Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   22 / 82

63K to 66K   out of 244.2K words

yayi shiru, ya ɗauki numfashi mai nauyi yana dubanta da ido kai tsaye, yana ji zuciyarsa na son faɗa mata gaskiya amma kalmomi sun makale...

Dakatawa yayi saboda kada taji haushi akan ya bayyana irin ƙaunar da yake yiwa fiancée ɗinsa...

Amal lumshe idonta tayi zuciyarta na bugawa, ganin Maleekh yana ƙoƙarin sanar mata cewa shine 'Leekh ɗinta..."


Sai ta ɗago idanunta a hankali, ta tsaya kallon shi, zuciyarta na cewa: “Shin zan iya furta masa cewa nine Fiancée ɗinka?…”

Muryar Maleekh ne ya katse ta da cewa.

"Yanzu zamu iya tafiya, amma ki sani… bazan taɓa barin ki ba, ko da duniyar nan ta ɗauka cewa mun rabu. Ki adana wannan magana a zuciyarki."

Amal ta kasa cewa komai, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Sai kawai ta ɗan girgiza kai, idonta cike da hawayen farin ciki da tsoro lokaci guda.

Ya kamo hannunta, suka nufi falo tare.

Bayan sun shiga babban falo, sun tarar da su Ammy, Farha, Arfat da Islam.
Wani murmushi mai cike da fifiko da kishi ya bayyana a fuskar Farha..

Farha ta haɗe fuska, tana tsaki sannan ta ce..

" Tafiya zakiyi Amal?, to ai kuwa gwara ki tafi domin nan ba wurinki bane. Allah ya raka taki gona, sannan Allah ya baki miji ɗan tasha kamar ke, kuyi rayuwar ƙasƙanci irin na ƴan tasha, ya kuma baku ƴaƴa masu irin tarbiyyarku na ƴan tasha…"

Amal ta juyo tana kallon ta sannan tayi murmushi tare da mayar mata da amsar cewa..

"Amin ya Allah tinda gashi nan a gabana..."

Tayi maganar tana nuna Maleekh..

Farha ta wurga mata harara tare da haɗiye maganarta..ganin zata raina mata hankali...

Ammy idonta akan Maleekh cikin isa da gadara ta ce


"Na gode da ka fahimce ni, Maleekh. Wannan ce dama ɗaya da zan tabbatar da kai ɗana ne nagari. Amal… Allah ya raka ki lafiya."

Amal ta sunkuyar da kai cikin kunya, zuciyarta na bugawa domin Ammy na mata gwarjini, amma sai taji hannun Maleekh ya ƙara matse nata da ƙarfi...

Har zasu juya sai ga Arfar ta wurgo mata jakar kayanta da tazo dashi, tana faɗin

"Tsaya ki ɗauki tsiyarki nan, shin awa zaki bar wannan kazantar kayan ki?..."

Amal sunkuyawa tayi ta ɗauki jakar..

Maleekh kuwa nuni yayi wa Arfat cewa
"Zai dawo zata shiga hannunsa..."

Arfat kukan shagwaɓa ta fara yi tana kallon Ammy, da sauri taje ta faɗa jikin Ammy tana shishshige mata kamar zata koma ciki, dake ita ce ƙarama..kuma ƴar auta a wurin Ammy, domin a wurin Abbah akwai ƙaramar Arfat ƙanwar A'isha...

Ba tare da wani ƙarin magana ba, suka fita. Maleekh ya ja Amal da kansa har zuwa mota.
Ya buɗe mata ƙofa cikin kulawa, ta shiga, sannan shima ya zagaya ya zauna a kujerar driver.
A nan security ya buɗe musu gate, suka fita a ɗari daga gidan...

Sunyi tafiya sosai kafin su fita daga unguwar Maitama..

Suna tafiya akan titunan Abuja cikin nutsuwa. Dukansu babu wanda ya ce komai, amma zuciyoyinsu suna ta magana, kowannensu yana ji kamar ana rura musu wutar soyayya..

Doguwar tafiya suka yi, sai dai ba su fita daga Abuja ba. Amal na sa ran tashar mota zai nufa, domin ta koma Kaduna. Amma sai taga ya tsaya a bakin wani tsararren gida mai katanga babba, cike da tsaro, ya fara hon da mota.

Bai ɗauki lokaci ba maigadi ya buɗe musu gate. Maleekh ya shiga ciki da mota cikin nutsuwa..

