Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   51 / 53

150K to 153K   out of 157.3K words

ga suna da dangi irinna ?auyen-?ayau haka kamar su Innaye ba, ko daga mu'amalar da Ummansu take yi da ?an'uwan mijinta, ma?wafta da basu da shi da almajirai, ya kamata ace ta koya daga halin arzikin iyayenta.

Ta rasa ta yadda aka yi tayi sakacin da har ta bari shaiWan yaci galaba a kanta ta dinga tsula irin wannan tsiyar, kamar bata san inda yake mata ciwo ba. Sai ga shi mutanen da ta daWe tana cuta musu, sun samu damar ramuwa a kanta basu rama ba, a madadin haka ma suka yafe mata, sannan suka bi ta da karamci mai tsayawa a zuciya.

Lallai ta gode ma Allah da yasa ta gane kuskurenta tun lokaci bai ?ure mata ba. Alhamdulillah!


*********


Washe gari da misalin ?arfe huWu na yamma direba ya aje Bintu a ?ofar gidan Zulai. Domin can gidan Mummy ta fara zuwa, bata tarar da kowa ba sai Hajja, bayan gaisuwar mutunci da girmamawa da ya shiga tsakaninsu Hajja ta sanar da ita Zulai ba ta nan, ta tafi can gidanta ta Webo wasu kayayyaki, saboda gobe za ta tafi Fa?o.

Bata Sata lokaci ba tasa direba ya juya da ita bayan ta yi mishi kwatancen gidan, zuciyarta cike da addu'ar Allah yasa kar sake samun saSani.

Cikin sa'a kuwa ko da ta isa ta tarar da ita a gidan, tana tsaye a bakin ?ofar Falonta da jakunkunan kaya a gabanta maigadi yana kwasa yana lodawa a boot Win motarta.

"Ke kuma Lafiya haka wata ?ozai-?ozai da ke?"
Tambayar da Zulaikha ta fara jefa mata kenan tana mata wani kallo mai cike da wula?anci da ?as?anci.

Ko kaWan Bintu bata bari Sacin rai ya bayyana a fuskarta ba. Ta sani duk cikin ?an'uwan Hafiz daga Rakiya, sai Zulai, sai Ladidi a rashin ha?uri. Don haka tun kafin ta shigo ta sa ran za ta fuskanci fiye da haka.

"Allah ya huci zuciyarki Hajiya Zulai. Don Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga, na rantse da girman Allah ba tsiya ne ya kawo ni ba. Na zo ne kawai don in nemi gafarar irin abubuwan da na aikata miki a baya, shi kenan ba wani abu ba."

"Bintu?"
Zulai ta kira sunanta da mamaki.
"Ke ce kuwa?"
Ta sake tambayarta mamakinta na daWa ninkuwa. Domin ita sam ba ta da labarin zuwan Bintu Fa?o, abinda ya wakana da kwanan da tayi.
"Ko dai wani wula?ancin ne kika sake zuwa kiyi min? Idan ma wula?ancin ne kin san na dama ki na shanye ki."

"Wallahi ba haka bane Zulai, yafiyar dai da kika ji na ce ita nazo nema. Idan kuma baki yarda ba, kina iya kiran Innaye a waya ki tambayeta, don shekaran jiya na je can, acan ma na kwana, ban bar Fa?o ba sai da na tabbatar sun yafe min ita da su Aunty Balira."

"Shi kenan! Shigo, Bismillah."
Zulai ta faWa sannan ta matsa mata daga hanyar shiga cikin falon, har lokacin mamakin da take yi bai bar kan fuskarta ba. Kafin ta zauna sai da ta shiga kicin ta Wauko ma Bintu ruwa da lemu.

"Gidanki ya yi kyau sosai Zulai, Allah ya sanya albarka ya ?ara zaunar da ku lafiya."
Bintu ta faWa fuskarta na bayyana gaskiyar asirin zuciyarta ta tona, kamar ba gidan bane a wancan karon hassada da kishi da ba?in ciki suka rufe mata idanu ta kasa yaba kyawunshi a wancan lokacin.

"Uhmmm! Amin."
Zulai ta amsa a ta?aice.

Ruwan ta tsiyaya a kofi ta sha kaWan, sannan ta buWe baki ta sake ro?ar yafiyar Zulai cikin ?an?an da kai, har tana ?an ?ananun hawaye.

