Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   75 / 82

222K to 225K   out of 244.2K words

kuka da hararar Maleekh,
​Maleekh ya kalli video tas. Ya kalli Abbah Abdulsamaad (Mahaifin Amal) yadda yake magana da murya mai rauni. Duk da cewa bidiyon yana zargin mahaifinsa, Maleekh ya lura da wasu abubuwan mamaki waɗanda ba kowa ya lura da su ba.

​Abubuwan da Maleekh Ya Lura da su:

A lokacin da mahaifin Amal ke jawabi, Maleekh ya lura da yadda hannun Abbanta yake kaɗa yatsunsa a ɓoye.

​Yana ɗan girgiza kai, yana ƙibkibta idanu a wani yanayi na musamman.

​Maleekh ya fahimci cewa wannan alamar sirri ce, wanda ke nuna cewa akwai lauje cikin naɗi kuma an tilasta wa Abban Amal jawabin.
​Bayan ya gama kallo, ya zare memory ɗin, ya miƙe jiki a sanyaye..

​Amal ta kasa jurewa, tayi masa tambaya mai zafi, tana harararsa.

“To! Shin wata shaida ka samu? Kana so ka kare mahaifinka ne? To mahaifinka shine mutumin da ya kashe mun mahaifi!…”

​Maleekh ya tsaya cak! Wani mugun zafi ya kama shi a zuciyarsa saboda rashin yarda da zargin da take yi masa. Fushin da ya ji ya sa shi manta da rauninsa gaba ɗaya.

​A fusace ya darara mata tsawa mai ƙarfi, ya ɗaga mata hannu da cewa,

“Enough, you stupid girl!”

​Zuciyarsa ce take raɗaɗi kamar wuta. Nan da nan idanunsa sukayi jawur, yana kallon cikin kwayar idanunta kai tsaye!

​ “Ke, abun farin ciki ne a kama mahaifina da zargin kisa? Me yasa zai kashe babban abokinsa wanda yake alhinin rashinsa har yanzu? Shin meyasa zai ɗauke ki tamkar ɗiyarsa alhalin shi ya kashe mahaifinki? Kin taɓa samun farmaki ko hantara a wurinsa? Kin taɓa ganin wani sauyin fuska a tattare da shi?…”

​Amal ta yi shiru, ta kasa bashi amsa. Ta tuna da tausayi da girmamawar da Abbah Maleekh ya nuna mata.
​Maleekh ya harzuka da rashin amsarta da kuma zarginta na ƙarya. Ya daka mata tsawa da murya mai ƙarfi: “Answer me!”

​Amal ta tsorata da tsawar, ta fara hawaye ba zato ba tsammani.

​Maleekh ya fahimci cewa magana ba zai kai su ko'ina ba. Abbansa yana buƙatar ceto nan take.
​A fusace, ya yi wa su Islam hannu, ya tattara jariransa.

“Islam, Arfat! Ku biyo ni! Za mu nufi asibiti! Za mu ga Abbah! Kuma za mu gano gaskiya!…”

​Islam ta rungume Ar’y (Ar’haan), Arfat kuma ta riƙe Lihaam. Haka suka fita da gaggawa, suka bar Amal ita kaɗai a tsaye a cikin falon, zuciyarta cike da ruɗani da kuma nadamar zargin da ta yi.

Yayin da Maleekh da ƙannensa ke kan hanyarsu ta zuwa asibiti, Amal ta tsaya a falo, hankalinta a ruɗe. Ta kasa yarda cewa Maleekh ya dawo, kuma ta yi masa mugun zargi.

​Amal ta ɗauki memory ɗin da suka manta akan TV stand, ta saka a Plasman nan take. Ta fara kallon bidiyon cike da damuwa da kuma ruɗani. Tana maimaita kallon akai-akai, tana neman alamar makirci da Maleekh ya faɗa, amma ta kasa samun hujja daban mai ƙarfi.

