Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   43 / 53

126K to 129K   out of 157.3K words

dariyar tana haWawa da Wan jijjiga shi.
"Bintu ruwa ya ?are ma Wan kada bai gama wanka ba, daWina da gobe saurin zuwa..."
Ta sake ?yal?yalewa da dariya a hankali don kar ta tashi Aadil. Zuciyarta cike da wani irin farin ciki mara misaltuwa.


******


?arfe biyu da ?an mintuna na tsakar rana ya isa Fa?o. Kamar ko wane lokaci, haka ?an'uwa da abokan arziki suka tarbe shi da matsananciyar murna. Shi kuma ya buWe bakin aljihu kamar yadda ya saba yayi musu yayyafin alkhairi.

Da?yar ya samu ya ?waci kansa suka keSe da mahaifansa, bayan sun sabunta gaisuwa ne yake sanar da su muhimmin abinda yake tafe da shi a wannan rana. Wani abu da ya lura da shi shi ne daga Innaye har Baffa farin ciki ya gaza Soyuwa a fuskokinsu daga jin wannan labarin, wannan shi ya ?ara tabbatar mishi lallai ba?in ciki da takaicin munanan halayen Bintu ya daWe yana damun iyayensa.

Tambaya Waya da Baffa yayi mishi shi ne
"Ka faWa ma Alhaji Lurwanu?"

"Ban riga da na faWa mishi ba Baffa. Amma ina komawa gida in sha Allah ayau zanyi ?o?arin sanar da shi."
Ya amsa kanshi yana ?asa.

"Lallai ya kamata ka sanar da shi da gaggawa, saboda kar su Abubakar su je ya zama ya ji labari daga bakinsu, ka ga idan aka yi hakan ba'a kyauta ba."

"In sha Allah zan faWa masa ayau Baffa."

Bayan sun gama magana da su Innaye ya fita da nufin zuwa gidan Anty Balira ya gaishe ta. Wani arashi da ya tarar shi ne acan ya tarar da Aunty Rakiya da Aunty Ladidi sun je gaishe da Aunty Balira da tayi zazzaSi kwanaki biyu da suka wuce.

Farin ciki sosai ya bayyana a fuskokinsu, sa'ilin da suka gama gaisawa yake faWa musu zai auri Kareema ?anwar mijin Zulai. Addu'o'i kyawawa da fatan alkhairi suka yi mishi, sannan Aunty Balira ta tashi ta zagaya banWaki.

Kuma kun san irin banWakunan da ake yi a ?auye, can nesa da Wakunan gida ake yi saboda masai ne ake yi na gargajiya.

"Haba! Ko kai fa Hafizu? Amma me ake da mace mai mugun ba?in hali da kafirin munafunci da kissa irin Bintu?"
Kalaman da suka fara fita daga bakin Aunty Rakiya kenan bayan ta tabbatar Aunty Balira ba ta jin me take cewa.

Nan fa kamar an matsi bakunansu su biyun suka buWe baki suka dinga kora ma Hafiz labarin irin cin kashin da Bintu tayi ta musu ba sau Waya ba ba sau biyu ba. Amma saboda tsabar munafunci idan yana gurin sai ta dinga musu haba-haba kamar za ta haWiye.

Suman zaune kawai Hafiz yayi yana jin waWannan ba?a?en labarai masu barazanar fasa mishi zuciya. Tabbas idanunshi sun buWe, kuma ya fahimci kissa da munafuncin Bintu, amma bai taSa tsammanin ta daWe tana wasan kwaikwayo da fahimtarshi har na tsawon lokaci haka ba.

Bai ?ara shiga cikin tashin hankali ba sai da Aunty Ladidi ta ce
"Ni fa duk waWannan munanan halayen nata abu Waya da idan na tuna har yanzu yake min ciwo a zuciya shi ne yadda da gangar ta so kashe Innaye... Yo ta so kashe ta mana. Tunda ai likitan nan na asibitin Nasin Ham (Nursing home) Ya faWa ma Aunty Balira cutar da ke damun Innaye daban magunguna da alluran da aka yi ta zurkuWa mata daban, har ya ?ara da cewa lallai duk likitan da ta ba Innaye waWannan magungunan ta so kawai ta illata ta ne..."

