Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
ambaton wannan batu a bakin sa, wallahi zan rubuta masa takardar kora a nan take. Na rantse da ikon Allah zan tabbatar da ya bar wannan campany ba tare da second chance ba!”
Ta ɗan ɗaga kai cikin izza ta ƙara da cewa:
“Kar ku manta, ko da ban mallaki kujerar CEO ba, yanzu ni ce assistant CEO. Kuma ikon ɗaukar hukunci a hannuna yake. Don haka kowa ya kashe wutar gabansa, ya kula da aikinsa. Ku tuna..."
Ta maida kallonta kan matan da ta kama tana cewa:
"Mata ne ku, ba ku san irin makomar da Allah ya tanadar ba. Kada ku yi min hukunci da sharri, domin yau ni ce, gobe wata ce.”
Ta ɗora glass ɗinta a idonta, ta juyo cikin izza ta nufi ƙofar fita. Takunta na ƙara amo a cikin shiru da kowa ya yi.
Sai ta ce kafin ta fita:
“Na gama magana. Ku tuna da abinda na faɗa.”
Ta fice ta nufi motarta.
Gaba ɗaya ma’aikatan suka tsaya shiru, suna kallonta cike da mamaki. Wasu suka lumshe ido suna cewa:
“Wallahi wannan yarinya ƙarfin hali gareta sosai. Duk da kuwa an yi mata sharri, sai ta tsaya ta kare kanta.”
Wani ya ce:
“Eh… wannan izza da kwarin gwiwa ba kowa ke da shi ba.”
Bayan Amal ta fice daga cikin campany cikin izza, harabar ofishin ta yi shiru kamar wuta ta mutu. Duk ma’aikatan kowa da abinda yake tunani, babu wanda ya iya sake yin magana.
Sai PA ɗin Maleekh, ya fito daga cikin corridor. Shi ya shaida komai tun lokacin da Amal ta tsaya ta tara ma’aikatan. Ya tsaya yana kallon fuskar ma’aikatan da suka yi ƙasa da kai cikin kunya.
Ya ɗan gyara murya ya ce:
“Kun ga wannan abin da ya faru yau? Wannan yarinya ta nuna muku cewa bata da rauni a zuciyarta. Duk wani sharri da za ku ƙirƙira mata, wallahi za ta iya fuskantarsa da ƙarfin hali. Idan har tana iya tsaya ta kare kanta haka, to ta cancanci a ƙira ta shugaba.”
Sai ya ɗan yi shiru ya kalli su biyun da Amal ta fallasa a gaban kowa.
Ya ce:
“Kuma ku, ku ji tsoron Allah. Wannan abu da kuka yi ba magana bace ta office. Aikin ku ne ya kawo ku nan, ba rayuwar wani ba. Ku ma ku iya tunanin kanku, me zai faru idan wata rana aka yi muku sharri irin wannan? Kada ku kuskura ku kuma.”
Daga nan ya ɗan juya yana kallon sauran ma’aikatan gaba ɗaya:
PA ɗin Maleekh ya ce:
“Na ga yawanku kunyi shiru, kun girgiza kai. Wannan darasi ne. Kar ku manta duk wanda ya ƙi yin aiki da hankali da mutunci, wallahi Amal ba zata taɓa bari ya lalata campany ba. Kuma ni kaina zan tsaya a bayanta.”
Ya jinjina kai ya ce a hankali:
“Ko da kuwa Maleekh baya nan, Amal ta riga ta tabbatar da kanta a matsayin mai ikon ɗaukar hukunci. Ku kiyaye.”
Sai ya juya ya koma cikin office ɗinsa, barin ma’aikatan da ke jinjina da cewa Amal ta nuna ƙarfin hali da cikakken iko.
Da dare bayan kowa ya watse daga campany, PA ɗin Maleekh ya ɗauki waya ya ƙira ɗakin asibitin da yake kwance. Bayan sallama da gaisuwa, aka miƙa masa wayar zuwa Maleekh...
PA ya ce:
“Boss, ina fatan jikinka ya ɗan sauƙa?”
Maleekh
Ya ɗan murmusa da rauni sannan ya ce:
“Muna nan, Allah na tare damu… Amma ka fadamin gaskiya, me yake faruwa a campany? Na ga har yanzu baku kawo mun daily report ba.”
