Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   41 / 53

120K to 123K   out of 157.3K words

Ga waya nan ku dinga magana, shi Win ma ban yarda ya wuce sau uku a rana ba. Ina fatan ka fahimce ni?"

"Na fahimta Mummy."
Ya amsa a ladabce.

Har ya kama hanya zai fita ta kira shi.
"Da alama dai kun daidaita da ?anwartaka. Zan tuntuSeta yau da dare saboda gudun yin kitso da ?war?wata. Idan ta tabbatar min da amincewarta kayi ?o?arin zuwa Fa?o cikin satinnan ka sanar da iyayenka halin da ake ciki, idan sun shirya ko zuwa watan gobe sai ka turo kawai ayi mai gaba Waya a wuce gurin. Nima nan zan sanar da iyayenta maza, tunda an fahimci juna kuma da sanayya ta ko wane Sangare to gaskiya babu wani amfanin Sata lokaci. Ko kana da wani shiri ne da kake bu?atar jinkiri...?"

"Ba ni da wani shiri Mummy."
Ya katse ta da matsanancin farin ciki bayyane a fuskarsa.
"Ai ni Wallahi ko gobe ne a shirye nake a Waura auren kawai a wuce gurin. Na gode Mummy. Allah ya ?ara girma."

"Amin ya rabb! To ina fatan Bintu dai ta sani?"
Ta sake jefa mishi tambayar, tare da ?ure shi da kallo tana ?o?arin karantar yanayinsa.

?an shiru yayi yana sosa ?eya, amma har lokacin fara'ar da ke fuskarsa bata Sace ba. Can kuma sai ya ce
"Gaskiya bata sani ba Mummy... Amma zan faWa mata. A daren nan ma in sha Allah zan sanar da ita. Gobe idan naje Fa?o sai in sanar da su Baffa."

"To madallah! Allah ya tabbatar mana da abinda yafi zama mafificin alkhairi. Ni dai don Allah ina ro?onka alfarma... A matsayinka na miji, kasan irin kalaman da za kayi amfani da su gurin faWa ma Bintu al'amarin. Tsakani da Allah kishiya babu daWi, amma tunda umarnin Allah S.W.T ne ba mu da yadda za muyi. Ka bi ta sannu a hankali, cikin tausasan lafuzza da ?an?an da kai. Sannan ka nusar da ita auro Karima ba shi ke nufin soyayyarta ya ragu a zuciyarka ba..."

A matsayinta na Babba, haka ta sake Sata wasu lokutan tana nusar da shi irin tausasan hanyoyin da zai bi wajen sanar ma Bintu zai auri Karima. Bai bar gidan Mummy ba sai ?arfe sha Waya na dare. Zuciyarsa cike taf da farin ciki.

Yana tu?i a hanyarsa ta komawa gida sai wa?e-wa?e yake saboda murna da yayi masa yawa. Ya ma rasa wa ya kamata ya kira ya fara yi ma wannan daddaWan albishir Win? Har ya Waga waya zai kira Zulai, sai ya ga dare yayi sosai. Sai kawai ya buge da kiran Ibrahim abokinsa Wan gidan Abba Lurwanu yayi mishi albishir.

Kamar yadda ya zata, Ibrahim Win yayi murna sosai da sosai. Don yana Waya daga cikin ?an adawar Bintu, masu nusar da shi tun a baya ire-iren kura-kuran da Bintun ke aikatawa amma sam idonsa ya rufe, ba ya ji ba ya gani saboda soyayya da ya rufe masa idanu.

"Shi kenan! Ka ga yanzu za'ayi balancing, idan su Aunty Balira sun zo za su samu gurin da za a tarbe su da haba-haba babu wula?anci, tozarci, ko kyara."

"?warai kuwa Ibbu"

Suna magana a waya Ibrahim Win yana ?ara bashi shawara kan kar ya kuskura ya haWa Bintu da Karima gida Waya har ya isa cikin gidanshi. A lokacin sha biyu saura ?an mintuna. Sallama yayi ma Ibrahim da cewar za su haWu bayan ya dawo Fa?o su ?arasa maganar ya katse wayarsa.