"WaWanne irin zantukan banza ne kuke faWa ma Hafizu haka Rahina?"
Aunty Balira ta katse ta cikin tsawa da Sacin rai.

Firgigit suka yi duk su biyun, sai a lokacin suka dawo hayyacinsu suka lura da wasu zafafan hawaye da ke kwaranya a idanun Hafiz. Duk da sun san gaskiya suke faWa, sai kuma jikinsu yayi sanyi ?alau da ganin irin hawayen da ke gudu akan fuskarsa.

FaWa Aunty Balira ta rufe su da shi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, a ?arshe ta ce su Sace mata da gani tunda su ba su da hankali suna so su shiga tsakanin mata da miji.

Sum-sum suka saka hijabansu suka fice daga Wakin, jikinsu sanyi ?alau, kamar an she?a musu ruwan sanyi.

Kusa da Hafiz Aunty Balira ta zauna ta fara rarrashinshi da tausasan kalamai. Duk da ta nuna Sacin ran abinda su Rakiya suka yi amma ko kaWan bai ji ta ?aryata maganganun da suka faWa mishi ba.

Sai da ta daWe tana rarrashinshi sannan da?yar ya tsagaita sharSen hawayen da yake yi. Ya Waga kanshi yana kallonta da idanunsa jajaye ya ce cikin rawar murya
"Amma... Amma... me yasa baku taSa ankarar da ni ko ku fito ?arara ku faWa min irin abubuwan da ke faruwa ba...?"

"Ta ina za mu samu ?warin gwuiwar faWa maka Hafizu bayan duk mun fahimci irin son da kake mata, sannan mun ga yadda idanunka suka rufe ruf a kanta. Ca nake don a sama maka sau?i ne Baffa ya Wauki Zulai sukutun da guda ya aura maka amma ka watsa masa ?asa a ido?"

A karo na biyu du?ar da kanshi yayi ya cigaba da sharSen hawaye, a zuciyarsa yake tuna yadda ya ?e?ashe ?asa ya biye ma Bintu ya kasa yi ma iyayensa biyayya. Ya daWe a haka kafin ya iya tsayar da hawayen da?yar! Ya laluba aljihunsa ya Wauko damin kuWi yayi mata alkhairi kamar yadda ya saba, ya bata na Ladidi da Rakiya, sannan ya bata wanda za ta raba ma ?an'uwansa mata da suke uba Waya.

Jikinsa a sanyaye ya mi?e yayi mata sallama zai wuce, har zaure ta raka shi tana sake haWa shi da girman Allah kar ya kuskura ya ce zai hukunta Bintu da laifukan da suka gabata.
"Ka gode ma Allah da yasa idanunka suka washe akan halinta. Ka ga yanzu sai ka sake sabon lale akan zamantakewar da za kayi da ita. Mu dai Allah ya sani bamu ri?e ta arai ba."
Da haka suka rabu.

Ko da ya koma gida gurin Innaye, duk yadda ya so su sake tauna zancen ta ?i bashi damar haka. Da murmushi a fuskarta take ?ara tabbatar mishi ita bata ri?e Bintu arai ba, kuma bata yafe mishi ba idan ya hukunta Bintu da laifukan da suka gabata.

A karo na barkatai ya du?a har ?asa ya sake neman yafiyarta, ta ?ara jaddada mishi ta yafe sannan ya fita gurin Baffa.

A can Win ma dai zancen suka sake taunawa, a matsayin Baffa namiji, ya sake bashi shawarwari masu kyau na yadda zai zauna da Bintu, a yanzu, da kuma bayan ya ?ara aure. Kamar haWin baki shi ma dai sake jaddada mishi yayi kar ya kuskura ya ce zai Wauki wani mataki akan Bintu. Abinda ya wuce a barshi a wanda ya wuce.

Yamma li?is ya bar Fa?o, bakunan iyaye da ?an'uwanshi cike da addu'ar Allah ya maida shi Abuja lafiya.

Da yake tun yana hanya ya kira Abba Lurwanu ya sanar da shi akwai muhimmiyar maganar da yake so suyi, amma yanzu yana hanyar komawa Abuja, idan Allah ya sa ya koma lafiya kuma dare baiyi sosai ba zai tsaya a gidanshi suyi maganar.