Ba tare da wani ja'inja ba a mamakance Zulai ta ce ta yafe mata. Don ita ganin al'amarin take yi kamar a shirin film ko kuma tatsuniya, jira kawai take yi taga ?arshen shi ta samu sararin furta ?urungus!
Sai kuma ta ga har Bintu ta tashi tafiya bata yi wani yanayi da zai bayyana yafiyar da ta nema ba har zuciyarta bane.

A mutunce suka yi sallama, Bintu tana ta godiya ma Zulai kan yafiyar da tayi mata cikin ?an?anin lokaci, har ta fita waje ta koma cikin falon, ga tsammanin Zulai za ta tambayi ina Aadil yake ne, sai ta ji ta ce
"Taimaka min da lambarki mu dinga gaisawa mana Zulaikha? Kin san bahaushe ya ce yawan gaisuwa ya fi yawan faWa."

"Haka ne."
Ta amsa a Warare, da alamun har lokacin mamaki da kaWuwa bai sake ta ba, ta karanto mata lambar wayar ita kuma Bintu tana shigarwa cikin wayarta. Sai da ta gama tsaf sannan ta sake yi mata godiya ta fita a falon, fuskarta cike da murmushi.

Zulaikha tana jin ?arar rufe get alamun Bintu sun wuce ta rarumo wayarta da sauri ta danna kiran lambar Innaye, tana Wauka daga can Sangaren, ko gaisuwa bata tsaya sunyi ba ta fara kakabin al'amarin
"In da ranka ka sha kallo Innaye... Wai fa Bintu ce tazo har gidana neman gafara kan irin wula?anci da cin mutuncin da tayi min a baya..."

"To menene a ciki Zulai? Ai ta yi kyan kai da bata tsaya girman kai ya hanata aikata abinda ya kamata ba. Mu ma ta zo nan har da kwana. Ina fatan dai kin yafe mata ba tare da tashin-tashina ba?"

"To ya zanyi Innaye? Na dai yafe ba don halinta ba..."

"To madallah! Zan kira ki anjima. Barin sallami Baffanku, kwaWon rama nake masa..."

Jin sunan kwaWon rama yasa miyaun bakinta tsinkewa, A shagwaSe ta ce.
"Innaye ni ma zan ci, a tsinko da yawa gobe da wuri a kwaWanta min kafin mu ?araso."

"Allah ya tsare, Ubangiji ya kawo ku lafiya."
Innaye bata jira ta amsa ba ta katse wayar.


********



Yau kwananta huWu da dawowa daga Fa?o. Sosai hankalinta ya ?ara kwanciya, kwana biyu ta ?ara a gidan Aunty Sadiya sannan ta tattara kayanta ta koma gidan Daddy.

Yau ne ta yanke shawarar za ta kai ma Hafiz ziyara har Ofishinsa. Saboda idan ba can Win ta je ba, babu in da za ta samu ganinsa suyi magana ta nutsuwa fuska da fuska. Ta daWe da sani ko ta kira shi bazai zo ba, baya ma Waukar wayarta, balle har ta sararin faWa mishi abinda take so.

Bata sha wahalar samun iso zuwa Ofishinsa ba, saboda duk an santa a ma'aikatarsu Hafiz Win. Tana sanye ne da sutura ta mutunci, hijabin jikinta ya sauka har ?asan gwuiwoyinta, sai daga can ?asa ake ganin sket Win jikinta na atamfar Super Holland. Duk da fuskarta ta yi fayau saboda rama, amma ta yi kyau abinda, kuma da yake jikinta mai kyau ne babu ma wanda zai kalle ta ya ce ta kai shekaru talatin da huWu, balle har ayi tunanin ta yi aure ko kuma ace ta haifi Aadil, in dai za'a faWi gaskiya, Bintu tana cikin kyawawan mata ajin farko. Kuma kyawunta na Waya daga cikin dalilin da yasa ta daWe tana taka rawa a rayuwar Hafiz.

Tsawon da?i?u talatin suka Sata suna musayar kallo a tsakaninsu. Hafiz da idanu cike da mamaki da yanayin rashin murna da ganinta, ita kuwa Bintu da fuska mai cike da kewa... wata matsananciyar ?auna da ta gaza Soyuwa ta bayyana a fuskarta.

