Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 53

24K to 27K   out of 157.3K words

gaggauce yana jan tsaki.

Zuciyarsa cike da Sacin ran kalmar da Zulaikha ta faWa. Shi yasa sam ba ya shiri da yarinyar, bata iya magana ba. Wasu lokutan haka take sakin maganganu kamar ta ci kashi.

Bai daWe da fita ba ya dawo cikin Wakin, Bintu na biye da shi cikin shirinta na fita aiki, sai Sata fuska take yi kamar anyi mata dole.

Amma ko da Hafiz ya juya yana nuna mata Innaye da yi mata ?arin bayanin kwana da tayi da zazzaSi, sai tayi saurin daidaita fuskarta zuwa yanayin jimami da tausayawa.

Duk abinda take yi, ?asa-?asa Zulaikha ke kallonta zuciyarta cike da mamakinta. Tana sane ko gaishe ta bata yi ba, don har lokacin Sacin ran cin mutunci da tozarcin da tayi mata jiya bai bar zuciyarta ba.

A tausashe Bintu ta kalli Hafiz tana mishi ?arin bayani bayan ta Wan tattaSa jikin Innaye sama-sama. A lokacin ita ma Innaye ta farka, ta buWe idanunta a jigace tana rarraba idanu a tsakaninsu.

"Sweetheart, ka kwantar da hankalinka. Daman dole za'a sami irin waWannan ?ananun matsalolin. Magunguna da alluran da na kawo mata masu kyau ne sosai, don haka a karon farko dole ta fuskanci irin waWannan matsalolin, tunda a iya tsawon rayuwarta bata taSa amfani da magunguna masu kyau da ?arfin waWannan ba. Cikin ?an?anin lokaci za ta daina fuskantar zazzaSin, magungunan kuma za su fatattaki duk wani typhoid da maleria da yake jikinta."

Da damuwa sosai a fuskarsa ya ce
"Yanzu babu wani taimako da za'a iya mata ta daina fuskantar zazzaSin? Ki dubi fa yadda idanunta suka yi zuru-zuru zazzaSin dare Waya kawai."

"I'm sorry to say gaskiya babu. Haka nan za muyi ha???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~??uri ta cigaba da shan magungunan. Ka san kuma jiki-jiki, kowa da yadda magani da allura ke aiki a jikinshi. Ita wannan alamun shi ya bani tabbacin magani da alluran sun karSe ta, kuma fa ba lallai yau tayi zazzaSin ba. Ka kwantar da hankalinka pls."

Sai kuma ta mayar da hankalinta kan Innaye, a tausashe ta fara gaishe ta da jiki.
"Sannu Innaye. Allah ya ?ara sau?i. Yanzu dai Zulai ki kamata zuwa bayi a wanke mata baki tayi break fast, sai inyi mata allura kafin in fita. In sha Allah za ta samu sauki sosai."
Ta ?arasa maganar idanunta na kan Zulaikha da har lokacin ta ?i yarda ta Waga fuska su kalli juna cikin ido.

Ko kafin Zulaikha tayi yun?urin Waga Innaye da ko magana bata iyawa har Hafiz ya tarairayota zuwa jikinsa a tausashe ya zaunar da ita.
"Sannu Innaye. Allah ya baki lafiya."

Innaye dai ba baka sai kunne, ta kasa amsawa, sai raba idanu take yi tsakanin shi da Zulaikha da suke ta jera mata sannu kamar za su ari baki.

TaSe baki Bintu tayi ta fice daga Wakin bayan ta ba Hafiz uzurin bari taje ta ?arasa shiryawa kafin Innaye ta gama.

"Zanyi wanka... Sai inyi sallah."
Innaye tayi maganar a hankali sosai yadda har basu ji abinda ta ce ba sai da Hafiz ya kara kunnensa daidai bakinta.

Zaunar da ita yayi a gefen gadon ya jingina mata filo, da rawar jiki ya shige banWaki ya sirka mata ruwan wanka. Har cikin banWakin ya kai ta ya umarci Zulai ta taimaka mata tayi wanka da alwala kafin ya fice daga banWakin.

