Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   12 / 53

33K to 36K   out of 157.3K words

tambaye ta shi ma yana dariya.
"Kar ki ga laifina fa, kin san abinki da sabon shiga..."

"Ban ga laifinka ba My dear. Kawai dai tambayar ce ta saka ni dariya. Ciki ba ya fara sai ya kai wata huWu, ka ga ni yanzu ne nake cikin wata biyu. Amma kamar gobe ne za ka ji ya fara motsi, har ma ka taSa da hannayenka ka dinga jin babyn yana motsawa."

Daga irin yadda take mishi ?arin bayani, za'a gane cike take da farin ciki. Shi ma da yake saurarenta da farin ciki sosai a fuskarsa ya bata dukkan hankalinsa.

Hirar sabon cikin da take Wauke da shi, shi ya taka muhimmiyar rawa gurin rage mishi ?arfin damuwar da zuciyarsa take ciki dangane da ciwon Innaye. Sun daWe suna hira cikin farin ciki da annashuwa, kafin suka yi sallama da?yar bayan ya ga kiran mahaifinsa na shigo masa.

Bayan gama waya da Baffa sallah kawai yayi ya sake ficewa daga Wakin zuwa na Baffa. Daga can Waukarsa yayi kai tsaye suka koma asibiti.

Ko da suka shiga Wakin, barci suka tarar da ita tana yi. Aunty Balira kuma tana zaune akan dadduma tana lazumi, da alamun sallah ta idar.

"Ya jikin nata? Barcin take yi har yanzu? Ta farka kuwa?"
Baffa ya tambayi Aunty Balira fuskarsa da damuwa bayan sun zauna a gefen gadon da babu kowa akai.

"Jiki da sau?i Baffa. Eh ta farka, har ma ta rama sallolin da suke kanta. Kuma Alhamdulillahi babu galabaitannan kamar da safe, da alamun sau?i in Allah ya yarda."

"Ma sha Allah! Allah yasa sau?i ya Wore. Ni gobe da safe zanyi sammakon komawa gida, sai zuwa jibi kuma. Allah yasa dai yau kar ta sake kwana da wannan zazzafan zazzaSin irin na jiya, domin da alamun kwana da zazzaSin shi ke sa ta yini a galabaice."

"In sha Allah baza ta kwana da shi ba. Domin wani likita ya sake shigowa ya duba ta Wazu, a lokacin idanunta biyu. Ya tambayeta yadda take ji tayi mishi ?arin bayani. Ban dai san me ya ce ba don naga yayi ma ma'aikatan jinyan da suke biye dashi bayani da turanci, kuma yayi rubutu a jikin babban katin Innaye da yake ri?e a hannunsu."

Tana aje numfashin maganarta Hafiz ya karSe da cewa
"Ba matsala. Yanzu kafin in tafi zan je in samu likitan in ji halin da ake ciki. Ni ma gobe da safe zan koma Abuja, ana nema na a gurin aiki. Duk yadda ake ciki zan karSi lambar likitan mu dinga magana da shi. Jibi zan biyo jirgi in sake duba jikin nata."

"Ai ka ma yi zamanka gurin aiki kar ka samu matsala Hafizu. Tunda ga waya ai Allah ya sau?a?a al'amarin, duk yadda ake ciki ita Balira sai ta kira da dinga sanar da kai. Allah yayi albarka ya ba Rahina lafiya."

"Ameen Baffa."
Suka amsa gaba Waya.

Kamar yadda ya ce, kafin su bar asibitin sai da yaje gurin Likitan da ke kan aiki a daren ya binciki halin da ake ciki. Babu wata matsala mai girma, sai wasu ?arin allurai da zai siya saboda gwajen-gwajen da suka fita a ranar.

?arfe goma na dare suka bar asibiti zuwa hotel Win da suka yi masauki.


***** *****


Yayi mamaki sosai lokacin da Likita ya tabbatar mishi Innaye tana Wauke da ciwon Suger a jikinta. Jininta kuma ya hau sosai fiye da yadda ake tsammani. Typhoid da Maleria da Bintu ta ce shi ke damun Innaye shi ma akwai, amma kaWan, basu yi ?arfin da za'a haWa ta da manyan magungunan da za su dinga wujijjiga jininta ba.

