Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   24 / 53

69K to 72K   out of 157.3K words

ta zabge gaba Waya kamar wacce ta kwana ta yini tana amai da gudawa.

Duk irin maganganun da Bintu take yi tana jin ta. Ta kunna wayarta ya fi sau talatin don kiran can ?auye ta bada wasiyyar halin da take ciki, amma da yake matsiyaciyar waya ce da ta kawo sai ta Wauke. A ?arshe ma wayar sai ta daina kawowa. Tsananin tashin hankali yasa ta zube a ?ofar bayi tana sharSan hawaye, hannayenta duk biyu dafe da bakinta, don kar sautin kukanta ya fita balle har ta ?ara janyo ma kanta wani tashin hankalin daga Bintu.

Tana cikin wannan halin ne taji an fara ?wan?wasa ?ofar Wakin da Wan ?arfi. Idanu ta zazzaro a tsorace, ta cire hannuwanta daga baki ta Wora a kai hankalinta a tashe. Ko da ta ji ?wan?wasar ya ?i tsagaitawa sai ta yanke ma kanta shawarar gara ta fara ?wallah ihu, wata?ila idan aka ji ihunta ya karaWe gidan wasu daga cikin ma'aikata suyi ?o?arin kawo mata Wauki.

Ta buWe baki za ta yanka ihu kenan sai ta ji muryar Hafiz a fusace yana cewa
"Zulai don ubanki baza ki zo ki buWe ?ofa in fitar da ke daga gidannan ba? Na rantse da Allah idan kika yi wasa zan ficewata in ?yale ki da Bintu, in yaso ba caka miki wu?a ba, idan taga dama ma ta ?ona ki ?urmus! Ko babu komai an rage mugun iri a doron ?asa..."

Tsulum! Ya ganta a gabansa ba tare da ya ji sadda ta buWe ?ofar ba. Kallo Waya yayi mata ya gane a bala'in firgice kuma a tsorace take, Zulai da ba ta ?aunar zama ba hijabi sai ga ta tsaye a gabansa ?i?am babu hijabi babu Wankwali. Rigar ma duk ta tattare, har yana hangen wani sashe daga farin fatar cikinta. Ko da ya kalli idanunta duk sun zurma ciki sun canja kala.

Da bala'in haushi da takaicinta da ke cike da zuciyarsa ya galla mata harara.
"Ina hijabinki?"

Da saurin gaske ta koma cikin Wakin jikinta na rawa ta fito ri?e da hijabin a hannunta, ta ma kasa sanyawa, sai da ya daka mata tsawa da umarnin ta saka hijabin mana, sannan ta saka a baibai tana ta zare idanu tana waige-waige don kar Bintu ta shammaceta ta caka mata wu?a.

Lura da yayi Zulaikha fa ba ta a cikin nutsuwarta, harara ya sake galla mata sannan yasa hannu ya finciki hannunta Waya ya matsar da ita daga ?ofar Wakin ya shige ciki. ?ankwalinta da ya gani yashe a ?asa, wayarta da ke ajiye a ?ofar bayi da takalmanta da suke ajiye a bakin ?ofa ya Wauka ya cusa mata a cikin jakar kayanta.

Duk abinda yake yi shi ma a gurguje yake yi da tsoron kar Bintu ta fito ta tarar da Zulai a falon. Bai tsaya ba ta umarnin su je ba kawai ya finciki hannunta da sauri tana biye da shi tana harharWewa har suka fice daga cikin falon.

Bai saki hannunta ba, sai da ya buWe ?ofar baya na motar ya zaunar da ita a ciki, ya aje jakar kayanta a kusa da ita sannan ya mayar da ?ofar ya rufe.

Mal Musa har ya taso a zatonshi tare za su fita amma sai Hafiz ya dakatar da shi.
"Yanzu zan je in dawo Mal Musa, ba nisa zanyi ba. Idan na dawo sai mu koma Ofis."
Makullin motar ya amsa ya shiga mazaunin direba ya figeta a guje suka bar gidan.

Hankalin Zulaikha bai fara kwanciya ba sai da taga sun bar unguwar gaba Waya, sun harba kan babban titi suna ta Sanana gudu. A fili taja wani nannauyan ajiyar zuciya da yasa Hafiz Wan kallonta ta cikin madubi.

