Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 53

12K to 15K   out of 157.3K words

abinda ya shafe ta in banda yanzu da aka zo mata da maganarta.

Taja wani zazzafan numfashi ta fesar. ?acin ran da ya bi ruwa sanadiyyar kama aikinta gadan-gadan ya fara taso mata sannu a hankali.

"Yanzu tana ina?"
Ta tambaya a ta?aice, har lokacin bata Waga fuskarta ta kalli Karima ba.

FaWa mata inda ta zaunar da Innaye yasa Bintu ta Waga kai da sauri tana aika mata da wani kakkausan kallo.
"How dare you da za ki zaunar da ita inda aka tanada don ma'aikatan asibitin nan?Me yasa baki zaunar da ita a reception inda ko wane mara lafiya yake zama ba?"

A ladabce Karima ta sunkuyar da kanta ?asa ta fara ba Bintu ha?uri, hankalinta a tashe. Domin bata daWe da fara aiki a asibitin ba, tsoronta Allah tsoronta tayi abinda zai sa ta janyo ma kanta matsala daga fara aikin da take tsananin alfahari da samunsa.

"Shi kenan! Amma ki kiyaye gaba. Duk wata doka na asibiti ki tabbatar kin kiyaye shi sau da ?afa. Bayan haka wannan tsohuwar da kike gani ?azama ce ta ?arshe mai Wauke da cututtuka mabanbanta a jikinta, gara tun wuri kiyi nesa da al'amarinta. Ki maida ita reception ta zauna ta jira ni, zan kira direba yanzu ya mayar da ita inda ta fi wayau. Je kiyi abinda na ce."

Jiki a sanyaye Karima ta fice daga Ofishin tana jinjina maganganun Dr. Bintu a zuciyarta. Haka ta koma inda ta bar Innaye da yanayin da ba shi suka rabu ba.
"Kiyi ha?uri Innaye. Likita ta ce in zaunar da ke a reception ki jira ta. Za ta kira direba ya mayar da ke gida."

"To ba komai Karimatu. Na gode, Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari. Idan kin koma gida ki gaishe min da Kakarki da mahaifiyarki."
Ta faWa ba tare da ta maganar da nisa ba, ganin yanayin Karima da irin maganar da ta faWa mata in ji Bintu yasa ta tunanin wata ?ila Bintun ta faWi mummunar magana ne a game da ita.

Duk da yadda take jin rashin ?arfin jiki saboda yunwa, haka ta ?warara kanta ta mi?e tsaye ta fara tafiya a hankali zuwa waje ba tare da ta san ina ne reception Win ba.

Watsar da duk wasu maganganu da Bintu ta faWa mata tayi ta ?arasa da sauri ta ri?e ma Innaye hannu. SaSanin sadda suka shiga cikin asibitin suna hira da dariya, a yanzu babu mai cewa komai har suka ?arasa reception ta zaunar da ita.

Sallama tayi ma Innaye da addu'ar samun sau?i sannan ta kama hanyar komawa gurin aikinta. Innaye ta raka ta da idanu.
10)




Tana daf da Sace ma ganin Innaye sai ta dawo a gaggauce
"Innaye kin karya kumallo kuwa?"
Ta tambaye ta duk da ta san gwajin da aka yi ma Innayen ana yin shi ne kaWai ga waWanda basu ci abinci ba.

"Ban ci komai ba Karimatu. Ai an ce wannan gwajin kafin a ci abinci ake yi. Yanzu dai idan na koma gida zan karya, na san abincin kari na can Auta ta ajiye min."
Ta ?arasa maganar idanunta na kallon ?aton agogon da ke manne a jikin bangon gurin, wanda ya nuna ?arfe goma sha biyu saura minti ashirin.

"To shi kenan. Allah ya ?ara sau?i. Bari in kawo miki Maltina ki sha kafin ki koma gidan. Wannan rashin ?arfin jikin naki ina ga har da yunwa ne ya galabaitar da ke."
Bata jira amsawar Innaye ba ta wuce ciki zuwa Ofishin da suke zama inda ta ajiye jaka da sauran kayayyakinta.

Maltina ta Wauka a jakarta da samosa guda biyar a cikin robar take away ta fice a gaggauce ta kai ma Innaye. Bata tsaya amsa godiya da saka albarkar da take mata ba ta koma ciki ta kama ayyukan da suke gabanta.

