Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   22 / 53

63K to 66K   out of 157.3K words

faWa mata maganar banza? Yi maza ki ba ta ha?uri kafin in tattaka ki anan gurin"

A tsorace, ta Waga idanu ta sake kallonsa. Ganin yadda yake zazzare mata idanu kamar zai haWiye ta yasa da saurin gaske ta kawar da idanunta ta mayar kan Bintu da take tsaye a bayansa hannayenta harWe a ?irji, da alamun al'amarin ba ?aramin daWi yayi mata ba. Domin idan ba idanun Zulaikha ke mata gizo ba sai taga kamar murmushi Bintu take yi.

A tsorace da salon kare kai ta fara magana bakinta na rawa
"Yaya ita ce fa..."

"Na tambaye ki ?arin bayani?"
Ya katse ta cikin tsawa.
"Za kiyi abinda na umarce ki ko sai na tattaka ki a tsakiyar falon nan?"

Lokaci Waya itama ranta ya Saci, a ganinta wannan ai rashin adalci ne ?arara. Taya zai yanke hukunci kai tsaye ba tare da jin dalilin da yasa ta mayar ma da Bintu ba?ar magana ba? Har ta tsuke baki alamun baza ta ba Bintu ha?urin ba, sai dai duk abinda zayyi yayi, idan yaso ya kashe ta.

Sai kuma wani sashe na zuciyarta ya tunasar da ita matsayin Yayan yanzu a gurinta. ?in aikata abinda ya umarceta matu?ar ba saSon Allah bane kamar ta gayyato ma kanta tsinuwar mala'ikun rahama ne.
"Kiyi ha?uri."
Ta faWa cikin fushi bakinta a zumSure.

Guri ya nema ya zauna kan Waya daga cikin kujerun falon ya fara zazzaga mata faWa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Da alamun haushin abinda ya faru da shi a ?auye yake son saukewa a kanta bayan ba ita ta kar zomon ba.
"Bazai yiwu ba. Bazan taSa yarda da irin wannan rainin da iskancin da kika saba yi mana ba. Idan ma za ki saka ma kanki nutsuwa da karatun ta nutsu gara ki saka, tun wuri gara ki sauke duk wani rawar kai da wani gigi da yake damunki, idan ba haka ba na rantse da Allah ba ?aramin wahala za ki sha da ni a gidannan ba.

Ko ban faWa ba ke kanki kin sani, ta ko wane Sangare na rayuwa matata gaba take da ke. Ta sha gabanki fiye da yadda kike tsammani, in dai kika ce raini da tsaurin idanu za ki nuna mata, lallai kuwa zan kawar da duk wata sanayya da dangantaka in koya miki hankali fiye da yadda kike tsammani..."

Bai san Zulaikha kuka take yi ba, sai da ya ji shesshe?arta ya cika falon. Duk da haka bai sassauta faWan da yake yi ba, sai ma ?ara caccaSa mata ba?a?en maganganu yake yi kamar bai san daga inda ta fito ba, duk da sunan ?wa??waran kashaidi da jan kunnen ta kiyaye irin zaman da za tayi a gidansa da kuma iyalinsa.

Bintu da matsanancin farin ciki ya gama ?ume ta, kamar ta zuba ruwa a ?asa tasha take ji. Sai da ya daWe yana cin zarafin Zulaikha ita kuma tana ta rusa kuka kafin a yangace ta ?arasa inda yake zaune, akan cinyarsa ta zauna, ta Salle maSallai biyu na gaban rigarsa ta fara shafa ?irjinsa ba tare da kunyar idanun Zulaikha ba.
"Ayya mana My dear... don Wan wannan abin da ya faru ne kake Sata ranka haka? Ka san fa halin Zulai ciki da waje, ni kawai ina mata uzuri ne saboda har yanzu yarinya ce, da ?uruciya a kanta. Kayi shiru haka pls, ka ga da gajiya a jikinka har yanzu, kar ka bari abinda bai kai ya kawo ba ya taSa min zuciyata."

Shiru yayi yana mayar da numfashi, da alamun maganganunta ba ?aramin taSa shi suka yi ba.

