Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   31 / 53

90K to 93K   out of 157.3K words

hankali da fargaba irin wannan ba.

Ko da ya kira wayar Zulaikha ya ji kiran ya shiga, daga bisani kuma aka katse sannan aka kashe wayar gaba Waya. Wani wawan bugawa ?irjinsa yayi, lokaci Waya kuma kamar aikin asiri zazzaSin jikinsa ya dawo Wanye jagab.

Cikin ?an?anin lokaci sai ga shi akan gado yana rawar Wari. Wani abin dariya da tausayi shi ne, duk da wannan hali da yake ciki ba kansa yake tunani ba, tunaninsa wane irin hali Zulaikha take ciki a wannan lokacin? Me yake damunta? Me yasa ta kashe mishi waya? Har ya Waga waya zai kira Mummy ko Karima don a duba mishi halin da take ciki sai ya tuna ai duk sun fice gurin ayyukansu.

Lambarta ya sake gwada kira, a kashe. Ya ?ara gwadawa ba sau Waya ba ba sau biyu ba, amma duk amsa Waya na'uwa take maimaita mishi. Wannan lambar da yake kira a kashe take.

Jikinsa a sanyaye ya ajiye wayar gefe Waya, hankalinsa a tashe, ga wasu ?an ?ananun ?wallah na matsanancin damuwa da zazaaSi da suka taru a kwarmin idanunsa.

Ya Wauki fiye da awa Waya yana cikin wannan hali, kafin ya yun?ura ya mi?e tsaye a wahalce ya fice daga Wakin, sannu a hankali ya fice daga Sangaren nasa gaba Waya ya nufi cikin gida Sangaren su Mummy.

Yana shiga, ya hangi mai aiki Rahina tana jera abinci kan teburi. Da rawar jiki ta zube ?asa, za ta fara gaishe shi ya katse ta da tambayar

"Ina Zulaikha?"

"Tana Wakin Hajja za ta yi mata kitso..."

Kafin ta gama faWa har ya bar gurin, kai tsaye Wakin Hajja ya nufa ba tare da wani tunani ba. Siririyar sallama Waya kacal yayi, bai jira an amsa ba ya buWe ?ofar Wakin yasa kai ciki, Hajja ya gani, kwance akan kujera. Da alamun tsifa take yi barcin ya kwashe ta, domin ga kan nan a buWe ta kwance rabi saura rabi.

A hankali ya koma da baya da baya ya fice daga Wakin sannan yaja mata ?ofa. Daga nan, Wakin Zulaikha ya nufa kai tsaye, yana tafiya, amma ji yake kamar ba ya sauri don tsananin Wokin son tozali da kyakkyawar fuskarta da gane ma idanunsa wane hali take ciki?

Ko da ya isa ?ofar Wakin, ita ko arzikin sallama Wayan ma bata samu ba. Hannun ?ofar kawai ya kama ya buWe ya cusa kansa cikin Wakin.

A firgice Zulaikha da take zaune a gefen gado ta buga tagumi da hannu bibiyu ta mi?e tsaye. Hankalinta a tashe, tsawon da?i?u sittin suka Sata suna kallon ?uda a tsakaninsu ko wanne ?irjinshi na bugawa fat-fat.

Kamar wacce aka tsikara, aka ankarar kuma sai tayi saurin komawa ta zauna da sauri bayan ta tuna da irin rigar da ke jikinta. Duk da ba mai bayyana tsiraici bace, amma ta kamata ?warai. Sannan babu hijabi ko mayafi a jikinta, ga kanta babu Wankwali, lallausan gashin kanta da yasha gyaran saloon a barbaje, amma tana ga gara shi da Wan sau?i sau?i a bisa ace ta cigaba da tsayuwa a gabansa da matsattsiyar riga. Mi?ewa domin zuwa Waukar Wankwali ko mayafi kuma kamar ta ba shi damar ?are mata kallo gaba da baya ne.

"Allah ya baki ha?uri Beby. Ki yafe min don Allah... kalamaina ne suka jefa ki a cikin damuwa har ya saka ki kuka ko?"
Yayi maganganun da rauni sosai a cikin muryarsa.
[2/8, 9:20 PM] Fareeda Abdallah: Duk da yadda maganganunsa suka daki zuciyarta, ta kasa Wagowa ta ?ara kallonsa a karo na biyu. Balle kuma har ta iya buWe baki ta amsa masa. A madadin Waya daga cikin biyun ma, sai idanunta ne suka ?ara ciccikowa da hawaye. Lokaci Waya suka fara sauka Wis, Wis, a jikinta.

