Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
zata shiga ba.
Yayin da Amal ke shirin guduwa ta bar asibiti tare da jariranta, Inna tana kuwa tana kokarin hanata tafiya.
Inna ta riƙe hannun Amal da ƙarfi tana faɗin “Amatu! Na san me nake yi! Ni na gudu da ke daga Kaduna saboda na san su waye ainihin masu kisan gilla! Ba mahaifin Maleekh bane! Wallahi Alhaji Wadata ne! Shi da Alhaji Gusau!”
Amal ta fizge hannunta, fuskarta cike da fushi ta ce,
“Inna! Ki daina faɗin haka! Abbana ya faɗa da bakinsa! Ba zan saurari karya ba! Shi ne ainihin azzalumi da ya ci amanar abokinsa! Sai da ya kashe su sannan ya fake da fuskar tausayi! Shi ma Maleekh saboda ɗan ahalinsu ne, shiyasa bai gaya mun gaskiya ba!”.
Amal ta ƙi yarda da Inna, saboda karyar bidiyo ta yi mata gagarumar tasiri a zuciyarta.
A can wani gefen kuma, Zayd yasan kullin makirci ne na mahaifinsa da Alhaji Gusau. Ya yanke shawarar tunkarar mahaifinsa duk da tsananin tsoro..
Zayd yana magana da ƙarfi, cike da hawaye ya ce, “Daddy! Me yasa! Me yasa kuka yi irin wannan muguntar? Ya isa haka! Zan fita fili in faɗi gaskiya, cewa ku kuka kashe iyayen Amal, ba Abbah Maleekh ba!”
Alhaji Wadata ya ɗauke Zayd da mari, yana huci ya ce,
“Rufe mana baki! Wannan sirri ne na rayuwarka! Idan ka kuskura ka fita da wannan gaskiya, zan sa a kashe ka, kuma za a kashe wanda ka sanya a cikin zuciyarka! Ka manta da hakan!”
Hajiya Sa’adatu itama ta daka masa tsawa da cewa, “Indai ka fitar da gaskiya, to wallahi tallahi saina tsine maka duniya da lahira! Ka zaɓi farin ciki na gidan nan, ko kuma faɗawa cikin wuta!”
Zayd ya kasa magana, ya kasa jurewa barazanar iyayensa da kuma tsinewa. Ya yi shiru da batun, amma fushin adalci ya cika zuciyarsa...
Hospital.
Amal ta samu nasarar kutsa kai cikin ɗakin da Abbah yake kwance. An cire wasu na'urorin lura don kula da shi sosai.
Abbah yana kwance, sanye da Oxygen, idanunsa a rufe. Doctor ya sanar da ya yi paralysis, bai iya motsi ko magana ba.
Amal ta tsaya kusa da gadonsa, hawaye na zuba a fuskarta, cike da fushi da ƙiyayya.
Muryarta na rawa take faɗin “Ka ji daɗi! Ka ji daɗi da abin da ka aikata a rayuwa! Ka kashe Abbana! Ka ci amanar abokinka! Yanzu kuma kunama ta cije ka!…”
“Ka kashe su da wuta, yanzu kuma Allah ya ɗaure ka! Ka ga yadda ake yi wa mutum mummunan azaba? Ina Mallam Maleekh yake? Ko da yake, shima yana sane da cin amanar nan!…”
“Zan yi amfani da wannan jini da ka bari a jikina (tagwaye) in nuna wa duniya cewa kai azalumi ne kuma macuci! Ba zan taɓa yarda cewa Maleekh mutumin kirki bane, tunda kai ne Abbansa!”
Islam da Arfat sun shigo ɗakin a lokacin. Suka ji tsatsar maganganun Amal a kan mahaifinsu wanda ke kwance a kayan aiki na numfashi.
Islam cike da fushi ta ce, “Ke! Ki daina! Ki rufe mana baki! Ba za ki zo ki ciwa mahaifinmu mutunci ba, alhali yana kwance! Wannan sharri ne!…”
Arfat ta matso gaban Amal, fuskarta cike da hawaye da fushi ta ce, “Ki fita daga nan! kuma ki fice daga rayuwarmu! Ƙarya kike yi! Ba zaki zarge mu da kisan kai ba!…”
Amal ta ce, "meye a cikin rayuwar takun banda sharri..."
Islam ta ce, "Duk da sharrin da muke da shi bai hanaki haɗa jini damu ba ai.."
