Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   28 / 53

81K to 84K   out of 157.3K words

ni kaWai."
Ya ?arasa mata magiyar a marairaice, lokaci guda kuma yana Wan jan hannunta zuwa inda wayar take ajiye akan kujera.

Kamaluddeen, babban Wan Mummy Saudah kuma baban Imam, wanda ziyarar aiki na tsawon watanni shida ya kai shi ?asar Gambia. Watanninshi biyu acan ?asar Zulaikha ta zo gidan, har izuwa yanzu da yake wata na biyar acan ?asar ko sau Waya bai taSa gaisawa da Zulaikha a waya ba.

Sai dai yana ganin hotunanta jefi-jefi a status Win ?anwarsa Karima. Sannan labarin Aunty Zulai a bakin Imam Wan shi sai dai idan bai kira a waya an haWa shi da yaron ba. Tun yana kore hirarta daga bakin Wan har ya ha?ura, domin matu?ar yana so hirar shi da yaron yayi tsawo to kashi biyu cikin uku na hirar labarin Aunty Zulai da irin yadda take kula da yaron ne.

Idan ya zauna shi kaWai har mamaki yake yi, na yadda a cikin ?an?anin lokaci sha?uwa mai girma ya shiga tsakanin Imam da Aunty Zulai amma bai shiga tsakanin yaron da Safina da ta kasance ?anwa a gurin marigayiya Aisha mahaifiyar Imam ba.

Yau dai haka kawai, shi da kanshi ya ji a ransa lallai ya kamata ya ga Aunty Zulan nan ya gaisa da ita. Sannan yayi mata godiyar irin kulawar da take ba yaronsa, ko a Sangaren Haddar karatun Al?ur'ani mai girma na yaron da a baya yake tafiyar wahainiya, amma a yanzu ba ?aramin nisa yayi ba, abin mamaki har ya kusa haWa izufi goma cif a kansa.

Ko da uban ya tambayeshi ya akai haddarshi take sauri yanzu? Kai tsaye yaron ya faWa mishi Aunty Zulai ce take ?ara mishi, kuma tayi ta maimaita mishi cikin nutsuwa da lalama har sai ya haddace.

Duk diramar da yake gudana tsakaninta da Imam na yadda yake ?o?arin janyo ta zuwa gurin wayar ita kuma tana tirjewa, tana ba shi wasu ?ananun uzurirrika marasa muhimmanci yana jin su. Amma ba ya hangen fuskarta sosai sai gefen kafaWunta. Shi kaWai ta cikin wayar, babu abinda yake yi sai murmushi.

"Haba Aunty Zulan Imamu. Kiyi ha?uri mana don Allah, yau dai Waya ki gaisa da Baban Imamu shi ma yaga wacece Auntyn Imam."
Mummy da take zaune acan kan dining ta saka baki don kawo ?arshen ta?addamar da ke tsakanin Imam da Zulaikha.

"To Mummy."
Zulaikha ta amsa a kunyace, don bata san Mummy na zaune a falon ba. A kunyacen dai ta bi bayan Imam da har lokacin ya ?i sakin hannunta har suka ?arasa kusa da wayar.
Da?yar ta iya Waga kai ta saci kallon fuskarsa, wani kwarjini da haiba sosai da yayi mata a idanunta yasa babu shiri ta zube a ?asa ta fara gaishe shi a daburce.
"Ina yini...? Au! Ina kwana...? Lah! Yi ha?uri... Good evening."
Ta ?arasa maganar a tsorace da tunanin kila ma ba ya jin hausa.

Da wani irin tattausan murya mai tafe da zallar kwarjini da mazantaka ya fara magana, har lokacin murmushin da yake yi bai bar kan fuskarsa ba.
"Aunty Zulan Imam! Barka da yamma. Ai ni ya kamata in gaishe ki, saboda ?o?arin da kike yi wajen jure surutun Imam. Na gode. Allah ya saka miki da alkhairi."

"Amin. Nima na gode."
Ta amsa a kunyace sannan ta tashi da Wan gudu-gudu har tana harWewa ta wuce Wakinta. Mummy da Kamal suka bi ta da kallo fuskokinsu cike da murmushi. Shi kuwa Imam me zaiyi in ba ?yal?yala dariya ba.

