RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   52 / 53

153K to 156K   out of 157.3K words

bayanin halin da ake ciki, Tambaya Waya da yayi ma Bintu shi ne
"Tausayin halin da kika shiga sanadiyyar rabuwarki da Hafiz, da irin mawuyacin halin da kika sake faWawa ranar da kika ga hoton auren Hafiz yasa na karya gwuiwata na ro?i mahaifinshi ya kira Hafiz ya tilasta mishi mayar da ke Wakinki. A yanzu da ke da kanki ki ke ganin rabuwar ta fi alkhairi a tsakaninku, ina fatan baza ki sake Waga mana hankali da koke-koken baza ki iya rayuwa ba tare da mijinki ba?"

"In sha Allahu hakan baza ta sake faruwa ba Daddy."
Ta amsa idanunta a ?asa, wasu sabbin hawayen suna tsattsafo mata amma tayi ?o?arin haWiyewa.

"Shi kenan. Allah hakan shi ne mafi alkhairi a tsakaninku."

"Amin thumma Amin."
Umma da Aunty Sadiya suka amsa cikin haWin baki.

Sallamarsu Daddy yayi suka koma falon Ummansu. Yayi shiru cikin tunani, zuciyarsa cike taf da rashin jin daWin al'amarin. Can kuma sai ya Waga waya ya kira Abba Lurwanu ya kora mishi bayanin duk halin da ake ciki.

Shi ma sosai ya nuna alhini akan lamarin, daga bisani kuma ya ?arke da addu'ar Allah yasa haka shi ne mafi alkhairi. Bayan gama waya da Abba Lurwanu kai tsaye lambar Baffa ya lalubo ya danna mishi kira, bayan sun gaisa, a nutse ya faWa mishi duk abubuwan da ke faruwa.

Da farko sosai Baffa ya Waga hankalinshi, saboda a tunaninshi duk laifin na Hafizu ne, sai da Daddy yayi mishi bayani gwari-gwari, da irin hujjojin da Bintu ta bashi sannan yayi sanyi, da rashin jin daWi da alhini sosai a muryarsa shi ma yayi ta jera addu'ar tabbatuwar abinda ya fi zama mafi alkhairi tsakanin ma'auratan biyu.



******



"Yaya? Wai kuna duba lokaci kuwa? Yanzu fa ?arfe goma sha Waya saura kwata na dare, daga yini Waya har yanzu baku dawo min da Wana ba. Gaskiya in dai haka ne yinin bazan sake baku aron shi ba."
Zulai tayi maganar tana kumbura baki, kamar Hafiz Win yana gabanta.

Dariyar Kareema da Hafiz da take jiyowa ?asa-?asa ta cikin wayar yasa ta sakin baki galala.
"Kinga Zuly, gara ma ki kwanta kiyi barcinki. Aadil ya dawo gida kenan. Tun Wazu ma ya yi barci, haba!! Yaye fin wata Waya ai kinyi na Allah da Annabi. Ke ma ki huta ki ji da lafiyarki."
Kareema tayi maganar daga can Sangaren har lokacin da dariya a muryarta.

"Kar ku min haka Aunty Kareema, kina sane dai na faWa ma su Innaye gobe da Aadil zan je Fa?o..."

"Jibi idan Allah ya kaimu mu ma muna tafe. Don haka ki kwanta kiyi barci, gobe kafin ku wuce ki barma Mummy duk kayanshi zan aiko a karSa."
Hafiz bai jira ?orafin da za ta sake yi ba ya katse wayarsa.

Tsananin haushi yasa bata duba tazarar lokaci da ke tsakanin inda take da ?asar da Abban Imam ya je ba ta lalubo lambarsa ta danna mishi kira. Kiran farko da na biyu bai Wauka ba, sai a kira na uku ya Wauka, da magagin barci a muryarsa ya ce
"Beb...!"

Kukan da ta sakar mishi yasa shi wartsakewa ba shiri. Hankalinshi a tashe ya fara tambayarta lafiya? Me yake faruwa?

"Ba Yaya bane da Aunty Karima..."
Ta amsa mishi a shagwaSe.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke na samun nutsuwa sannan ya sassauta murya ya ce
"Su basu san da a taSa min ke gara aje a rungumi transformer bane? Amma dai faWa min, me suka yi miki don in san irin matakin da zan Wauka a kansu."