Arfat ta ce, "ha haka kika nace mana, muna korarki kamar wata kariya amma kina ƙara tuso kanki kamar wata mayya, sai dai kika samu gurbi a cikin ahalin da kike raina wa.."
Amal ta daka tsawa tana faɗin "Ku dallah ku rufe mun baki, a wata rayuwar takun masu amfani da jinin al'umma..."
Islam ta ce, "a haka kuma mun rufa miki asiri, ƴar bola kawai..."
Amal cikin fusata ta zabga mata mari tare da faɗin "ni ƴar bola ce amma ai da dukiyar mahaifina kuke amfanu wa..."
Nan suka fara dambe, suna shirin faɗa a cikin ɗakin. Sai Ammy ta shigo da gudu, ta raba su cikin kuka.
tana raba su, muryarta a raunane, “Ku dakata! Ku dakata! Ya isa! Ku bar ta ta tafi!…”
Amal ta fita daga ɗakin tana faɗin maganganu, da cewa
“Babu ni, ba kuma iyalan ku! Kuma jarirai na, Ar’haan da Lihaam, ba za su taɓa shiga cikin ahalinku ba! Na rantse da Allah! Ban ƙaunar Maleekh tunda shima ɗan ahalinku ne! Zan bar garin nan!”
A wannan ranar, an sallami Amal da tagwayenta. Sai da Inna ta mari Amal a gaban mota jin abin da ta aikata, maganganun rashin da'a da ta riƙa faɗa. Haka suka koma can gidansu rai a ɓace...
Abban Maleekh kuwa har yanzu jikinsa ba sauƙi.
Wannan bidiyon da aka baza ya yi mummunan tasiri a Kotu. Kotun ta fara neman Abbah (wanda yake paralysis) domin za a kama shi don amsa tambayoyi kan kisan abokinsa.
Amma sakamakon halin da yake ciki yanzu za'a bar shi ya ɗan samu sauƙi tukun.
☆☆☆☆☆☆
Cikin daren wata rana, ƙungiyar Boko Haram sun afka musu sansanin cikin bazata. Nan da nan, yaƙi mai zafi ya kaure. Sojojin, tare da jarumta da tsari, sun yi martani mai tsauri.
Maleekh ('Lion') ya kasance a sahun gaba na yaƙin. Yana jagorantar Sojojin, yana amfani da dabaru na musamman (tactics) da ya koya. Duk da mantuwarsa, basirarsa ta yaƙi ta bayyana.
An yi ruwan harsasai da kukan bindigogi a ko'ina. An kashe Sojoji da yawa a cikin wannan yaƙin na tsawon lokaci.
Yayin da Maleekh ke tsaka da faɗa da wasu 'yan Boko Haram, wani ɗan Boko Haram wanda ke ɓoye a baya ya samu damar buga masa ƙarfe mai tsauri (metal bar) a kan sa cikin ƙarfin tsiya.
Maleekh ya ji wani mugun zafi wanda ya fi zafin yaƙin da yake yi.
Ya fara jin 'Zuuuuuuu' a kunnensa, kuma duniya ta fara juyawa masa. Yana ganin dishi-dishi a idanunsa. Wani abu kamar haske ya shige shi..
Cikin ƙiftawar ido, ya faɗi sumamme a tsakiyar filin yaƙin. Wannan buguwar ƙarfe ta biyu a kan kansa (bayan faɗuwar rami) ita ce makullin tunawa da kwakwalwarsa ke buƙata.
Bayan an yi yaƙi mai tsawo kuma an yi wa ƴan Boko Haram galaba, abu ya lafa. Sojojin sun ragu sosai, wasu sun mutu, amma sun kashe ƴan Boko Haram da yawa.
Sojojin da suka rage suka fara neman waɗanda suka ji rauni. Sun samu Maleekh a kwance sumamme, wanda ya yi kama da ya mutu. Sun ɗauke shi, suka kai shi wurin jinya na sansanin.
Washegari da asuba, kafin hasken rana ya fito sosai, Maleekh ya farfaɗo.
Ya buɗe idanunsa, a lokacin ya yi tsammanin ganin Amal a gefensa. Ya tuna tafiyarsu ta daji, guduwarsu, da kuma wurin da ya faɗi.
Maleekh cikin raunannen murya, ya ce “Amal!… Ina Amal!?”
Ya farka da sunan Amal a bakinsa!
