina ya ɗauka fa?..."
Matar ta ce
"Kiyi haƙuri Hajiya ai nasan Alhaji baya Nigeria shiyasa na ƙira a wannan wayar gida..."
Ammy ta daka tsawa da cewa:
"Yi mun shiru dallah, ko ma menene ai kya bari mu haɗu kafin muyi wannan maganar.."
Matar ta ce
"Au kina nufin ki ce yanzu ba ke kaɗai kika ji wannan sirrin ba?.."
Ammy ta ja dogon tsaki tare da kashe wayar...
Ammy a wayen ce ta kalli Maleekh tana huci ta ce:
"Maleekh! Na ga alamar shaidan ya rufe maka ido koh? Kan ‘yan uwanka zaka yi musu irin wannan duka kamar dabbobi? Wlh yau ka wuce gona da iri! Kai ɗan banza ne, kai mara mutunci ne!!"
Maleekh idonsa Kan ta ya ce:
"Ni ɗan banza ne saboda na kare mutuncin matata? Ko saboda na hana su cin zarafin yarinyar da nake so? Ke kika ƙulla komai Ammy! Ke kika sa su zuwa gidansu Amal su yi mata dukan tsiya? Har kika kai ga haɗa baki da boka wajen zubar da jinin marainiya?! Wlh ki sani, a wannan karon baza ki taɓa cin nasara a kaina ba! Boka? Boka Ammy?..."
Ammy tana nuna shi da yatsa ta ce:
"Maleekh, ka saurareni da kyau, ni ce mahaifiyarka, ni ce na haife ka, ni ce na raine ka! Amma saboda wata ƙaramar yarinya matsiyaciyar ‘yar jarida zaka zubar da mutuncin ‘yan uwanka da ni kaina? Ka duba Arfat nan! Ka buga ta har ta suma! Farha nan jini ke zuba daga goshinta! Sannan ka tsaya a gabana kana faɗa mun maganganu son ranka, wai wannan shi ne mutumin da nake ƙira ɗana?!"
Maleekh ya matso kusa da ita, muryarsa na rawa da fushi ya ce:
"Idan kina so ki sani Ammy, kina gab da zubar da mutuncin mahaifiya a idona in har kika ci gaba da zuwa wurin waɗancan dabbobin bokaye, wallahi ban taɓa jin haushin ki irin yau ba. Kin yi amfani ta hanyar boka wurin niyyar zubar da jinin mutum, zaki biya boka akan ya cutar da rayuwar yarinya, sannan kike so in auri wacce take son jefa rayuwarki cikin haɗari? Ta sanadiyyar wannan ballagazar ƴar shaye-shaye kike son ki tarwatsa rayuwarki saboda ita, Ammy?...To wallahi sai dai ranar mutuwata na ƙarshe zan bar Amal ta shiga cikin sharrin ku...!"
Ammy ta buge ƙirjinsa da hannuwa, tana ihun takaici tare da faɗin;
"Wayyo Allah! Kai ne kaɗai ɗan da na haifa zai zama abin kunya a duniya? kai ne kaɗai ka bijire mun, ka zubar da darajata saboda wata zabiyar yarinya? To ka ji da kyau, wallahi tallahi gobe za’a ɗaura aurenka da Farha, ko ka so ko kar ka so. Wannan magana ta ƙare!"
Maleekh ya ce:
"Wallahi sai dai a ɗaura auren da gawa ta!! Ke da Farha da kowa duka ku ji da kyau, wallahi bazan aure ta ba! Bana son ta, bana son ta, bana buƙatar ta! Idan kin nace, to ki shirya zaman makoki!!"
Ammy ta girgiza kai, tana hawaye na fushi ta ce:
"Ka faɗi haka ko Maleekh? To ka sani, daga yau kai ba ɗana bane! Kai ba daga cikina ka fito ba! Nayi Allah wadai da haihuwarka, wlh sai na nuna maka babu wanda zai fi ƙarfina! Amal zata zama gawa a hannuna, kuma zaka dawo hannuna ciki kuka!!"..