​Maleekh da ƙannensa suka isa asibiti.
​Ammy tana zaune a bakin ɗakin Abbah cikin tsananin damuwa da kuka. Ganin Maleekh a tsaye, cikakke kuma ba tare da rauni ba, ya zama kamar abin al'ajabi a gare ta.
​Ammy ta taso da gudu ta rufo shi, ta rungume shi tana kuka mai tsanani.

​Muryarta na rawa, cike da murna da zafi ta ce. “Maleekh! Kaine ka dawo gare ni?! Na gode Allah! Na gode Allah da Ya dawo da kai! Na yi tunanin na rasa kowa!…”

​Maleekh ya rungumeta da ƙarfi yana faɗin, “Mom! It’s okay! Na dawo! Kuma Abbah zai tashi da yardar Allah! Ba za mu bar shi ba!…”

​Ammy ta ɗago, ta ga Islam da Arfat riƙe da tagwaye!

Cikin tsananin mamaki da rawar murya ta ce, “Yara na! Waɗannan kuma…? Ina uwar tasu?”

​Islam cikin jin haushin Amal ta ce, “Mun barta a gida. Ba za ta yarda ta zo ba.”

​Ammy ta yi shiru, ta fahimci cewa rikicin bidiyon ya raba kan Maleekh da Amal.

​Maleekh ya shiga ɗakin Abbah. Abbah yana kwance, ya ƙazantu da na'urorin jinya. An tabbatar da cewa zuciyarsa ta ɗan tsaya ne, kuma na'ura ce ke riƙe da numfashinsa. Likita ya sanar da su cewa zai ɗauki lokaci mai tsawo kafin ya farfaɗo.
​Maleekh ya zauna a gefen gadon, ya riƙe hannun Abbansa mai sanyi. Hawaye na zubo a idanunsa saboda rashin adalci da azabar da Abbansa ke fuskanta.

​Maleekh yana magana cikin raunanniyar zuciya.
“Abbah! Ba zan taɓa yarda cewa kai ne ka aikata wannan ba! An yi maka sharri a ƙasar nan, kuma an yi maka sharri a cikin zuciyar masoyiyata! Amma na rantse da Allah, za mu wanke ka! Zan yi amfani da kowane irin ƙarfi da Allah ya ba ni don in fito da gaskiya! Ka sani cewa yaran nan suna nan! Ba zan bari kaddarar cin amana ta raba mu ba!”

​Maleekh ya sumbaci hannun Abbansa, ya ƙuduri aniyar fara yaƙi da makircin duk wanda ya aikata haka..

​Bayan wasu awanni, Amal ta gaji da kallon bidiyo mara ƙarin bayani. Ta ƙuduri aniyar samo gaskiyar al’amarin da kanta. Haka ta koma gidanta tare da Inna.
Bayan ta isa,
​Inna ko kallonta bata yi ba saboda fushin yadda Amal ta zargi Alhaji Abdul-Majeed da iyalansa..

​Inna cikin sanyin murya ta ce, "Kin fasa tafiyar ne? Meyasa kika dawo? Ina jariran?”

​Amal cikin gajiyar zuciya ta ce,
“Suna wurin Maleekh. Ya dawo...”

​Inna ta zabura! Farin ciki ya shige ta! Ta san cewa yanzu Allah ya ba ta damar yin amfani da shaidarta ta gaskiya ga mutumin da ya dace..

​Inna ta zabura, ta yafa mayafinta ba tare da ko kallon Amal ba ta ce,
“Maleekh ya dawo? Yana ina?!”

​Amal ta bata amsa a takaice “Yana asibiti wurin Abbansa.”

​Inna ta fita a guje! Ta ɗaura niyyar sanar da Maleekh gaskiyar al'amarin. Ta san cewa Amal tana da ƙaramar ƙwaƙwalwa kuma ba za ta fahimce ta ba. Yanzu Maleekh ne shugaban gida, kuma shi ne wanda zai iya fahimtar komai...
_NEXT NEXT NEXT_

asmeetahwriter✍️

*🎤AMALEEKH🎤*


*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.