Ya tuna sunansa (Maleekh), ya tuna Abbah, ya tuna Ammy, ya tuna dukkan rayuwarsa kafin ya shiga rami. Buguwar ƙarfen ta dawo masa da kwakwalwarsa!
Maleekh ya miƙe da sauri duk da raunin da ke kan sa.
Ya duba hannayensa da jikinsa yana faɗin “Ni ne Maleekh!… Maleekh Abdul-Majeed! Ina sansanin Sojoji ne? Me nake yi a nan? Na tuna! Na tuna komai!”
Sojojin da suka ga Lion ya dawo, kuma yana ƙiran wani suna Amal, sun yi mamaki sosai. Sun san cewa Lion ya sake samun kwakwalwarsa.
Maleekh ya fara tambayoyi nan take game da Abuja, iyayensa, da kuma Amal. Wannan tunawar ta Maleekh ta faru ne a daidai lokacin da ake zargin mahaifinsa da kisan kai, kuma Amal ta yi tsammanin cin amana daga dukkan su...
_NEXT NEXT NEXT_
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 89 to 90
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Bayan kwana biyu da farfaɗowar Maleekh, an kammala shirye-shiryen dawowarsa hayyacinsa. Sojoji biyu sun rakoshi har zuwa bakin babbar hanya, suka tabbatar da ya shiga motar haya lafiya zuwa Abuja. Suka biya masa kuɗin mota kuma suka yi masa bankwana cike da kewa saboda 'Lion' ya bar su.
A cikin Abuja kuwa, Amal ta ƙuduri aniyar barin garin. Tana ganin Abban Maleekh a matsayin maƙiyi, kuma Inna ta ƙi yarda da bin ta saboda tana da yakinin gaskiya..
Inna tana hawaye ta ce, “Amatu! Ba zan iya bin ki ba! Ba za ki gudu daga gaskiya ba! Ki yi wa rayuwarki adalci!”
Amal sam taƙi yarda da abin da Inna take faɗi, ta bar Inna cike da fushi, ta ɗauki tagwayenta da kayansu. Ta shiga Napep don zuwa bakin babbar hanya inda za ta samu motar haya zuwa Kaduna..
A bakin babbar hanyar Abuja, aka sauƙe Amal. Ta fitar da keken jariran (Baby Stroller) mai ƙarfi, wanda ke da wurin kwanciya na jarirai biyu (tagwaye). Ta kwantar da Ar’haan da Li’y a ciki, ta sa musu bulun botul (Pacifiers) a bakinsu, suna tsotsa cikin nutsuwa.
Ta juya baya don ba wa mai Napep kuɗinsa.
Ikon Allah! Wani iska mai ƙarfi ne ya zo, tyres na keken jariran suka goce ba tare da an lura da hakan ba. Keken ya fara tafiya da kansa a kan gangaren hanya, yana gudu a hankali.
Amal tana riga-runguma da mai Napep a kan canjin kuɗi (change), ba ta san haɗarin da ke zuwa ba..
Juyowar da Amal za ta yi, sai ta ga babu yara! Babu kekensu! A ruɗe ta fara waiwayawa.
Can ta hango keken jariran yana gudu, yana tunkarar babban titi mai cike da motoci masu gudu!
Amal ta jefar da jakarta da ke hannunta, ta fara gudu da tsananin ihu don taro su.
Cikin ihu take faɗin, “Yarana! Ku taimake ni! Motoci! Ku tsaya!…”
Gudu take, amma mutane a gefen titi babu wanda ya yi tunanin taimako. Sai dai tsayawa suna ɗaukar bidiyo da kallo saboda sun ga abin mamaki.
Keken jariran ya hau babban titi na Abuja, inda motoci ke gudu da tsananin gaske!
Dai-dai lokacin da keken jariran ke shirin shiga tsakiyar motoci, sai ga wani zabgegen mutumi ya sha gabansu da tsananin gudu da ƙarfi.
Wanda ya sauƙo daga motar haya 'yan mintoci kaɗan da suka wuce, ya tsallake hanya zuwa bakin titi! Ya ga haɗarin da ke zuwa, kuma ya yi amfani da karfinsa don ceton tagwayen..
Ya riƙe keken da ƙarfi, ya hana shi shiga cikin motoci!
Amal ta iso wurin tana haki da kuka. Ta rufu kan jariranta, tana rungume su cike da godiya ga Allah.
A fusace cikin tsananin zafin nama da fushi a kan rashin kulawarta da ya jefa yaran cikin haɗari:
Ya ce, “Me kike yi! Me yasa zaki bar yara haka! Baki da hankali!….”
