RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   17 / 53

48K to 51K   out of 157.3K words

da take ri?e da shi. Sai kuma ta ce
"Abincin dubu goma zai cika wannan kular ba?"

Duk yadda yaso hana kanshi dariya sai da ya Wan ?ya?yata kafin ya amsa da
"Ai abinci garau-garau na dubu talatin ma bana jin zai cika kular nan. Abuja ne nan fa Aunty, Sai dai kawai aje a siyo na yadda ya samu kuyi maneji."

KuWin gudummuwar da suka tara ma Hafiz da bai karSa jiya ba ya ce ta ajiye mishi zuwa safe gaba Waya ta mi?a ma Mal Musa.
"Ga lambar wayata, don Allah idan ka siyo ka kawo min a sirrance. Ka kira ni nan zan fito in karSa."

Wannan abinci da aka siyo musu, shi ya rufa musu asirin yunwar da Bintu ta barsu da shi da rana har zuwa dare. Da daddaren ma gajiya sukai da kukan ?ananun yara ta kira Rakiya da Ladidi suka shiga can cikin gidan gurin Bintu, shi ne fa har aka yi wannan Satacciyar.


*****
*****


Kamar yadda Aunty Sadiya ta al?awarta musu, cikin ?an?anin lokaci aka wadata su da lafiyayyar dafadukar macakaroni da taji kifin gwangwani. Bayan ruwan gora da aka kai musu har katan huWu, katan shida aka kai musu na kalolin lemuka mabanbanta.

Duk yadda ?amshin abincin ya gama baWe falon da suke ciki daga buWe kular, ko kusa su Aunty Balira basu matsa gurin ba balle har su nuna sha'awar son ci kamar yadda sauran suke nunawa a fili.

Gwaggo Asabe, uwargidan Baba Abubakar ita ta jagoranci rabon abincin da ya ishi kowa a wadace, har suka bar saura a kula. Hatta waWanda suka fara barci duk an tashe su sun wanko baki sun fara cin abinci, duk da a lokacin ?arfe goma sha Waya na dare ta gota da ?an mintuna.

Gwaggo Asabe ita ta Wauki na su Aunty Balira ta kai musu har inda suke zazzaune sun buga tagumi. Ajiye musu tayi, sannan ta koma ta Wauko nata abincin ta zauna a gefensu.
"Rayuwar duniya ha?uri ake yi ?a?an nan, ko baku faWa ba, da yawanmu a cikin nan mun san abinda yake damunku kuma yake ci muku tuwo a ?warya. To amma ya za kuyi? Su fa wasu ?an binnin haka suke, sai dai mu cigaba da ha?uri da mayar da komai ba komai ba a matsayinmu na waWanda Allah ya ?addara ma rayuwa a ?auye. Don Allah ku ci abinci, idan kun yi ha?uri, duk gobe za mu koma inda muka fi wayau. Sannan ina mai baku shawara, kar ku kuskura ku bari matar Wan'uwanku ta shiga tsakanin kyakkyawan zumuncinku, tunda dai shi ba haka yake muku ba."
Cokali ta ciko taf da Macaroni da tunda ta fara magana ?amshinshi yake baWaWe mata hanci ta cusa a baki.
"Kuma..."
Ta cigaba da magana tana shishita da baki saboda zafi da daWin macaroni da ya haWe mata guri Waya, amma tsabar yadda maganar ke cin ranta ta kasa ha?uri ta gama haWiye abincin da ke bakinta.
"Imu-imu... manya da muka zo sunan nan... munyi shawara a tsakaninmu ko mun koma gida baza mu taSa bada labarin abinda matar Hafizu tayi mana ba. Domin Hafizu shi ne namu, daga gare shi kuwa bamu fuskanci wula?anci ko kaWan ba. Kun ga don abinda matarsa tayi mana ai sai muyi mishi uzuri. Abinda ya rage muku dai ku kwaSi bakunan ?annenku, don idan mu manya munyi shiru ba lallai su suyi shiru da bakunansu ba. Musamman ma da ya kasance gaba Wayanku ba ?an Waki Waya bane."
Daga haka bata sake cewa komai ba ta mayar da hankali kan abincinta ta cigaba da saka loma, a hanzarce, kamar mai tsoron wata a cikinsu za ta cinye nata ta ce ta ?ara mata.
[1/7, 10:17 PM] Fareeda Abdallah: Wannan zazzafan abinci kuma daddaWa, da duk loma Waya sai an haWa da kifin gwangwani da aka dafo musu a ?arshen dare, ga Lemu da ruwan gora a wadace, shi ya goge duk yinin da suka yi suna Wame-Wame da yunwa. Kamar dai ba su bane a Wazu duk basa cikin walwala da karsashi, lokaci Waya hira ta game falon, sai shewa suke suna dararraku a tsakaninsu.

