Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   40 / 53

117K to 120K   out of 157.3K words

kwarmin idanunta.

Kuma karaf a idon Hafiz. Amma wani abin mamaki shi ne, duk waWannan tausasan kalaman, da waWannan hawayen da suka cigaba da sauka a idanunta kamar an buWe famfo, ko gezau baiyi ba balle har ya ruWe ya fara Sare-Saren jiki yana rarrashinta kamar yadda yake yi a baya. Sai ma wani siririn tsaki da yaja ?asa-?asa ya nemi bakin gado ya zauna, wayarsa da take ajiye gefe Waya ya janyo ya fara latsawa sannu a hankali.

Wani matsanancin tsoro ne ya tumbatsa a zuciyar Bintu. Abu ne da bata taSa tsammani daga Hafiz ba shakulatun Sangaro da zubar hawaye a idanunta. Abu kamar aikin asiri? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Daga zubar hawaye na kissa sai na gaske suka koma zuba a idanunta.

Kamar za ta share shi, amma niyyarta na yaye Aadil gobe kuma Ummanta take so ta yaye mata shi domin har sun gama magana da ita Umman tun kwanaki yasa ta ja sanyayan ?afafunta kusa da shi ta jingina kanta da kafaWarsa tana cigaba da shesshe?ar kuka. Da rawar murya irinta wacce kuka ke neman cin ?arfinta ta ce
"My dear yaye yaro Wan shekara Waya abu ne da ake bu?atar ya kasance kusa da mahaifiyarsa. Musamman da ya kasance Aadil yaro ne mai masifar ?ulafuci ga ?wuiya, ka ga kuma ko babu komai ya saba da su Umma, sannan ga Mashku wacce duk tashen ?wuiyar da yake yi sam ba ya mata. Ba ka ganin idan aka kai shi can Fa?o gurin mutanen da bai san su ba, bai taSa ganinsu ba, bai saba da su ba, zai iya shiga wani mummunan hali da ba'a fata?"

Bai amsa mata ba, bai kalle ta ba, sannan bai fasa danna wayar da yake yi ba.

Ita kuma bata gaji ba ta cigaba da magana cikin ?an?an da kai da magiya, daga jingina kai a kafaWunsa sai ta zame zuwa ?asa ta haWa hannayenta biyu alamar ro?o ta cigaba da cewa
"Ina ro?onka don Allah ka yi ha?uri My dear, Umma ta yaye a yanzu, nan gaba kaWan ko shekaru biyu idan ya cika a duniya ni da kaina zan haWa kayanshi ka kaishi gurin Innaye ya kwana musu biyu..."

Wani mahaukacin kallo da ya watsa mata kamar zai rufe ta da duka yasa ta ajiye numfashin maganarta ba tare da ta shirya ma hakan ba. Ajiye wayarsa yayi, ganin haka yasa taja da baya da sauri, don a tsammaninta zai kai mata hannu ne karo na farko a tarihin rayuwar aurensu.

"Uhmmmm! Bintu kenan! Na rasa abinda ya rufe min idanu tun a baya na kasa gano munana kuma ba?a?en halayenki!! Yanzu saboda ba ki da kirki ni kike kallo tsakiyar idanuna kina kiran iyaye da ?an'uwana wasu mutane can??? To bari in faWa miki, ko Aadil zai mutu saboda ?wuiya da rashin sabo Innaye ita za ta yaye shi..."

Izuwa wannan lokacin, duk yadda ta kai ga ?o?arin danne Sacin ranta kasawa tayi. Ranta a Sace ta mi?e tsaye ta tsaya a gabansa suna musayar kallo, da Sacin rai mai bayyana maWaukakin tashin hankali ta ce
"Amma gaskiya tsakani da Allah idan kayi min haka baka min adalci ba Hafiz. Saboda Allah ya kake so yaron da ya taso cikin gata, tsafta, tarairaya, shagwaSa irin Aadil ya gudanar da ?azantacciyar rayuwa irinta su Innaye...?"
Tahowar tafin hannunsa kawai ta gani a cikin idanunta, a zafafe ta yun?ura za ta ja da baya ankara da hakan da yayi yasa shi saka hannunsa na hagu ya finciko wuyar hijabinta.