Da gaskiyar Mal bahaushe da yake ma yunwa take da mare hankali. Innaye bata san yunwar da take ji ya kai ?ololuwa ba sai da taga Maltina da Samosa a hannunta. Jiya da daddare ba wani abincin kirki ta ci ba saboda tunanin rayuwar gidan Abdul-hafiz da makomarsa a can gaba, da wannan dalilin yasa take jin cikinta a rarake kamar wacce ta kwana ta yini bata ci ba. Duk yadda ta kasance dattijuwa mai tsananin kunyar idanun jama'a bata damu da mazauna gurin ba ta buWe robar Samosa ta Wauka ta fara ci tana korawa da Maltina. Kafin ace kwabo, ta cinye gaba Waya.

Lumshe idanu tayi tana hamdala a zuciyarta saboda jin yadda a ?an?anin lokaci ta ?ara dawowa cikin hayyacinta. Ashe kaso sittin na gajiya da galabaitar da tayi yunwa ce, yanzu kuwa da ta samu mahaWi sai ga shi ta dawo hayyacinta sosai tana jin ?arfi a jikinta.

?ara gyara zama tayi idanunta a lumshe tana shan A.c a zuciyarta kuma tana Istigfari da Hailala kafin ta ankara ta fara gyangaWi.

"Wai barci kike yi? Ki tashi ga direba can zai mayar da ke gida."
Ta ji muryar Bintu bagatatan a kanta kamar a cikin mafarki.

A hankali kuma a nutse ta buWe idanunta ta zuba a cikin na Bintun. Ita ma fuskarta babu walwala ko kaWan kamar dai yadda fuskar Bintu yake. Sai kuma ta kawar da idanunta daga Bintu ta maida kan agogo, ?arfe goma sha biyu da minti goma sha takwas na rana.

Bata ce komai ba sai mi?ewa da tayi tsam ta tsaya tana kallon Bintu.
A fakaice, Bintu ta harari gefen Innaye, ta ?ara Sata fuska sannan ta nufi hanyar fita. Innaye ta rufa mata baya zuciyarta na ?ara cika da tsoron halayen Bintu da sannu a hankali suke ?ara bayyana.

Har suka ?arasa gurin motarta inda direba ke zaune a mazaunin direba bata sake ce ma Innaye komai ba. Ita ma Innaye bata ce mata cikanki ba.

Kamar sadda za su zo asibitin, ?ofar baya na motar Innaye ta buWe ta zauna sannan ta mayar da ?ofar ta rufe da ?arfi.

'Ta Allah ba taki ba. Duk muguntarki haka za ki ga motar nan ki ?yale ko ?warzane baki isa kiyi mata ba.'
Bintu ta faWa a zuciyarta, cike da jin haushin irin bugun ?ofar da Innaye tai ma motar ta.

Dogon tsaki ta ja kafin ta mayar da idanunta kan direba.
"Bala kayi tu?i a nutse fa. Kana dawowa ka tabbatar ka wanke min motar ciki da waje saboda ?ura da gudun kwasar cututtukan da ban san farkonsu ba bare ?arshensu. Ina fatan ka gane?"

"Na fahimta Ranki ya daWe. Sai na dawo."
Ya amsa a ladabce.

Baya ta matsa, shi kuma ya tayar da motar, tana tsaye tana kallonsu har suka fice daga cikin asibitin kafin ta koma ciki tana sake jan tsaki sama-sama.


******


"Hmmm! Na ce ba... Au! Ina kwana Baba?"
A Wan daburce Zulaikha ta sake gaishe da Rabi a karo na uku.

Ba tare da damuwa ko nuna yanayin gundura ba ta amsa gaisuwar da murmushi fal a fuskarta. Haka kawai, Zulaikhan burge ta take yi, basu taSa yin wata doguwar magana ba tun da suka zo gidan, amma idan ta je can inda aka sauke su za ta kai musu abinci ta ga irin taSara da shagwaSar da yarinyar ke ma mahaifiyarta abin dariya da burgewa yake ba ta.

