Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   19 / 53

54K to 57K   out of 157.3K words

take nunawa idan ta je ?auyen duk Baffa yana gani. Amma saboda dattako sai yake kawar da kai, kuma daga Sangaren Innaye bata taSa masa ?orafi ba.

Irin ?orafin da Yayyen Hafizun suke yi ma idan suka je gidan acan Abuja duk yana ji. Rakiya a cikin ?a?ansa ta kasance ba ta da rufi, ko a waya ya kira ta cikin hikima ya tambayeta halin da gidan Wan nasa ke ciki ba ta Soye masa komai.

Hankalinsa bai ?ara tashi ba sai da Innaye ta je jinya gidan Hafizu, abubuwan da suka biyo baya sun Waga masa hankali ba kaWan ba. Amma saboda kar ya raba zumuncin da ke tsakanin ?a?anshi yasa yayi saurin kashe maganar, tunda ya lura ?arara har yanzu Hafiz bai fara ganin laifin Bintu ba. Matsananciyar soyayyar da yake mata yasa a kullum alkhairanta kawai yake kallo.

Zuwan da suka yi barka gidan, yasa jikinsa ya ?ara yin sanyi. Duk irin naWe tabarmar kunyar da Bintu tayi yana sane, ai wawa ba mahaukaci bane. Da wannan dalilin yasa da gangar ya tura mata da yara zuwa suna duk don dai ya ?ara gwada hankalin Bintun.

Bayan dawowarsu suna da irin labarin da ya samu daga bakin Rakiya da sauran ?a?ansa yasa shi yanke tsammani akan Bintu. ?arara ya gane manufarta na ?o?arin janye Hafiz daga gare su iyayensa da ?an'uwansa, idan kuma hakan bai samu mata ba, babban burinta shi ne duk wani dangin Hafiz ya daina zuwa inda suke acan Habuja. Wannan kuma abu ne da bazai taSa yiwuwa ba, da wannan dalilin yasa shi yin amfani da karin maganar nan ta malam bahaushe da yake cewa
"Ranar na ka sai na ka."
Duk cikin ?a?an dangi ya duba kaf bai ga wacce zai aura ma Hafizu ta samu dama-dama idan ba Zulaikha ba.

Duk da kwanciyar da al'amarin yayi a zuciyarsa, baiyi gaggawar aikatawa ba sai da ya Wauki kwanaki yana Istikhara. Kuma cikin hukuncin Allah lamarin sai ?ara kwanciya yake yi a zuciyarsa.

Ko da ya tunkari ?an'uwansa da maganar haWa auren, yayi matu?ar mamaki da yaga sun goya mishi baya. Ta Sangaren dangin Innaye kuwa su ma addu'ar fatan alkhairi kawai suke yi.

Ya riga ya sani, idan da inda zai samu tasgaro daga Innaye ne, shi yasa ko da suSul da baka baiyi gangancin sanar da ita wanda zai aura ma Zulaikha ba. Ita kuwa Zulai duk haukar da za tayi za ta gama, aure ne an Waura kuma in Allah ya yarda mutu ka raba.

Shi kuwa mai gayya mai aiki Hafizu duk da bai sanar da shi halin da ake ciki ba a wannan karon ya sha alwashin nuna mishi lallai fa da kai da kaya duk mallakar wuya ne.'

Nannauyar ajiyar zuciya Baffa yaja ya sauke, ya cigaba da kallo da sauraren ?an'uwansa da na Innaye da suke ta mata maganganu na kwantar da hankali, suna ?ara nuna mata idan fa tayi ha?uri, kuma ta kwantar da hankalinta, lallai aure tsakanin Zulai da Hafizu alkhairi ne. Amma har lokacin ta tafasa sauke bata ce musu ba, sannan bata daina sharar hawaye ba.

"Assalamu alaikum"
Sallamar da Hafiz yayi da nutsattsiyar murya yasa duk mazauna Wakin suka mayar da hankalinsu da idanuwansu kan ?ofar, kafin suka amsa sallamarsa.
[1/11, 6:51 AM] Fareeda Abdallah: Hafiz na shiga cikin falon, Innaye tayi gaggawar mi?ewa tana tangaWi ta shige cikin uwar Wakinta. Wasu sabbin hawaye suna sake Salle mata, zuciyarta cike taf da tausayin Autarta.

