Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   39 / 53

114K to 117K   out of 157.3K words

"Yaya mun gode da ziyara, ku gaida gida. In Allah Ya yarda idan na fara fita ni zan zo in muku yini."

Daga shi har ita sun san ta fada ne kawai, ba zuwan za tayi ba. Ita kuwa a ranta tuni ta gama kudurtawa nan da shekara biyar masu zuwa idan muna raye ba lallai su ga keyarta a cikin gidansu ba.

Ya kasa amsa ma Zulaikha, sai Wan murmushi da ya sakar mata. Ya Waga hannunshu da?yar ya cusa a aljihu, ya ?irgo dubu ashirin ya aje mata a gefen hannun kujera. Bai saurari godiyar da take masa ba yaja kafa jiki a sanyaye ya fice daga falon, Bintu ta bi shi a baya tana saSe da Aadil a kafaWa, ko arzikin sallama su Zulai basu samu daga bakinta ba.

Sai da suka isa gurin mota sannan Hafiz ya lura da Kamal na biye da su a baya, sallama yayi mishi a mutunce kafin ya wuce masallaci. Kunya duk ta cika Hafiz, saboda irin rashin kirkin da matarsa ta zuba a gidan ?anwarsa kuma a gaban mijinta. Shi kuwa Kamal da yake wayayyen mutum ne, ko a fuska bai nuna ma Hafiz rashin jin daWin abinda ya faru ba ba.

Hafiz ya tayar da mota kenan sai ga wata motor tana ?o?arin shigowa, a dole ya dakata har sai da wancan motar ta shigo, ta samu gurin perking kafin ya fara ?o?arin fita da motarsa.

Kamar an ce ya kalli wancan motar da ta shigo, karaf! Idanunsa suka faWa cikin na Karima da take zaune a mazaunin direba, da waya ma?ale a kunnenta tana magana tana sakin murmushi akai-akai. A gefenta Imam ne gishingiWe akan kujera yana barci.

Akan idanunshi Zulai ta fito daga cikin gidan da saurinta da bayyananniyar murna a fuskarta ta ?arasa gurin motar Karima, buWe ?ofar mai zaman banza tayi, ta rungumo yaron cikin tsananin kauna da kulawa ta Wauko shi cak ta fito da shi daga cikin motar, a lokacin ita ma Karima ta fito, suka wani kashe hannu da Karima alamar da ke nuna amincin da ke tsakaninsu.

Bai san cewa ya saki baki da hanci yana kallonsu ba sai da Bintu ta taSa shi tana tambayar lafiya? mai yake kallo?
"Karima ce fa ?ar gidan Mummy Saudah, baka santa bane ko akwai wani abu ne a tsakaninku?"
Ta ?arasa tambayar ?arshen da salon da ke bayyana zargi ?arara a muryarta.

Bai ce mata komi ba, ya cigaba da jan motar a sanyaye suka fice daga gidan.

A cikin mota haka ta cigaba da mita kamar cin ?wan makauniya, duk dai akan kallon da ya ?ure Karima da shi kamar bai taSa ganinta ba. Shi kuwa ta tafasa sauke bai ce mata ba sai da suka ?arasa gida, sannan ya fara sauke mata kwandon bala'i da tashin hankali irin wanda bai taSa mata ba, duk dai akan irin wula?anci da tozarcin da tayi masa a gidan Zulai. Da irin yadda take wula?anta danginsa a Soye amma a gaban idanunsa sai ta dinga nuna mishi tana ?aunarsu.

Itama da yake a wuya take haka ta biye mishi yana faWa tana faWa, kamar za su ba hammata iska. Daga karshe ma da abin ya kai ta ma?ura haka ta nannaWo wani murgujejen zagi ta laulayawa ?auyensu da kafatanin mutanen da ke rayuwa a ?auyen.

?if! Ya Wauke wuta na wasu ?an da?i?u, kafin ya farfaWo ya nuna kanshi da yatsarsa manuniya, fuskarsa Wauke da matsanancin mamakinta ya ce
"Bintu! Ni kike kallon tsakiyar idanuna ki zagi ?auyen da na fito da duk mutanen cikinta? Har da ni da iyaye da dangina fa kenan? Kika cewa iyayena da dangina kucakan ?auye? Masu datti dangin ?azanta da dauWa? Ashe dangina ba danginki bane?"