Wannan dalilin yasa ko da ya shiga Abuja ?arfe goma na dare ya wuce gidan Abba Lurwanu. Acan ya ci abincin dare, bayan sun gama tauna maganar neman aurenshi da Kareema sannan ya kama hanyar komawa gida.

Da wannan gajiya da Sacin ran ne bayan isarsa Bintu ta so ta kunno ma kanta bala'i shi kuma ya karta mata kashaidi, haWe da rantsuwar ba don rayukan mutane uku mafiya muhimmanci a gare shi ba (Baffa, Innaye, Aunty Balira) Da yanzu wani zancen ake yi tsakaninsu ba wannan ba.



************
Ta Wauki tsawon mintuna ashirin a tsaye inda ya barta, jikinta sanyi ?alau. Zuciyarta a cunkushe, ta ma rasa wani irin takamaimai tunani ya kamata tayi.

A ?arshe dai da taga tsayuwar bazai fissheta ba sai taja ?afafunta a sanyaye ta koma cikin falon. Har ta Wofana mazaunanta akan kujera, sai kuma ta mi?e tsaye tsulum kamar an tsunguleta.

Wayarta da ke ajiye can gefe Waya ta Wauka ta fara tafiya zuwa Wakinta. A hannunta tana lallatsa wayarta, lambar Raudha ta lalubo ta danna mata kira ba tare da duba tsalawar da dare yayi ba.

Wayar tana daf da tsinkewa Raudha ta Wauka da magagin barci sosai a muryarta.
"Bintu? Lafiya kike kuwa? Me ya faru?"
Ta jera mata tambayoyin a rarrabe.

"Yi ha?uri Raudha na tashe ki kina barci... Daman zan faWa miki abinda ya faru bayan dawowar Hafiz ne..."

"Toh! Toh!! Ina jinki!!! Amma Ina fatan dai ya dawo miki da Aadil?"
Ta tambayeta da murya mai cike da Woki da sakankancewa.

"A'a! Bai dawo da shi ba."
Ta amsa da rawar murya.
"Alfarmarki nake nema don Allah Raudha."
Ta sake faWa muryarta na ?arasa karyewa sosai. Don tsabar fitina da bala'in da ta saka ma ranta duk yadda nonuwanta ke ciwo suna tsikarinta saboda yaye ko jin su ba ta yi. Ba komai ke ?ara karya ma Bintu zuciya ba sai idan ta tuno ita tana nan a birni irin Abuja Aadil Wanta yana wula?antaccen ?auye irin na su Innaye, ?auyen da ko ita da girmanta bata taSa gigin yin kwana Waya a ciki ba.

Ta sani aminci ne mai ?arfi tsakaninta da Raudha. Babu wani alfarma da za ta nema gurin Raudha ta ?i yi mata kamar yadda ita ma a Sangarenta za ta iya yin komai don kare martabar Raudha.

"Kin sani kin wuce komai a gurina Bintu. FaWi duk abinda kike so kawai inyi miki ki ga aiki da cikawa."
Cewar Raudha daga can Sangaren da muryar da ke nuna da dukkan gaskiyarta take magana.

Nannauyar ajiyar zuciya Bintu ta sauke, ta lalubi gefen gadonta ta zauna sannan ta cigaba da magana.
"Ina wannan mutumin naki na filin jirgin ?asa wanda ke samar mana da ticket Win zuwa Kaduna a sau?a?e?"

"Lurwanu? Yana nan. Me kike so yayi miki?"

"Ki tura masa sa?o a darennan ya tanadar mana da ticket biyu na jirgin gobe da safe. Bazan iya ba Raudha, Wallahi tallahi bazan taSa iya barin Aadil ya kwana biyu a ?auyennan ba. Goben nan zan je in Wauko shi, duk abinda Hafiz zaiyi ya daWe baiyi ba..."

"To me ma ya isa ya yi? Ai shi kansa ya san ba shi da gaskiya... Duk inda za aje a dawo kin fi shi gaskiya Bintu, kamar yadda kika fi shi girman ha??i akan Aadil har a gurin Allah... Don haka kar ma ki wani Waga hankalinki. In banda ma tun safennan bamu yi tunanin zai iya barin Aadil acan ba ai da tun ayau za muje mu Wauko shi. Ki kwantar da hankali ?awata..."

