Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   47 / 53

138K to 141K   out of 157.3K words

hoton free wedding pic na Hafiz da Amaryarsa Kareema ba.

Zuciyarta ?una, raWaWi, zafi, azaba take yi mata, kamar za ta faso ?irjinta ta fito don tsananin ba?in ciki da takaici.
"Yanzu shi kenan? Tana ji tana gani za ta sadaukar da mijin da ta gama shan wahalar Wawainiyarsa ga wata banza can da bata san darajarsa ba?"

?arin ba?in cikinta shi ne, Hafiz Win ne da kanshi ya saka kyawawan hotunan a status Win shi na whatsapp.
"Yanzu shi kenan har Hafiz ya manta da babinta a rayuwarsa?"

Yatsa ta saka, ta ?ara zumin Win hoton fuskarsa tana ?ara kallon wani masifaffen kyau da yayi. Dama can Hafiz mai kyau ne, kyawunsa na Waya daga cikin abinda yasa take mutuwar son Hafiz. Domin idan ba faWa aka yi ba, irin kyawun Hafiz da gayunsa ko rantsuwa aka yi babu kaffara za a ce bai haWa jini na kusa ko na nesa da mutanen ?auye ba.



*Assalamu alaikum*


Ina yininku? Akwai set Waya na maganin mata wanda wani malami ya haWa bisa amana. Amma don girman Allah ?ar'uwa ki ji tsoron Allah idan kin san ba kya fama da matsala tsakaninki da mijinki kar ki siya. Saboda maganin ya taSo wani Sangare na mallaka, wata ?ar'uwa ce da mijinta ke neman mata aka haWa ma maganin. To kuma cikin hukuncin Allah sai auren ya mutu kafin isowar maganin, kun ji dalilin da yasa na tallata maganin. KuWin maganin 10k ne. Idan baki shirya ba don Allah kar ki taSo ni ta pc.

Maganin rashin haihuwa.
Cutar sanyi na infection ko wani iri.
Maganin cancer ko wane iri.
Maganin wankin nono ga masu jego.
Maganin sanyi na masu jego.
Da sauran cututtuka in sha Allah muna da ingantattun magunguna na gargajiya akan farashi mai sau?i=?O?
07039080978, 09077591726

"Yanzu haka za ta zauna ta naWe hannu a ?irji ta zura ido tana ji tana gani wata mace can da ba ita ba ta mallaki Hafiz bayan ita ta gama shan wahala da shi?"
Ta sake tambayar kanta a fili. Lokaci Waya jikinta ya Wauki rawa kamar ana kaWa mata ganga.
Umarnin zuciyarta jikinta ya bi, ba don ranta yana so ba ta talubo lambar Hafiz ta danna mishi kira. Cikin ?an?anin lokaci wayar ta fara ringing daga can Sangaren, ?arar da yake bugawa kamar da sautin bugun zuciyarta.

Daga can Sangaren Hafiz, barci yake yi hankalinsa kwance. Sun shafe fiye da mintuna talatin suna hira da Kareema a waya tana ta zuba mishi shagwaSa da ?ananun koke-koke. wacce rashin ganinta da baya yi kwanaki biyar kenan wai an Soye ta ana mata gyaran jiki, ko ya je sai dai ya gama hira da Zulai da Hajja yasa shi rage zuwa gidan, sai dai bini-bini kaWan zai kira ta, ko kuma ita ta kira shi tayi ta ?ara rikita shi da zafafan kalamai na soyayya.

Yana cikin nutsuwa ?warai, irin nutsuwar nan da shi da kanshi idan aka titsiye shi bazai iya tuna lokacin da yake cikin makamanciyar wannan nutsuwar ba. Bintu, da duk wani abu da ya shafeta ya tattara shi ya ajiye gefe Waya.

Daman a gyaran gidan da yayi duk wasu abubuwa nata da suke cikin Wakinsa ya tattara ya mayar mata da su Wakinta. Idan ya kwanta, barcinsa yake kwasa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ko mafarki zaiyi na Karima yake yi, saboda ita ce a cikin zuciyarsa.

Gaf da kiran zai tsinke, ya jiyo vibration Win wayar kamar a mafarki. Da?yar ya iya mi?a hannunsa ya lalubo wayar, ba tare da ya duba mai kiran ba kawai ya Wauka ya kara a kunne.