Allah ya sani, wannan lamari ko kusa bata yi murna da shi ba. Da ace Baffa yayi shawara da ita tun farko, Wallahi baza ta taSa goya masa ba. Kuma ko a yanzu da tana da ikon tilasta Hafizu ba tare da zuciyar Baffa ta yi ba?i ba a take za ta sa ya saki Zulaikha.

A ganinta, zaman Zulaikha a yanzu babu aure har zuwa sadda wani mijin zai bayyana ya fi gaggawar aura mata Hafiz da aka yi. A ture ma batun Hafiz da ko kusa ba ya ?aunar Zulaikha tun tana ?ar ?arama. Bintu? Bintu fa? Bintun nan da ta kasance azzaluma kuma makirar da take ?o?arin bin duk hanyar da ta san za ta raba Hafiz da iyaye da ?an'uwansa? Ita fa Malam ya Wauki Zulai haihuwar ?auye rainon ?auye girman ?auye ya mi?a ma Bintu ita a matsayin kishiya.

Tun daga zuwanta jinya gidan Hafizu, da irin abubuwan da suka biyo baya, ta yanke tsammanin Bintu za ta ?aunace su. Shi yasa ko da ta samu labarin abinda ya faru ga masu zuwa suna ta bakin Balira bata yi wani mamaki ba. Ta san in dai Bintu ce za ta aikata fiye da haka.

Ita yanzu ta wace hanya za ta bi ta dakatar da wannan mummunan al'amari???

A falo kuwa, daga kallon fuskar Haf??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????iz za'a fahimci irin mamakin da zuciyarsa ta shiga na ganin taron dangi haka a falon mahaifiyarsa. Amma sai bakinsa bai furta ba, ya dur?usa a ladabce, ya bi su da gaisuwa Waya bayan Waya har zuwa kan Baffansa.

"Hafizu an samu ?arasowa? Barka da sauka. Ya hanya?"
Baffa yayi maganganun idanunsa cikin na Hafiz.

Saukar da idanunsa ?asa yayi daga kan Zulaikha da yake kallo zuciyarsa cike taf da mamakin barcin banza da wofi haka da take yi ?atuwarta da ita a cikin Babanninsu. Lallai da a kusa da ita ya zauna, babu abinda zai hana shi fakaitar idanun mazauna falon ya manna mata wani zazzafan tsungule da zaiyi sanadiyyar tashinta a firgice.
"Eh! Na ?araso Baffa. Ayi ha?uri da jinkirin amsa kiran da nayi, hakan ya faru ne bisa dalilin manyan ba?i da muke da su a gurin aiki. Sai da muka sallame su sannan na kamo hanyar tahowa..."

"Ai babu komai. Tunda dai ka iso lafiya Alhamdulillahi. Le?a nan Chemis Win Habu idan yana nan yazo ya duba min Zulai, sumewa tayi. Tun Wazu ake yayyafa mata ruwa har yanzu bata farfaWo ba..."

"Subhanallahi! Suma kuma Baffa?"
Yayi tambayar da Wan damuwa a fuskarsa.
"Me yake damunta haka? Wani mummunan abu ne ya faru da ita har ya jefa ta cikin halin suma?"
Ya ?ara jera ma Baffa tambayoyin tun kafin ya samu amsar tambayar farko.

Sai kuma ya mi?e zumbur! Ya fice daga falon, tunawa da yayi duk minti Waya da zai ?ara a falon fa hankalinta na ?ara nisa ne. Gara ya taho da Habun idan aka samu nasarar farfaWo da ita sai ya samu amsar tambayoyinsa a nutse.

Jim kaWan bayan minti goma suka shiga cikin gidan shi da Habubakar. A lokacin, duk Babanni da Kawunnansa da suke cikin falon sun watse. Baffa ne shi kaWai, zaune kan kujerar da ke kusa da wanda Zulaikha ke kwance da casbaha a hannunsa yana ja.



****** ******

"Aure kuma Baffa?"
Yayi tambayar hankalinsa a tashe. A zaune yake a ?asa. Amma tsananin tashin hankalin yadda zancen auren ya duke shi bai san lokacin da ya mi?e tsaye ba. Da rawar murya ya sake cewa
"Kuma Auren ma a rasa wacce za'a aura min sai Zulai? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!"
Taga-taga yayi kamar zai faWi da saurin gaske ya zauna akan kujerar kusa da wacce Baffa ke zaune a kanta.