*Writing and Storytelling By*

Asma'u Muhammad Auwal

Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*

*MARUBUCIYAR:*

*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*

Bauchi State Nigeria.

*WhatsApp 09065443871*

Follow my channel 👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


BOOK ONE page 91 to 92

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹


A cikin Abuja, zanga-zangar ta yi ƙarfi saboda zargin Alhaji Abdul-Majeed da kisan kai. Hakan ya sa go-slow ya tsananta, kuma Inna ta makale a hanya.

​Amal kuwa ta damu matuƙa da jariranta da Maleekh ya riƙe, sannan ga Inna bata dawo ba. Tana ganin Maleekh ya ɗauke su don fansa saboda zargin da ta yi masa.
​Misalin ƙarfe 8 na dare, Amal ta nufi asibiti ganin bazata iya jure kwana ba tare da jariranta ba..


​A daidai lokacin da ta isa, sai ga hargowa! Wuta ta kama a wani ɓangare na asibitin. Makiyan Abbah ne suka turo 'yan daba don su ƙona shi gaba ɗaya.
​Mutane suna ta fitowa da gudu daga cikin asibitin. Ammy tana tura gadon da Abbah yake kwance kai, tana fitowa da gudu.
​Wani ɗan daba ne ya fito da gudu da jarkar petur (gallon of petrol) a hannunsa. Ya wurgar da ita a gaban Amal da ke tsaye.
​Amal ta ɗauki jarkar tana dubawa! Zuciyarta tana bugawa da mamakin dalilin da yasa za a ƙona asibitin!

​Dai-dai lokacin da Amal ke tsaye riƙe da jarkar petur, Maleekh ya iso da gudun gaske a motarsa.
​Inna ma ta iso a lokaci guda da mai Napep bayan sun samu wurin wucewa.
​Amal kamar wacce aka daskarar da ita, tana tsaye riƙe da jarkar petur a hannunta, tana kallon wutar da ke ci.
​Nan take, kowa ya zagaye ta!

​Inna cike da mamaki da zargi ta furta “Amatu! Yanzu ƙiyayyar taki har takai ki ƙona asibitin kowa-da-kowa ya mutu? Har zaki zo ki kashe Alhaji Abdul-Majeed?…”

​Amal ta zaro ido tana kallonsu! Ta kasa cewa komai. Makirci ya karya ta lokaci guda..

​Ammy tana kuka da mamaki ta ce, “Amal! Kin zo ki ƙona Abbanku? Saboda kina tunanin shi ya ƙona iyayenki? Wani irin zuciya ne da ke haka?…”

​Maleekh ya kasa magana! Zuciyarsa sai harbawa take da ƙarfi! Wani irin tsanar Amal ya shige shi! Ya tuna duk faɗan da suka yi, da yadda ta zargi Abbansa! Ya ɗauka ta shirya wannan ne don ramuwar gayya!
​Nan motar agaji na ruwa ta iso, aka fara kashe wutar.

​Maleekh ya tunkari Amal a fusace. Ya yi mata wani irin shaka mai ƙarfi, ya shake mata wuya sosai yana zaro manya idanunsa.

​“Macuciya! Kin zo ki kashe Abbana! Kin so ki hallaka iyalaina!…”


​Amal ta ɗage numfashinta! Da ƙyar take jan numfashi, tana riƙe da hannun Maleekh da yake sha'ke da wuyanta.
​Idanun Maleekh sukayi jawur saboda fushi da raɗaɗi. Motar ‘yan sanda (Police) ta iso nan take..

Daƙyar aka janye hannun Maleekh daga sha'kar da yayi mata, cikin fusata ya sake ta. Ya kalli ’yan sanda, ya yi umarni da ƙarfi cikin zafin rai.