Amma kasancewar shi mutum ne ba mai zurfafa damuwa ko bincike akan al'amura ba sai ya bar komai akan akasin na'urar gwaji aka samu a asibitin da Bintu take aiki. Ko a fuska bai canja mata ba, kuma har lokacin bai sanar da ita an kwantar da Innaye a asibiti ba. Tarairayarta yake yi sosai suna rainon cikin jikinta cikin nutsuwa da soyayya.

Duk da ya kwana uku rabonshi da asibitin, amma ya saki kuWi sosai ana yi ma Innaye duk abinda ya dace. Kuma cikin hukuncin Allah kwalliya tana biyan kuWin sabulu, sosai Innaye ke samun sau?i, zazzaSi kuwa tunda suka je asibitin bata ?ara kwana da shi ba.

Jikin Innaye yayi kyau sosai fiye da yadda ake zato. ?a?anta da ?an'uwa makusanta da suka je asibitin duba ta kowa da kyakkyawan labarin sau?in da take samu yake komawa gida. Ko da ta kwana huWu Baffa ya koma duba ta bakinsa kasa rufuwa yayi don murna.

Minti Waya biyu sai ya kalle ta da fara'a ya ce
"Alhamdulillah! Rahina sau?i ya samu, Allah ya ?ara lafiya."

Tun tana amsa mishi har ya koma ba ta kunya a gaban Wiyarsu ta fari Balira. Ita kuwa sai dariya take ma iyayen nata, daga ?arshe ma ficewa tayi daga Wakin ta basu guri domin su zanta a tsakaninsu.

Kwanan Innaye bakwai a asibiti aka rubuta musu sallama. Kuma a wannan ranar ne Hafiz ya bi jirgin ?arfe takwas na safe zuwa Kaduna, ?arfe sha Waya da rabi a asibitin tayi mishi.

Ba ?aramin murna da farin ciki yayi ba da ganin yadda Innaye ta warke garas! Kamar ba ita ce mare lafiya ba, har wani kumari tayi na musamman saboda kyakkyawan kulawan da take samu a asibitin. Domin a yanzu duk wata harka kuWi ke magana, yana daga can Abuja yasa aka bincika mishi gidan abinci na musamman a Kaduna safe, rana, yamma suke kai ma Innaye lafiyayyen abinci da ya kamata masu ciwon suger su dinga ci.

Ba Innaye da take mare lafiya ba, hatta Balira me zaman jinya ta yi kyau sosai, jikinta ya nuna hutu da cin abinci mai daWi da lafiya.

Bayan murnar ganin Innaye ficewa yayi zuwa Ofishin likita shi da Aunty Balira aka ?ara musu cikakken bayani na irin abincin da za ta kiyaye ci a matsayinta na mai ciwon suger da hawan jini. Da kalolin abincin da jikinta ya fi bu?ata a yanzu. Sannan ya karSi tulin magungunan da likita ya rubuta mata, saboda yadda ya saki kuWi shi ne ya biyo su canji ma. Amma saboda sanin ya kamata sai bai karSi ko sisi ba, ya ce ya bar ma marasa lafiyan da ba su da ?arfi.

Aunty Balira tana harhaWa kayayyakinsu ya fice zuwa kasuwa. Kayayyakin abincin da likita ya lissafa musu na masu ciwon suger ya siya da yawa, sannan ya samu shatar lafiyayyar mota ya biya direba, suka ?arasa asibiti aka Wauki Aunty Balira da Innaye suka kama hanya sai ?auyen Fa?o.

?arfe uku dai-dai suka isa, basu daWe ba suka juyo saboda a ranar yake son komawa Abuja. Albarka kam Hafiz ya sha ta daga bakin Iyaye, ?an'uwa, da jama'ar gari. WaWanda a baya suka dinga hum-hum-hum da zancen yadda ya dawo da Innaye cikin matsanancin ciwo daga gidanshi sai ga shi su ne kan gaba wajen saka mishi albarka.

Sun bar ?auyen bakinshi har kunne. Nutsuwa ta musamman yake ji a sassan jikinsa saboda yadda ya zama sanadiyyar faranta ma Iyaye da ?an'uwanshi rai, daman kullum abinda yake buri kenan.