Kasancewar idanunsa ?ur yake a kanta, hakan ya bashi daman ganin hawayen da take yi. Hankalinsa a tashe, da wani maWaukakin sauri yaja jikinsa zuwa gare ta. Ba tare da damuwa ko fargabar komai ba yasa gwuiyawunsa a ?asa, hannayensa biyu na rawa, yasa hannu ya Wago fuskarta suka kalli juna a karo na biyu.

"Kuka kike ?ara yi Zulaikha?"
Ya jefa mata tambayar, da wata irin sha?a??iyar murya kamar wanda zazzafar mura ta ri?e mishi ma?oshi.
"Kiyi ha?uri. Ki yafe min. Ni ma ba yin kaina bane, Allah ne ya jarabce ni. Kiyi ha?uri don Allah... Amma na rantse da Allah ban fara son ki don zan iya dainawa ba. Ki daure ki bani dama Zulaikha..."

"Gobe, zan... tafi gida... can ?auyenmu..."
Ta katse shi da faWin haka cikin kuka da karkarwar murya.

"Dummmm!"
Haka ?irjinsa yayi wani mummunar bugawa, kansa ya sara duk a lokaci Waya. Tsananin mutuwar jiki da mummunan tashin hankalin da ya ?ara lulluSe shi yasa bai san sa'adda ya saki fuskarta yayi zaman ?an bori a gabanta ba.

Ya haWiyi wasu kauraran miyau daki biyu da?yar, masu masifar Waci da kaurin da ke barazanar yaga mishi ma?ogwaro.
"Saboda... Saboda... Saboda na ce ina son ki ina son aurenki shi yasa za ki tafi???"
Ya tambayeta da?yar, bayan yayi ta ?o?arin harhaWa kalmomin da zaiyi amfani da su gurin tambayarta suna suSucewa a harshensa.

Tunawa da tayi da inda suke ita da shi, da kuma tunanin ako wane lokaci daga yanzu Aunty Karima za ta iya dawowa cikin gidan. Kuma da ta dawo, wacce za ta fara nema a gidan bayan Mummy ita ce.

Ba ma a gansu a yanayin da suke zaune ita da shi yayi zaman dirshan a gabanta kaman mai ro?on gafara ba, a ganshi a cikin Wakinta ma babban ?alubale ne a gare ta, kuma abin a saka musu ayar tambaya ne da zargi.

Don haka ta daure, ta ?warara zuciyarta. Abinda ta lura da shi shi ne tabbas Abban Imam da gasken-gaske yake yi, tunda har ya iya ajiye kunya da kamun kansa ya biyo ta har cikin Wakinta, abinda bai taSa ko kwatanta yi ba. Ko Wakin Karima da ta?e ?anwarsa ba shiga yake yi ba, balle ita da ta kasance ba muharramansa ba.

Abinda ta lura da shi shi ne, a yadda yake Winnan zaune dirshan a gabanta, idan ba wata ?wa??waran magana Waya ya ji daga bakinta ba bazai fita mata a Waki salin-Alin cikin sau?i da kwanciyar hankali ba.

"A'a!"
Ta faWa a hankali.
"Wallahi ba saboda ka ce kana so na bane zan tafi gida. Kawai dai na yi ma Innaye wani al?awari ne kafin tahowata..."
Tayi Wan shiru, kafin ta cigaba da magana a kunyace.
"Na mata al?awarin duk sadda na samu wani Namijin da ya nuna sha'awar aure na a yadda nake, zan koma can ?auye, domin aje can a nemi aure na... Ko baza ka bi ni ?auye ba Abban Imam?"

"Zan bi ki. Na rantse da Allah zan bi ki."
Ya amsa mata da sauri.
"Ai ko cikin ramin macizai kika shige da sunan asalinki, Zulaikha ni mai iya jure duk wani cizo da sara ne in shiga cikin ramin don zuwa neman aurenki. Daman dai babban buri na shi ne in ji shin kin amince da soyayyar da nake miki? Za ki bani damar mallakar zuciyarki ta hanyar buWa min filin guri inyi dashen kyawawan furanni? Ina so ki fahimci ni da gaske nake son ki, ki amince min don Allah... In Allah ya yarda baza ki taSa yin da na sani a tarayyarmu ba."

