Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   13 / 53

36K to 39K   out of 157.3K words

ya samu karSuwa a cikin gidansu Zulai. Amma gare ta babu yabo babu fallasa, saboda dalilai mabanbanta.

Dalili na farko shi ne Mudan yana da mata. Duk da a shekaru Mudan Win bai haura shekaru ashirin da biyar a duniya ba yana da mata Waya da ?a?anshi uku. Auren miji mai mata kuwa abu ne da Zulaikha bata taSa tsammanin yin shi ba.

Dalili na biyu kuwa shi ne matar Mudan mai suna Yahanasu. Tun a wancan lokacin kasancewar Zulai me tsawon ?afa duk da Yaha ta girme mata da shekaru biyu sun yi zamanin ?an matanci da juna, tun a wancan lokacin jininsu sam bai haWu da na Yaha ba. Dukkansu ba su da ha?uri kamar zawayi.

Yahanasu akwai bala'in son girma ita kuma Zulai akwai ta da raini, musamman ga babban da ta zubar da girmanta. To ita kuma Yaha akwai shiga abinda babu ruwanta. Ga masifa da bala'i kamar ruwan shan ta, duk yawan taron jama'a ba ta kunyar ta kwaSe mayafi su dambatu da wacce ta shiga hanyarta.

Allah dai ya kiyaye duk wannan rashin jituwar tasu har Yaha tayi aure Zulai bata taSa ba ta damar da za su ba hammata iska ba. Saboda ita kura ce, ga tsoro ga ban tsoro, akwai dai baki kamar me amma da an zo batun dambe yanzu za'a neme ta a rasa. Sam ta tsani abinda zai sa ta haWa jiki da wata in dai ba an shammaceta ba.

Dalili na uku shi ne shi kanshi Mudan Win a halayenshi mutum ne mai tsananin iko da rashin ha?uri. Da shi da matarsa kamar an duba halayyarsu ne aka haWa su aure. Amma kuma wani ikon Allah suna zaman lafiya sosai, domin Yaha ta iya bi da halayenshi.

Wadannan dalilai uku suka hadu suka sa duk da zancen Mudan ya shiga gidansu Auta bata dauke shi wani kayan gabas ba. Haka take ta jan shi da dadi babu dadi har zuwa sadda aka tsayar da ranar aure a tsakaninsu. A lokacin ne ta dan nutsar da hankalinta guri daya ta fara daukarshi da daraja.

A lokacin kuma sai Yahanasu ta taso ta gaba da sakonnin tanadin da tayi mata na masifa da bala'i kala daban-daban matuk'ar tayi kuskuren auren mijinta. Ashe tun fara neman auren yana yi a b'oye ne bai fad'a mata ba kuma ?an'uwa da mutanen gari ba'a sami wanda ya tsegunta mata halin da ake ciki ba har sai da aka tsayar da rana sannan ta san halin da ake ciki.

Wannan tashin hankali da matsanancin kishin da Yaha ta Wora ma ranta shi ya taso mata da na?uda gadan-gadan, lokacin haihuwarta baiyi ba. Ga mummunar Wabi'ar mutanen ?auye ta rashin wayewa da zuwa asibiti musamman idan na?uda ta taso.

Wannan ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?dalilin yasa ta sha ba?ar wahala, kamar baza tayi ba a hannun Ungozoma na gargajiya kafin aka kwashe ta zuwa asibiti. Kuma cikin hukuncin Allah duk da asibitin babu wasu ?wararrun likitoci ko malaman jinya ana zuwa bata cika awa uku ba ta haifi Wanta namiji.

Wannan haihuwa ya zo ma Mudan da iyayensa da ita kanta Yaha da wani gagarumin farin ciki da basu taSa tsammani ba. Na Waya saboda duk ?a?ansa uku da Yaha ta haifa mata ne. Na biyu kuma a ranar ne ya kai amfanin gonarsa kasuwa suka yi gagarumin tsadar da basu taSa yi ba. Kuma a ranar ne ya samu nasarar siyan mota golf wacce ya daWe yana buri Allah bai nufa ba sai a wannan rana.