Dogon tsaki ta ja babu alamun nadama ko kaWan a fuska da kalamanta ta amsa da
"Allah suturi bu?wui in ji kishiyar mai mageWuwa. Can ga su gada wallahi, wannan tarkacen ba da ni ba. Kaje dai can ka ji da danginka kai da suka zame maka dolen dole ba ni ba. Kuma zancen gaskiya ka ma nisantani da su da tarkacen da ya kwasosu, don tuni na daWe da fahimtar yadda ba sa ?aunata ko kaWan. Daga yau kar in ?ara ganin ?afar wani ya tako min gida. Tunda nayi kawaicin da kawar da kan ka ?i gani, gwara in fito Saro-Saro in fada maka kawai tunda ka ?i fahimta! Itama wannan mai gwala-gwalan idanun da jiki kamar na yan dambe, ka fada mata hawainiyarta ta kiyayi ramata, kada ta kuskura ta zo min gida wallahi!"

Ta juya fuu ta wuce Wakinta tana maganganu
"Auren banza da na wofi! Daga gani wannan auren babu inda zai je, don kuwa ba sa'an aurenta ta aura ba. Wannan jikin da ta saki wai ita ta ganta a cikin daula ta jindaWi tana ganin ta tsinci dami akala, to tasan cewa ba mai Worewa bane...!"
Ta shige Waki ta tura ?ofar bam! Bugun da ya ji shi kamar akan fuskarsa.

Ya kama baki hannunsa Waya dafe da kai ya haWiye wani kakkauran miyau. Zancen mamaki ma ba a magana, don kuwa yau dai Bintu ta shayar da shi ruwan mamaki kala-kala. Ya gama fahimtarta sarai, bakin ciki da hassada ne dan?are a cikin ranta ba wani abu ba. WaWannan abubuwa biyu kuma su suka ja mata gora gurin fallasa wacece ainahin Bintun da bai taSa sani ba.

Da kyar ya iya Waga kafa ya bar gidan. Ya shiga masallaci yayi sallah. Ya jima a masallacin yana lazumi, gaba daya ranshi kamar an cire mishi komai ya ma kasa tunanin komai.
Daga karshe ya tashi ya shiga motarshi yayi ta zagaye a cikin garin Abuja ba tare da takamaiman wajen zuwa ba.

Bai koma gidan ba sai can gab da magriba. Wani tunanine yake ta yawo a kanshi tun da ya idar da sallar la'asar, abin ya kasa fita a cikin ranshi duk kuwa da yadda yaso ya yakice tunanin.

Zai iya cewa wannan tunanin ma shi ya mantar da shi Sacin ran da Bintu ta ?unsa mishi. Don bai tuna da saSanin da suka yi ba sai da ya shiga falon gidan. Ya same ta ta ci kwalliya, shima Aadeel ta shirya shi tsaf.

Da yake ita Win ?wararriya ce a iya kissa da kisisina sai ta tare shi da matsananciyar farin ciki, soyayya, ?auna, da tarairaya, kafin ya ce komai ta rushe da kuka tasa gwuiwa a ?asa tana bashi ha?uri.

Hankalinta bai kwanta ba sai da taga ya saki fuskarshi, ya kuma tabbatar mata da komai ya wuce. Sannan cikin rawar jiki ta gabatar mishi da kalolin girke-girke irin waWanda ta tabbatar yana so.
Shi ya ma manta rabonshi da ?wa??waran abinci tun karin safe, sai lemo da snacks da ya ci kaWan a gidan Zulai.

Duk yawon da yayi a cikin gari ruwa kawai ya dinga WaWWakawa cikinshi, ba ya jin yunwa, balle ya tsaya ko gidan abinci ne ya shiga ya cika ciki.

Duk ?amshi da haWuwar da abincin yayi ranar dai kasa ko kallonshi yayi balle yayi tunanin ci. Haka ta bishi har cikin dakinshi tana ta kwarkwasa. So tayi ta hillaceshi kamar yadda ta saba don maganar ta ?arasa wucewa, amma ya ki damar hakan.