Cikin sauri da sada?arwa haWe da faWuwar gaba tayi gaggawar runtse idanunta tana jira taji saukar mari a kumatunta, sai kuma taji shiru. Sakan Waya, biyu, uku, a hankali ta Wan buWe idanu ta saci kallonsa sai taga hannunsa ma?ale a iska daf da kumatunta. Ko da ta kalli fuskar Hafiz da sauri ta sauke idanunta ?asa saboda irin fusata da hucin da taga yana yi kamar zai ci babu.

"Kin ci sa'a! Kin ci sa'a Bintu tun da na tashi a rayuwata ban taSa ganin Baffa ya daki Innaye ko Waya daga cikin matansa ba. Don haka ba na fatan ni Wansa ace na fara dukar matata. Amma idan giyar wake kike sha ki ci gaba da aibata Iyaye, ?an'uwa, ?auyen Fa?o a gabana. Na rantse da Allah sai na koya miki hankali ta inda baki taSa tsammani ba. Kuma ina sake faWa miki, Wallahi Tallahi Aadil ko mutuwa zaiyi Innaye ce za ta yaye shi ba Ummanki ba."

Wuyan hijabinta da ya sha?e ya wancakalar da ita, tayi taga-taga za ta faWi, da?yar ta iya tsayawa guri Waya. Bai sake kallonta ba ya Wauki wayarsa, wallet Winsa da makullin motarsa ya fice daga Wakin bayan ya ja mata wani dogon tsaki.

Ko bayan fitarsa ta daWe cikin shiru, bayyanan tashin hankali da maWaukakin tsoro ?arara a fuskarta. Duk da wannan taratsin da ya mata ko kaWan ba ta ji a ranta za ta iya saduda ya Wauki Aadil ya kaishi gurin Innaye ba. Abu ne da sam-sam bazai taSa yiwuwa ba ko da za suyi tashin hankalin da ya ninka wannan ya ?ara ninkawa. Don haka ta watsar da zancen ta fara tunanin yadda gobe da sassafe za tayi sammakon Wauke Aadil daga gidan tun ma kafin ya farka daga barci, za ta gani, ko idan ta kai ma Ummanta Aadil yana da ?warin gwuiwar da zai iya zuwa ya Wauko shi?

Can kuma sai idanunta ya faWa kan agogo bayan ta ji ?arar ficewar motarsa daga gidan, ?arfe tara da minti goma sha bakwai na dare.

"Ina my dear yake haramar zuwa a darennan?"
Ta tambayi kanta a fili.

Lokaci Waya kuma sai tunanin yadda yake yawan yawace-yawace a cikin kwanakin ya faWo mata a rai. ?irjinta ne yayi kwance-kwance ya buga daram!
"Na shiga uku ni Bintu? Kar dai ace yawon zuwa club My dear ya tsira abinda ba halinsa ba?"

Ta sake tambayar kanta hankalinta a tashe. Domin tunanin yi mata kishiya a soyayya balle har ya fara neman aure abu ne da ko a mugun mafarki bata taSa hasashen zai iya faruwa ba.
******



A hankali yake tu?a motar, jefi-jefi idanunsa na sauka akan fuskar wayar yana kallon lambar Karima da yayi saving sunanta da ?urratul-ayni. Kamar bazai kira ba, sai kuma ya danna mata kira, domin a yadda zuciyarsa ke tafarfasa ita ce kawai zaiyi tozali da kyakkyawar fuskarta ya nemi Sacin ran da ke dan?are a zuciyarsa ya rasa.

Har ya cire ran za ta Wauka sai kuma ta Waga a lokacin da kiran ke daf da tsinkewa. Bayan sallama, shiru tayi daga can Sangaren tana jan fasali irinna macen da ake bibiya ana neman soyayyarta. Domin har yanzu ba wai ta sake mishi bane, jan zarenta take yi yadda take so shi kuma yana bibiye da ita sawu da ?afa, abinda ke ?ara fasa mata kai kenan tana ci gaba da murza kambunta yadda take so.

"?urratul Ayn..."
Ya kira ta a tausashe.

"Na'am.... Nurul-?alb"
Ta amsa shi da wani irin salo da ko a fili ko a waya bata taSa gwada mishi irinsa ba.

