Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   38 / 53

111K to 114K   out of 157.3K words

Bayan ya gama kwashe kofunan da suka Sata yakai kicin. Ya dawo ya ce mata bari yaje Wakinsa ya Wauko abu sai su tafi, har yana bata tukwuicin sumbata saboda duk yadda yayi da ita su shiga cikin Wakinshi ko nata ta ?iya. Yana shiga Waki, ita kuma ta gudu cikin gidan ta shige Wakin Hajja...'

Maganarsa ne ya katse mata tunanin da take yi.
"Kin san fa Wazu ba ?aramin tashin hankali na shiga ba bayan fitowata cikin falo ban ganki ba."

Hannunta yaja suka fara takawa a hankali zuwa Sangarensu, lokaci Waya kuma yana cigaba da yi mata bayanin irin damuwar da ya shiga bayan nemanta da yayi ya rasa a cikin falon.
"Bayan duba ki da nayi tayi lungu da sa?o har ?ar?ashin gado da cikin durowa da cabinet na kicin ban ganki ba. Afujajan na fito ina duba ki a harabar gida, binciken inda kika shige bayan dube-dube lungu da sa?on fulawoyi ni ne har gurin mai gadi ina tambayarshi ko ya ga fitar ki? Da mamaki sosai a fuskar Baba maigadi ya tabbatar min babu wacce ta fita a darennan.

Na yi yun?urin zuwa Sangaren Mummy ya fi sau hamsin amma sai in kasa, tunda bata san mun zo gidan ba. Kuma bayan haka Kin san miye tunani da fargabata?"

Girgiza kai tayi. Kafin ya cigaba da cewa

"Idan na shiga duba ki me zan ce musu? Kin fita ba da sanina ba? ko kuma wani abu nayi miki kika gudu don ceton kanki? Kin dai san halin Mummy da tambayar ?wa?waf. Da waWannan dalilan yasa nayi fakare a ?ofar Sangarenmu kamar maraya, daga bisani kuma na fara safa da marwa tsakanin Sangarenmu da na Mummy, zuciyata cike da addu'ar duk inda kika shige Allahu yayi gaggawar bayyana min ke. Sai kuma ga shi da yake Allah maji ro?on bawa ne, ya tausashi zuciyar Hajja ta fito min da ke a lokacin da ban taSa tsammani ba."

A daidai lokacin suka isa ?ofar Sangarensu, da hannu Waya ya tura ?ofar, kasancewar har lokacin hannunsa na dama na sar?afe da hannunta na hagu.

"Kar dai ki manta, ki yi Bismillah! Don kore shaiWanin da ya fara zuga ki ki gudu ki bar mijinki."
Ya faWa idanunsa na cikin nata.

A tare duk su biyun suka yi murmushi. Suka Waga ?afafuwansu na dama lokaci Waya za su shigar, kamar haWin baki kuma a fili suka ambaci Bismillahirrahmanir raheem.

A karo na biyu lallausan murmushi suka sake haske junansu da shi kafin suka shigar da ?afafuwansu na hagu. Har lokacin yana ri?e da hannunta ya mayar da ?ofar ya rufe, ya murza Wan makulli, yaja hannunta suka nufi cikin Wakinsa.
"Kiyi ha?uri. ?azu na tsorata sosai, kar in barki a falo ko in shigar da ke Wakinki ki sake tafiya ki barni..."

"Bazan sake ba. Kayi ha?uri."
Ta katse shi a marairaice tun kafin ya aje numfashin maganarsa.

"Na yi! Amma duk da haka bazan kai ki Wakinki ba. ?aki na za mu je, domin can Win ma kamar naki ne, akwai komai da za ki bu?ata a ciki. Na san kina jin barci ko?"

"Eh! Ina ji."
Ta amsa a hankali. Zuciyarta cike fal da fargabar da take ta ?o?arin dannewa kar ya bayyana a fili.

Ko da suka shiga cikin Wakin a gefen faffaWan gadonsa ya zaunar da ita, cikin lallaSawa da tarairaya kamar wata sarauniya. Jikinsa na rawa-rawa ya shige gurin ma'ajiyar kayan sawansa, ya buWe Sangaren da kayayyakin sakawarta ne sababbi sha?e da gurin. Kama daga laces, atamfa, shadda, har zuwa kayan barci da Inner wears.