Bintu kuwa mayar da hankalinta kan Zulai da har lokacin take kuka tayi da wadataccen murmushi a fuskarta.
"Kin ga Zulai yi shiru, share hawayenki. Daga waWannan maganganun na Yayanki dai ya isa yasa ki hankalta, ki san yanzu fa ba da bane. Idan wancan karon ganin idanun Innaye yasa kin tsula tsiyarki yadda kike so wannan karon baza kiyi ki ci riba ba. ?auki jakarki ki tafi can Sangaren da kuke sauka ki yi wanka ki huta, gurin a share yake a goge, tun bayan tafiyar su Aunty Balira da aka gyara ba na jin yanzu ya sake yin ?urar da zai sa ki sabon shara."


[1/23, 10:25 PM] Fareeda Abdallah: Duk ba?a?en maganganun da take yaSa ma Zulaikha a fakaice tana jin ta, kuma tsaf ta fahimci sa?on da take aika mata. Amma a madadin ta mi?e ta aikata umarnin da Bintu tayi mata, sai kawai ta ?ara gyara zama ta cigaba da kukan da take yi.

"Au! FaWan Yayan naki bai ishe ki ba kenan ko? Ki tashi ki tafi masaukinku na ce tun kafin ranshi ya ?ara Saci..."

Cikin Sacin rai da muryar kuka Zulaikha ta katse Bintu da cewa
"Ni fa bazan zauna acan Sangaren ni kaWai ba. Tun a gida ma ai Innaye cewa tayi a matsayina na..."

"Wa ya tambaye ki wani matsayi da kike da shi a gidannan? Za ki rufe mana baki a gurin nan ko sai na Wora hannu a jikinki?"
Hafiz ya katse ta da saurin gaske tun kafin ta ?arasa Saram-Saramar da take niyyar yi.

Sunkuyar da kai ?asa tayi ta cigaba da jan shesshe?ar kuka. Ba ta ma da niyyar tashi ta Wauki jakarta balle har Bintu ta saka ran za ta aikata abinda ta umarce ta. A mamakance, Bintu take kallon Hafiz, sai kuma ta kalli Zulaikha. Duk ga zatonta cikin tsawa da faWa zai sake balbale Zulai da umarnin ta tashi ta tafi can Sangaren da suke sauka.

Amma a madadin ta ji ya faWi abinda take tsammani, sai kunnuwanta suka jiyo mata kalamansa kamar saukar aradu yana ce mata
"Sweetheart! Ki ?yale ta anan. Kin ga ita kaWai ce, can Sangaren ba?i yayi mata girma, baza ta iya zama ita kaWai acan ba. Tunda ga Mashku anan sai su zauna a Waki Waya..."

"Bazai yiwu ba gaskiya My Dear. Mashku ko a gida ba ta yarda ta haWa Waki da su Amina ?annenta ballantana ta haWa da wacce bata sani ba. Tunda akwai wadatar Wakuna anan Win, ita ma sai ta Wauki Waki Waya tayi amfani da shi. Excuse me pls! Bari in duba girki."
Ta mi?e daga jikinshi da sauri ba tare da jiran abinda zai sake cewa ba.

Da haka aka bar maganar saukar Zulaikha a can Wakunan BQ. Shi da kanshi ya tashi, yaje ya buWe mata Waya daga cikin ?ayatattun Wakunan da suke nan ?asa, sannan ya koma gurinta fuskarsa a Waure ya umarci ta Wauki jakarta zuwa cikin Wakin.

Tana shiga, ya mayar da ?ofar ya rufe, kusa da inda take tsaye ya ?arasa a bazata ya dam?o kunnenta na dama da yake cikin hijabi ya murWa, a gigice ta buWe baki za ta ?wallah ihu da saurin gaske ya toshe mata baki bayan ya saki kunnen da sauri.
"Kin san Allah? Muddin kika yi gangancin faWa ma matata an Waura mana aure da ke acan gida na rantse sai na Satar da ke a cikin garin nan, sai dai duk abinda zai faru ya faru."

Cizon da ta gantsara mishi a tafin hannu yasa shi sakin bakinta da sauri ya matsa baya yana yarfe hannu, ga dukkan alamu ya ji zafi sosai.
"Cizo na kika yi?"
Ya tambayeta fuskarsa a Waure.