Tun bayan shigowar yarinyar, da ajiye tsadaddun kulolin abincin mai gidan da tayi ta gaishe ta a karo na farko, ta lura da yadda yarinyar take saiSi wajen fita kamar akwai wani abu da take so.

Har ta kusa fita sai ta juyo da sauri ta sake gaishe ta a karo na biyu, ko bayan da ta amsa gaisuwar, sai ta Wan tsaya shiru ta ?ura mata idanu.
A karo na ukun kuma har ta fita sai ta sake dawowa ta gaishe ta.

Kamar baza ta amsa ba, duba da yadda Hajiya Bintu ke ta kwakkwafarta a kan ba?in tun ranar da suka zo gidan sai kuma ta yanke shawarar yi mata magana ganin yanzu ai Hajiyar ba ta nan.

"?an matan Mamanta ya aka yi? Gaisuwa Waya biyu ai ya isa ko? Kin ga tun shigowarki na lura kamar akwai maganar da kike so kiyi amma kina ta nu?u-nu?u. Kina bu?atar wani abu ne? Kar ki damu, faWi ko me kike so yanzu in Wauko miki."

Kamar damar da Zulaikha take bu?atar samu kenan. Da sauri ta ce
"Ummm! Daman zan tambaye ki ne don Allah. Jiya da rana har kika tafi baki kawo mana abinci ba, kin manta da mu ne?"

?an shiru Rabi tayi kamar tana tunani, sai kuma ta amsa kai tsaye da cewar
"A'a! Ban manta da ku ba. Hajiyar ce ta ce ba sai nayi abincin rana ba, ko da na tuna mata da ba?i kuma sai ta ce ba abinda ya shafe ni bane. Ta aike ni can gidansu daga can kuma na wuce gida..."

"Da gaske haka kuka yi Baba?"
Zulaikha ta katse ta da tambayar da yanayin mamaki fal a fuskarta.

"Eh da gaske, me zai sa inyi miki ?arya? Kin san daman a Sangaren girki abincin da nake dafawa a gidannan na masu aiki ne kawai, sai kuma ba?i idan akwai.

Abincin maigidan ita da kanta take dafawa. To tunda ta ce ba sai nayi ba ai kin ga ba ni da hurumi ko ikon da zan ce dole sai anyi ko?"

"Uhmmmm haka ne."
Zulaikha ta amsa a mamakance.
"Lallai ma!"
Ta ?ara faWa tana sake jinjina girman al'amarin. Ita daman tun jiya ta san da gangar Bintu ta hana su abinci, amma saboda tsananin ?warewarta a ?arya da iya shirya zance sai ta ce bata san ba'a kai musu abinci ba.
"Ba damuwa. Ta yi ma kanta."
Ta sake faWa ranta a Sace.

Da sassarfa ta kama hanyar ficewa daga kicin Win Rabi ta bi ta da kallo.
A zuciyarta take harhaWa Waya bisa biyu tana hasaso abinda ya faru bayan tafiyarta. To ko dai wannan shi ne dalilin da yasa ta ga waWannan tsadaddun kulolin na abincin Oga a hannun Zulaikha? Kulolin da ko gurin wanke-wanke Hajiya ta jaddada mata lallai ta dinga musu wanki na musamman, sannan da an gama wankewa a kife a kwando a saka towel a goge a mayar da su ma'adanarsu, ba tare da an haWa su da tarkacen kaya ba...

"Amma Baba Rabi ita Hajiyar ta faWa miki matsayinmu a gurin maigidannan kuwa?"
Maganar da Zulaikha tayi ya dawo da ita cikin tunaninta ba tare da ta san sa'adda ta dawo cikin kicin Win ba.

"A'a! Bata faWa min ba. Abu Waya dai da na sani ku Win danginshi ne, don Hajiya Bintu ta sha faWin shi ke da ?an'uwa ?auyawa..."

"Ba ?an'uwa ?auyawa kaWai bane. Ita wannan tsohuwar ba?auyiyar da kike ganina tare da ita, mahaifiyarshi ce."
Zulaikha ta faWa idanunta ciccike da hawaye. Kafin Rabi da ta buWe baki tayi magana ta cigaba da cewa
"Ita ce ta sha wahalar na?uda ta haifo shi zuwa wannan duniyar. Ni kuma da kike gani kamar ba kowan kowa ba, ?anwarsa ce da suka fito ciki Waya. Saboda Allah da Annabi idan da adalci ya kyautu ace an hana uwar da ta sha wahalar haihuwa da rainon Wanta abincin da shi wannan Wan nata ne yake nemowa da guminsa?"