"Ayya mana Daddyn Aadil, baka yi murna da ganina bane?"
Ta faWa da sassanyar murya.

"Uhmmm! Bintu kenan."
Ya yi maganar da yanayin takaici.
"Me ya kawo ki nan?"
Ya sake faWa tun kafin tayi magana.

"Zan iya zama?"
Ta kore tambayarshi da na ta tambayar.

"Uhmmm! Idan kin so"
Ya amsa a ta?aice.

Da sanyin jiki sosai ta taka a hankali zuwa inda aka tanadi kujerun zaman ba?in da suka zo Ofis Win. Zuciyarta cike da ba?in cikin yadda son zuciyarta ya janyo rugujewar matsananciyar soyayyar da Hafiz yake mata.
'Ya rabbb!'
Ta faWa a hankali, sannan ta sausauta murya ta fara gaishe shi da tambayar bayan rabuwa.

"Lafiya ?alau Alhamdulillah!"
Amsar da ya bata kenan a ta?aice, da yanayin gundura ?arara.
"Me ya kawo ki nan?"
Ya sake tambayarta a ta?aice.

"Kayi ha?uri Daddyn Aadil. Na sani duk ni na jawo abubuwa suka taSarSare har haka a tsakaninmu. Ina mai sake baka ha?uri a karo na uku..."

"Bintu!! Me ya kawo ki nan??"
Ya jefa mata tambayar da murya mai bayyana Sacin rai ?arara.

Jikinta ne ya ?ara sanyi, gwuiyawunta suka ?ara saki, kamar wacce ta kwana ta yini tana zawo.
Da?i?u talatin ta Sata tana kallon cikin idanunshi tana karantarsu, ?irjinta ne ya buga daram!!! Domin babu abinda take gani sai matsananciyar tsanarta.
"Na zo ne in ji makomar zamantakewar aurenmu daga bakinka..."

"Makoma?"
Ya tambaye ta.
"Wace makoma kike magana kuma Bintu?"
Ya sake tambayarta da tsawa-tsawa.
"Na zaci duk makomar da kike magana akai na riga da na bayyana miki ta sa?on text message tun ranar da aka tilasta min ba da son raina ba na mayar da ?addararren aurenki...?"

"?addararre Hafiz?"
Ta tambaye shi muryarta na rawa.
"Auren nawa ne kake kira ?addararre Hafiz?"
Ta sake faWa hankalinta a tashe, bayan ta mi?e tsaye, idanunta a warwaje. Hannayenta duk biyu dafe da ?irji.

"Kina mamaki ne Bintu?"
Ya tambayeta yana ?ar dariya, amma irin dariyar nan ta zallar takaici.
"Ai idan na kira aurenki da ?addararre na yi miki da sau?i Bintu. Ko dai kin manta irin makirce-makirce da kissa da tuggun da kika yi ta haWawa a zamantakewarmu ne? Kai... Ni kam me za'ayi da mace irinki Bintu? Iyaye da ?an'uwana na jini kika so raba ni da su fa... Shi yasa a kullum ba na gajiya da godewa Allah da yasa idanuna suka buWe tun lokaci bai ?ure min ba... Allah na gode maka..."

"Ha...fiz..."
Ta katse shi da rawar murya, jin da tayi zuciyarta na neman bugawa saboda zafin ba?a?en maganganun da yake yayyaSa mata. Maganganun da ita da kanta ta san gaskiya yake faWa, gaskiya mai masifar Waci da ma?a?i a zuciya.
"Na sani, ni da kaina na aikata kura-kurai masu yawa a baya... Kura-kurai masu girma da gyaruwarsu sai a hankali, domin ba a taSa Sari a kwashe duka. Me yasa a yanzu da nake neman tuba baza ka bani dama ta biyu ba? Sannan abu Waya da nake so ka sani shi ne, sam ban zo Ofishinka don ?ara fama gyambon da tun asali ni ce sanadiyyar samuwarshi ba. Alfarmarka nake nema Hafiz, dama ta biyu kawai nake bu?ata a gurinka... Kwanaki uku da suka wuce na je Fa?o na nemi yafiyarsu Innaye, kuma duk sun yafe min ba tare da wani tashin tashina ba. Shekaran jiya na je gidan Zulai, ita ma na ro?e ta gafara, kuma ta tabbatar min ta yafe min har ma munyi musayar lambar waya a tsakaninmu. Me yasa baza ka kwaikwaya daga halin Iyaye da ?an'uwanka ba...?"