Hafiz yana Waya daga cikin mutanen da suke da Wabi'ar idan suka farka daga barci mai nauyi suna Waukar wasu sakanni kafin suyi magana. Don haka ko da ya Wauki wayar, shiru yayi yana Wan mayar da numfashi a hankali.

Shesshe?ar kuka da ya fara jiyowa yana tashi ?asa-?asa ta cikin wayar yasa shi ?arasa wartsakewa. Ya Wan buWe idanu kaWan, sai kuma ya ciro wayar daga kunnensa ya kalli fuskarta. Ganin Bintu ce akan layi yasa fuskarsa faWaWa da yanayin mamaki, mamaki na sosai, ba kaWan ba fa. Abu ne da anan kurkursa bai taSa tsammanin ganinsa akan wayarsa ba. Da wannan dalilin yasa dole yayi mamaki.

Har ya Waga wayar zai katse, sai kuma wata zuciyar ta bashi shawarar ya Wauka. Bai san me ke tafe da ita ba, kuma duk da sun rabu, ko don darajar Wa da yake tsakaninsu ai an rabu ba'a rabu bane.

Da wannan dalilin yasa shi mayar da wayar a kunnensa, haWe da yin Wan gyaran murya ?asa-?asa. Gyaran muryar da ya tabbatar ma da Bintu yana saurarenta.

"Hafiz... Yanzu shi kenan Hafiz?"
Tayi maganar cikin rawar murya. Bata jira ya amsa ba ta cigaba da cewa
"Saboda Allah ka yi min adalci kenan? Bayan duk rashin adalcin da kayi min ka rasa sakayyar da za kayi min sai na auren Kareema? Haba Hafeez! Kareema fa? ?ar gidan Mummy Saudah, wannan local Win yarinyar... Bayan tozarcin auren kuma ka rasa sakayyar da za kayi min sai ta saki... Ina duk al?awurran da kai min Hafeez?"
Ta ?arasa maganar haWe da fashewa da wani ?a??arfan kuka da yake tahowa tun daga ?ar?ashin zuciyarta.

A Sangaren Hafeez kuwa da sauri ya cire wayar a kunnensa, saboda yadda sautin kukan ya dira a kunnensa da ?arfi... Kamar tana barazanar fasa masa dodon kunne.

Wani abin mamaki shi ne duk irin yadda ta jero maganganun da salon a tausaya mata, take kuma rusa kuka kamar ?aramar yarinya, irin kukan da ya daWe a fili ko a waya bai ji Bintu ta yi irinsa ba. Ko kaWan maganganunta basu taSa mishi zuciya ba, sai ma wani Wan ?aramin murmushi da ya suSuce a fuskarsa, ya daWe yana sakin lallausan murmushi kamar tana kallonsa, yana jin saukar kukanta a kunnensa kamar busar sarewa.

"Bintu..."
Ya kira sunanta a hankali, bayan ya ji ba ta da niyyar tsagaitawa a kukan da take yi.
"Ki saurara da kukan nan muyi magana, idan ba haka ba Wallahi zan kashe wayata."
Yayi maganar cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara.

Ta sani tsaf zai aikata abinda ya faWa, musamman a yanzu da ?arfi da yaji ma?iyanta suka ci galabar cusa mishi tsanarta a zuciya. Don haka a sannu-sannu ta fara rage kukan har ta daina gaba Waya.

Nannauyar ajiyar zuciya ya ja ya sauke a hankali, sannan ya cigaba da magana da wata irin murya mai bayyana rashin damuwa ko mis?ala zarratin da halin da take ciki.
"Kin ga barci nake yi fa... kiran wayarki ne ya tashe ni. Don Allah idan ba ki da abin cewa mai muhimmanci ki ?yale ni in huta Bintu."

Da?yar ta iya ri?e wayar saboda tsananin kaWuwar da tayi sakamakon jin irin kalaman da ke fita a bakinsa. Har ga Allah ta yi tsammanin kalaman rarrashi da ban hakuri ne za ta ji suna fita daga bakinsa. Wannan wane irin mummunan al'amari ne haka ya dabaibaye kyakkyawar zamantakewarsu? Gaskiya duk wanda yayi wani ?ulli don wula?anta tubalin zamantakewarsu baza ta taSa yafe mishi ba...