Tun daga wannan ranar, bata sake yarda gaisuwa ta waya ko ta Vid call ya shiga tsakaninta da Baban Imam ba. Don a yadda take ji a zuciyarta kamar ma tsoronshi take ji, shi yasa sawunta a likkafa da ta ga an fara gaisawa da shi za ta zame ta gudu zuwa Wakinta.


***** ******


[2/3, 12:04 AM] Fareeda Abdallah: "Sweetheart?"
Ya kira ta a tausashe.

Siririyar hamma ta sake, cikin saiSi da mutuwar jiki ta sake gyara kwanciyar kanta a ?irjinshi.
"Na'am...My Dear."
Ta amsa aWan shagwaSe.

Lallausan gashin kanta ya cigaba da shafawa, yana mata waiwayi sannu a hankali. Kamar bazai yi magana ba, can kuma sai ya ce
"Jibi idan Allah ya kaimu, ki shirya da wuri. Tare za mu tafi Fa?o..."

Da saurin gaske ta Wago kanta tana kallonshi cikin ido, sai kuma tayi la?was! Ganin shi ma kallonta yake yi, yana karantar yanayinta. Saukar da ?wayoyin idanunta ?asa tayi a hankali, sai kuma ta mayar da kanta ?irjinsa ta kwantar, duk a ?o?arinta na danne maWaukakin tashin hankalin da yake taso mata.
"Aadil just 4 month yake da a duniya. Ba ka tsoron muyi doguwar tafiya da shi ya kwashi iskar hanya? Ka san mura a jikin jarirai fa, yanzunnan sai ta zame musu Nemonia..."

"Babu abinda zai faru in sha Allah! Za mu tafi tare da shi, kuma mu dawo lafiya. Ki tuna fa yaushe rabonki da Fa?o? Tun bayan haihuwar Aunty Balira, to ga Babyn nata nan har yayi 2years. Duk irin jinyar da Innaye baki samu kin je gaisheta ba saboda laulayin ciki. An haifi Aadil har yau Innaye bata taSa Waukar gudan jinina ba balle ta saka mishi albarka. Jibi tare za mu tafi tabbas, ku shirya da wuri."

"To shi kenan! Allah ya kaimu."
Ta amsa da sanyin jiki, duk zuciyarta a ?untace. Amma ba ta da yadda za tayi ta nuna mishi, saboda ko kaWan ba ta ?aunar abinda zai sake janyo wani saSani ko mis?ala zarratin a tsakaninsu.

Shiru suka yi duk su biyun, kowa da irin mabanbantan tunanin da yake yi a zuciyarsa. A haka barci ya kwashe su.

Washe gari da yamma, bayan sun dawo guraren aikinsu, suna zaune a falo suna hira. Tana zaune a gefensa, Aadil na ri?e a hannunsa yana mishi wasa, yaron kuma sai dariya yake yi, da alamun ya fara gane fuskar Babansa.

A tausashe ya kalleta ya ce
"Gobe idan muka je gida, duk irin magana ko tambayar da za'a yi miki game da Zulai ki amsa musu da to kawai, ki kuma tabbatar musu muna zaune lafiya ?alau. Kin gane?"

"Eh!"
Ta amsa, ba don ta gane Win ba.

"Good. Duk da tun bayan faruwar al'amarin har yau bamu zauna ni da ke na warware miki yadda al'amuran suka faru ba, domin a ganina sam hakan ba shi da wani amfani, tunda dai matsalar na riga na maganceta. Amma na san a wancan lokacin Raudha ta yi miki bayani kamar yadda nayi mata, ko ba haka ba?"

"Haka ne."
Ta amsa, a zuciyarta take sake tunano cikakken bayanin da Raudha tayi mata wancan lokacin, wanda har yayi sanadiyyar zubda makaman kishinta, hankalinta ya kwanta luf kamar tsumma a randa.

"Madallah! To ko bayan da na magance matsalar har yanzu su Innaye basu san takamaimai halin da ake ciki ba. Akwai lokacin da na tsara zan musu cikakken bayanin komai, yadda ransu bazai Saci da ni ko ke ba, amma ba yanzu ba. Don haka gobe idan mun je ki kama bakinki, kar ki kuskura ki bada wata kafar da zai sa su gane akwai matsala tsakaninmu da Zulai. Kin gane ko?"

"Eh"
Ta amsa a sanyaye.