Su Aunty Balira kuwa duk da maganganun da Gwaggwo Asabe tayi musu tsattsakuran abincin kawai suka yi, duk dadinsa da d'andanon da yake fitarwa kamar mad'aci haka suke jin sa a bakunansu, ba don komai ba kuwa sai don yadda zukatansu babu dad'i. Ko da suka gama ba tare da sun tankawa kowa ba suka bar gurin zuwa makwancinsu.

Sai da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tasa ha?ar?arinta akan katifa, ta ciro wayarta a cikin ?ar pose, sannan taga kiran da aka rasa na Hafizu har guda biyar. Ta rasa dalilin da yasa haka kawai ta ji baza ta iya magana da shi a daren ba, a ta?aice ma tausayinsa ne ya cika mata zuciya. Wannan fa shi ne misalin karin maganar nan ta bahaushe da yake cewa
"Ga doki har doki amma ?afar na sakaina."

Hafizu yaron arziki, Wan albarka mai son zumunci da ?aunar iyaye da ?an'uwansa. Amma sam baiyi sa'ar matar aure ba. Mace ta gari kuwa ga duk namijin da ya same ta an bashi rabin addininsa ne in ji fiyayyen Halitta SAW, sai ya ji tsoron Allah a sauran rabin.

'Ko yaushe rayuwar iyalin Hafizu za ta saisaitu?'
Ta tambayi kanta da kanta. Domin Bintu dai in dai ba wani iko na Allah ba bata ga alamar canji a gurinta ba, yadda ta san halayenta tana amarya, a yanzu ma babu wani canji sai ma abinda ya karu.

Ga kuma masifaffen so da suka san Hafizu yana yi mata, balle su saka ran kila acan gaba ya dauki kwakkwaran matakin gyara, ko kuma yayi hobbasa ya kara aure ko zai dace da wacce za ta kaunace shi don Allah kuma ta kaunaci 'yanuwansa a yadda suke.
"Uhmmm! Allah kai ka san karatun kurma."
Ta fada a fili da murya kasa-kasa.

Sai kuma tunanin Innaye ya fado mata arai.
'Baiwar Allah'
Ta fada a zuciya. Ita ta san ko Innaye bata fada ba sanin mugayen halayen Bintu ne yasa tunda suka iso akai-akai take kiranta don jin ba wata damuwa ko? Ita dai bata ce mata komai ba don gudun kar ta daga mata hankali.

Nannauyar ajiyar zuciya taja ta sauke. Ta danna maSallin kashe wayar ta kashe gaba Waya don ma kar ya sake kiranta, gobe idan ya dawo sa hadu. Sannan a yadda ta yanke shawara, ita dai da bakinta baza ta yi ma kannenta da suke uba daya magana a kan kar su bada labarin abinda matar Hafizu tayi musu ba.

Shi da ya gayyaci azo mishi suna, har yana daukar shatar motoci, bayan ya san halin matarsa sarai ba kaunar 'yanuwanshi take yi ba. Shi ya kira ma kansa tonon asiri a cikin dangi.

Lumshe idanunta tayi ta fara karanto addu'ar kwanciya barci. 'Yan'uwanta ma da suke kwance kowa da irin tunanin da take yi a zuciyarta, daga karshe ko sai da safe basu iya yima juna kamar yadda suka saba ba. Barci ya dauke su a mabanbantan lokuta.


******


Washe gari duk yadda yaso su dawo Abuja da safe basu samu isowa ba sai misalin sha biyu ds kwata na rana. Daga filin jirgi kuma kai tsaye Ma'aikatarsu aka wuce da su, hankalinsa duk ba'a kwance ba, saboda har lokacin bai samu yayi magana da Aunty Balira ba.