Haka tana ji tana gani ya sake yin wanka ya sanya wani yadi mai kyau ya fita. Ta bishi da kallo jiki a sanyaye. Ranta ya gama bata cewa lallai yau ta tsokanowa kanta faWan da yafi karfinta.

*****

Da misalin karfe takwas da yan mintuna na dare Hafiz yayi sallama a kofar falon gidan Mommy Saudah, sai da ya jira aka amsa daga ciki, aka yi mishi izinin shiga kafin ya danna kai cikin falon.

Karima da Hajja kaWai ya samu a zaune a falon suna kallo TV. Ya samu kujera ya zauna bayan ya gaishe da Hajja ta amsa a mutunce.

Da sanyin murya Karima ta gaishe shi, bayan ya amsa ta mi?e a nutse ta nufi kicin don kawo mishi ruwa da abin taSawa. A fakaice yabi bayanta da kallo, a zuciyarsa yake jin ?arin nutsuwa ta musamman.

Gorar ruwan faro da madarar hollandia ta fara ajiye mishi, sannan ta koma cikin kicin ta kawo mishi Meat pie sha?e da faranti, da alamun ba'a daWe da gama soyawa ba, don sai ?amshi yake yi.

"Yaya Bismillah! Ya su Aunty Bintu da Aadil?"
Ta tambaye shi.

Bayan ya amsa mata da lafiyarsu ?alau ta sanar da shi Mommy tana amsa waya ne, idan ta gama za ta fito.

Don haka ya zauna anan yana sauraren hirar da suke yi da Hajja, lokaci bayan lokaci yana Wan tsoma musu baki idan Hajja ta sako shi cikin hirar. A kaikaice yake ?are ma Karima kallo, wani iko na Ubangiji kuma sai yaji tunanin da yake ta taunawa a cikin ranshi yana ?ara kwanta mishi sosai da sosai.

A da kam, ya riga ya gama ?udurtawa ranshi cewa shi fa Mijin mace Waya ne. Sam! ba shi da wani ?udiri na karin aure. Amma a yanzu, sai yake jin cewa zai iya, kuma zai yi. Ba wai kuma don kawai munanan halayen Bintu da suka bayyana ?arara a idanunshi ba, ba kuma wai don ba ta kaunar danginshi da iyayenshi ba, sai don kawai samun damar cin moriyar karin maganar nan ta bahaushe da ya ce gida biyu maganin gobara.

Duk da dai rashin kaunarta ga danginshi shi ya fara Warsa masa tunanin lallai ya kamata ya nemi mafita. Aka ce ranar naka sai naka, daWin zama sai bare. A matsayinsa na namiji kuma yana da gida nasa na kansa bai kamata ace ?an'uwansa idan suka shigo garin Abuja basu da gurin zama a gidanshi ba.

Karima ?a a gurin Mummy Saudah, ita kaWai ce ?a mace tilo da yake jin zuciyarsa ta nutsu da ita kuma ta yarda da tarbiyar da ta samu. Kuma a yadda yaga sha?uwa da ?auna tsakaninta da Zuly yasan baza ta taSa ?in iyayenshi da ?an'uwanshi ba ko da sun fi haka ?auyanci.

Yini yayi a ranar yana tunanin al'amarin. Wani abun ikon Allah kuma sai yake jin har wani SurSushin soyayyar Karimar ke taso mishi a zuciyarsa. Da wannan dalilin yasa yayi ta addu'a sosai, ko a hanyarsa ta zuwa gidan yana tu?a mota yana addu'ar idan babu alkhairi a al'amarin kar Allah ya bashi ikon ?arasawa gidan balle har ya samu sararin furta abinda ke ranshi. Ya tabbatar da alkhairi a lamarin ne jin yadda yake ta ?ara samun nutsuwa da kwanciyar hankali a tunanin Karima da son aurenta cikin gaggawa.

Ko da Mommy ta fito falon, bayan sun gaisa Hajja da Karima shigewa Wakunansu suka yi bayan sun bayar da uzurin za su je su gabatar da sallar isha'i.

A karo na uku ya sake kallon Mommy ya sunkuyar da kai yana Wan sosa ?eya.