​“Ita ta sa wutar! Tayi babban laifi! Don haka ina umartar ku da ku tafi da ita can Station! Zaman prison ya wajaba a kanta! Ku ɗauke ta!”


​Ammy cikin kuka ta ce, “Maleekh! Me kake shirin aikatawa!?”
​Maleekh ya ɗaga mata hannu, ya hana ta magana: “Mom! Abinda ya dace nayi! A tafi da ita!”
​Amal tana kuka, bakinta ya rufe, ta kasa cewa komai. Jami’an ‘yan sanda suka kama ta!
​Maleekh ya juya, ya kalli gadon da Abbah yake kwance ido a rufe.

​ “Ba shiri! Za mu canza masa asibiti! Ko ma ƙasar waje za a fita dashi! Gobe zan kai shi Hospital Ethiopia!” a cewar Maleekh.

​Ya yanke hukuncin kamawa da fitar da Abbansa daga ƙasar a cikin tsananin fushi da baƙin ciki, yana mai cewa Amal ce ta yi hakan. Ba tare da yayi bincike ba kawai hukunci ya yanke.



​Washegari da asuba, shirin Maleekh na fitar da Abbah zuwa Ethiopia ya fara. Ammy ta kasa yarda da yadda Maleekh ya yi wa Amal rashin adalci, har ya yanke mata hukunci ba tare da sauraro ba.

​Ammy cikin kuka da damuwa ta ce,
“Maleekh! Zaka bar ƙasar kuma Amal tana can a tsare! Kuma ga jariranta ko wata basu yi ba da haihuwa! Ya zakayi kayi haka? Wannan ba dabi’a mai kyau bace!…”

​Maleekh ya dubi Ammy. Zuciyarsa ta cika da tunanin cin amana da kisan kai wanda ya danganta wa Amal.

Cikin tsaurin fuska da yanke hukunci ya ce,
“Ba daɗe wa zanyi ba a can. Idan na kaishi, akwai manyan kwararrun likitoci a can da zasu kula dashi. Kwana biyu kawai zanyi na dawo. Kafin na tafi zan aiko wa yaran da madara mai kyau na jarirai. Ita kuma zata cigaba da zama a can cell!”

​Ammy ta sake faɗin damuwarta game da tagwayen da suke buƙatar nono na uwa.

​“Amma ai uwarsu tana raye, kuma suna da nono! Sai a rinƙa basu madara? Sun yi ƙanƙanta sosai!…”

​Maleekh ya girgiza kai, ya ƙuduri aniyar yin abin da ya yi “Kawai ki bar komai a hannu na! Kar ki damu! Amal daga Cell sai Prison na mata! Yara kuma ba yau ake haifan jarirai kuma mahaifiyarsu ta mutu ba! Zan siya musu madara mai inganci wanda zasu cigaba da sha! Innarta kuma zata dawo nan gidan saboda ta samu masu kula da ita! Ni yanzu zamu nufi Airport!”


​Ba tare da ɓata lokaci ba, Maleekh ya ɗauki Abbah cikin tsari mai kyau zuwa Filin Jirgi. An fita da Abbah a na'urar tallafin numfashi (life support), aka shiga jirgi mai zaman kansa (private jet) zuwa Hospital Ethiopia don kulawa ta musamman.
​Maleekh ya aika musu da madarar yara (Infant Formula) masu inganci da yawa don ci gaba da ciyar da tagwayen.

​Bayan Maleekh ya tafi, Inna ta dawo gidansu Maleekh kamar yadda ya umarta.
​Ammy ta tarbe ta da hannu bibbiyu..

An bata ɗaki na musamman..

​Inna (A Zuciyarta) tana maganar cewa
“Alhaji Wadata! Na san ka! Na san sirrinka! Yanzu Maleekh ya dawo, zan bashi dukkan abin da na gani a daren nan! Ba zan bari ka kuma hallaka wannan yaro marar laifi (Maleekh) ba!”