"Eh Win"
Ta amsa a tsiwace, zuciyarta cike fam da takaicinsa.
"Kuma na rantse da Allah idan ka sake min irin wannan cin mutuncin a gaban matarka sai na kira Baffa da Innaye na faWa musu duk irin wula?ancin da kake min tunda kazo da ni garinnan."

A fusace ya mi?a hannu zai dam?o ta. Da mugun sauri ta zille masa, sannan ta ?walla wani gigitaccen ihun da yasa ba shiri ya fice daga Wakin da saurin gaske jin da yayi karaWin ihun na barazanar toshe mishi dodon kunne.

A guje Bintu ta fito daga ?aramin kicin Winta suka yi kiciSis da shi a tsakiyar falon.
"Lafiya ? Ihun me nake ji? Kar dai ace dukanta kayi?"
Bintu ta tambaye shi da damuwa a fuskarta. A zuciyarta kuma addu'a take yi Allah yasa dukan Zulaikha yayi.

"Yarinyar ba ta da kunya Sweetheart. Idan ba taSa lafiyarta nayi ba baza ta shiga taitayinta ba. Bari in je Waki, ki kawo min abincina sama."
Yana gama faWin haka ya fara hawa matakalar sauri-sauri. Zuciyarsa cike da damuwa da ?uncin aura mishi Zulaikha da aka yi.

Gaba Waya kanshi ya kulle, ya ma rasa ta ina ya kamata ya Sullo ma al'amarin? Ga shi ya rasa hanyar da zai bi wajen sanar ma da Bintu yanzu matsayin mata Zulaikha take a gurinsa. Domin bai manta irin al?awurran da suka Wauka ma junansu kafin aure da kuma bayan aure ba.

A al?awuran da ya Wauka mata akwai, ita kaWai ?wallin ?wal ta ishe shi rayuwar duniya. Ita kuma kaWan daga cikin al?awuran da ta Wauka mishi shi ne ako wane hali wuya ko daWi za ta kasance tare da shi, za ta bashi ?ololuwar farin ciki fiye da wanda yake tsammanin samu daga gare ta. Za kuma tayi duk iya mai yiwuwa wajen bashi dukkan tarairaya da soyayyar da zai kawar da hankalinshi daga kan ko wace mace sai ita ?wallin ?wal.

To ga shi tun ba'a je ko ina ba an fara samun karya al?awari daga gare shi, shi kam ya zayyi ne? Ina zai sa kansa? Kuma ta wace hanya zai Sullo ma wannan ?addararren aure da su Baffa suka ?ulla masa?


****** ******
Zulaikha mai bala'in son girma sama da ?asa ta kalle ta, sai kuma ta Wanyi dariya. Tana jin wani girma na ?ara mamayeta, daga yadda ta ga yanayin jikin Mashkura Wan daidai kamar na Bintu, duk ga tsammaninta bata wuce shekaru goma sha biyar ko sha shida ba.
"Uhmmm! Ta ina kika taSa ganin anyi ?awance tsakanin ?ar birni da ?ar ?auye? Sannan kuma ni ba yarinya bace fa, na girme ki nesa ba kusa ba, shekaruna sha takwas cif..."

Sassanyar dariyar da Mashkura ta ?yal?yale da shi yasa Zulaikha tayi sakalau da baki tana kallonta. Sai da tayi dariyarta ma'ishi kafin ta ce ma Zulaikha
"Shekaru sha takwas ne kike faWin kin girme ni nesa ba kusa ba? To ni shekaruna ashirin da Waya, Wallahi da gaske nake miki. Kawai don kin ganni da Wan ?aramin jiki ke kina da ?iba shi ne kike min kallon ?aramar yarinya? Sannan in banda ke da abin ki, da ni da nake birni da ke da kike ?auye ai duk Allah ne ya halicce mu. Babu wacce ta fi wani a gurin Allah sai wacce ta fi tsoronsa. Sannan kuma ?awance ba'a shekaru bane, shekaru lambobi ne kawai. Ni dai don Allah ki karSi tayin ?awance na, kin ga, yanzu ma dai bani lambar wayarki."