Tana ?ananun kuka ta bashi labarin duk abinda ya faru.

?an murmushi ya saki, amma ko da wasa bai bari murmushi ya bayyana a muryarshi ba ya fara rarrashinta yana kakabin rashin kyautawar da suka yi mata.
"Amma ba komai, sun yi ma kansu. Kiyi zuciya kin ji ki ?yale musu Wan su. Abinda ma nan da sati uku zan dawo mu du?a da noma mu ma mu samo namu Wan. Kila ma a karon farko ?an'uku za ki haifa min, ai na san Matata jaruma ce ko?"

Dariya ta fara ?yal?yalawa sannan ta katse wayar bayan ta ce
"Ni dai sai da safe. I love you wujiga-wujiga Hubbyna."


******** *******


*_BAYAN SHEKARU BIYU_*


"Ina ga kamar duk mun gama siyayyar da ya kamata muyi ko ?urratul-ayn?"
Hafiz ya tambayi Kareema cikin kulawa, kyakkyawar babynsu ?ar watanni Shida mai sunan Innaye ana kiranta da Najma saSe a kafaWarsa. Ita kuma Kareema tana ri?e da hannun Aadil wanda ya girma sosai ya ?ara wayau, idan ma sani mutum yayi ba, sai ayi tsammanin ya shekara biyar a duniya. Ya yi kyau sosai cikin kayan turawa da aka saka masa, kallo Waya za ayi mishi a fahimci yaro Wan gatan iyayensa gaba da baya.

"Eh kamar dai mun gama Nurul-?alb! Mu je mu biya Bill Win kawai, idan da wani abu da muka manta ma ai gobe rana ce. Mu je kawai, tun Wazu Zuly take kira na wai mai lallen ta kusa gama mata."

"Ok!"
Ya amsa a ta?aice, sannan suka nufi gurin biyan kuWi.

Kusan duk inda suka gitta sai sun zama abin kallo a idanun jama'a saboda tsananin haWuwar da suka yi. Da ganinsu an ga masoya da suke bala'in son juna, ga ?a?ayensu guda biyu gwanin ban sha'awa.

Cikin ?an?anin lokaci Hafiz ya biya duk bill Win yaran shagon suka kwasa musu manyan ledojin kayan zuwa gurin motarsa.

'Zulaikha ce ta haihu, tun farkon auren da tayi Sari sau Waya bayan watanni biyar da aurensu, a lokacin ita kanta bata san da cikin ba. Allah bai sake ba ta wani rabon ba sai da ta shafe watanni takwas, a hakan ma sai da Innaye tasa aka karSo mata maganin sanyi da na haihuwa a wani ?auye can nesa da su. (Masu bu?atar ingantaccen maganin sanyi da na haihuwa ko na cancer su tuntuSeni ta wannan lambar 07039080978)

A watan da ta sha maganin cikin hukuncin Allah ta samu ciki, haka ta raini cikin a wahalce cikin kulawa da tarairaya daga mijinta Abban Imam, Sarkuwarta Mummy, kakarsu Hajja, Kareema da Hafiz, Innaye, Baffa, yayyenta har Allah yasa ta haihu lafiya. Ta haifi Wanta namiji ?ato da shi.

Tun da aka yi haihuwar Hafiz ba ya nan, yana can Lagos ma'aikatarsu ta tura shi sai jiya ya dawo, sayayyan kayan barka ne suka zo yi shi da Kareema.'

Suna daf da ficewa daga gurin Bintu ta sawo kai cikin Store Win. Kallon-kallo aka tsaya yi na wasu da?i?u tsakanin Hafiz da Bintu, saboda shekara Waya kenan cif ba ta Nigeria.

'Bayan ri?o da kalmar nan ta Mal bahaushe da ya ce idan so cuta ne, ha?uri magani ne. Ta sha wahala ba kaWan ba duk a ?o?arinta na yakice Hafiz daga zuciyarta. Haka ta dinga murgina rayuwar da daWi babu daWi cikin godiya ga hukuncin Ubangiji ta cigaba da aikinta, amma da taimakon MD Winsu ta samu canjin gurin aiki, saboda ba ta son tana ganin Kareema balle har ta dinga jin Wacin rabuwa da Hafiz.