Mamaki ne ya kamata, sai kuma ta Wan saki dariya tana cewa
"Hafiz? Wai ni Win na zama sarkuwarka ce? A sanina dai girmamawa ce a tsakaninmu amma babu ?ar kunya ko Soye-Soye. Yaushe muka fara ?ar haka da kai?"

A kunyace ya saki dariya, kafin yayi ?arfin halin cewa
"Mommy yau dai zuwa nayi da ?o?on bara wajenki, ban san yadda za ki Wauki al'amarin ba shi yasa nake jin wani iri. Amma tunda kin bu?aci in faWa zan faWa."
?an shiru yayi, sai kuma ya cigaba da cewa
"Ki dubi girman Allah ki bani auren Karima. Na miki alkawarin zan rike miki ita da amana da mutunci!"

A bazata, zancensa ya sauka a kunnen Mommy. Shi yasa tayi Wan shiru tana jinjina girman maganar a zuciyarta. Sai kuma ta koma ta jingina da kujera tana kallonshi a nutse, kafin murmushi ya Salle a fuskarta.
"Hafiz, da gaske kake yi ko da wasa?"

"Da gaske nake yi Mummy. Wallahi tallahi da gaske nake yi."
Ya rantse mata don ma ta tabbatar shi fa ba da wasa yake yi ba.

"Madallah! Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Amma ina so ka sani a wannan gaSar babu abinda zan iya maka, iyaka in ce ka zage dantse ka nemi amincewa a wajenta, idan ta yarda, tabbas babu wanda zai kaini farinciki da jindadin wannan al'amari. Zuriyar Innaye da Baffa ai abin farin ciki da alfahari ne ?ara haWuwa da su a karo na biyu."

Lallausan murmushi ya saki da jin kalamanta yana jinjina kai sannu a hankali.


******
****** ******


"My dear..."
Ta kira sunanshi da taushin murya

"Na'????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
am!"
Ya amsa da yanayin muryar da ke bayyana gaf yake da fara barci.

Duk da fahimtar hakan da tayi, bai sa ta fasa faWin maganar da ke bakinta ba. Saboda gobe tun da wuri take so ta kira Mashkura ta wuce da Aadil gurin Ummansu ko za ta huta da masifar tsotson da ya tsiro mata da shi a kwanakinnan.
"Daman ina so in faWa maka ne, gobe asabar in sha Allah zan yaye Aadil..."

"Yaye dai Bint?"
Ya tambayeta a mamakance. Kafin ta amsa ya yun?ura ya Waga kansa daga cinyarta ya zauna suna fuskantar juna.
"Na zaci shekararsa Waya ne? Har ya isa yaye?"

"Ya isa mana My dear... Yana tafiyarsa ko ina, kuma yana cin abinci sosai. To me ya rage?"
Tayi maganar bayan ta kwaSe fuska don ma kar yace zai hana ta.

Jinjina kai yayi, sannan ya ce
"Kin ga mu kuwa iyayenmu ba tafiya ko cin abinci ne ma'aunin yaye yaro ba. Sai yaro ya kai shekara Waya da rabi, idan yakai Win ma sai yayi ha?ora fi?a, idan baiyi har watanni ashirin yaro yana yi ana bashi nono, daman ko a addinance watanni talatin ne ciki da shayarwa..."

"Watanni talatin dai My dear..?"
Ta katse shi da sauri bakinta na rawa.

"?warai kuwa! Watanni talatin."
Ya amsa mata, don ?ara tabbatarwa har yana jinjina mata kanshi.

"Bazan iya ba. Allah ya sani bazan taSa iyawa ba. Ka tausaya min don girman Allah... Kai baka ga yanzu yanda yake neman fin ?arfina da tsotso ba?"
Ta jefa mishi tambayar idanunta ciccike da ?an ?ananun ?wallah.

"Ki kwantar da hankalinki. Ni daman tunda kin yi niyyar yaye shi bazan hana ki ba Bintu. Allah ya raya mana shi."

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke na samun kwanciyar hankali. A hankali ta amsa da
"Amin ya rabb!"

Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na ?an wasu da?i?u. Can kuma sai ta ce
"Gobe tun da safe Mashkura za ta zo ta wuce da shi can gida gurin Umma..."