Duk yadda Zulaikha ke zillewa a dole ta saki jiki da Mashku har suka yi musayar lambobin waya. Da yake Mashku irin yarannan ne da in suna son ka suna so ne da dukkan zuciyarsu, tana da miskilanci amma idan ta so hira sosai take sakin jikinta tayi har da ?ya?yata dariya. Balle kuma ta haWu da Zulaikha ga barkwanci ga wauta, cikin ?an?anin lokaci sha?uwa ta shiga tsakaninsu.

Yadda suka bararraje a tsakiyar gadon suna hira da dariya, kamar sun daWe da sanin juna. Har Mashkura ta fice zuwa kicin ta haWo musu tea mai kauri a kofuna biyu, suna sha suna hira.

A daren, Mashkura ta tura ma Zulaikha fina-finai masu yawa a cikin wayarta. Sannan ta ?ara da wayar mata da kai kan yadda ake amfani da wayar Android, ta kuma koya mata games Win da ta tura mata masu daWi da za su taimaka gurin Webe mata kewa da zaman kaWaita.

Tunda ita Mashkura ba zaman gidan sosai ta cika yi ba, kullum da safe takwas zuwa tara na safe take ficewa zuwa makaranta.

Ba tare da kunya ko wani kwana-kwana ba Zulaikha ta faWa ma Mashkura ita fa ba ta jin turanci.
"Kin san karatunmu na ?auye, ba Waya ne da naku na birni ba. Sai dai na iya karatun hausa fiye da yadda kike tsammani, turancin ne dai ?an ?ananun kalmomi kawai nake iya ji in fahimci abinda ake nufi."

"Kar ki damu. Don wannan ai ba wata matsala bace. Sannu a hankali zan tsara mana jadawalin da za mu dinga bi ina koyar da ke abubuwa masu yawa, idan kika mayar da hankali kuma kika nace cikin wata uku bakinki zai goge da turanci kamar ?anwar mangwafak! Kin san shi karatu naci yake so, sannan kuma hausa ya fi turanci wahalar koyo, tunda kika iya karatun hausa, turanci bazai wahalar da ke ba in Allah ya yarda."

Maganganun Mashkura ba ?aramin daWaWa ma Zulaikha rai suka yi ba. Sai godiya take zuba mata kamar ma har ta iya turancin. Allah ya sani a yanzu ba ?aramin son ta koyi turanci take yi ba. Ta iya a baki, idan an faWa ta san me aka ce, kuma ta iya mayar da martani da yaren turanci, sannan idan ta gani a rubuce ta karanta ta kuma fahimci me ake nufi.

Idan ta iya waWannan, Waya daga cikin manyan burikanta sun cika. A da can baya bata taSa damuwa da koyon turancin ba, bata ma Wauke shi a wani kayan gabas ba. Sai bayan shigowar Bintu cikin ahalinsu ne ta gane lallai fa ta tafka kuskure rashin mayar da hankalinta a karatun boko. Ba ma kamar yadda minti Waya biyu Bintu take goranta mata da munanan kalmomi kamar jahila, da?i?iya, ba?auyiya, wawuya, a ganinta, rashin iya turancin shi ke sa Bintu goranta mata da waWannan munanan kalmomin.

Mashkura bata bar Wakin ba sai misalin ?arfe Waya da minti arba'in na dare. Sun rabu duk su biyun zukatansu cike da farin cikin hirar da ta gudana a tsakaninsu.

Har Zulaikha ta kwanta, ta Waga hannu za ta fara karanto addu'ar barci kenan sai ga Mashkura ta sake shiga cikin Wakin bakinta Wauke da siririyar sallama.
"Kiyi ha?uri da ni ?awata. Yau dai na hana ki barci."
Ta faWa tana murmushi. Kayayyaki masu Wan dama da suke ri?e a hannunta ne ta zube su a gefen gadon, ta fara WaWWaga su Waya bayan Waya. Kayan barci ne masu kyau da laushi sosai a ido har kala uku, riga da wando biyu, sai kuma riga ?ar ciki da ta samanta guda Waya. Sai kuma Abaya sababbi masu kyau sosai kala uku.
"Ban san ko nayi miki karambani ba. Allah yasa dai kina saka kwance, duk da dai kamar sabbi suke a gurina. Domin bayan sau Wai-Wai ban ?ara saka su ba. Na kawo miki ne ko kina so, na ga manya ne, za suyi daidai da jikinki."