WaWannan maganganun na Raudha, su suka zaftare kaso arba'in cikin Wari na damuwar da ke dan?are a zuciyar Bintu. Da wannan dalilin yasa bayan sun gama waya da Raudha har ta iya samun ?warin gwuiwar zuwa kicin ta haWa tea mai kauri ta sha. Ta Salli paracetamol guda biyu ta haWiya, ta sake yin wanka sannan ta bi lafiyar gado.

Ko tunanin Hafiz bata yi ba balle tayi gigin zuwa Wakinshi su kwanta. Abinda bai taSa faruwa ba tsakanin su biyun raba makwanci tunda suka yi aure, in dai ba tafiya Hafiz yayi ba.


*********


Washe gari tunda sassafe Hafiz ya ji ?arar tada motar Bintu, yana kwance a kan gadonshi. Tunda ya tashi yayi sallar asubahi a makare saboda rashin barci da bai samu yi da wuri ba, ya kasa fita ya duba ta tashi ko bata tashi ba?

Azkhar ma sama-sama ya yi ya sake bin lafiyar gado da nufin yin ramuwar barci. Ya kwanta kenan ya ji tashin motar Bintu, mamaki ne ya kama shi har ya tambayi kanshi.
'Ina Bintu take niyyar zuwa ba tare da ta faWa mishi ba?'

Sanin ko daga can asibitinsu ne aka yi mata kiran gaggawa tana faWa mishi kafin ta fita yasa shi yin mamakin fitar tata a yanzu. A hankali ya ya ye bargon da yake lulluSe da shi ya sauka daga kan gadon, ko kafin ya fita daga Wakin ma har mai gadi ya buWe mata get ta fice daga gidan.

Don haka bai Sata lokacin duba Wakinta ba ya san ita ce ta fita, tunda direbansu ba ya nan. Idan ba ita ba wa zai Wauki motarta ya fita da ita da sassafen nan.

Ko da ya koma cikin Wakinsa, har ya kwanta, sai kuma yayi tunanin bai kamata ya ri?e Bintu har ya banzatar da al'amarinta haka ba. Tunda su kansu iyayenshi sun ro?e shi alfarmar kar ya kuskura ya hukunta Bintu da laifukan da suka gabata.

Wayarsa ya Wauko, ya lalubo lambarta ya danna mata kira, sannan ya kara wayar a kunnensa yana jiran ta Wauka ya ji me yasa ta fitan sassafe haka? Don a saninsa yau ba ta da aiki in dai ba wani muhimmin abu bane ya taso mata.

A can Sangaren Bintu, tana ganin kiran ta jaa wani dogon tsaki ranta a Sace.
"Aikin Sur in ji tusa! Ai kuma sai ka yi. Na rantse da Allah idan za ka kira sau dubu bazan Wauka ba. Kai ma ka WanWana ka ji idan a kira mutum ya ?i Wauka da daWi. Don ma dai ni da hannuna bazan iya blocking Win ka bane kamar yadda ka yi min."

Ita kaWai a cikin mota tana tu?i tana masifa har ta isa gidan Raudha. Ko da ta shiga ciki basu wani Sata lokaci ba suka fito, domin a shirye ta tarar da Raudha. Motar ta suka sake shiga mai gadi ya buWe musu ?ofa ta figi motar a guje suka bar gidan.

Kamar yadda suka tsara, komai ya tafi musu daidai yadda Bintu ta so. ?arfe goma sha Waya da minti hamsin na safiya mai taxi Win da suka Wauki shata tun daga Kaduna yayi fakin a ?ofar gidansu Innaye.

Tana gyara zaman ?wamemen ba?in gilashi no respect da ta siya a Kaduna ta saka a idanunta take cewa da direba.
"Malam ka Wan jira mu kaWan, kamar yadda na ce maka ba daWewa za muyi a ciki ba. Yaro kawai zan Wauko ka juya da mu inda ka Wauko mu."

"Babu damuwa Hajiya. A fito lafiya."
Ya amsa a ladabce.

Har sun nufi zauren gida?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 n Raudha ta dakatar da ita, zip Win jakarta ta zage, ta cusa hannu a ciki ta Webo cingam guda huWu ta mi?a ma Bintu biyu itama ta Sare biyu ta watsa a baki ba tare da kunyar idanun mutane da ke kallonsu ba.
"Saka wannan a baki ki tauna cikin ?warewa ?awata. Kin san sheggun ?auyen nan in bi ki nuna musu ke ma ?ar iskar kanki bane baza su baki Aadil a sau?a?e ba. Kuma ko da wasa idan muka shiga kar ki kuskura kunyar ?ar iskar tsohuwar nan ya hana ki yayyaSa mata ba?a?en maganganu..."