PA Ya yi gyaran murya, zuciyarsa cike da damuwa ya ce:
“Hakane Boss… Amma akwai abu da na ga ya kamata ka sani kai tsaye. Yau bayan Madam Amal ta kammala aikinta, ta fito ta iske wasu daga cikin ma’aikatan suna gulmarta… suna cewa wai ‘yar club ce, da kuma zancen zubar da ciki. Boss, wallahi duk ma’aikata sun tsaya suna ji.”
Maleekh ya runtse ido, zuciyarsa ta sake raɗaɗi, amma ya ce a hankali:
“To, me tayi?”
PA ya ce:
“Wallahi, ta tsaya a gabansu cikin izza. Ta tara su gaba ɗaya, ta fallasa waɗanda suka fara gulmar, ta wulakanta su a gaban jama’a, sannan ta gargaɗi dukkanin ma’aikata cewa idan har wani ya sake taɓo wannan batun, zai fuskanci takardar kora. Boss, komai ta yi cikin natsuwa da ƙarfin hali.”
Shiru ya cika ɗakin, Maleekh yana maida numfashi da nauyi. Duk da jin haushin Amal da yake yi tun daga asibiti, zuciyarsa ta girgiza da jin irin tsayuwar da ta yi a kan mutuncinta...
Ya ɗago kai yana kallon PA ɗin da yake cikin call ya ce:
“Duk wanda ya sake gulmar Amal a campany, kai da kanka zaka rubuta mun sunansa. Ba zan yarda wani ma ya wulakanta ta a ofishin nan ba. Kowane mutum yana da kurakurai, amma wannan ba dalili bane da zai sa a raina assistant CEO. Kaji ko?”
PA da murmushi cikin girmamawa ya ce:
“Na ji sir. Zan tabbatar babu wanda ya kuma.”
Maleekh ya lumshe ido, zuciyarsa ta kumbura da abubuwa biyu: haushin Amal saboda sakamakon zubar da ciki da yake tunani, da kuma ƙarfin hali da ta nuna a bainar jama’a.
Ya ja numfashi a hankali ya furta:
“Amal… kin zame min raɗaɗi...”
Bayan PA ya katse wayar, Maleekh ya jingina da filo yana rufe idanuwansa. Zuciyarsa na juyawa tsakanin soyayya da ƙiyayya.
Sai ga Ammy ta shigo ɗakin da tray a hannu, ta kawo masa tea. Ta zauna kusa da shi tana tambayar:
“Ya jikinka ɗana? Har yanzu kana ɗauke da damuwa ne?”
Maleekh da murmushi ya ce:
“Alhamdulillah Ammy, jikina ya ɗan sauƙa sosai.”
Ammy ta ce:
“Toh Allah ya ƙara lafiya. Campany fa? Ban ji kana magana akai ba yau. Wane irin labari kake samu daga can?”
Maleekh ya buɗe ido ya dubeta, ya ɗan yi shiru kamar yana tunani. Sai ya ƙara gyara kwanciya, ya ɗan yi murmushi ya ce:
“Komai lafiya. Ayyuka suna tafiya yadda ya dace. PA yana kula da komai, babu wani rikici.”
Ammy ta gyaɗa kai cike da gamsuwa ta ce:
“Toh madallah. Kar ka damu da komai sai lafiyar ka. Ni dai har yanzu bana jin daɗin ganin waccan yarinyar (Amal) tana zagaye ofis ɗinka. Amma dai idan har kana bukatar hakan, zan tsaya a gefe tunda Doctor ya ce a bar ka cikin natsuwa.”
Maleekh ya ɗan saki murmushi marar sauti, zuciyarsa na motsi. Bai ce komai ba sai cewa da yayi:
“Na gode Ammy… komai zai zo daidai da iznin Allah.”
Ya rufe maganar da wannan, bai taɓa bari ta ji labarin abinda Amal ta fuskanta a ofishinsa ba. Ya ƙuduri aniyar boye komai daga iyayensa, saboda baya so wani ya ƙara wulakanta Amal a gabansa even da yake shi ma yana jin haushinta a zuciyarsa.
Sai dai zuciyarsa ta furta a ransa:
“Amal… duk da na tsane ki, bana son wani ya tauye mutuncinki.”....
_NEXT! NEXT!! NEXT!!!_
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 43 to 44
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Bayan tattaunawar da yayi da Ammy, an bar shi shi kaɗai a ɗakin.
Ya jingina da filo yana sauƙe ajiyar zuciya. Kalaman PA suna yawo a kunnensa:
“Madam Amal ta tsayar da ma’aikata gaba ɗaya, ta nuna musu ƙarfi da izza… ta gargaɗe su cewa idan aka sake maganar ta, zata kori kowa.”