Amma tsabar tashin hankali bai ma san abinda ya aikata ba. Hannayensa biyu na rawa ya Waga ya kamo hannayen Baffa ya ri?e a cikin nasa
"A'a Baffa! Don girman Allah kayi ha?uri... idan ma wasa kake min ka daina. Na rantse da Allah zuciyata gaf take da bugawa. TaSa ka ji yadda bugunta ya ?ara matsanancin sauri saboda tashin hankalin da wannan wasan ya jefa ni a ciki."

Da saurin gaske, yaja hannun Baffa ya cusa a cikin rigarsa ya taSa dai-dai saitin zuciyarsa.
"Ka ji ko Baffa? Don Allah ka daina min irin wannan wasan. Irin wasan nan ne fa ko a musulunce ma ba shi da kyau..."

"Ba da wasa nake yi maka ba Hafizu. Lallai da gaske yau na Waura aure tsakanin kai da Zulaikha. Idan kuma ban isa bane, sai ka Wauki duk matakin da kake so."
Tsam! Baffa ya mi?e tsaye, ya karSe hannayensa daga na Hafizu. Sannan ya fice daga cikin Wakin.

A kunnensa ya ji Hafizu yana jan
"Laahaula walaa ?uwwata illah billahil-aleeyul-azeem"


******

Tun da aka samu nasarar farfaWowarta, ta kifa fuskarta a cinyar Innaye da take ri?e da ita, babu abinda take yi sai rusa kuka kamar za ta haWiyi zuciya ta mace.

Ita ma Innaye kukan take yi, tsakanin ita da Zulaikha an rasa wanda zai fara cewa komai.

Baffa ne ya Waga labulen falon da siririyar sallama a bakinsa, fuskar nan tasa a murtuke tamau, babu sau?i ko kaWan. Tun da Innaye ta Waga kai ta kalle shi sau Waya bata sake marmarin kallonsa ba.

"Idan kun gama kukan, ki haWa mata duk kayayyakinta, domin gobe idan Allah ya kaimu za ta bi mijinta. In yaso daga baya idan ta kwantar da hankalinta ?an'uwanta sa bi ta da sauran kayayyakin da aka tanadar mata..."

A fiegice Zulaikha ta mi?e zaune tana kallon Baffa. Ta buWe baki za ta yanka ihu ya daka mata wani gigitaccen tsawan da yasa ba shiri ta haWiye kukanta.
"Idan na sake jin ihunki a gidannan, na rantse da Allah sai na baki mamakin da baki taSa tsammani ba."

Da mazarin jiki kuma a tsorace ta ru?un?ume Innaye tare da cusa fuskarta a jikinta tana sauke ajiyar zuciya sauri-sauri. Har Baffa ya fice daga Wakin bata sani ba.

"Kiyi ha?uri Auta..."

"Innaye tun da na taso Yaya ba ya so na ba ya ?aunata. Idan na kuskura na shiga gidanshi a matsayin matarsa ni na san kashe ni kawai zai yi."
Ta katse Innaye cikin gunjin kuka, bayan ta tabbatar Baffa ya fita.

"Idan ya kashe ki, ko kuma ya bari muguwar matarsa tayi miki wani mummunan abu, duk su biyun hukuma ba ?yale su za ta yi ba Auta. Ki kwantar da hankalinki, ni kaina wannan auren bai min ba, kuma bazan taSa yarda da tabbatuwarsa ba."

Jin wannan jimlar maganar ?arshe ta Innaye, yasa sannu a hankali ta fara rage ?arfin kukan da take yi, sai sauke ajiyar zuciya. Ita daman ta san Innaye ta fi Baffa son ta nesa ba kusa ba, domin ta ?ara samun nutsuwa a zuciyarta yasa ta ce
"Da gaske Innaye? Za ki sa Yaya ya sake ni?"

"?warai da gaske. Dole ma ya sake ki, domin shi da kanshi na tabbata ba son wannan al'amarin yake yi ba, HaWi ne na Baffanku kawai. Amma ya zama dole a yanzu ki kwantar da hankalinki, ki bi Yayan naki ku tafi, ko na sati Waya ne. Na fi so in aikata komai a sirrance yadda Baffanku bazai ga laifi na ko naki ba. Ko ke kina so Baffanku yayi fushi da ke ne?"

