Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   45 / 53

132K to 135K   out of 157.3K words

kafaWunta.

Wata iriyar siririyar dariya take saki sannu-sannu gwanin ban sha'awa. Sai da suka sake ?ure ta da kallo sai suka ga ashe Laptop ne ajiye akan wani Wan teburi da ke gabanta. Bisaga dukkan alamu Vidio call take yi da mijinta.

Duk da ta ji ?arar buWe ?ofa alamun an shigo bata tsaya da dariyar da take yi ba, kuma bata Waga kai ta kalli su Bintu da suka yi suman tsaye suna kallonta ba. Sai da ta gama dariyar sannan a tausashe da wata iriyar siririyar murya ta ce ma Abban Imam ya bata minti biyar anyi ba?i.

Daga can cikin laptop Win sumbatar hannayensa yayi ya hura mata, ba tare da kunyar idanun su Bintu ba ta mayar mishi da martani sannan ta katse kiran.

Mayar da hankalinta kan su Bintu tayi, kallon sakan goma tayi musu sannan ta buWe baki a hankali ta ce
"Au! Ashe ma ku ne."
Ta faWa tana Wan yamutsa fuska da salon wula?anci da tozarci.

Bintu da takaici da ba?in cikin irin canjin da ta sake gani na sosai a jikin Zulai yake neman kaita kushewa bata san sadda ta buWe baki cikin Waga murya ta lailayo wata bamagujiyar ashar ta maka mata ba.

Da Wan sauri Zulaikha ta saka yatsarta manuniya ta toshe kunnenta Waya, sannan da yanayin muryar da ta goge da furta kalaman turanci cikin ?asaita ta ce
 Keep it low, you are so loud

Bintu da bata taSa tsammanin bayan wayewar da Zulai tayi har turanci ta iya ba taga-taga tayi za ta kifa saboda tsananin yadda maganar ya dake ta.

Da saurin gaske Raudha ta yar da belt Win hannunta ta ri?o Bintu kafin ta kai ?asa. Fincikewa Bintu tayi, hankalinta tashe da irin tozarcin da Zulai tayi mata ta yi zaman ?an bori a ?asa, sannan ta Wora hannu biyu akai ta saka kuka wi-wi kamar ?aramar yarinya.

Hankalin Raudha a tashe ta ce
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Miye haka kike yi Bintu? Kuka a gaban wannan yarinyar ai sai ki ja ma kanki raini da tozarci..."

"Raini? tozarci? wula?anci na nawa kuma Raudha? Baki ji irin kalaman da ta furta min bane?"
Tayi maganar cikin kuka wasu sababbin hawaye na sake Salle mata.
"Ki ce mata ta bani Wana. Kuma Allah ya isa tsakanina da ita da duk danginsu. Kuma na rantse da Allah basu ci bulus ba duk sai na saka ?an sanda sun ci kutumar ubansu..."

Zulaikha tana hakimce akan kujera, babu abinda take yi sai ?yal?yala dariya amma a hankali. Gogewar da tayi yasa hatta dariya idan za tayi yanzu a ?asaice take yi.

Kukan da Bintu take rusawa ba ?aramin faranta mata rai yayi ba. Jin irin maganganun da take furtawa yasa ta Waga waya ta kira Hafiz yana Wauka ta saka a hands free.

Su Bintu basu san ta kira shi ba sai jin muryar Hafiz suka yi ya karaWe kunnuwansu yana ce ma Zulai
"Hello Sis! How far?"

"Normal Luvly Bro."
Ta faWa da salon ?ara cusa ma Bintu haushi, kafin yayi magana ta sake cewa
"Yaya kai ne ka turo Bintu ta zane ni da belt sannan ta Wauki Aadil...?"

"Zana kuma Zulaikha?"
Ya katse ta cikin tashin hankali.

"Eh! Ga su nan rirri?e da belt ita da wannan figaggiyar ?awar tata wai za su min duka."
Ta ?arasa maganar a shagwaSe.

"Ke kuma sai ki tsaya su zane ki? Ke ce fa Zulai shago ta Innaye. Ko rayuwar birni yasa kin zama saiwar-sala ne?" Yayi mata kirarin da Baffa yake mata tana ?arama, saboda tsabar ?arfinta, duk yarinyar da ta kuskura suka haWa ?ashi da Zulai duk girmanta sai ta kai ta ?asa. Shi ne Baffa ke kiranta Shago ta Innaye.