"Na amince!!!"
Ta amsa a kunyace, sannan ta sa tafukan hannayenta biyu ta rufe fuskarta tana murmushin jin kunya. Wani matsanancin daWi da farin ciki na ratsa duk wani lungu da sa?o na zuciya da sassan jikinta.

"Alhamdulillah!"
Ya faWa da yanayin da ke bayyana matsanancin farin ciki. Da ya rasa abinda zai ?ara bayan kalmar hamdalar kawai sai ya juya zamansa ya fuskanci gabas, yayi sujudus-shukur.

Ya daWe yana jera kalaman godiya ga mahalicci kafin ya mi?e zaune ya fuskanci Zulaikha itama ya fara mata godiya, da al?awurra kala-kala na irin yadda zai kula da ita ya riritata idan har Allah ya tabbatar da aurensu.

Ita dai ta kasa cewa komai, sai murmushi kawai take ta jifanshi da shi, zuciyarta cike da matsanancin farin cikin da ta daWe bata tsinci kanta a cikin makamancinsa ba.

"Abban Imam, ya kamata ka tafi Sangarenka pls! Kar a shigo a ganka a cikin Wakina."
Ta tunatar da shi cikin sanyin murya, ganin kamar ya ma manta a inda yake.

"A'a ni dai, ban gaji da ganin kyakkyawar fuskarki ba gaskiya Beby."
Ya faWa da dukkan gaskiyarsa, har yana ?ara gyara zaman dirshan a gabanta.

Zazzaro idanu tayi da farko, sai kuma ta Wan Sata fuska. A shagwaSe ta ce
"Ni dai don Allah ka tafi, ba ga waya ba za mu cigaba da magana? Don Allah ka fita. Ka ga fa tun Wazu kitso zan je inyi ma Hajja, na san yanzu ta gama tsifa. Kuma ma Aunty Karima ta kusa dawowa, bazan ji daWi ba gaskiya idan aka tarar da kai anan, don Allah ka tafi."

"Zan tafi. Amma bisa sharaWi Waya..."

"Menene sharaWin?"
Ta katse shi da tambayar tun kafin ya rufe baki.

"Ki Waukar min al?awarin za ki kunna wayarki, kuma idan na kira za ki Wauka, sannan baza ki sake kashe wayar saboda ni ba."

"Na yi al?awari. In sha Allah zan kiyaye, bazan sake kashewa ba."
Ta amsa mishi da murmushi a fuskarta. Domin ta zaci wasu sharuWWa ne masu wahala, da taji sau?a?an sharuWWa ne yasa ta amsa har da murmushinta.

A maimakon ya mi?e ya fice, sai yayi tagumi ya ?ura mata idanu.

"Menene kuma?"
Ta tambayeshi tana Wan tura baki gaba.

"Ina son ki ne..."

"Ni ma haka. Abban Imam don Allah ka tafi..."

Da saurin gaske ya fice daga Wakin tun kafin ta gama maganar da take yi, fuskarsa cike fal da murmushi.


******


Duk da zancen tafiyar Zulaikha ya zo ma Mummy, Karima, Hajja a ?urarren lokaci, bayan ?orafi da nuna mata Sacin ran rashin sanar da su batun tafiyar akan lokaci, ita kuma ta Wauki laifin Wungurugum ta Wora akan Hafiz cewa shi ne bai sanar da ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ita za su tafi tare ba sai a ranar. Haka suka haWa mata tsaraba mai yawa da za ta tafi ma da iyaye da ?an'uwanta.

Karima dai hankalinta sam ya ?i kwanciya da tafiyar Zulaikha. Gani take kamar idan Zulan ta tafi baza ta dawo ba kamar yadda ta ce. Minti Waya biyu sai ta kalle ta ta ce
"Zuly ina fatan dai ba tafiyar gaba Waya za kiyi ba? Don Allah kar kiyi mana haka, bamu shirya rabuwa da ke a yanzu ba."

"Ki kwantar da hankalinki Aunty Karima. Zan dawo in sha Allah, ai kin ga ko kayayyakin sawa ta ma ba duka na Wiba ba. Zan dawo, don Allah ki daina damuwa."