Yana shiga cikin falo ya tarar da Bintu zaune a kan kujera, idanunta ?yam akan ?ofar shiga cikin falon tana jiran ganin ta inda zai Sullo. SaSanin Wazu da ya barta sanye da kayan barci, yanzu ta ci kwalliya ne cikin wata ?ar Singilar rigar mama da wata yaloluwar Wan kamfai. Fuskarta da kwalliya raWau kamar wacce take shirin zuwa gurin perty.

Ko kusa baiyi mamakin ganinta ido biyu ba, don yana daga cikin Wabi'arta da ke faranta mishi rai duk inda ya je in dai yana garin Abuja to Bintu ba ta taSa kwanciya tayi barci sai ta jira ganin dawowarsa gidan lafiya.

Abu Waya da ya Wan bashi mamaki shi ne tattausan murmushin da ta fara watso mishi tun daga inda take zaune, sannan ta mi?e tsaye cikin yau?i da lan?wasa, ta fara tafiyar mage tana wani yayyarfe yatsu tana karkaWa mishi ?irji, lokaci guda tana haWawa da fari da idanu har ta ?arasa inda yake tsaye ?yam yana kallonta.

Iya duniya aka ce ya fi iya mota, kamar dai ba Bintu ne suka rabu tana kuka shi kuma ya fita da Sacin rai mai tsanani ba. Hannu ya buWe mata yana mayar mata da martanin murmushi, ita kuma a slow motion ta shige cikin ?irjinsa. A tare duk su biyun suka sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Basu tsaya a nan ba, kamar mayunwata haka suka kamo bakin juna suka fara tsotsa tamkar sun samu alawa. Tun daga nan bakin ?ofa, al'amura suka fara kankama, duk su biyun suka watsar da fushi da Sacin ran juna suka cigaba da ?o?arin faranta rayukansu.

Daga bisani dai can-cak Hafiz ya Wauki Bintu suka haura sama.


*******



Hafiz ya riga ya karanci Bintu kamar yunwar cikinsa, ya sani tunda tayi al?awarin yaye Aadil a washe garin ranar asabar, babu abinda zai sa ta fasa aniyarta.

Ya kuma sani tun da ta ambaci Ummanta ne za ta yaye shi, to tabbas gurin Ummanta za ta kai shi sai dai duk abinda zaiyi ya daWe baiyi ba.

Da wannan dalilin yasa shi gwada mata babba babba ne. Kuma wanda ya riga ta kwana dole ya riga ta tashi, duk sammakonta, shi a tafe ya kwana.

Suna idar da sallar asubah a masallaci, ko da ya koma gida ya tarar da ita har ta idar da sallah ta koma barci. Da wannan damar yayi amfani gurin aiwatar da shirinsa a gurguje, ko da ya shiga Wakin Aadil, ga manyan jakunkuna nan har guda uku ta sha?e da kayan sakawarshi da duk wasu abubuwan bu?atarsa. Don haka Wauka kawai yayi ya fice da su ya zuba a boot Win motarsa. ?akinsu ya koma inda Aadil Win ke kwance can gefe guda a gadonsa yana barci cikin nutsuwa. Bismillah yayi sannan yasa hannu a nutse ya Wago yaron ya rungume a ?irjinsa yana Wan jijjiga shi don kar ya farka.

SaWaf-saWaf ya fice daga Wakin don kar ya tashi Bintu. Kuma wani ikon Allah shi ne duk yadda ta kasance ba ta da nauyin barci har Hafiz ya samu nasarar ficewa daga gidan Bintu ko ?arar motarsa bata ji ba.

Sai da ya fara mi?ar hanya sosai sannan ya Waga wayarsa ya kira Innaye, bayan sun gaisa, ya sanar da ita ga shi nan ya kamo hanyar zuwa Fa?o, kuma tafe yake da Aadil za ta yaye shi a can.

"Ita Fatiman da hankalinta da nutsuwarta ta dam?a maka yaron da cewa ka kawo shi in yaye muku shi a nan?"
Tambayar farko da Innaye ta fara yi mishi kenan.

Har ya yi niyyar yanko ?arya ya faWa mata, sai kuma ya yanke shawarar gara ya faWa mata gaskiya kawai, saboda gudun abinda zai je ya zo.
"A'a Innaye! A matsayina na ubansa ni ne kawai nayi ra'ayin in kawo shi gurinki mahaifiyata ki yaye min shi..."