​Inna yanzu tana zaune tare da tagwayen da kannen Maleekh, tana jiran dawowar Maleekh don ta bayyana gaskiya...

🪸🪸🪸

Amal tana Station, inda aka sanya ta a cikin Cell (kurkuku na ɗan lokaci).

Washegari antashi da hukunta Amal.
​ƴar Sanda cikin tsaurin fuska da baƙin ciki take faɗin
“Ke! Har kina da ƙarfin hali zuwa asibiti! Ki nemi kashe mutumin kirki wanda ya ɗauke ki tamkar ɗiya! Ba zaki ga daɗi ba a hannun mu!”

​An yi wa Amal dukan tsiya! An horar da ita sosai saboda zargin kisan kai da kuma ƙona asibiti.
​Amal tana cikin azaba..


​Alhaji Wadata ya ji labarin ƙonewar asibiti da kuma kamawar Amal a matsayin wacce ta kawo wuta. Yayi farin ciki sosai.

​Yana faɗin cewa,

“Wannan shine tsari mafi sauƙi! Yanzu za a zarge ta da kisan kai da ƙonawa! Makarinta ma ya gujeta! Sun sauƙake mun aiki!”

​Ya kuma ji labarin cewa Maleekh ya tafi Ethiopia da Abbah..


Alhaji Wadata ya lura da tausayin Zayd da kuma yunkurinsa na son tona gaskiya. Ba tare da bata lokaci ba, ya sanya aka ɗaure Zayd a wani ɗaki na sirri a gidansa.

A ɗakin sirri yake kallo Zayd tare da faɗin.

“Ba za ka taɓa tona min asiri ba! Kai ma za ka shiga azaba har sai na gama da Maleekh da iyalansa!”


Shiri na gaba Alhaji Wadata ya nemi Malaminsa (bokaye) ya bashi Laya (sihiri) don rufe bakin dukkan shaidu waɗanda za su iya tona sirrinsa.
​Malami ya bashi laya mai tsanani....

A gidansu Maleekh kuwa, Inna tana zaune ita kaɗai a ɗaki tana tunanin yanda zata gaya wa Maleekh gaskiyar lamarin..
A Zuciyarta take faɗin,

“Za ni gaya wa Maleekh… Wadata ne!…” Ta yi ƙoƙarin buɗe baki “Mmm… mmm…” Bakinta ya kasa motsi!..


Bayan kwana biyu da dawowar Maleekh daga Ethiopia, ya yi amfani da ƙarfin ikonsa da kuma tasirinsa a cikin siyasa don shure ƙarar da ake tuhumar Abbansa da kisan kai. An rufe komai.
​Bayan ya huta a gida ya rungumi jariransa (waɗanda ke sanya shi cikin nishaɗi), ya nufi Station don ganin Amal...

Bayan ya isa.
​Maleekh ya tsaya a bakin Cell, tare da ƴan sanda biyu a gefensa. Yana ganin Amal a ɗaure, ga tabon dukan da aka mata a fuska da jiki..

​Maleekh cikin sanyin murya a tsanake ya ce, “Kun yi mata rauni sosai, hakan kuskure ne saboda macece! Amma abinda ta shuka, shi take girbewa! Ku ɗaga mata ƙafa saboda uwar ƴaƴana ce!”

​ƴan Sanda suka ce “Okay Sir, za a kiyaye.”

​Maleekh ya tambayi ko ta ci abinci, kuma aka ce A’a. Ya umarce su da su bata abinci nan take.