WaWannan dalilai suka tattaru suka sa yake Waukar haihuwar nan da wani irin girma da ?ima kamar ba'a taSa mishi haihuwa ba. Shukuranu shi ne sunan da yake kiran yaron tun kafin ranar raWin suna ta zo, saboda a ganinsa duk waWannan alkhairan sun zo ne dalilin haihuwarsa.

Tun a washe garin ranar da akayi haihuwar ya fara yi ma Zulaikha nacin taje tayi ma Yahanasu barka, wacce aka sallamota daga asibiti bayan ta kwana ta yini. Amma haka tayi ta mishi yawo da hankali har dai ranar ta biyar da aka yi haihuwar inda ta fito ?e?e-?e?e ta faWa mishi baza ta je ba.

Shi kuma yasha alwashi sannan ya rantse da girman Allah idan bata je ma Yaha barka ba bazai aure ta ba. Zai gwada mata ya fi ta Wanyen kai.


******


Tun da ya fito yayi tozali da Baffa, nan take yanayin fuskarsa ya canza daga farin cikin da ya fito da shi zuwa ba yabo ba fallasa.
"Au! Baffa kai ne da safen nan?"
Ya faWa yana Wan ciccijewa.

Duk da ganin yadda ya canja fuska farat Waya daga ganinshi bai hana Baffa faWaWa tasa fuskar da murmushi ba.
"Assalamu alaikum!"
Yayi mishi cikakkiyar sallama haWe da mi?a ma Mudan Win hannu.
A kunyace ya Wan kawar da fuska yana sosa ?eya. Sai kuma ya Wan du?a ?asa a ladabce ya fara gayar da Baffa, ba tare da ya mayar mishi da hannu kamar yadda Baffa ya bu?ata ba.

Bayan musayar gaisuwa a tsakaninsu da tambayar lafiyar masu jego Wan shiru ne ya ratsa tsakaninsu. Can kuma sai Baffa ne ya karya shirun da cewa
"Jiya na dawo da daddare nake jin wasu zantuka na shirme daga bakin Zulai. Amma kasancewar kai ne namiji mafi girma a kanta ban Wauki maganganunta da muhimmanci ba. Sai ma faWa da nayi mata na mi?a mata laifin gaba Waya duk da bansan cikakken bayanin abinda ya faru ba.

Domin a ?a'ida shari'a ba ta yiwuwa da jin Sangare Waya. Wannan dalilin yasa nayi sammakon zuwa jin abinda ya faru sannan in baka ha?uri. Don Allah kayi ha?uri, ka san Zulai yarinya ce har yanzu akwai ?uruciya a kanta..."

"Shekarunta goma sha takwas ne kake kira mata yarinta Baffa?"
Ya katse shi da faWin haka yana ?ara Waure fuska.

Shi dai Baffa bai sake cewa komai ba. Tun da ya katse shi sai kawai ya sakar mishi ragamar maganar ya tsaya yana saurarenshi.

Lura da hakan da Mudan yayi yasa shi naWe hannaye a ?irji idanunsa na kallon gefe ya cigaba da sakin duk irin maganganun da suka zo bakinshi.
"In dai za mu faWa ma kanmu gaskiya babu wani ?uruciya a jikin Zulai. Yarinyar da duk sa'anninta sun tara ?a?a huWu biyar ita ake kira ma ?uruciya? Tsabar raini ne kawai da iskanci, kuma daman tun farko an faWa min. Ta riga ta ri?a ta gandare a gidansu ko na aure ta baza ta taSa jin magana ta ba. Sannan kuma tana ji da kanta don Yayanta na da kuWi tana zuwa Habuja ita gani take ta fi ?arfin mazajen ?auyen nan. Kuma tana ganin duk ?an matan ?auyennan ita kaWai ce ta samu nasarar gama sakandare tana ta?ama da boko shi yasa take jin ita Win ta kai wata shegiya.

Bayan abinda ya faru jiya ni gaskiya na riga na yanke ma kaina shawara, tunda dai ita fitsararriya ce, ni da zan aure ta ma tun yanzu ban isa in bata umarni ta aikata cikin daWin rai ba to ina ga mun yi aure? Kana ganin ni da hankalina zan yarda in auri macen da take min gani-gani ne? Ita fa a yadda na lura gani take kamar alfarma tayi min idan ta aure ni.
Don haka gaskiya sai dai kuyi ha?uri Baffa..."

