Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 53

27K to 30K   out of 157.3K words

ji ba gani sam ta ?i tsayawa ta saurare shi shi ne abinda ya ?ara Waga hankalinsa zuwa ?ololuwa. Afujajan ya mi?e tsaye ya fice daga cikin Wakin, can jikin famfon da ke tsakar gurin ya hangi Zulaikha zaune ta tasa kayan wankinsu a gaba tana zaune dirshan a ?asa tana matsar ?wallah.

Kaman zararre, ya ?arasa gurinta da sauri.
"Kukan me kike yi?"
Ya tambayeta cikin tsawa.

A tsorace ta Waga idanu ta kalle shi. Maimakon ta amsa tambayar da yayi mata kuma kamar haWin baki itama sai ta fashe mishi da ?a??arfan kuka.

"Gida kike son tafiya?"
Ya sake jefa mata tambayar hankalinsa a tashe.

Da saurin gaske ta dinga gyaWa mishi kai alamar eh kamar ?aramar yarinya, ta kasa buWe baki ta amsa mishi saboda kuka.

"Ki haWa kayayyakinku bari inje in dawo mu tafi yanzu."
Ya sake faWa hankalinsa a dagule.

Yana kallonta ta kwashi kayan wankin nasu da ko ji?awa bata yi ba ta wuce cikin Wakin da sassarfa jikinta na rawa.

Jikinsa a sanyaye yaja ?afafunsa da yake ji kamar baza su iya Waukarsa ba ya wuce zuwa Sangarensu.

A yadda ya tsara da farko, ?arasa shiryawa zaiyi yaje gurin aiki ya Wan rage wasu ayyukan kafin yazo su tafi. Amma da zaran ya tuna irin kukan da ya bar Innaye tana yi, sai hankalinsa ya ?ara Wugunzuma.

Ya rasa abinda ke mishi dad'i, a kasalance ya k'arasa shiryawa ya fice daga falon ya nufi can tsakar gidan ya sanar da direba ya canja motar da za su fita da ita. Ba Ofis za su ba can ?auye za su je.

"?auye a yanzu Oga? Allah yasa dai lafiya?"
Direba ya jefa mishi tambayar fuskarshi na bayyana damuwa.

"Lafiya ?alau. Innaye ce ta matsa lallai a mayar da ita gida yau."
Ya amsa mishi yana cigaba da tafiya zuwa Sangaren Innaye, wayarsa na hannunsa yana daddanawa don kiran Bintu ya sanar da ita abinda yake faruwa.

Kamar ta mi?e ta taka rawa take ji don tsananin farin cikin da ya sauka a zuciyarta lokaci Waya daga jin bayanin da yake mata. Amma da yake ta ?ware a nuna yanayin da ba haka bane a zuciyarta sai ta kwantar da muryarta sosai, cikin yanayin damuwa da jimami ta ce mishi
"Sweetheart ?auye kuma? To ya bayanin sauran alluranta da suka rage na kwana biyu? Kuma ka san halin mutanen naka dai da rashin kulawa, idan suka tafi da magungunan nan ba lallai su kiyaye ba ta akan lokaci ba. Kar ciwon ya dawo baya fa..."

"To ya zanyi mata Bintu?"
Ya katse ta da kalar tasa damuwar da yake ji kamar ya Wora hannu aka yaita rusa ihu.
"Duk irin kalaman da ya kamata in yi amfani da su gurin yi mata bayani sam ta ma ?i saurarata. Ni babban damuwata ma Wallahi ba ragowar allurai da magungunan bane, ki tuna yadda na Wauko Innaye daga gida.

Ko da dai ba ta da lafiya amma ke kin san yanayin jin jikinta ko kaWan bai kai yanzu ba. Ki duba yadda ta rame ta lalace, raunin tsufa ya bayyana ?arara a jikinta. Ko tafiya ba ta iya yi ita kaWai fa sai an ri?e ta, saboda Allah idan na mayar da ita a irin wannan halin da take ciki me mutanen gida za su ce a kaina?"