"Saboda ni Win ba su bane da kika saba raina ma hankali kina buga su kamar Tamaula. Look Bintu, salo-salo na munafurcinki kin daWe kina buWa min shafi bayan shafi, ko wannan neman yafiyar da kika yi na tabbata wani salon munafurcin ne. Bari in sake maimaita miki, idanuna ya daWe da washewa a kanki Bintu, yanzu kar nake kallonki. Ki tattara kayanki ki koma Fa?o idan har kina mu cigaba da zama... idan ba haka ba kuwa sai in ce Allah raka taki gona..."

"Me kake nufi Hafiz?"
Ta tambaye shi da maWaukakin tashin hankali a fuskarta.

Sai da yayi taku biyu zuwa gabanta sannan ya ce
"Ina nufin in dai baza ki koma Fa?o ki zauna da su Innaye ba, ni kuma bazan cigaba da ri?e igiyar auren ki ba. Zan sake baki takardarki ki je can ki sami wani mijin da bashi da iyaye ?auyawa..."

"Anya kana so na kuwa Hafiz?"
Ta jefa mishi tambayar ?irjinta na bugawa, domin bata san irin amsar da zai fito daga bakinsa ba.

"A da kenan Bintu. A yanzu kuwa ko rantsuwa nayi miki babu kaffara Kareema ta daWe da mamaye filin da a baya mallakinki ne... Idan akwai wata ?ar kimarki da ta rage a idanuna bai wuce ta kasancewarki uwar Aadil ba, a bayan haka kuwa na rantse da Allah kallonki ma ba ?aramin ba?in ciki da takaici yake saka ni ba."

Da saurin gaske Bintu ta lalubi kujerar da ke bayanta ta zauna, jin da tayi lokaci Waya wani hajijiya mai ?arfi yana neman kifar da ita a ?asa.
"Na gode Hafiz. Na gode ?warai."
Tayi maganar da muryarta da lokaci Waya ya sha?e, ya shige can ciki kamar wacce aka ma?urewa ma?ogwaro.

Dafe kanta da taji yana bugawa da ?arfi kamar ana sara mata guduma tayi, idanunta a lumshe. A zuciyarta take ta janyo duk irin addu'ar da ya zo mata. Ta daWe a cikin wannan halin sannan da?yar ta Wan dawo cikin nutsuwarta, ta sake buWe baki da?yar ta ce
"Allah ya sani ni har yanzu ina son ka Hafiz... Sannan in da ace ina da tabbacin kana so na, zama a Fa?o tare da su Innaye ba komai bane, ko babu komai zan ?ara gogewa da wani sabon ilimi na zamantakewar rayuwar duniya wanda da can ban san shi ba."
Ta Wanyi shiru tana mayar da numfashi a wahalarce, da?i?u sittin ta Wauka sannan ta cigaba da magana
"A fahimtata da zaman aure yarjejeniya ta amincewar zamantakewa tsakanin mutane biyu, ba nau'i ne na cutarwa ko bautarwa ba. Kuma ko wane aure akwai wasu muhimman turaku da suke ri?e da wannan aure, So, ?auna, Yarda, amincewa haWe da yima juna uzuri su suke taka muhimmiyar rawa gurin jan ragamar ko wane zamantakewar aure zuwa tudun mun tsira. Daga abinda na fahimta a kalamanka na yanzu Hafiz ba ka so na, sannan kuma ka daWe da yanke min tsammanin zan shiryu, don haka da waWannan dalilan ina ga babu amfanin cigaba da zaman aure a tsakaninmu..."
Tana zuwa nan a maganganunta ta fara shesshe?ar kuka da ?arfi, amma duk da haka bata tsagaita ba sai da ta kai aya
"Allah ya sani ina daga cikin matan da matsananciyar soyayya ta yi kaWan ta rufe min idanu inyi zaman kwantai da wula?anci a gurin Wa namiji... Bazan yi zaman cutuwa sannan inyi ha?urin da babu lada in hallaka ba, sannan kai ma in halakar da kai, saboda rashin ?auna zai sa baza ka iya sauke nauyin ha??ina da ya rataya a wuyarka ba. Don haka, ina ro?on mu kawo ?arshen wannan tafiyar Hafiz... Allah ya sada mu da alkhairinsa."