Wani zirrrr da ya ji tun daga tsakiyar kansa zuwa babbar yatsarsa yasa shi saurin gangarawa gefen titi tun kafin ya buga ma motar gabansa. ?ara ?an?ame wayar yayi a kunnensa kamar me tsoron kar a ?wace masa. Ya sake yin ?asa ?asa da muryarsa yana jin yadda zuciyarsa ke bugu sauri-sauri da matsanancin soyayyar Kariman. Allah ya sani yana son Karima, irin soyayyar nan mai saiSi da shiga cikin zuciya sannu sannu kafin malallakiyar zuciyar ya ankara ta yi masa mugun kamu.

Idan za a ritsa shi da wu?a shi da kanshi bazai ce ga abinda ke ?ara jansa a afka ma soyayyarta ka'in da na'in ba. Lallai sai yanzu ya ?ara yarda so tsuntsu ne, yana tashi haihata-haihata daga wannan bishiyar ya koma wancan. Bazai ce ya daina son Bintu ba, amma fa shi baya jin ta a ransa kamar yadda yake jin Karima.

Da gaske yanzu idan za a bashi Al?ur'ani zai rantse da Allah Karima yake so! Karima yake ?auna!! Da Karima yake burin yin rayuwar aure na har abada!!!

"Ina so in ganki ?urratul-ayn! Yanzu...!"
Ya sake faWa da murya ?asa-?asa.

Shiru tayi na ?an wasu da?i?u! Ta buWe baki za tayi magana sai yayi saurin katse ta da cewa
"Kar ki ce min a'a dare yayi don Allah sanyin idaniyata. Ina cikin matsananciyar damuwa, tabbas idan banyi tozali da kyakkyawar fuskarki ba zanyi kwanan ba?in ciki ne a wannan dare."

"Me yake damunka Nurul ?alb? Wa ya taSa min kai ?"
Ta tambaye shi da murya mai bayyana damuwa da damuwarsa.

"Ke kaWai nake son gani kawai... I'm very sure hankalina zai kwanta idan na ganki. Pls ?urratul-ayn"
Ya sake faWa cikin magiya, ba tare da ya amsa Waya daga cikin tambayoyinta ba.

"Shi kenan! Allah ya kawo ka lafiya. Amma yanzu ina asibiti..."

"Ga ni nan zuwa."
Bai jira ta sake cewa komai ba ya katse wayar. Tayar da motar yayi ya harba kan titi a guje yana jin yadda zuciyarsa ke tsallen baWaken murnar za tayi tozali da muradinta.

A can Sangaren Karima, narai-narai tayi da idanu tana kallon Hibba haWe da cewa
"Na shiga uku Hibbah! Mijin Aunty Bintu ne fa...!"

"And so what?"
Hibba ta katse ta haWe da gallah mata harara.
"Wani lokacin ke dai banza ce Wallahi Karima. Na rantse da Allah da tuntuni na san da wannan labarin da tuni kun daWe da wuce wannan matakin. Sai me don mijin Bintu ne? Haramun ne? Uban me kuka haWa da Bintun da har kike shakkar auren mijinta?"
Taja dogon tsaki ta sake gallah ma Karima harara a karo na biyu sannan ta cigaba da cewa
"Dama ace Bintun wata mutuniyar arziki ce shi ne har za ki Wan ji wani War don mijinta na son ki. Na zaci ke kika bani labarin irin yadda Bintun take wula?anta iyaye da danginsa don sun kasance ?auyawa? Kuma baya ga haka ma ko asibitin nan nazo gurinki ai ina ganin yadda take wula?anta ku Nurses tana daka muku tsawa don kawai ta?amar ita likita ce. Don haka ki aje wata Bintu a gefe Waya ki rungumi masoyinki da gasken-gaske.

In dai har za ki ji shawarata, ki bashi dukkan goyon baya Wari bisa Wari. Tunda kika ga Mummy ita da kanta ta zaunar da ke tana faWa miki kyawawan halayen Hafiz Win, alamun da ke nuna ta yi na'am da al'amarin Wari bisa Wari kawai dai ba ta son yi miki tilas ne.

Yanzu dai duk ba ma wannan ba, tashi ki shiga bayi ki wanke fuskarki kizo in miki kwalliya sama-sama don kar ya ganki garau-garau duk kin jigata da aiki..."