Ya riƙe damtsenta da ƙarfi, ya ɗagota sama, ya kai hannunsa zai mare ta saboda tsananin fushi…
Sai kawai idonsa ya sauƙa akan fuskarta!
Maleekh ya daskarar da hannunsa a sama! Ya kasa motsi.!
“Amal!… Amal!…”
Ita kuwa Amal ta rufe ido sosai tana ƙoƙarin kare fuskarta daga marin. Can da ta ji shiru, sai ta buɗe idonta a hankali…
Itama idonta ya sauƙa a kan fuskar Maleekh!
Ta ruɗe, ta zazzaro ido, baki a sake, tana kallonsa da mamaki! Maleekh ne! Cikin tsari da tsananin kyau!
Amal da Maleekh sun tsaya, ido cikin ido, a kan titin Abuja. Firgici da mamaki sun cika fuskokinsu. Maleekh a matsayin Jarumi mai Rauni da Tunani ya dawo masa.
Amal muryarta na rawa, kamar ta ga fatalwa ta ce,
“Maleekh! Maleekh ne!…”
Maleekh ya jefa hannunsa da ya daskare a sama, ya shafa kansa. Cikin murya mai rauni ya ce,
“Amal! Ni ne Maleekh! Ta ya kika tsira?! Nasan daman dole zaki tsira domin fatana kenam! Me kike yi anan? Kuma me kike yi da waɗannan yaran?!”
Amal ta fara kuka da tsananin zafi saboda ta tuna zargin bidiyon
“Abin da nake so na sanar da kai shine, na ƙi ka yanzu! Ka rabu da ni! Ban san yaya ka tsira ba! Amma me ya kawo ka nan! Ka zo ka kashe ni ne? Saboda kaji labarin asirinku ya tonu shine zaka bayyana? Ka ga cewa ka yi nasarar cin amana!”..
Maleekh ya ƙara fusata. Bai fahimci ma’anar cin amana da take faɗa ba. Sam bai fahimci abin da take nufi ba.
“Cin amana kuma! Waɗannan yaran fa? Me ya haɗa ki da su! Me yasa zaki jefa su cikin haɗari! Wane ne ubansu!?”
Amal ta rungume jariranta da ƙarfi, tana kare su da jikinta.
“Maza bar nan! Ba ruwanka! Su ba naka bane! Su ba ‘yan ahalinku bane! Abun takaici ne kawai kuka zo ku cece su daga haɗari! Ka rabu da ni!”
Maleekh ya dube ta da mamaki na ƙiyayya da take nuna masa, sannan ya kalli jariran da ke cikin stroller. Sai ya fara jin wani bugu a zuciyarsa wanda ya fi zafin yaƙin da aka yi masa. “Shin kin haukace ne? Kodai baki yi farin cikin ganina bane?..yanzun ina kike shirin zuwa? Waima yaran waye waɗannan?..."
Wani mai wucewa wanda ya lura da rikicin su, ya gane Maleekh wanda labarinsa ya yadu. Ya matso kusa da su.
Mai Wucewa ya kalli Maleekh sannan ya ce,
“Kai ne Maleekh? Kai ne ɗan Alhaji Abdul-Majeed? Labarinku ne ya cika garin nan! Ana zargin Mahaifinka da kisan abokinsa! Yanzu Kotu tana nemansa a yayinda yake kwance a gadon asibiti..!”
Maleekh ya daskare a wurin! Kisan kai? Abbana? Wani zafi ya ƙara kama kansa..
Cikin rashin fahimta ya ce,
“Zargin me? Wane Abbana? Kotu kuma? Wace irin magana ce wannan!”
Mai Wucewa ya ce.
“Bidiyo ya nuna hakan! An nuna mahaifin yarinyar nan (Amal) yana jawabin cewa Abbanku yana ƙoƙarin kashe shi don ya ci dukiyarsa! Shi yasa yarinyar nan take shirin guduwa! Tana tsoron kar a kashe ta!”
Maleekh ya juya, ya kalli Amal, cike da tashin hankali da kuma zargin cewa ta yarda da wannan ƙaryar har tana nuna masa ƙiyayya..
Maleekh ya riƙe kansa, wanda yana ɗan jin zafin raunin da ya ji.