Da saurin gaske ta du?un?une gogaggen hijabinta ta cusa a baki saboda kukanta da ya ?ara ?arfi, sannan ta fice daga Ofis Win da sassarfa tana sharSen hawaye.

In da Allah ya taimaketa shi ne da direba ta je Ofis Win, ba don haka ba lallai da sai dai ta Wauki shatar Taxi ya mayar da ita gida, domin a irin wannan halin da take ciki sam baza ta iya tu?a mota ba.

"Baba Mamuda gidan Aunty Halima za ka kaini."
Ta faWi haka ga direba bayan sunyi nisa a kan hanyarsu ta komawa gida.

"To Hajiya Likita. An gama, Allah ya huci zuciyarki ya yaye miki abinda yake damunki."
Direban ya faWa da murya mai bayyana damuwa da halin da Bintu ke ciki.





******


"Anya Bintu kin yi tunani mai zurfi kuwa? Kina ganin rabuwarki da Hafiz shi ne zai zama maslaha a rayuwarki?"
Aunty Sadiya ta faWi haka da murya mai bayyana damuwa sosai, bayan ta gama sauraren duk irin bayanin da Bintu tayi mata cikin kuka da tashin hankali.

Ita kanta ta shiga cikin Wimuwa. Kuma ta sani duk irin abubuwan da suka faru a zamantakewar auren Bintu laifin Bintun ne. Amma bata yi tsammanin bayan sakkowa da Bintu tayi ta gane kuskurenta har tayi aniyar gyarawa Hafiz zai cigaba da ri?e laifukanta a zuciyarsa ba.

"Kiyi ha?uri Aunty... In sha Allah hakan shi ne mafi alkhairi."
Bintu ta amsa da sha?a??iyar murya, ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
gwanin ban tausayi. Idanunta sun kumbura sun yi tulu-tulu saboda kukan da ta Wauki tsawon lokaci tana yi.

"Shi kenan Bintu. Za mu cigaba da taya ki addu'a Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi. Amma dai na so ace kin ?ara zurfafa tunani. Mata da yawa Bintu suna rayuwa ne a gidan mazajensu ba tare da wata aba wai ita soyayya ba. Idan za ki tara mata Wari, ko wacce za ki ji dalili ne mabanbanta ke zaune da ita a gidan mijinta ba don tana jin wani mashahurin daWi ba..."

"Bazan iya ba Aunty."
Bintu ta katse ta da sauri.
"Allah yana gani bazan iya irin wannan zaman ba. Da dai ace in ?are rayuwata a irin wannan zaman da ?arara miji ya nuna min kuma ya faWa min ba ya so na, na rantse da Allah gara in ha?ura da auren gaba Waya. Ban ce bazan iya ha?uri a cikin rayuwar aure ba, ha?urin da na san ina cutuwa ne gaskiya bazan taSa iyawa ba..."

"To Aadil fa? Yanzu ko rayuwar Waya-Wayan Wan da Allah ya baki bai isa yasa ki ha?uri da Ubansa ba Bintu? Malam bahaushe fa cewa ya yi duk bakin da ya furta so a farko, ko daga baya ya zo ya furta ?i Sacin rai ne yasa shi faWin haka. Ki tausaya ma rayuwar yaron ki."

"Uhmmm! Aunty kenan! Ni fa duk wata shaci-faWi ta Malam bahaushe ba da ni za'ayi ta ba. Ina duba maslahar rayuwata ne, idan da rabon mu sake zama can gaba wata ?ila mu haWu, amma a yanzu kam na rantse da Allah ko son Hafiz zai kashe ni bazan koma gidansa ba.
Batun Aadil kuma yara da yawa suna rayuwa ba tare da mahaifiyarsu ba, kuma Allah yana raya su cikin aminci. In da ace mutuwa nayi kuma fa?"

"Shi kenan. Tunda har kin rantse. Yanzu sai ki tashi mu tafi can gida gurin Daddy, tunda dai ta inda aka hau ta nan ake sauka."


*******


Ko da suka je ma Daddy

51 / 53