Irin yadda yake jan numfashi yana saukewa a zafafe cikin damuwa shi ne abinda ya Wan so Waga mata hankali. Alal ha?i?a a yanzu kam shi ya bata tausayi ba halin da Innaye ke ciki ba. Don haka tayi shiru tana tunanin da zai samar mishi da mafita, duk da dai ba ta ?aunar cigaba da zaman su Innaye a gidanta saboda damuwarsa kaWai yasa ta cewa
"To ko dai za ka mata dabara ne kai tafiyarka Ofis ne ka ?yale su a gida? Idan bata ganka ba ai dole ta ha?ura da zancen tafiya gida ayau Win. In yaso idan zan dawo gida sai in taho mata da wasu magungunan saSanin wanda take sha, duk da dai ba haka na so ba."

Da yake wayar da yake yi a ?ofar shiga Sangaren da Innaye take ne, ya buWe baki zai ba Bintu amsa kawai sai ganin Zulaikha yayi ta fito tana ri?e da Innaye, sun shirya tsaf! Da alamun gajiya sukai da jiransa suka fito.

Ransa a Sace ya galla ma Auta harara kafin yayi ma Bintu sallama a gaggauce, ba tare da ya bata amsa kan shawarar da ta bashi ba.
"Me yasa kika fito da ita ba tare da nayi miki umarni ba? Ko an faWa miki na gama shirye-shiryen tafiya ne...?"

"Yaya ba fa laifi na bane. Tun Wazu ita ta matsa min in fito da ita, da nace mata baka shirya ba sai cewa tayi mu fito ko a motan haya ne mu tafi. Ta rantse ta sake rantsewa da Allah ita kam ba ta ?ara kwana a gidannan."

Sau uku yana buWe baki da nufin yin magana amma ya rasa ta cewa. Sai kawai ya juya zuwa tsakar gidan suka bi bayanshi, shi kaWai yake ta ?wafa yana jan tsaki saboda tsananin damuwa da ?uncin zuciya.

Direba yana kan wanke motar da za suyi tafiya a cikinta ganin fitowar su Innaye a dole ya dakata. Yadda aka tarairayota yasa da saurin gaske ya kai hannu zai buWe ?ofar baya sai Hafiz ya riga shi buWewa.

Da sassarfa ya ?arasa ya karSe ta a hannun Zulaikha ya ?arasa da ita cikin mota ya zaunar da ita. Idanunshi akan Zulaikha har lokacin bai saki fuskarsa ba ya ce
"Shiga kusa da ita ki zauna, idan ta gaji da zama ki kwantar da ita a jikinki."

"To Yaya. Amma ban fito da kayanmu ba, bari in je in kwaso..."

Da tsawa sosai a muryarsa ya katse ta tun kafin ta aje numfashin maganarta.
"Dallah shiga cikin mota zan je in kwaso muku. Kuma ina fatan kin haWa har da sauran magungunanta da alluran da suka rage?"

"Eh."
Ta amsa da sanyin murya. A zuciyarta kuma cewa tayi
'Bala?a??e, ka ci kanka kasha ba?in ruwa. Gidanka ne dai ko kana so ko ba ka so yau za mu bar shi.'
Da sauri ta shige cikin mota ganin har lokacin bai daina aika mata da wani fusataccen kallo ba.

Kayansu gaba Waya a ghana most go Waya ne. Don tabbatar da bata manta da magunguna da alluran Innaye ba sai da ya buWe jakar ya gansu sannan ya maida jakar ya rufe ya Wauka zuwa mota.

Saboda irin jan ?afar da yai tayi za su tafi baza su tafi ba, ya shiga cikin Sangarensu ya ?i fitowa akan lokaci kuma shi ba wani takamaimai abu yake yi ba basu bar gidan ba sai ?arfe goma da rabi na safe. Tun da Hafiz yayi aure, zuwanshi ?auye ya kwana Waya bai fi sau bakwai ba.

Duk sa'adda za su tafi asubanci suke bugawa yadda za su isa da wuri, ya gama duk abinda zaiyi zuwa la'asar su Wauko hanyar komawa Abuja, komai dare a gida yake kwana.

Ko a yanzu direba ya zaci irin waWancan tafiyoyin da suka saba yi ne na yini Waya. Don haka ya ?ure manejin mota yana ta zabga gudu kamar masu shirin barin ?asar.

Ko da suka isa Kaduna baiyi niyyar tsayawa ba sai da Hafiz ya ce mishi ya tsaya ya sai ma su Innaye abinci, a lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar azahar a wasu masallatai.