***** ****** *****

"Wai me kike nufi Zulai?"
Ya tambayeta ransa a Sace.

?ara Waure fuska tayi tamau ta juyar da kanta can gefe guda. Uffan bata ce ba balle ma yasa ran za ta tanka mishi.

?wafa yayi mai ?arfi. Ya sake jan tsaki a karo na barkatai. Cikin matsanancin fushi da fusata ya ce
"Kin san Allah? A wannan karon za mu samu gagarumin matsala da ke. Wata uku kenan ina bin ki kina ja na a ?asa, a yanzu da bikinmu yazo gaf idan kin isa ki cigaba da wula?antani Allah ya tsinen. Zan nuna miki gaba nake da ke ta ko wane Sangare. In banda iskanci da rainin ajawali irin naki ke har kin isa..."

"Wai don Allah Mudan ya kake so inyi ne?"
Ta katse shi ita ma ranta a Sace.

"Auwoo!"
Ya faWa baki buWe yana kallonta da mamaki.
"Tambayata ma kike ya nake so kiyi? To bari in sake maimaita miki. Umarni nake baki a matsayina na wanda za ki aura nan da sati uku. Ki shirya gobe da yamma ki je ma Yahanasu matata barkar haihuwar da tayi..."

"Uhmmm! Mudan kenan."
Ta katse shi tun kafin ya aje numfashin maganarsa.
"Ka yi ka gama. Saboda Allah in banda ?i faWi irin naka ta ina aka taSa haka? Don kawai za ka aure ni haifata kayi? Ko kuwa don za ka zama mijina sai aka ce dole idan matarka ta haihu sai na je mata barka? Bayan haka ma duk ?auyen nan waye bai san irin mahaukacin kishin da Yaha take yi da ni ba?"

"Yaha kai tsaye?"
Ya faWa a mamakance. Kafin ta amsa ya cigaba da cewa
"Matar tawa ce kuma Uwargidanki kike kiran sunanta kai tsaye kamar wata sa'arki?"

Sai da ta murguWa baki dama da hauni sannan ta amsa da
"To ita Yahan uwata ce da bazan kira sunanta kai tsaye ba? Matar da tun kafin in shiga gidanta matsayin kishiya take aiko min da manya-manyan zagi da Alkaba'iran da ta tanadar min iri-iri idan na kuskura na aure ka shi ne don ta haihu kawai ni daWi miji zan je mata barka? Na rantse da Allah babu inda zan je. Sai dai duk abinda zai faru ya faru."

"Au! Haka kika ce?"

"?warai kuwa!"
Ta amsa kai tsaye ba tare da wani shakka ko tsoro ba.

"To shi kenan! Yayi kyau Zulai. ZaSi yanzu ya rage gare ki, ko dai ki shirya tsakanin yau, gobe, jibi ki je ma Yahanasu barka ko kuma in fasa aurenki. Zan aiko ?an'uwana sati na sama su karSi duk kayan auren da na aika da shi gidanku. In banda ?addara ma da ?uruciyana ke har kin isa in ce zan aure ki tsofai-tsofai da ke? Shekarunki sha takwas fa... Ki faWa min duk ?auyen nan wace ganWaWemiyar budurwa ce mai shekarunki zaune a gida bata yi aure ko kuma ta taSa aure ba? Kawai don kin samu za a rufa miki asiri sai ki dinga tsammani tsoronki ake ji? Daman tun kafin in sako kai a neman aurenki mutane da yawa sun faWa min baza kiyi min biyayya ba, saboda kin gama tsofewa a gida kina goga kafaWa da gyatumarki gani kike dai dai kike da kowa... To ni ba tsoronki nake yi ba. Kuma ina sake tabbatar miki in banda wasu dalilai babu abinda zai kawo ni neman auren tsohuwar budurwa kamar ki..."

Zafafan maganganun da ya saki baki yana yaSa mata masu kama da saukar ruwan dalma a kunnuwanta yasa bata san sa'adda tasa hannu biyu ta toshe kunne sannan ta ?walla wani mahaukacin ihu hankalinta a tashe. Hakan bai ishe ta ba, sai da ta ?ara da du?ewa a ?asa ta rushe da ?a??arfan kuka kamar wacce aka zo wa da albishir Win mutuwar iyayenta.