"Kina ji na?"
Hafeez ya sake faWa.
"Ina tunanin sau?a?a miki nayi ta hanyar yi miki abinda kike so Bintu. Bazai taSa yiwuwa mu cigaba da tafiya a haka ba, ke ma kin sani.
Iyaye da ?an'uwana sun fiye min kowa da komai a wannan duniya. Ke kuma babu wanda kika tsana sama da su, don haka na sama miki sau?i ta hanyar yanke ala?arki da mutanen da kika fi tsana a rayuwarki.

Don Allah Bintu ki manta da ni, kamar yadda nima na daWe da mantawa da ke. Na kama hanyar nemo wacce rayuwarta za tayi daidai da rayuwata ta ba?auye da rayuwar ?an'uwana ?auyawa. Don haka ina miki fatan alkhairi, da addu'ar dacewa da miji muradin rayuwarki, wanda ba shi da wata ala?a ta kusa ko ta nesa da ?auyawa.

Idan da abinda ya rage tsakanina da ke a yanzu, bai wuce Wa Waya da Allah ya bamu ba. Albishir Waya da zanyi miki shi ne ni bazan raba ki da Wanki ba, lokaci bayan lokaci zan dinga kawo shi gurinki kina ganin lafiyarshi. Amma fa ki sani, rayuwar ?auyennan da kika tsana tabbas sai Aadil ya ratso ta wannan hanyar kamar yadda ni mahaifinsa na ratsa har nazo kan wannan matakin da nake ciki.

Sannan ina sake gargaWinki ki daina kira na a waya idan ba da wani ?wa??waran dalili ba. Kayanki na gidannan tuni an tattara miki su an kulle a Wakinki, da wasu daga cikin Wakunan BQ, duk sadda kika shirya ko ta text message ki sanar da ni za ki turo ?an'uwanki su kwashe miki kaya.

Amaryata tana da matsanancin kishi, ko kaWan bazan bari ki zama sanadiyyar da ba?in ciki zai ratso ta tsakiyar farin cikin matata abin son zuciyata ba..."

?it! Bintu ta katse wayar daga Sangarenta, saboda yadda kalamansa suke babbakata kamar ana zuba mata tafasasshen ruwan dalma, tun daga tsakiyar kanta har zuwa diga-diginta. Wasu irin zafafan numfarfashi take ja, kamar mai cutar numfashi. Da farko a zaune take a tsakiyar gado, ba tare da sanin yadda aka yi ba sai gata a tsakiyar Wakin tana safa da marwa.

Ashe wani tashin hankalin ya fi gaban ayi mishi kuka? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Gaba Waya kukan Waukewa yayi daga idanunta, sau uku tana Waga hannu ta Wora akai da nufin ta ?walla wani matsiyacin ihu, sai kuma ta ji muryarta ya ?i fitowa sam! kamar wacce aka sha?ewa ma?ogwaro.

Daga yadda take jan numfashi da ?yar, tana haWawa da shishitu da baki, sai take jin kamar iskar Wakin ne yake neman yi mata kaWan. Kamar ma dai idan ta cigaba da zama a cikin Wakin lallai ajali zai risketa a gaggauce. Ga shi yau ita kaWai ce a Wakin, Mashkura tana can gidan Yaya Abubakar, balle idan ta yanke jiki ta faWi Mashkura ta kawo mata Wauki.

Ba tare da duba kayan barcin da ke jikinta ba ta kama hanyar fita daga Wakin. Tana tafe tana tangaWi kamar wacce ta sha kayan maye. Ba tare da duba tsalawar dare ba, kai tsaye Sangaren mahaifinta ta nufa.

Cikin hukuncin Allah tana shiga falon Daddynta ta tarar da shi zaune a kan dadduma can gefe guda, da alamun sallah ya idar, domin ga Al?ur'ani nan ajiye a gefensa, hannunsa kuma ri?e da casbaha yana ja.

?arar buWe ?ofar da ya ji ne yasa shi waigawa a mamakance, domin ya san babu mai shigowa Wakinsa falonsa a irin wannan lokaci sai Hajiya. Ita kuma tun Wazu ta shigo, ya ma barta a cikin Waki tana barci. Ganin Bintu ce yasa motsin tasbihi da bakinsa ke yi tsagaitawa, ya ?ura mata idanu yana kallon yadda ta ?ara yin zuru-zuru a cikin kwanakin, kamar wacce ta Wauki wasu watanni masu yawa tana jinya.