Maleekh ya lumshe ido, zuciyarsa ta haɗu da soyayya da haushi.
Ya tuna result ɗin Amal, ya tuna rashin gaskiyar da yake zargin ta da shi, sannan kuma sai ya tuna irin ƙarfin zuciyar da ta nuna a campany, tana kare mutuncinta da mutuncin sa kai tsaye.
Hawayen takaici suka tsaya masa a ido, ya furta cikin zuciyarsa:
“Amal… me yasa kika zama min tamkar dafin da nake sha kullum? Duk da ina zargin ki, ban so wani ya kalle ki a matsayin marar mutunci.”
Sai ya runtse ido, yana jin ciwon zuciya da soyayya suna rikici a ransa.
Amal kuwa ta dawo da mota gida, ta shiga falon.
Inna na zaune tana duba TV, tana kallonta da idon da ya cika da zargi.
Amal da sallama cikin ladabi ta ce:
“Inna sannu da hutawa…”
Inna ta kawar da kai, da dariyar raini ta ce:
“Kin dawo kenan? Ko daga aiki kike, ko daga club ɗinki! Domin ai ban ga bambanci ba.”
Amal ta tsaya cak tana kallonta.
Ta ji kamar zuciyarta zata fashe, amma ta daure cikin nutsuwa ta ce
“Inna, na dawo daga aiki ne, ina wakiltar Maleekh a campany. Ni ba ‘yar club bace.”
Inna ta buga hannu a kujera cikin tsawa ta ce:
“Ke da aka ɗauke ki cikin jini daga club, da likitoci suka tabbatar kin zubar da ciki… kina da bakin cewa ba ‘yar club bace? Ke ce bala’in rayuwar Maliku!”
Amal ta matse hawayenta, tana girgiza kai.
Sai ta taka kusa da Inna, ta ce da murya mai rauni mai cike da gaskiya:
“Inna, wallahi ban taɓa bin wani namiji ba banda Maleekh. Kaddara ce kawai ta jawo abin da ya faru, amma da zuciya ta zan shaida miki ni ba ‘yar iska bace. Ni masoyiyarsa ce, shi kuma masoyina ne. Komai ya faru, Allah zai fitar da gaskiya.”
Inna ta ja tsaki tare da faɗin:
“Sai dai ki ci gaba da mafarki, domin Maliku yanzu ba ya son ki! Kuma bana so ki kara zancen shi a gabana.”
Amal ta kalli Inna da idanuwan da suka cika da hawaye, amma ta ƙara murya da ƙarfin hali cewa:
“Inna, ko da duniya ta ƙi ni, zan ci gaba da tsayawa da gaskiya. Domin soyayya tsakanina da Maleekh, ƙaddara ce. Ba wanda zai iya goge abin da aka rubuta.”
Ta juya tana hawaye, ta haura sama kai tsaye ɗakinta, ta faɗi kan gado tana kuka...
Bata ankara ba ta ji an turo ƙofar ɗaki da ƙarfi..
Inna ta shigo ɗakin Amal da masifa, tana huci kamar wuta..
Ta dafa bango tare da faɗin:
“Ni dai wallahi Amal, baki isa ki tozarta ni ba. Ke kika jawo abin kunyar nan, yanzu za ki zo kina min gadara a gidan nan? Wacece ke a nan gidan?”
Amal ta miƙe a fusace, idonta akan Inna tana zazzaro ido ta ce:
“Inna kin wuce gona da iri! Me na yi miki da kike ta zagina kullum? Ko kin manta ni jikarki ce? Idan kika ci gaba da mun haka wallahi zan wurgar da ke daga wannan gidan, sai dai ki koma can Kaduna ki ci gaba da masifa a can! Wannan gidan gida na ne, da sunana a rubuce a jikin takardun gidan nan..!”
Inna ta zaburo, ta kama ƙugu tana jijjiga kamar wacce zata yi dambe ta ce:
“Au? Gidanki? To sai naga ‘yar iskar da zata bani umarni a gidan nan. Kina so in koma Kaduna saboda ki kawo tsinannun samarin club ɗinki gidan nan koh? To ki ji tsoron Allah Amal, bazan taɓa barin gidan nan ba wallahi, kuma zan nuna miki ni na fi ki bariki, karuwa kawai!”..