Harara ya sake gallah mata, ya ?ara da jan wata doguwar tsaki, ya saki wata ?a??arfan ?wafa.

Duk abinda yake yi tana jin shi, amma ko kallo bai ishe ta ba. Sai ?ara gyara zamanta tayi akan kujera a fili ta fara godiya ga Allah, addu'a lokaci Waya tana haWawa da sambatu.
"Allah na gode maka da ka kuSutar da ni. Allah kasa ko mutuwata ce tazo bazan mutu a wula?ance hannun wacce ba ta so na, ba ta ?aunata, kuma bata san darajar rayuwata ba. Na yi dambe iri-iri zamanin yarintata, na ga dambe-dambe kala-kala a rayuwata. Amma irin wannan ta'addancin damben da ake amfani da wu?a mai shegen tsini da kaifi ban taSa yi ba, kuma ban taSa gani ba. Sai yau a gurin matar birni da take tutiya da wayewa amma ta bari linzamin kishi ya ja ta zuwa hauka, har take yun?urin aikata abinda ni ?ar ?auye bazan taSa aikatawa ba..."

"?iiiiiii..."
Ya taka wani wawan burki da yasa ta katse surutan da take yi a tsorace. Ta Waga kanta a firgice tana kallonsa. Sai taga ashe har ya gangara gefen titi bata sani ba, hankalinta a tashe take kallon yadda ya buWe ?ofarsa a fusace ya fita daga cikin motar.

Tana kallonshi, har ya gangara gurin wani mai kanti da yake can gefen hanya. Baza ta iya cewa ga takamaimai abinda ya aikata a gurin ba, tunda hangen bayansa kaWai take yi daga cikin mota. Yana hanyar dawowa dai ta hango shi yana saka wani abu a cikin aljihun rigarsa.
: Duk da bata taSa yin doguwar tafiya a motar haya ba, amma ta gama sakankancewa tashar mota zai kai ta ya saka ta a motar zuwa Fa?o. Bata ankara duk doguwar tafiyar da suke yi ba tasha suka nufa ba sai da taga ya faka motarsa a ?ofar wani gida madaidaici amma kuma mai kyau tun daga waje.

"Fito muje."
Ya umarceta bayan ya fita waje, fuskarsa a Waure tamau. Babu walwala ko mis?ala zarrah.

A tsorace ta kalle shi, ta sake kallon ?ofar gidan da suke tsaye a gabansa. A marairaice ta ce
"Yaya ina ne nan Win ka kawo ni? Dan girman Allah kayi ha?uri ka saka ni a motar zuwa gida. Wallahi gaba Waya a firgice nake da Habujan nan, ka taimaka ka mayar da ni gurin Innaye inda na fi wayau."

Sai ga hawaye sun zubo mata shar... Da rawar murya ta cigaba da cewa
"Ni Wallahi daman auren nan yadda kake jin tsanarsa a ranka na ma fi ka jin tsananin tsanarsa a zuciyata. Ka kwantar da hankalinka, idan ka mayar da ni gida salin-alin na yi al?awarin zan bi duk hanyar da ya kamata gurin wanke ka a gaban Baffa da Innaye. Bazan taSa bari su ga laifinka ba, Wallahi da gaske nake yi..."

"Za ki koma gida, amma ba yanzu ba. Don haka gara ma ki rufe min tsattsamar bakinki tun kafin in canza shawarar da na yanke. Fito muje."
Ya sake ba ta umarnin da tsawa a muryarsa.

Tana hawaye, ta fito daga cikin motar ta tsaya Wan nesa da shi. Shi ya buWe motar ya fito mata da jakar kayanta, ya zage zip Win ya fito mata da takalminta ya bata umarnin ta sa a ?afafunta. Bayan ta saka ya sake umartarta da ta gyara hijabinta da yake a baibai, har ta gama gyara hijabin hawayen idanunta basu daina sauka a guje kamar an buWe famfo ba.

Hannu yasa a aljihunsa ya zaro kuWi masu Wan dama za su kai dubu ashirin ?an Wari biyar-biyar ya dam?a mata a hannunta.
"Ki ri?e wannan, ko za ki bu?aci wani abun ba ni a kusa. Nan Win gida ne na mutanen kirki da karamci ba na so ki ishe su da bani-bani. Kina ji na?"