Kayan barci masu kyau sosai ya Wauka mata ya fice daga gurin ya nufi inda take zaune. Daga irin yadda ta takure kanta ta naWe hannaye cikin ?irjinta kamar mai jin sanyi ya kusa saka shi dariya, amma sai ya daure baiyi dariyar ba.
"Babe sanyi kike ji?"
Ya tambayeta a tausashe.

"A'a! Barci kawai nake ji."
Ta amsa a kasalance.

"Sorry. Ga kayan barci na Wauko miki. Yanzu dai ki shiga bayi kiyi wanka sai ki canja kayan jikinki zuwa na barci ki kwanta."

Har ta buWe baki za ta ce mishi ta yi wanka tun a gida, sai kuma tayi shiru bayan ta tuna yadda Aunty Balira ke ta jaddada mata banda yi ma miji musu. Kayan barcin hannunsa ta karSa, ta mi?e tsaye a hankali tana kallonshi ?asa-?asa.
"Ina ne banWakin?"

Da yatsarsa manuniya ya nuna mata inda banWakin yake, ita kuma bata Sata lokaci ba ta nufi hanyar zuwa banWaki tana tafiya kalalau-kalalau kamar kazar da ?wai ya fashe ma a ciki.

Duk yadda yake ta Woki da zakwaWin wannan dare don maimaita wainar da suka soya jiya, tsoro da fargabar da yake gani ?arara a cikin idanuwanta ya hana shi taSuka komai.

Ta bakin Hajja ce, matarsa sabuwar shiga ce a komai, lallai ya kamata ya bita sannu a hankali, idan ba haka ba kuwa da sannu zai haifar da gagarumin tsoron gamuwa da shi a zuciyarta.

Bayan ta yi wankan shi ma yayi, rungumeta da yayi tsantsan a ?irjinsa, bayan haka bai mata komai ba suka yi barci har ladanin masallacin unguwar ya kwaWa kiran sallar asubah.


********


A kwanakin da suka biyo baya amarci suke zubawa tsantsa abinsu, soyayya zallah ake shimfidawa a gidan, mai tsafta da burgewa, wanda ko kaWan babu algus a cikinta.

Karima da ta je gidan a cikin satin, kasa rufe bakinta tayi. Cikin Wan kankanin lokaci har sun kara yin wani fresh su biyun, fata ta kwanta luwai-luwai, saboda hutu da kwanciyar hankali, ga kuma lafiyayyun abinci da ake dafawa daga gidan Mommy ana kai musu.

Ga Zulaikha gwana ce da ta kware wajen tarairaya da kulawa da Kamal, a Sangaren auratayya ne dai sai a hankali take sabawa. Ta gama karantar mijinta ciki da bai, tasan duk wani abu da ke faranta mishi rai kuma ta kware akan shi.

Karima Tana zaune tana kallonsu akan kujera 2 seater, kankana da abarba suke sha wanda Zulaikha ta yanka musu bayan zuwanta. Yadda Kamal yake wani zuba ma Zuy shagwaba son ranshi kamar wani karamin yaro shi ne abin ke bata mamaki, ita kuwa ta dage tana ta tarairayarshi, sun hade kawuna suna ta kus-kus suna dariya ba tare da kunyar idanunta ba, sai ta kama ma suke sanyata cikin hirarsu.

Ana nan kuma sai ya tashi wai zai shirya yaje ya gaida su Mommy, Zulai kuma ta tashi ta bi bayanshi bayan ta ba Karima uzurin za ta raka shi sama ya shirya.

Karima tana nan zaune shiru-shiru tana jira har aka fi minti ashirin babu duriyarsu. Abin ma ya kasa bata haushi ko dariya, sai kawai ta yayimi jakarta ta fita. A ranta tana fadin idan sun kara ganinta a gidan su mata abinda suka ga dama.

Gaf da za ta fita sai ga Zuly ta biyo bayanta a sukwane, ta hau sunne kai tana bata hakuri cikin dadin murya, da kyar ta samu ta lallasheta suka koma cikin gida. Shi kuma ya musu sallama ya tafi.

Sai lokacin suka samu lokacin zama su yi hira sosai. Kwarai Karima ta yabawa yanayin da ta gansu a ciki, har cikin ranta tayi murna da fatan Allah Ya dorar da su akan wannan rayuwa da soyayya har abada. Itama kuma tana yiwa kanta fata da dacewa da samun rayuwar aure irin wannan.