"Don Allah ki bari Hibbah, ni ba wani kwalliya da zanyi..."

Ai ko kafin ta rufe baki har Hibba ta finciki hannunta taja ta da ?arfi suka fara tafiya zuwa banWaki.
"Wallahi baki isa ba. An faWa miki namiji irin Hafiz da sanyin jiki ake samun hankalinsu? Ko don kina ganin Allah ya kashe ya baki? To in faWa miki ko kina da kyau sai kin ?ara da wanka kamar yadda ba'a bori da sanyin jiki."

A ?asa da mintuna goma sha biyu Hibba ta yi ma Karima sassau?ar kwalliyar da ya ?ara fito da ita fes! Ta tsiyayi humrah ta shafa mata. Don saboda tsabar sabo da gayu da gwalli duk inda Hibba za ta saka ?afa a cikin jakarta akwai komai da za ta bu?ata na kwalliya. Ko don ya kasance sa'na'arta ne oho!!!

Kamar yanzu dai, ?anwar Hibban aka kwantar a asibitinsu Karima, mahaifiyarta ita ta yini da mare lafiyar ita kuma Hibba za ta kwana da ita. Duk da sanin jinya za ta je asibiti hakan bai hana ta zuwa da kayan kwalliya da Waya daga cikin kalolin humrar da mahaifiyarsu take sayarwa ba. Ashe rabon tayi ma Karima amfani da kayan kwalliyar ne.

Karima aikin yamma tayi, tun tuni ya kamata ta tafi, amma ganin Hibba ya saka ta zama tana rage mata dare, bayan ta kira Mummy ta faWa mata ba sai an turo mata direba ba, direban gidansu Hibba zai dawo da ita gida.

Hira ne yayi hira har Allah ya matsi bakinta take ba Hibbah labarin irin naci da matsanancin son da Hafiz ke mata. Bayan ta gama zage ta tas kan irin wasa da dama Waya da Allah ya jefo mata sannan ta Suge da bata shawarwarin yadda za ta sauke duk wani izzah da aji ta ?ara ru?o wuyan Hafiz Win ?am! Ta yadda bazai taSa gigin barinta ba. Suna cikin wannan tattaunawar ne Hafiz ya kira ta a waya, shi ne fa har ta fara gwada masa kulawa da soyayya wanda da can ba ta wani nuna masa saboda tsoron abinda zai je yazo idan zancen soyayyarsu ya koma kunnen Bintu.

Isowar Hafiz harabar asibitin ya yi daidai da isar Dr. Raudha aminiyar Bintu na ?ud-?ud cikin asibitin. Ita a ranar aikin dare take da shi. Mamaki ne ya kamata don ta san Bintu aikin safe tayi, tunanin ko wani abu yazo karSa ma Bintu a cikin asibitin yasa tayi watsi da mamakin ta cigaba da latsa waya tana ?o?arin danna kiran lambar Mamanta har Hafiz ya shige cikin asibitin akan idanunta.

Tsayawar da tayi amsa waya a cikin mota yasa tayi kyakkyawan ganin da yasa wayarta ya suSuce daga hannunta ya faWa kan cinyarta. Bata ko bi ta kan wayar ba ta cigaba da kallon Hafiz da Karima da suka jero suna takun da ke bayyana ?arara masoya ne su biyun. Kamar ita ce Bintu, saboda wani ba?in ciki da kishi da ya rufe mata idanu, a haukace ta yun?ura za ta buWe motar ta fita sai kuma tayi gaggawar saka ma kanta linzami.

Wayarta ta rarumo da sauri, bata bi ta kan muryar mahaifiyarta da take ji yana fita a cikin wayar ba ta katse kiran a gaggauce, hannunta har rawa yake yi gurin lalubo lambar Bintu ta danna mata kira, amma wani abin ba?in ciki da takaici shi ne wayar Bintun a kashe take.

Cikin ?asa da sakan hamsin sau huWu tana gwada kiran Bintu na'ura na faWa mata wayar a kashe take. Baki da hanci buWe zuciyarta tumbatse da maWaukakin mamaki ta cigaba da bin su Hafiz da kallo har suka shige cikin motarsa shi da Karima. Tsoro ne sosai ya ?ara kamata ganin yadda Hafiz ya buWe ma Karima ?ofar da za ta shiga yana kashe ta da lallausan murmushi. Idan ma ba idanunta ne ke mata gizo ba, sai taga kamar har wani Wan du?awa Hafiz Win yayi ma Karima alamun girmamawa.