​Islam da Arfat sun zo tare da shi, riƙe da tagwaye. Sun tsaya a nesa don Amal ta ga jariranta daga nesa ba tare da an bata su ba.
​Ƴar sanda ta shiga ta ajiye mata kular abinci a ƙasa. Abincin shine farar shinkafa da mai da dakakken yaji, sai tattasai da attaruhu a roba daban mai zafi sosai.
​Amal tana zaune, ta dubi abincin sosai. Ta ɗago tana kallon Maleekh da rinannun idanuwanta (cike da azaba da jarumta).


​Cikin rashin kula da abincin, Amal ta miƙa hannu, ta ɗauki dogon tattasai mai tsananin zafi, ta kai bakinta tana taunawa a hankali! Sannan ta ɗauki attaruhu (hot chili pepper) tana ci.
​Islam da Arfat sun zaro ido suna kallonta! Ƴan sanda sun shiga mamaki! Duk abincin da aka bata tun kwana bakwai bata ci, amma yanzu tana cin kayan miya masu tsananin zafi!
​Ko zafi bata ji! Haka take cinye su, idonta akan Maleekh!
​Maleekh ya fahimci cewa Amal tana aiko masa da saƙon cewa tana da ƙarfin hali da jarumta, ba za ta rushe ba!

​Maleekh Ya yi murmushi a hankali sannan ya furta,
“Dakyau! Jaruma! Irin wannan jarumtar ai ko nima zan iya!…”

​Ya kalli ɗaya daga cikin ƴan sanda:

​“Ku miƙo mun tattasan da attaruhun nan! Nima na kwada jarumtar!”

​Aka miƙo masa tattasai da attaruhu a hannu. Yana kallon ƙwayar idanun Amal da sukayi jawur, ya sa attaruhu a bakinsa yana taunawa!
​Da hanzari ya tofar da na bakinsa! Ya fara shishshitu!

​Cikin ruɗewa da gigicewa yake faɗin “Ku ban ruwa! Ku ban ruwa! Kuyi sauri!…”

​Aka bashi bottle na ruwan sanyi. Ya kafa kansa ya fara gwangwada! Sai da ya ga bayan bottle ɗin, duk da haka bai daina shishshutun ba! Sai zaro harshe yake kamar tsohon maye!
​Arfat tana riƙe da Lihaam, sai kunshe dariya take tana kallon Maleekh! Islam kuwa ta ƙafe idonta akan Amal saboda mamaki da ƙarfin hali irin nata!
​Amal ko kibta ido bata yi. Ta cinye tattasai da attaruhun nan tasss!

​A hankali, cikin tsokana ta furta, “Akwai ƙari ne?…”

​Duk zaro ido suka yi suna kallonta! Ko irin shishshitun da Maleekh ya yi bata yi ba!

​Maleekh ya jijina kai cikin mamaki da girmamawa ga jarumtar Amal (amma ya ci gaba da nuna hukunci a zahiri).
​Ya miƙa wa ƴan sanda takardar Kotu na tura Amal zuwa Prison (gidan yari) na mata, inda zata cigaba da zama acan.
​Daga nan, suka juya suka tafi, suka bar Amal a Cell...

Bayan Maleekh ya dawo, ya yi amfani da ƙarfin ikonsa don sanyaya al’amarin zargin kisan kai a kan Abbah. A hukumance, an rufe ƙarar kuma Abbah ba ya cikin haɗari na kamawa a Kotu.

​A gida, Inna tana ƙoƙari sosai don gaya wa Maleekh gaskiya. Sau biyar kenan tana tare shi, amma sihirin Alhaji Wadata ya hana ta.
​Yau ma, kamar kullum, ta tsayar da shi zai wuce part ɗinsa.

​“Daman akwai maganar da nake so gaya maka dangane da wannan al’amarin…”

​Maleekh cike da mamaki ya ce, “Al’amarin ai biyu ne Inna. Akwai na Abbana, sannan akwai na Amal.”

​Inna ta ce, “Akan na Abbanka…”

​Ya ce, “To, ina jinki.”

​Inna ta tsaya, ta yi shiru. Ta kasa furta

75 / 82