"Wani gidan?"
Ya sake tambayarta a mamakance. Kafin ta amsa ya sake cewa
"Ba wani gida da za ki kai shi fa. Ki haWa kayanshi idan zan tafi Fa?o gobe zan wuce da shi gurin Innaye..."

"Amma dai wasa kake yi ko?"
Ta tambaye shi da murmushi a fuskarta. Don ita har ga Allah da dukkan gaskiyarta ta Wauka da wasa yake mata. Bata tabbatar da gaske yake mata ba sai da cikin ?an?anin lokaci ya haWe girar sama da ?asa yayi murtuk sannan ya ce

"Wasa? Zancen raha muke yi da zan miki wasa ko kuwa na zama abokin wasanki ne? Look Bintu, na gama yanke wannan zancen tun ba yau ba. Tun da kika haifi Aadil daga ke har shi sau Waya kuka taSa taka ?afa zuwa Fa?o. Idan a matsayinki na matata kin yanke mu'amala da iyaye da ?an'uwana na zuba miki idanu shi baki isa ki yanke ala?arsa da su ba. Su Win wajib Win sa ne. Don haka gobe zan tafi da Aadil gurin Innaye ta yaye shi acan, fa?at!!"

Sau uku tana buWe bakinta tana rufewa amma ta kasa furta komai saboda tsananin yadda maganganunsa suka yi mata mugun dukan da yasa jikinta mutuwa murus!! Kalaman bakinta suka ?afe ?af! Miyaun bakinta ya bushe ?amas! Ta rasa abinda za ta ce masa kamar yadda ta rasa abinda ya kamata ta fara aiwatarwa da gaSSan jikinta. Abu Waya dai da yake ta amsa kuwwa a zuciyarta amma bakinta ya kasa furtawa shi ne ko sama da ?asa za su haWe a gobe, babu yadda za'ayi ta bari Hafiz ya Wauki Wanta ?wara Waya ?wallin ?wal ya tafi mata da shi ?auyen Fa?o.

Wani Wan tunani da ya tsirga mata a zuciya yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Sannu a hankali, ta Wan tsuguna kaWan, kamar makauniya sai ta fara lalubar bakin gado da hannunta Waya sannan ta Wosana mazaunanta. Idanunta tsaye ?yam a kanshi kamar wacce ta warke makanta.

Ta sani, idan ta ce za ta biyo mishi da sigar tashin hankali babu abinda hakan zai haifar sai ?ara samar da ?atoton giSi a zamantakewarsu. Dama yaya lafiyar giwa balle ta yi hauka? Tun watanni biyu baya da suka kai ziyara gidan matsiyaciya Zulai har ta kasa mallakar zuciyarta tayi ta aikata abubuwan da ?arara suka fallasa ma Hafiz ba ta ?aunar ?an'uwansa har yau basu koma kamar tif da taya irin yadda suke a baya ba.

Ba faWa suke yi ba, suna gudanar da komai lafiya ?alau, musamman daga gare ta da ya kasance kullum tana ?ir?irar sabbin abubuwa don ?ara janyo hankalin mijinta gare ta. Amma ita da kanta ta sani Hafiz ya canja mata, irin canjin nan da baza a kira shi Wari bisa Wari ba, amma fa lallai canjin ya wawuke hamsin bisa Wari. Kaso hamsin Win ne take ta lallaSawa tana ta-ka-tsan-tsan don kar a sake samun matsala daga gare ta.

A karo na biyu, ta sake sauke nannauyar ajiyar zuciya. Tayi narai-narai da idanunta tayi ?asa da su sosai. Da sanyin murya mai bayyana tsananin ladabi da biyayya ta ce
"Allah ya huci zuciyarka Abban Aadil. Ubangiji Allah ya huci zuciyarka. Wa ce ni in ce zan raba Aadil da kakanninsa? Ni a su wa? kuma ko ni da kake ganin kamar na yanke ala?ata da su wallahi ba haka bane... Kawai dai na Wan ja baya ne har zuwa sadda za su huce sosai saboda abinda ya faru na lamarin Zulai... Don Allah kayi min kyakkyawar fahimta masoyi..."
Ajiye maganar yayi daidai da silalowar wasu siraran hawaye daga

39 / 53