Amal ta sau murmushin takaici sannan ta ce:
“Inna, na ga baki ɗauke ni a mazannin jika ba, meyasa bazaki kyale ni naji da abin da ke da mu na ba? Can ba sauƙi, nan ma ba sauƙi shin ya ku ke so nayi da raina? Ko kina so na mutu ne?..."
Inna cikin ɗaga murya ta ce:
"To ki mutu manaaaa, da wannan abun kunyar da kika jawo mana ai gwara mutuwar ki..."
Amal ta ɗaga muryarta sosai, tana cewa:
“Kafin ki ga mutuwata bari na wurgar dake tukun! Ki ji! Jarababbiyar tsohuwa kawai, kin mayar da gidannan gidan masifa! Daga yau, babu ruwanki da ni, babu ruwanki da Maleekh!”
Amal ta riƙo hannun Inna da ƙarfi ta jawo ta. Inna tana ihu tana cewa:
“Ki sakeni munafuka! Ke ba kya ji tsoron Allah?! Ni kike ja kamar yarinya?!”
Amal bata saurare ta ba, ta ja ta har bakin ƙofa. Sai da ta ture ta waje gaba ɗaya, ta rufe ƙofa da ƙarfi “paahhhtttt!!” sannan ta saka key tana huci...
Amal ta jingina da ƙofar tana huci, zuciyarta na bugawa da ƙarfi, Inna kuma tana waje tana ci gaba da tsinewa da masifa kamar zata tarwatse...
Zuwa ta yi ta kwanta kib da ciki tare da lumshe ido...tana tunani har bacci ɓarawo ya ɗauke ta..
🤦♀️🧞♀️
Amal tana zaune a kan kujerarta, biro a hannu amma gaba ɗaya zuciyarta ta tattare ne da damuwar Maleekh. Zuciyarta ta tsinke, idonta ya rinƙa lumshewa da nauyin tunani.
Kwatsam krrriiiin ta ji an turo ƙofar office ɗinta a hankali. Bata san lokacin da ta ɗago kai ba, sai idonta ya sauƙa akan Maleekh!..
Sanye da fararen suit, farar riga, farin wando, farin tie duk ya haɗu tamkar mala’ika ya sauƙo. Fuskar sa cike da annuri, murmushi ya mamaye kyakkyawar fuskarsa, idanuwansa masu tsananin haske suka zuba kai tsaye cikin nata.
Amal ta tsaya cak! Jikinta ya ɗauki rawa. “Ya Maleekh…” ta furta a hankali cikin ruɗani.
Shi kuwa ya ɗan daga hannu alamar “zo nan”.
Amal ta tsaya naƙe-naƙe kamar mai mafarki, amma ƙarshe ta miƙe, da sauri ta nufi inda yake. Da zarar ta isa ƙofar office ɗinta sai ya juyar da kai ya fita. Ita kuwa tana biye dashi a guje.
Ƙafafuwansu suna ɗaukar sauti a kan tsalelakun bene suna hawa beni can sama-sama har sai da suka kai top floor na company, beni mafi tsayi wanda daga nan idan ka leƙo ƙasa za ka ga mutane kamar ƙwari.
Sai da zuciyar Amal ta tsaya lokacin da ta ga inda Maleekh ya tsaya, bakin gefen building, inda babu komai sai sararin sama a samansa da kuma tsalelakun ƙasa a gaban sa.
Ya juyo yana murmushi mai cike da annuri akan fuskarsa. Ya ɗaga hannayensa biyu yana buɗewa kamar yana ce mata “shigo ki faɗa jikina”.
Amal ta furta cikin kuka:
“Ya Maleekh… wallahi na yi kewarka… wallahi ina sonka!”
Tayi gudu da karfi ta nufi inda yake domin rungume shi. Sai dai kafin hannunta ya rufe kirjinsa - battt!- ya ɓace kamar hayaki.
Amal kuwa ta yi gaba! Hannayenta suna a buɗe, ƙafafunta suka zame ta faɗa cikin sararin ƙasa daga tsayin beni!
Ta ware hannaye tana kukan tsoro cikin iska ta ce:
“Yaaa Maleeeekh…!!!”
Iskar sama na kaɗawa a kunnenta, zuciyarta ta riga ta amince cewa mutuwa ta iso. Idanunta sun kulle suna jiran ƙarshen faɗuwa...
Sai kawai Amal ta farka a razane! 😱
Tana kan gadonta, jikinta na rawa, zufa ya wanke fuskarta. Numfashinta na fita da ƙyar kamar wacce ta yi tsere.