"Bazan karSe shi ba."
Ta katse shi cikin faWa tun kafin ya aje numfashin maganarsa. Ta cigaba da magana muryarta na rawa kamar za ta saka kuka.
"Yi sauri ka mayar mata da Wanta. Idan ba haka ba Wallahi ko ka zo da shi wahalar banza kawai za ka yi don sai ka koma mata da shi."

Ta ja numfashi sannan ta cigaba da cewa
"So kake in karSi Wan ta ta zo ta tozarta ni a cikin jama'a sannan ta Wauki Wanta? Ita da kanta Bintun da take babba yaushe har ta iya sakin jiki tayi rayuwa a cikinmu ?auyawa balle har tayi kuskuren bari Wanta ?wallin ?wal ya rayu da mu? Dama yaya lafiyar giwa balle ta yi hauka? Mayar mata da Wanta, in da rabon mu rayu da ?a?an binni zan rayu da na Zulai, na san Kamalu ko kyauta na ce ina so ya bani Wansa bazai hana ni ba..."

Tsananin zafi da raWaWin da maganganun Innaye suka yi masa yasa bai san sa'adda ya katse wayarsa ba. Gangarawa gefen titi yayi ya faka motar. Ya daWe cikin shiru, zuciyarsa ba abinda take yi sai tafarfasa. Idanuwannsa ciccike da hawaye saboda irin ba?a?en maganganun da Innaye ta yayyaSa masa.

Lokaci bayan lokaci yana waigawa kujerar baya ya kalli Aadil da yake kwance a Wan gadonsa na cikin mota, har wannan lokacin barcinsa yake yi hankalinshi kwance.

'Yanzu shi kenan Bintu ta gama cin galaba a kanshi? A matsayinshi na miji bai da iko da gida da iyalinshi sai yadda Bintu ta tsara ko ba ya so haka za ayi? Yanzu yadda ya Wauko Aadil haka zai mayar mata da shi yana ji yana gani sai dai ta kai shi gurin Ummanta?"

Bai taSa shiga matsananciyar da-na sanin biye ma Bintu da yai ta yi irinna yau ba. Ba ma da na sanin biye mata ba, a yau har da na sanin aurenta ya yi. Wane irin zamantakewa ne ace ?an'uwa da iyayen miji ba su da ikon zuwa gidanshi su sakata su wala yadda suke so?

"Ya hayyu ya ?ayyum! Bi rahmatika astageethu, aslihlee sha'anee kullah, wala takilnee Warfata ayn"
Ya faWa a fili idanunsa a lumshe, zuciyarsa cike da sakankancewa da neman agaji.

Ya daWe sosai yana maimaita addu'ar, har zuwa wani lokaci sannan ya buWe idanunsa da suka canja launi zuwa jajaye. Amma a maimakon ya cigaba da tafiya da motar hanyar da zai fice daga Abuja, revers yayi, ya mi?e hanyar komawa zuwa cikin gari, zuciyarsa babu daWi ko kaWan.



****** ******



A karo na saba'in da biyu ta Waga waya ta danna kiran lambar Hafiz, amma wani abin takaici shi ne da kiran ya fara alamun zaiyi ringing, sai ya katse, sai su rubuta mata User busy. Bisa ga dukkan alamu Hafiz dai kulle lambarta yayi don kar ta same shi a waya.

Haushi da ba?in ciki yasa tayi cilli da wayar jikin bangon gado, a karo na biyar ta sake Wora hannu bibiyu akai ta fashe da wani ?a??arfan kuka kamar wacce aka isarwa da mummunan labarin mutuwar iyayenta biyu ta hanyar hatsarin mota.

Da madungure ta sauka daga kan gadon tana rusa kuka, takai gwauro ta kai mari a tsakiyar Wakin. Duk tunaninta shi ne ya ?u?e ne akan ina Hafiz yake haramar kai mata Wanta Aadil?

Tun bayan da ta farka daga nannauyan barcin da ya kwasheta da misalin ?arfe takwas da minti ashirin na safe, ta shige bayi tayi brush. Ko da wasa hankalinta bai kai kan gadon Aadil ba balle har ta fahimci ba ya kwance a ciki sai bayan da ta fita zuwa ?aramin kicin Winta na sama, ta haWo tea ta koma Wakin tana kurSa a hankali saboda wani masifaffen yunwa da take ji kamar anyi mata yasa a cikinta.