Can Sangarensu ya koma a gaggauce. ?akinsa ya shige ya sauya kayan jikinsa saboda yamutsewar da yayi a dalilin hidimta ma Innaye, bai Sata lokaci ba ya fice daga cikin Wakin ya wuce kicin. Tsaye yayi yana Wan tunanin abinda ya kamata yayi, sai kuma ya buWe kayan karin kumallon da Bintu ta shirya mishi a cikin basket zai wuce da shi Ofis ya Wauko Waya daga cikin kulolin da ya siyo ma Innaye ya sake musu gaba Waya. Jikinsa sai rawa yake yi, bai ce ma Bintu da take tsaye tana kallonsa komai ba ya fice daga kicin Win.

Duk abinda yake yi tana tsaye tana kallonshi ranta a Sace, ta kasa ce mishi komai saboda ?uncin zuciya. Bayan fitarsa a fili take ?ara Allah wadarai da zuwan Innaye gidanta. Domin a zuwansu ne ta ga abubuwa mabanbanta da bata taSa tsammanin za ta gansu daga Sangaren Hafiz Win ba.

Tun bayan zuwansu kwanaki biyu kawai ta Wauka tana yi musu abinci a mutunce kuma sau uku a rana. A rana na uku ta sakar ma mai aikinta Rabi ragamar komai na su, aka koma basu dafaffen abinci sau Waya a rana.

Ita da kanta ta Webi kayan tea da flask da kofuna ta kai musu can Sangaren da suke. Sannan ta zauna cikin gwari-gwari tayi musu bayanin da ta Wauki tsawon da?i?u tana tsarawa a zuciyarta.
'Innaye ga waWannan kayayyakin. Kayan tea ne wadatacce da za ku dinga amfani da su gurin karyawa a iya tsawon kwanakin da za kuyi a gidannan, idan sun ?are kar kuji komai a faWa min. Sannan a Sangaren abincin rana da yamma, na faWa ma Baba Rabi ta dinga dafa komai a wadace tana zubo muku isasshe a kula wanda zai ishe ku cin rana da dare.

Kuyi ha?uri, kun san yanayin aikina ba na zama bane, a mafiyawancin lokuta ni da My dear abincin dare ko na safe kawai muke iya ci tare cikin nutsuwa saboda yanayin aikinmu na da banbancin lokuta.

Ko a cikin kwanaki biyunnan da kuka ga na samu lokacin kula da ku sosai hutu ne na samu a gurin aiki. Yanzu kuma hutun ya ?are, ina fatan za ku fahimce ni kuma kuyi min uzuri.'

A lokacin, daga yadda Innaye tai ta saka mata albarka tana ?ara ?arfafa mata gwuiwa akan aikinta na ceton rayukan al'umma ya tabbatar mata Innaye ta gamsu da maganganunta Wari bisa Wari.

Shi kuma Hafiz kasancewarsa irin mazajennan masu sakarwa matayensu ragamar komai bai taSa tuhumar ko me za ta ko ta aikata ba. Ko da yaga an daina kai ma su Innaye abin karyawa sai dai sun?in biredi kawai bai taSa tambayarta dalili ba.

Ko yanzu ba ta tsammanin zai nuna mata wani Sacin rai, amma irin wannan Sare-Saren jikin da yake yi akan tsohuwar shi ne abinda yake ?ona mata zuciya. A ganinta ba komai zai ?ara janyo mata a gurinsu ba sai ?as?anci da rashin godiya akan duk abinda za ta musu nan gaba.

'Saboda Allah in banda salon zubar da mutunci da niyyar janyo mata tozarci kayan karin kumallon da ta hana idanunta komawa barci ta shirya musu ita da shi shi ne zai juye nashi gaba Waya ya kai musu?' Dogon tsaki taja Sacin ranta na ?ara hauhawa.

Ta daWe a gurin tana sa?e-sa?e kafin ta wuce ta cigaba da shiryawa, duk bayan mintuna take jan tsaki ?asa-?asa idan ta tuno abinda ya faru. Haka nan ba don ranta na so ba ta sake raba nata abincin gida biyu ta zuba mishi rabi a kulolinsa.

Ko da Hafiz ya koma cikin Wakin, a kan dadduma ya tarar da Innaye tana sallah a zaune. Ita kuma Zulaikha tana tsaye jikin gado tana gyara shimfiWar gadon.

Kusa da Innaye ya zauna, ya buWe kulolin abincin ya fara zuba mata. Lafiyayyen alalen dankalin turawa ne da miyan ganye, a gefe guda kuma ga kunun gyaWa da aka dama shi da madara, yayi fari kar gwanin ban kyawun kallo a idanu. Sai ?amshi yake fitarwa.