"Kin san wannan ai dole ne Raudha. Yadda raina ya Saci Wallahi dole nata ya ninka nawa Saci. Mu je. Shegu yaran ?auye dubi yadda suke kallonmu kamar mayu... kurwanmu kur!!!"
Ta ?arasa maganar da Wan ?arfi tana kallon wani yaro Wan tsamurarre da tulelen ciki wanda tun Wazu yake tsaye gefe ya ?ura musu idanu.

Bayan ta Sare cingam Win ta watsa a baki sai ta nufi cikin gidan tana sake tamke fuska. Raudha na biye da ita a baya itama da nata fuskar a haWe babu sassauci ko kaWan.


******


A cikin gidansu Innaye, misalin ?arfe goma sha Waya da kwata na safiyar ranar, Aunty Balira, Rakiya, Ladidi suka yi ma gidan dirar mikiya.

Bayan barinsu gidan Aunty Balira jiya, da daddare ta kira su kan cewa su tambayi mazajensu su haWu su ukun su je suyi ma Innaye Allah sanya alkhairin aure da Hafiz zaiyi. Wannan shi ne abinda ya kawo su, ashe rabon suyi kiciSus da Hajiya Bintu ne.

Suna zaune a tsakar Wakin Innaye kan tabarma suna shan Fate da Mama Laraba tayi, hira suke da dararraku a tsakaninsu ukun, Innaye tana zaune a kan kujera tana saka musu baki jefi-jefi.

Suna cikin wannan halin ne suka ga an yaye labulen Wakin, kwatsam! Sai ga Bintu ta bayyana da Raudha tsaye a bayanta, sai taunar cingam suke yi ?aras-?aras cike da tsantsar raini da fitsara.

Da farko duk ?amewa suka yi ana kallon-kallo a tsakaninsu. Sai Aunty Rakiya ta karya shirun da cewa
"A'uzubillahi minasshaiWanirrajeem."

Da matsanancin Sacin rai a muryar Bintu ta ce
"Kan'uba!! Amma lallai Rakiya kin ci uwar rainin wayau. Ni za ki kalla kiyi wa a'uziyya? To Me kike nufi?"

"Me kuwa nake nufi in banda korar shaiWan da nayi? Idan banyi a'uziyya ba me kike so inyi? In ba shaiWaniya a cikin siffar mutane ba wacece za ta shigo Waki mai daraja irinna sarkuwarta babu sallama...?"

"Rakiya!"
Innaye ta kira sunanta da Wan tsawa-tsawa a muryarta.
"Ya isa haka nan."
Ta sake faWa tana ?o?arin sassauta muryarta.

A karo na biyu ta mayar da idanunta kan Bintu ?irjinta na bugawa kaWan-kaWan. Ta daWe da sanin Bintu ba ta da mutunci, amma tsantsagwaron rashin mutunci irin wanda take ?o?arin shimfiWa musu yau bata taSa ganin ta yi ba. Tunaninta Waya ne, Bintu ta ji Hafiz zai auri ?anwar mijin Zulai shi ne ta zo ta sauke musu rashin mutunci don a tsammaninta da haWin bakinsu ake shirin ?ulla auren.
"Fatima lafiya? Me yake tafe da ke?"
Ta tambayeta bayan ta tuna zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya.

Yatsarta manuniya tasa ta ja gilashinta ?asa kaWan, ya zama tana kallonsu Waya bayan Waya ta saman gilashi. Cingam Win da ke bakinta ta tauna yayi ?as, ta huro shi yayi ?aton balo-balo ta fasa sannan ta fara magana tana yamutsa fuska kamar tana sha?ar warin kashi.
"Innaye... Kin ga ina ganin mutuncinki, kuma da gaske ina ganin girmanki. Bana tunanin tunda na auri Hafiz wani sa'insa ya taSa shiga tsakanina da ke, don haka kar ki bari mu fara ayau. Salin-alin ki bani Wana in tafi da shi..."

"Saurara Bintu! Wani

43 / 53