"Ni Win ce dai. Har gobe ruwa na maganin dauWa Yaya."
Ta amsa tana dariya.

"Yauwa ?anwata. Kina ji na? Bintu da ?awarta mahaukata ne a cikin riguna. Cikin su biyun duk wacce tayi gigin taSa ki nayi miki izini ki Waga ta sama ki nuna ma Allah sannan ki damfarata da ?asa... Allah yasa ma su kakkarya ?asusuwan baya... kin ga ko babu komai an rage miyagun iri da basu san darajar mutane ba. Kuma a hukumance ba ki da laifi, biyo ki suka yi har muhallinki, kuma ?wararren lauya za mu Wauka ya kare ki a kotu da cewar garin kare kanki ne tsautsayi ya afka musu..."

Dariyar da yayi ma Zulaikha yawa yasa ta katse kiran tana cigaba da ?yal?yala dariya. Tsawon wasu da?i?u ta Wauka sannan ta tsaida dariyar Wif kamar Waukewar ruwan sama.

Da Waurarriyar fuska take kallon Bintu da jiniyar kukanta ya tsaya sai tsiyayar hawaye.
"Kin dai ji ko? Ko a gurin mijinki farashinki ya riga ya daWe da faWuwa ?asa war-was! Sakarya kawai!!!"

Daga Bintu har ?ar kanzagi Raudha an rasa wanda zai tanka ma Zulai da miyagun kalaman da take yaSa ma Bintu.

Har sai da ita da kanta Zulaikha ta gama jan aji ta cigaba da gargasa mata maganganu masu Waci.
"Tabbas! ?anki Aadil yana hannuna. Don haka ki daina wahalar da kanki kina yawo daga wannan gida zuwa wancan gida kina nemanshi. Yana gurina, kuma idan sama da ?asa za su haWe na rantse da Allah bazan taSa baki shi ba, matu?ar ba Yaya da kanshi bane yazo ya karSe shi kamar yadda ya kawo min shi. Ku tashi ku Sace min da gani kafin inyi rehazal Win irin dukan da na sha yima su Ladiyo a dandali akan ku."
Ta ?arasa maganar haWe da mi?ewa tsaye.

A ?auyen Fa?o, Raudha ce take jan Bintu ita kuma tana turjewa. Ayau kuma Bintu ce ta mi?e tsaye ta ri?e hannun Raudha ta ja ta a fusace suka fice daga falon, ba tare da sun Wauki belt Win da suka kashe dubu goma sha biyar gurin siyansu ba.

Suna fita daga cikin falon, Zulaikha ta ?yal?yale da dariya har tana tafa hannuwa. Al'amarin ya yi mata daWi ba kaWan ba, zuciyarta cike da godiya ga Allah da ya kasance babu kowa a gidan daga ita sai Imam.

Mummy da Karima tun safe suka yi sammakon tafiya gurin aiki. Ita kuma Hajja ?arfe tara da rabi ta shirya ta tafi rabon dabino da sweet na auren Karima da Hafiz da aka tsayar nan da sati huWu masu zuwa.

Tun jiya da daddare Aunty Rakiya ta kira ta a waya ta bata labarin duk irin ba ta kashin da suka yi da Bintu. Kuma ta jaddada mata lallai ta zama cikin shiri, domin bisa ga dukkan alamu baza ta rusina ba sai ta gano inda Wanta yake kuma ta karSe shi.
"Kar ki kuskura ki Waga mata ?afa Zulai. Dukan da naso inyi mata anan ban samu dama ba don Allah ki cika min wannan burin."
Cewar Aunty Rakiya, muryarta cike da takaicin yadda har yau bata samu damar WunWuma ma Bintu jiki ba.

"Kar ki damu Aunty. Ai ita Bintu ta san karonmu da ita babu daWi. Za ta kwashi kashinta a hannu."
Ta amsa tana dariya.

Tun daga lokacin take ta addu'ar Allah yasa idan Bintu ta tashi zuwa su Mummy basa nan, sai kuwa ga shi addu'arta ta karSu.