"A'a! A'a Mudansiru!! Don Allah don Annabi kayi ha?uri. Kar ka ce ka fasa aurenta don Allah. Na Wauki al?awari zan yi mata faWa sosai, idan ta kama da duka ma Wallahi zan haWa mata. In Allah ya yarda baza ta sake ?in bin umarninka ba, kayi ha?uri don Allah."
Baffa ya faWi maganganun cikin tashin hankali, idanunsa sun kaWa lokaci Waya sunyi jaa saboda tsananin tashin hankali da damuwa.

Duk da maganganun Mudan Win sun ?ona masa zuciya, musamman in da ya kira Zulai da shegiya. Amma zai iya shanye fiye da haka akan dai ace ya fasa auren Zulai, a cikin waWannan ?idayayyun kwanakin da suka rage ya aurar da ita. Da wannan dalilin yasa bai tsaya tunkarar iyayen Mudan ba tunda dai shi ne mai aure, kuma shi Mudan Win ba yaro bane tunda har ya tara iyali.

Sannan bai tsaya turo Waya daga cikin ?an'uwansa gurin Mudan Win ba ya zo da kansa, zuwa da kai ai ya fi sa?o. Kuma yadda zai ?as?antar da kai yaba Mudan ha?uri ya san ba lallai ne ?an'uwansa su iya yin haka ba.

?an shiru Mudan yayi yana ciccijewa yana hura hanci, irin a dole shi fa an takura shi Winnan. Kamar bazai tanka ba, amma kuma wani tunani da yayi yasa shi cewa.
"Baffa... Ni fa gaskiya na gama magana. Amma tunda ka ce za ka mata faWa zan je inyi shawara, duk yadda ake ciki zuwa yamma ko gobe za ka ji ni. Na barka lafiya, a gaida iyali."
Yana gama faWin haka da saurin gaske ya wuce ya ba Baffa guri, don ma kar ya sake tare shi da wasu kalaman magiya da ban ha?urin da yake ji babu abinda za su canja matu?ar Zulai bata sauke girman kanta ta je ma Yahanasu barkan haihuwa yau ko gobe ba.

Haka Baffa ya bar ?ofar gidan Mudan jikinsa a sanyaye, jan ?afafunsa yake tayi hankalinsa tashe har Allah yasa ya isa gida lafiya. Saboda tsananin damuwa duk yadda Innaye ke ta bin shi da kallon tuhuma ya kasa sanar da ita yadda suka yi, ya bari ne tukunna sai ya ji tsayayiyar magana daga bakin shi Mudan Win. Ita kuma Innaye saboda tsananin ladabi da biyayya irinna matan da ta kasa titsiye shi da tambayar yadda suka yi, sai kawai ta kawo ido ta zuba masa tana cigaba da addu'ar tabbatuwar auren kamar yadda aka saka shi.

[1/1, 12:01 AM] Fareeda Abdallah: Tun safe har yamma babu wata ?wa??waran sa?o da Baffa ya samu daga Mudan ko wakilansa. Tsananin tashin hankali da damuwa yasa ya kasa faWa ma ?an'uwansa halin da ake ciki.

Idan ya kalli Zulaikha da ita ma tun bayan abinda ya faru jiya sam ba ta cikin walwala sai yaji kamar zai saka kuka.

Ya sani ko Zulai ta ?i Allah a wannan gaSar da bikinta yazo daf baza ta taSa so ace an fasa bikin ba. Kwanakin baya da kunnensa ya ji hirar Zulan da Yayarta Balira, tana faWa mata ita kanta tana so ace yau ga shi tayi aure, amma tunda mijin bai zo ba ya za tayi da ranta?
'Wallahi Aunty Balira ko da kuke ganin kamar ba na damuwa ina damuwa fa, amma ya na iya da abinda ya gagari tuwo in ji kishiyar ?onanniya? Mudan da kuke ganin kamar ina wula?anta shi don kar ya aure ni ina da dalilai da dama da nake ganin bamu dace da juna ba ni da shi. Amma ya zanyi? Tunda babu wanda ya fito neman aure na bayan shi? Haka nan zan aure shi. Ina ta addu'ar idan aurensa alkhairi a gare ni Allah ya tabbatar da shi.'
A Lokacin da ya tsinkayi waWannan maganganun, a zauren gidan ne tayi ma Yaya Balira rakiya za ta koma gidanta, shi kuma ya sako kai zai shiga gidan da yaji maganar da suke yi sai ya tsaya ya saurara.