Da yake ko bayan an isa Kaduna tafiya ce mi?a??iya zuwa ?auyen Fa?o, ga kuma tsiya irinta ?arfen nasara da ba ta da tabbas. Bayan tsayawa gyara da suka yi a garin Kujama basu isa Fa?o ba sai La'asar.

Sun isa ?ofar gidansu Innaye daidai lokacin da aka fito sallar la'asar a babban masallacin da yake ?ofar gidan.
'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un'
Hafiz ya faWa a zuciyarsa hankalinsa a tashe.

Ko kafin ya waiga yayi ma Zulaikha umarnin ta dakata da buWe ?ofar sai mazan da suke fitowa daga masallaci sun ragu har ta riga ta buWe ?ofar Sangarenta, ta zura ?afafunta zuwa waje, fuskarta cike da matsanancin farin ciki na ganinta a ?ofar gidansu.

Kafin ma ya kira sunanta har ta fita waje. Bai ?ara tabbatar da rashin hankali da wautar Zulai ba sai da yaji ta buWe murya tana ?wala ma mahaifinsu da yake tsaye suna magana da Ladan kira.

"Baffah... Mun dawo."
Hakan bai ishe ta ba sai da ta ?ara da
"Zo ka ga Innaye ba ta da lafiya sosai."

Wannan maganar da ta faWa shi ya dawo da hankalin gaba Waya mazan da suke tsaye a gurin zuwa kan motar Hafiz. Kun san mutanen ?auye da kara, Wuuuuu kusan gaba Waya suka yo gurin motar.

Babu abinda ke fita a bakunansu sai
"Assha! Subhanallahi! Hajiya Rahina jikin ya motsa kenan."

Tsananin damuwa da Sacin ran abinda Zulaikha ta aikata yasa idanun Hafiz suka cicciko da hawaye. Ba shi da yadda ya iya, haka nan ya buWe ?ofar Sangarensa ya fita waje ya tarbi mahaifinsa da sauran mutanen gurin da suka rufu a kanshi suna mishi jajen ya mai jiki? Haka nan yake ta amsa musu cikin rashin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Bai san Yaya aka yi ba yana cikin mazan nan sai ganin matan gidansu abokan zaman Innaye yayi sun fito, suna sanye da zumbula zumbulan hijabai, biye a bayansu Zulai ce tana musu jagora zuwa gurin motar Sangaren da Innaye ke kwance.

Kafin ya ce wani abu har Zulai ta buWe musu ?ofar, su kuma suka tarairayo Innaye da gajiyar zaman mota da rashin ?arfin jikin da take fama da shi ya ?ara ramar da ita. Suna ri?e da ita sannu a hankali suke amsa gaisuwar mazan da suke mata ya jiki har suka shigar da ita cikin gidan.
Kamar wutar daji, haka zancen gaggarumin rashin lafiyar da Innaye ta dawo da shi ya fantsama a ?auyen Fako cikin kankanin lokaci.

Suna tsaye a ?ofar gida, bayan watsewar maza masu jajantawa yana yi ma mahaifinsu da yan'uwansa biyu ?arin bayanin ciwon Innaye bazai iya ?ididdige yawan matan da suka shiga cikin gidan duba jikin Innaye ba.

Kun san ?auye da kara da mayar da al'amarin wani nasu. Balle kuma Innaye da ta kasance mace ta mutane, kowa nata ne. DaWin gushi kuma macece da hannuwanta yake a buWe, sam abin hannunta bai rufe mata idanu ba.

Hatta kishiyoyinta biyu in dai batu na adalci da gaskiya za su fad'a ba ?aramin daWin zama da ita suke ji ba. Da gangar baza a zage ta ba sai dai son zuciya ko zalunci da ba'a raba zukatanmu na ?a?an Adam da shi.

Duk nisan da gidajen Yayyinshi suke da shi cikin ?an?anin lokaci har labarin yadda ya dawo da mahaifiyarsu ya iske su a gidajensu. Ko kafin ya saSulewa tambayoyin mahaifinsu ya shiga cikin gidan har yayyenshi sun iso.

Shi kanshi idanunshi duk sun faWa ciki saboda fargaba, gajiya, da tashin hankali. Idan ya kalli direbanshi sai yaji ya bashi tausayi, saboda yau ko arzikin ruwa da furar da ake tarbarshi da shi bai samu ba.