Sauran yan'uwansa kuma da yake ta kira akai-akai yana tambayar lafiyarsu duk sun tabbatar mishi lafiya kalau suke. Ko da ya bukaci a bashi Aunty Balira a waya ya kasa samunta sai suke ta bashi uzurirrika mabanbanta, wadanda sam basu kwanta mishi arai ba. Ya rasa dalilin da yasa, haka kawai zuciyarsa ta ki nutsuwa guri daya.

A bangaren Bintu ma suna ta waya cikin kulawa da kaunar juna kamar yadda suka saba, ko da ya tambayeta lafiyar yan'uwan nashi da yadda suka kwana sake tabbatar mishi tayi suna cikin koshin lafiya.
"Na je da Baby Aadil mun gaisa da su da safe. Ya dade ma a goye bayan Aunty Balira."
Ta yanko karya ta gilla mishi duk don ta sake kankaro ma kanta girma a gurinshi, sannan ta cigaba da cewa
"Kuma tun da sassafe Aunty Sadiya ta jagoranci aikin wadataccen abin karyawa aka kai musu. Yanzu haka kiris ya rage a gama abincin rana da soya naman suna a mika musu, tunda sun ce baza su sake kwana ba yau za su koma gida. Dazu da Raudha za ta shigo ma take ce min ta ga direbobin da suka kawo su sun iso."

Da matukar murna da jin dad'i a muryarsa yake mata godiya da saka albarka.
"Shi yasa a kullum nake kara son ki Bintuna, Allah ya barmu tare. Sai na dawo. A shafa min kan Babana."

Da haka suka yi sallama bayan ta mayar mishi da martanin zakakan kalaman soyayya.

Dakyar ya yakice ayyukan komai ya isa gidan misalin karfe biyu saura kwata na rana. Kuma kamar yadda Bintu ta sanar da shi, ya tarar da abinci waja-waja a gurin yan'uwansa, alamun suna cikin alkhairi dumu-damu. Sun ci, sun koshi, sunyi hani'an, ga kasusuwan naman kaji nan a cikin farantan abincin da suka gama ci, babbar alamar da ke nuna ba'a basu abinci lami ba.

Ya tarar duk sun gama shiryawa, jakunkunan kayansu da wadanda suka kullo a leda duk suna ajiye a falo. Da alamun dai shi kadai suke jiran dawowarsa.

Musayar murmushi ne ya gudana tsakaninsa da Aunty Balira bayan 'yan'uwan sub gama jerangiya wajen yi mishi sannu da zuwa. Shi kuma ya bi Innoni da Gwaggwagganninsu daya bayan daya ya gaishe su.

Ficewa yayi, Aunty Balira ta rufa mishi baya suka kebe can gefe guda.
"Ya hanya? Fatan an dace da abinda aka je nema?"

"Alhamdulillahi Aunty. Me ya samu wayarki? Ina ta kira ba ta shiga, kuma na kira su Aunty Ladidi su had'a mu a waya suna ta bani wasu kalar amso shi..."

"Wayata batir ke da matsala."
Ta katse shi tun kafin ya gama korafin.
"Sai mun koma gida in Allah ya yarda zanyi kokari in canja batirin."

"A'a ba sai kun koma gida ba. Idan na shiga ciki akwai wata karamar waya Torching screen zan dauko miki sai ki saka layinki ki ci gaba da amfani da ita."

"Menene Tochan scrub?"
Ta tambaye shi da yanayin kauyanci. Kafin ya amsa sai ta sake cewa
"Ohoo! ko kana nufin waya 'yar sha-fa? Idan ban manta ba kamar ita naji Zulai na cewa tochan scrub."
Sai kuma tayi dariya ta cigaba da cewa
"Ina ni ina waya 'yar sha-fa Hafizu? Barni dai da mai maballai na. Na fi gane amfani da ita a saukake. Waya 'yar sha-fa a k'auye hannun mata sai irin su Zulai da suka yi boko, idan kuma za ka bani in tafi mata da shi to?"

"Ko ke ma za ki iya amfani da ita Aunty Balira. Kun ki karbar canjin da zamani yazo da shi shi yasa har yanzu kuke a guri daya. Ni ke nayi niyyar ba wayar ba Zulai ba. A sannu za ki saba amfani da ita."