Bai gushe yana kallonta ba har zuwa sadda ta ?arasa inda yake ta zube a gabansa.
"Na tuba... Na bi Allah na bi ka Daddy... Ka taimaka min... Wallahi ina matsanancin son Hafeez... Bazan iya rayuwa babu shi ba..."
Tana zuwa nan a maganganunta ta fashe da wani ?a??arfan kuka...



******* *******



Tuwon girma aka ce miyarsa nama. Tun ana gobe Waurin auren Hafiz da Kareema, su Baffa da sauran tawagar maza ?an Waurin aure da WaiWaikun mata ?an biko suka dira a babban birnin tarayya Abuja.

Biki ne da duk da an saka kwanakin a ?urarren lokaci amma fa an shirya ta ko wane Sangare. Kuma ?arin abin ban sha'awar shi ne ta ko wane Sangare suna murna da haba-haba da al'amarin. Ga wanda bai sani ba ma sai yayi tsammanin wannan auren shi ne na farko da Hafiz zaiyi a rayuwarsa ta duniya.

Taron biki ne na gani a faWa aka shirya a gidan Abba Lurwanu, gidan Mummy Saudah, sai dai babban gangamin kuma yana can Fa?o gidan Innaye. saboda Hafiz ya sha alwashin bayan an gama Waura aure, anyi dinner a ranar za'a kai Amarya gidan Abba Lurwanu ta kwana, washe gari da sassafe za'a wuce da ita Fa?o. A ta?aice dai, baza'a kai Amarya gidanta ba sai ta kwana ta hantse a Wakin Innaye, saSanin Bintu da iyakarta gidan Abba Lurwanu aka wuce da ita gidan Hafiz.

Kamar wancen auren na Bintu, wannan karon ma Abba Lurwanu ne ya zama waliyyin Ango, kuma shi ya biya mishi sadaki. Yana zaune a tsakiyar su Baffa, da mahaifin Bintu, wanda ya ke ta dariyar ya?e, daga can ciki kuwa yana jin zafin yadda Bintu tayi wasa-rere da damarta har tayi saken da waWannan nagartattun mutane masu halin girma da kawaici suke neman kuSuce mata a matsayin surukai.

Kamar Baffa bai samu labarin rashin mutuncin da Bintu taje har tsakiyar Wakin Innaye ta shimfiWa ba. Haka ya saki fuska sosai suka gaisa da mahaifin Bintu, kuma wani ?arin halin girman shi ne duk inda Alh Lurwanu ya ja shi, in dai mahaifin Bintu na gurin kai tsaye yake dam?o hannunsa su gabatar da al'amarin su uku. Wanda bai sani ba sai yayi tsammanin ?an'uwanta ne mai ?arfi

Misalin ?arfe uku na rana, Baffa da ?an'uwansa maza da suka halarci Waurin aure sun gama shirin komawa Fa?o. Daga Sangaren Abba Lurwanu, mahaifin Bintu, Hafeez an haWa ma su Baffa sha tara ta arziki. Domin har wannan lokacin mahaifin Bintu na tare da su, yana ta dama-dama da Baffa yana ?ara karantar kirkinsa.

Har sun yi sallama, suna tsaye a jikin motar da Baffa zai shiga, Daddyn Bintu yayi suSul da baka wajen furta maganar da tun Wazu take mishi ?ai?ayi a ma?oshi.
"Mal Aminu, ina dai sake baka ha?uri game da kuskuren da Bintu tayi, don Allah idan ka je gida aba Innaye da sauran Yayyen Hafizu da duk waWanda Bintu ta Sata ma ha?uri. Ba goyon bayanta nake yi ba, amma ina tabbatar maka a zaman gidan da Bintu take yi ta shiga taitayinta, ayi ha?uri... Don Allah a taushi Hafizu, bayan kwana biyu yayi ha?uri ya maida ita Wakinta kafin ta gama iddah!"

Da saurin gaske Baffa ya saki hannun ?ofar da yake ri?e da shi, jin kalaman da ke fita daga bakin Daddyn Bintu. Domin ko da wasa Hafizu bai faWa mishi ya saki Bintu ba, duk da a wancan ranar bayan ya koma gida Rahina da kanta ta faWa mishi duk irin tijarar da Bintu taje tayi musu.
"Maganar me kake yi Alhaji? Ban... fahimta ba. Kar dai ka ce min Hafizu ya saki matarsa ba tare da sani na ko na mahaifiyarshi ba?"