?auri biyu ya zuba alalen dankalin a faranti, ya sa cokali ya buWa cikinsa yadda zaiyi saurin shan iska. Kunun gyaWar ma Wan madaidaici ya zuba a kofi ya saka cokali yana jujjuyawa don kunun yasha iska da sauri.

Ya du?ufa kan abinda yake yi har bai san Innaye ta idar da sallar ba sai da ya jiyo muryarta ?asa-?asa ta kira sunanshi.
"Hafizu?"

"Na'am Innaye. Kin idar? Sannu ya jikin naki?"
Ya amsa yana kallonta a tausashe.

"Jiki Alhamdulillahi Hafizu."
Ta sake amsawa da sanyin murya sosai. Sai kuma ta mayar da idanunta kan Zulaikha da itama ta tsaya da gyaran gadon da take yi tana kallonta cikin kulawa da tausayawa.
"Sannu da ?o?ari Auta. Jiya ban bari kinyi barci ba. Allah yayi miki albarka."

"Amin Innaye. Allah ya ?ara miki lafiya da nisan kwana."

"Amin ya rabb!"
Hafiz yayi gaggawar amsawa tun kafin Innaye ta amsa. Ta buWe baki za tayi magana ya riga ta da cewa
"Innaye kiyi shiru haka nan. Kin ga jikinki babu ?arfi, ki karya sai ki sha magani, Bintu za tayi miki allura kafin ta fita aiki."

"To"
Ta amsa a sanyaye. A zuciyarta take ji kamar ta ce mishi a dakata da magani da alluran, amma da ta tuno irin bayanin da ta ji Bintu tana yi mishi Wazu sadda ta farka barci sai bata furta abinda yake zuciyarta ba.

A baki yai ta bata abincin yana ba ta kunun tana kurSa a hankali har sai da ta kawar da kanta alamun ta ?oshi.

"Ki daure ki ?ara ko kaWan Innaye, kin san wasu magungunan rashin isasshen abinci a ciki yana sa su wahalar da mutum."

"Na ?oshi Hafizu. In dai ba so kake in amayar da wanda ya shiga cikina ba."
Ta faWa tana ?o?arin yin murmushi amma ya gagara saboda tsananin yadda ta jigata da ciwon dare Waya kacal.

Kafin yayi magana Bintu tayi sallama ta shiga cikin Wakin, idanunta kan agogon da ke Waure a tsintsiyar hannunta take cewa
"My dear lokaci ya tafi sosai fa, sai kira na ake yi a Ofis. Ta gama break fast Win?"

"Eh! Ta gama."
Ya amsa shi ma yana sauke idanunsa kan agogon bangon da ke cikin Wakin. ?arfe takwas da mintuna talatin da uku.

Bintu idanunta ta mayar kan Innaye da fuskarta yayi zuru-zuru, idanunta suka zuz-zurma ciki sosai, ciwon dare Waya kawai gaba Waya ya sa kamanninta ya canja, tsufanta ya bayyana ?arara. Haushi da tsanar Innaye da yayi kaka-gida a zuciyarta ya hana Wan guntun tausayin da ya taso mata yin tasiri.
"Innaye ina kwana? Ya ?arfin jiki?"

"Lafiya ?alau. Da sau?i Alhamdulillah"
Ta amsa da yanayin maganar da take yi ?asa-?asa tun da ta idar da sallah.

"Allah ya ?ara sau?i."
Tayi addu'ar a gaggauce. Muryar Hafiz kawai ta ji ya amsa mata. Cikin rashin damuwa ta Wauki ledar magungunan Innaye da ke ajiye a gefe guda ta fito da su ta fara harhaWa ruwan alluran, duk abinda take yi cikin sauri ne tana yi tana kallon agogo.

Babu wani tausasawa Innaye ta juya baya ita kuwa ta zurkuWa mata alluran biyu ba tare da tantance inda ya kamata tayi mata ba. Ta Salli magungunan kamar jiya shi kuma ya mi?a ma Innaye, ya tsiyayi ruwan gora a kofi ya mi?a mata ta haWiyi maganin.

"Zulai sakko ki ga magungunan da za ki ba Innaye da rana."
Bintu ta faWa idanunta kan Zulaikha da take zaune a gefen gado tun bayan shigarta cikin Wakin.