Da?yar ya ?waci kanshi a hannun mahaifinshi da ?an'uwan Innaye da suke ta tuhumarshi yadda aka haihu a ragaya ya shige cikin gidan, lokacin ?arfe biyar da minti goma na yamma.

Ganin yadda Yayyenshi suka tasa Innaye da aka yi mata wanka tana kwance akan darduma a gaba suna ta sharSan kuka, ita kuma Zulaikha tana gefe cikin nata kukan take ba su labarin mafarin ciwon Innaye yasa idanunshi rufewa, bai san lokacin da ya nufe ta gadan-gadan zai rufe ta da duka yana surfa mata zagi ba.

A guje, kuma a tsorace Zulaikha ta daka tsalle ta ru?un?ume Aunty Rakiya sannan ta ?wallah ihu tana karaWin a ceceta zai kashe ta.

"Hafizu me zan gani haka?"
Ta jefa mishi tambayar tana bin shi da wani irin kallo mai nuna tozarci ?arara. Kafin ya amsa ta cigaba da cewa
"Me tayi maka za ka doke ta? Kawai daga tana faWa mana yadda aka yi mahaifiyarmu ta kamu da wannan gagarumin ciwon shi ne za ka duke ta don zalunci da son zuciya? Ashe daman ?arya kake faWa mana cikin kwanakinnan idan muka kira ka muna tambayar ya jikin Innaye? To me kake nufi? Iye? Na ce me kake nufi Hafizu? Ko so kayi sai ta mutu sannan ka sanar mana da...?"

"Kul! Kul!! Kul Rakiya... A kul!!! Kar in sake jin irin wannan mummunar maganar na fita daga bakinki."
Mahaifinsu da shigarsa cikin Wakin kenan ya tarar da ita tana wannan faWan ya katse da tsawatarwa.

Guri ya nema kan kujera ya zauna idanunshi akan Innaye. Har yanzu gani yake kamar idanunshi ne ke mishi gizo, ya kasa gasgata wai Innaye ce tayi irin wannan rama da tsofewar a cikin kwanaki takwas kacal da barinta garin Fa?o. In banda yana da tabbacin duk lalacewar zamani babu ta yadda za'ayi a haWa baki da Wa a cutar da uwa mafi soyuwa a zuciyarsa da tabbas zai ce da haWin bakin Hafizu aka ?ara kwararraSa jikin Innaye sanadiyyar magunguna da allurai.

Amma kuma da ya tuna komai yana faruwa ne da ikon mahaliccin sammai da ?assai. Sannan wasu cutukan ba sa tashi a jikin mutum sai an sha wasu magungunan, kuma haka kawai idan Allah ya tashi gwada ikonsa ba cikin kwanaki huWu ba, a cikin yini Waya ma yana iya jarabtar bawa da cutar da ta ninka wannan. Sai yayi saurin kore zargin magunguna da alluran da Bintu take ba Innaye har ma yayi istigfari.

Kawar da idanunsa yayi daga kan Innaye ganin yadda tun shigarsa cikin Wakin ?ananun hawaye ke ta tsattsafa a kwarmin idanuwanta ta kasa cewa komai. Ko tunanin me take yi a zuciyarta? Sanin gaibu sai Allah.

Umarnin zama yayi ma Hafiz da tun maganganun da Yayarsa Rakiya ta caccaSa masa yake tsaye kamar mutum-mutumi. Kallo Waya za'a mishi a hango gagarumin Sacin rai da tashin hankali a tare da shi.
"Hafizu ne mi guri ka zauna."
Ya sake umartarshi a karo na biyu cikin Waga murya, ganin umarnin farko da yayi mishi hankalin Hafiz Win yayi nisa cikin tunani har bai san yana mishi magana.

Daga nan inda yake tsaye, kawai ya sulale zuwa ?asa ya zauna ba tare da damuwa da inda ya zauna ko kuma yanayin gurin da ya zauna ba.

Nasiha mai ratsa jiki sosai mahaifinsu yayi musu, ?arara ya nusar da su muhimmancin yarda da ?addara mai kyau da mara kyau.
"Cuta, mutuwa, rayuwa, abubuwa ne da babu wani bawa da ya isa ya saka ma wani bawa su sanadiyyar magani ko wani allura face sai da yarjewar Ubangiji. Don haka daga yanzu, kar in ?ara ji Waya daga cikinku ta ce sanadin magani da allurar da matar Hafizu tayi ma Rahina (Asalin sunan Innaye) ne yasa ciwo suka tasar mata haka. Ina fatan kun fahimce ni?"
Ya ?arasa maganar da Waga murya.