Amal ta zaro ido, zuciyarta ta tsaya cak. Wannan gida ya bambanta da duk wanda ta taɓa gani. Tsari ne na alfarma, gininsa na zamani, duk an zagaye gidan da tsararrun tiles, da manyan trees masu kyau da burgewa a cikin harabar.

Tana dafe da kirji, ta juya tana kallonsa da mamaki:

Cikin rawar murya ta ce

"Nan ɗin wani gida ne? Nifa so nake na koma Kaduna… nabar Inna ita kaɗai. Ka kuma ce za ka kai ni tashar mota…"

Maleekh bai ce mata komai ba, sai ya kashe motar, ya fito.
Ya zagaya ya buɗe mata ƙofar jikinsa cike da ƙarfi da izza, sannan ya riƙe hannunta.

Tana tsaye a inda take kamar an dasa ta, ya ja ta cikin ƙarfin ikon da yake da shi a kanta.

Maleekh da muryarsa da na cika da iko ya ce

"Ki tsayar da tambayoyin ki..."

Ya shigar da ita ciki.


Gidan ya cika da tsari irin na masu kuɗi. Dogayen glass windows suna kyalli da hasken, lambu mai kyau ya zagaye shi, flowers masu launi suna ta kaɗawa da iska, sai kamshin fresh roses da ya gauraye da iska. Amal ta tsaya tana kallon kowane ɓangare, zuciyarta na wani irin bugawa...

Da haka ya shigar da ita ciki, wani tsararren falo ne mai girma, ya tsaru sosai..

Maleekh ne ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon,
Amal cikin ɓacin rai take kallon Maleekh kamar zata yi kuka ta ce

"Wai me kake shirin aikata wa haka? na ce ina buƙatar komawa Kaduna, shine ka kawo ni wannan gidan? me kake nufi dani Maleekh? kana so aita zargi nane? baka ji abinda mahaifiyarka take faɗi akaina ba?.."

Tana cikin wannan masifar ne sai ga sautin takun ƙafafu daga sama. Amal ta ɗago ido tana kallon stairs ɗin dake zagaye da golden railing.

A hankali wata dattijuwa ta bayyana daga upstairs,
Tana sanye da dankararren less mai launin shuɗi da silver, an yi mata ɗaurin ɗan kwali mai kyau wanda ya ƙara mata ƙima, duk da tsufarta.

Amal ta tsaya cak. Zuciyarta ta buga. Ido ya sauƙa kan fuskarta da ta shafe shekaru tana gani, amma a yanzu ta canza ganinta a irin wannan gidan...

Cikin rawar murya ta furta:

"Inna?... Innaaaaaa!"

Ta ruga da gudu kamar yarinya, ta rungumi Inna gam a jikinta, hawayenta na zuba kamar fanfo...

Amal cike da mamaki da kuka take faɗin

"Inna! Taya kika zo nan Abuja? me yasa kika baro Kaduna?..."

Inna ta shafa kanta da hannunta mai sanyi. Ta yi murmushi, sai kawai ta ce:

"Ki tambayi Maliku mana..."

Amal ta janye jikinta kaɗan tana kallon Inna cikin mamaki.

Inna ta ci gaba da magana cikin natsuwa:

"Kin dai san tsufa baya barin mutum yayi surutu sosai. Amma ki sani wannan Maliku ɗin mutumin kirki ne. Tunda kika tafi Abuja, yasa can Kaduna ana kula dani: abinci mai kyau, ruwan sha mai kyau, sutura masu tsada. Jiya Jiya yasa aka kawo ni nan Abuja aka ajiye ni a cikin wannan gida. Yace gidan nan na mu ne…"

Amal ta juya a ruɗe tana kallon Maleekh da hawaye a idonta...

Maleekh ya miƙe daga kujerar da yake zaune, ya matso kusa da ita cikin natsuwa. Ya ce

"Amal… ba wai na ajiye ki a gidan mu ba ne kawai. Na yi haka ne saboda gidan da nake gina muku bai kammalu ba sai jiya. Aka kammala shi. Shi yasa na sa aka kawo Inna nan gidan domin nan gidan sadaukarwa ne. Hallak mallak naku ne. Ko da a misali mun rabu, kada ki taɓa tunanin za ki mayar mun da gidan nan."

Ya saka hannu cikin aljihunsa, ya fitar da wasu takardu. Ya miƙa mata da hannunsa cikin kulawa.

Sannan ya ci gaba da faɗin

"Ga takardun gidan. An rubuta shi da sunanki, Amal Abdulsamaad."