Tunda ta le?a harabar tsakar gidan taga babu motar Hafiz ta san ya wuce Fa?o kamar yadda ya saba duk ranar asabar. In dai ba ita ta Waga Aadil daga kwance ba tayi mishi wanka yana kai misalin ?arfe goma zuwa goma da rabi na safe yana barci. Shi yasa hankalinta bai kai kan ba ya cikin gadonsa ba.

Sai da ta gama shan tea, ta mayar da kofin kicin, ta koma cikin Wakin ta shige banWaki ta haWa ma yaron ruwan wanka. Tana yaye net Win saman gadonshi da niyyar Waukan yaron sai taga wayam. Da farko ta zaci idanunta ne ke mata gizo, don haka sai ta Wan mutsittsika idanunta don su ?ara washewa. A lokacin ne fa ta tabbatar ba ya nan. Ai a sittin ta fice zuwa Wakinta inda ta haWa kayayyakin Aadil. Suma suka ce Wauke mu inda kika ajiye.

Da yake ta san yadda suka rabu da Hafiz Win a daren jiya, bata tsaya wani raba Waya biyu ba ta san Hafiz ne ya shammaceta ya Wauke mata yaro.
"Kan ubancan kayyasa. Ni Hafiz zai shammata? Na rantse da girman Allah yadda ka Wauke shi ka tafi da shi kai da ?afafunka za ka dawo da shi, zan ga ?ar iskar tsohuwar da take da ?warin gwuiwar ri?e min Wa a ?auyen ?ayau idan ita ce tayi min na?uda ta haifo min shi."
Tayi maganganun cikin masifa da bala'i, bakinta har tartsatsin miyau yake yi don tashin hankali.

Da farko har za ta bari ya isa sannan ya dawo mata da Wanta, domin tana da tabbacin in dai Innaye da ?a?anta ba giyar wake suke sha ba baza su ri?e mata Wa a ?auye ba. Can kuma sai taga ai idan ta bari Hafiz ya tafi da Aadil ya wuni mata da Wa a ?auye ba tare da amincewar ita uwar Wan ba ai ya gama cutar da ita, cutarwa ta ?arshen-?arshe.

Don haka afujajan ta koma Wakinsa inda tayi barci ta Wauki wayarta akan durowar bedside ta lalubo lambarsa ta fara danna mishi kira. Zuciyarta cike da alwashi iri-iri da barazana da rantse-rantsen da za tayi mishi kan idan bai dawo mata da yaronta yanzu-yanzu ba za su samu mummunar saSani, irin saSani da balbalin bala'in da bai taSa tunanin za su samu ba a tarihin rayuwar aurensu.

Sau uku kacal t????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
a samu nasarar kiran ya shiga bai Wauka ba, tun daga waWannan ukun, duk sadda kiran yayi kamar zai shiga sai a saka mata user busy.

A cikin da?i?u sittin da suka biyo baya, ta yi kuka, ta yi kuka, irin matsanancin kukannan da tunda uwarta ta haifeta bata taSa yin irinshi ba. Domin a wannan lokacin zuciyarta ta fara tunanin idan su Baffa suka ri?e Aadil a can Fa?o kamar yadda Hafiz yake so ya za ta yi?

Cikin kuka da majina ta fara rantse-rantse tana shan alwashi...
"Na rantse da girman Allah... ko sun ri?e shi gobennan zan yi sammakon tafiya in karSo Wana, in sama da ?asa za su haWe Wallahi Tallahi sai sun ba ni yarona. Idan kuwa sun ?i ko da ?an sanda da sojoji ne sai na je na amso yaro na, duk abinda zai faru ya daWe bai faru ba..."

Kamar a mafarki sai taji Mai gadi yana buWe get Win gidan, da saurin gaske ta matsa jikin window, zuciyarta cike da fatan Hafiz ne ya canja ?udurinsa ya dawo mata da Wanta, duk da wani sashe na zuciyarta na faWa mata abu ne mare yiwuwa Hafiz ya fasa ?udurinsa a sau?a?e.