Shiru yayi yana cigaba da yi ma Wanshi wasa. Can bayan wasu da?i?u ta matsa kusa da shi ta rungume shi ta gefen kafaWarsa.
"Na gode My dear... Na gode. Ina ro?on Allah yabar ?auna da tabbatacciyar soyayya a tsakaninmu. Da ace a wancan lokacin baka Wauki matakin da ya dace ba, na tabbata da yanzu na daWe a kushewata..."

"Shshshshhhhhhh! Kar ki sake faWan irin wannan maganar."
Ya katse ta da sauri, jin tana zancen mutuwa.

"Na daina Daddyn Aadil. Allah ya huci zuciyarka."

Bai amsa ba, sai lallausan murmushi da ya sakar mata, kafin ya mayar da hankali kan Aadil yana cigaba da yi mishi wasa.


*****


Washe gari da sassafe suka kama hanyar tafiya Fa?o kamar yadda suka tsara. Saboda a ranar yake so suje su dawo. Bayan motarshi sha?e yake dam da tsaraba, saboda a wannan karon ba tsarabarsa bace kaWai, har da zannuwan da Bintu ta lodo da sunan za tayi tsaraba wa su Innaye.

Wani irin shirin jibga-jibgan kayan sanyi da Bintu tayi ma Aadil shi kaWai ya isa abin dariya. Amma a zahirin gaskiya kayan ta saka mishi ba don iskar hanya bane, ta saka mishi ne duk a ?o?arinta na kiyaye yaron daga kwasar cututtuka saboda Waukar da take tunanin zai sha a hannun mutanen gidansu Hafiz.

Da yake gudu sukai ba na wasa ba, ?arfe goma sha Waya da rabi ta yi musu ne a ?ofar gidansu Hafiz na ?auyen Fa?o. Wani sau?i da Hafiz yake ganin sun samu shi ne taron sunan Balki, ?ar Wakin Umma laraba da ake yi anan gidan Baffan.

Haihuwar fari ce, kuma ta zo mata da gardama. Shi yasa tun daga can asibiti kai tsaye gidan iyayenta aka dawo da ita domin ta samu ingantaccen kulawa. Yau ta kama suna, don haka sun tarar da gidan Baffan ne dam?am da ?an'uwa da abokan arziki, wanda hakan ko kusa baiyi ma Bintu daWi ba, domin ta san jagwalgwalon da Aadil zai sha a hannun mata ?an ?auye sai ya ninka wanda tayi tsammanin zai sha da farko.

Motar na fakawa, kafin ma tayi yun?urin saka yaron a Wan abin Waukarsa mai kama da kwandon Waukar jarirai ta kulle shi har Hafiz ya Wauki yaron daga cinyarta.

Ya buWe mota ya fice waje sannan ya saSa Wan a kafaWarsa
"Fito muje. Kin ga na manta yau ake sunan Balkin Umma Laraba. Kin ga shi kenan ma mun samu sau?i, ba sai munyi ta jelar zuwa gidajen ?an'uwa a gaisa ba. Na san duk za mu tarar da su a nan gida."

"Haka ne."
Ta amsa da?yar! Tana jin yadda bakinta ke wani irin Waci kamar ta tauna flagyl.

Tun kafin su shiga cikin gidan, har labarin isowarsu ya riga isa cikin gidan. Ko kafin Bintu ta fito daga cikin mota har wasu daga cikin ?an'uwansu sun lulluSe jikin motar suna yi musu barka da zuwa.

"Yauwa... Sannunku. Labaran, Inusa, ina su Kadiri? Ku zo a buWe muku boot ku kwashi kaya ku shiga da su cikin gida."
Ya faWa da fara'a sosai a fuskarsa, idanunsa na kan ?annensa maza da yayi ma umarnin kwasar kaya.

"Hafizu? Ina Zulai? Baku taho da ita ba?"
Indo ta tambaye shi bayan ta ga Bintu ce kaWai ta fito daga cikin motar, kuma ta rufe ?ofar ba tare da ta ga fitowar Zulai ba.