Amal kamar zata haɗiyi ranta tsabar farin ciki, haka take tsalle tana farin ciki haɗe da kukan farin ciki, kamar zata rungume shi domin sauran kaɗan ta rungume shi sai kawo ta juya ta sake rungumar Inna...

Tana faɗin
"Ya Allah! Na gode, na gode..!
Inna! Inna! Wannan duk ya faru saboda soyayya ne?!..."

Inna ta shafa kanta tana murmushi.

A wannan lokacin suka ji motsin mutane. Sai ga wasu dattijan mata biyu sun bayyana daga cikin corridor. Suna sanye da uniform masu tsabta, kowannensu da nutsuwa a fuska.

Maleekh ya nuna su da hannu.

Yana faɗin

"Waɗannan su ne masu aikin gidan gaba ɗaya. Su zasu kasance tare da ku, ki ɗauke su kamar uwaye."

Amal ta kalle su cikin mamaki da farin ciki. Idonta ya sake cicciko da hawaye.

A zuciyarta ta ce:

"Wannan Maleekh… ni kaina ban san me zan ce game dashi ba. Allah ya sani…"

Da sallama da girmamawa, dattijan mata biyun masu aikin gidan suka ƙaraso kusa da Amal. Dukansu suna ɗauke da murmushi irin na masu hidima masu gaskiya.

Ɗaya daga cikinsu mai ƙiba kaɗan ta yi gaisuwa cikin ladabi:

"Sannu da zuwa, Hajiya Amal. Munji daɗin zuwan ki. Daga yau za ki ɗauke mu tamkar ‘yan uwa. Ba aikin gidan kawai muke ba, muna nan ne don mu kula da ku da gaskiya da zuciya ɗaya."

Ɗayar itama ta ɗora da cewa:

"Ni sunana Goggo Rabi, ita kuwa wannan ita ce Goggo Hauwa. Mun daɗe muna hidima a gidajen manyan masu kuɗi a Abuja, amma yau wannan shi ne karon farko da muke jin daɗin zama gidan da ya dace sosai. Zamu kula da ke da Inna kamar iyayen mu. Ki kwantar da hankalinki."

Amal ta kasa boye farin cikinta. hawayenta na zuba cikin murmushi.

Amal ta ce

"Na gode sosai, Allah ya saka muku da alheri. Wallahi ban san yaya zan nuna godiyata ba… Amma zan ɗauke ku kamar iyaye na..."

Maleekh da ya tsaya gefe yana kallon ikon Allah, murmushi kawai ya yi. Bai ce komai ba sai ya ƙara jin daɗin ganin Amal cikin farin ciki.


Bayan sun zauna na ɗan wani lokaci, Amal ta fara nuna sha’awar ta ga dukkan tsararren gidan. Maleekh ya lura da hakan, ya miƙa hannu yana kallonta cikin kulawa:

"Zo, Amal. Bari na nuna miki gidan ki daga yau."

Ta yi dariya mai cike da kunya, ta miƙe ta kama hannunsa cikin nutsuwa. Suka fara zagaye cikin gidan.

→ Babban Falon Gida:
Babban falo ne mai faɗi da tsayi. An ƙawata shi da luxury Italian sofas, an jera su a geometric design. Babban chandelier mai sheƙi yana rataye a rufin sama mai tsawo, yana haskawa tamkar rana ta sauƙo. TV mai faɗin bango yana manne a gaban su tare da sound system mai cike da ƙarfi. Amal ta tsaya tana girgiza kai cikin mamaki.

Amal cikin zuciyarta ta ce

"Wannan gidan da kaɗan gidan su Maleekh ya fishi tsaruwa..."

→ Kitchen:
Kitchen ɗin kuma tsararre ne irin na zamani. Granite countertops, microwave, oven, coffee machine da duk wasu kayan girki na zamani suna cikin tsafta da tsari. Goggo Hauwa ta nuna mata kowanne bangare, tana cewa: “Nan ne gidan ki, duk abinda kike buƙata yana nan.”

→ Upstairs:
Suka haura bene, Amal tana jin ƙamshin flowers da aka tanadar a cikin hallway. A gefen hagu akwai guest rooms guda uku, kowanne da toilet. A dama kuwa akwai library mai ɗauke da littattafai daga turai har da na larabci, sai ɗakin hutawa da ya sha kayan alatu..

→ Bedroom ɗinta da aka tanadar.
A ƙarshe suka isa wani ɗaki mai kama da ɗakin sarauta. Bed ɗin king-size ne, an yi masa canopy da curtains masu siliki. Ɗakin ya sha kyawawan paintings, sai wardrobe na glass da aka shirya mata kayan da aka siya daga supermarket...