Da sauri ta girgiza kai, alamar a'a!

"Yauwa! To kin ga da wannan dalilin ya zama dole in bi komai a sannu, cikin hikima da ?warewa. Don haka mataki na farko da za mu bi yanzu shi ne ki daina koke-koken nan da kike yi, kar Baffanku ya sake shigowa yaga kina kuka, saboda ba na so ko kaWan ya Warsa a zuciyarsa baza kiyi masa biyayya ba. Na fi so duk wani laifi ya fito ta Sangaren Hafizu da matarsa, kin gane ko?"

?aga kai tayi, alamar eh!

Mi?ewa Innaye tayi ta shiga uwarWakinta ta bar Zulaikha zaune akan kujera, ta buga tagumi da hannu bibiyu. Zuciyarta a Wage, a yadda take ji kamar ta janyo sati Wayannan tayi ta wuce Innaye ta saka Yaya ya sake ta. Tana waWannan tunane tunanen sai ga sallamar yayyenta su Balira.

Da yake su ma duk sun samu labarin irin halin da Innaye da Zulaikha suke ciki, duk yadda al'amarin auren ya daWaWa musu zuciya ko kaWan basu nuna ba. Jimami da damuwa suka ara mai yawa suka yafa a fuskokinsu.

Bayan gaisuwa da jaje da suka yi ma Innaye nan kusa da Zulaikha suka zauna suna ?ara tausarta da daWaWan kalamai. Ko da suka fahimci ?udurin Innaye na son raba auren kuma har suka fahimci Zulaikha ta hau kan maganganun ta zauna daram! Sai kawai suka cigaba da Wora ta akan hakan, suna tabbatar mata ai dole ma a raba auren. Amma a zukatansu sam ba sa fatan hakan ya kasance.

Da waWannan kalaman hilatar har Balira ta samu ta tsefe mata kai. Ita kuma Rakiya ta Waura mata ?unshin gargajiya da ta taho da shi daga gidanta.

"Ku fa duk dama kun daina wahalar da kanku, auren da duka-duka bazai wuce sati Waya ba waWannan gyaran ai ba su da wani amfani."
Ta faWa tana zumSura baki, kanta na kwance kan cinyar Aunty Balira ana tace mata kai a hankali. Ri?e a hannunta wayar Balira ce da Hafiz ya bata tana shiga nan ta fita can.

"Duk da haka dai Autan Innaye, ko ba don auren ba za ki bar gari ko na kwana Waya ne ai kya gyara jikinki."
Rakiya ta amsa mata a tausashe.

Ita Ladidi can cikin Waki ta shige tana taya Innaye harhaWa ma Zulaikha kayan sawarta sabbi a jikin jakar ghana most go, da duk wasu abubuwa da ta san Auta za ta iya bu?ata a cikin kwanaki bakwan da za tayi a gidan Hafizu.

[1/12, 12:03 AM] Fareeda Abdallah: Duk yadda Aunty Ladidi ta so Innaye ta ?ara yawan kayan cikin jakar ?iyawa tayi. Daga ?arshe ma balbaleta da faWa tayi ta ce idan baza ta taya aikin bakinta alekum ba ta fice ta ba ta guri.
"Tafiyar da kowa ya tabbatar ba ta zama ba ce menene na girin-giWishin zuba kaya da yawa a jaka?"

"Haka ne kuma Innaye. Allah ya baki ha?uri."
Ta faWa tana ?umshe dariya.

Sai da Innaye ta fita waje Wauro alwalar sallar magriba sannan Ladidi tayi gaggawar ?ara yawan kayayyakin, sosai ta zaune jakar yadda kayan ciki suka yi ?asa, sannan ta ?ara wasu masu yawa ba tare da ta tsaya shirya su a nutse ba don tsoron kar Innaye ta shigo.

Zuwa bayan Magriba, babu laifi Zulaikha ta fito a amarya sak! An wanke mata kai tas! Bayan an gama ?unshi kafin ya kama Aunty Rakiya ta yaryaWa mata ?ananun kitso masu kyau sosai. Kuma da yake tana yalwar gashi mare cika sai tsawo kuma ba?i ?irin kitson ba ?aramin kyau yayi ba. ?aya daga cikin Sabbin kayanta Balira ta bata ta saka a jiki da sabon hijabi.