Da la'asariyya li?is yana zaune a cikin turakarsa ya ?walla ma Bilya Waya daga cikin ?ananun ?a?ansa kira.
"Salamu alekum. Ga ni Baffa."
Yaron ya faWa a ladabce, bayan ya dur?usa har ?asa a gaban Baffa.

"Yi maza Wakin Innaye ka kira min Zulai."

"To Baffa."
A guje yaron ya fice daga Wakin yana haWawa da ?an tsalle-tsalle. Ba'ayi cikakken mintuna uku ba sai ga sallamar Zulaikha a ?ofar Wakin.

Sai da ya amsa, yayi mata umarnin shiga sannan ta shiga cikin Wakin. Tana sanye da wani zumbulelen hijabi kamar mai takaba. Idanun nan sunyi kozai-kozai sun kumbura alamun ta sha kuka, a bakin kofa ta tsuguna.
"Ga ni Baffa."
Ta fad'a da dasasshiyar murya.

"Zulaikha?"
Ya kira sunanta a tausashe.

"Na'am Baffa"

Shiru yayi yana sake kare mata kallo na wasu dakiku kafin ya cigaba da cewa.
"Da safe na je har gida na sami Mudansiru. Irin maganganun da na ji daga bakinsa a kanki sam ban ji dad'insu ba. Amma na yi mishi uzuri, saboda ban san girman laifin da kika yi mishi ba har idanunshi suka rufe ya farfaWa min waWannan maganganun."

Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba
"A ta?aice dai, ya faWa min cewa kin raina shi. Sam bakya bin umarninshi a matsayinshi na wanda yake niyyar aurenki. Da wannan dalilin yasa na kira ki yanzu don in tambaye ki gaskiyar abinda ya faru. Kuma ina ro?onki don Allah ba don ni ba ki ji tsoron Allah ki faWa min gaskiyar abinda ya haWa ku."

A cikin Wabi'un Zulaikha da kusan duk ?an gidansu suka shaide ta akai shi ne ?arya ba ya daga cikin halayenta. Za ta fito ta faWi gaskiya ko da ita ce da laifi. Don haka a yanzu ma bata yi ?asa a gwuiwa ba wajen sanar ma da Baffa gaskiyar abinda ya faru.

Bayan ta gama sanar da shi kuma ta ?ara da faWa masa babban dalilin da yasa ta ?i zuwa barkan matarsa kamar yadda ya nema.
"Baffa, matarsa Yahanasu tun zamanin ?anmatacinmu da su ta tsane ni. Ban samu sau?inta ba sai da tayi aure. Amma jin zancen mijinta yana neman aure na babu irin ba?a?en maganganu da munanan zagin da ba ta aiko min. Kwanaki can har aiko min tayi muddin na kuskura na auri mijinta ta rantse da girman Allah a daren ranar za'a fitar da gawata a gidanta. Innaye shaida ce, duk irin maganganun da take min aike Innaye ta sani. Ban taSa faWa maka bane don kar ku ga kamar ba na son auren ne.

Duk na faWa ma Mudan amma ya ?i fahimtata. Tsorona Allah tsorona in je mata barka tayi min lahani, ko kuma ta ?ulla min sharrin da zan shiga bakin duniya. Wannan shi ne dalilin da yasa kai tsaye na ce mishi bazan je ba."

Tsawon mintuna biyu Baffa ya kasa magana, babu abinda yake sai jujjuya maganganun Zulaikha a zuciyarshi. A karo na biyu ya sake sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan yayi mata umarnin komawa cikin gida.

Bayan sallar isha'i ya shiga Sangaren Innaye da nufin yi mata sai da safe, tunda ranar ba girkinta bane. Daga yadda idanuwanta suka zurma ciki lokaci yasa matsanancin tausayinta ya ?ara lulluSe shi, bai shiga cikin falonta da niyyar zama ba, amma lura da halin da take ciki yasa shi zama kan kujera nesa da ita kaWan yana yi mata nasiha kan muhimmancin yarda da ?addara mai kyau da mare kyau a matsayinta na cikakkiyar musulma.