"Au! Sharri za kiyi min daga faWan gaskiya?"
Ya tambayeta hankalinsa a tashe da irin kukan da take ruwasa kamar ?aramar yarinya.
"To ni kin ga tafiyata. Ina zaune lafiya baza ki ?ulla min jakar tsaba ba in tafi kaji su tsattsaga."
Kamar wal?iya, Sat ya fice daga cikin zauren a gaggauce.

Baiyi second biyar da ficewa ba Innaye da abokiyar zamanta Mama Laminde da ?ananun matasan gidan Isiyaku da Labaran suka sawo kai a guje cikin zauren.

A hannayen matasan, manyan sanduna ne suka ri?o suna ta zare idanu kamar za su ci babu, domin duk a tsammaninsu wani mugun abun Mudan yake ?o?arin aikatawa ga Zulaikha ita kuma ta ?wala wannan ihun.

Ganinta ita kaWai du?e a ?asa tana rusa kuka sannan babu alamar wani mummunan abu ya faru da ita yasa suka yi turus! A tsaye guri Waya.
"Ina yake?"
Matasan suka haWa baki gurin tambayarta.

Ita kuwa Innaye cewa tayi
"Me ya faru Auta?"
Ta tambayeta hankalinta a tashe.
"Ina Mudan Win?"
Ta sake jefa mata tambayar tana jin wani faWuwar gaba da bata san dalili ba.
Ta sake jefa mata tambayar tana jin wani faWuwar gaba da bata san dalili ba.

Idanu kaca-kaca da hawaye ta Wago kanta da?yar tana kallon Innaye ta ce cikin kuka da Sare-Saren baki.
"Wai... wai... wai... cewa yayi bazai auri tsohuwar budurwa kamata ba..."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!"
Mama Laminde, Isiya, da Labaran suka haWa baki gurin jan salatin hankulansu a tashe.

Ita kuwa Innaye, DaSas! ta nemi guri ta zauna a cikin zauren tana jin wani jiri-jiri na neman kayar da ita daga zaunen da take.

Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai daga cikin gidan Umma Laraba ce ta sake fitowa bayan ta idar da sallar isha'i da take yi a gaggauce. Ko kafin ta bud'e baki ta tambayi abinda ke faruwa ta gansu haka sunyi jugum-jugum ga Zulai tana tsugune a k'asa tana rusa kuka sai ga Baffa ya sawo kai cikin zauren.

"Lafiya? Me yake faruwa anan? Waye ya mutu?"
Ya jera musu tambayoyin da saurin lokaci Waya fuskarsa na rikiWewa zuwa yanayin tashin hankali.

"Baffa. Wai Mudan ne ya ce ma Zulai bazai auri tsohuwar budurwa kamarta ba."
Isiya yayi ?arfin halin faWa ma Baffa yana sharce gumin da ya lulluSe goshinsa.

"Zancen banza kenan. Don wannan ?ar maganar shi ne kuka tsaya anan kamar anyi mutuwa? Ke kuma Rahina da girmanki maimakon kiyi ?o?arin kwantar da lamarin sai ki Suge da zama a ?asa kamar wata ?aramar yarinya? Ku tashi da Allah mu shiga cikin gida. Ai zancen aure ya wuce lokaci Waya ace an fasa kamar wani wasan yara. Kun binciki gaskiyar me ya faru ne? Duk ku kwantar da hankalinku. Babu abinda zai faru sai alheri in Allah ya yarda. Ku wuce mu shiga ciki na ce."
Ya ?arasa maganar da faWa-faWa.

Da sauri Zulaikha ta mi?e ta shige ciki da gudu tana cigaba da rusa kuka, domin har lokacin zafin maganganun da Mudan ya yayyaSa mata bai fara sassautuwa ba a zuciyarta.

Innaye kuwa saboda yadda maganar fashin auren ya buge ta baga-tatan sai da abokan zamanta suka kamata sannan ta iya mi?ewa tsaye, suka rankaya gaba Waya zuwa cikin gidan Baffah na biye da su a baya. Kowa a cikinsu da tunani mabanbanta a zuciyarsa.