Sai can bayan isha'i sannan ta bar gidan lokacin da Kamal din ya koma.

Sai da Zulaikha ta cinye sati uku cif ana kai musu abinci daga gidan su Mommy kafin ta fara cancada musu kalolin girke-girken da ta kware akai na gargajiya da na bature.

Rigima kuma sai ta koma akan a dawo mata da Imamu gidan. Shi kuwa gogan tsoron akai shi can yake, kulawar da ake bashi tayi kasa, a raba musu ita biyu. Shi ne yake ta mata kauce-kauce da bada excuses iri-iri.

Ita kuwa da ta ga haka sai ta dangana shi ga Mommy, ita ta dage tsakaninta da Allah a bar mata Imamu, shi kuma yace ai Imamu ya riga ya zama dan gidan Mommy. Ta hakura kawai ta lalubi junior Imamu. Sai gata tana kuka riri har abin ya so basu dariya. Har cikin ranta tana kaunar zama da yaron.

Ga zaman kadaici da take tunanin shiga ciki idan Baban Imam din ya koma bakin aikinshi ka'in da na'in.

Daga karshe dai Mommy ta kashe rigimar ta hanyar raba musu gardama, tace Imam zai dinga zuwa yana yi musu weekend duk karshen sati, sannan a ranakun karatu watarana zai dinga zuwa da yamma yana kai dare daga can makaranta. Duk da ba haka taso ba, a haka dai aka tashi.

Suna komawa gida ya hau kalallameta da dadin baki da ban hakuri don ya kula dai hukuncin da Mommy ta yanke ba haka taso ba. Daga karshe dai ya samu ya shawo kanta da kyar. Don kuwa shi yasan yar kayanshi, ya kuma san ta yadda yake shawo kan abinshi.


******


Watansu biyu da aure, rayuwarsu na tafiya cikin tsari da ban sha'awa. Rayuwace suke shimfidawa mai kyau da tsafta wacce babu boye-boye da cutarwa a cikinta.

Kamal yana girmama matarshi da Waukaka duk wani sha'ani nata, haka itama tana kaffa-kaffa da al'amuranshi, kuma tana iyaka kokarinta wajen ganin ta kyautata mishi yadda yakamata.

A cikin satin ne kuma kwatsam ba zato ba tsammani Bintu da Hafizu suka kai musu ziyara. Bayan sun buga rikici mai yawa har Hafiz yayi mata rantsuwar idan bata shirya sun tafi gidan tilon ?anwarsa ?wallin ?wal da take aure a garin Abuja ba za ta haWu da mummunan Sacin rai daga gare shi.

Haka ta shirya ranta a Sace, bakinta a gaba, ta ja tsaki ?asa-?asa ya fi sau hamsin kafin su isa gidan. Tun daga bakin gate ta fara buWe idanu tana kalle-kalle. Lokaci Waya zuciyarta ta ?ara jagulewa, komai ya ?ara kwance mata.

Tun sadda aka yi bikin, taji labarin irin gidan da aka kai Zulai a bakin Mashku, amma ko da wasa bata yi tsammanin irin wannan tsararre kuma haWaWWen gidan aka kai Zulai ?ar ?auyen ?ayau ba. Da gaskiyar bahaushe da yace gani ya kori ji.

Ashe haka gidan yake da masifar kyau tun daga bakin gate sai kace a kasar turawa? Aka ce ido wa ka raina? Ya ce wanda ya saba gani kullum! Duk ?ayatuwar gidansu da irin kwalliyar da ke ciki sai taji ta raina kyawunshi saboda gani yau da gobe.

Kai tsaye falon gidan aka yi musu masauki, ta zauna akan kujera tana yatsine-yatsine na rainin ajawali. Ita da kanta ta sani ko hasidin Iza hasadin idan ya gani sai ya yaba, amma don tsananin tsanar da take ma Zulai yasa ta?i ba zuciyarta damar bayyana irin kyawun da gidan yayi mata akan fuskarta.

Falon a gyare yake ?al, ga wani daddaWan ?amshi kuma tattausa na turaren wuta da yake fitarwa. Kasancewar ranar Assabar ce, Kamal yana gida, bayan zaman mintuna biyar da suka yi suna jiran masu gidan suka fito shi da ita a lokaci guda.