?uri tayi da idanunta jikin motar da take shigowa sannu a hankali har ta ?arasa shigowa tsakar gidan. Nannauyar ajiyar zuciya taja ta sauke, motar Aminiyarta Raudha ce.

Tana nan tsaye a jikin window har Raudha ta gama daidaita fakin Win motar ta kashe ta fita. Hakan yasa ta saki labulen windon ta fice daga Wakin da sassarfa, zuciyarta na ?ara Wugunzuma.

Kamar an buWe famfo sabbin hawaye suka sake Salle mata, haka ta sauka ?asa ta tari Raudha a falo fuskarta kaca-kaca da hawaye, ga idanunta da suka kumbura suka canja launi saboda tsabar daWewa tana rusa kuka.

"Raudha... Hafiz ya kashe ni..."
Kalaman da ta fara faWa ma Raudha kenan cikin matsanancin kuka da rawar baki, bayan ta ru?un?umeta a tsakiyar falon.

Ita kuwa Raudha ga tsammaninta Bintu ta gano Hafiz yana soyayya da Karima ne. Daman kuma takanas-ta kano abinda ya kawo ta gidan kenan ta faWa mata. Ashe kaya ne ya tsinke a gindin kaba. Don haka sai cewa tayi
"Uhmmm! KaWan daga cikin halin maza kenan! Ai da can da muke faWa miki ba cewa kika yi Hafiz ya sha ban-ban da sauran maza ba? Yanzu wa gari ya waya Bintu?"

Bintu dai ba baka sai kunne, illa iyaka ma sai ?ara ?arfin kukanta take yi tana rerawa kamar tashin jiniyar motar ?an sanda.

Da fuska mai cike da tausayi Raudha ta ri?e kafaWar Bintu taja ta suka zauna a kujera mazaunin mutum uku, a tausashe ta ce
"Kiyi ha?uri Bintu! Na san abin da ciwo to amma ya kika iya da abinda ya gagari wuta? Kukan nan da kike ta rusawa sam ba mafita ba ce. Idan ma za kiyi shiru mu nemi mafita gara kiyi shiru. Yanzu ina shi Hafiz Win?"

"Ya tafi da shi fa Raudha... Ya tafi da shi... Ni babban damuwata idan Aadil ya farka bai ganni ba kuma bai ga Umma ko Mashku ba wane irin firgita da tashin hankali zai shiga? Na rantse da girman Allah akan Waukar min Wa da Hafiz yayi ya tafi da shi wannan tsinannen ?auyen ba tare da izinina ba sai munyi gagarumin tashin hankali da shi."

Galala Raudha tayi da baki tana kallon Bintu ba tare da ta gane maganganun da take yi ba. Ganin dai ta kasa raba Wayan biyu yasa ta cewa
"A'a! Wai tsaya Bintu, akan me kike magana ne?"

Ba tare da damuwa ko tuhumar irin maganganun da ita Raudha ta fara yi ba Bintu ta kora mata bayanin duk halin da ake ciki na tafiya da Aadil yaye gurin Innaye.

"Kam bala'i!! Amma gaskiya Hafiz ya gama raina ki Bintu. Ko da yake ni banga laifin Hafiz ba sai na ki, tun farko ke ce kika ba shi yarda Wari bisa Wari shi yasa har yaga wallenki ya fara gara ki yana wula?anta ki yadda yake so."
Raudha ta faWa cikin tsantsar takaici da ba?in ciki. Kafin Bintu ta ce wani abu ta cigaba da cewa
"Saboda in dai ba burin ya wula?antaki ya tozarta ki ba ta ya za'ayi ya Wauki kyakkyawan yaro ajebo irin Aadil kuma Wan shekara Waya kacal ya kaishi wannan ?azantaccen ?auyen na su? Wannan burin kashe miki Wa kawai yake da shi. Idan kuwa kika bari kuka cigaba da tafiya a haka! Na rantse da Allah sunanki sorry...!"

Maganganun Raudha babu abinda suke ma Bintu illa ?ara tunzurata. Shi yasa hawaye ya ?i tsayawa a idanunta, ga wani fitinannen ciwon kai da ya addabeta amma don tsananin ba?in ciki da takaici ta kasa daina kuka.

Sai

41 / 53