Kamar an buWe famfo, haka hawaye ke kwaranya a idanunta. Ita kuwa Rabi, tunda ta buWe baki ta kasa rufewa, balle har ta iya ?arfin halin amsa tambayar da Zulaikha tayi mata. Allah ya sani bata taSa tsammanin Innaye mahaifiyar Oga Hafiz bane, duk ga tsammaninta ta fi tunanin ko dai wata Gwaggwansa ce daga ?auye.

Babbar hujjarta kuwa shi ne, duba da yadda daga Hajiya Bintu har Alhaji Hafiz al'amarin tsohuwar basu Wauke shi da wani gagarumin muhimmanci ba. Hujja ta biyu kuwa shi ne, babu wata kamanni ta musamman tsakaninshi da Innaye, Wan gara-gara ma Zulaikha, suna yanayi a fisge...

"Ban ?ara sanin haka duniya take da faWi da tarin abin mamaki Wauke da mutane mabanbanta ba, sai da Bintu ta shigo cikin ahalinmu. Ko da muke ?an ?auye, bamu taSa tsammanin akwai wani tazara na musamman tsakanin Wan birni da na ?auye ba, ko kuma banbanci tsakanin talaka da mai kuWi. Duk a tunanina mu da ku bayin Allah ne da babu wanda ya fi wani a gurinsa sai wanda ya fi tsoronsa... Amma a yanzu na samu ?arin ilimi, ya zama dole mu cigaba da raSewa a ?auyenmu don rayuwar birni da mutanen birni sun fi ?arfinmu ta ko wane Sangare."
Tana gama faWin haka ta fice daga cikin kicin Win da sauri, lokaci bayan lokaci take kai hannu saman fuskarta tana share hawaye.

Ta fito tsakar gidan kenan da nufin zuwa can Sangarensu aka wangale get Win gidan. Kamar baza ta waiga ba, sai kuma ta juya sannu a hankali tana kallon motar da ta shigo. Ganin motar Bintu ce yasa ta ware idanu tana kallon motar da kyau domin ganin ta ina Innayenta za ta fito?

Kallo Waya za'a yi mata, a fahimci jikinta a sanyaye yake sosai.

Zulaikha yarinya ce mai shekaru goma sha bakwai. Amma irin yarannan ne da tun suna ?anana suke da masifar wayau da manyancen iya magana. Ko don ta rayu a hannun Dattijuwa Innaye ce? Allah masani.

Ganin fitowar Innaye daga cikin mota ita ma da nata yanayin sanyin jikin yasa tayi ?o?arin watsar da nata damuwar ta ?arasa gurin Innaye da sauri.

"Innaye? Me yake faruwa? Jikin naki ne?"
Ta jera mata tambayoyin da hanzari fuskarta na bayyana damuwa da tashin hankali. A lokaci Waya kuma tana Wan tattaSa jikin Innayen domin jin ko akwai zafi?

Hannayenta Innaye ta kamo ta ri?e, da murmushi a fuskarta ta amsa da cewa
"Jiki Alhamdulillah Auta. Kawai dai na gaji ne. Amma babu komai, muje ciki."

"To Ma sha Allah! Allah ya ?ara lafiya."
Ta amsa tana jin kwanciyar hankali kaso hamsin cikin Wari na damuwarta.

Haka suka kama hanyar zuwa Sangarensu suna ri?e da hannun juna cikin kulawa. Babu mai cewa komai a cikin su biyun, ko wacce da tunanin da take yi a zuciyarta.

Suna ?arasawa ciki, ta zaunar da Innaye a gefen gado ta sa hannu ta zare mata hijabin jikinta.
"Sannu Innaye. Allah ya ?ara lafiya. Ai dole ki galabaita, jiya fa duk farkin barcin da zan yi sai in ga idanunki biyu. Ga shi yau da sassafe baki samu komawa barci ba kuka fice zuwa asibiti. Ko kinyi barci ne acan asibitin?"