Ita kuwa Karima sai wani rausaya take yi tana rangwaWa haWe da fari da idanu. Ko rantsuwa tayi babu kaffara akan idan ba matsananciyar soyayya ba ce a tsakaninsu babu yadda za ayi ta gansu a cikin wannan yanayin.
"TaSWijan! Namiji! Namiji!! Mugu Wan masara ana goyonka kana gemu... Don ubanki Bintu ki buWe waya in baki labarin kaWan daga cikin sakayyar da Hafiz zai miki kan irin alwashin da kika daWe kina sha akan shi ya fita daban a cikin maza."
Ta yi maganganun cikin masifa kamar za ta ci babu, a lokaci guda kuma tana cigaba da gwada kiran lambar Bintu. Wanda har lokacin na'ura ke sake tabbatar mata wayar a kashe take.

Ita kaWai a cikin motar take masifa tana zage-zage kamar za ta ci babu. A Lokaci guda kuma tana shan alwashin kaloli mabanbanta na cin uban Karima da za suyi ita da Bintu gobe a ofis idan an wayi gari.
"Kuga min shegiyar yarinya sumumu-kasau ashe ?asungurmar munafuka ce? Ko da yake ai maganin Bintun ma da ta sakarwa uwarta Hajiya Sauda fuska, ai ga sakayyar sakin fuska nan ta fara gani. Tana niyyar wanke zu?e?iyar Wiyarta ta bashi ya aura."

Tana wannan masifar har bata san lokacin da motar Hafiz ya bar harabar asibitin ba. Waigawa kawai tayi taga inda motarsa take ba shi sai filin gurin.

Ta ja tsaki ya fi sau hamsin, duk yadda mahaifiyarta take ta biyo bayan kiran wayarta ta kasa Wauka. Duk da magana ce mai muhimmanci suke yi. Ta sani a yadda take fusacen nan ko ta Wauka baza ta iya mayar da hankali su cigaba da magana ta nutsuwa ba.

A ?arshe sai kashe wayar tayi, ta figi jakarta da wayar ta fice daga cikin motar ta nufi cikin asibitin. A zuciyarta take ?udurta yadda za ta ci uban duk wata nurse budurwa da ta tarar da ita a bakin aiki a wannan daren.
'Munafukai, Algungumai, duk bakinsu Waya matsiyata. Ashe bayan kwarkwasa da gwalli da suke yi ma Likitoci maza har mazajen likitoci mata basu bari ba. Duk za su ci ubansu Waya bayan Waya.'

Da wannan ?udurin ta ?arasa cikin asibitin zuciyarta cike da addu'ar Allah ya haWa da ?anmatan nurses Win asibitin, musamman waWanda ta san sun fi shiri da Karima.


******


Wannan gwaggwaSar canjin bazata da aka samu bagatatan a cikin tafiyar soyayyar da a farko shi kaWai yake kiWansa kuma yake rawarsa ba ?aramin faranta masa zuciya yai ba. Tuni ya manta da Bintu, Sacin ran da ta cusa mishi da duk wani abu da ya shafe ta.

Ba ma kamar yadda minti Waya biyu a hirar da suka gabatar da Karima sai ta ambaci Innaye, ko kuma ta ambaci kirkin ?an'uwansa. A cikin hirarsu har ta bashi labarin haWuwarta na farko da Innaye, da yadda jininsu ya haWu farat Waya. Amma ko da wasa bata bashi labarin yadda Bintu ta wula?anta Innaye a wancan lokacin ba saboda gudun tayar da husuma tsakanin ma'aurata.

Sun yi hira na awa Waya cif bayan isarsu gidan Momy Sauda. Kamar bazai tafi ba, sai da Momyn ta kira shi a waya tayi mishi tatas kan cewa baza ta yarda da irin wannan rashin adalcin tun yanzu ba.

"Allah ya huci zuciyarki Mummy. Zan tafi yanzu, sai da safe. Gobe idan Allah ya kaimu da yamma zan zo..."

"Kar ma ka fara Hafiz, hira sau biyu a sati ya isa.

40 / 53