Da farko ?in motsawa tayi, sai da Hafiz ya daka mata wani gigitaccen tsawa kafin ta taso da sauri ta tsuguna gaban Bintu tana zumSura baki.

"Ki shiga taitayinki da ni na rantse da Allah. Idan ba haka ba kafin in fita Ofis na rantse sai na koya miki hankali..."
Hannun da Innaye ta Waga masa alamar dakatarwa yasa shi katse maganar ba tare da ya kai ?arshen maganar ba.


Kala uku a cikin magungunan ta ware ta nuna ma Zulaikha da cewar su za ta ba Innaye tasha da rana.
"Ki kiyaye fa, kar ki kuskura shirme da wawancinki yasa ki dawo min da treatment baya. Domin yadda ta fara shan magani da allurannan kuskure kaWan za a samu na jinkirin shan maganin aiki ya dawo baya, ba fata nake yi ba amma irin ciwukan da za su taso mata sai sun fi waWanda tayi fama da su a baya."
Ta yi maganganun cikin faWa-faWa tana aika ma Zulaikha mummunan kallo.

Bata amsa ba, a madadin tayi magana ma Waga idanunta tayi a fili itama ta galla ma Bintu wata matsiyaciyar harara kafin ta mi?e ta koma gurin zamanta gefen gado.

Baki buWe Bintu ta bi ta da kallo, fuskarta cike fal da mamaki. Ta buWe baki za tayi magana da sauri Hafiz da yake ankare da komai ya Wan taSe ta, suna haWa idanu ya girgiza mata kai sannan ya nuna mata Innaye da ?wayoyin idanunsa.
?asa-?asa tayi ?wafa kafin ta mi?e tsaye, fatan ?ara samun sau?i tayi ma Innaye sannan ta kama hanyar ficewa daga Wakin.
"My Dear ni kam na wuce. Sai munyi waya."
Bata jira amsawarshi ba ta fice daga Wakin.

Aka ce albarkacin kaza ?adangare ke shan ruwan kasko. Albarkacin Innaye, yasa duk yadda Zulaikha ta Sata ma Hafiz rai bai ce mata komai ba har ya gama tarairayar Innaye ya fice daga Wakin bayan yayi musu sallama zai wuce Ofis.

Da harara Zulaikha ta raka shi har ya Sace ma ganinta.

Innaye dai jingina tayi da jikin bango ta lumshe idanunta. A yanzu babu zazzaSi a jikinta, amma fa ba ta jin ?arfi ko mis?ala zarratin, sakayau take jin ta kamar an kwashe duk wani ?warin jiki da Allah ya huwace mata. Tana a haka har barci ya fara Waukarta.

"Innaye ko za ki dawo kan gado ki kwanta sai in gyara tsakar Wakin?."
Maganar da Zulaikha tayi shi ya farkar da ita daga barcin da ya fara Waukarta.

Bata ce komai ba, sai yun?urin mi?ewa da ta fara yi, da sauri Zulaikha tazo ta kamata ta mi?ar da ita, tana tallabe da ita har sai da ta kwantar da ita akan gadon ta rufa mata bargo a rabin jikinta.

Kafin ta gyara Wakin sai da ta zauna ta take cikinta tayi nak! Tana cin alalen dankalin turawan tana korawa da daddaWan kunun gyaWar a zuciyarta take zabga Allah ya isa ga Bintu da a dabarance ta daina basu dafaffen abinci lokacin karyawa sai dai su sha shayi.

Ita kam da yake rainon ?auye ne abu mai suger da safe bai cika damunta ba. Ko a gida idan akwai Wumamen tuwo ko sauran abincin da aka dafa da daddare sam ba ta kallon kokon da ake damawa a rarraba ma yaran gida a cikin kofuna ?ananu. ?umamen Tuwo take sakawa ta zambaWa yaji ta cika cikinta tayi nak, sai ta kai ?arfe Wayan rana da ?oshinta ko da an samu jinkirin gama abinci sanadiyyar Wanyen itace ko gawayi.

Bayan ta gama karyawa tattare kuloli da farantai da kofuna tayi gefe Waya ta gyara tsakar Wakin ?al, har mopping Win kan tiles Win tayi ya fita fes! Sannan ta maida hijabin jikinta ta bi lafiyar gado ta kwanta gefen Innaye domin ta rama barcin da bata samu yin isasshe jiya ba.