Lokaci Waya aka fara kallon-kallo tsakanin Daddyn Bintu da Abba Lurwanu. Da?yar Daddy ya iya buWe baki ya ce
"Tun wancan ranar da taje Fa?o tayi ma iyalinka rashin kyautawa, da kuma washe gari da taje nan gidan ?anwarsa tayi mata rashin mutunci. Hafizu yaje har gida ya faWa min duk abinda ya faru, sannan ya bani takardarta na saki Waya..."

"Assha! Assha!! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!! Amma kuwa Hafizu baiy????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  i aiki da hankali ba... Wa ya faWa mishi cikin sau?i ake sakin matar da aka fara tara zuri'a da ita? Ya sani, da ya faWa mana zai aikata ni ko mahaifiyarshi babu wanda zai lamunci haka. Ina zuwa, bari in kira shi."
Yana wannan maganar ne yana latsa wayarsa da nufin lalubo lambar Hafiz.

"Abu dai duk baiyi daWi ba Baffa. Ni kaina bai faWa min ba sai bayan da komai ya gama faruwa. Kuma tunanin kun sani tunda ance rashin kyautawar ku tayi ma shi yasa na bari sai bayan an kwaranye hidimar bikinnan sai in kira in baku ha?uri in ro?i alfarmar a mayar da ita Wakinta. Muje daga ciki sai ka kira shi Baffa."

Ko da suka koma cikin falon Abba Lurwanu, kira na farko da aka yi ma Hafiz bai Waga ba, sai a kira na biyu ya Wauka, da alamun yana cikin abokansa ne, don ga muryarsa nan ana ji suna dararraku.

"Assalamu alaikum! Baffa ya hany..."

"Hafizu ka keSe yanzunnan daga cikin mutanennan. Ina son yin magana da kai me muhimmanci."
Abba ya bashi umarni.

"To Baffa!"
Ya amsa a ladabce, sannan ya katse kiran. Mintuna biyu tsakani ya sake kiran lambar Baffan, yana Wauka ya faWa mishi ya keSe.

Da faWa sosai a muryar Baffa yake magana.
"Hafizu? Ina ganin ka yi hankali tunda ka fara aje yara ashe har yanzu da sauran rina a kaba? Me yasa ka saki matarka uwar ?a?anka?"

"Baffa..."

"Ka ga ni ban nemi jin wani ?arin bayani daga gare ka ba. Tabbas na sani Fatima bata kyauta ba, amma hukuncin saki ya yi girma sosai akan Wan wannan laifin. Matar da aka fara tara iyali da ita, an riga an zama Waya, da daWi babu daWi ha?uri ake yi a cigaba da gungurawa in ba wata muguwar ?addara ba da ba'a fata har zuwa sadda za ta birne ka ko kai ka birne ta. Akwai hanyoyin ladabtar da mace masu yawa ba tare da an kai ga saki ba. Don haka ina ro?o tare da umartarka ka mayar da ita Wakinka, bayan haka na yarje maka ka Wauki duk irin matakin da ka so a kanta matu?ar bai saSa ma addininmu ba."

Shiru Hafiz ya yi na tsawon da?i?u sittin, a cikin waWannan da?i?un, babu abinda zuciyar Daddy da Abba Lurwanu ke yi sai luguden daka. Aminci ne mai ?arfi tsakanin su biyun, don haka damuwar da ke damun Waya ta shafi Wayan. Amma saboda adalci da dattako irinna Abba Lurwanu baiyi niyyar tauye Hafiz don faranta ran Amininsa ba.

"Shi kenan Baffa. Ka zama shaida, na mayar da matata Fatima-Bintu Wakinta."
Hafizu ya faWa da cusasshiyar murya.

"Na gode. Allah yayi maka albarka. Ubangiji ya haWa maka kan matanka."
Baffa ya jero addu'o'in da farin ciki a muryarsa.

"Amin ya Allah. Na gode Baffa, Allah ya ?ara lafiya da nisan kwana. Ubangiji ya mayar da ku gida lafiya."

"Amin ya rabb"
Su Baffa suka amsa gaba Waya. Fuskokinsu cike da matsanancin farin ciki.

Mayar da Bintu Wakinta da Hafiz yayi ba ?aramin farin ciki ya jefa zuciyar Abba da Daddy ba. Shi yasa har Baffa ya shige cikin mota basu daina jera mishi kalaman godiya ba, abin ma sai

47 / 53