"To shi kenan. Na gode Allah ya kara arziki."

Da murmushi a fuskarsa ya amsa addu'ar da tayi mishi cikin jin dad'i. Har yayi mata sallama kan cewa zai shiga cikin gidan sai ya fito ya sallame su ta ce to.

Ya fara tafiya sai ta kira sunanshi
"Hafizu?"

"Na'am Aunty. In zo ne?"
Ya fada a ladabce. Girmanta yake gani ba kadan ba, domin idan babu Innaye a guri tudu biyu Balira ke ci a gurinsa, Uwa kuma babbar Yaya.

"Kayi hakuri. Kudin gudummuwar da muka kawo maka na ara, idan mun koma gida zan sayar da tunkiya sai in ba Innaye ta ajiye maka kudin..."

"Na bar miki halak-malak Aunty."
Ya katse ta da murmushi a fuskarsa.

Martanin murmushinsa ta mayar masa tayi godiya, tana tsaye a gurin tana kallonsa har ya bace ma ganinta.
Nannauyar ajiyar zuciya taja ta sauke kafin ta koma cikin dakunan da aka yi musu masauki.


******


"Wai me yasa a hotunan taron suna da kika tura min jiya ko daya ban ga hoton su Aunty Balira ba?"

Kasancewar tambayar tazo mata a bazata ne, kiris ya rage ta fad'ar da Aadil da yake rike a hannunta tana kokarin saka mishi nono a baki. Da saurin gaske ta rik'o shi, idanunta a kasa ta ce a daburce.
"Iye! Na'am! Me ka ce Sweetheart?"

Da yake hankalinshi na kan turaren da yake fesawa a jikinsa, sam bai ga yanayin rud'anin da ta shiga ba. A nutse ya sake maimaita mata tambayar da yayi mata.

"Uhmmm!"
Ta fara jan ajiyar zuciya ta sauke, a zuciyarta take ?ara tsara abinda za ta fada mishi ya gamsu.
"Ka san halin su Aunty Balira fa, wai ganin a cikinsu da dattijai da ?ananun yara yasa ta ce kawai ba sai sun je can ba, za suyi taronsu a gida. Da wannan dalilin yasa aka bar musu komai a wadace muka tafi. Ga kyaututtukansu can ma a Waki na, Wazunnan su Aunty Sadiya suka gama packaging."

"Ok!"
Ya amsa a takaice.

Suna hira yana bata labarin yadda tafiyarshi ta kasance har ta gama ba Aadil nono, suka jera suna hira kasa-kasa har suka fice daga d'akin. Tana biye da shi har gurinsu Aunty Balira, duk da yadda kirjinta ke bugawa haka ta daure ta fuske, ko kadan bata nuna wani alamun firgicin gamuwa da su ko tsoron kar su bi ta da wani mummunan kallo ba.

Cikin hukuncin Allah kuma sai suka bi ta a yadda ta zo musu, kadaran-kadahan suka amsa gaisuwar da take ta bin su da shi a ladabce.

Kannenta ne suka yi sallama a kofar falon suka fara shigowa hannayensu rike da jakunkunan da aka zuzzuba ma su Aunty Balira kyaututtukan suna..

Kyaututtuka ne aka hada musu na girma, domin cikin ko wane jaka akwai turmin zani mai kyau ba roba ba, turaren wata a cikin kwalba madaidaiciya, Sunkin sabulun wanka, sai katon kalandar hoton jariri Aadil. Haka ta bi su daya bayan daya ta mika ma kowa a ladabce. Bayan ta ba su Aunty Balira nasu haka sake basu jakunkuna biyar a kaima Innaye, Biyar a kaima Baffa, ta bayar da uku-uku a kai ma kishiyoyin Innaye. Abu dai tubarakallah, kamar ba Bintun nan da take gwada musu wulakanci akan abinci ba, kamar kuma ba ita ce jiya ta rufe idanu ta ci musu mutunci ba.

Su Aunty Balira bin ta kawai suke da idanu, zukatansu cike da matsanancin mamakinta, wato yanzu da yake a gaban d'anuwansu ne, dubi yadda take yi kamar za ta kwanta musu.