Tana wannan dariyar ta Wauki wayarta da Laptop ta wuce cikin Waki inda Aadil ke kwance yana barci cikin kwanciyar hankali. Yaron da a kwana Waya da tayi da shi ta fahimci sam ba shi da damuwa, idan anji kukanshi yunwa yake ji. Da an bashi abinci zai cigaba da wasa da Imam, wanda zazzaSin dare da yayi ya hana shi tafiya makaranta a ranar.



*******



Tun da ta figi motar suka fice a guje daga gidan Mummy Sauda, tsakanin ita da Raudha an rasa wanda zai fara kore zaman ?uda da yake tsakaninsu. Sai dai daga yanayin yadda Bintu take sauke zazzafan huci akai-akai, take murza sitiyarin da uban ?arfi kamar shi ya kar zomon, take ?ara taka giyar motar tana ?ara gudu kamar wacce za ta kai wasi?a, za a fahimci matsanancin Sacin ran da yake dan?are sun?i-sun?i a zuciyarta.

Da farko ta yi tunanin ita da kanta za ta ladabtar da Zulai, amma a yanzu ta yanke shawarar gara ta haWa ta da su Aunty Balira hukumar ?an sanda su koya musu hankali. Gudun da take zurawa yanzu ba ko ina ta nufa ba sai ofishin kwamishinan ?an sanda.

Kiran da Babbar Yayarsu Aunty Sadiya tayi mata, shi ya katse duk wani hanzari da take tafe da shi. Kamar baza ta Wauka ba, sai kuma ta Waga bayan ta yi tunanin haka kawai Aunty Sadiya ba ta kiran mutum a waya sai da ?wa??waran dalili.

"Helloo Aunty..."

"Bintu kina ina ne?"
Ta katse ta da tambayar da muryar da ke bayyana rashin wasa.

Har Bintu ta buWe baki za ta faWa mata gaskiya, sai kuma tayi tunanin gara kawai tayi mata ?arya. Domin za ta iya dakatar da ita daga ?udurinta.

"Ga ni a hanya zan koma gidana..."

"Gidanki ko gidan Hafiz?"
Ta sake jefa mata tambayar a tsawace. Kafin Bintu ta amsa ta cigaba da cewa
"Anya Bintu ko dai kin fara shaye-shaye ne bamu sani ba? To duk inda kika nufa ina umartarki da gaggawa ki juyo kizo ki sameni a gidan Daddy... Tunda hauka da rashin hankali da rashin kunyar Wan fari yasa ki iya rufe ido ki zazzagi uwar mijinki da yayyensa sai ki dawo gida ki cigaba da zama a Wakin Mashku... Ga takardarki Hafiz ya kawo min ni kuma na kawo ma waWanda suka haife ki..."
?it! Wayar ta katse, daga can Sangaren Aunty Sadiya.

Bintu da ta kasance cikakkiyar bahaushiya gaba da baya, kalaman Aunty Sadiya duk da da hausa tayi su sai suka sauka a kunnenta kamar da wani irin yare ne da bata taSa sani ba. Sam! bata fahimci me maganganun suke nufi ba, infact bata ma fahimci inda suka nufa ba. Da wani yanayi mai wuyar fassaruwa ta kalli Raudha, kasancewar a handsfree ta saka wayar bayan ta Waga
"Ko kin fahimci inda maganganun Aunty Sadiya suka nufa?"

Tsaf! Raudha ta fahimta. Amma tsoron aji mutuwar sarki a bakinta ga shi suna tsakiyar babban titi yasa tayi saurin gyara yanayin tashin hankalin da maganganun Aunty Sadiya suka jefa ta tace
"Nima dai ba wani fahimta nayi ba. Amma na san bai wuce ace Hafiz ya kai ?ararki gidanta ita kuma taje ta faWa ma su Mummy. Don haka ina ga ki bar batun zuwa gurin kwamishina yanzu, kije ki ji kiran da take miki."

"To shi kenan. Bari in fara sauke ki a gida..."

"Ai ba ma sai kin kaini gida ba Bintu. Sauke ni anan in samu taxi ya ?arasa da ni. Gara kiyi gaggawar zuwa kiji dalilin kiran, idanma wasu ?arerayin Hafiz ya shirya miki kiyi gaggawar warwarewa da bayanin gaskiyar abinda ya faru. Idan basu yarda ba kina iya kira na in bada shaida."

"Na gode Raudha. Allah yabar ?auna da zumunci. Shi yasa a kullum ba na gajiya da godiya ga Allah da ya bani ke matsayin babbar ?awa."