"Shi ma ya fasa auren Auta ta ko?"
Ta katse shi da tambayar da raunin murya.

"Eh toh! Bazan ce eh ba bazan ce A'a ba. Domin har zuwa yanzu ban samu wata gamsasshiyar amsa daga gare shi ba kamar yadda ya ce zai min aike. Kawai dai mu cigaba da addu'a."

"Uhmmm! Allah ya jisshe mu alkhairi."
Abinda ta iya cewa kenan ta sunkuyar da kanta ?asa. Har Baffa ya fice daga falon bata iya sake ce mishi komai ba.

A wannan dare, idan Baffa ya ce ya yi cikakken barci na awa Waya yayi ?arya. Duk yadda yake ganin kamar abin bazai dame shi ba inaa... Mama Laminde da take da girki tun tana mishi nasiha da tausasan kalamai har dai ta gaji ta zuba ma sarautar Allah idanu. A ?arshe ma juya baya tayi ta kwanta ta ?yale shi yana ta tufka da warwara.

Babban damuwarsa Waya ne, idan Mudan ya ce ya fasa auren Zulai a waWannan kwanakin wa za'a samu kuma yayi ?undubalan fitowa ya ce zai aure ta? Ya sani duk maganganun da Zulai ta faWa masa akan Yaha gaskiya ne, domin Rahina tana faWa masa, amma duk su biyun basu Wauki hargagin Yahan da muhimmanci bane domin a ganinsu surutu ne kawai irinna mace me mahaukacin kishi.

Sannan shi da kanshi sai yau ya ?ara yarda da halin Mudan da ake ta faWa mishi na rashin ha?uri da rashin iya magana. Amma duk waWannan abubuwan bai Wauke su da muhimmanci ba, babban burinsu shi da Rahina shi ne su aurar da Zulai.

Domin anyi ittifaki a yanzu dai duk faWin ?auyen Fa?o babu yarinya budurwa da take da shekarun Zulai. Sa'anninta duk suna Wakin mazajensu da ?a?ayensu.

Tun da daWewa da ace shi mutum ne mai yarda da camfi da tuni ya daWe da fantsama gurin masu magunguna yana nema ma Zulai taimako. Domin da yawan mutane na ganin Aljani ne ya aure ta. Wasu kuma na ganin nauyin jini take da shi, dole sai an nemi taimako sannan za ta sami mashin-shini.

Maganar ta saka ma kanta girman kai don ta yi boko ko kuma don Hafizu yana da gida a Habuja ne yasa take Waga ma samarin ?auyen kai bai taSa ji ba sai yau a bakin Mudan.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke a karo na barkatai. Ya Wauki ?ar ?aramar wayarsa mai tocila da take ajiye kusa da shi ya danna ta kawo haske ya duba lokaci, ?arfe uku da minti ashirin da bakwai na tsakiyar dare.

Hasken tocilar wayar ya kunna, sannan ya mi?e tsaye ya buWe ?ofa hannunsa ri?e da buta ya fita can tsakar gidan ya Wauro alwala. Ya sani duk wani tunani da sa?e-sa?e baza su samar mishi da mafita ba. Don haka ya ?arasa daren yana mi?a kukanshi ga mai kowa mai komai mahaliccin sammai da ?assai da abinda ke cikinta.

Washe gari ko da ya tashi zuciyarsa babu damuwa kamar na jiya. Da asubah bayan idar da sallah ya tare ?an'uwansa sha?i?ai guda uku da suke uba Waya ya faWa musu duk halin da ake ciki, sun nuna alhini sosai.

Sannan suka daWe suna tausarsa da daWaWan kalamai. A ?arshe suka Suge da addu'ar Allah ya kaWe fitina yasa su ji alkhairi.

Ko da ya shiga gida, ya le?a matansa gaba Waya yadda suka tashi turakarsa ya shiga ya kwanta. Yana tasbihi da hailala daga kwance nannauyan barci yayi awon gaba da shi.

?arfe goma da rabi na safe Innaye ta shiga Wakinsa ta tashe shi. Idanunta sun kaWa sunyi jaa, da?i?u talatin ya Sata yana kallonta kafin a hankali

13 / 53