Kafin ya amsa ma Indo ?anwarsa Halima ta mi?a hannu da nufin karSan Aadil, nan take kuwa ya sakar mata shi ba tare da wani damuwa ba.
"Oyoyo Babanmu! Tubarkallah ma sha Allah! Kai ne haka kayi kukkuSeSe barakallah? Hajiya Bintu sannunku da zuwa."
Bata jira amsawar Bintu ta take ta ?o?arin haWiye wani gululun takaici da ya tsaya mata a wuya ba ta wuce da yaron cikin gida.
"Zulai tana gida Indo, ban zo da ita ba. Ai ita da zuwa gida sai ta yi wata shidda cif a Wakin aurenta. Idan ba na manta ba haka Baffa ya saka doka ga duk ?a?ansa mata da suka yi aure, kin ga bai kamata a karya dokar daga kanta ba."

Kafin ma Indo ta amsa nan take sauran ?an'uwa da suke gurin suka fara yi mishi surutun wannan ai wayau ne. Tunda ita Zulai Wan gida ta aura ai ko bayan sati biyu ne da yin aure za ta iya zuwa gida.

Shi dai bai sake cewa komai ba sai dariya da yake ta bin su da shi, har suka shiga cikin gidan. Bintu na biye da su a baya ranta na ?ara Saci, ganin yadda da yawansu suka nuna kamar basu santa ba, babu irin wannan Sare-Saren da rawar jikin da suka saba yi mata acan baya idan tazo garin. Yanzu ta Wan'uwansu da ?ar'uwarsu kawai suke yi, ga Wan laSuSun Wanta kuma an Wauke shi an shige da shi cikin ?auyawa, salon ya sha?i numfashi mai cike da cututtuka irin wanda bai saba sha?a ba. ?asa-?asa taja tsaki, tana ?ara haWe fuskarta, a haka har suka shiga gidan suna gaisawa da mata ba ta da wani walwala har suka ?arasa Wakin Innaye.

Bayan mitar da ?an'uwa suka yi ta mishi na rashin zuwa da Zulaikha, har a fuskar Innaye sai da ya fahimci rashin jin daWinta da bata ga Zulai a tare da su ba.

"Auta ita kaWai kuka baro min a gida kenan Fatima?"

"Ba ita kaWai bace Innaye. Akwai ?anwata Mashkura. Kuma Daddyn Aadil shi ya ce baza ta biyo mu ba sai ta cike wata shida, saboda kar Baffa yayi faWan zuwanta gida."
Bintu ta faWi maganganun a Warare, kanta a ?asa, tana jin yadda kaifafan idanun Innaye masu cike da kwarjini suke yawo a sassan jikinta.

Aunty Rakiya da Aunty Ladidi kuwa ?arara suka ce mishi ai dama bai zo da Bintu ba.

"Saboda Allah Hafizu kana sane da yadda duk muke Wokin ganin Zulai, amma kawai sai ka wani zo da Bintu ita kaWai?"
Cewar Aunty Ladidi tana kyaSe baki.

Aunty Rakiya ce ta karSe zancen da cewa
"Ita ma Bintun da tayi zamanta. Yaushe rabonta da garin? Ni Wallahi na zaci ma ta yanke da zuwa kenan. Zulai da take ?ar nan dai na san baza ta taSa ?in zuwa ba ko da za su zo kullum! Amfanin auren na gida..."

"Ke dallah rufe mana baki. Bana son shirme, kuje ku kawo musu kunun za?i mai sanyi kafin a ?arasa abinci."
Aunty Balira ta katse su fuskarta a Waure.

Sum-sum suka fice suna guna-guni, Hafiz ya bisu da kallo ?asa-?asa, zuciyarsa duk ba daWi da yadda aka karSi Bintu. Bayan kuma a ganinshi rashin zuwanta laifinshi ne, tunda da ya matsa mata tazo, tabbas za ta zo ko da zuciyarta ba ya so. Balle ma ya san Bintu baza ta taSa ?in asalinshi ba.

Bintu da take ta rarraba idanun ta ina za'a mi?o mata Wanta fiye da awa Waya sai ga shi an kawo shi yana ta tsala ihu. Hankalinta a tashe, ko ta manta a inda take ne? Ta mi?e zumbur tana zare idanu, da saurin gaske ta mi?a hannu ta karSe shi tana Wan dudduba jikinshi
"Me aka mishi ne haka yake kuka? Sam bai taSa irin wannan kukan ba tunda na haife shi..."