Tun da yammacin ranar, bayan Abban Imam ya gama ramakon barcin da ke kanshi, ya fitineta a waya da tambayar me take so a matsayin tsaraba? Ita kuma tana ta sake maimaita mishi ba ta son komai.

Duk da haka dai be yarda ba, ana idar da sallar magriba ya Wauki Karima da Imam suka shiga kasuwa siya mata tsaraba. Tunda yayi-yayi da ita tazo su je ta ce baza ta je ba.

Ba tare da jin zafin kuWin da zai kashe ba haka Karima ta zage ta zaSo mata turamen zannuwa masu kyau da tsada, ta Wauki shaddoji kala uku da turaruka, sannan ta Wibi ?ananun abubuwa wanda Zulaikha za ta raba ma sauran mutanen gidansu. Domin labarin ahalinsu Zulaikha ba wanda bata faWa mata ba, sai dai kawai ace bata san su a idanu ba.

A ?arshe bayan sun gama siyayya gaba suka ?ara zuwa wajen sayar da wayoyi. Wayar samsung ya siya mata mai kyau da tsada ya biya kuWin komai suka fice daga gurin.

Ita dai Karima sai murmushin farin ciki take saki lokaci bayan lokaci, domin tun kwanaki ta fara fahimtar take-taken Yayan nata akan Zuly, amma da yake duk su biyun suna ta nu?u-nu?u, sai ta kawo idanu ta zuba musu. A yau kam ta tabbatar da gaskiyar komai, duk da Yayan nata mutumin kirki ne mai hannun kyauta, wannan uban siyayyar ba kowa za'a iya yima ba sai wacce zuciya ke tsananin So da ?auna.

Daga Zulaikha har mutanen gidan babu wanda ya faWa ma Imam washe gari za ta tafi, saboda gudun irin rikicin da zaiyi. Kawai sun bari ne idan ya dawo makaranta washe gari sai yaga ba ta nan.
Tsoro ne sosai ya kama Zulaikha da ganin irin tsarabar da Abban Imam ya kawo mata, a gabansu Mummy. Jikinta na rawa ta mi?e tsaye, idanunta a warwaje ta ce
"Mummy... Don Allah ku rufa min asiri. Na rantse da Allah idan na tafi da kayayyakinnan gida daga Innaye har Baffa sai sun kusa karairaya ni. Don Allah ku bar su, waWanda kuka haWa min ke da su Hajja ma na rantse da Allah sunyi yawa, kawai dai zan tafi da su ne in faWa a gaban Yaya cewa ke kika bani, idan basu yarda ba sai in kira a waya kiyi musu ?arin bayani..."

"Kin san Allah baki isa ba. Kin karSi tsarabar kowa sai nawa da nake shirin aurenki za ki ce baza ki karSa ba?"
Abban Imam ya faWa ransa a Sace, ba tare da kunyar idanun Hajja da Karima da suke gurin ba, kuma sam basu taSa sanin da zancen soyayyar ba sai yanzu da bakinsa ya suSuce ya faWa.

"Ayyyuririririiiiiiii"
Hajja ta kama hanci ta rangaWa ?a??arfan guWa. Fuskarta na bayyana matsanancin farin ciki da jin wannan daddaWan labari.

Mummy da Karima kuwa me za suyi ba dariya ba. Ita kuwa Zulaikha ina ma ?asa zai tsage ta shige don kunya? Da?yar ta iya juyawa da sassarfa ta gudu zuwa Wakinta.

Sai a lokacin, shi kanshi ya tuna da Saram-Saramar da yayi. Amma da yake shi namiji ne sai kawai ya fuske ya daka ma Karima tsawa da tambayar wa take ma dariya?

"A'ah Yaya! Yanzu fa lallaSani ya kamata kayi gaskiya... Domin a Sangaren Zuly ka san dai ina da ?arfin sakawa da hanawa, don haka gara ka bi ni a sannu kar in Sata maka budget."

Waige-waigen neman abinda zai jefe ta da shi yasa ta mi?e da saurin gaske ta wuce zuwa Wakin Zuly tana ?yal?yala dariya. Ko da ta shiga, haka ta tasa Zulaikha da tsiya da tsokana har sai da taga za tayi mata kuka sannan ta rabu da ita.