Ta dafe kirjinta tana hawaye tare da faɗin:
“Ya Allah… ashe mafarki ne… Ya Maleekh! Me yasa kake min haka a mafarki?…”
Ta kwanta ta sake lumshe ido amma tsoron da ya mamaye ta bai bari ta sake samun nutsuwa ba...
Amal tana kan gadonta amma har yanzu hawayen mafarkin na gangarowa. Hannunta na rikicewa akan kirjinta tana ji kamar zuciyarta zata tsage.
Ta ce cikin rawar murya:
“Ya Allah… me yasa mafarkina kullum akan Maleekh ne? Me yasa zuciyata ta kasa kwanciya sai na ganshi? Shin wannan ƙauna zata hallaka ni ne?…”
Ta rufe fuska da hannuwanta, numfashinta na fita da ƙarfi. Cikin zuciyarta ta fara addu’a, tana roƙon Allah ya yaye mata wannan ƙunci. Amma ko da take addu’a, hoton Maleekh ɗin nan da murmushinsa mai ɗauke da annuri bai fita daga ranta ba.
🕊️
Kwatsam, ƙarar ƙofar ɗaki ta turo. Amal ta yi saurin jan gyale ta rufe kanta, tana share hawayenta...
Inna har ta buɗe baki zata zazzago masifarta sai kawai ta ga wanin irin kallon da Amal take mata, abin da yafi tsoratar da ita shine ganin yanda kwayoyin idanuwanta suka ƙara girma ga sun yi jawur kamar gobara...
Inna a tsorace ta saki murmushin dole tana faɗin:
“Amatu… har yanzu baki tashi ba? Ko baki shirya zuwa campany ɗin bane yau?”
Amal ta girgiza kai a hankali, ta ce da muryar da ta yi rauni sosai:
“Inna… nayi mafarki, kuma sai yanzu zuciyata ta tsaya. Naga Ya Maleekh… naga kamar zai tafi ya barni har abada…”
Inna ta tsura mata ido, ta sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi. Sai ta ce da ƙarfin hali:
“Kin dai san mafarki ba komai bane. Amma Amal, idan kina son kwanciyar hankali to ki guji abin da zai sa ki zama zance a idon mutane. Kiyi tunani sosai, duniya ba ta da tabbas.”
Amal ta miƙe a hankali ta tako gaban Inna, ta manta da ƙiyayyar da Inna ke mata...Kuma Innan ma ganin halin da Amal ke ciki yasa ta tsure...
Amal ta dafa hannun Inna a tausashe ta ce:
“Inna ki yi min addu’a kawai. Domin zuciyata bata yarda da kowa sai shi, kuma idan na rasa shi… na rasa komai a rayuwata.”
Inna ta girgiza kai, bata iya cewa komai ba. Ta fita a hankali, ta bar Amal cikin tunani mai nauyi.
Bayan Inna ta fita, Amal ta sake fashewa da kuka.
Tace:
“Ya Maleekh… idan da gaske baka sona, me yasa zuciyata ba zata iya barinka ba? Me yasa ko a mafarki sai ka dawo kana rikitar da ni?…”
Sai ta ɗauki wayarta ta sake ƙiran lambar Maleekh, amma kamar kullum switched off.
Bayan tayi kuka ta wanke fuska, Amal ta ɗaura gyale ta fito da nufin zuwa hospital...Domin sake ganawa da Maleekh, zuciyarta tana bugawa da sauri, kamar zata faɗi. A zuciyarta tana faɗin:
“Zan je domin tabbatar da Ya Maleekh ko yana raye, zan duba idan har yanzu yana raye… Allah yasa yana numfashi, domin mafarkin da nayi ya nuna cewa ya mutu...”
Ta shiga motarta a gaggauce, ta tafi ba tare da tsayawa ko’ina ba har ta iso gate ɗin hospital..
🏥
Tana shiga ciki da sauri ta tambayi nurse:
“Please, ɗakin da aka kwantar da patient Maleekh pag?”
Nurse ɗin ta kalleta a tausashe sannan ta ce:
“Sorry Madam… an sallame su jiya da yamma. Sun koma gida.”
Amal ta tsaya cak! Numfashinta ya tsaya na wasu daƙiƙu..
“Me… me kika ce? An sallame su?”
Nurse ɗin ta gyada kai:
“Eh, family ɗinsa sun zo sun ɗauke shi. Ba a nan yake yanzu ba.”
Amal ta riƙe handbag ɗinta da ƙarfi. Idonta ya cika da hawaye, ta juya a hankali ta fice daga hospital