******


Darare uku masu kama da darare dubu saboda masifar tsawonsu a gurin Zulaikha Innaye ta kwashe tana fama da bala?a??en zazzaSi mai zafin gaske kamar baza ta wayi gari ba.

Wani ikon Allah kuma da asubahi tayi sai zazzaSin ya sauka. Haka za ta yini cikin rashin ?arfin jiki da kasala, ba ciwon jiki kaWai ba, hatta tafin ?afafun Innaye jin su take kamar an kwashe ?asusuwan da suke taimaka mata gurin yin tafiya an bar zallar tsoka kaWai. Dai dai da zuwa banWaki sai Zulaikha ta ri?e ta sannan take iyawa, sallah kuwa tun ranar farko da ta fara yi a zaune har yau bata ?ara samun ?warin gwuiwar yi a tsaye ba.

Innaye ta rame ta zabge ta tsuke kamar ba ita ba. Tsufa da galabaita sun bayyana ?arara a jikinta. Ba Innaye da take fama da ciwon cikin dare ba, hatta Zulaikha da take jinya duk ?ibar nan ta fara zazzagewa.
Ita kanta kallo Waya za'a yi mata a fahimci rashin nutsuwa da rashin kuzari a tattare da ita.

Shi kuwa Hafiz duk yadda ciwon Innaye yake Waga mishi hankali har lokacin bai ji a jikinsa ya kamata Bintu ta canja ma Innaye magunguna da allurai ba. Maganar da ta faWa mishi tun ranar farko ita ya ri?e daram a zuciyarsa
'Jikin Innaye bai taSa karSar magunguna masu kyau da ?arfin waWannan ba shi yasa a yanzu dole za ta galabaita na kwana biyu. A bayan waWannan cututtukan lafiya wadatacciya ce za ta biyo baya fiye ma da wanda suke nema.'
Da waWannan kalaman yake ta dannar zuciyarsa da irin damuwa da tashin hankalin da yake ciki.

Abu Waya dai da ya iya yi shi ne kullum bayan ya dawo sallar asubahi zai umarci Bintu ta haWa ma Innaye lafiyayyen abin kari, idan ta gama ya kwasa ya fice musu da shi.

A rana ta uku har yayi ma Innaye sallama zai tafi Ofis bayan Bintu tayi mata allurai ta bata magunguna ta fice gurin nata aikin Innaye ta ri?o gefen rigarsa.

"Innaye? Sannu. Akwai abinda kike so inyi miki kafin in tafi Ofis ne?"
Ya tambayeta a tausashe bayan ya dawo ya zauna a kusa da ita.

"Hafizu, gida nake so ka mayar da ni yau. Ko da mutuwa za ta Wauke ni na fi so ta Wauke ni a cikin iyalaina."
Tayi maganar da?yar, shi kanshi bai ji abinda ta ce ba sai da ya kai kunnensa daidai bakinta.

Hankalinsa ne ya ?ara Wugunzuma fiye da wanda yake ciki. A yadda ya Wauko Innaye da ?arfi-?arfinta ko kusa bazai so ya mayar da ita can ?auyensu yadda ta fara kwararraSewa haka ba.

Saboda ba ya son Waga ma ?an'uwa da mahaifinshi hankali ne yasa shi tun fara zazzaSin daren Innaye kullum sai ya gargaWi Zulaikha kar ta kuskura idan Waya daga cikin Yayye, mahaifinsu, ?an'uwa suka kira Innaye don jin yanayin jikinta tayi suSul da bakan sanar da su irin ciwon da ya taso ma Innaye gadan-gadan.

Daga bisani ma karSe wayar Innaye da ke hannun Zulaikha yayi ya kashe. Ya zama sai lambarshi kaWai ake kira aji ya jikinta, shi kuwa duk wanda ya kira shi ya san abinda yake faWa musu. Ko sun nemi yin magana da ita kai tsaye yake kawo wani ?a??arfan uzuri ya basu.

Hankalinsa a tashe ya gyara zama zai fara kalallame Innaye da daWin bakin tayi ha?uri ga mamakinsa da tsoro kawai sai ta fashe mishi da kuka. Wani abu da bai raSa faruwa tsakaninshi da ita ba.

Wannan kuka da Innaye take yi hai?an ba

9 / 53