Maleekh girgiza kai ya yi cikin kuka ya ce:
“Ki ci gaba da shirinki, Ammy! Ban yi mamaki dan kin ce ni ba ɗanki bane, sannan kin yi Allah wadai da haihuwana, zuciyarki ta riga da ta dusashe, boka ya ɓata miki imanin ki, tausayina ya dusashe a ranki, kin nuna cewa Allah bashi da ikon komai sai boka, kin nuna cewa boka yafi Allah wanda ya halicce ki, a duniya kika tarar da boka, Allah kuma baki ma san yanayinsa ba, baki taɓa ganinsa ba ko a mafarki, ƙarfin ikonsa kawai kike ji da kuma abubuwan da yake aiwatar wa ba tare da ganinsa ba, amma duk da hakan baki ɗauki hakan a matsayin darasi ba....gaskiya ne, saboda Allah ya baki lafiya, wadata, dukiya shiyasa zaki saka masa ta hanyar yin shirka da kuma tsine wa ɗanki wanda ya halitta a cikin cikinki, ni ɗin fa kyauta ne wanda Allah ya baki Ammy..."
Haka yake kuka yana magana, gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, idanuwansa kamar jini tsabar jan da suka yi..
Ya ci gaba da cewa:
"Ammy! Wasu fa haka suke neman haihuwa amma Allah bai basu ba, sun nemi magani har sun gaji, sun roƙi Allah amma saboda ba wannan a cikin kaddararsu basu samu ba, amma ke Allah ya baki ni kuma iya nine namijin da Allah ya baki shine zaki yi watsi dani?...
Soyayyata da Amal kaddara ce ta Ubangiji, Allah ne ya ɗora mun sonta...
Idan na zaɓi matar aure bisa halal, ba tare da sa6a wa dokokin Musulunci ba, ba laifi nayi ba. Idan uwa ta tsine saboda haka, wannan tsinuwa bata da tushe, kuma zata iya dawo wa gare ta kamar yadda hadisi ya nuna...
Manzon Allah ﷺ ya ce:
“Ku guji tsinuwar iyaye, domin tsinuwarsu tana komawa ga wanda aka tsinewa kamar yadda kibiyar da aka harba take komawa ga mai harbawa.”..
Wannan yana nuna cewa, idan uwa ta tsine wa ɗa ba bisa hujja ba, Allah na iya karɓa saboda girman matsayin iyaye, amma kuma hakan na iya jawo mata alhakin da ba zata iya ɗauka ba..
Allah baya karɓar addu’a ta zalunci. Kuma wannan tsinuwa ba zata hana ƙaddarar Allah ba, domin aure da wanda ake so hukuncin Allah ne, ba wanda zai canza shi...
Ayar Qur’ani, Allah yana cewa:
“Babu wata masifar da za ta same ku face da izinin Allah. Kuma wanda ya yi imani da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah ne Masani akan dukkan abubuwa.”
(Surat At-Taghabun: 11)
A Hadisi
Manzon Allah ﷺ ya ce:
“Ka yi imani cewa abin da ya same ka, ba zai wuce ka ba, kuma abin da ya wuce ka, ba zai same ka ba. Alkalami ya riga ya bushe da abin da aka rubuta.”
(Tirmidhi Sahih)
Maleekh yana kai wannan kalaman, ya juya cikin sanyin rai, Ya bar falon, ya wuce part ɗinsa ba tare da ya waiwayi kowa ba.
Ammy, kama kanta tayi tare da dokuwa akan kujera tana kuka...
☆
Maleekh ya shige ɗakinsa. Zuciyarsa tana bugawa kamar zata fito. Kalaman Ammy suna maimaituwa a kunnensa..
Voice echo a cikin kwakwalwarsa:
"Kai ba ɗana bane… Kai ba daga cikin jikina ka fito ba… Nayi Allah wadai da haihuwarka!"..
Maleekh dafe kansa ya yi yana girgiza shi da ƙarfi.
Murya na rawa yake faɗin:
"Why Ammy…? 😭 Why Ammy!! Why Ammy!!!"
(Ciwon kai ya tsananta, a ruɗe ya miƙe tare da ɗaukar ƙarfen flower vase ya fasa babban mirror ɗinsa.. Glass ya tarwatse a ƙasa. Ya ci gaba da farfasa duk wani abu na glass a ɗakin, yana ihu kamar mahaukaci.)
Maleekh yana ihu, yana