Tun watannin baya da suka shuWe bayan gama jinyar da Innaye ta sha da?yar, kamar baza ta kai labari ba. Tana gama warkewa ta ba Baffa labarin duk yadda sukai da Zulaikha a gidan Hafizu, dangane da maganar samarin da suke son ta tana dakatar da su tun ma kafin zancen ya kawo kunnuwansu.

"Ikon Allah"
Ya faWa da mamaki a fuskarsa.
"To ko menene dalilinta na taka musu birki?"
Ya sake tambayar Innaye.

"Ai ba ta da wani dalili Baffansu. Akwai wani dalili ne da ya wuce wauta irin nata?"
Innaye ta amsa a tausashe.

Da Sacin rai a fuskarsa ya cigaba da magana bayan ta kai aya a maganganunta.
"Amma Zulai an yi shashashar yarinya. Yanzu ita daman ta san tana da samarin amma shi ne ko da wasa bata taSa turo ko mutum Waya guri na ba? Tana ganin yadda kullum hankalinmu da na jama'ar gari yake kanta saboda daWewar da tayi bata yi aure ba? In banda Allah yasa bana sha'awar yi ma ?a?ana auren dole na rantse da tuni na daWe da bayar da sadakar Zulai.."

"Ai yanzu dai duk wani jira da damuwar rashin mashinshini ya ?are in Allah ya yarda. Kayi ha?uri, shi aure lokaci ne. Babu mamaki yanzu ne lokacinta yazo. Yanzu dai ya kake ganin za a Sullo ma al'amarin?"

Shiru yayi yana jujjuya sunayen samarin da Zulai ta faWa ma Innaye sun taSa yi mata maganar suna son ta a zuciyarsa. Ganin duk su ukun babu wanda ba nagartacce ba yasa shi cewa
"Yanzu dai ina ga zan aika a tuntuSe su ne Waya bayan Waya. Tunda dukkansu sun fito ne daga nagartattun gidaje, kuma a fahimtata da Wan gajeren sanin da nayi musu yara ne masu kyawawan halaye. Ko ma dai yaya ne, maganar aure ta wuce wasa, duk wanda na samu tsayayyiyar maganar har yanzu yana son ta dole in ?ara faWaWa bincike domin gudun yin kitso da ?war?wata."

"Haka ne kam! To Allah ya zaSa mana abinda yafi alkhairi."
Innaye tayi addu'ar fuskarta da bayyanannen farin ciki.

Kamar yadda Baffa ya al?awarta ma Innaye. Tun a daren ranar ya naWa wakilai ya tura su gurin Khalilu, Waya daga cikin samarin da Zulaikha ta ambata ya taSa furta yana son ta.

Amma cikin hukuncin Allah bayan gama sauraren jawabin wakilan kai tsaye ya faWa musu a yanzu dai kam akwai wacce yake so. Har ma an kai kuWin na gani ina so gidansu yarinyar.
"Tsahare ce ?ar gidan Mal Isiya. Ayi ha?uri, sai dai inyi ma Zulai fatan alkhairi da addu'ar Allah ya haWa ta da wanda ya fi ni."

Haka wakilan Baffa suka bar gurin jikinsu a sanyaye. Su kuwa sauran samarin biyu Yusufa da Sani da farko duk sun amince har lokacin suna son ta. Amma daga baya ba tare da sanin me ya faru ba daga gidajensu aka aikewa Baffa da wakilai Wauke da sa?on yayi ha?uri. Zancen soyayya ma bazai yiwu ba balle har a kai ga maganar aure a tsakaninsu. Ba kuma tare da sun faWi wani ?wa??waran dalili da zai gamsar da Baffa dalilin fasawar tasu ba.

Ranshi a Sace ya shige cikin gida ya huce haushinshi akan Zulai ta hanyar yi mata wankin babban bargo sannan ya wuce turakarsa ya barta a tsakar gidan tana kuka.

Kasancewar zancen duniya da baya Suya balle kuma a ?auye irin Fa?o da ya kasance ?aramin gari sai ga zancen bibiyar samarin Zulai ya fasu. Shi Mudan tun kafin a aika mishi ya bayyanar da kanshi, a cewarsa ya daWe yana son ta. Amma ganin yadda ta ?are tsakaninta da abokinshi Khalilu yasa bai taSa yun?urin faWa mata ba.

Cikin ?an?anin lokaci

12 / 53