A raunane ta Waga mishi kai alamar ta ji.

Hannunsa ya sake cusawa a aljihu ya zaro wata farar takarda da take a nannaWe, Wan shiru yayi yana kallon takardar. Sai kuma ya sake naWe takardar sosai ya mi?a mata
"Ki Soye wannan a cikin kayanki, idan kin samu nutsuwa kin dawo cikin hankalinki sai ki karanta..."

"Takardar mece ce Yaya?"
Ta tambaye shi tana Wan jujjuya takardar a hannunta.

"Muhimman bayanai ne waWanda ba ni da lokacin da zan iya Satawa wajen karanto miki su da bakina. Allah yasa dai su Baffa basu yi asarar kuWin tara ba, domin da turanci na rubuta. Wuce muje."

Jikinta a sanyaye ta bi bayansa, ranta a Sace da ba?ar maganar da ya gwaSa mata da ya ce anyi asarar kuWin tara. Ta sani tabbas asarar kuWin taran aka yi, domin baza ta iya karanta dogon rubutu da turanci ba. Sai a wannan lokacin Mashkura da al?awarin da tayi mata na koya mata karatun turanci ya faWo mata a zuciya.
'Ba komai. In da rai, da rabo.'
Ta ayyana hakan a zuciyarta, sannan ta fara ?o?arin tsayar da hawayen da take yi ganin har sun isa ?ofar gidan ya fara ?wan?wasawa.

"Waye?"
Muryar namiji dattijo ya tambaya daga cikin gidan.

"Baba ni ne. Hafiz ne."
Ya amsa da girmamawa.

Cikin sauri aka buWe ?ofar daga ciki. Daga yadda dattijon yake gaisar da Hafiz da girmamawa sosai har yana Wan du?awa ?asa yasa ta fahimci Mai gadin gidan ne.

"Ina kwana."
Ta gaisar da tsohon a mutunce da sha?a??iyar murya bayan sun gama gaisawa da Hafiz. A daraje ya amsa mata, sannan ta bi bayan Hafiz da taga ya nufi cikin gidan kai tsaye.

Daga yadda yake kutsawa lungu da sa?o na gidan har suka isa Wan madaidaicin falon matar gidan yasa ta gane Yayanta ba ba?o bane a cikin gidan. Ita dai tana biye da shi a baya, da alamun gajiya ?arara a fuskarta.

Ko da ya zauna akan kujera ita a ?asa ta zauna, ta nannaWe ?afafunta a cikin hijabi, hankalinta a tashe. Ta rasa dalilin da yasa sam hankalinta ya kasa kwanciya da wannan ba?on muhallin da ya kawo ta, don dai kawai ba ta da yadda za tayi ne.

Sallamar da matar gidan tayi ta shigo cikin falon yasa ta Waga kai a hankali ta saci kallonta. Kyakkyawar dattijuwa, wacce gayu, gyara, cin abinci masu gina jiki suka taka muhimmiyar rawa gurin Soye shekarunta. A haka idan aka bar Zulaikha za ta iya rantsewa da Allah Aunty Balira ta girmi matar, amma kuma a zahirin gaskiya ba haka bane.

Tana waWannan tunane-tunanen har matar ta zauna, suka gaisa da Hafiz. Sai da Hafizu ya katse mata tunani ta hanyar kiran sunanta sannan ta iya gaisar da matar.

"Lafiya ?alau. Ya kike?"
Matar ta amsa mata a mutunce, sannan ta ?ara da tambayarta lafiyarta, da fara'a sosai a fuskarta take kallon Zulaikha, kamar dama can daWe da saninta.

"Lafiya ?alau nake."
Ta amsa cikin sanyin murya, tana jin Wan nutsuwa kaWan a zuciyarta da ganin fara'ar da ke fuskar matar. Bata yi kama da mugaye ba sam!

"Kar dai ka ce min kaima yau baka je Ofis ba?"
Matar da Hafiz ke kira Mummy ta tambaye shi bayan ta mayar da hankalinta kan shi.