Amal ta tsaya tana rufe da fuska cikin farin ciki, hawaye na bin kuncinta cikin murmushi.

Ta ce

"Wannan duk saboda ni ne, ya Allah!..."

Inna ta shigo daga baya tana dariya, ta ce:

"Ki gode wa Allah, ki gode wa Maliku. Wannan duk bai yi miki komai ba idan kika cigaba da kasancewa mai kirki da biyayya."

Amal ta juya tana kallon Maleekh. Idonsu suka haɗu. Numfashinta ya tsaya cak. Taji kamar ta ce masa: “Kai ne Leekh ɗina.” Amma ta daure, ta janye idonta cikin kunya.

Maleekh kuwa ya juya da murmushi mai cike da ɓoyayyen nufi. A zuciyarsa ya ce:

"Kada ki manta, Amal… duk wannan kyautar, akwai fansa a bayan sa."....
NEXT NEXT NEXT...

asmeetahwriter✍️

*🎤AMALEEKH🎤*


*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.


*Writing and Storytelling By*

Asma'u Muhammad Auwal

Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*

*MARUBUCIYAR:*

*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*

Bauchi State Nigeria.

*WhatsApp 09065443871*

Follow my channel 👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


BOOK ONE page 25 to 26

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹


Bayan ya tabbatar da cewa Amal da Inna sun zauna lafiya a cikin sabon gidan da ya mallaka musu, Maleekh ya juya ya koma gida.

Zuciyar Ammy har yanzu cike take da nauyin bacin rai.

Da ya shiga falo ya tarar da ita zaune akan sofas tana fuskantar plasman. Sai da ya zauna a gefenta ya kama hannunta cikin ladabi sannan ya furta:

“Mom, ki yafe mun. Na ga halin da kika shiga saboda Amal, amma na tabbatar da cewa daga yau ba zan sake sa ki cikin kunci saboda ita ba..”

Ammy ta ɗago ido ta kalle shi, tana nazarin maganarsa.

“Kana nufin ba za ka sake ɗora ta a kan zuciyarka ba, Maleekh?”

Ya jinjina kai cikin nutsuwa, muryarsa na fita da yanayin rarrashi.

“Ina bada mahimmanci a soyayyarki Mom, wannan karon na yi abin da ya dace. Amma ki fahimce ni, ba zan iya rabuwa da ita ba. Ko da me zai faru, zuciyata ta amince da ita.”

Shiru ya ratsa tsakanin su. A zuciyar Ammy, akwai sassaucin rai, amma tunanin alƙawarin da tayi wa Farha na Aura mata shi sun riga sun yi katutu. Duk da haka ta ce da ƙasa-ƙasa:

“To shikenan, Allah Ya kyauta. Amma ka sani, idan ta ci amanarka… ba zan taɓa yafewa ba, tin da ka nuna ban isa na rabaka da Amal ba amma inaso ka sani cewa bazaka ƙi Auran Farha ba..."

Maleekh ba yanda ya iya haka ya tashi ya nufi part ɗinsa...

🌹

Tun daga wannan rana, soyayya mai zafi ta shiga tsakanin Amal da Maleekh.

Amal ta fara samun kwanciyar hankali, zuciyarta ta ji sabuwar rayuwa ta buɗe gare ta. Idan Maleekh bai zo ba, to tabbas za su yi waya har zuwa ƙarfe sha biyu na dare...


Sai dai… duk da wannan kulawa da gaskiyar soyayya da yake nuna mata, a zuciyar Maleekh akwai wani abu da ba ya iya fadar wa kowa. Duk lokacin da ya rungumu Amal cikin ƙauna, sai wani muryar zuciya ta yi masa ƙira:

“Ka tuna, wannan soyayya ba ta kawar da manufarka ba. Fansar ka har yanzu tana nan.”..


Bayan cika wata guda da zamansu a Abuja, soyayya ta fara ƙara ƙarfi tsakanin Amal da Maleekh. Duk da cewa akwai sirrin gida da bai bayyana ba, har yanzu babu wanda yasan Maleekh ya siya wa Amal gida...

A yau kuwa, Maleekh yana cikin ofishinsa, yana jingina da kujerar executive, yana kallon files a gaban laptop ɗinsa. Da Bluetooth a kunnensa yana waya da Amal, muryarsa cike da kasala ya ce:

“Amal, yau kam na wuni ofishin nan. Tun safe har yanzu ban motsa ba. Kuma fa yunwa kamar zata kashe ni.”