"Wannan Wan yalolon jinjirin me kuwa za'a mishi a gidan Kakanninshi?"
Aunty Balira ta katse ta da sauri, daman tana cike da ita ganin yadda tun Wazu ita kaWai take ta wani ciccin magani kamar wacce aka tilastawa zuwa. Da Hafizu kaWai suke hira da Innaye.

Jin irin tambayar da Aunty Balira ta gwaSa mata yasa ta dawo hayyacinta, lokaci Waya tayi la?was, ta koma gurin zamanta tana jijjiga yaron.

"Bai wuce zafi ne ya dame shi ba saboda uban kayan sanyin da kika jibga mishi bayan ba wani sanyi ake yi ba. Ki rage mishi kaya, ki bashi ruwa da nono zaiyi shiru."

Hafizu dai kanshi na ?asa, a kunyace da irin rashin karar da Bintu ta nuna a gaban Innaye. Duk da bai wani ga laifinta ba, ko shi hankalinshi ba ?aramin tashi yayi ba da jin irin ihun da Wan ke callarawa tun kafin su iso Wakin. Baiken Bintu Waya da ya gani shi ne rashin nuna kara a gaban Innaye da Aunty Balira.

Wannan ziyara dai ba Bintu kaWai ba, hatta Hafizu ba wani daWinta yaji ba. Saboda yadda ya zaci Innaye za ta nuna Woki sosai irinna ?aunar abin cikin ?wai da yafi ?wan daWi bata wani nuna ba. A ta?aice ma yaron ko cikakken mintuna uku baiyi a hannunta ba ta mi?a shi ga Aunty Balira, ita kuma tana karSa ta mi?a shi ga Bintu.

Haka suka zagaya Wakunan sauran matan gidan suka gaishe su, ko ina suka je tambayar ina Zulai? Ya take? Me yasa ba'a zo da ita ba? Gaba Waya ya ?arasa dusashe Wan hasken Bintu da ya rage a gidan.

Ko tsarabar da aka raba na zannuwa da kuWi da sunanta a wula?ai sukai ta yi mata godiya, babu wani rawan jikin da suka saba yi idan ta musu kyauta a baya.

Duk tsawon awoyin da suka yi a ?auyen Bintu ta kasa cin komai. Sai Wan ruwan goran swan da ta ciro a cikin jakarta kawai take iya kurSa saboda yadda bakinta ke ta bushewa kamar mai azumi. Daman ba abincinsu take ci ba, ba ta shan ruwan ?auyen, amma a cikin babbar jakar hannunta akwai robar takeaway sha?e da snacks, don tsananin takaici da ba?in cikin da suka sha?a mata ta kasa buWe jakar ta ciro balle har ta samu ?warin gwuiwar ci a gaban mutane.

Shi kuwa Hafizu ba ruwanshi, kunun za?i mai sanyi da Aunty Balira ce tayi aikatau Winsa ya sha sosai, shinkafa da miya da Umma laraba ta aiko musu da shi a kwanon samira sabo ya Wiba ya take cikinsa, ko tayi bai Sata lokacinsa wajen yi ma Bintu ba. Domin ya san ba ci za tayi ba, ya sani tun da daWewa tsarinta ne ba ta iya cin abincin gidan sha'ani.

Har suka gama zamansu Baffa bai dawo ba. Amininsa ne ya rasu acan ?auyen Guraji, nesa da su kaWan. Tun safe Baffan yayi sammakon tafiya can gurin jana'iza, har yanzu uku da rabi bai dawo ba.

Sai sa?on kuWi masu kauri Hafizu ya bar masa a hannun Innaye, ita kuma Bintu ta bada shaddoji kala uku da turaruka kala biyu a ajiye masa.

"Sannu da Wawainiya Fatima. Mun gode, Allah ya saka da alkhairi ya raya zuri'a."
Innaye tayi ma Bintu addu'a da murmushi a fuskarta, a zuciyarta take jinjina atamfofi kala uku da Bintun ta bata abokan zamanta kuma kala bibiyu.

?arfe uku da rabi Hafizu suka sallaci la'asar, suka yi sallama da mutanen gidan gaba Waya, ?an'uwa suka rako su har gurin mota ana musu addu'ar Allah ya kiyaye hanya ya mayar da su gida lafiya.

Da Amin suke ta amsawa har suka shige cikin mota, direba yaja suka kama hanyar komawa gida.

Nannauyan ajiyar zuciya Bintu ta sauke idanunta a

28 / 53