?an sosa ?eya yayi, kafin ya amsa da
"A'a! Na je Mummy. Wani Wan rikici ne ya mayar da ni gida. Don Allah alfarma nazo nema idan bazan takura miki b..."

"Dalla rufe min baki. Ashe Wa yana neman alfarma a gurin wacce take kamar mahaifiyarsa? Me kake bu?ata Hafiz? Feel free and ask me anything, in sha Allah bazai gagara ba."

Duk da ya san babu abinda zai nema gurin Hajiya Balkisu ta gagara yi mishi, ?ara tabbatar mishi da hakan da tayi a yanzu ba ?aramin daWi da nutsuwa ya ?ara samu a zuciyarsa ba.
"Na gode Mummy."
A nutse ya cigaba da yi mata bayanin abinda ya kawo shi gidanta a daidai wannan lokacin
"Wannan yarinyar da kike gani, ?anwata ce, Sunanta Zulaikha. Jiya da na tafi gida nazo da ita, aurenta nan da sati uku ne sai aka samu matsala daga can Sangaren mijin ya ce ya fasa.

To kin san lamarin ?auye da ?ananun maganganu, wannan dalilin ne yasa Baffana ya ce in taho da ita nan ko za ta samu nutsuwa. To kasancewar tun asali babu shiri tsakaninsu da Bintu, kwananta Waya kawai har sun fara samun saSani, rikicin ne yasa har sai da na tsallake ayyukan Ofis na koma gida... Kawai don dai a samu maslaha, shi yasa na Waukota na kawo ta nan ta Wan kwana miki biyu.

Baza ki samu matsala da ita ba in sha Allahu, duk wasu aikace-aikace za ta taya ki. Da farko na yi tunanin in kai ta gidan Abba Lurwanu sai kuma naga kamar an gudu ne ba'a tsira ba, daga cikin gidan baza'a rasa wanda zai kira Baffa ya faWa mishi halin da ake ciki ba."

Zulaikha dai kanta a ?asa, zuciyarta cike da ba?in ciki da takaicin yadda saboda tsananin ?iyayyar da Yaya yake mata ba ya iya jingina mata matsayin matarsa. DaWin abin ba shi kaWai yae ?in auren ba, ita kanta ta tsani auren, kila ma fiye da yadda ya tsana. A yadda take ji gara ta ?are rayuwarta babu aure da dai ace ta tabbata matsayin matarsa ba ya son ta ba ya ?aunarta. Saurin kawar da tunanin tayi, lokacin da ta ji Mummy na cewa

"Allah sarki. Babu komai in sha Allah Hafiz, ka san lamarinmu na mata sai ha?uri. Kuma na ji daWi sosai da baka bari ka samu saSani da matarka akan ?anwarka ba, tunda dai ko wacce tana da Sangaren muhimmancinta da ha??inta da yake wuyanka. Ka barta anan Win, kuma ba kwana biyu ba, iya tsawon satittika ko watannin da su Baffa suke so tayi ka barta tayi anan Win. Ba mu da damuwar hakan in sha Allah."

Da murmushi a fuskarta ta mayar da kallonta kan Zulaikha ta ce
"Zulaikha? Za ki zauna nan tare da ni ko?"

"Eh Mummy."
Ta amsa a hankali.

"Yauwa! Kin ga nima ba ni kaWai bace a gidan, akwai mahaifiyata Hajja, da Yayanku Fadil, da ?anwarsa Kareema, sai yaron Fadil mai suna Imam. Ko da na tafi Ofis i'm very sure zaman kaWaita bazai dame ki ba. Kin ji ko? Ki saki jikinki kamar kina gidanku. Kuma ina fatan daga Sangarenki baza ki kira su Baffa ki faWa musu Yayanki ya canja miki muhalli ba?"

"Eh! In sha Allah bazan faWa musu ba."

"Yauwa! Madallah! Hafiz za ka iya tafiya."

Godiya mai yawa ya sake yi ma Mummy har sai da ta nuna mishi Sacin ranta kafin ya daina godiyar, sallama yayi mata. Ko kallon Zulaikha baiyi ba ya fice daga gidan.