Sai da aka yi watanni huWu cif da rabuwarsu wata rana kwatsam ta koma gida daga gurin aiki ta tarar Hafiz ya kai Aadil hutu gidansu. A wannan ranar ta yi kuka a Soye kamar babu gobe, zuciyarta cike da tunanin baya da abubuwan da suka faru a cikinta.

Sai daga bisani ta wartsake ta rungume Wanta tsam tana sha?ar daddaWan ?amshin da ke fita a jikinsa. Daga bisani ta fara ina aka saka ina aka aje da shi zuciyarta cike da jin daWi, ko kaWan bata ga alamun wani wahala a jikin Wanta ba. Sati biyu cif yayi a gidan sannan Hafiz ya aika direba da sa?on jibi zai aika a Wauko shi. Zuwa jibin kuwa biyu bisa uku na tattalin arzikinta haka ta ?arar da shi akan sayi banza sayi wofi na siyayyar yaron, boot Win motar Hafiz cike taf da kayayyakin tsarabar yaron aka mayar da shi gida.

Tun daga sannan, duk sadda yaron suka samu dogon hutu yana aike mata da shi har zuwa sadda suka shafe shekara guda cif a cikin wannan rayuwar mai rangwamen daWi ga Bintu, mai cike da daWin daWi ga Hafiz, saboda bayan kulawa, tarairaya, nutsuwa, kwanciyar hankali, soyayya, ?auna da yake samu daga Kareema ya samu Waukaka sosai ako wane fanni na rayuwarsa.

Kwatsam! Sunan Bintu ya fito a cikin wasu gungun likitoci guda talatin da gwamnati ta Wauki nauyinsu don zuwa yin couse na shekara guda a ?asar India. Wannan dama da Bintu ta samu shi ya zama sanadiyyar manta baya a gare ta, ta cicciSa rayuwarta zuwa tudun mun tsira ta fuskanci gaba, a yanzu haka bayan kammala couse Win ta dawo ne da mijinta a hannu. Likita ne Wan'uwanta Dr. Hashim, ya taSa aure sau Waya amma matarsa ta rasu, masifar ?aunar Bintu yake yi yayinda a Sangarenta za'a ce babu yabo babu fallasa.

Tun kafin su dawo Nigeria, iyayen Hashim sun mi?a komai na kayan aure gidansu Bintu, yanzu haka bikin saura sati biyar da kwanaki biyu.

Lokaci Waya Hafiz da Bintu suka yi saurin wayancewa daga kallon da suke ma juna, saboda idanuwan Kareema da take tsaye kamar mutum-mutumi tana kallonsu, da wani irin yanayi mai wahalar fassara a fuskarta.

"A'a! Mummyn Aadil ku nake gani haka? Ya kuke? Ya bayan rabuwa kuma?"
Bintu tayi saurin jero maganganun ga Kareema, fuskarta cike taf da dariyar ya?e. A zuciyarta kuwa ya?i take da shaiWanin da ke neman Warso mata wani banzan tunani akan Hafiz daga ganinsa sau Waya bayan shekaru biyu da suka shafe basu ?ara haWuwa ba.

"Aunty Bintu ashe kin dawo? Shi ne babu ko labari ai da mun zo miki sannu da zuwa ni da Yaro na."
Kareema ta faWa tana dariya. Kafin Bintu ta ce komai Kareema ta sake cewa ga Aadil cikin harshen turanci.
"Aadil ka ga Ummee ta dawo? Je ka gaishe ta kayi mata oyoyo."

Da gudu Aadil ya tafi ya rungume ?afafun Bintu yana murnar ganinta. Cike da ?auna ita ma Bintu ta tsuguna daidai tsawon yaron tana biye ma surutunsa. Aadil Win ne ma yake faWa mata ai Auntynshi Zulai ta haifi baby boy ?atoto.

Tsakanin Hafiz da Bintu an rasa wanda zai fara cewa da kowa komai har sai da Kareema ta karSi makullin motar da ke ri?e a hannunsa bayan ta bashi uzurin za ta buWe boot a zuba kayayyakin da suka siya.

"Dr. Bintu! Hope kin dawo lafiya."
Hafiz ya karya gwuiwa matsayinsa na namiji ya tambayeta da muryarsa mai cike da kwarjini.

Ba ?aramin namijin ?o?ari tayi ba gurin danne tsohon mikin da ke taso mata a zuciyarta ta amsa mishi a mutunce. Sannan ta gaishe shi, ta ?ara da tambayarsa bayan rabuwa.