"Barci kuma Auta?"

"Eh mana. To ba naga akwai gadajen da ake kwantar da marasa lafiya ba?"
Ta amsa tana tura baki da murmushi a fuskarta.

"Eh haka ne! Amma ai ana kwantar da waWanda jikinsu yayi tsanani ne. Ni kuwa kin ga har yanzu da sauran ?arfin jiki a tattare da ni..."

"Amma Innaye kin ci abinci bayan an gama gwajin da aka ce za'a miki kafin ki karya?"
Ta katse ta da sauri bayan ta tuno sun fita daga gidan Innaye bata karya ba.

"Uhmmm!"
Ta ja numfashi ta sauke a kasalance. Kamar baza ta ?ara yin magana ba daga wannan ajiyar zuciyar, sai kuma ta ce.
"Auta! Wato da gaske ne duk lalacewar al'umma ba'a rasa na kirki. Yau ba don Allah ya haWa ni da wata yarinya ?ar arziki wacce ta san ya kamata ba da yanzu wani zancen ake yi ba wannan ba. Wata kila, da sai dai matar gidan ta dawo ta sanar da ku babu yadda nake, an kwantar da ni ranga-ranga a asibiti. Amma da yake ko cikin lalatattu ba'a rasa na kirki sai Allah ya agaje ni da taimakonsa na gaggawa a lokacin da banyi tsammani ba. Alhamdulillahi! Je ki tara min ruwan wanka inyi sai in alwala, ga shi can ana kiran sallah a masallaci..."

"Me ya faru da ke a asibitin Innaye?"
Zulaikha ta tambaye ta tana jin babu daWi sosai a zuciyarta. Daman tun bayan ficewarsu take ta ji a ranta lallai a rashin kirkin Bintu za ta fa iya wula?anta Innaye ganin babu idanun kowa a kansu.

Ganin wayar Innaye ajiye a gefen gado yasa ranta ya ?ara jagulewa, tayi tunanin da akwai waya a hannun Innaye, idan ta ga abinda bai gamshe ta ba za ta iya kiran Yayansu yaje asibitin ya Wau mataki.

"Maimaita abinda ya wuce sam ba shi da wani amfani Auta. Balle kuma kin san hali na abu idan ba na alkhairi bane ban cika son maimaita labarinshi ba..."

"Don Allah ki faWa min Innaye."
Tayi maganar kamar za ta saka kuka.

"Bazan faWa miki ba Auta. Domin jin babu abinda zai ?are ki da shi. Nasihar da zan miki a wannan gaSar Waya ne rak! Mu mutanen ?auye ne, can ?auyen, can ne duniyar da muka buWi idanu da ita. Kuma kaso casa'in da biyar cikin Wari na mutanenmu acan suke farawa kuma su ?are rayuwarsu.

A mafiyawancin lokuta duniyar sauyawa take yi. Idan Allah yayo ki cikin masu tsawon rai yanzu kika fara rayuwarki, ban san ko kina daga cikin WaiWaiku kuma tsirarun da Allah ya ?addari za su tsallake ?auyenmu suyi rayuwa a wani guri na daban ba. Idan Allah ya ?addara miki haka, ki ji tsoron Allah. Kar ki kuskura don wani ni'ima da Allah yayi miki ki wula?anta mutanen ?auye, ko ki wula?anta na ?asa da ke.

Je ki tara min ruwan wanka, kafin in fito ki je cikin gidan ki samu mai aikinnan ta baki abinci ki kawo min, idan kuma babu, ki zo ki haWa min shayi."

Duk wasan da ke tsakaninta da Innaye a wasu lokutan kamar jika da Kaka. Ta san irin lokacin da take tubure mata da ?an rigingimu, ta kuma san lokacin da take Waukar abinda ta faWa da muhimmanci.

Don haka a wannan gaSar, duk yadda ta so jin abinda ya faru a asibitin sai bata ?ara cewa komai ba. Ta mi?e tsam, ta shige banWaki ta tara ma Innaye ruwan wanka a bokiti.

Ko da ta fito, sai ta tarar Innaye har ta gama shirin shiga wankan, don haka bata sake Sata lokaci ba ta fice zuwa cikin gidan da wani irin taku na musamman.

5 / 53