Amal ta yi dariya a ɗayan ɓangaren wayar, ta furta cikin shagwaɓar soyayya:

“Tin da kai baka iya jiran girkin wata mace sai nawa. To ka kwantar da hankalinka, bari na haɗa maka delicious food da hannuna, zan kawo maka yanzu.”

Maleekh ya rufe ido da murmushi, zuciyarsa na bugawa da farin ciki. Daman haka yake son ji domin yana son cin girkin Amal mai daɗin gaske...

“Yawwa tawan wallahi wannan shi ne burina. Ina jiran ki.”

Wayar ta yanke, shi kuma ya cigaba da kallon agogo, yana jiran zuwanta kamar wani yaro mai jiran a sauƙe abinci...


Bayan lokaci mai tsawo, sai yaji knocking a ƙofar office ɗin. Da kasala ya ce:

“Yes, come in.”

Ƙofar ta buɗe a hankali, sai ga Farha ta shigo cikin shigar riga da wandon jeans na kanty, ta sha kwalliya tana ɗauke da basket ɗin kulolin abinci. Ta yi kyau matuƙa, sai ƙamshin turare take...

Maleekh da ganinta sai ya miƙe tsaye, fuskarsa cike da mamaki da rashin jin daɗi.

“Farha? Me ya kawo ki nan?”

Farha ta ɗan bubbuga ƙafafunta, kamar wata yarinya mai jin daɗin shagwaɓa, sannan ta ce:

“Kai Ya Maleekh, kenam ba zan iya zuwa inda kake ba? Naga tun safe baka dawo gida ba, na ƙira PA ɗinka yace har yanzu kana office. Na san yunwa kake ji, shiyasa na haɗo maka girki na kawo.”

Ta miƙa basket ɗin tana murmushi.

Maleekh ya kawar da fuska gefe, zuciyarsa na tafarfasa ya ce

“Farha, ki koma da abincinki. Ni dai na ƙoshi. Kuma ban ce ki kawo min girki ba. Wane irin abu ne haka?”

Farha ta matso kusa, idonta cike da hawaye na shagwaɓa ta ce

“Haba Ya Maleekh, kasan ina sonka sosai. Ba zan bari ka zauna da yunwa ba.”

Maleekh ya dafe kansa da ɓacin rai ya ce

“Na ce ki koma da abincin nan! Ko yau na saba kaiwa wannan lokacin ban koma gida ba? Don Allah Farha ki daina tada mun hankali. Please join yourself.”

Ya ƙarasa yana ɗaga muryarsa...


Kafin rigimar ta lafa, sai suka ji ƙofa ta turo da sauri. Security ɗin ofishin ya shigo cikin ladabi ya ce

“Sir, akwai baƙuwa a waje. Ta ce tana da appointment da kai.”

Da zarar Maleekh ya ji haka, zuciyarsa ta yi tsalle, ya san Amal ce.

Ya ɗaga hannu yana nuna Farha da basket ɗinta.

“Daga yau ku daina bari kowa ya shigo mun office haka ba tare da izini ba. Ko wannan (ya nuna Farha), ko kuma waccan. Idan na ce ku bari ne za ku bari. Otherwise, kar ku sake.”

Security ya gyaɗa kai cikin girmamawa, sannan ya juya. Sai ga Amal ta bayyana a ƙofar ofishin, hannunta ɗauke da kulolin abinci, da murmushi a fuskarta.

“Assalamu alaikum.”

Cikin nutsuwa ta shigo, amma tana ɗaga kai ta kalli Farha tsaye, tana riƙe da basket ɗinta. Amal ta dakata cak, zuciyarta ta ɗan buga, tana kallon Farha da mamaki da tsoro a lokaci guda.

Farha ta haɗiye miyau, ta furta cikin ƙiyayya:

“Kai kai kai! Ashe wannan yarinyar bata koma inda ta fito ba? Wannan matsiyaciyar ƴar gari, ubanta me take a Abuja? Kenan Ya Maleekh har gida ka kama mata a nan Abuja?”

Amal ta runtse ido da ƙarfi, kafin ta buɗe baki, Maleekh ya furta.

“Farha, wannan bai shafe ki ba. Don Allah ki fita daga ofishina yanzu.”

Ya nufi Amal da murmushi, yana karɓar basket ɗin hannunta.

“You’re welcome abar ƙauna. Fatan kin haɗa min wannan girkin da ɗanɗanon ki.”

Amal ta yi murmushi a hankali, muryarta cike da soyayya:

“Na kawo maka irin wanda kafi so. Fatan zaka ci da ɗanɗano.”

Farha

22 / 82