Tsananin murna da farin ciki, yasa Zulaikha ta kasa cewa komai. Lokaci Waya tayi ?wal-?wal da idanunta, can kuma sai ga hawaye shar... sun zubo daga kwarmin idanuwanta. Lallai sai a yanzu ta ?ara yarda da maganar Mashku da ta ce ba halinsu Waya da Bintu ba. Ashe haka Allah ke ikonsa dare Waya ya haWa ?auna a zukatan bayinsa?
"Na gode Mashku. Na gode, Allah yabar ?auna da zumunci."
Kalaman da take ta maimaitawa kenan cikin kuka da dariya, sai WaWWaga kayan take yi tana jinjina kyawunsu a idanunta.

Ko Mashku bata faWa ba, daga yanayin kyawun kayan sun isa su bayyana maka masu tsada ne sosai. In dai ba ta manta ba za ta iya rantsewa da Allah ba'a taSa yi mata kyautar kaya irin haka kuma daga bare wacce basu haWa komai da ita ba.

"Don Allah ki daina hawayen nan da kike yi. Miye don na baki Wan wa?annan kayan? Ba komai bane fa, kuma don ma yanayin jikinmu ba Waya bane ai Wallahi da sai na haWa miki akwati guda. Ni kin ga ma tafiyata tunda baza ki daina kuka ba. Allah ya tashe mu lafiya."
Da sauri ta fice daga Wakin taja mata ?ofa, fuskarta yalwace da farin ciki.

Ko bayan fitar Mashku, ta daWe bata yi barci ba. Bayan ta gama matsar ?wallar da take yi murza key tayi a ?ofar Wakin ta kulle. Ta canja ?wan lantarki zuwa mai haske ta fara gwada kayan Waya bayan Waya.

Wani ikon Allah kamar da man can kayan domin ita aka siya. Sunyi mata dai-dai, kuma sunyi mata a wadace, basu yi kaWan ba sannan basu yi mata yawa yadda take saka manyan riguna ba. Ba ma kamar Abayoyin nan, sai ta fito shar a ciki kamar wata balarabiya, kasancewar tana da hasken fata.

Saboda murnar ganin yadda tayi kyau sai juyi take yi a gaban madubi tana ?yal?yala dariya ita kaWai a cikin Waki. Gaba Waya ta manta da damuwar Bintu, Hafiz da wani ?addararren aurensa da aka Waura mata.
"Ashe daman haka nake da kyau?"
Ta tambayi kanta a fili tana dariya.
"Gaskiya daga yanzu zan zo nima in koyi gayu ko gurin Mashkura. Kuma bazan sake yarda Innar Hadiza (Telarta acan Fa?o) tayi min burguza-burguzan Winkunan nan da take min ba. ?an cas-cas za ta dinga min irinna ?an gayu, musamman ma dai yanzu da zan koyi turanci. Ta sake ?yal?yalewa da dariya tana shafa ?an yiri-yirin kitson da suke kanta.

Ko da ta cire kayan naWe su tayi tsaf ta shirya su can ?asan jakar kayanta, sannan ta mayar da sauran kayan ta rufe zip Win jakar. Kafin ta kwanta, ?arfe uku saura minti goma sha biyar. Da yake tana cikin farin ciki ga bashin barcin da yake kanta bata daWe ba nannauyan barci yayi awon gaba da ita.

Sabo da yin sallar asubah akan lokacinta shi ya tasar da ita, da?yar ta iya mi?ewa bayan ta yi salati da addu'o'i tana tangaWi ta faWa banWaki.

Alwala da ruwa mai Wumi da tayi shi ya taimaka mata gurin dawowa hayyacinta. Ko da ta koma cikin Wakin, kafin ta kwanta sai da ta murza makullin ?ofar Wakin ta buWe, sannan ta saka babban hijabi ta tayar da sallah. Bayan ta idar tana cikin yin azkhar kamar yadda ta saba nannauyan barci

22 / 53