"Eh! Mun ji Baffa. Za mu kiyaye in Allah ya yarda."
Gaba Waya yayyen suka haWa baki gurin faWin haka.

"Ke Zulai?"
Ya kira Auta da tsawa-tsawa.

A tsorace ta amsa tana sake ma?ure jikinta a na Yayarta Rakiya.

"Daga yanzu, kar in sake ji kin ba wani ko wata labarin magani da alluran da aka yi ma Rahina. Kina ji na?"

"Kayi ha?uri Baffa. Bazan sake ba."
Ta amsa a tsorace bakinta na rawa.

"Sannan ku kuma ko da wasa kar ku kuskura ku ce za ku bari wani saSani ya gitta tsakaninku da Wan'uwanku don Wan wannan abun da ya faru. Idan za ku yima lamarin duba da idanun basira, tsoro da fargaban irin tashin hankalin da za mu shiga idan muka ji labarin halin da take ciki shi yasa shi Soye mana komai. Wannan dalilin kaWai ya isa yasa muyi mishi uzuri. Kai Hafizu a matsayinka na ?arami ba Yayyinka ha?uri."

Cikin ?an-?an da kai, da nuna nadama a fili ya ba su ha?uri kamar yadda Baffa ya umarce shi. Tare da al?awarin abu makamancin wannan bazai sake faruwa ya tafka irin wannan kuskuren na Soye musu ba.

Cike da ?auna suka karSi tubansa. Yaya Rakiya da ta jefe shi da munanan kalamai ita ma ta bashi ha?uri.

Cikin kankanin lokaci suka fahimci junansu, bayan mahaifinsu ya kara janyo hankalinsu akan kar su kuskura ko da wasa su bari wannan abu da ya faru yasa su canja ma Bintu fuska a matsayinta na matar kaninsu.
"Na tabbata irin k'aunar da yarinyar nan take yi ma Hafizu bazai taba bari ta iya cutar da mahaifiyarsa da gangar ba. Kar ku bari shaid'an la'ananne yayi galaba a zukatanku kun ji ko?"

"To Baffa! Allah ya kara lafiya da nisan kwana."

Kiran sallar magriba yasa Baffa da Hafiz ficewa daga d'akin. Su ma matan fita suka yi waje don d'auro alwala.

Kamar 'yar karamar yarinya haka aka tasa Innaye da tarairaya da kulawa ta ko wane 'bangare, ba daga 'bangaren yaranta da mijinta ba, ba daga 'bangaren kishiyoyi, danginta da abokan arzikinta ba. Haka aka tara mata kwanonin abinci fiye da goma a gabanta.

Amma saboda yanayin bakinta da babu dad'i dak'yar ta iya tsakurar tuwon dawa miyan gatsiga da aka aiko da shi daga gidan k'aninta Iro. A k'arshe dai shayi aka had'a mata mai kauri shi ma kad'an tasha ta ce ta k'oshi.

Farin cikin tsintar kanta a cikin iyalanta kaWai ya taka muhimmiyar rawa gurin dakushe rashin ?arfin da take ji a jikinta. Duk da bata furta ba, amma sosai yanayin fuskarta ke ?o?arin nunawa har Auta ta fahimci haka.

"Innaye? Ko dai gobe da safe mu bi Yaya mu sake komawa Habuja ne?"
Auta ta tambayeta cikin tsokana ganin yadda akai akai take bin ?a?anta da kallo tana ?o?arin sakin murmushi.

A yanzu ma murmushin ta ?ara yi, bata ce komai ba sai da?uwa da ta Waga yatsunta tayi ma Auta. Su kuma sauran ?a?an nata suka yi dariya.

A daidai lokacin Hafiz yayi sallama ya shiga Wakin, hannunsa ri?e da jakar kayan su Innaye. A bayansa kuma direbansa ne Wauke da katan Win ruwan gora guda uku, bayan ya gaishe da mazauna cikin Wakin ya ?ara yi musu ya

10 / 53