A gefenta ta zauna, ta cigaba da bata shawarwari, a fakaice kuma tana ?ara yi ma Wan'uwanta kamfen. Domin al'amarin ba ?aramin daWaWa mata zuciya yayi ba.


[2/9, 10:20 PM] Fareeda Abdallah: Saboda yadda Abban Imam ya kafa ya tsare a dole aka yi raba dai-dai tsakanin tsarabarsa da ta su Mummy. Aka rage yawan na su, aka zuba wasu daga cikin nashi. Sauran kuma aka haWa a cikin babban jaka aka ajiye a Wakin Mummy da cewa bayan sati Waya da tafiyarta ahalin gidan gaba Waya za su kai mata ziyara can ?auye, a lokacin sai a tafi da sauran kayan a matsayin tsarabar da suka yi mata.

Wayar da ya siya mata kuwa ba don ranta na so ba tana ji tana gani Aunty Karima ta kwashe komai nata da ke cikin tsohuwar wayar, ta mayar mata a sabuwar wayar, tana kwashe kayayyakin tana mata mitar yadda komai aka ce ta tafi da shi sai ta ce a'a, ita tana tsoron Baffa da Innaye.

"Wannan wayar dai ko kin je gida da ita na tabbata basu san kuWinta ba balle ayi miki faWa. Kina zuwa ki mayar ma da Aunty Balira tsohuwar tata, tunda daman aro ta baki. Ki ce musu Mummy ce ta siya miki wannan, na tabbata baza suyi miki wani faWa ko ?orafi ba."

Yarda da Aminci mai yawa ne ke tsakanin Zulaikha da Karima. Ta yadda a tarihin Zulaikha Wai Wai ne abinda Karima bata sani ba, daga cikin abubuwan da har yau Zulaikha ta kasa buWe baki ta ba Karima labari aurenta da Hafiz yana ciki.

Auren da tunaninsa kaWai ke tsittsinka mata zuciya. Amma dai tana addu'a, kuma tana fata da ya?inin wannan tafiya gidan da za tayi ya kawo ?arshen komai, kuma ?arshen komai Win ya taho a sau?a?e.


******


Tafiya Fa?o a wannan satin sam-sam ba ya cikin lissafinsa, saboda satin da ya wuce ya je. A yadda ya tsara, sai sati na sama zai tafi.

Amma maganganun Zulaikha da suka tsaya mishi a zuciya yasa ya katse komai da ya tsara gudanarwa a asabar Win ya shirya tafiya Fa?o.

Da damuwa sosai a fuskar Bintu take mishi ?orafin tafiyar, saboda sun riga sun gama tsara ziyarar muhimman guraren sha?atawa za suyi a wannan weekend Win.

"Kiyi ha?uri Sweetheart. Wallahi tafiyar ce tazo min bazata. Amma duk yadda ake ciki zanyi ?o?arin dawowa da wuri, idan lokaci bai ?ure ba sai mu fita, idan kuma lokaci ya ?ure sai mu bari lahadi."

Da haka suka rabu, ba don ranta ya so ba tayi mishi rakiya har bakin ?ofa, sannan ta karSi Aadil daga hannunshi, ya sumbaceta a kunci kafin ya fice daga falon tana mishi addu'ar Allah ya kiyaye hanya.

Da yake shirin tafiyar a fusace yayi ta, ana idar da sallar asubah babu daWewa suka fita shi da direba, ?arfe shida rabi na safe yana ?ofar gidan Mummy. A lokacin Zulaikha ko wanka bata yi ba.

A ta?aice ma tana kicin tana yi ma Imam gashin Meat pie da yace zai tafi da shi makarantar Tahfeez. Wayarta kuma na Waki, shi yasa yayi ta kira bata san yana yi ba.

A ?arshe sai Mummy ya kira, ya faWa mata ga shi a ?ofar gida. Don Allah ta faWa ma Zulai ta fito su wuce, idan ya dawo da yamma zai shigo.

Da Sacin rai a muryar Mummy ta fara mishi faWan ?in faWa mata tafiyarsu da yayi.
"Hafiz? Wani irin tafiya ne ka shirya haka tun da wuri baka sanar da ni za ka tafi da Zulaikha ba? Sai jiya take sanar da ni a ?urarren lokaci wai ka ce tare za ku tafi gida.

31 / 53