"Kar ki damu Bintu. Kin cancanci fiye da haka a gurina."

Da haka suka rabu, zuciyar Bintu cike da karsashi da ?warin gwuiwa, ita kuwa Raudha zuciyarta cike da fargaba, da addu'ar Allah yasa Hafiz ba sakin Bintu yayi ba. Tunda da kunnenta ta ji maganar takarda, to wace takarda ce kuwa za ayi maganarta idan ba ta saki ba?

Bintu tana shiga layin gidansu da mota, ta hangi motar Hafiz na fitowa daga cikin layin. Lokaci Waya zuciyarta ta ?ara ?untata da Sacin rai.
'Kenan zancen Raudha ya tabbata?'

"Uhmmm! Namiji kenan! ?udan zuma ga za?i ga harbi. Na rantse da Allah ko me za kayi Hafiz kai da su Umma baku isa ku hana ni ?watar ?ancina ba a matsayina na uwa."
Tayi maganar a fili cikin masifa, ko da suka zo gitta juna da?yar ta iya dannar zuciyarta bata buWe gilashi ta watsa mishi da?uwa ba.

Ta ja motarta a guje ta wuce shi ma ya cigaba da tafiya, ko Wan horn Winnan babu wanda ya latsawa juna, kamar dai ba su ne masoyannan da suke bala'in ?aunar junansu ba.

Ko da ta isa gida, da farko ta shiga ne da wani irin fitinannen izza da jiji da kai. Sai da taga ba a cikin falon mahaifiyarta bane Aunty Sadiya da sauran yayyenta maza uku suke zaune. Suna cikin falon mahaifinta ne, kuma ?arin Waga hankali a gareta shi ne idanun magahaifiyarsu da Aunty Sadiya ya yi jajur, alamu ?arara da ke nuna sun ci kuka sun gode Allah.

Tun daga nan jikinta ya fara sanyi. A Warare ta nemi kan kafet ta tsuguna, bayan ta yi sallama babu wanda ya amsa mata a cikinsu.

"Daddy..."

Wani gigitaccen tsawa da mahaifinta ya daka mata yasa bata san sadda ta zame daga tsuguno tayi zaman ?an bori a ?asa ba. Lokaci Waya idanunta suka kawo ruwa, lallai wannan shi ne a dake ka a hana ka kuka.

Bata daddara ba da tsawan da yayi mata ba, don ta sha alwashin baza ta taSa bari shirunta ya ja Hafiz ya ci galaba a kanta ba, cikin rawar murya da saurin baki ta sake cewa
"Daddy don girman Allah ka bari inyi muku bayanin gaskiya..."

"Ba ma bu?atar wani bayani na gaskiya daga bakinki Bintu."
Ya sake katse ta a karo na biyu, da yanayin magana mai bayyana Sacin rai a fili.

Kafin ta amsa ko ?o?arin kare kanta ya cigaba da cewa
"Mun ji gaskiyar zance daga bakin yayyen mijinki biyu da aka kira a waya aka saka su a handsfree. Sannan Mun ji rekodin Win muryarki jiya da kika je tsakiyar Wakin sarkuwarki a can ?auyensu kika yi mata cin mutunci na ?arshe ita da ?a?anta. Sannan mun ji bayanin yadda kika je gidan ?anwar mijinki yau za kiyi mata duka. Daga nan Sangarenki kuma Yayarku ga ta nan ta kora mana bayanin duk irin rashin mutuncin da taga kin yi ma dangin mijinki lokacin haihuwar Wanki. Wannan shi ya ?ara tabbatar mana da gaskiyar maganganun mijinki da ?an'uwansa. Don haka ki ri?e bayanin gaskiyarki, wata ?ila za tayi miki amfani a gaba. A ?arshe dai ungo wannan."
Ya ?ar?are maganar haWe da Waukar wata farar nannaWaWWiyar fallen takardar da tun shigarta cikin falon bata lura da ita ajiye kusa da shi ba, sai yanzu da ya Wauka ya mi?a mata.

Da farko ?in karSa tayi, sai da Yayanta Faru? da yafi sauran zafi ya ?unduma mata ashariya haWe da yun?urawa zai mare ta sannan ta karSi takardar a tsorace. Lokaci Waya Jikinta ya Wauki rawa, kamar wacce aka watsawa ruwan sanyi lokacin hunturu.