“Wannan ƙarya ne! Zargin sharrin Abbana! Amma ke… Amal! Ke ma kin yarda da wannan sharri har kike cewa kin ƙi ni! Kin yarda Abbana makiyin ku ne!…”
Amal ta gane cewa Maleekh gaskiya yake faɗa saboda tsananin raɗaɗin da yake ciki. Tunanin da ta yi na cewa Maleekh ya san komai ya zama ƙarya..
Maleekh ya kalli jariran da ke cikin keken, cike da tsananin tausayin kansa, ya durƙusa a gaban keken, ya kalli Ar’haan da Li’y. Wani abu ne ya cake shi a saitin zuciya.
“Waɗannan … su wanene… sun yi kama da ni… suna da… wani annuri da na sani…”
A lokacin Maleekh ya tuna da sadaukarwarsu a ruga. Ya tuna da kwana uku da aka ba su. Ya duba jariran da kyau.
Ya jefa kansa sama, ya kalli Amal da idanu waɗanda suke rufe da hawaye.
“A-mal! Waɗannan… ba yaranmu bane! Su ne tagwayenmu! Sun zo ne! Sun zo?!…”
Ya ɗauki Ar’haan da Lihaam a hannunsa, yana kuka da murna da azaba lokaci guda.
“Ba zaki gudu ba! Ba zan bari a kama Abbana ba! Ba zan bari a cutar da shi ba! Kin yi shari’a a kaina, kin yi a kan Abbana! Yanzu lokaci ne na wanke shi!…”
Maleekh bai bai wa Amal damar musawa ba. Ya riƙe hannunta da ƙarfi, ya saka ta a Napep (Keke Napep), shima ya shiga tare da jariransa a hannunsa. Sun nufi gida..
Amal muryarta na rawa ta ce, “Ni ba zan je gidanku ba! Bazan sake shiga gidan maciya amana ba!…”
Maleekh ya dube ta sannan ya ce, “Rufe mun baki! Ba mu da lokacin faɗa! Kaddara ta haɗa mu a nan! Zaki bi ni! Ba zan bari a cutar da Abbana ba!”
Bayan an sauƙe su a gidan, kai tsaye ciki suka nufa.. Maleekh ne ya tura ƙofar falon, ya shiga da tagwayensa a hannunsa, da Amal a bayansa.
A falon, Ammy tana asibiti jinyar Abbah. Sai Islam da Arfat ne ke zaune cikin tsananin baƙin ciki da kuma ruɗanin bidiyon.
Kannen sun ɗaga kai, suka ga Maleekh! Sun ganshi tsaye kuma yana riƙe da tagwaye!
Suka zama kamar sun ga fatalwa!
Islam ce ta fara yin ihu ta miƙe tana faɗin. “Yaya Maleekh!…”
Arfat ta miƙe itama, da muryar kuka “Yayana!…”
Nan da nan, suka ru ga da gudu, suka rungume shi, suna kuka mai tsanani da godiya da murna.
Maleekh yana riƙe da su, yana hawaye ya ce, “Na dawo! Kuna lafiya! Ina Ammy? Me ke faruwa?”
Bayan sun saki Maleekh, sai suka ga Amal a bayansa. Farin cikin su ya koma kallo na fushi da baƙin ciki.
Islam ta harari Amal, cikin tsanaki ta ce. “Me kike yi a nan! Bayan kin zagi Abbanmu! Ba kya jin kunya!…”
Arfat itama ta ce, “Ki fita daga nan! Yaya Maleekh, me ya kawo ta nan! Wannan macuciya ce! Ta yarda da ƙaryar bidiyon nan!…”
Maleekh ya ɗaga musu hannu yana faɗin, “Shiru! Ku dakata! Ba mu da lokacin faɗa! An gama zargin sa! Yanzu za mu gano gaskiya! Ina bidiyon!?”
Maleekh ya ajiye tagwayensa a hannun Islam da Arfat (wanda hakan ya rage musu fushi). Ya buƙaci su bashi memory ɗin da bidiyon ke ciki.
Islam ta ba shi memory ɗin. Ya saka shi a babban Plasman falonsu. Sun kunna bidiyon, Maleekh ya zura ido sosai yana nazari (analysis) na bidiyon.
Amal ma ta matso, tana kallo saboda tsananin sha’awa na yadda Daddynta ke jawabi, tayi kewar fuskarsa sosai.
Ya zauna a gaban Plasman sosai don nazarin bidiyon da ake zargin mahaifinsa da kisan kai. Amal ta tsaya a gefe, tana