'Makira, in Allah ya yarda alkadarinki ya kusa karyewa.'
Aunty Rakiya tayi addu'ar a zuciyarta tana harararta kasa-kasa.

Kyaututtukan basu tsaya anan ba, Aunty Sadiya da kanta ta shiga falon ta bi su da kullin naman suna da yaji, kowa kullinsa daban. Sannan ta bayar da na Innaye da Baffa, da kishiyoyin Innaye.

Hafiz yana tsaye a gefe yana kallon duk abinda ke faruwa, da yake bai san dawan garin ba. Har ga Allah zuciyarsa cike take taf da farin ciki ganin yadda aka karrama yan'uwansa.

Musamman idan ya kalli yadda dattijan cikinsu ke ta zuba murmushi suna kalaman godiya da saka albarka. Su kuma yaran matan suna ta dararraku suna kara yi ma Bintu addu'ar Allah ya raya Aadil ya kara daukaka, ya kuma kare ta daga sharrin makiya da mahassada.

'Yanuwansa uku ne kawai basu yi magana ba, amma labarin da fuskarsu ke bayyanawa karara shi ne suna cikin farin ciki da wannan karamci da aka yi musu.

'Lallai Bintu ta fidda ni kunya. Alhamdulillah'
Kalaman da yake ta maimaitawa kenan a zuciyarsa dad'i yana k'ara lullube shi.

Bayan duk wadannan kyaututtukan, haka ya sake bin duk yawansu da naira dubu biyar-biyar. Ya sake ba su Baban Yasi wadataccen kudin da za su sake cika tankunansu taf har da raran canji, sannan suka kama hanyar tafiya. Kusan kowa aka kalla a cikinsu baki har kunne, saboda matsanancin jin dadin alkhairan da suka samo a gidan Hafizu.

A lokacin karfe uku da rabi na yamma, amma da yake komai dare suna saka ran gida za su kwana in Allah ya yarda. Shi yasa basa fargaban dare da zai iya musu a hanya, fatansu dai Allah ya tsare ya mayar da su gida lafiya.


*******


[1/8, 11:02 PM] Fareeda Abdallah: "Yauwa! Gara da Allah ya shigo da ke yanzu. Na riga na gama yanke shawara gobe idan Allah ya kaimu, bayan sallar azahar za a daura auren Zulaikha da duk wanda Allah ya kaddari shi ne mijinta in sha Allahu."

Tsananin yadda maganar ya duke ta yasa bata san sa'adda ta saki kwanon shan ruwan da ke rike a hannunta ba. Wani jiri ne ya debe ta nan take tayi taga-taga za ta fad'i, da saurin gaske tayi gaggawar dukewa zuwa kasa ta dafe kujerar da ke kusa da bakin kofa.

"Subhanallahi! Rahina? Lafiya kuwa? Ba ki da lafiya ne?"
Baffa ya jero mata tambayoyin da sauri hankalinsa a tashe. A gaggauce ya mike tsaye, ya tsallake huhun goro da dabino da suke ajiye a gabansa ya karasa kusa da ita yana jera mata sannu.

Shi ya kama ta ta mike ta zauna da kyau akan kujerar da ke kusa da ita. Sai sannu yake jera mata ganin yadda take ta hada zufa kamar mare lafiya, ta kasa magana, sai numfarfashi take yi tana kure shi da wani irin kallo da ya rasa gane inda ta dosa.
"Sannu! Daman ba ki da lafiya ne?"
Ya sake tambayarta.

Dakyar ta iya girgiza mishi kai, alamar a'a lafiyarta kalau. Sau uku tana yunkurin yin magana kafin dakyar ta iya kwato kalmomin
"Wa za ka aura mata Malam?"

"Ko wani bawa dai ba ya wuce kaddararsa Rahina. Sa'annan matar mutum kabarinsa. Don Allah ki kwantar da hankalinki, wani ba ya taba auren matar wani. Kuma kin san da son zuciya dai bazan taba yima 'yarki auren da bai kamata ba. Ki kwantar da hankalinki don Allah."
Ya fad'i maganganun a tausashe, idanunsa na kanta yana ?ara karantar yanayinta.

Ta daWe

17 / 53