Daga ganin yadda Zulai ta ?ara yin Sul-Sul, farar fatarta da ya dusashe saboda zaman ?auye ya goge ya tsatso kamar a taSa ta jini ya Sullo, daga kallon fatar za a fahimci jikinta sumul-sumul yake sai shekin hutu da jindadi yake fitarwa.

Daga cikin matsakaicin hijabin da ke jikinta suke hangen kananun kayan da take sanye da shi. Shi kuwa gogan nata gaba-daya ya kasa dauke idanunshi a kanta sa'ilin da take zirga-zirgar Wauko musu Wan abin taSawa da ji?a ma?oshi.

Ta tare su da fara'arta, sosai fuskarta ya bayyana jin daWin ganinsu. Har kasa tasa gwiwoyinta ta gaishe da Hafiz. Shi kanshi Hafiz Win bakinshi ya ki rufuwa ganin irin kyau da tayi da girma da nutsuwar da ya bayyana a tattare da ita. Babu wannan yarinta da gigin da ya saba gani a jikin Zulan Innaye.

Bintu kuwa ba?in ciki kamar zai kashe ta, ita kaWai take ?ara kumbura tana han?oro kamar za ta fashe. Jindadi da farincikin da ta gani a tattare da Zulai ya bala'in ?ona mata rai. Wani rashin wayau da ta yi kuma shi ne kasa boye hakan da tayi.

Hassada da bakinciki da kishi suka bayyana a fuskarta ?arara. Ita duk a tunaninta wai me wannan banzar Zulai Win take da shi ne da zata kasance a cikin irin wannan daular? Yarinyar da ko karatun sakandare bata fita da sakamako mai kyau ba? Yarinyar da tayi rayuwar kauyen kayau? Wacce ta rayu a cikin duhun jahilci da rashin wayewa? Amma ace yau ita ce a cikin babban birnin tarayya, a cikin unguwar da sai wane da wance suke zama a cikinta?

Shi daman Kamal irin matasan nan ne masu kwarjini da nutsuwar da in ba sabo kukayi sosai a tsakaninku ba basa iya sakin fuska da jiki suyi hira. Ita kuwa Zulai ko da taga take-taken Bintun sai tayi banza da ita, ta share ta, ta mayar da hankali kan Wan'uwanta suna hirar yaushe gamo. Aadeel da ke hannun Bintu ma da taga tana ta wani kara rirrike shi da kankameshi don kar ma ta amshe shi sai tayi kamar ma bata ganshi ba.

Tana zaune kusa da mijinta tana sunne kai cikin kunya sa'adda Hafiz ya fara tsokanarta kan irin ?iban da ta ?ara, a nutse Kamal Win ke tare mata suna dariya su ukun, kamar sun ma manta da Bintu a cikin falon.

Izuwa sa'adda suka yi mintuna talatin a cikin gidan, Bintu ta kai ma?ura wajen takura, so take yi su tafi, amma ko kallonta Hafiz baya yi balle tayi mishi alamar su tafi.

Daga ?arshe dai da taga hirar tasu ta ?i ?arewa sai ta fara saka hannu tana tsikarinsa. Ta yi na Waya, ta yi na biyu bai kalleta ko ya tanka ta ba, tana tsikarinsa na ukun kuwa ya daka mata wani gigitaccen tsawa ranshi a Sace.
"Wai ke miye matsalarki ne?"

A tsorace kuma a kunyace ta saukar da ?wayoyin idanunta ?asa, ta kasa ce mishi komai saboda kunyar wannan tsawar mai cike da tozarci da yayi mata a gaban Zulai da take gani babban ma?iyiyarta.