"Lafiya ?alau. Congratulation."
Ya amsa gaisuwar a ta?aice, ya ?ara da yi mata murna.

Amsawa tayi cikin sanyin murya, sannan ta mi?a hannu ta karSi Najma da ke ri?e a hannunsa tana yi mata wasa lokaci guda kuma tana tambayar sunanta.

Karima da take zaune a cikin mota tana kallon duk abinda yake faruwa, shiru tayi ?irjinta na bugawa, zuciyarta na suya saboda kishi. ShaiWan da iya ?ayata abu kuma sai take ga kamar har wani murmushi na musamman Hafiz da Bintu suke sakar ma juna. Ta samu sau?in damuwarta ne sanadiyyar addu'o'i da tayi ta ja cikin zuciyarta.

Kamar Hafiz ya san halin da Kareema ke ciki sai cewa ya yi
"Bari mu wuce, ?urratul Ayni na jiranmu a cikin mota. Duk da de waccan weekend Win a gida gurinsu Umma Aadil ya yi gobe da safe direba zai kawo miki shi ku gaisa, zuwa yamma sai a dawo da shi. Saboda jibi sunan Zulai, za su tafi da wuri."

"Na gode ?warai Daddyn Najma. In sha Allah nima zan le?a gidan sunan don mu gaisa da su Aunty Balira. Allah ya raya."

"Amin."
Ya amsa sannan ya karSe ?a?anshi ya nufi mota, ita kuma ta tsaya tana kallon bayanshi, zuciyarta na ?una da tafarfasa. Dama ta sani, za'a daWe bata daina da na sanin kura-kuran da ta aikata har suka janyo rabuwarta da Hafiz ba.

Da ?yar ta iya haWiye ?wallar da ya taho mata kafin ta juya da sauri ta shige cikin Mall Win.


********

Bubbuga ?afa ta fara yi a shagwaSe sannan ta ce
"Ni dai gaskiya Aunty Ruwan wankannan ya yi zafi da yawa. Don girman Allah ki surka. Wallahi ni kaWai na san azabar da nake sha idan kika Webo tafasasshen ruwan zafin nan a tawul kika danna min a baya."

Da?uwa Aunty Balira tayi mata, ta ?ara da cewa
"?aniyarki Zulai, Wankan jego idan ba'a yi da tafasasshen ruwa ba da me kike so ayi? Ba kya so jikinki ya yi ?arfi ki samu lafiya a gaggauce da juriya fiye da da ne?"

Shiru tayi, sai kuma ta amsa a hankali
"Ina so mana Aunty. Amma azabar ruwan zafin ne ba sau?i..."

"Kin san Allah Aunty ki daina biye ma Zuly. Ki gargashe ta da kyau yadda ya kamata, idan ruwan ma ya fara sanyi ki ?walla min kira in ?aro tafasasshe. Gaba Waya Yaya Kamal ya sangartata kamar ba mace ba."
Kareema da take zaune a cikin Wakin ana yi mata lalle ta tsoma bakinta a cikin zancen da suke yi, tana maganar tana dariya.

Da fuskar tausayi Zulaikha ta ce
"Ba komai! Ba komai Aunty Kareema. Na gode. Na san zama na da ke. Kuma wannan maganar da kika faWa kamar a kunnen Abban Imam..."

Da sauri Kareema ta ce
"Aaaa ni kar ki ?ulla min jakar tsaba in tafi kaji su tsattsaga.. Ba ruwana. A kanki Abban Imam idanunshi rufewa yake yi..."

"Kamar yadda na Yaya Hafiz suke rufewa a kanki ba."

A tare duk su biyun suka yi dariya.
Haka suka ci gaba da hira da raha a tsakaninsu har ruwan ya Wan sha iska kaWan sannan aka yi wankan.
Tana fitowa daga bayin ta ji shigowar motar Abban Imam cikin gidan, da saurin gaske ta cire tawul Win da yake kanta, ta Wauki babban hijabinta ta saka ta kama hanyar fita daga Wakin da sauri, bata saurari Kareema da ke ?walla kiran sunanta ba.