Ko kafin ta saka kayan sai da tayi narai-narai kamar za ta fashe da kuka. Tuntuni daman ?arfin hali kawai take yi, kalaman Innaye ne kawai idan ta tuna yake saka ta jin Wan ?arfi-?arfi da kwanciyar hankali.
"Saboda me zan saka sabon kaya? Ni bazan sa ba Aunty. Idan na saka sabon kaya ai kamar na ma nuna ma jama'a ina son auren nan ne."
Tayi maganar bakinta a gaba.

"DaWina da ke Auta akwai ki da wauta. Ca nake tuni kun gama magana da Innaye kan za kiyi basaja baza ki ?ara nuna Sacin ranki akan auren ba? Ta yadda idan komai ya tafi yadda ta tsara Baffa bazai ga laifinki ko na ta ba?"

"Eh!"
Ta amsa cikin Sacin rai da waswasi.

"To maza Wauki kayannan ki sanya. Wannan duk cikin shirin ne. Idan kuma kina so shirin naku ya Saci ne kar ki saka kayan."
Aunty Balira na gama faWin haka ta fice daga Wakin.

Haka Zulaikha ta Wauki kayan ta saka ba don ranta na so ba. A maimakon ta sake fita falo cikin ?an'uwanta, sai kawai tayi kwanciyarta akan gado, daman tana fashin sallah. Zuciyarta cike da sa?e-sa?e, ta kuma rasa dalilin da yasa tun da rana ?irjinta ke bugawa ?asa-?asa.

Yinin ranar gaba Waya Innaye ta ?arasa shi ne fuskarta a Winke tsaf! Duk matan da sukai ta shigowa yi mata Allah ya sanya alkhairi, haka take amsawa babu walwala ko kaWan, don ma kar mace ta ?ara cewa wani abu bayan Allah sanya alkhairin. Hatta abokan zamanta da sauran yaran gida sun rasa gane kanta, a dole suka kama kansu, suka cigaba da harkokinsu da Baffa da fuskarsa ta ?arasa yinin cike da fara'a ta musamman. Domin haka kawai yake jin wani nutsuwa da kwanciyar hankali na saukar masa.

Duk inda Yayye da ?annen Hafizu suke nemansa don suyi masa Allah ya sanya alkhairi sama ko ?asa sun neme shi sun rasa a cikin gidan da waje. Ga kuma motarsa a ?ofar gida, ga direbansa a ?ofar gida, amma ba shi ba labarinsa. Tun da aka kira sallar la'asar ya lallaSa yana jiri ya fice daga Wakin Baffa, har zuwa bayan sallar isha'i babu wanda ya ?ara saka shi a ido.

"Ku ?yale shi, duk inda ya shiga ma zai fito ne. Shi ai ba ba?o bane, ciki da wajen ?auyen nan babu inda bai sani ba. Duk inda ya shiga bazai Sata ba."
Kalaman da Baffa yayi musu kenan lokacin da ya ga damuwa da jajen Hafizu da suke yi ya fara yawa.

Mata masu aure haka nan suka bar gidan bayan isha'i ba tare da sun ganshi ba. Amma duk sun ?uduri aniyar washe gari da sassafe za su dawo su gaisa da Hafizun, suyi masa Allah ya sanya alkhairi sannan su bashi amanar ?ar'uwarsu.

Hafiz bai bayyana ba sai a masallaci wajen sallar asubah, ana idar da sallah kuma yayi wuf zai fice da sauri ?an'uwansa da jama'ar gari da suke son taya shi murna suka lulluSeshi. Haka nan ya tsaya ba don ranshi ya so ba, fuskarshi da ?ar dariyar da ana kallo an san na ya?e ne.

Bayan ya ?waci kansa da?yar daga cikin mutane suna hanyar zuwa gida ?aninsa ke tambayarsa.
"Yaya ina ka shiga ne? Jiya sama da ?asa mun neme ka mun rasa, sai direba da motarka kawai a waje. Mun tambayi direba ya ce shi kanshi bai san inda kake ba."

"Uhmmm! Ina nan!"
Abinda ya iya cewa kenan a ta?aice.

Ko da suka shiga gidan, Waya bayan Waya ya bi Wakin kishiyoyin Innaye ya gaishe su. Duk Wakin da ya shiga, sai da ya Sata lokaci saboda nasihar

19 / 53