?asa-?asa yaja tsaki, sai da ?yar ya iya mayar da hankalinshi kan Kamal suka cigaba da tattaunawa kan halin da ?asarmu ta tsinci kanta a ciki. Zuciyarsa cike da tunanin murWaWWen hali irin na Bintu.
'Tun a mota ya faWa mata zai barta a gidan Zulai ita da Aadil su ?arasa yini, idan aka yi sallar magriba sai ya koma ya Wauko ta. A cikin mota bata ce masa za ta zauna ko baza ta zauna ba, shi kuma ganin ta yi shiru sai ya Wauka ta amince ne. Tunda suka shiga gidan, ganin take-takenta yasa shi tunanin baza ta zauna ba. Shi da kanshi a zuciyarsa ya rushe shawarar da ya yanke na barinta a gidan, amma yadda take ciccin magani tana Sata rai abu ne da bai taSa tsammani daga gare ta ba. Sai a yau ya ?ara tabbatarwa da gaske ne Bintu ba ta ?aunar ?an'uwansa, abinda Innaye da ?an'uwansa suka daWe suna yi mishi hannunka mai sanda yayi kamar ba ya gani.'

Ana kiran sallar Azahar, Hafiz da Kamal suka tashi don su je suyi alwala. Zumbur! Itama Bintu ta mi?e a tsammaninta tafiya za suyi, don hankalinta ba shi akan hirar da suke yi bata san sun mi?e da nufin yin sallah bane, ita dama ko gyalenta bata cire ba balle ayi tunanin ta ji daWin zama.

A mamakance Hafiz ya juya yana kallonta
"Wai ina kike shirin zuwa Bintu? Ki zauna muje muyi sallah mana!"

Ganin da Wan sassauci a fuskarsa ba kamar Wazu ba yasa ta yi kwaba-kwaba da fuska, a hankali ta ce
"Wallahi ba na jin daWi ne My dear, don Allah muje ka sauke ni a gida sai kayi sallar a can. Aadeel ma na ji jikinshi kamar da zazzaSi."

Tsananin haushi da takaici yasa Hafiz kasa magana, ?arin ba?in cikinsa ga Kamal da Zulai duk suna tsaye suna jinsu, ya sani tun Wazu sun fahimci hassada da ?yashi ke Wawainiya da Bintu, a yanzu kuwa daga yadda tayi magana ko ?aramin yaro zai fahimci karya ce kawai take shirgawa ba kunya ba tsoron Allah.

Ya sani idan basu tafi ba, Bintu baza ta taSa nutsuwa tayi yadda yake so a gidan Zulai ba, ta dinga kunyata shi kenan tana zubar mishi da mutunci. Karo na biyu da ya sake ?arewa Bintu kallo, zuciyarsa cike da tunanin irin maganganun su Anty Balira a kan Bintu, da irin abubuwan da take nunawa akan idanunshi tun shigarsu gidan Zulai ayau. Ayar tambayar da ya daWe da Wiga mata a take ta koma alamar motsin rai!!

Ya kasa daina mamaki, ashe da gasken-gaske Bintu ba ?aunar ?an uwanshi take yi ba? Da gaske ne abinda ake mishi shaguSe a kanta? A wannan karon lallai idanunshi sun washe.

"Uhmmm!"
Yayi ?wafa a fili. Ya ?ara tamke fuska idanunshi a kanta da salon bayar da umarni ya ce
"Bintu ki zauna inje inyi sallah in dawo."
Har yayi shiru sai kuma ya ?ara da cewa
"Na zaci idan da ?auna da soyayya gidan Zulai kamar gidan Mashku yake a gurinki?"
Ya jefa mata tambayar yana ?ara tsattsareta idanu.

Da saurin gaske ta taSe baki, ta ?ara da wani zazzare idanu kamar wacce ta ji yayi wani babban saSo a maganarsa.
"Gidan Mashku dai?"
Ta tambayeshi da mamaki sosai a muryarta. Kafin ya amsa ta ?ara da cewa da cewa
"Mashkura ?anwata fa? A'ah wallahi! Wannan misalin sam bai ko kusa hawa ba. Kada ma ka ?ara jona min wannan ka-re-ren! In banda ma ?addara me haWo gabas da yamma me zai haWa kifi da kaska?"

Tsananin mamaki da takaicin maganganunta yasa shi kasa ce mata komai, sai baki da ya ai hangame yana kallonta, Kafafunshi suka daskare guri Waya kamar an zare mishi laka.

Ita kuwa Zulai, dariya maganganun Bintu suka bata, a ?asaice, ta saki wata siririyar dariya kafin ta kalli Kamal, da taushin murya sosai ta ce
"Abban Imam kar ka makara sallah fa, lokacin yana ?o?arin wucewa"

Ta sake mayar da idanunta kan Hafiz da murmushi a fuskarta ta ce

38 / 53