Cikin mita da mamakin rashin ta idon Zulaikha a fuskar Aunty Balira ta ce
"Uhmmm! Ai in dai Zulai ce za kiyi ki gama, ba ta haWa lokacin mijinta da komai duk da jego take yi. Ni da nake gidannan ai ina shan kallo. Shi yasa sati biyu kacal zanyi in tattara komatsaina in koma inda na fito. Ga Hajja nan, da taimakon Mummy sai su Wora daga inda na tsaya."

"Ki ?yale su kin ji Aunty, idan kika yi sati biyun anan, kawai mu wuce gidanmu ki ?arashe sauran kwanakin a can..."

"TaSWijan! Ashe kuwa da na yi gudun gara na faWa zago. Bazan iya da rashin kunyar Hafizu ba, ke dai da kunya a idanunki, Hafizu kuwa kunya ta bi can! Shi ya bi nan."

A kunyace Kareema ta sunkuyar da kanta ?asa tana dariya. Ita ma Aunty Balira dariya ta yi.
Can kuma sai ta fara jajen mutanen Fa?o masu zuwa suna, har yanzu basu iso ba saboda basu fito gida da wuri ba.

Su Aunty Rakiya sun iso ne daf da kiran sallar magriba. Nan take gidan ya ?ara kaurewa da hayaniya. Dom ma dai tunda cikin ya tsufa suka koma Sangarensu na can gidan Mummy, a can ta haihu. Don haka ba su da matsalar gurin saukar ba?i.



******


Washe garin suna, yaro ya ci suna Abdulfatah. Taron sunan da ya haWa gagga-gaggan ?an gayu abokan aikin Abban Imamu da na Mummy. Suna ne aka yi na ?an gayu, an dafa kalolin abinci sun yi kala goma. Sannan duk wani abu da za'a ci, a sha, ba daga gidan aka dafa shi ba.

Tun da wuri waWanda aka ba kwangilar dafa abincin suka taho da yaran da za su raba abincin. Duk yawan mutanen da suka taru a gidannan sunan sun ci, sun sha, sun ture, saboda komai a wadace ake zubowa.

Mutanen Fa?o kuwa sai da suka yi ta cizon yatsa saboda yadda suke ganin kiSi-kiSi na abinci an ci kaWan an barshi, ga guri nesa, balle su ce za suyi guzuri su tafi da shi gida.

Misalin ?arfe uku na rana Bintu da Aunty Sadiya, Mashkura, da Ummansu suka isa gidan sunan. Nan take kallo ya koma sama, saboda yadda Bintu ta haWu ta haWe, ta fito a Dr. Bintu sak! Dama in dai gurin gwalli, kwalliya, ?walisa ne in dai aka haWu da Bintu to a shafa lafiya, ita Win ?arshe ce.

Abinku da ?an ?auye da basa rabo da tsegumi, nan take suka fara hum-hum-hum ana ai tsohuwar matar Hafizu ce. Sai dai tambarin rashin kirki da aka yi mata a baya yasa bata yi wani kwarjini ba a idanunsu, duk da yadda ta dinga bin su tana gaisar da su cikin girma da mutuntawa.

Turamen zannuwa uku masu tsadan gaske da rigunan Baby guda huWu Bintu ta kaima Zulaikha. Sannan ta kawo wani babban akwati sha?e da kayan arziki ta dam?a a hannun Aunty Balira cewa ta kai ma Innaye. Duk waWanda za a ba da sunayensu manne a jikin kayayyakin.

Rakiya da Ladidi iyayen ri?o da rashin mantuwa. Ko kaWan bata wani burge su ba. Sai dai duk yadda suke ta cin magani suna share Bintu a dole suka saki fuskarsu, saboda yadda take ta musu shisshigi tana jan su da hira da dariyarta, kamar ma bata san suna Waure mata fuska ba.

Bintu shigewa cikinsu tayi sosai, kamar ita Win ?ar'uwar Zulai ce ta jini. A Canjin kaya kala na bakwai da Zuly tayi ita Bintun ce tayi mata sassau?ar kwalliya ba Hibba ba.
"Bari in Wan tsara miki fuska mana ?anwata. Ni ma fa na iya kwalliyar nan, amma abubuwa da yawa a yanzu sun sha min kai ba ma na ko samun lokacin yin kwalliya sosai."
Bintu ta faWa lokacin da taga Hibba ta shigo da akwatin kayan makeup Winta za tayi kwalliya

52 / 53