Mummy da kanta ta shiga kicin ta kawo ma Zulaikha lafiyayyiyar sakwara miyar agushi, wacce ta ji naman rago zu?u-zu?u a cikin miyar. Sannan ta kawo mata ruwa da lemu ta ajiye mata a gabanta.
"Baby ki ci abinci, idan kin gama ga kicin can ki shiga da farantan ciki. Ga kuma Waki can na tsakiya daga Sangaren dama, ki shiga ciki ki ajiye jakar kayanki, akwai banWaki a ciki sai kiyi alwala, daga yau nan ne Wakinki, kin ji ko?"

"To Mummy, na gode! Allah ya saka da alkhairi. Ubangiji ya ?ara girma."

"Ameen. To ni bari in shiga ciki inyi sallah."

"To Mummy! A fito lafiya."

Idanunta na kan matar da a zuciyarta take jin nutsuwa da ita har ta Sace ma ganinta. Kafin ta ci abincin, sai da ta shiga Wakin da aka nuna mata a matsayin nata ta ajiye jakar kayanta, ta shiga banWaki ta wanko hannuwanta duk biyu ta fito zuwa falo ta zauna a gaban abincin.
"Uhmmm! In ba gayu irinna ?an birni ba ta ina sakwara zai ciwu da cokali?"
Ta tambayi kanta a fili tana Wan murmushi, bismillah tayi, ta gutsuri sakwarar ta Webi miya ta kai bakinta.
"Uhmmm!"
Ta faWa tana jin wani masifaffen daWi mai barazanar tsinke mata kunnuwa.

"Allah na gode maka da ka rabo ni daga gidan Bintu. Ko babu komai daga irin tarbar da aka min anan na san in Allah ya yarda bazan rasa abinda zan ci ba."
Ta faWa tana sake yanko ?aton lomar sakwarar da ya daku lu?wui kamar ba da hannu aka daka ta ba, ta haWa da miya mai yawa ta kai bakinta.

Bata san tana jin yunwa sosai ba sai da taga cikin ?an?anin lokaci ta cinye manyan ?ullin sakwara guda biyu, duk yawan namomin da ke cikin miyan haka ta cinye tas, ta shanye ragowar miyan ta suWe kwanon tas kafin ta kwashe su zuwa kicin.

Wanke-wanke kaWan ta gani a cikin sink, tattare hijabinta tayi ta haWa da nata farantan ta wanke su tas ta kife a cikin kwandon da ta gani a gurin. Goge ruwan da ya Wan zuba tayi da mopper kafin ta fice daga cikin kicin Win ta nufi Wakinta don sauke farali.

[1/30, 5:32 PM] Fareeda Abdallah: ***** *****


"Haba don Allah! Ta ina aka taSa irin wannan rayuwa? Ace mace gandamemiyar budurwa baza ta iya tu?e tuwon dawa lu?wui ta haWa shi da lafiyayyiyar miyar kuka wacce ta ji daudawa ba? Ni kam ba haka nake ba, sunana Karimatu aka saka miki amma sam ba haka halina yake ba. Yanzu saboda Allah da Annabi idan Allah ya haWa ki aure da dattijo maciyin tuwo fa? Ya za kiyi...?"

Wacce ake yiwa sababin ?ara zumSuro baki gaba tayi ranta a Sace ta ce
"Allah ma baya sa haka ba Hajja. Ni kam in Allah ya yarda bazan taSa auren tsoho ba balle kuma ya kasance mai masifar son tuwo, tuwon ma ya wuce na shinkafa, ya tsallake tuwon semo, ya shallake tuwon garin surfaffen masara har sai an gangara tuwon dawa. Kuma da kike ta wannan mitar kina min sababi ca nake sadda za ki fita na tambayeki abinda kike son ci zaSi biyu kika bani? Ke fa kika ce ko inyi miki sakwara ko tuwon dawa, da naga bazan iya tuwon dawan ba shi ne na miki sakwara. Kuma ki tambayi Mummy ki ji tun bayan fitarki da safe ban zauna ba sai da na gama haWa miki lafiyayyiyar sakwara miyan agushi, amma da yake ke ba'a miki gwaninta duk gidannan ba wanda bai ci abincin ya jinjina min ba sai ke, kuma saboda tsabar sabo da yi tun kafin

24 / 53