Duk da bata buWe takardar ta ga ko ta mece ce ba haka kawai jikinta ke bata babu alkhairi ko kaWan tattare da wan????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? nan takarda.

Yayanta Abubakar ne ya fara magana shi ma da nashi salon Sacin ran.
"Kin bani kunya Bintu. Na rantse da Allah ban taSa tsammanin irin wannan munanan halayen daga gareki ba. Haba!! Sai kace wacce bata yi ilimin boko da Arabi ba? Ta ina kika taSa ji mata ta fi uwa da ?an'uwa? To bari in sake tuna miki, ana canja mata, amma ba a taSa canja uwa da ?an'uwa. Don haka kin ga yanzu ga sakamakon ?o?arin raba miji da danginsa nan kin karSa, zai canja ki, amma bazai taSa canja ?an'uwansa ba. Dubi nan"
Wayarsa ya buWe ya lalubo hoton Invitation card Win Auren Hafiz da Karima ya matsa har kusa da inda take zaune tana rawar Wari ya aje mata a cinyarta.

Duk yadda ta so ta runtse idanu don kar ta karanta hoton I.V Win kasawa tayi, raWau idanunta suka sauka akan hoton, cikin ?an?anin lokaci ta haWa ba?a?en ta karanta sunayen da ke manne a jikin hoton.

Wata wawuyar bugawa zuciyarta ya yi, cikin ?an?anin lokaci ta fara jan numfarfashi da?yar, kuma sama-sama kamar mai cutar athma. Hannunta shi ya jagoranci umarnin zuciyarta gurin warware fallen takardar da ke dam?e a hannunta don ganin me ta ?unsa.

_".... Hafiz Aminu Fa?o na saki matata Fatima Bintu saki Waya..."_

Kalaman da suka manne a cikin idanun zuciyarta kenan, kuma kalaman da suka ?ara assasa hauhawar bugawar zuciyarta fiye da misali.

A haukace, cikin Wimuwa, gigita, ficewar hayyaci Bintu ta mi?e tsaye a zabure. Tayi taku Waya, biyu, uku, sai kuma ta zauna daSas! Ta Waga idanu a gwalale ta kalli Ummansu da Aunty Sadiya. Sai kuma kamar tsikarin basir ta ?walla wani gigitaccen ihu! Sai kuma ta Wauke ?if! Kamar an saka seletef an Waure mata baki.

Da saurin gaske ta sake mi?ewa tsaye, ta tattare siket Win jikinta za ta yanka da gudu Yayanta Aliyu da yake mata kallon wacce gigita yasa ta haukace yayi gaugawar dam?o kafaWunta, da ?arfin gaske ya girgiza kafaWunta haWe da ?walla kiran sunanta da ?arfi.

"Yaya... Hafiz... Ya sake ni... Na mutu..."
Daga faWin haka sai ta tafi luuuu ta kife a kafaWunsa a sume.
********



Tabbas da gaske ne... A yayinda saki ya shiga tsakanin ma'aurata biyu wanda ya kasance bai da gaskiya shi zai fi jigatuwa. Irin haka ne ya kasance a Sangaren Bintu. Shi kuwa Hafiz kwanakin da suka biyo baya harkokinsa yake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Shirin aurensa yake yi a nutse, rashin Bintu a gidanma sai ya bashi damar cin karensa babu babbaka. Soyayya mai lasisi kuma irin ta bugawa a jarida suke sha shi da Karima, a gefe guda kuma Zulaikha tana ?ara ?arfafa masa gwuiwa akan duk wasu shirye-shirye nasa.

Sai a yanzu ne ya fahimci ma'anar karin maganar da Aunty Balira take yawan faWa masa na *RANAR NAKA SAI NAKA...*, In banda Zulai ta kasance nasa ta ina ?aramar yarinya kamar Zulai da ko haihuwa bata yi ba za ta karSi yayen Aadil?

Sai ga Hafiz duk yadda yake yawan faWi a baya cewa Zulai ba ta da hankali yanzu ba shi da abokiyar shawarar da ya wuce Zulai. Tsarin yadda za'a fasalta gidansa a canja masa tsari, da yadda za'a fitar da gurin saukar ba?i ?an'uwansa duk da ita yayi

45 / 53